Categories
LUK

LUK 18

Misali na wadda Mijinta Ya Mutu da Alƙali

1 Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu’a, kada kuma su karai.

2 Ya ce, “A wani gari an yi wani alƙali marar tsoron Allah, marar kula da mutane.

3 A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gābana.’

4 Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane,

5 amma saboda gwauruwar nan ta dame ni, sai in bi mata hakkinta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.’ ”

6 Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya faɗa!

7 Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?

8 Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa’ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”

Misali na Bafarisiye da Mai Karɓar Haraji

9 Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,

10 “Waɗansu mutum biyu suka shiga Haikali yin addu’a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji.

11 Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu’a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.

12 Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka.’

13 Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’

14 Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”

Yesu Ya sa wa ‘Yan Yara Albarka

15 Waɗansu suka kawo masa ‘yan yaransu domin ya taɓa su. Ganin haka sai almajiransa suka kwaɓe su.

16 Amma Yesu ya kira ‘yan yara wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.

17 Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na’am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”

Shugaban Jama’a Mai Arziki

18 Wani shugaban jama’a ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”

19 Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci, sai Allah kaɗai.

20 Kā dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi zina. Kada ka yi kisankai. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

21 Sai ya ce, “Ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.”

22 Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”

23 Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske.

24 Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!

25 Ai, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”

26 Waɗanda suka ji wannan magana suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”

27 Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”

28 Sai Bitrus ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka.”

29 Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko ‘yan’uwansa, ko iyayensa, ko kuma ‘ya’yansa, saboda Mulkin Allah,

30 sa’an nan ya kasa samun ninkinsu mai yawa a yanzu, a Lahira kuma ya sami rai madawwami.”

Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi

31 Sai ya keɓe sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi, za mu Urushalima, duk abin da yake rubuce kuma game da Ɗan Mutum, ta hannun annabawa zai tabbata.

32 Gama za a bāshe shi ga al’ummai, a yi masa ba’a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau.

33 Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.”

34 Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.

Warkar da Makaho Mai Bara a kusa da Yariko

35 Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara.

36 Da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko mene ne.

37 Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne yake wucewa.”

38 Sai ya ɗaga murya ya ce, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

39 Sai waɗanda suke gaba suka kwaɓe shi ya yi shiru. Amma ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”

40 Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, ya tambaye shi,

41 “Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani!”

42 Yesu ya ce masa, “Karɓi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”

43 Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama’a suka yabi Allah.

Categories
LUK

LUK 19

Yesu da Zakka

1 Yesu ya shiga Yariko. Yana ratsa garin,

2 sai wani mutum mai suna Zakka, babba ne a cikin masu karɓar haraji, mai arziki ne kuma,

3 ya nemi ganin ko wane ne Yesu, amma ya kasa ganinsa saboda taro, don shi gajere ne.

4 Sai ya yi gaba a guje, ya hau wani durumi don ya gan shi, don Yesu ta nan zai bi.

5 Da Yesu ya iso wurin, ya ɗaga kai ya ce masa, “Zakka, yi maza ka sauko, domin yau lalle a gidanka zan sauka.”

6 Sai ya yi hanzari ya sauko, ya karɓe shi da murna.

7 Da suka ga haka, duk suka yi ta gunaguni, suka ce, “A! A gidan mai zunubi dai ya sauka!”

8 Sai Zakka ya miƙe, ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ka ga, rabin mallakata zan ba gajiyayyu. Kowa na zalunta kuwa, zan mayar masa da ninki huɗu.”

9 Yesu ya ce masa, “Yau kam, ceto ya sauka a gidan nan, tun da yake shi ma ɗan Ibrahim ne.

10 Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”

Misali na Fam Goma

11 Da suka ji abubuwan nan, Yesu ya ci gaba da gaya musu wani misali, gama yana kusa da Urushalima, suna kuma tsammani Mulkin Allah zai bayyana nan da nan.

12 Sai ya ce, “Wani mutum mai asali ya tafi wata ƙasa mai nisa neman sarauta yă dawo.

13 Sai ya kira bayinsa goma, ya ba su fam guda guda, ya kuma ce musu, ‘Ku yi ta jujjuya su har in dawo.’

14 Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu.

15 Ana nan, da ya samo sarautar ya dawo, sai ya yi umarni a kirawo bayin nan da ya bai wa kuɗin, ya ga ribar da suka ci a wajen jujjuyawar.

