Categories
AFI

AFI 4

Ɗayantuwar Ruhu

1 Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku,

2 da matuƙar tawali’u, da salihanci, da haƙuri, kuna jure wa juna saboda ƙauna.

3 Da ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar da Ruhu yake zartarwa, kuna a haɗe a cikin salama.

4 Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan.

5 Ubangiji guda ne, bangaskiya guda, da kuma baftisma guda.

6 Allah ɗaya ne, Ubanmu duka, wanda yake bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.

7 Amma an ba kowannenmu alheri gwargwadon baiwar Almasihu.

8 Saboda haka, Nassi ya ce,

“Sa’ad da ya hau Sama ya bi da rundunar kamammu,

Ya kuma yi wa ‘yan adam baye-baye.”

9 (Wato, da aka ce “ya hau” ɗin, me aka fahimta, in ba cewa dā ya sauka a can ƙasa ba?

10 Shi wanda ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau a can birbishin dukkan sammai, domin yă cika kome.)

11 Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,

12 domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar Ikkilisiya, domin a inganta jikin Almasihu,

13 har mu duka mu riski haɗa kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai maƙamin cikakken mutum, mu kuma kai ga matsayin nan na falalar Almasihu.

14 An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu.

15 A maimakon haka, sai mu faɗi gaskiya game da ƙauna, muna girma a cikinsa ta kowace hanya, wato Almasihu, shi da yake shugabanmu.

16 Domin ta gare shi ne dukkan jiki yake a game, yake kuma a haɗe, ta wurin gudunmawar kowace gaɓa, ta wurin kuma aikin kowace gaɓa daidai jikin yake ƙara girma, yana kuma ingantuwa da halin ƙauna.

Sabon Rai a Cikin Almasihu

17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku sāke yin zama irin na al’ummai, masu azancin banza da wofi.

18 Duhun zuciya yake a gare su, bare suke ga rai wanda Allah yake bayarwa, sabili da jahilcin da yake a gare su, saboda taurin kansu.

19 Zuciyarsu ta yi kanta, sun dulmiya a cikin fajirci, sun ɗokanta ido a rufe ga yin kowane irin aikin lalata.

20 Ba haka kuka koyi al’amarin Almasihu ba,

21 in da a ce kun saurare shi, an kuma koya muku ta gare shi ne, wato yadda gaskiya ta Yesu take.

22 Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke a ciki, wanda yake lalacewa saboda sha’awoyinsa na yaudara,

23 ku kuma sabunta ra’ayin hankalinku,

24 ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.

25 Saboda haka, sai ku watsar da ƙarya, kowa yă riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne.

26 In kun husata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana,

27 kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.

28 Kada ɓarawo ya ƙara yin sata, a maimakon haka sai ya motsa jiki yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami abin da zai ba matalauta.

29 Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.

30 Ku kuma kula, kada fa ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda aka hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa.

31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke, da kowace irin ƙeta.

32 Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.

Categories
AFI

AFI 5

Ku Yi Zaman Haske

1 Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, in ku ƙaunatattun ‘ya’yansa ne.

2 Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.

3 Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.

4 Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.

5 Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.

6 Kada wani ya hilace ku da maganar wofi, gama sabili da waɗannan zunubai ne fushin Allah yake aukawa a kan kangararru.

7 Saboda haka, kada ku yi cuɗanya da su,

8 domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske,

9 domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.

10 Ku dai tabbata abin zai gamshi Ubangiji.

11 Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su.

12 Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da suke yi a asirce.

13 Duk abin da aka kawo a gaban haske a san ainihinsa, gama duk abin da aka san ainihinsa ya haskaka.

14 Saboda haka aka ce,

“Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu.

Almasihu kuwa zai haskaka ka.”

15 Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima.

16 Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.

17 Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji.

18 Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha’a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu,

19 kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku.

20 Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne.

Maza da Mata

21 Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu.

22 Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa.

