Categories
1 TIM

1 TIM 2

Gargaɗi a kan Addu’a

1 Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu’a, ana godo, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane,

2 da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan maƙamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.

3 Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu,

4 wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.

5 Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum,

6 wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa.

7 Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma (gasikya nake faɗa, ba ƙarya ba), mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

8 Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu’a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba.

9 Mata kuma su riƙa sa tufafin da suka dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu’ulu’u, ko tufafi masu tsada ba,

10 sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadarsu.

11 Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya.

12 Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru.

13 Ai, Adamu aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u.

14 Ba kuma Adamu aka yaudara ba, amma matar ce aka yaudara, har ta keta umarni.

15 Duk da haka kuwa, ta wurin haifar ‘ya’ya sai ta kai ga kammala, muddin ta nace wa bangaskiya, da ƙauna, da zama a tsarkake, da kuma kamunkai.

Categories
1 TIM

1 TIM 3

Sharuɗan Zama Shugabannin Ikkilisiya

1 Maganar nan tabbatacciya ce, cewa duk mai burin aikin kula da ikkilisiya, yana burin yin aiki mai kyau ke nan.

2 To, lalle ne mai kula da ikkilisiya yă zama marar abin zargi, yă zama mai mace ɗaya, mai kamunkai, natsattse, kintsattse, mai yi wa baƙi alheri, gwanin koyarwa kuma.

3 Ba mashayi ba, ba mai saurin dūka ba, amma salihi, ba kuma mai husuma ba, ba kuwa mai son kuɗi ba.

4 Lalle ne yă iya sarrafa iyalinsa da kyau, yana kuma kula da ‘ya’yansa, su yi biyayya da matuƙar ladabi.

5 Don kuwa in mutum bai san yadda zai sarrafa iyalinsa ba, ta ƙaƙa zai iya kula da ikkilisiyar Allah?

6 Lalle ne kuma, kada yă zama sabon tuba, don kada yă daga kai yă burmu a cikin hukuncin da aka yi wa Iblis.

7 Banda haka kuma, lalle ne yă zama mai mutunci ga waɗanda ba su a cikinmu, don kada yă zama abin zargi, yă faɗa a cikin tarkon Iblis.

Sharuɗan Zama Mai Hidimar Ikkilisiya

8 Haka kuma masu hidimar ikkilisiya, lalle ne su zama natsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin ƙazamar riba.

9 Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta.

10 Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar.

11 Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu aminci ta kowace hanya.

12 Masu hidima kuma su zama masu mata ɗaya ɗaya, masu sarrafa ‘ya’yansu da sauran iyalinsu da kyau.

13 Masu hidimar da suke aikinsu sosai, suna samar wa kansu kyakkyawan suna, da kuma ƙaƙƙarfar amincewa ga bangaskiyarsu ga Almasihu Yesu.

Asirin Addininmu

14 Ina sa zuciya in zo a wurinka ba da daɗewa ba, amma ina rubuto maka waɗannan abubuwa.

15 don in ya zamana na yi jinkiri, za ka san irin zaman da ya kamata a yi a jama’ar Allah, wadda take ita ce Ikkilisiyar Allah Rayayye, jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.

16 Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai,

An bayyana shi da jiki,

Ruhu ya nuna shi adali ne,

Mala’iku sun gan shi,

An yi wa al’ummai wa’azinsa,

An gaskata da shi a duniya,

An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.

Categories
1 TIM

1 TIM 4

Faɗi a kan Malaman Ƙarya

1 To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu,

2 ta wurin makircin waɗansu maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu lalas.

3 Su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.

4 Domin duk abin da Allah ya halitta kyakkyawa ne, kada kuma a ƙi kome muddin an karɓe shi da godiya,

5 gama an tsarkake shi ta wurin Maganar Allah da addu’a

Amintaccen Bawan Almasihu

6 In kana tuna wa ‘yan’uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau.

7 Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah.

8 Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.

9 Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum.

10 Saboda wannan maƙasudi muke wahala, muke ta fama, domin mun dogara ne ga Allah Rayayye, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman masu ba da gaskiya.

11 Ka yi umarni da waɗannan abubuwa, ka kuma koyar da su.

12 Kada ka yarda kowa yă raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka.

13 Kafin in zo, ka lazamci karanta wa mutane Littattafai, da yin gargaɗi, da kuma koyarwa.

14 Kada ka shagala da baiwar da aka yi maka, wadda aka ba ka ta wurin annabci, sa’ad da dattawan ikkilisiya suka ɗora maka hannu.

15 Ka himmantu ga waɗannan abubuwa, ka kuma lazamce su ƙwarai, don kowa yă ga ci gaban da kake yi.

16 Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, domin ta yin haka za ka ceci kanka da masu sauraronka.

