Categories
ROM

ROM 5

Abubuwan da Kuɓutarwa Take Kawowa

1 To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

2 Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah.

3 Banda haka ma, har muna taƙama da shan wuyarmu, da yake mun sani shan wuya take sa jimiri,

4 jimiri kuma yake sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma yake sa sa zuciya,

5 ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.

6 Tun muna raunana tukuna, Almasihu ya mutu a daidaitaccen lokaci, domin marasa bin Allah.

7 Da ƙyar za a sami wanda zai ba da ransa, saboda mutum mai adalci, ko da yake watakila saboda mutum mai nagarta wani ma sai yă yi kasai da ransa.

8 Amma kuwa Allah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.

9 To, tun da yake a yanzu an kuɓutar da mu ta wurin jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan.

10 In kuwa tun muna maƙiyan Allah aka sulhunta mu da shi ta mutuwar Ɗansa, to, da yake an sulhunta mu, ashe kuwa, za a fi kāre mu ta wurin rayuwarsa ke nan.

11 Banda haka ma, har muna fariya da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami sulhun nan a yanzu.

Adamu da Almasihu

12 To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi.

13 Lalle fa zunubi yana nan a duniya tun ba a ba da Shari’a ba, sai dai inda ba shari’a, ba a lasafta zunubi.

14 Duk da haka kuwa mutuwa ta mallaka tun daga Adamu har ya zuwa Musa, har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi irin na keta umarnin da adamu ya yi ba, wanda yake shi ne kwatancin mai zuwan nan.

15 Amma fa baiwar nan dabam take ƙwarai da laifin nan. Ai, in laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa masu ɗumbun yawa mutuwa, ashe ma, alherin Allah, da kuma baiwar nan, albarkacin alherin Mutum ɗaya, Yesu Almasihu, sai su yalwata ga masu ɗumbun yawa fin haka ƙwarai.

16 Baiwar nan kuwa dabam take ƙwarai da hakkokin zunubin mutum ɗayan nan. Don kuwa hukuncin da aka yi a kan laifin mutum ɗayan nan, shi ya jawo hukuncin hallaka. Amma baiwar nan da aka yi a sanadin laifofi da yawa, ita take sa kuɓuta ga Allah.

17 In kuwa saboda laifin mutum ɗayan nan ne mutuwa ta yi mallaka ta wurinsa, ashe kuwa, waɗanda suke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwar nan ta adalcin Allah, sai su yi mallaka fin haka ƙwarai a cikin rai, ta wurin ɗayan nan, wato Yesu Almasihu.

18 To, kamar yadda laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci, haka kuma aikin adalci na Mutum ɗayan nan ya zama wa dukan mutane sanadin kuɓuta zuwa rai.

19 Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta wurin biyayyar Mutum ɗaya za a mai da masu ɗumbun yawa masu adalci.

20 Shari’a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske.

21 Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.

Categories
ROM

ROM 6

Mutuwa ga Zunubi, Rayuwa ga Almasihu

1 To, me kuma za mu ce? Ma ci gaba da yin zunubi ne domin alherin Allah yă haɓaka?

2 A’a, ko kusa! Mu da muka mutu ga zunubi, ƙaƙa za mu ƙara rayuwa a cikinsa har yanzu?

3 Ashe, ba ku sani ba duk ɗaukacinmu da aka yi wa baftisma a cikin Almasihu Yesu, a cikin mutuwarsa aka yi mana baftismar ba?

4 Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka ta da Almasihu daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.

5 Tun da yake mun zama ɗaya da shi wajen kwatancin mutuwarsa, ashe kuwa, za mu zama ɗaya ma a wajen tashinsa.

6 Wato, mun sani an gicciye halayenmu na dā tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu ƙara bauta wa zunubi.

7 Wanda ya yi irin wannan mutuwa kuwa, an kuɓutar da shi daga zunubi ke nan.

8 Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun gaskata za mu rayu tare da shi kuma.

9 Mun sani tun da yake an ta da Almasihu daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba ke nan, mutuwa ba ta da sauran wani iko a kansa.

10 Mutuwar nan da ya yi kuwa, ya mutu ne sau ɗaya tak ba ƙari, saboda shafe zunubanmu, amma rayuwar da yake yi, yana rayuwa ne, rayuwa ga Allah.

