Categories
1 BIT

1 BIT 3

Hakkin Aure

1 Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,

2 don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku.

3 Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa,

4 sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali’u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.

5 Don dā ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu,

6 kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma ‘ya’yanta ne muddin kuna aiki nagari, ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.

7 Haka kuma, ku maza, ku yi zaman ɗa’a da matanku, kuna girmama su, da yake su ne raunana, gama ku abokan tarayya ne na Allah. Ku yi haka don kada wani abu ya hana ku yin addu’a tare.

Shan Wuya don Adalci

8 Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar ‘yan’uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali’u.

9 Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.

10 Domin,

“Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri,

Sai ya kame bakinsa daga ɓarna,

Ya kuma hana shi maganar yaudara.

11 Ya rabu da mugunta,

ya kama nagarta,

Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.

12 Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci,

Yana kuma sauraron roƙonsu.

Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”

13 To, wa zai cuce ku in kun himmantu a kan abin da yake nagari?

14 Amma ko da za ku sha wuya saboda aikata abin da yake daidai, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoronsu, kada kuma ku damu.

15 Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali’u da bangirma.

16 Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata.

17 Zai fi kyau a sha wuya ga yin abin da yake nagari, in haka nufin Allah ne, da a sha don yin abin da ba daidai ba.

18 Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.

19 Da ruhun ne kuma ya je ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku shela,

20 wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa’ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.

21 Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu,

22 wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala’iku da manyan mala’iku da masu iko suna binsa.

Categories
1 BIT

1 BIT 4

Amintaccen Mai Riƙon Amanar Alherin Allah

1 Tun da yake Almasihu ya sha wuya a jiki dominmu, sai ku ma ku ɗauki irin wannan ra’ayi. Ai, duk wanda ya sha wuya a jiki, ya daina aikata zunubi ke nan,

2 domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha’awar zuciya ba, sai dai nufin Allah.

3 Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al’ummai suke son yi, ya isa haka nan, wato zaman fajirci, da mugayen sha’awace-sha’awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama.

4 Suna mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, kuna zarmewa, kuna aikata masha’a irin tasu, har suna zaginku.

5 Amma lalle su ba da hujjojinsu ga wannan da yake a shirye ya yi wa rayayyu da matattu shari’a.

6 Shi ya sa aka yi bishara har ga matattu ma, waɗanda ko da yake an yi musu hukunci a cikin jiki kamar mutane, su samu su rayu a ruhu kamar Allah.

7 Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu’a.

8 Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.

9 Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba.

10 Duk baiwar da mutum ya samu, yă yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan’uwansa, a kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri iri ne.

11 Duk mai wa’azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al’amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

Shan Wuyar Kirista

12 Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa a gare ku.

13 Amma, muddin kuna tarayya da Almasihu a wajen shan wuyarsa, sai ku yi farin ciki, domin sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa, ku yi farin ciki da murna matuƙa.

14 Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah yā tabbata a gare ku.

15 Sai dai kada shan wuyar ko ɗaya daga cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi.

16 Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗaukaka Allah saboda wannan suna.

17 Don lokaci ya yi da za a fara shari’a ta kan jama’ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?

18 “In adali da ƙyar ya kuɓuta,

Me zai auku ga marar bin Allah da mai zunubi?”

19 Saboda haka, sai duk masu shan wuya bisa ga nufin Allah su danƙa ransu ga Mahalicci mai aminci suna aikata abin da yake daidai.

Categories
1 BIT

1 BIT 5

Ku Yi Kiwon Garken Allah

1 Don haka, ku dattawan ikkilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikkilisiya, ɗan’uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi,

2 ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma.

3 Kada ku nuna wa waɗanda suke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan.

4 Sa’ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa.

5 Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali’u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali’u alheri.”

6 Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari.

7 Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku.

8 Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame.

9 Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan bangaskiyarku, da yake kun san ‘yan’uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya.

10 Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.

11 Mulki yā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

Gaisuwa

12 Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan’uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi.

13 Ita da take a Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma, ɗana, Markus.

14 Ku gai da juna da sumbar ƙauna.

Salama tă tabbata a gare ku duka, ku na Almasihu.

Categories
2 BIT

2 BIT 1

Gaisuwa

1 Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.

2 Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu Ubangijinmu

Kiranku da Zaɓenku

3 Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa,

4 waɗanda kuma ta wurinsu ya yi mana baiwa da manyan alkawaransa masu ɗaukaka ƙwarai, domin ta wurin waɗannan ku zama masu tarayya da Allah a wajen ɗabi’arsa, da yake kun tsira daga ɓācin nan dake a duniya da muguwar sha’awa take haifa.