Categories
1 TIM

1 TIM 5

Wajibi ga Juna

1 Kada ka tsauta wa dattijo, sai dai ka roƙe shi kamar mahaifinka. Samari kuma ka ɗauke su kamar ‘yan’uwanka,

2 tsofaffi mata kuma kamar uwayenka, ‘yan mata kuwa kamar ‘yan’uwanka, da matuƙar tsarkaka.

3 Ka girmama gwauraye mata, waɗanda ba sa da mataimaka.

4 In wata gwauruwa tana da ‘ya’ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.

5 Gwauruwa marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaici, ta dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu’a dare da rana.

6 Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye.

7 Ka umarce su a game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.

8 Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.

9 Kada a lasafta gwauruwa a cikin gwauraye, sai dai ta kai shekara sittin, ba ta yi aure fiye da ɗaya ba,

10 wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi ‘ya’ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.

11 Amma kada ka lasafta gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, a cikin gwaurayen, don in zuciyarsu ta kasa daurewa a game da wa’adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure,

12 hukunci yā kama su ke nan, tun da yake sun ta da wa’adinsu na farko.

13 Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba.

14 Saboda haka, ina so gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su tafiyar da al’amuran gida, kada su ba magabci hanyar zarginmu.

15 Gama waɗansu ma har sun bauɗe, sun bi Shaiɗan.

16 Duk mace mai bi, da take da dangi gwauraye mata, sai ta taimake su, kada a nauwaita wa ikkilisiya, don ikkilisiyar ta samu ta taimaki gwauraye marasa mataimaka.

17 Dattawan ikkilisiya da suke a riƙe da al’amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda suke fama da yin wa’azi da koyarwa ba.

18 Domin Nassi ya ce, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi sa’ad da yake sussuka.” Ya kuma ce, “Ma’aikaci ya cancanci ladarsa.”

19 Kada ka yarda in an kawo ƙarar wani dattijon ikkilisiya, sai dai da shaidu biyu ko uku.

20 Masu yin zunubi kuwa, sai ka tsawata musu a gaban dukkan jama’a, don saura su tsorata.

21 Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra.

22 Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanka a tsarkake.

23 A nan gaba ba ruwa kaɗai za ka sha ba, sai dai ka sha ruwan inabi kaɗan saboda cikinka, da kuma yawan laulayinka.

24 Zunuban waɗansu mutane a fili suke, tun ba a kai gaban shari’a ba. Zunuban waɗansu kuwa, sai daga baya suke bayyana.

25 Haka kuma, kyawawan ayyukan waɗansu a fili suke, waɗanda ba haka suke ba, ba za su tabbata a ɓoye ba.

Categories
1 TIM

1 TIM 6

1 Duk ɗaukacin masu igiyar bauta a wuyansu, su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci a girmama su matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwar nan.

2 Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su ‘yan’uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su.

Bin Allah da Wadar Zuci

Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu.

3 Duk wanda yake wata koyarwa dabam, bai kuwa yarda da sahihiyar maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwar da ta dace da bautar Allah ba,

4 girmankai ya ciccika shi ke nan, bai san kome ba, yana da muguwar jarabar gardama da jayayya a kan maganganu kawai, waɗanda suke jawo hassada, da husuma, da yanke, da mugayen zace-zace,

5 da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.

6 Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa.

7 Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba.

8 To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.

9 Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.

10 Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.

Famar Gaske saboda Bangaskiya

11 Amma, ya kai, bawan Allah, ka guje wa waɗannan abubuwa, ka dimanci aikin adalci, da bin Allah, da bangaskiya, da ƙauna, da jimiri, da kuma tawali’u.

12 Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa’ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.

13 Na gama ka da Allah mai raya kome, na kuma gama ka da Almasihu Yesu, wanda ya yi shaida, kyakkyawar shaidar nan, a gaban Buntus Bilatus,

14 ka bi umarninsa, ba tare da wani aibi ko zargi ba, har ya zuwa bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu,

15 wannan kuwa makaɗaicin mamallaki, abin yabo, Sarkin sarakuna. Ubangijin iyayengiji zai bayyana shi a lokacinsa.

16 Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.

17 Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.

18 Sai dai su yi nagarta da bijinta a wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri.

19 Ta haka suke kafa wa kansu kyakkyawan tushe don nan gaba, domin su riƙi rai wanda yake na hakika.

20 Ya Timoti, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun sāɓo na banza da wofi, da yawan musu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi.

21 Waɗansu kuwa, a garin taƙama, da haka har sun kauce wa bangaskiya.

Alheri yă tabbata a gare ku.