11 Haka ku ma sai ku lasafta kanku kamar ku matattu ne ga zunubi, amma kuna a raye rayuwa ga Allah, ta wurin Almasihu Yesu.

12 Saboda haka, kada ku yarda zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha’awarsa.

13 Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.

14 Domin zunubi ba zai mallake ku ba, tun da yake ba shari’a take iko da ku ba alherin Allah ne.

Bayin Adalci

15 To, ƙaƙa? Wato, sai mu yi zunubi don shari’a ba ta iko da mu, sai alherin Allah? A’a, ko kusa!

16 Ba ku sani ba, shi wanda kuke miƙa kanku a gare shi domin yi wa biyayya, lalle ku bayi ne na wanda kuke yi wa biyayya ɗin (ko bautar zunubi wanda ƙarshensa mutuwa ne, ko bautar biyayya wadda ƙarshenta adalci ce)?

17 Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku.

18 Da aka ‘yanta ku kuma daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin adalci.

19 Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi’arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.

20 Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.

21 To, wace fa’ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne.

22 Amma a yanzu da aka ‘yanta ku daga bautar zunubi, kun zama bayin Allah, sakamakonku shi ne tsarkakewa, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.

23 Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

Categories
ROM

ROM 7

Ƙiyasi da Aure

1 Ya ‘yan’uwa, ko ba ku sani ba, shari’a tana da iko da mutum, muddin yana raye ne kawai? Da waɗanda suka san shari’a fa nake.

2 Misali, mace mai aure, shari’a ta ɗaure ta ga mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar auren ke nan.

3 Don haka, muddin mijinta yana da rai, in ta auri wani, sai a kira ta mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar wannan aure, ko da ta auri wani kuwa, ita ba mazinaciya ba ce.

4 Haka kuma ‘yan’uwana, kun zama matattu ga Shari’a, ta wurin jikin Almasihu, domin ku zama mallakar wani, wato, wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu ba da amfani ga Allah.

5 Ai, dā sa’ad da muke zaman halin mutuntaka, muguwar sha’awa wadda faɗakarwar Shari’a take sa a yi, ita take aiki a gaɓoɓinmu, tă wurin haddasa mutuwa.

6 Amma a yanzu mun ‘yantu daga Shari’a, mun mutu daga abin da dā ya ɗaure mu ke nan, har muna iya bauta wa Allah da sabon rai da Ruhu, ba da tsofaffin rubutattun ka’idodi ba.

Damuwa wadda Zunubin da Yake a Cikinmu Take Haddasawa

7 To, me kuma za mu ce? Shari’a zunubi ce? A’a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka, da ba domin Shari’a ba, da ban san zunubi ba. Da ba domin Shari’a ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba.

8 Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri iri a zuciyata. Gama da ba domin shari’a ba, da zunubi ba shi da wani tasiri.

9 Dā kam, sa’ad da ban san shari’a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu.

10 Umarnin nan kuwa, wanda manufarsa a gare ni rai ne, sai ya jawo mini mutuwa.

11 Don kuwa zunubi ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya yaudare ni, ta wurinsa kuwa ya kashe ni.

12 Domin haka Shari’a da kanta mai tsarki ce, umarnin kuma mai tsarki ne, daidai ne, nagari ne.

13 Wato, abar nan da take tagari ta jawo mini mutuwa ke nan? A’a, ko kusa! Zunubi ne ya jawo, domin ya bayyana kansa shi zunubi ne, gama ta wurin abar nan tagari ya jawo mini mutuwa, ta dalilin umarnin nan kuma, zunubi ya bayyana matuƙar muninsa.

14 Mun dai san Shari’a aba ce ta ruhu, ni kuwa mai halin mutuntaka ne, bautar zunubi kawai nake yi.

15 Ban ma fahimci abin da nake yi ba. Don ba abin da nake niyya yi, ba shi nake aikatawa ba, abin da nake ƙi, shi nake yi.

16 To, idan abin da ba na niyya, shi nake yi, na yarda ke nan Shari’a aba ce mai kyau.

17 Ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.

18 Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.

19 Nagarin abin da nake niyya yi kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa.

20 To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.

21 Sai na ga, ashe, ya zama mini ka’ida, in na so yin abin da yake daidai, sai in ga mugunta tare da ni.

22 Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari’ar Allah.

