Categories
KOL

KOL 4

1 Ku iyayengiji kuma, ku riƙi bayinku da gaskiya da daidaita, da yake kun sani ku ma kuna da Ubangiji a Sama.

2 Ku lazamci yin addu’a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah,

3 mu ma ku yi mana addu’a Allah ya buɗe mana hanyar yin Maganarsa, mu sanar da asirin Almasihu, wanda saboda shi ne nake a ɗaure,

4 domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.

5 Ku tafiyar da al’amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci.

6 A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.

Gaisuwa

7 Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan’uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji.

8 Na aiko shi a gare ku musamman, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.

9 Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan’uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.

10 Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.

11 Yasuwa kuma da ake kira Yustus yana gaishe ku. Wato, cikin abokan aikina ga Mulkin Allah, waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya.

12 Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu’a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.

13 Na shaide shi, lalle ya yi muku aiki ƙwarai da gaske, da kuma waɗanda suke na Lawudikiya da na Hirafolis.

14 Luka, ƙaunataccen likitan nan, da Dimas suna gaishe ku.

15 A gayar mini da ‘yan’uwa na Lawudikiya, da kuma Nimfa da ikilisiyar da take taruwa a gidanta.

16 Sa’ad da aka karanta wasiƙar nan a gabanku, ku sa a karanta ta kuma a gaban ikilisiyar da take a Lawudikiya, ku kuma ku karanta tasu, wato ta Lawudikiyawa.

17 Ku kuma faɗa wa Arkibus ya mai da hankali ya cika hidimar da Ubangiji ya sa shi.

18 Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna. Ku tuna da ɗaurina. Alheri yă tabbata a gare ku.

Categories
1 TAS

1 TAS 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah uba da Ubangiji Yesu Almasihu.

Alheri da salama su tabbata a gare ku.

Bangaskiyar Tasalonikawa da Irin Zamansu

2 A kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku a cikin addu’armu,

3 ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.

4 Domin mun sani, ‘yan’uwa, ƙaunatattu na Allah, shi ya zaɓe ku,

5 domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana,

6 har kuka zama masu koyi da mu, da kuma Ubangiji, kuka kuma karɓi Maganar Allah game da farin cikin da Ruhu Mai Tsarki yake sawa, ko da yake ta jawo muku tsananin wahala.

7 Ku ma har kuka zama abin koyi ga dukan masu ba da gaskiya a ƙasar Makidoniya da ta Akaya.

8 Domin daga gare ku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko’ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana, ba sai lalle mun faɗa ba.

9 Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,

10 ku kuma saurari komowar Ɗansa daga Sama, wanda ya tasa daga matattu, wato Yesu, mai kuɓutar da mu daga fushin nan mai zuwa.

Categories
1 TAS

1 TAS 2

Hidimar Bulus a Tasalonika

1 Ai, ku da kanku kun sani, ‘yan’uwa, ziyartarku da muka yi, ba a banza take ba.

2 Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.

3 Ai, gargaɗin da muke yi muku babu bauɗewa ko munafunci a ciki, balle yaudara,

4 sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu, ya damƙa mana amanar bishara, haka muke sanar da ita, ba domin mu faranta wa mutane rai ba, sai dai domin mu faranta wa Allah, shi da yake jarraba zukatanmu.

5 Yadda kuka sani, ba mu taɓa yin daɗin baki ko kwaɗayi ba. Allah kuwa shi ne shaida.

6 Ba mu kuwa taɓa neman girma ga mutane ba, ko a gare ku, ko ga waɗansu, ko da yake da muna so, da mun mori ikon nan namu na manzannin Almasihu.

7 Amma mun nuna taushin hali a cikinku, kamar yadda mai goyo take kula da goyonta.

8 Saboda kuma muna Kaunarku ƙwarai da gaske ne shi ya sa muke jin daɗin ba da har rayukanmu ma saboda ku, ba yi muku bisharar Allah kaɗai ba, don kun shiga ranmu da gaske.

9 Ya ku ‘yan’uwa, kuna iya tunawa da wahala da famar da muka sha, har muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku, duk sa’ad da muke yi muku bisharar Allah.

10 Ku shaidu ne, haka kuma Allah, game da irin halin da muka nuna muku, ku masu ba da gaskiya, wato halin tsarki da na adalci da na rashin aibu.

11 Domin kun san yadda muka yi wa kowannenku gargaɗi kamar uba da ‘ya’yansa ne, muna ta’azantar da ku, muna kuma ƙarfafa muku umarnin, cewa

12 ku yi zaman da ya cancanci bautar Allah, wanda yake kiranku ga mulkinsa da ɗaukakarsa.