16 Sai na farko ya zo gabansa, ya ce, ‘Ya ubangiji, fam ɗinka ya jawo fam goma.’

17 Sai shi kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.’

18 Sai na biyun ya zo, ya ce, ‘Ya ubangida, fam ɗinka ya jawo fam biyar.’

19 Shi kuma ya ce masa, ‘Kai ma na ba ka mulkin gari biyar.’

20 Wani kuma ya zo, ya ce, ‘Ya ubangiji, ga fam ɗinka nan! Dā ma a mayani na ƙulle shi, na ajiye.

21 Domin ina tsoronka, don kai mutum ne mai tsanani, son banza a gare ka, kakan girbi abin da ba kai ka shuka ba.’

22 Sai ya ce masa ‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari’a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba?

23 To, in haka ne, don me ba ka ajiye kuɗin nawa a banki ba, da dawowata in ƙarɓa, har da riba?”

24 Sai ya ce wa na tsaitsaye a wurin, ‘Ku karɓe fam ɗin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.’

25 Suka ce masa, ‘Ya ubangiji, ai, yana da fam goma.’

26 ‘Ina dai gaya muku, duk mai abu a kan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai a karɓe masa.

27 Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”

Mutanen Urushalima sun Marabci Yesu

28 Da Yesu ya faɗi haka, ya yi gaba zuwa Urushalima.

29 Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu,

30 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wani aholaki a ɗaure, wanda ba a taɓa hawa ba. Ku kwanto shi.

31 Kowa ya tambaye ku, ‘Don me kuke kwance shi?’ ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa.’ ”

32 Sai waɗanda aka aika suka tafi, suka tarar kamar yadda ya faɗa musu.

33 Suna cikin kwance aholakin, masu shi suka ce musu, “Don me kuke kwance aholakin nan?”

34 Sai suka ce, “Ubangiji ne yake bukatarsa.”

35 Sai suka kawo shi wurin Yesu. Da suka shimfiɗa mayafansu a kan aholakin, suka ɗora Yesu.

36 Yana cikin tafiya, sai mutane suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya.

37 Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu’ujizan da suka gani.

38 Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!”

39 Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce masa, “Malam, ka kwaɓi almajiranka mana!”

40 Ya amsa ya ce, “Ina dai gaya muku, ko waɗannan sun yi shiru, to, duwatsu ma sai su ɗauki sowa.”

41 Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka,

42 ya ce, “Da ma a ce a yanzu kun san abubuwan da suke kawo salama. Amma ga shi, a yanzu a ɓoye suke a gare ku.

43 Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,

44 su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan’uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”

Yesu Ya Tsabtace Haikali

45 Sai ya shiga Haikali, ya fara korar masu sayarwa,

46 ya ce musu, “Ai, a rubuce yake cewa, ‘Ɗakina zai kasance ɗakin addu’a.’ Amma ku kun maishe shi kogon ‘yan fashi.”

47 Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama’a suka nema su hallaka shi.

48 Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama’a hankali.

Categories
LUK

LUK 20

Ana Shakkar Izinin Yesu

1 Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso,

2 suka ce masa, “Gaya mana da wane izini kake yin abubuwan nan, ko kuwa wa ya ba ka izinin?”

3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku gaya mini,

4 baftismar da Yahaya ya yi, daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?”

5 Sai suka yi muhawwara da juna suka ce, “In mun ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

6 In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ sai duk jama’a su jajjefe mu, don sun tabbata Yahaya annabi ne.”

7 Sai suka amsa masa, suka ce, ba su san daga inda take ba.

8 Yesu ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”

Misali na Manoman da suka Yi Ijarar Garkar Inabi

9 Sai ya shiga ba jama’a misalin nan, ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya ba waɗansu manoma ijararta, ya kuma tafi wata ƙasa, ya daɗe.

10 Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa a gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dūka, suka kore shi hannu wofi.

11 Ya kuma aiki wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka wulakanta shi, suka kore shi hannu wofi.

12 Har wa yau dai ya aiki na uku, shi kuwa suka yi masa rauni, suka kore shi.

13 Sai mai garkar ya ce, ‘Me zan yi ke nan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana. Kila sa ga girmansa.’

14 Amma da manoman suka gan shi, suka yi shawara da juna suka ce, ‘Ai, wannan shi ne magajin. Mu kashe shi mana, gādon ya zama namu.’

