Categories
2 KOR

2 KOR 13

Kashedi da Gaisuwa

1 Wannan shi ne zai zama zuwana na uku a gare ku. Lalle ne kuwa a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.

2 Na gargaɗi waɗanda suka yi zunubi a dā, da kuma saura duka, a yanzu kuma da ba na nan ina yi musu gargaɗi, kamar yadda na yi sa’ad da nake nan a zuwana na biyu, cewa in na sāke zuwa ba zan sawwaƙe musu ba.

3 In dai nema kuke yi ku tabbata, cewa da izinin Almasihu nake magana, to, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.

4 Ko da yake an gicciye shi ne da rashin ƙarfi, duk da haka a raye yake ta ikon Allah. Mu ma marasa ƙarfi ne kamarsa, amma a game da al’amuranku da za mu zartar, a raye muke tare da shi, ta ikon Allah.

5 Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin!

6 Muna fata ku gane, mu ba mu kāsa ba.

7 Amma muna roƙon Allah kada ku yi wani mugun abu, ba don mu mu zama kamar mun ci gwajin kawai ba, sai dai domin ku yi abin da yake daidai, ko da yake za ku ga kamar mun kāsa.

8 Domin ba dama mu sāɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar.

9 Gama farin ciki muke yi in muna raunana, ku kuna ƙarfafa. Addu’armu ita ce ku kammala.

10 Ina rubuta wannan ne sa’ad da ba na tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.

11 Daga ƙarshe kuma, ‘yan’uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.

12 Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.

13 Dukan tsarkaka suna gaishe ku.

14 Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.

Categories
GAL

GAL 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, manzo, ba kuwa manzon mutum ba, ba kuma ta wurin wani mutum ba, sai dai ta wurin Yesu Almasihu, da Allah Uba, wanda ya tashe shi daga matattu,

2 da kuma dukan ‘yan’uwa da suke tare da ni, zuwa ga ikilisiyoyin ƙasar Galatiya.

3 Alheri da salama na Allah Uba su tabbata a gare ku, da na Ubangijinmu Yesu Almasihu,

4 wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu, domin yă cece mu daga mugun zamanin nan, bisa ga nufin Allahnmu, wato Ubanmu.

5 Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.

Ba wata Bishara

6 Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara,

7 alhali kuwa ba wata bishara dabam, sai dai akwai waɗansu da suke ta da hankalinku, suna son jirkitar da bisharar Almasihu.

8 Amma ko mu, ko kuma wani mala’ika daga sama, in waninmu zai yi muku wata bishara dabam da wadda muka yi muku, to, ya zama la’ananne!

9 Kamar yadda muka faɗa a dā, haka yanzu ma nake sāke faɗa, cewa kowa ya yi muku wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, to, yă zama la’ananne!

10 To, wato ni son mutane nake nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya? Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.

Shigar Bulus Manzanci

11 Ina so in sanar da ku, ‘yan’uwa, bisharar nan da na sanar ba ta ɗan adam ba ce,

12 domin ba daga wurin mutum na samo ta ba, ba kuma koya mini ita aka yi ba, sai dai ta wurin bayyanar Yesu Almasihu a gare ni ne na same ta.

13 Kun dai ji irin zamana na dā a cikin addinin yahudanci, yadda na riƙa tsananta wa Ikkilisiyar Allah ƙwarai da gaske, har ina ta watsa ta,

14 yadda kuma a cikin addinin Yahudanci har na tsere wa yawancin tsararrakina a cikin mutanenmu, na himmantu ƙwarai da gaske ga bin al’adun kakanninmu.

15 Amma sa’ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, ya ji daɗin

16 bayyana Ɗansa a gare ni, domin in sanar da shi ga al’ummai, ban yi shawara da ɗan adam ba,

17 ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba, sai nan da nan na je ƙasar Larabawa, sa’an nan na komo Dimashƙu.

18 Bayan shekara uku kuma sai na tafi Urushalima ganin Kefas, na kuwa kwana goma sha biyar a gunsa.

19 Amma ban ga ko ɗaya a cikin sauran manzanni ba, sai dai Yakubu ɗan’uwan Ubangiji.

20 Abin nan da nake rubuto muku fa, ba ƙarya nake yi ba, a gaban Allah nake faɗa.

21 Daga baya kuma, na tafi ƙasar Suriya da ta Kilikiya.

22 Amma kuwa ikilisiyoyin Almasihu da suke a ƙasar Yahudiya, ba su san ni ido da ido ba tukuna.

23 Sai dai kawai sun ji an ce, “Wanda dā yake tsananta mana, ga shi, a yanzu yana sanar da bangaskiyar nan da dā yake ta rusawa!”