5 Saboda wannan dalili musamman, sai ku yi matuƙar himma, ku ƙara bangaskiyarku da halin kirki, halin kirki da sanin ya kamata,

6 sanin ya kamata da kamunkai, kamunkai da jimiri, jimiri da bin Allah,

7 bin Allah da son ‘yan’uwa, son ‘yan’uwa kuma da ƙauna.

8 In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

9 Domin duk wanda ya rasa halayen nan, to, makaho ne ko kuwa ganinsa dishi-dishi ne, ya kuma mance an tsarkake shi daga zunubansa na dā.

10 Saboda haka, ya ku ‘yan’uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Domin in kun bi waɗannan halaye, ba za ku fādi ba har abada.

11 Ta haka kuma, za a ba ku cikakken ‘yancin shiga madawwamin mulki na Ubangijinmu Mai Cetonmu Yesu Almasihu.

12 Don haka, lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da yake kun san su, kun kuma kahu a kan gaskiyar nan da kuke da ita.

13 A ganina daidai ne, muddin ina raye a cikin jikin nan, in riƙa faɗakar da ku ta hanyar tuni,

14 da yake na sani na yi kusan rabuwa da jikin nan nawa, kamar yadda Ubangijinmu Yesu Almasihu ya yi mini ishara.

15 Aniyata ce, a kowane lokaci ku iya tunawa da waɗannan abubuwa bayan ƙauracewata.

Ganin Ɗaukakarsa Muraran

16 Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa’ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran.

17 Domin sa’ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,”

18 mu ne muka ji muryar nan da aka saukar daga sama, don muna tare da shi a kan tsattsarkan Dutsen nan.

19 Har wa yau kuma, aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku, ku mai da hankali a gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranar nan, gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku.

20 Da farko dai, lalle ne ku fahimci wannan cewa, ba wani annabci a Littattafai da za a iya fassarawa ta ra’ayin mutum.

21 Domin ba wani annabcin da ya taɓa samuwa ta nufin mutum, sai dai mutane ne Ruhu Mai Tsarki yake izawa, Allah yana magana ta bakinsu.

Categories
2 BIT

2 BIT 2

Annabawan Ƙarya da Malaman Ƙarya

1 Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama’a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.

2 Da yawa kuwa za su bi fajircinsu, har za a kushe hanyar gaskiya saboda su.

3 Mahaɗantan malaman nan na ƙarya za su ribace ku da tsararrun labarunsu. An riga an yanke hukuncinsu tun dā, wanda zai hallaka su a shirye yake sosai.

4 Da yake Allah bai rangwanta wa mala’iku ba sa’ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,

5 tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa’azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa’ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,

6 da yake kuma ya mai da biranen Saduma da Gwamrata toka, ya yi musu hukuncin hallaka, ya mai da su abin ishara ga marasa bin Allah,

7 da yake kuma ya ceci Lutu adali, wanda fajircin kangararru ya baƙanta masa rai ƙwarai

8 (don kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci),

9 ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari’a,

10 tun ba waɗanda suka dulmuya a cikin muguwar sha’awa mai ƙazantarwa ba, suke kuma raina mulki.

Masu tsaurin ido ne su, masu taurin kai kuma, ba sa jin tsoron zagin masu ɗaukaka.

11 Amma kuwa mala’iku, ko da yake sun fi su ƙarfi da iko, duk da haka, ba su ɗora musu laifi da zage-zage a gaban Ubangiji.

12 Amma waɗannan mutane, kamar daddobi marasa hankali suke, masu bin abin da jikinsu ya ba su kawai, waɗanda aka haifa, don a kama a kashe, har suna kushen abubuwan da ba su fahinta ba, lalle kuwa za su hallaka a sanadin ɓacin nan nasu,

13 suna shan sakamakon muguntarsu. Sun ɗauka a kan jin daɗi ne a yi annashuwa da rana kata. Sun baƙanta, sun zama abin kunya. Sun dulmuya ga ciye-ciye da shaye-shaye, suna ta nishaɗi a cikinku.

14 Jarabar zina take a gare su, ba sa ƙoshi da yin zunubi. Suna yaudarar marasa kintsuwa. Sun ƙware da ƙwaɗayi. La’anannun iri!

15 Sun yar da miƙaƙƙiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal’amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta.

16 Amma an tsawata masa a kan laifinsa, har dabba marar baki ma ta yi magana kamar mutum, ta kwaɓi haukan annabin nan.

17 Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.

18 Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,

19 suna yi musu alkawarin ‘yanci, ga shi kuwa, su da kansu bayin zamba ne. Don mutum bawa ne na duk abin da ya rinjaye shi.

20 In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan.

21 Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa’an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki.

22 Ai kuwa, karin maganar nan na gaskiya ya dace da su cewa, “Kare ya cinye amansa,” da kuma, “Gursunar da aka yi wa wanka ta kome ga birgima cikin laka.”