Categories
2 TIM

2 TIM 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, don sanar da alkawarin nan na rai wanda yake ga Almasihu Yesu,

2 zuwa ga Timoti ƙaunataccen ɗana.

Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.

Kada Ka Ji Kunya

3 Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa’ad da nake tunawa da kai a cikin addu’ata ba fāsawa.

4 Sa’ad da nake tunawa da hawayenka, nakan yi began ganinka dare da rana, domin in yi farin ciki matuƙa.

5 Ina tunawa da sahihiyar bangaskiyarka, wadda da farko take tare da kakarka Loyis, da mahaifiyarka Afiniki, a yanzu kuma na tabbata tana tare da kai.

6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwar nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗora maka hannuwana.

7 Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.

8 Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,

9 wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil’azal, a cikin Almasihu Yesu,

10 wadda a yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai Cetonmu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara.

11 A wannan bishara an sa ni mai wa’azi, da kuma manzonta, da mai koyarwarta kuma.

12 Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.

13 Ka yi koyi da sahihiyar maganar da ka ji daga gare ni, da bangaskiya da ƙauna da take ga Almasihu Yesu.

14 Kyakkyawan abin nan da aka ba ka amana, ka kiyaye shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, wanda yake zaune a zuciyarmu.

15 Ka dai sani duk waɗanda suke ƙasar Asiya sun juya mini baya, a cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas.

16 Ubangiji yă yi wa iyalin Onisifaras jinƙai, don sau da yawa yake sanyaya mini zuciya, bai kuwa ji kunyar ɗaurina da aka yi ba.

17 Har ma da ya zo Roma, sai ya neme ni ido a rufe, ya kuwa same ni.

18 Ubangiji ya yi masa jinƙai a waccan rana. Ka dai sani sarai yadda ya yi ɗawainiya mai yawa a Afisa.

Categories
2 TIM

2 TIM 2

Amintaccen Sojan Almasihu

1 Saboda haka, ya kai ɗana, sai ka ƙarfafa da alherin da yake ga Almasihu Yesu.

2 Abin da ka ji a guna a gaban shaidu masu yawa kuwa, sai ka danƙa wa amintattun mutane, waɗanda su ma za su koya wa waɗansu.

3 Kai kuma ka jure wa shan wuya, kana amintaccen sojan Almasihu Yesu.

4 Ai, ba sojan da yake a bakin dāga da ransa zai sarƙafe da sha’anin duniya, tun da yake burinsa shi ne yă faranta wa wanda ya ɗauke shi soja.

5 Mai wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ba zai sami ɗaukaka ba, sai ko ya bi dokokin wasan.

6 Ma’aikaci, ai, shi ya kamata yă fara cin amfanin gonar.

7 Ka yi tunani a kan abin da nake faɗa, Ubangiji kuwa zai ba ka fahimtar kome.

8 Ka tuna da Yesu Almasihu fa, shi da aka tashe shi daga matattu, na zuriyar Dawuda bisa ga bisharata,

9 wadda nake shan wuya saboda ita, har nake ɗaure kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.

10 Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.

11 Maganar nan tabbatacciya ce,

“In mun mutu tare da shi, za mu rayu ma tare da shi,

12 In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi,

In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,

13 In ba mu da aminci, shi kam ya tabbata mai aminci,

Domin ba zai yi musun kansa ba.”

Yardajjen Ma’aikaci

14 Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.

15 Ka himmantu, ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara Maganar gaskiya daidai.

16 Ka yi nesa da masu maganganun banza na sāɓo. Sai daɗa jan mutane zuwa ga rashin bin Allah suke yi,

17 maganarsu takan haɓaka kamar gyambo. A cikinsu har da Himinayas da Filitas,

18 waɗanda suka bauɗe wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da bangaskiyar waɗansu.

19 Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”

20 A babban gida, ba kayan zinariya da na azurfa ne kawai ba, har ma da na itace da na yumɓu, waɗansu don aikin ɗaukaka, waɗansu kuwa don ƙasƙantaccen aiki.

21 Kowa yă tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai zama ma’aikaci mai daraja, tsarkakakke, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.

22 Don haka, sai ka guje wa mugayen sha’awace-sha’awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.

23 Ka ƙi gardandamin banza marasa ma’ana, ka san lalle suna jawo husuma.

24 Bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa, gwanin koyarwa, mai haƙuri,

25 mai sa abokan hamayyarsa a kan hanya da tawali’u, ko Allah zai sa su tuba, su kai ga sanin gaskiya,

26 su kuɓuce wa tarkon Iblis, su bi nufin Allah, bayan da Iblis ya tsare su.