24 Sai suka ɗaukaka Allah saboda ni.

Categories
GAL

GAL 2

Sauran Manzanni Sun Karɓi Bulus

1 Bayan shekara goma sha huɗu na sāke komawa Urushalima tare da Barnaba, na kuma ɗauki Titus.

2 Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al’ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.

3 Kai, ko Titus ma da yake a tare da ni, ba a tilasta masa yin kaciya ba, ko da yake shi Bahelene ne.

4 Maganar nan ta tashi saboda ‘yan’uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen ‘yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.

5 Amma ko kaɗan ba mu sakar musu ba, ko da taƙi, domin gaskiyar bishara tă zaune muku.

6 Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.

7 Amma da suka ga an amince mini in yi wa marasa kaciya bishara, kamar yadda aka amince wa Bitrus ya yi wa masu kaciya bishara,

8 (domin shi da ya yi aiki a zuciyar Bitrus ya sa shi manzo ga masu kaciya, shi ne kuma ya yi aiki a zuciyata, ya sa ni manzo ga al’ummai),

9 sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al’ummai, su kuwa gun masu kaciya.

10 Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.

Bulus ya Tsawata wa Bitrus a Antakiya

11 Amma da Kefas ya zo Antakiya, sai na tsaya masa fuska da fuska don laifinsa a fili yake.

12 Don kafin waɗansu su zo daga wurin Yakubu, yakan ci abinci da al’ummai. Amma da suka zo, ya janye jiki ya ware kansa, yana tsoron ɗariƙar masu kaciyar nan.

13 Haka ma sauran Yahudawa masu bi suka nuna fuska biyu kamarsa, ko da Barnaba ma sai da suka ciwo kansa da munafuncinsu.

14 Amma da na ga dai ba sa bin gaskiyar bishara sosai, na ce wa Kefas a gaban idon kowa, “Kai da kake Bayahude, in ka bi al’adar al’ummai ba ta Yahudawa ba, yaya kake tilasta wa al’ummai su bi al’adar Yahudawa?

Ceton Yahudawa duk da Al’ummai ta wurin Bangaskiya

15 “Mu da aka haifa Yahudawa, ba al’ummai masu zunubi ba,

16 da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari’a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari’a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari’a.

17 In kuwa ya zamana, sa’ad da muke neman kuɓuta ga Allah ta wurin Almasihu, an tarar har mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, Almasihu yana hidimar zunubi ne? A’a, ko kusa!

18 Amma in na sāke ginin abin da dā na rushe, na tabbata mai laifi ke nan.

19 Gama ni ta wurin Shari’a matacce ne ga Shari’a domin in rayu ga Allah.

20 An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.

21 Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari’a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”

Categories
GAL

GAL 3

Shari’a ko Bangaskiya

1 Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ɗauke hankalinku? Ku da aka bayyana muku Yesu Almasihu gicciyeyye sosai.

2 Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu saboda bin Shari’a ne, ko kuwa saboda gaskatawa ga maganar da kuka ji?

3 Ashe, rashin azancinku har ya kai ga haka? Da kuka fara da Ruhu, ashe, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa?

4 Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banzan ne!

5 Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu’ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari’a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?

6 Haka ma Ibrahim “ya gaskata Allah, bangaskiyan nan tasa kuma, aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”

7 Wato kun ga ashe, masu bangaskiya su ne ‘ya’yan Ibrahim.

8 A cikin Nassi kuwa an hango, cewa Allah zai kuɓutar da al’ummai ta wurin bangaskiya, wato, dā ma can an yi wa Ibrahim bishara cewa, “Ta wurinka za a yi wa dukkan al’ummai albarka.”

9 To, ashe, masu bangaskiya su ne aka yi wa albarka a game da Ibrahim mai bangaskiyar nan.

10 Gama duk waɗanda suke dogara da bin Shari’a la’anannu ne, don a rubuce yake cewa, “Duk wanda bai tsaya ga aikata duk abin da yake rubuce a littafin Shari’a ba, la’ananne ne.”

11 To, a fili yake, ba mai samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari’a, domin “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”

12 Shari’a kuwa ba ta dangana ga bangaskiya ba, domin ta ce, “Wanda ya aikata ta, ta gare ta ne zai rayu.”

13 Almasihu ya fanso mu daga la’anar nan ta Shari’a, da ya zama abin la’ana saboda mu, domin a rubuce yake cewa, “Duk wanda aka kafa a jikin itace, la’ananne ne.”