23 Don miji shi ne shugaban matarsa, kamar yadda Almasihu yake shugaban Ikkilisiya, wato, jikinsa, shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin.

24 Kamar yadda Ikkilisiya take bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali.

25 Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikkilisiya, har ya ba da kansa dominta,

26 domin ya miƙa ta ga Allah, tsarkakakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin Kalma,

27 domin shi kansa yă ba kansa Ikkilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu.

28 Ta haka ya wajaba maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan suke yi wa. Ai, wanda ya ƙaunaci matarsa, ya ƙaunaci kansa ke nan.

29 Domin ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa, kamar yadda Almasihu yake yi wa Ikkilisiya,

30 domin mu gaɓoɓin jikinsa ne.

31 “Saboda haka ne, mutum sai ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki guda.”

32 Wannan asiri muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikkilisiya.

33 Duk da haka dai, sai kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta yi wa mijinta ladabi.

Categories
AFI

AFI 6

Biyayya da Ƙauna

1 Ku ‘ya’ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai.

2 Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,

3 don al’amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”

4 Ku ubanni, kada ku sa ‘ya’yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.

5 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya, da hali bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya ɗaya, Almasihu kuke yi wa ke nan,

6 ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai kamar bayin Almasihu masu aikata abin da Allah yake so, da zuciya ɗaya,

7 kuna bauta da kyakkyawar niyya domin Ubangiji kuke yi wa, ba mutane ba.

8 Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi.

9 Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku sani, shi wanda yake Ubangijinsu da ku duka, yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe.

Makaman Allah Duka

10 A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.

11 Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis.

12 Ai, famarmu ba da ‘yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.

13 Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.

14 Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku,

15 shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku.

16 Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita.

17 Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah,

18 a koyaushe kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu’a.

19 Ni ma ku yi mini, domin in sami baiwar yin hurci, in yi magana gabagaɗi, in sanar da asirin bishara,

20 wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. Ku dai yi mini addu’a, duk sa’ad da nake yin bisharar, in bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi.

Gaisuwa

21 A yanzu kuwa, don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da nake a ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa, amintaccen mai hidimar Ubangiji, zai sanar da ku kome.

22 Na aiko shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, ya kuma ƙarfafa muku zuciya.

23 Salamar Allah Uba da ta Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata ga ‘yan’uwa, tare da ƙauna game da bangaskiya.

24 Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.

Categories
FILIB

FILIB 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.

2 Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.

Addu’ar Bulus domin Filibiyawa Masu Bin Almasihu

3 Ina gode Allahna duk sa’ad da nake tunawa da ku,

4 a kullum kuwa a kowace addu’a da nake muku duka, da farin ciki nake yi.

5 Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu.

6 Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.

7 Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.

8 Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi.

9 Addu’ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa,

10 domin ku zaɓi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu,

11 kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.

Manufar Rayuwata, Almasihu Ne

12 ‘Yan’uwa, ina so ku sani, al’amuran nan da suka auku a gare ni, har ma sun yi amfani wajen yaɗa bishara,

13 har dai ya zama sananne ga dukan sojan fāda da sauran jama’a, cewa ɗaurina saboda Almasihu ne.

14 Har ma galibin ‘yan’uwa cikin Ubangiji suka ƙarfafa saboda ɗaurina, sun kuma ƙara fitowa gabagaɗi, su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.

15 Lalle waɗansu suna wa’azin Almasihu saboda hassada da husuma, amma waɗansu kam, saboda kyakkyawar niyya ne.

16 Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara.

17 Waɗancan kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin ɗaurina.

18 Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Almasihu, na kuma yi farin ciki da haka. I, zan yi farin ciki kuwa.

19 Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu’arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu.

20 Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.

21 Domin ni, a gare ni, rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce.

22 In ya zamanto rayuwa zan yi a cikin jiki, to, zan yi aiki mai amfani ke nan. Amma na rasa abin da zan zaɓa.

23 Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa.