Categories
2 TIM

2 TIM 3

Halin Ƙarshen Zamani

1 Amma ka fahimta, a zamanin ƙarshe za a sha wuya ƙwarai.

2 Mutane za su zama masu sonkai, da masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu zagezage, da marasa bin iyayensu, da masu butulci, da marasa tsarkaka,

3 da marasa ƙauna, da masu riƙo a zuci, da masu yanke, da fajirai, da maƙetata, da maƙiyan nagarta,

4 da maciya amana, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah,

5 suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.

6 A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha’awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali,

7 kullum suna koyo, amma kullum sai su kāsa kaiwa ga sanin gaskiya.

8 Kamar yadda Yanisu da Yambirisu suka tayar wa Musa, haka mutanen nan kuma suke tayar wa gaskiya, mutane ne masu ɓataccen hankali ƙwarai, bangaskiyarsu kuwa ta banza ce.

9 Amma ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.

Gargaɗin Bulus ga Timoti na Ƙarshe

10 Kai kam, ka riga ka kiyaye koyarwata, da halina, da niyyata, da bangaskiyata, da haƙurina, da ƙaunata, da jimirina,

11 da kuma yawan tsanani, da wuyar da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutar da ni daga cikinsu duka.

12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna ga Almasihu Yesu, za su sha tsanani.

13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.

14 Amma kai kuwa, ka zauna a kan abin da ka koya, ka kuma haƙƙaƙe, gama ka san wurin waɗanda ka koye su,

15 da kuma yadda tun kana ɗan ƙaramin yaro ka san Littattafai masu tsarki, waɗanda suke koya maka hanyar samun ceto ta dalilin bangaskiya ga Almasihu Yesu.

16 Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci,

17 domin bawan Allah yă zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.

Categories
2 TIM

2 TIM 4

1 Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari’a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa,

2 ka yi wa’azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.

3 Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.

4 Za su toshe kunnensu ga jin tatsuniyoyi.

5 Kai kuwa, sai ka natsu a cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.

6 Ni fa tsiyaye ni ake yi kamar hadaya, lokacin ƙauracewata kuma ya gabato.

7 Na sha fama, famar gaske, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.

8 Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.

Waɗansu Umarnai

9 Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina da hanzari,

10 domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.

11 Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka ɗauko Markus ku zo tare, gama yana da amfani a gare ni a wajen yi mini hidima.

12 Tikikus kuwa na aike shi Afisa.

13 Sa’ad da za ka taho, ka zo da alkyabbar nan da na bari a wurin Karbus a Taruwasa, da kuma littattafan nan, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.

14 Iskandari maƙerin farfarun nan ya yi mini mugunta ƙwarai, Ubangiji zai yi masa sakayyar aikinsa.

15 Kai ma, ka mai da hankali da shi, gama ya hauri maganarmu, mummunan hauri.

16 A lokacin da na ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.

17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al’ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.

18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

Gaisuwa

19 Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras.

20 Aratas ya dakata a Koranti. Tarofimas kuwa na bar shi a Militas, ba shi da lafiya.

21 Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan ‘yan’uwa.

22 Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.

Categories
TIT

TIT 1

Gaisuwa

1 Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu,

2 duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil’azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,

3 ya kuwa bayyana maganarsa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa’azin da shi Allah Mai Cetonmu ya amince mini in yi, bisa ga umarninsa,

4 zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka.

Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.

Aikin Titus a Karita

5 Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al’amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikkilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka,

6 sai wanda ya kasance marar abin zargi, mai mace ɗaya, wanda ‘ya’yansa suke masu ba da gaskiya, waɗanda ba a zarginsu da aikin masha’a ko na kangara.

7 Lalle ne kuwa, kowane mai kula da ikkilisiya, da yake shi mai riƙon amana saboda Allah ne, yă zama marar abin zargi, ba mai taurinkai ba, ko mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai saurin dūka, ko mai kwaɗayin ƙazamar riba.

8 Amma yă kasance mai yi wa baƙi alheri, mai son abu nagari, natsattse, mai kirki, tsarkakakke, mai kamunkai,

9 mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.

10 Don kuwa akwai kangararrun mutane da yawa, da masu surutan banza, da masu ruɗi, tun ba ma ɗariƙar masu kaciyar nan ba.

11 Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama’a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.

12 Wani annabi na Karitawa ya ce, “Karitawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye, haɗamammu.”

13 Shaidar nan tasa kuwa gaskiya ce. Saboda haka, dai ka tsawata musu da gaske, domin su zama sahihai a wajen bangaskiya,

14 a maimakon su mai da hankali ga almarar Yahudawa, ko kuwa dokokin mutane masu ƙin gaskiya.

15 Ga masu tsarkin rai duk al’amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al’amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.

16 Suna cewa sun san Allah, amma suna sāɓa masa ta wurin aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani a wajen yin aiki nagari.