14 An yi wannan kuwa domin albarkar nan da aka yi wa Ibrahim ta saukar wa al’ummai ta wurin Almasihu Yesu, mu kuma ta hanyar bangaskiya mu sami Ruhun nan da aka yi alkawari.

Shari’a da Alkawari

15 To, ‘yan’uwa, bari in yi muku misali. Ko alkawari na mutum ne kawai, in dai an riga an tabbatar da shi, ba mai soke shi, ba kuma mai ƙara wani abu a kai.

16 To, alkawaran nan, an yi wa Ibrahim ne, da kuma wani a zuriyarsa. Ba a ce, “Da zuriya” ba, kamar suna da yawa. A’a, sai dai ɗaya kawai, aka ce, “Wani a zuriyarka,” wato Almasihu.

17 Ga abin da nake nufi. Shari’ar nan, wadda ta zo shekara arbaminya da talatin daga baya, ba ta shafe alkawarin nan da Allah ya tabbatar tun tuni ba, har da za ta wofinta shi.

18 Don da gādon nan ta hanyar Shari’a yake samuwa, ashe, da ba zai zama na alkawarin ke nan ba. Amma Allah ya bai wa Ibrahim ta wurin alkawari ne.

19 To, mece ce manufar Shari’a? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyar nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin mala’iku ne, ta hannun matsakanci.

20 Matsakanci fa ba domin ɗaya ba ne. Amma Allah ɗaya yake.

Manufar Shari’a

21 Wato, Shari’a ta zama saɓanin alkawaran Allah ke nan? A’a, ko kusa! Domin da an ba da wata shari’a mai iya ba da rai, da sai a sami adalcin Allah ta hanyar bin Shari’ar nan.

22 Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.

23 Tun kafin bangaskiya ta zo, a cikin ƙangin Shari’a muke a kulle, sai a lokacin da bangaskiya ta bayyana.

24 Ashe kuwa, Shari’a ta zama uwargijiyarmu da ta kai mu ga Almasihu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya.

25 A yanzu kuwa da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a hannun wata uwargijiya.

26 Domin dukanku ‘ya’yan Allah ne, ta wurin bangaskiya ga Almasihu Yesu.

27 Duk ɗaukacinku da aka yi wa baftisma ga bin Almasihu, kun ɗauki halin Almasihu ke nan.

28 Ba sauran cewa Bayahude ko Ba’al’umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu.

29 In kuwa ku na Almasihu ne, ashe, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda ne kuma bisa ga alkawarin nan.

Categories
GAL

GAL 4

1 Ana nufin, magaji, muddin yana yaro bai fi bawa ba, ko da yake yana da mallakar dukkan kome.

2 A hannun iyayen goyo da wakilai yake har zuwa ranar da mahaifinsa ya sa.

3 Haka yake a gare mu, wato sa’ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al’adun duniya muke.

4 Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari’a,

5 domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari’a, a mai da mu a matsayin ‘ya’yan Allah.

6 Tun da yake ku ‘ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, yana kira, “Ya Abba! Uba!”

7 Don haka, kai ba bawa ba ne kuma, amma ɗa ne. Da yake ɗa ne kuma, to, magāji ne bisa ga ikon Allah.

Alhinin Bulus a kan Masu Bangaskiya

8 Dā da ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu gumaka, waɗanda ga ainihi ba a bakin kome suke ba.

9 Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al’adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?

10 Ga shi, al’adun ranaku, da na watanni, da na lokatai, da na shekaru ba sa wuce ku!

11 Amma kun ba ni tsoro, kada ya zamana na yi wahala a kanku a banza!

12 Ina roƙonku, ya ku ‘yan’uwana, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma in zama kamar yadda kuke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba.

13 Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku bishara a zuwana na fari.

14 Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na’am da ni kamar wani mala’ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa.

15 To, ina daɗin nan da kuka ji a game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni!

16 Ashe, wato na zama abokin gābarku ne don na gaya muku gaskiya?

17 Waɗannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su raba ku da mu, don su ma ku yi habahaba da su.

18 Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba.

19 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!

20 Da ma a ce ina tare da ku a yanzu in sauya muryata! Gama na ruɗe a kan sha’aninku.

Ishara da Hajaratu da Saratu

21 Ku gaya mini, ku da kuke son Shari’a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne?

22 Domin a rubuce yake, Ibrahim yana da ‘ya’ya biyu maza, ɗaya ɗan kuyanga, ɗaya kuma ɗan ‘ya.

23 Ɗan kuyangar nan, an haife shi ne bisa ga ɗabi’a, ɗan ‘yar kuwa ta cikar alkawarin ne.