15 Sai suka jefa shi a bayan shinge, suka kashe shi. To, me ubangijin garkan nan zai yi da su?

16 Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka, suka ce, “Allah ya sawwaƙe!”

17 Amma ya dube su, ya ce, “Wannan da yake a rubuce fa cewa,

‘Dutsen da magina suka ƙi,

Shi ne ya zama mafificin dutsen gini?’

18 Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje, amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”

Biyan Haraji ga Kaisar

19 Nan take malaman Attaura da manyan firistoci suka nema su kama Yesu, don sun lura a kansu ne ya ba da misalin, amma suna jin tsoron jama’a.

20 Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki ‘yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi.

21 Suka tambaye shi suka ce, “Malam, ai, mun sani maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi.

22 Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?”

23 Shi kuwa ya gane makircinsu, ya ce musu,

24 “Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.”

25 Sai ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

26 Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.

Tambaya a kan Tashin Matattu

27 Sai waɗansu Sadukiyawa suka zo wurinsa (su da suke cewa, ba tashin matattu),

28 suka tambaye shi suka ce, “Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan’uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba ɗa, lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan’uwansa ‘ya’ya.

29 To, an yi waɗansu ‘yan’uwa maza guda bakwai. Na farko ya yi aure, ya mutu bai bar na baya ba.

30 Na biyun,

31 da na ukun kuma suka aure ta. Haka dai, duk bakwai ɗin suka aure ta, suka mutu, ba wanda ya bar ɗa.

32 Daga baya kuma ita matar ta mutu.

33 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai ɗin sun aure ta.”

34 Sai Yesu ya ce musu, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna aurarwa.

35 Amma waɗanda aka ga sun cancanci samun shiga wancan zamani da kuma tashin nan daga matattu, ba za su yi aure ko aurarwa ba.

36 Ba shi yiwuwa su sāke mutuwa, don daidai suke da mala’iku, ‘ya’yan Allah ne kuwa, da yake ‘ya’yan tashin matattu ne.

37 Game da tashin matattu kuwa, ai, Musa ma ya faɗa, a labarin kurmin, inda ya kira Ubangiji, Allahn Ibrahim, da Allahn Ishaku, da Allahn Yakubu.

38 Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba. Don a wurinsa duka rayayyu ne.”

39 Sai waɗansu malaman Attaura suka amsa suka ce, “Malam, ka faɗi daidai.”

40 Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.

Tambaya a kan Ɗan Dawuda

41 Amma ya ce musu, “Ƙaƙa za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?

42 Domin Dawuda da kansa a Zabura ya ce,

‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

“Zauna a damana,

43 Sai na sa ka take maƙiyanka.” ’

44 Dawuda ya ce shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”

Yesu Ya Fallashi Malaman Attaura

45 Ya ce wa almajiransa a gaban dukan jama’a,

46 “Ku yi hankali da malaman Attaura, masu son yawo a cikin manyan riguna, masu so a gaishe su a kasuwa, masu son mafifitan mazaunai a majami’u, da mazaunan alfarma a wurin biki.

47 Su ne masu cin kayan matan da mazansu suka mutu, masu yin doguwar addu’a don ɓad da sawu. Su za a yi wa hukunci mafi tsanani.”

Categories
LUK

LUK 21

Sadaka wadda aka Saka

1 Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu arziki suna saka sadakarsu a baitulmalin Haikali.

2 Sai ya ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta saka rabin kobo biyu a ciki.

3 Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta saka a ciki, ya fi na sauran duka.

4 Domin duk waɗannan sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk kuɗinta na abinci.”

Yesu Ya Faɗi irin Rushewar da za ta Sami Haikali

5 Waɗansu suna zancen Haikali, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan sadaka, sai ya ce,

6 “In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan’uwansa da ba a baje shi ba.”

Alamu da Tsanance-tsanance

7 Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, a yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa’ad da suke shirin aukuwa?”

8 Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su.

9 In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”

10 Sa’an nan ya ce musu, “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki.

11 Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al’amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama.

12 Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami’u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana.

13 Wannan zai zama muku hanyar ba da shaida.

14 Saboda haka, sai ku ƙudura a ranku, a kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba.

15 Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba.

16 Ko da iyayenku ma da ‘yan’uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.

17 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana.

18 Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo.

19 Jurewarku ce za ta fisshe ku.”

Yesu ya Faɗi irin Ribɗewa da za ta Sami Urushalima

20 “Sa’ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa’an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.