24 Amma in wanzu a cikin jiki, shi ya fi wajabta saboda ku.

25 Na tabbata haka ne, na kuwa sani zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku yin farin ciki,

26 ku kuma sami ƙwaƙƙwaran dalilin yin taƙama da Almasihu ta wurina, saboda sāke komowata gare ku.

27 Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra’ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa,

28 ba kwa kuwa jin tsoron magabtanku sam. Wannan kuwa ishara ce a gare su ta hallakarsu, ku kuwa ta cetonku, isharar kuwa daga Allah take.

29 Gama an yi muku alheri, cewa ba gaskatawa da Almasihu kawai za ku yi ba, har ma za ku sha wuya dominsa,

30 kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda kuke ji nake sha har yanzu.

Categories
FILIB

FILIB 2

Ƙasƙantar Almasihu da kuma Ɗaukakarsa

1 In akwai ƙarfafawa a cikin Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku,

2 to, albarkacinsu ku cikasa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna ƙaunar juna, nufinku ɗaya, ra’ayinku ɗaya.

3 Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali’u, kowa yana mai da ɗan’uwansa ya fi shi.

4 Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan’uwansa ma.

5 Ku ɗauki halin Almasihu Yesu,

6 wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba,

7 sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam.

8 Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye.

9 Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da yake birbishin kowane suna,

10 domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa,

11 kowane harshe kuma yă shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba.

Haskakawa Kamar Fitilu a Duniya

12 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.

13 Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.

14 Kome za ku yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama,

15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai, ‘ya’yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,

16 kuna riƙe da maganar rai kankan, har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama, cewa himmata da famana ba a banza suke ba.

17 Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.

18 Haka ku ma, ya kamata ku yi farin ciki, ku kuma taya ni farin ciki.

Timoti da Abafaroditas

19 Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timoti da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku.

20 Ba ni da wani kamarsa, wanda da sahihanci zai tsananta kula da zamanku lafiya.

21 Dukansu sha’anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba.

22 Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.

23 Shi ne nake fata in aiko, da zarar na ga yadda al’amarina yake gudana.

24 Na kuma amince har ga Ubangiji, ni ma da kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.

25 Amma na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas ɗan’uwana, abokin aikina, abokin famana kuma, wanda kuka aiko ya yi mini ɗawainiya.

26 Yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya.

27 Lalle ya yi rashin lafiya, har ya yi kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayinsa, ba kuwa shi kaɗai ba, har ni ma, don kada in yi baƙin ciki a kan baƙin ciki.

28 Saboda haka na ɗokanta ƙwarai in turo shi domin ku yi farin cikin sāke ganinsa, ni kuma in rage baƙin cikina.

29 Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane,

30 domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.

Categories
FILIB

FILIB 3

Adalci Mai Gaskiya

1 A ƙarshe kuma ‘yan’uwa, ku yi farin ciki da Ubangiji. Sāke rubuto muku waɗannan abubuwa bai gundure ni ba, ga shi kuwa, domin lafiyarku ne.

2 Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da mugayen ma’aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan jikin nan!

3 Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta wurin Ruhu, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba mu kuma dogara da al’amuran ganin ido,

4 ko da yake ni ina iya dogara da al’amuran ganin ido, in dai nake so. In kuma akwai wanda yake tsammani yana iya dogara ga al’amuran ganin ido, to, ni na fi shi.

5 An yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Biliyaminu, Ba’ibrane ɗan Ibraniyawa, bisa ga Shari’a kuwa ni Bafarisiye ne,

6 a wajen himma kuwa mai tsananta wa Ikkilisiya ne ni, wajen aikin adalci kuwa bisa ga tafarkin Shari’a, marar abin zargi nake.

7 Amma dai kowace irin riba na taɓa ci, na ɗauka hasara ce saboda Almasihu.

8 Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yă zama nawa,

9 a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina ba, wanda ya danganta da bin Shari’a, sai dai da adalcin nan wanda yake tsirowa daga bangaskiya ga Almasihu, wato, da adalcin nan wanda yake samuwa daga Allah ta wurin bangaskiya.