24 Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawari biyu suke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina’i, mai haihuwar bayi, wato Hajaratu ke nan.

25 To, ai, Hajaratu Dutsen Sina’i ce a ƙasar Larabawa. Ita ce kwatancin Urushalima ta yanzu, don ita da ‘ya’yanta duk a bauta suke.

26 Amma Urushalima ta sama, ai ‘ya ce, ita ce kuma uwarmu.

27 Domin a rubuce yake cewa,

“ki yi farin ciki, ya ke bakarariya da ba kya haihuwa,

Ki ɗauki sowa, ke da ba kya naƙuda,

Don yasasshiya ta fi mai miji yawan ‘ya’ya.”

28 To, ‘yan’uwa, mu ma ‘ya’yan alkawari ne kamar Ishaku.

29 Kamar yadda dā, shi da aka haifa bisa ga ɗabi’a ya tsananta wa wanda aka haifa bisa ga ikon Ruhun, haka a yanzu ma yake.

30 Amma me Nassin ya ce? “Ka kori kuyangar da ɗanta, don ko kaɗan ɗan kuyangar ba zai ci gādo tare da ɗan ‘ya ba.”

31 Saboda haka ‘yan’uwa, mu ba ‘ya’yan kuyanga ba ne, na ‘ya ne.

Categories
GAL

GAL 5

Ku Dāge a Cikin ‘Yanci

1 Almasihu ya ‘yanta mu, ‘yantawar gaske. Don haka sai ku dāge, kada ku sāke sarƙafewa a cikin ƙangin bauta.

2 To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku kome ba ke nan.

3 Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari’a.

4 Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari’a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah.

5 Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.

6 In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.

7 Dā, ai, kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku bin gaskiya?

8 Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.

9 Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa.

10 Na dai amince da ku a cikin Ubangiji, ba za ku bi wani ra’ayi dabam da nawa ba. Wannan da yake ta da hankalinku kuwa zai sha hukunci, ko shi wane ne.

11 Amma ‘yan’uwa, in da har yanzu wa’azin yin kaciya nake yi, to, don me har yanzu ake tsananta mini? In da haka ne, ashe, an kawar da hamayyar da gicciyen Almasihu yake sawa ke nan!

12 Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!

13 Ya ku ‘yan’uwa, don ‘yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da ‘yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.

14 Don duk Shari’a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

15 Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.

Albarkar Ruhu da Halin Mutuntaka

16 Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba.

17 Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so.

18 In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari’a ba ta da iko da ku, ke nan.

19 Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci,

20 da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya,

21 da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.

22 Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,

23 da tawali’u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari’a ta kama su.

24 Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha’awace-sha’awace iri iri.

25 In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al’amuranmu ta wurin ikon Ruhu.

26 Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.

Categories
GAL

GAL 6

Ku Ɗauki Wahalar Juna

1 Ya ku ‘yan’uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali’u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.

2 Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari’ar Almasihu.

3 Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan.

4 Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa’an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.

5 Lalle kowa yă ji da kayansa.

6 Duk wanda aka koya wa Maganar, yă ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.

7 Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.

8 Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami.

9 Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.

10 To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama’ar masu ba da gaskiya ba.

Kashedi da kuma Gaisuwa

11 Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da nake muku da hannuna!

12 To, mutanen nan masu son nuna bijinta cikin jiki, su ne masu son tilasta muku yin kaciya, don gudun shan wuya saboda gicciyen Almasihu.

13 Ai, ko waɗanda aka yi wa kaciya ma ba sa kiyaye Shari’a. Sonsu ne a yi muku kaciya, don su yi fāriya da ku a kan an yi muku kaciya.

14 Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha’anin duniya, duniya kuma ta yar da sha’anina.

15 Kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu.

16 Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka’idar nan, wato Isra’ilar gaske ta Allah.

17 Daga nan gaba kada kowa ya ƙara damuna, domin a jikina ina da tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.

18 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku, ‘yan’uwa. Amin.

Categories
AFI

AFI 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, zuwa ga mutanensa tsarkaka da suke a Afisa, amintattu a cikin Almasihu Yesu.

2 Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Albarku na Ruhu a Cikin Almasihu

3 Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,

4 domin kuwa ya zaɓe mu a cikin Almasihu tun ba a halicci duniya ba, mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa.