21 Sa’an nan waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, su gudu su shiga duwatsu, na birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni.

22 Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.

23 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama’an nan.

24 Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al’ummai duka. Al’ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”

Komowar Ɗan Mutum

25 “Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al’ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa.

26 Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al’amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.

27 A sa’an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.

28 Sa’ad da waɗannan al’amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”

Aya a kan Itacen Ɓaure

29 Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa,

30 da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan.

31 Haka kuma sa’ad da kuka ga waɗannan al’amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato.

32 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku.

33 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

Gargaɗi a Zauna a Faɗake

34 “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.

35 Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa.

36 Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu’a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al’amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”

37 Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.

38 Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su saurare shi.

Categories
LUK

LUK 22

An Ƙulla Shawara gāba da Yesu

1 To, idin abinci marar yisti, wanda ake ce da shi Idin Ƙetarewa, ya gabato.

2 Sai manyan firistoci da malaman Attaura suka yi ta neman yadda za su kashe shi, amma kuwa suna tsoron jama’a.

3 Sai Shaiɗan ya shiga Yahuza, wanda ake kira Iskariyoti, ɗaya daga cikin sha biyun nan.

4 Sai ya tafi ya yi shawara da manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali a kan yadda zai bāshe shi a gare su.

5 Sai suka yi murna, suka kuma yi alkawarin ba shi kuɗi.

6 Shi kuwa ya yarda, ya kuma nemi hanyar bāshe shi a gare su bayan idon jama’a.

Yesu Ya Ci Jibin Ƙetarewa tare da Almajiransa

7 Sai ranar idin abinci marar yisti ta zo, wato, rana da ake yanka ɗan ragon Idin Ƙetarewa.

8 Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.”

9 Suka ce masa, “Ina kake so mu shirya?”

10 Ya ce musu, “Ga shi, da shigarku gari, za ku gamu da wani mutum ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi har zuwa cikin gidan da ya shiga.

11 Ku ce wa maigidan, ‘Malam ya ce, ina masaukin da zai ci Jibin Ƙetarewa da almajiransa?’

12 Shi kuwa zai nuna muku wani babban soron bene mai kaya a shirye. A nan za ku shirya mana.”

13 Sai suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya faɗa musu, suka shirya Jibin Ƙetarewa.

Cin Jibin Ubangiji

14 Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi.

15 Ya ce musu, “Ina so ƙwarai ko dā ma in ci jibin nan na Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wuya.

16 Gama ina gaya muku ba zan ƙara cin sa ba, sai an cika shi a Mulkin Allah.”

17 Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha.

18 Ina gaya muku, daga yanzu, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai Mulkin Allah ya bayyana.”

19 Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.”

20 Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku.

21 Amma ga shi, mai bashe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni.

22 Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!”

23 Sai suka fara tambayar juna ko wane ne a cikinsu zai yi haka.

Mūsū a kan Ko wane ne Babba

24 Sai musu ya tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne babbansu.

25 Sai ya ce musu, “Sarakunan al’ummai sukan nuna musu iko, mahukuntansu kuma sukan nema a ce da su, ‘Mataimakan jama’a.’

26 Amma ku kam ba haka ba. Sai dai wanda yake babba a cikinku yă zama kamar ƙarami, shugaba kuwa yă zama kamar mai hidima.

27 Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abinci ba ne? Ga shi kuwa, ina a cikinku kamar mai hidima.

28 “Ku ne kuka tsaya gare ni a gwaje-gwajen da na sha.

29 Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka, ni ma nake ba ku iko,

30 ku ci ku sha tare da ni a mulkina, ku kuma zauna a kursiyai, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra’ila.

Bitrus zai yi Mūsun Sanin Yesu

31 “Bitrus, ya Bitrus, Shaiɗan ya nemi izinin sheƙe ku kamar alkama, ya kuwa samu.

32 Ni kuwa na yi maka addu’a, kada bangaskiyarka ta kāsa. Kai kuma, bayan da ka juyo, sai ka ƙarfafa ‘yan’uwanka.”

33 Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, a shirye nake in bi ka har cikin kurkuku, ko kuma Lahira.”

34 Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

Jakar Kuɗi, Burgami da Takobi

35 Ya kuma ce musu, “Sa’ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.”

36 Ya ce musu, “Amma a yanzu duk mai jakar kuɗi yă ɗauka, haka kuma mai burgami. Wanda kuwa ba shi da takobi, ya sayar da mayafinsa ya saya.