23 Amma ina ganin wata ka’ida dabam a gaɓoɓina, wadda take yaƙi da ka’idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ƙa’idar nan ta zunubi wadda take zaune a gaɓoɓina.

24 Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan, wanda yake kai ni ga mutuwa?

25 Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Ashe kuwa, ni a kaina, da hankalina, hakika Shari’ar Allah nake bauta wa, amma da jikina ka’idar zunubi nake bauta wa.

Categories
ROM

ROM 8

Rayuwa a Cikin Ruhu

1 Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.

2 Ka’idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ta ‘yanta ni daga ka’idar zunubi da ta mutuwa.

3 Abin da ba shi yiwuwa Shari’a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.

4 Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari’a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu.

5 Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al’amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al’amuran Ruhu.

6 Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala’muran Ruhu kuwa rai ne da salama.

7 Don ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari’ar Allah, ba kuwa zai iya ba.

8 Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.

9 Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.

10 In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah.

11 In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.

12 Domin haka, ‘yan’uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa.

13 In kuna zaman halin mutuntaka, za ku mutu ke nan, amma in da ikon Ruhu kuka kashe ayyukan nan na halin mutuntaka, sai ku rayu.

14 Duk waɗanda Ruhun Allah yake bishe su, su ne ‘ya’yan Allah.

15 Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A’a, na zaman ‘ya’ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!”

16 Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu ‘ya’yan Allah ne.

17 In kuwa ‘ya’ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.

18 Ai, a ganina, wuyar da muke sha a wannan zamani, ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakar da za a bayyana mana ba.

19 Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar ‘ya’yan Allah.

20 An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya,

21 gama za a ‘yantar da halitta da kanta ma, daga bautar ruɓewa, domin ta sami ‘yancin nan, na ɗaukaka na ‘ya’yan Allah.

22 Mun dai san dukan halitta tana nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda, har ya zuwa yanzu.

23 Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na ‘ya’yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.

24 Sa’ad da aka cece mu ne muka yi wannan sa zuciya. Amma kuwa, ai, sa zuciya ga abin da aka samu, ba sa zuciya ba ce. Wa yake sa zuciya ga abin da ya samu?

25 In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.

26 Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.

27 Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.

Mun Zarce A Ce da Mu Masu Nasara Ne

28 Mun kuma sani al’amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.

29 Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin ‘yan’uwa masu yawa.

30 Waɗanda ya ƙaddarar nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar. Waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.

31 To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?

32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?

33 Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne yake kuɓutar da su!

34 Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu!

35 Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi?

36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Saboda kai ne ake kashe mu yini zubur,

An lasafta mu kamar tumakin yanka.”

37 Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu.

38 Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala’iku, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko,

39 ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.

Categories
ROM

ROM 9

Allah Ya Zaɓi Isra’ila

1 Gaskiya nake faɗa, ni na Almasihu ne, ba ƙarya nake yi ba. Lamirina, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana ba da shaida,

2 cewa ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata.

3 Da ma a la’ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, ‘yan’uwana na kabila!

4 Su ne Isra’ilawa. Da zama ‘ya’yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari’a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.

5 Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.

6 Ba cewa Maganar Allah ta fādi ba, don ba duk zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ilawa na gaske ba.

7 Ba kuwa duk su ne ‘ya’yan Ibrahim ba, wai don suna zuriyarsa. Amma an ce, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.”

8 Wato, zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ‘ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.

9 Alkawarin kuwa shi ne, “Baɗi war haka zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.”

10 Banda haka ma, sa’ad da Rifkatu ta yi ciki da mutumin nan ɗaya, wato, kakanmu Ishaku,

11 tun ba ta haifi ‘ya’yan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau–don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa–

12 aka ce mata, “Wan zai bauta wa ƙanen.”

13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakubu na so, Isuwa na ƙi.”

14 To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin adalci ke nan? a’a, ko kusa!

15 Domin ya ce wa Musa, “Wanda zan yi wa jinƙai, zan yi masa jinƙan, wanda zan nuna wa tausayi kuwa, zan nuna masa tausayin.”