Categories
2 BIT

2 BIT 3

Alkawarin Zuwan Ubangiji

1 Ya ƙaunatattuna, wannan ita ce wasiƙa ta biyu da na rubuto muku, a kowaccensu kuwa na faɗakar da sahihan zukatanku ta hanyar tuni.

2 Ina so ku tuna da yin faɗin annabawa tsarkaka, da kuma umarnin Ubangiji Mai Ceto ta bakin manzannin da suka zo muku.

3 Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna biye wa muguwar sha’awarsu,

4 suna cewa, “To, ina alkawarin dawowarsa? Ai, tun a lokacin da kakannin kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.”

5 Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa.

6 Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka.

7 Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari’a, a hallaka su.

8 Amma ya ku ƙaunatattuna kada ku goce wa magana gudar nan, cewa ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekara dubu ne, shekara dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.

9 Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma’anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.

10 Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa’an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.

11 Tun da yake duk abubuwan nan za a hallaka su haka, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi zaman tsarkaka masu ibada,

12 kuna sauraron ranar Allah, kuna gaggauta zuwanta! Da zuwanta kuwa za a kunna wa sammai wuta, su hallaka, dukkan abubuwa kuma da suke a cikinsu, wuta za ta narkar da su.

13 Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin summai da sabuwar ƙasa a inda adalci zai yi zamansa.

14 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, tun da kuke jiran waɗannan abubuwa, ku himmantu ya same ku marasa tabo, marasa aibu, masu zaman salama.

15 Ku ɗauki haƙurin Ubangijinmu, ceto ne. Haka ma, ƙaunataccen ɗan’uwanmu Bulus ya rubuto muku, bisa ga hikimar da aka ba shi,

16 yana magana a kan wannan, kamar yadda yake yi a dukan wasiƙunsa, akwai waɗansu abubuwa a cikin masu wuyar fahinta, waɗanda jahilai da marasa kintsuwa suke juya ma’anarsu, kamar yadda suke juya sauren Littattafai, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.

17 Don haka, ya ku ƙaunatatuna, da yake kun riga kun san haka, ku kula kada bauɗewar kangararru ta tafi da ku, har ku fāɗi daga matsayinku.

18 Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada. Amin! Amin!

Categories
1 YAH

1 YAH 1

Kalmar Rai

1 Shi da yake tun fil’azal yake nan, wanda muka ji, muka gani da idonmu, muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, a game da Kalmar Rai,

2 wannan Rai kuwa an bayyana shi, mu kuwa mun gani, muna ba da shaida, muna kuma sanar da ku Rai madawwamin nan wanda tun dā yake tare da Uba, aka kuwa bayyana shi gare mu,

3 to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu.

4 Muna kuma rubuto muku wannan ne domin farin cikinmu ya zama cikakke.

Allah Haske Ne

5 Wannan shi ne jawabin da muka ji a gunsa, muke sanar da ku cewa Allah haske ne, ba kuwa duhu gare shi ko kaɗan.

6 In mun ce muna tarayya da shi, alhali kuwa muna zaune a duhu, mun yi ƙarya ke nan, ba ma aikata gaskiya.

7 In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.

8 In mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta tare da mu.

9 In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.

10 In mun ce ba mu yi zunubi ba, mun ƙaryata shi ke nan. Maganarsa kuma ba ta tare da mu.

Categories
1 YAH

1 YAH 2

Almasihu Mai Taimako Gun Allah

1 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu mai adalci.

2 Shi kansa kuwa shi ne hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka.

3 Ta haka za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umarninsa.

4 Kowa ya ce ya san shi, ba ya kuwa bin umarninsa, maƙaryaci ne, gaskiya kuma ba ta tare da shi.

5 Amma duk wanda yake kiyaye maganarsa, wannan kam, hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna cikinsa.

6 Kowa ya ce yana zaune a cikinsa, ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi ya yi.

Sabon Umarni

7 Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni nake rubuto muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne wanda kuke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai, shi ne maganar da kuka ji.

8 Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, da kuma gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma yana haskakawa.

9 Kowa ya ce yana a cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan’uwansa, ashe, a duhu yake har yanzu.

10 Mai ƙaunar ɗan’uwansa, a haske yake zaune, ba kuma wani sanadin sa tuntuɓe a gare shi.

11 Mai ƙin ɗan’uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi.

12 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, ina rubuto muku ne domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.

13 Ya ku dattawa, ina rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil’azal. Ya ku samari, ina rubuto muku ne domin kun ci nasara a kan Mugun nan. Ya ku ‘yan yara, ina rubuto muku ne domin kun san Uba.

14 Ya ku dattawa, na rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil’azal. Ya ku samari, na rubuto muku ne domin kuna da ƙarfi, Maganar Allah tana zauna a zuciyarku, kun kuma ci nasara a kan Mugun nan.

15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da yake a cikinta. Kowa yake ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam.