10 Muradina ke nan, in san Almasihu, in san ikon tashinsa daga matattu, in yi tarayya da shi a shan wuyarsa, in kuma zama kamarsa a wajen mutuwarsa,

11 domin ta ko ƙaƙa in kai ga tashin nan daga matattu.

Nacewa Gaba Gaba zuwa Manufar

12 Ba cewa, na riga na kai ga waɗannan ba ne, ko kuwa na zama kammalalle, a’a. sai dai ina nacewa ne, in riƙi abin nan da Almasihu Yesu ma ya riƙe ni saboda shi.

13 Ya ‘yan’uwa, ban ɗauka a kan cewa na riga na riƙi abin ba, amma abu guda kam ina yi, ina mantawa da abin da yake baya, ina kutsawa zuwa ga abin da yake gaba.

14 Ina nacewa gaba gaba zuwa manufar nan, domin in sami ladar kiran nan zuwa sama, da Allah ya yi mini ta wurin Almasihu Yesu.

15 Saboda haka ɗaukacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra’ayi. In kuwa a game da wani abu ra’ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.

16 Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.

17 Ya ku ‘yan’uwa, ku yi koyi da ni dukanku baki ɗaya, ku kuma dubi waɗanda zamansu yake daidai da gurbin da muka bar muku.

18 Domin da yawa waɗanda na sha gaya muku, yanzu kuma nake gaya muku, har da hawaye, suna bin Yesu, in ji su, amma su magabtan gicciyen Almasihu ne.

19 Ƙarshensu hallaka ne, Allahnsu ciki ne, rashin kunyarsu ita ce abar taƙamarsu, sun ƙwallafa ransu a kan al’amuran duniya.

20 Mu kuwa ‘yan Mulkin Sama ne, daga can ne kuma muke ɗokin zuwan Mai Ceto, Ubangiji Yesu Almasihu,

21 wanda zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, ya mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka, da ikon nan nasa na sarayar da dukkan abubuwa a gare shi.

Categories
FILIB

FILIB 4

Ku Yi Farin Ciki da Ubangiji

1 Saboda haka ya ‘yan’uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.

2 Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.

3 Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al’amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.

4 A kullum ku yi farin ciki da Ubangiji, har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki.

5 Bari kowa ya san jimirinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

6 Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roƙo, tare da gode wa Allah.

7 Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

Ku Yi Tunanin Waɗannan Abubuwa

8 Daga ƙarshe kuma, ‘yan’uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani.

9 Abin da kuka koya, kuka yi na’am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah mai zartar da salama zai kasance tare da ku.

Tabbatarwa da Kyautar da Filibiyawa Suka Aika

10 Na yi farin ciki da Ubangiji ƙwarai da yake a yanzu kam, kularku gare ni ta farfaɗo, ko dā ma kuna kula da ni, dama ce ba ku samu ba.

11 Ba cewa, ina kukan rashi ba ne, domin na koyi yadda zan zauna da wadar zuci a cikin kowane irin hali da nake.

12 Na san yadda zan yi in yi zaman ƙunci, na kuma san yadda zan yi in yi zaman yalwa. A kowane irin hali duka na horu da ƙoshi da yunwa, yalwa da rashi.

13 Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.

14 Amma kuwa kun kyauta da kuka taya ni cikin ƙuntatata.

15 Ku kuma Filibiyawa, ku kanku kun sani tun da aka fara yin bishara, sa’ad da na bar ƙasar Makidoniya, ba wata ikkilisiyar da ta yi tarayya da ni wajen hidimar bayarwa da karɓa, sai dai ku kaɗai.

16 Ko sa’ad da nake Tasalonika ma, kun aiko mini da taimako ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba.

17 Ba cewa, don ina neman kyautarku ba ne, a’a, nemar muku amfani nake yi, a ƙara a kan ribarku.

18 An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.

19 Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu.

20 Ɗaukaka tā tabbata ga Allahnmu, Ubanmu, har abada abadin. Amin! Amin!