37 Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa, ‘An lasafta shi a cikin masu laifi.’ Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo.”

38 Sai suka ce, “Ya Ubangiji, ai, ga takuba biyu.” Ya ce musu, “Ya isa.”

Yesu Ya Yi Addu’a a Gatsemani

39 Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.

40 Da ya iso wurin, ya ce musu, “Ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji.”

41 Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu’a.

42 Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi” [

43 Sai wani mala’ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi.

44 Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu’a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]

45 Da ya tashi daga addu’a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki.

46 Sai ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi addu’a, kada ku faɗa ga gwaji.”

An Ba da Yesu, an Kama Shi

47 Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama’a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi.

48 Amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, ashe, da sumba za ka ba da Ɗan Mutum?”

49 Da na kusa da shi suka ga abin da za a yi, suka ce, “Ya Ubangiji, mu yi sara da takuba ne?”

50 Sai ɗayansu ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama.

51 Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi.

52 Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama’a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi?

53 Sa’ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.”

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

54 Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa.

55 Da suka hura wuta a tsakar gida suka zazzauna, Bitrus ma ya zauna a cikinsu.

56 Sai wata baranya ta gan shi zaune a hasken wuta, ta zura masa ido, ta ce, “Ai, mutumin nan ma, tare da shi yake.”

57 Amma ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.”

58 Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma, ai, ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya ce, “Ya mutum, ba haka ba ne.”

59 Bayan wajen sa’a guda sai wani ya nace, ya ce, “Ba shakka mutumin nan ma tare da shi yake, don Bagalile ne.”

60 Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara.

61 Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

62 Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

An Yi wa Yesu Ba’a, an Dūke Shi

63 Sai mutanen da suke riƙe da Yesu suka yi ta masa ba’a, suna dūkansa.

64 Suka ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?”

65 Suka kuma yi ta masa baƙaƙen maganganu masu yawa, suna zaginsa.

Yesu a gaban ‘Yan Majalisa

66 Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama’a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce,

67 “To, in kai ne Almasihu, gaya mana.” Amma ya ce musu, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ba.

68 In kuma na yi muku tambaya, ba za ku mai da jawabi ba.

69 Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.”

70 Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.”

71 Sai suka ce, “Wace shaida kuma za mu nema? Ai, mun ji da kanmu daga bakinsa.”

Categories
LUK

LUK 23

Yesu a gaban Bilatus

1 Duk taronsu sai suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus.

2 Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama’armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.”

3 Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa.”

4 Bilatus ya ce wa manyan firistoci da taro masu yawa, “Ban sami mutumin nan da wani laifi ba.”

5 Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama’a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”

Yesu a gaban Hirudus

6 Da Bilatus ya ji haka, ya tambaya ko mutumin nan Bagalile ne.

7 Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.

8 Da Hirudus ya ga Yesu, ya yi murna ƙwarai, saboda tun da daɗewa yake son ganinsa, don ya riga ya ji labarinsa, yana kuma fata ya ga wata mu’ujiza da Yesu zai yi.

9 Sai ya yi ta masa tambayoyi da yawa, amma bai amsa masa da kome ba.

10 Manyan firistoci da malaman Attaura na nan a tsaitsaye, suna tsananta kai ƙararrakinsa ainun.

11 Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba’a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.

12 A ran nan sai Hirudus da Bilatus suka yi sulhu, don dā abokan gāba ne.

An Hukunta wa Yesu Mutuwa

13 Bilatus ya tara manyan firistoci da shugabanni da kuma jama’a,

14 ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama’a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba.

15 Hirudus ma bai samu ba, don ya komo mana da shi. Ga shi kuwa, bai yi wani abu da ya cancanci kisa ba.

16 Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”[

17 A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.]

18 Amma duk suka ɗauki ihu gaba ɗaya, suna cewa, “A yi da wannan ɗin, a sakar mana Barabbas!”

19 (Barabbas shi ne wani mutum da aka jefa a kurkuku, saboda wani tawayen da aka yi a birni, da kuma kisankai.)

20 Sai Bilatus ya sāke yi musu magana, don yana so ya saki Yesu.

21 Amma suka yi ta ƙwala ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”

22 Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”

23 Amma suka yi ta matsa lamba, suna ɗaga murya, suna cewa a gicciye shi, har surutunsu ya yi rinjaye.

24 Sai Bilatus ya zartar da hukunci a biya musu bukata.

25 Ya kuwa sakar musu wanda suka roƙa, wato, wanda aka jefa a kurkuku a kan laifin tawaye da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu, su yi masa abin da suke so.