5 Ya ƙaddara mu mu zama ‘ya’yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri,

6 domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.

7 Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,

8 wanda ya falala mana. Da matuƙar hikima da basira

9 ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu.

10 Duk wannan kuwa shiri ne, domin a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta wurin Almasihu, wato abubuwan da suke sama, da abubuwan da suke a ƙasa.

11 A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi,

12 domin mu da muka fara kafa bege ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa.

13 A cikinsa ne ku kuma da kuka ji maganar gaskiya, wato, bisharar cetonku, a cikinsa, sa’ad da kuka ba da gaskiya kuma, aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta.

14 Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.

Addu’a don Hikima da Sani

15 Saboda haka da yake na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukan tsarkaka,

16 ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa’ad da nake yi muku addu’a,

17 da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah,

18 a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,

19 da kuma ko mene ne girman ikonsa marar misaltuwa da yake zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa,

20 wanda ya zartar ga Almasihu sa’ad da ya tashe shi daga matattu, ya kuma ba shi wurin zama a damansa a samaniya,

21 a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma.

22 Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikkilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka.

23 Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.

Categories
AFI

AFI 2

Daga Mutuwa zuwa Rai

1 Ku kuma yā raya ku sa’ad da kuke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku,

2 waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al’amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu.

3 Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha’awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi’a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran ‘yan adam.

4 Amma Allah da yake mai yalwar jinƙai ne, saboda matsananciyar ƙaunar da yake yi mana,

5 ko a sa’ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku),

6 a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya.

7 Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu.

8 Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah,

9 ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.

10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

Zama Ɗaya da Almasihu

11 Saboda haka, ku tuna dā ku al’ummai ne bisa ɗabi’a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

12 Ku kuma tuna a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu, bare ne ga jama’ar Isra’ila, bāƙi ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya.

13 Amma a yanzu, a cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu.

14 Domin Almasihu shi ne salamarmu, shi wanda ya mai da Yahudawa da al’ummai ɗaya, wato ya rushe katangar nan da ta raba su a kan gāba.

15 Har ya soke Shari’ar nan mai umarni da dokoki, ta wurin ba da jikinsa, domin ta gare shi yă halicci sabon mutum guda daga mutanen nan biyu, ta haka yă kawo salama,

16 yă kuma sulhunta su duka biyu ga Allah, su zama jiki ɗaya ta wurin gicciye, ta haka yă kashe gābar.

17 Ya kuwa zo ya yi muku albishirin salama, ku da kuke nesa, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.

18 Domin ta gare shi ne dukanmu biyu muka sami isa gun Uba ta hanyar Ruhu guda.

19 Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan ‘yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma,

20 waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin,

21 dukan wanda aka haɗa tsarin ginin a cikinsa, yana kuma tashi ya zama haikali tsattsarka na Ubangiji.

22 A cikinsa ne ku kuma aka gina ku, ku zama mazaunin Allah ta wurin Ruhu.

Categories
AFI

AFI 3

Hidimar Bulus ga Al’ummai

1 Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al’ummai,

2 in dai kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah wanda aka yi mini baiwa saboda ku,

3 wato yadda aka sanar da ni asirin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a taƙaice.

4 A yayin da kuka karanta wannan, za ku iya gane basirata saboda asirin Almasihu,

5 wanda a zamanin dā ba a sanar da ‘yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,

6 wato, yadda ta wurin bishara al’ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.

7 An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa.

8 Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al’ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,

9 in kuma bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda shekara da shekaru yake a ɓoye a gun Allah, wanda ya halicci dukkan abubuwa.

10 An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala’iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.

11 Wannan kuwa bisa ga dawwamammen nufin nan ne da Allah ya zartar a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

12 A cikinsa muke da gabagaɗin isa ga Allah, da amincewa, ta wurin bangaskiyarmu a gare shi.

13 Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

A San Ƙaunar Almasihu

14 Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban,

15 shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna,

16 ina addu’a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa,

17 har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku,

18 har ku sami kaifin basira tare da dukan tsarkaka, ku fahimci ko mene ne fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta da zacinta, da kuma zurfinta,

19 ku kuma san ƙaunar da Almasihu yake yi mana, wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan falala ta Allah.

20 Ɗaukaka tā tabbata ga wannan da yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato, aikatawa ta ƙarfin ikonsa da yake aiki a zuciyarmu.

21 Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a cikin Ikkilisiya ta wurin Almasihu Yesu, har ya zuwa dukkan zamanai har abada abadin. Amin.