16 Ashe kuwa, abin bai danganta ga nufin mutum ko himma tasa ba, sai dai ga jinƙan Allah.

17 Don a Nassi an ce da Fir’auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”

18 Wato, yana nuna jinƙai ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.

19 Kila ka ce mini, “To, don me har yanzu yake ganin laifi? Wa zai iya tsayayya da nufinsa?”

20 Ya kai ɗan adam! Wane ne kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa magininsa, “Don me ka yi ni haka?”

21 Ashe, maginin tukwane ba ya iko da yumɓu, ya gina wata domin aiki mai martaba, wata kuma don kasasshen aiki, duk daga curi ɗaya?

22 To, ƙaƙa fa? Allah da yake yana so ya nuna fushinsa, ya kuma bayyana ikonsa, sai ya haƙura matuƙar haƙuri da waɗanda suka cancanci fushinsa, suka kuma isa hallaka,

23 Nufinsa ne yă bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya yi wa jinƙai, wato, waɗanda dā ma ya yi wa tanadin ɗaukaka?

24 Wato, mu ke nan da ya kira, ba kuwa daga cikin Yahudawa kaɗai ba, har ma daga cikin al’ummai.

25 Kamar dai yadda ya faɗa a Littafin Yusha’u cewa,

“Waɗanda dā ba jama’ata ba,

Zan ce da su ‘jama’ata,’

Wadda dā ba abar ƙaunata ba kuma,

Zan ce da ita ‘abar ƙaunata.’ ”

26 “A daidai wurin da aka ce da su, ‘Ku ba jama’ata ba ne,’

A nan ne za a kira su ‘’ya’yan Allah Rayayye,’ ”

27 A game da Isra’ila Ishaya ma ya ɗaga murya ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa ya kai kamar yashin teku, duk da haka kaɗan ne za su sami ceto.

28 Domin Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a duniya, ya gama shi tashi ɗaya.”

29 Kamar yadda Ishaya ya yi faɗa cewa,

“Da ba domin Ubangijin Runduna ya bar mana zuriya ba,

Da mun zama kamar Saduma,

An kuma maishe mu kamar Gwamrata.”

Isra’ila da Bishara

30 To, me kuma za mu ce? Ga shi, al’ummai da ba su nace da neman adalcin Allah ba, sun samu, wato, sun sami adalcin da yake daga bangaskiya.

31 Isra’ila kuwa da suka nace da neman hanyar adalcin Allah, suka kasa samunta.

32 Me ya sa? Don ba su neme ta ta hanyar bangaskiya ba, sai dai ta hanyar aikata aikin lada. Sai suka yi tuntuɓe da dutsen tuntuɓe,

33 kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Ga shi, na sa dutsen sa tuntuɓe a Sihiyona,

Da fā na sa faɗuwa.

Duk mai gaskatawa da shi, ba zai kunyata ba.”

Categories
ROM

ROM 10

1 Ya ‘yan’uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto.

2 Na dai shaida su a kan suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba.

3 Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar.

4 Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari’a, domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalcin Allah.

5 Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari’a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta.

6 Amma, a game da samun adalcin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau zuwa sama?” Wato, yă sauko da Almasihu.

7 Ko kuwa, “Wa zai gangara can ƙasa?” Wato yă ta da Almasihu daga matattu.

8 Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa’azi.

9 Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.

10 Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa yă sami ceto.

11 Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da shi ba zai kunyata ba.”

12 Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba’al’umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu’a a gare shi.

13 “Duk wanda kuwa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”

14 Amma ta ƙaƙa za su yi addu’a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, in ba mai wa’azi?

15 Ta ƙaƙa kuma za su yi wa’azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!”

16 Amma ba duka ne suka yi na’am da bisharar ba. Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?”

17 Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.

18 Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji.

“Muryarsu ta gama duniya duka,

Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”

19 Har wa yau, ina tambaya. Shin, Isra’ila kam, ba su fahimta ba ne? Da farko dai Musa ya ce,

“Zan sa ku kishin waɗanda ba al’umma ba ne,

Zan kuma sa ku fushi da wata al’ummar marar fahimta.”

20 Ishayan kuma ya fito gabagaɗi ƙwarai ya ce,

“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni.

Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.”