13 Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa’ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.

14 ‘Yan’uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da suke na Almasihu Yesu, waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,

15 waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa, suka kuma kore mu, ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuma da dukan mutane,

16 suna hana mu yi wa al’ummai wa’azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.

Nufin Bulus Ya Sāke Ziyartar Ikkilisiya

17 Ya ku ‘yan’uwa, ko da yake mun yi kewarku saboda an raba mu a ɗan lokaci kaɗan, duk da haka kuna cikin zukatanmu, mun kuwa ƙara ɗokanta mu gan ku ido da ido, matuƙar ɗoki.

18 Mun dai yi niyyar zuwa wurinku, ni Bulus, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma Shaidan ya hana.

19 Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba?

20 Ai, ku ne abin taƙamarmu, da abin farin cikinmu.

Categories
1 TAS

1 TAS 3

1 Saboda haka, da muka kasa daurewa, sai muka ga ya kyautu a bar mu a Atina mu kaɗai,

2 muka kuma aiki Timoti ɗan’uwanmu, bawan Allah kuma na al’amarin bisharar Almasihu, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku a kan al’amarin bangaskiyarku,

3 don kada kowa ya raurawa a cikin tsananin wahalar nan. Ai, ku kanku kun sani an nufe mu da haka ne.

4 Domin dā ma sa’ad da muke tare, mun gaya muku tun da wuri, cewa za mu sha wahala. Haka kuwa ya auku, kamar yadda kuka sani.

5 Saboda haka, ni ma da na kasa daurewa, sai na aika in sami labarin bangaskiyarku, da fatan kada ya zamana mai ruɗin nan ya riga ya ruɗe ku, famarmu kuma yă zama banza.

6 Amma ga shi, a yanzu da Timoti ya dawo daga wurinku, ya yi mana albishir a kan bangaskiyarku da ƙaunarku, da kuma yadda kuke tunawa da mu da alheri a koyaushe, har kuna begen ganinmu, kamar yadda mu ma muke yi.

7 Saboda haka ‘yan’uwa, cikin dukan wahala da ƙuncin da muka sha, an sanyaya mana zuciya a game da ku, albarkacin bangaskiyarku.

8 A yanzu kam a raye muke, in dai kun tsaya ga Ubangiji.

9 Wace irin godiya za mu yi wa Allah saboda ku, a kan matuƙar farin cikin da muke yi a gaban Allahnmu ta dalilinku!

10 Dare da rana muna nacin addu’a ƙwarai mu sami ganinku ido da ido, mu kuma cikasa abin da ya gaza wajen bangaskiyarku.

11 Muna fata dai Allahnmu, ubanmu, shi kansa, da kuma Ubangijinmu Yesu, ya kai mu gare ku.

12 Ku kuma, Ubangiji ya sa ku ƙaru, ku kuma yalwata da ƙaunar juna da dukan mutane, kamar yadda muke yi muku,

13 har ya tsai da zukatanku ku zama marasa abin zargi cikin tsarki a gaban Allahnmu, Ubanmu, a ranar komowar Ubangijinmu Yesu, tare da dukan tsarkakansa.

Categories
1 TAS

1 TAS 4

Zaman da Ya Dace a Gaban Allah

1 Daga ƙarshe kuma ‘yan’uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,

2 domin kun san umarnin nan da muka yi muku da iznin Ubangiji Yesu.

3 Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,

4 kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,

5 ba ta muguwar sha’awa ba, yadda al’ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.

6 A cikin wannan al’amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan’uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.

7 Ai, ba a zaman ƙazanta ne Allah ya kira mu ba, amma ga zaman tsarki ne.

8 Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

9 A game da ƙaunar ‘yan’uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.

10 Hakika kuwa kuna ƙaunar dukan ‘yan’uwa a duk ƙasar Makidoniya. Sai dai muna muku gargaɗi, ‘yan’uwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,

11 kuna himmantuwa ga zaman lafiya, kuna kula da sha’anin gabanku kawai, kuna kuma aiki da hannunku, kamar yadda muka umarce ku,

12 domin ku zama masu mutunci ga waɗanda ba masu bi ba, kada kuma ku rataya a jikin kowa.

Matattu da Waɗanda Suke a Raye a Zuwan Ubangiji

13 Amma ‘yan’uwa, ba mu so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙin ciki kamar yadda sauran suke yi, marasa bege.

14 Tun da muka gaskata Yesu ya mutu, ya kuwa tashi, haka kuma albarkacin Yesu, Allah zai kawo waɗanda suka yi barci su zo tare da shi.