Gaisuwa

21 Ku gai da kowane tsattsarka cikin Almasihu Yesu. ‘Yan’uwan da suke tare da ni suna gai da ku.

22 Dukan tsarkaka suna gai da ku, tun ba ma na fadar Kaisar ba.

23 Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.

Categories
KOL

KOL 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, tare da Timoti, ɗan’uwanmu,

2 zuwa ga tsarkaka da amintattun ‘yan’uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi.

Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.

Addu’ar Bulus domin Kolosiyawa Masu Bin Almasihu

3 A kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa’ad da muke yi muku addu’a,

4 saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,

5 saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,

6 wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.

7 Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,

8 ya kuma sanasshe mu ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.

9 Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu’a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu,

10 domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.

11 Allah yă dai ƙarfafa ku da matuƙar ƙarfi bisa ga ƙarfin ɗaukakarsa, domin ku jure matuƙa a game da haƙuri da farin ciki,

12 kuna gode wa Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gādon tsarkakan da suke a cikin haske.

13 Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,

14 wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato, gafarar zunubanmu.

Cikar Allah

15 Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba,

16 don ta gare shi ne aka halicci dukkan kome, abubuwan da suke a sama da abubuwan da suke a ƙasa, masu ganuwa da marasa ganuwa, ko kursiyai, ko masu mulki, ko masarauta, ko masu iko, wato, dukkan abubuwa an halicce su ne ta wurinsa, shi ne kuma makomarsu.

17 Shi ne a gaba da dukkan abubuwa, dukkan abubuwa kuma shi ne yake riƙe da su.

18 Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici.

19 A gare shi dukkan cikar Allah ta tabbata, domin Allah yana farin ciki da haka,

20 da nufin ta wurinsa, Allah yă sulhunta dukkan abubuwa da shi kansa, na ƙasa ko na sama, yana ƙulla zumunci ta wurin jininsa na gicciye.

21 Ku kuma dā a rabe kuke da Allah, maƙiyansa a zuci, masu mugun aiki.

22 Amma a yanzu ya sulhunta ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato, ta wurin mutuwarsa, domin ya miƙa ku tsarkakakku, marasa aibu, marasa abin zargi kuma a gabansa.

23 Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.

Hidimar Bulus zuwa ga Ikilisiya

24 To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,

25 wadda na zama mai hidimarta bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da Maganar Allah sosai,

26 wato, asirin nan da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, amma a yanzu an bayyana shi ga tsarkakansa.

27 Su ne Allah ya so ya sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Almasihu a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.

28 Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu.

29 Saboda wannan nake shan wahala, nake fama da matuƙar himma, wadda yake sa mini ta ƙarfin ikonsa.

Categories
KOL

KOL 2

1 To, ina so ku san irin yawan shan faman da nake yi dominku, da waɗanda suke a Lawudikiya, da kuma duk waɗanda ba su taɓa ganina ba.

2 Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu,

3 wanda shi ne taska, wato maɓoyar dukkan mafifitan hikima da sani.

4 Na faɗi wannan ne don kada kowa ya hilace ku da maganar yaudara.

5 Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.

6 Da yake kun yi na’am da Almasihu Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya a gare shi,

7 kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.

Dukkan Cikar Rai ga Almasihu Take

8 Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al’adar mutane kawai, wato, bisa ga al’adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.

9 Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata.

10 A gare shi ne aka kammala ku, wanda yake shi ne shugaban dukkan sarauta da iko.

11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Almasihu ya yi muku ce, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.

12 An kuma binne ku tare da shi a wajen baftisma, inda kuma aka tashe ku tare da shi saboda bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.

13 Ku kuma da kuke matattu saboda laifofinku, marasa kaciya ta jiki, Allah ya raya ku tare da Almasihu, ya yafe mana dukkan laifofinmu,

14 ya kuma yanke igiyar nan ta Shari’a da ta ɗaure mu da dokokinta, ya ɗauke ta, ya kafe ta da ƙusa a jikin gicciyensa.