21 Amma a game da isra’ila, sai ya ce, “Yini zubur ina miƙa hannuwana ga jama’a marasa biyayya, masu tsayayya.”

Categories
ROM

ROM 11

Sauran Isra’ila

1 To, ina tambaya. Wato, Allah ya juya wa jama’arsa baya ke nan? A’a, ko kusa! Ai, ni ma da kaina Ba’isra’ile ne, zuriyar Ibrahim, na kabilar Biliyaminu.

2 Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama’arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan Isra’ila, ya ce,

3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka, sun rurrushe bagadanka na hadaya. Ni kaɗai ne na ragu, suna kuwa neman raina.”

4 Amma me Allah ya amsa masa? Cewa ya yi, “Na keɓe wa kaina mutum dubu bakwai waɗanda ba su taɓa durƙusa wa Ba’al ba.”

5 Haka ma a wannan zamani akwai ragowa, waɗanda aka zaɓa saboda alherinsa.

6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.

7 To, yaya ke nan? Ashe, abin da Isra’ila take nema, ba su samu ba ke nan, amma zaɓaɓɓun nan sun samu, sauran kuwa sun taurare.

8 Yadda yake a rubuce cewa,

“Allah ya toshe musu basira,

Ya ba su ido, ba na gani ba,

Da kuma kunne, ba na ji ba,

Har ya zuwa yau.”

9 Dawuda kuma ya ce,

“Da ma shagalinsu ya zama musu tarko, abin shammatarsu,

Sanadin faɗuwarsu kuma, har aniyarsu ta koma kansu.

10 Idonsu kuma yă shiga duhu, har su kasa gani,

Ka kuma tanƙwara bayansu har abada.”

Ceton Al’ummai

11 Ina kuma tambaya. Faɗuwar da suka yi, sun faɗi ba tashi ke nan? A’a, ko kusa! Sai ma faɗuwarsu ta zama sanadin ceto ga al’ummai, don a sa Isra’ila kishi.

12 To, in kuwa duniya ta arzuta da hasararsu, wa zai kimanta yawan albarka, in adadinsu masu ɗungumawa ga Allah ya cika?

13 Da ku al’ummai fa nake. Tun da yake ni manzo ne ga al’ummai, ina taƙama da aikina,

14 ko ta wane hali in sa kabilata kishin zuci, har in ceci waɗansunsu.

15 Domin in an sulhunta duniya ga Allah, saboda yar da su da aka yi, to, in an karɓe su fa, ba sai rai daga matattu ba?

16 In curin farko tsattsarka ne, haka sauran gurasar ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma.

17 Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,

18 kada ka yi wa sauran rassan alwashi. In kuwa ka yi, ka tuna fa, ba kai kake ɗauke da saiwar ba, saiwar ce take ɗauke da kai.

19 Kila za ka ce, “Ai, an sare rassan nan ne, don a ɗaura aure da ni.”

20 Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah.

21 Da yake Allah bai bar rassan asalin ba, kai ma ba zai bar ka ba.

22 Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka.

23 Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, domin Allah yana da ikon sāke mai da su.

24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

Komar da Isra’ila ga Matsayinsa

25 ‘Yan’uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra’ilawa ne, har adadin al’ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.

26 Ta haka nan ne Isra’ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Mai Ceto zai zo daga Sihiyona,

Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”

27 “Cikar alkawarina a gare su ke nan,

Sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”

28 A game da bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, domin amfaninku ne kuwa. Amma a game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu.

29 Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.

30 Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a dā, amma a yanzu aka yi muku jinƙai saboda rashin biyayyarsu,

31 haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku.

32 Don Allah ya kulle kowa a cikin rashin biyayya, domin ya nuna jinƙai ga kowa.

33 Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!

34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”

35 “Wa kyauta ta shiga tsakaninsu da Allah, ya fara bayarwa,

Har da za a sāka masa?”

36 Ai, daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukkan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada. Amin.

Categories
ROM

ROM 12

Hadaya Mai Rai

1 Don haka ina roƙonku ‘yan’uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi.

2 Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.

3 Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.

4 Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa suke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba,

5 haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan’uwansa ne.

6 Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu,

7 in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa,

8 mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara’a.

Gargaɗi a kan Zaman Kirista

9 Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari.

10 A game da ƙaunar ‘yan’uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan’uwansa.

11 Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji.

12 Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu’a.

13 Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.

14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la’ance su.

15 Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.

16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali’u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.