An Gicciye Yesu

26 Suna tafiya da Yesu yake nan, sai suka cafke wani, mai suna Saminu Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa gicciye, yă ɗauka ya bi Yesu.

27 Sai taron mutane masu yawan gaske suka bi shi, da waɗansu mata da suke kuka, suke kuma gunji saboda shi.

28 Amma Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma ‘ya’yanku,

29 don lokaci na zuwa da za su ce, ‘Albarka tā tabbata ga matan da suke bakararru, waɗanda ba su taɓa haihuwa ba, waɗanda kuma ba a taɓa shan mamansu ba.’

30 Sa’an nan ne za su fara ce wa manyan duwatsu, ‘Ku faɗo a kanmu,’ su kuma ce da tsaunuka, ‘Ku binne mu.’

31 In fa irin abubuwan nan suna faruwa ga ɗanye, yaya zai zama ga ƙeƙasasshe?”

32 Waɗansu mutum biyu kuma masu laifi, aka kai su a kashe su tare da shi.

33 Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun.

34 Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri’a a kansu.

35 Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba’a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”

36 Soja kuma suka yi masa ba’a, suka matso, suka miƙa masa ruwan tsami,

37 suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!”

38 Sama da shi kuma aka yi wani rubutu cewa, “Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.”

39 Sai ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye ya yi masa baƙar magana ya ce, “Shin, ba kai ne Almasihu ba? To, ceci kanku mana, duk da mu!”

40 Amma ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsoron Allah ma ba ka yi, kai, da yake hukuncinka daidai da nasa?

41 Mu kam, daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikinmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.”

42 Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa’ad da ka shiga sarautarka.”

43 Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, yau ma za ka kasance tare da ni a Firdausi.”

Mutuwar Yesu

44 To, wajen tsakar rana ne kuwa, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

45 Hasken rana ya dushe. Labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu.

46 Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika.

47 Sa’ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!”

48 Sa’ad da duk taro masu yawa, waɗanda suka zo kallo suka ga abin da ya faru, suka koma, suna bugun ƙirjinsu.

49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi, tun daga ƙasar Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.

Jana’izar Yesu

50 To, akwai wani mutum mai suna Yusufu, mutumin Arimatiya, wani garin Yahudawa, shi ɗan majalisa ne, nagari ne, adali kuma.

51 Shi kuwa dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba, yana kuwa sauraron bayyanar Mulkin Allah.

52 Shi ne ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

53 Sai ya sauko da shi, ya sa shi a likkafanin lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe dutse aka yi, wanda ba a taɓa sa kowa ba.

54 Ran nan kuwa ranar shiri ce, Asabar kuma ta doso.

55 Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa.

56 Sai suka koma, suka shirya kayan ƙanshi da man shafawa.

Ran Asabar kuwa, sai suka huta bisa ga umarni.

Categories
LUK

LUK 24

Tashin Yesu daga Matattu

1 A ranar farko ta mako kuwa, da asussuba, suka je wurin kabarin da kayan ƙanshi da suka shirya.

2 Sai suka tarar an mirgine dutsen daga kabarin.

3 Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji ba.

4 Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali.

5 Don tsoro, matan suka sunkuyar da kansu ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman rayayye a cikin matattu?

6 Ai, ba ya nan, ya tashi. Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili

7 cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗan Mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.”

8 Sai suka tuna da maganarsa.

9 Da suka dawo daga kabarin suka shaida wa goma sha ɗayan nan, da kuma duk sauransu, dukan waɗannan abubuwa.

10 To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da suke tare da su, su ne suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa.

11 Su kuwa sai maganan nan ta zama musu kamar zance ne kawai, suka ƙi gaskatawa.

12 Amma Bitrus ya tashi, ya doshi kabarin da gudu. Ya duƙa, ya leƙa a ciki, ya ga likkafanin lilin a ajiye waje ɗaya. Sai ya koma gida yana al’ajabin abin da ya auku.

Almajirai Biyu a Hanyar Imuwasu

13 A ran nan kuma sai ga waɗansu biyu suna tafiya wani ƙauye, mai suna Imuwasu, nisansa daga Urushalima kuwa kusan mil bakwai ne.