16 Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha’awa irin ta halin mutuntaka, da sha’awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne.

17 Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.

Magabcin Almasihu

18 Ya ku ‘yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne.

19 Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.

20 Ku kam, Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya.

21 Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a’a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya.

22 Wane ne maƙaryacin nan, in ba wanda ya mūsa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda yake ƙin Uban da Ɗan.

23 Ba mai ƙin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan.

24 Ku kam, abin da kuka ji tun da farko, sai ya zauna a zuciyarku. In abin da kuka ji tun farko ya zauna a zuciyarku, ku ma sai ku zauna cikin Ɗan, da kuma Uban.

25 Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato, rai madawwami.

26 Ina rubuto muku wannan ne a kan waɗanda suke ƙoƙarin ɓad da ku.

27 Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.

28 To a yanzu, ya ku ‘ya’yana ƙanana, sai ku zauna cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu kasance da amincewa, kada kunya ta rufe mu a gabansa a ranar komowarsa.

29 Da yake kun san shi mai adalci ne, ku dai tabbata duk mai aikata adalci haifaffensa ne.

Categories
1 YAH

1 YAH 3

‘Ya’yan Allah

1 Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu ‘ya’yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.

2 Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu ‘ya’yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa’ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.

3 Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.

4 Duk mai aikata zunubi ya yi tawaye ke nan. Zunubi tawaye ne.

5 Kun dai sani an bayyana shi domin yă ɗauke zunubai ne, a gare shi kuma ba zunubi.

6 Kowa da yake a zaune a cikinsa, ba ya aikata zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.

7 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne.

8 Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.

9 Duk wanda yake haifaffen Allah, ba yakan aikata zunubi ba, domin irinsa yana a cikinsa a zaune, ba yakan aikata zunubi ba, da yake shi haifaffen Allah ne.

10 Ta haka sai a ga waɗanda suke ‘ya’yan Allah, da kuma waɗanda suke ‘ya’yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

Ku Ƙaunaci Juna

11 Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna,

12 kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan’uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuwa na kirki ne.

13 Kada ku yi mamaki, ‘yan’uwa, idan duniya take ƙinku.

14 Mu kam, mun sani mun riga mun tsere wa mutuwa, mun kai ga rai saboda muna ƙaunar ‘yan’uwa. Wanda ba shi da ƙauna, zaman mutuwa yake yi.

15 Kowa da yake ƙin dan’uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi.

16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda ‘yan’uwa.

17 Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan’uwansa da rashi, sa’an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa?

18 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya.

Amincewa Gaban Allah

19 Ta haka za mu tabbata mu na gaskiya ne, har kuma mu amince wa kanmu gaban Allah,

20 duk sa’ad da zuciyarmu ta ba mu laifi, saboda Allah ya fi ta, ya kuma san kome.

21 Ya ku ƙaunatattuna, in zuciyarmu ba ta ba mu laifi ba, sai mu je gaban Allah amincewa.

22 Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so.

23 Umarninsa kuwa shi ne mu gaskata da sunan Ɗansa Yesu Almasihu, mu kuma ƙaunaci juna, kamar yadda ya umarce mu.

24 Duk mai bin umarnin Allah kuwa a dawwame yake cikinsa, Allah kuma a cikinsa. Ta haka muka tabbata ya dawwama a cikinmu, saboda Ruhun da ya ba mu.

Categories
1 YAH

1 YAH 4

Ruhun Allah da na Magabci

1 Ya ku ƙaunatattuna, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku jarraba ku gani ko na Allah ne, don annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.

2 Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah.

3 Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne, wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, a yanzu ma har yana duniya.

4 Ya ku ‘ya’yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.

5 Su kuwa na duniya ne, shi ya sa suke zance irin na duniya, duniya kuwa tana sauraronsu.

6 Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah yakan saurare mu, wanda yake ba na Allah ba kuwa, ba ya sauraronmu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na ƙarya.

Allah Ƙauna Ne

7 Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.

8 Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna.

9 Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa.

10 Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.

11 Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna.

12 Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai, amma kuwa in muna ƙaunar juna sai Allah ya dawwama cikinmu, ƙaunar nan tasa kuma tă cika a cikinmu.

13 Ta haka muka sani muna a zaune a cikinsa, shi kuma a cikinmu, saboda Ruhunsa da ya ba mu.

14 Mun duba, muna kuma ba da shaida, cewa Uba ya aiko Ɗan ya zama Mai Ceton duniya.

15 Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.

16 Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah yake yi mana. Allah shi ne ƙauna wanda yake a dawwame cikin kauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa.

17 Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu kasance da amincewa a ranar shari’a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniyar nan.

18 Ba tsoro ga ƙauna, amma cikakkiyar ƙauna takan yaye tsoro. Tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna,

19 Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu.

20 Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin dan’uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai taɓa gani ba.

21 Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan’uwansa kuma.