15 Ya ƙwace makaman masarauta da na masu iko, ya kunyata su a fili, da ya yi nasara a kansu a kan gicciyen.

Ku Ƙwallafa Ranku a kan Abubuwan da Suke a Sama

16 Saboda haka, kada ku damu in wani ya zarge ku a kan abin da kuke ci, ko abin da kuke sha, ko kuwa kan rashin kiyayewar wani idi, ko tsayawar wata, ko Asabar.

17 Waɗannan kam, isharori ne kawai na abin da zai auku, amma Almasihu shi ne ainihinsu.

18 Kada ku yarda kowane mutum ya ɓata ku, da cewa shi wani abu ne saboda, ya ga wahayi, ya kuma lazamta da yin tawali’un ƙarya, in ji shi kuma yana yi wa mala’iku sujada. Irin wannan mutum kumbura kansa yake yi ba dalili, sai ta son zuciya irin na halin mutuntaka,

19 bai kuwa manne wa kan ba, wanda ta gare shi ne dukkan jiki yake amfana, yake kuma a haɗe, ta wurin gaɓoɓi da jijiyoyi, yake kuma girma da girman da Allah yake sawa.

20 Idan mutuwarku tare da Almasihu ta ‘yanta ku daga al’adun duniyar nan, me ya sa kuke zama har yanzu kamar ku na duniya ne? Don me kuke bin dokokin da aka yi bisa ga umarnin ‘yan adam da koyarwarsu,

21 kamar su, “Kada ka kama, kada ka ɗanɗana, kada ka taɓa”?

22 (Wato, ana nufin abubuwan da, in an ci su sukan ruɓa duka).

23 Irin waɗannan dokoki kam, lalle suna da’awar hikima ta wajen yin ibadar da aka ƙago, ta wurin yin tawali’un ƙarya da kuma wahalar da jiki, amma ko ɗaya ba su da wata daraja ga sarrafar halin mutuntaka.

Categories
KOL

KOL 3

1 To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah.

2 Ku ƙwallafa ranku a kan abubuwan da suke Sama, ba a kan abubuwan da suke a ƙasa ba.

3 Gama kun mutu, ranku kuwa a ɓoye yake a gun Almasihu cikin Allah.

4 Sa’ad da Almasihu wanda yake shi ne ranmu ya bayyana, sai ku ma ku bayyana tare da shi a cikin ɗaukaka.

Tsohon Rai da Sabon Rai

5 Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha’awace-sha’wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha’awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.

6 Saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake sauka a kan kangararru.

7 A dā kuna bin waɗannan sa’ad da suke jiki a gare ku.

8 Amma yanzu sai ku yar da duk waɗannan ma, wato fushi, da hasala, da ƙeta, da yanke, da alfasha.

9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun yar da halinku na dā, da ayyukansa,

10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

11 A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba’al’umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.

12 Saboda haka, sai ku ɗauki halin tausayi, da kirki, da tawali’u, da salihanci, da haƙuri, idan ku zaɓaɓɓu ne na Allah, tsarkaka, ƙaunatattu,

13 kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma sai ku yafe.

14 Fiye da waɗannan duka, ku ɗau halin ƙauna, wadda dukkan kammala take ƙulluwa a cikinta.

15 Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.

16 Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.

17 Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.

Zaman Dacewa na Sabon Rai

18 Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji.

19 Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kada kuma ku yi musu kaushin hali.

20 Ku ‘ya’ya, ku yi wa iyayenku biyayya ta kowane hali, domin haka Ubangiji yake so.

21 Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa ‘ya’yanku, domin kada su karai.

22 Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.

23 Kome za ku yi, ku yi shi da himma kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba,

24 da yake kun sani Ubangiji zai ba ku gādo sakamakonku. Ubangiji Almasihu fa kuke bauta wa!

25 Mai mugun aiki kuwa za a sāka masa da mugun aikin da ya yi, babu kuma tāra.