14 Suna ta zance da juna a kan dukan al’amuran da suka faru.

15 Ya zamana tun suna magana, suna tunani tare, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare.

16 Amma idanunsu a rufe, har ba su gane shi ba.

17 Yesu ya ce musu, “Wace magana ce kuke yi da juna a tafe?” Sai suka tsaya cik, suna baƙin ciki.

18 Sai ɗayansu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai kaɗai ne baƙo a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, ‘yan kwanakin nan ba?”

19 Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwa?” Suka ce masa, “Game da Yesu Banazare ne, wanda yake annabi mai manyan ayyuka da ƙwaƙƙwarar magana a gaban Allah da dukan mutane,

20 da kuma yadda manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi don a yi masa hukuncin kisa, suka kuwa gicciye shi.

21 Dā kuwa muna bege shi ne zai fanshi Isra’ila. Hakika kuma, bayan wannan duka, yau kwana uku ke nan da aukuwar wannan abu.

22 Har wa yau kuma, waɗansu mata na cikinmu, sun ba mu al’ajabi. Don sun je kabarin da sassafe,

23 da ba su sami jikinsa ba, suka komo, suka ce har ma an yi musu wahayi, sun ga mala’ikun da suka ce yana da rai.

24 Waɗansunsu da suke tare da mu kuma, suka je kabarin, suka tarar kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”

25 Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa!

26 Ashe, ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?”

27 Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.

28 Sai suka kusato ƙauyen da za su. Ya yi kamar zai ci gaba,

29 suka matsa masa suka ce, “Sauka a wurinmu, ai, magariba ta doso, rana duk ta tafi.” Sai ya sauka a wurinsu.

30 Sa’ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.

31 Idonsu ya buɗe, suka kuma gane shi. Sai ya ɓace musu.

32 Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta yi annuri ba, sa’ad da yake a hanya, yana bayyana mana Littattafai?”

33 Anan take, suka tashi suka koma Urushalima, suka sami sha ɗayan nan tare gu ɗaya, da kuma waɗanda suke tare da su,

34 suna cewa, “Hakika Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Bitrus!”

35 Su kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane shi a wajen gutsura gurasa.

Yesu ya Bayyana ga Almajiransa

36 Suna cikin faɗar waɗannan abubuwa, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama alaikun!”

37 Amma suka firgita, tsoro ya kama su, suka zaci fatalwa suke gani.

38 Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku?

39 Ku dubi hannuwana da ƙafafuna, ai, ni ne da kaina. Ku taɓa ni, ku ji, don fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”

40 Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.

41 Amma tun suna da sauran shakka saboda tsananin farin ciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da wani abinci a nan?”

42 Sai suka ba shi wata tsokar gasasshen kifi.

43 Ya kuwa karɓa, ya ci a gabansu.

44 Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”

45 Sa’an nan ya wayar da hankalinsu su fahimci Littattafai,

46 ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu,

47 a kuma yi wa dukan al’ummai wa’azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.

48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

49 Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya alkawarta. Amma ku dakata a birni tukuna, har a yi muku baiwar iko daga Sama.”

An Ɗauke Yesu zuwa Sama

50 Sai ya kai su waje har jikin Betanya. Ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.

51 Yana sa musu albarka ke nan, sai ya rabu da su, aka ɗauke shi zuwa sama.

52 Su kuwa suka yi masa sujada, suka koma Urushalima, suna matuƙar farin ciki.

53 Ko yaushe kuma suna a Haikali suna yabon Allah.

Categories
YAH

YAH 1

Kalman Ya Zama Mutum

1 Tun fil’azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.

2 Shi ne tun fil’azal yake tare da Allah.

3 Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.

4 Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.

5 Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.

6 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya.

7 Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa.

8 Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

9 Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.

10 Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba.

11 Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama’a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba.

12 Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama ‘ya’yan Allah,

13 wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.

14 Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.

15 Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ”

16 Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.

17 Domin Shari’a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance.

18 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.

Shaidar Yahaya Maibaftisma

19 Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa’ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne.

20 Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.”

21 Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A’a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A’a.”

22 Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?”

23 Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”

24 Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su.

25 Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”

26 Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba,

27 shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.”

28 An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.

“Ga Ɗan Rago na Allah”

29 Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!

30 Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’

31 Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra’ila na zo, nake baftisma da ruwa.”

32 Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.

33 Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’

34 Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”

Almajiran Yesu na Farko

35 Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu.

36 Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!”

37 Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.

38 Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?”

39 Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa.