17 Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al’amuranku su zama daidai a gaban kowa.

18 In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.

19 Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.”

20 Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”

21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.

Categories
ROM

ROM 13

1 Bari kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne.

2 Saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya, ya yi wa umarnin Allah ke nan, masu yin tsayayyar nan kuwa za a yi musu hukunci.

3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ba ne ga masu aiki nagari, sai dai ga masu mugun aiki. Kana so kada ka ji tsoron mahukunci? To, sai ka yi nagarta, sai kuwa ya yaba maka.

4 Domin shi bawan Allah ne, don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza yake riƙe da takobi ba. Ai, shi bawa ne na Allah, mai sāka wa mugu da fushi.

5 Saboda haka wajibi ne ka yi biyayya, ba domin gudun fushi kaɗai ba, amma domin lamiri kuma.

6 Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, don su mahukunta ma’aikata ne na Allah, suna kuma yin wannan aiki a koyaushe.

7 Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa.

8 Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari’a ke nan.

9 Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

10 Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari’a ce.

11 Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da muke a ciki, ai, lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusa da ceton nan namu a kan sa’ad da muka fara ba da gaskiya.

12 Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske.

13 Mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa, ko fasikanci da fajirci, ko jayayya da kishi ba.

14 Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka, don biye wa muguwar sha’awarsa.

Categories
ROM

ROM 14

Kada Ka Ɗora wa Ɗan’uwanka Laifi

1 A game da wanda bangaskiya tasa rarrauna ce kuwa, ku karɓe shi hannu biyu biyu, amma ba a game da sukan ra’ayinsa ba.

2 Ga wani, bangaskiyarsa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiyarsa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci.

3 To, kada fa mai cin kome ɗin nan yă raina wanda ya ƙi ci, kada kuma wanda ya ƙi cin nan, yă ga laifin mai ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi hannu biyu biyu.

4 Kai wane ne har da za ka ga laifin baran wani? Ko dai ya tsaya, ko ya faɗi, ai, ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.

5 Wani yakan ɗaukaka wata rana fiye da sauran ranaku, wani kuwa duk ɗaya ne a wurinsa. Kowa dai yă zauna a cikin haƙƙaƙewa, a kan ra’ayinsa.

6 Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah.

7 Duk a cikinmu ba wanda ya isar wa kansa a sha’anin rayuwarsa ko mutuwarsa.

8 Ko muna a raye, zaman Ubangiji muke yi, ko mun mutu ma, zaman Ubangiji muke yi. Ashe, ko muna a raye, ko kuma a mace, na Ubangiji ne mu.

9 Saboda haka ne musamman Almasihu ya mutu, ya sāke rayuwa, wato, domin ya zama shi ne Ubangijin matattu da na rayayyu duka.

10 To, kai, me ya sa kake ganin laifin ɗan’uwanka? Kai kuma, me ya sa kake raina ɗan’uwanka? Ai, dukkanmu za mu tsaya a gaban kursiyin shari’ar Allah.

11 Domin a rubuce yake,

“Na rantse da zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna mini,

Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”

12 Don haka kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.

Kada Ka Sa Ɗan’uwanka Yin Tuntuɓe

13 Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu yă zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan’uwansa,

14 Na sani, na kuma tabbata, a tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne yake marar tsarki.

15 In kuwa cimarka tana cutar ɗan’uwanka, ashe, ba zaman ƙauna kake yi ba. Kada fa cimarka ta hallaka wannan da Almasihu ya mutu dominsa.

16 Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga waɗansu.

17 Ai, Mulkin Allah ba ga al’amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

18 Wanda duk yake bauta wa Almasihu ta haka, abin karɓa ne ga Allah, yardajje ne kuma ga mutane.

19 Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da suke kawo salama, suke kuma kawo inganta juna.

20 Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutum yă zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta wurin abin da yake ci.

21 Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan’uwanku yin tuntuɓe.

22 Kana da bangaskiya? To, ka riƙe ta tsakaninka da Allah. Albarka tā tabbata ga wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi ba, a game da abin da hankalinsa ya ga daidai ne.

23 Wanda yake shakka, amma kuwa ya ci, ya sani ya yi laifi ke nan, domin ba da bangaskiya ya ci ba. Duk abin da ba na bangaskiya ba ne, zunubi ne.