15 Muna kuwa shaida muku bisa ga faɗar Ubangiji, cewa mu da muka wanzu, muke kuma a raye har ya zuwa komowar Ubangiji ko kaɗan ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba,

16 domin Ubangiji kansa ma zai sauko daga Sama, da kira mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika, da kuma busar ƙahon Allah. Waɗanda suka mutu suna na Almasihu, su ne za fara tashi,

17 sa’an nan sai mu da muka wanzu, muke a raye, za a ɗauke mu tare da su ta cikin gajimare, mu sadu da Ubangiji a sararin sama, sai kuma kullum mu kasance tare da Ubangiji.

18 Saboda haka, sai ku yi wa juna ta’aziyya da wannan magana.

Categories
1 TAS

1 TAS 5

Ku Zauna a Faɗake don Zuwan Ubangiji

1 Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ba lalle sai an rubuto muku kome ba.

2 Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.

3 Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.

4 Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, ‘yan’uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo.

5 Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.

6 Ashe, saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa.

7 Don masu barci da daddare suke barci, masu sha su bugu ma da daddare suke sha su bugu.

8 Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu.

9 Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu,

10 wanda ya mutu saboda mu, domin ko muna a raye, ko muna barci, mu zama muna tare da shi.

11 Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.

Gargaɗi da kuma Gaisuwa

12 Amma muna roƙonku ‘yan’uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda suke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi.

13 Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.

14 Muna kuma yi muku gargaɗi, ‘yan’uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.

15 Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane.

16 Ku riƙa yin farin ciki a kullum.

17 Ku riƙa yin addu’a ba fāsawa.

18 Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.

19 Kada ku danne maganar Ruhu.

20 Kada ku raina annabci,

21 sai dai ku jarraba kome, ku riƙi abin da yake nagari kankan.

22 Ku yi nesa da kowace irin mugunta.

23 Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

24 Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.

25 Ya ku ‘yan’uwa, ku yi mana addu’a.

26 Ku gai da dukkan ‘yan’uwa da tsattsarkar sumba.

27 Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan ‘yan’uwa wasiƙar nan.

28 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.

Categories
2 TAS

2 TAS 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.

2 Alheri da salama na Allah Uba, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Bayyanar Almasihu don Yin Hukunci

3 Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, ‘yan’uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.

4 Saboda haka, mu kanmu ma taƙama muke yi da ku a cikin ikilisiyoyin Allah, saboda jimirinku, da bangaskiyarku a cikin yawan tsananin da kuke sha, da ƙuncin da kuke a ciki.

5 Wannan kuwa ita ce tabbatar hukunci mai adalci na Allah, domin a lasafta ku a cikin waɗanda suka cancanci zama a Mulkin Allah, wanda kuke shan wuya dominsa,

6 domin kuwa Allah ya ga adalci ne, yă yi sakamokon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku,

7 yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala’ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,

8 yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.

9 Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa,

10 wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al’ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.

11 Da wannan maƙasudi, a kullum muke yi muku addu’a, Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta wurin ƙarfin ikonsa,

12 don a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu.

Categories
2 TAS

2 TAS 2

Sarkin Tawaye

1 To, a game da komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma taruwarmu mu sadu da shi, muna roƙonku ‘yan’uwa,

2 kada ku yi saurin jijiguwa a zukatanku, ko kuwa hankalinku yă tashi, saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu suke, cewa ranar Ubangiji ta zo.

3 Kada ku yarda kowa yă yaudare ku ko ta halin ƙaƙa, domin wannan rana ba za ta zo ba, sai an yi fanɗarewar nan, sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato, hallakakken nan.

4 Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.

5 Ashe, ba ku tuna ba, nakan gaya muku haka tun muna tare?

6 To, a yanzu dai kun san abin da yake tare shi, don kada ya bayyana kafin lokacinsa.

7 Ko a yanzu ma tawayen nan, wanda ba shi fahimtuwa, an fara shi, amma farawar abin da zai faru, sai an ɗauke wanda yake hana shi tukuna.

8 A sa’an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.

9 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al’ajabi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri iri,

10 yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto.

11 Saboda haka, Allah zai auko musu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya,

12 don duk a hukunta waɗanda suka ƙi gaskata gaskiya, suke kuma jin daɗin mugunta.