40 Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan’uwan Bitrus.

41 Sai ya fara samo ɗan’uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe.

42 Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.

Yesu Ya Kira Filibus da Nata’ala

43 Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.”

44 Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus.

45 Filibus ya sami Nata’ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.”

46 Nata’ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.”

47 Yesu ya ga Nata’ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba’isra’ile na gaske wanda ba shi da ha’inci!”

48 Nata’ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa’ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.”

49 Sai Nata’ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra’ila ne!”

50 Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al’amuran da suka fi haka ma.”

51 Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala’ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”

Categories
YAH

YAH 2

Biki a Kana ta Galili

1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan,

2 aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa.

3 Da ruwan inabi ya gaza, uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”

4 Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.”

5 Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”

6 A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al’adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida shida.

7 Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal.

8 Sa’an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai.

9 Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango,

10 ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa’an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”

11 Wannan ce mu’ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.

12 Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da ‘yan’uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can ‘yan kwanaki.

Yesu Ya Tsabtace Haikali

13 Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima.

14 A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma ‘yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu.

15 Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin ‘yan canjin, ya birkice teburorinsu.

16 Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.”

17 Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.”

18 Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu’ujiza za ka nuna mana da kake haka?”

19 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.”

20 Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?”

21 Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne.

22 Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.

Yesu Ya San Zuciyar Kowa

23 To, sa’ad da yake Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu’ujizan da ya yi.

24 Amma Yesu bai amince da su ba,

25 domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.

Categories
YAH

YAH 3

Yesu da Nikodimu

1 To, akwai wani Bafarisiye, sunansa Nikodimu, wani shugaban Yahudawa.

2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu’ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.”

3 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”

4 Nikodimu ya ce masa, “Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato, ya iya komawa a cikin uwa tasa ta sāke haifo shi?”

5 Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.

6 Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.

7 Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’

8 Iska tana busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito da inda za ta. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.”

9 Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, “Ƙaƙa wannan zai yiwu?”

10 Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan al’amura ba?

11 Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu.

12 In na yi muku zancen al’amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al’amuran sama?

13 Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama.

14 Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,

15 domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.

16 “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.

17 Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.

18 Duk wanda ya gaskata da shi, ba za a yi masa hukunci ba. Wanda kuwa bai ba da gaskiya ba, an riga an yi masa hukunci, domin bai gaskata da sunan makaɗaicin Ɗan Allah ba.

19 Hukuncin kuwa shi ne, haske ya shigo duniya, amma mutane suka fi ƙaunar duhu da hasken, don ayyukansu mugaye ne.

20 Duk mai yin rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu.

21 Mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a bayyana ayyukansa, cewa, da taimakon Allah ne aka yi su.”

Shi Lalle Ya Riƙa Ƙaruwa, Ni kuwa Raguwa

22 Bayan haka, Yesu da almajiransa suka tafi ƙasar Yahudiya. A nan ya jima da su, yana yin baftisma.

23 Yahaya kuma yana yin baftisma a Ainon kusa da Salima, domin da ruwa da yawa a can. Mutane kuwa suka yi ta zuwa ana yi musu baftisma.

24 Domin a sa’an nan ba a sa Yahaya a kurkuku ba tukuna.

25 Sai fa almajiran Yahaya suka tasar wa wani Bayahude da muhawara a kan maganar tsarkakewa.

26 Suka kuma zo wurin Yahaya, suka ce masa, “Ya shugaba, wanda dā kuke tare a hayin Kogin Urdun, wanda kai kanka ma ka shaida shi, to, ga shi, yana yin baftisma, har kowa da kowa yana zuwa wurinsa.”

27 Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Ba mai iya samun kome sai ko an ba shi daga Sama.

28 Ku kanku ma shaiduna ne a kan na ce ba ni ne Almasihu ba, amma an aiko ni ne ni riga shi gaba.

29 Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.

30 Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.

Wanda Ya Zo daga Sama

31 “Mai zuwa daga Sama yana Sama da kowa. Wanda yake na ƙasa asalinsa kuwa na ƙasa ne, maganar ƙasa kuma yake yi. Mai zuwan nan daga Sama yana Sama da kowa.

32 Abin da ya ji, ya kuma gani, shi yake shaidarwa, duk da haka ba wanda yake yarda da shaidarsa.

33 Duk wanda ya yarda da shaidarsa, ya haƙƙaƙe, cewa, Allah mai gaskiya ne.

34 Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba.

35 Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa.

36 Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”