Ya Zaɓe Ku Ku Sami Ceto

13 Ya ku ‘yan’uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya.

14 Domin wannan maƙasudi ya kira ku, ta wurin bishararmu, domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

15 Saboda haka, ‘yan’uwa, sai ku dage, ku kuma riƙi ka’idodin da muka koya muku kankan, ko da baka ko ta wurin wasiƙa.

16 To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta’aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,

17 yă ta’azantar da ku, ya kuma ƙarfafa ku ga yin kowane kyakkyawan aiki da magana.

Categories
2 TAS

2 TAS 3

Addu’a Dominmu

1 Daga ƙarshe kuma ‘yan’uwa, ku yi mana addu’a, Maganar Ubangiji ta yi saurin yaɗuwa, ta sami ɗaukaka, kamar yadda ta samu a gare ku,

2 a kuma cece mu daga fanɗararrun mutane, mugaye. Don ba duka ne suke da bangaskiya ba.

3 Amma Ubangiji mai alkawari ne, zai kuwa kafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan.

4 Mun kuma amince da ku a game da Ubangiji, cewa kuna bin umarnin da muka yi muku, za ku kuma riƙa bi.

5 Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunar nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.

Wajibi Ne a Yi Aiki

6 To, ‘yan’uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha’anin kowane ɗan’uwa malalaci, wanda ba ya bin ka’idodin da kuka samu a wurinmu.

7 Ai, ku kanku kun san yadda ya kamata ku yi koyi da mu, domin sa’ad da muke a tare, ba mu nuna muku lalaci ba,

8 ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nawaita wa kowane ɗayanku.

9 Ba don ba mu da halaliya a wurinku ba ne, a’a, sai dai don mu zama abin misali a gare ku kawai, don ku yi koyi da mu.

10 Ai, ko dā ma, sa’ad da muke a tare, mun yi muku wannan umarni, cewa duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.

11 Gama mun ji labari cewa waɗansunku malalata ne kawai, ba sa aikin kome, masu shisshigi ne kurum.

12 To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki da natsuwa, suna ci da kansu.

13 Amma ku ‘yan’uwa, kada ku gaji da yin aiki nagari.

14 In wani ya ƙi bin abin da muka faɗa a wasiƙar nan, sai fa ku lura da shi, kada ma ku yi cuɗanya da shi, don yă kunyata.

15 Amma kada ku ɗauke shi a kan abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a kan shi ɗan’uwa ne.

Sa Albarka

16 To, Ubangiji kansa, mai zartar da salama, yă ba ku salama a koyaushe a kowane hali. Ubangiji ya kasance tare da ku duka.

17 Ni Bulus, ni nake rubuto wannan Gaisuwa da hannuna. Ita ce kuwa shaidar kowace wasiƙata. Rubutun hannuna ke nan.

18 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku duka.

Categories
1 TIM

1 TIM 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai Cetonmu, da kuma na Almasihu Yesu abin begenmu,

2 zuwa ga Timoti, ɗana na hakika, ta wajen bangaskiya.

Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.

Faɗaka a kan Wata Koyarwa Dabam

3 Kamar yadda na roƙe ka, ka dakata a Afisa sa’ad da za ni ƙasar Makidoniya, ka gargaɗi waɗansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam,

4 kada kuma su ɓata zarafinsu a wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda sukan haddasa gardandami, a maimakon riƙon amanar al’amuran Allah da bangaskiya.

5 Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.

6 Waɗansu sun kauce wa waɗannan al’amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza.

7 Suna burin zama masanan Attaura, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle matsalar da suke taƙamar haƙiƙicewa a kai.

8 To, mun san Shari’a aba ce mai kyau, in mutum ya yi aiki da ita yadda ya wajaba,

9 yana kuma tunawa, cewa ita Shari’a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,

10 da fasikai, da masu luɗu, da masu sace mutane, da maƙaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya sāɓa sahihiyar koyarwar nan,

11 bisa ga bishara mai daraja ta Allah abar yabo, wadda aka danƙa mini.

Godiyar Bulus domin Jinƙai

12 Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijinmu, wanda ya ƙarfafa ni, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa,

13 ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya.

14 Alherin Ubangijinmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, a game da bangaskiya, da kuma ƙaunar da take ga Almasihu Yesu.

15 Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.

16 Duk da haka an yi mini jinƙai musamman, don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda a nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami.

17 Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.

18 Na danƙa maka wannan umarni, ya ɗana Timoti, bisa ga annabce-annabcen da dā aka faɗa a kanka, domin ka ƙarfafu ta wurinsu, ka yi yaƙi mai kyau,

19 kana riƙe da bangaskiya da lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.

20 Cikinsu har da Himinayas da Askandari, waɗanda na miƙa wa Shaiɗan, don su horo su bar yin sāɓo.