Categories
1 SAM

1 SAM 5

Akwatin Alkawarin Allah a wurin Filistiyawa

1 Sa’ad da Filistiyawa suka ƙwace akwatin alkawarin Allah a Ebenezer, suka kai shi Ashdod.

2 Suka shigar da shi cikin haikalin gunkinsu, Dagon, suka ajiye shi kusa da gunkin.

3 Kashegari da safe sa’ad da mutanen Ashdod suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Suka ta da shi, suka ajiye a wurinsa.

4 Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu.

5 (Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba su taka dokin ƙafar Dagon a Ashdod ba har wa yau.)

6 Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.

7 Da mutanen Ashdod suka ga yadda abin yake, sai suka ce, “Kada a bar akwatin alkawarin Allah na Isra’ila tare da mu, gama ya tsananta mana, mu da Dagon, allahnmu.”

8 Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila?”

Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can.

9 Amma da suka kai shi can sai Ubangiji ya hukunta birnin, ya gigita su, ya yi musu azaba da marurai, yara da manya.

10 Sai suka kai akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Amma da aka kai shi Ekron, sai mutanen Ekron suka fashe da kuka, suka ce, “Sun kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila don ya kashe dukanmu.”

11 Suka kuma aika a kirawo sarakunan Filistiyawa, suka ce, “Ku aika da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila zuwa inda ya fito don kada ya kashe mu duk da iyalinmu.” Dukan birnin ya gigita ƙwarai, gama Ubangiji yana hukunta su da tsanani.

12 Marurai sun fito wa mutanen da ba su mutu ba, mutane suka yi kuka domin allolinsu su cece su.

Categories
1 SAM

1 SAM 6

Filistiyawa Sun Komar da Akwatin Alkawari

1 Akwatin alkawarin Ubangiji ya yi wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.

2 Filistiyawa suka kirawo firistocinsu da bokayensu, suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku sanar da mu yadda za mu komar da shi inda ya fito.”

3 Sai firistocin da bokayen suka ce, “Idan za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila, dole ku aika da kyauta tare da shi domin zunubinku. Ba dama a komar da akwatin alkawarin hannu wofi. Ta haka za ku sami lafiya, za ku kuma san dalilin da ya sa ya yi ta hukunta ku.”

4 Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?”

Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.

5 Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye waɗanda suka lalatar da ƙasar, ku ba da girma ga Allah na Isra’ila, watakila zai ɗauke hukuncinsa a kanku, da allolinku, da ƙasarku.

6 Don me za ku taurare zukatanku kamar yadda Masarawa da Fir’auna suka taurare zukatansu? Sai da Allah ya wahalshe su tukuna kafin su sallami Isra’ilawa su tafi.

7 Yanzu kuwa ku yi sabon keken shanu, ku sami shanun tatsa biyu waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba, ku ɗaura wa shanun keken, amma ku tsare ‘yan maruƙansu a gida.

8 Sa’an nan ku sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken shanun, ku kuma sa siffofin maruran da na ɓerayen a cikin wani akwati ku ajiye a gefen akwatin alkawarin. Ku aika da waɗannan abubuwa tare da shi don yin hadaya ta laifi. Sa’an nan ku sa shi a hanya, a bar shi, ya tafi.

9 Ku zuba ido, ku gani, idan ya kama hanya zuwa Bet-shemesh, to, shi ne ya kawo mana wannan babbar masifa, amma idan ba haka ba, za mu sani ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”

10 Suka yi yadda aka faɗa musu, suka sami shanun tatsa biyu, suka ɗaura musu karkiyar keken. Suka tsare ‘yan maruƙansu a gida.

11 Suka sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken, da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran.

12 Shanun kuwa suka kama hanya sosai wadda ta nufi wajen Bet-shemesh, suna tafe, suna ta kuka, ba su kauce zuwa dama ko hagu ba, sarakunan Filistiyawa suna biye da su, har zuwa iyakar Bet-shemesh.

13 Mutanen Bet-shemesh kuwa suna cikin yankan alkamarsu a kwari. Da suka ɗaga kai sai suka ga akwatin alkawari, sai suka yi murna matuƙa.

14 Keken shanun kuwa ya shiga gonar Joshuwa mutumin Bet-shemesh, ya tsaya a wurin, kusa da wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun, suka yanka shanun suka ƙone su hadaya ga Ubangiji.

15 Lawiyawa kuwa suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji da akwatin da yake gefensa wanda aka sa siffofin zinariya a ciki. Suka ajiye su a kan babban dutsen. Mutanen Bet-shemesh kuwa suka miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu kuma a wannan rana.

16 Sarakunan nan biyar na Filistiyawa sun ga an yi wannan, sa’an nan suka koma Ekron a ran nan.

17 Waɗannan su ne siffofin marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin yin hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.

18 Suka kai siffofin ɓerayen nan na zinariya kuwa domin garuruwa biyar masu garu da ƙauyuka marasa garu na sarakunan Filistiyawa. Babban dutse inda suka ajiye akwatin Ubangiji yana nan har wa yau a saurar Joshuwa Bet-shemesh.

19 Sai Ubangiji ya kashe mutum saba’in daga cikin mutanen Bet-shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawari na Ubangiji. Mutanen kuwa suka yi makoki ƙwarai domin Ubangiji ya kashe mutane da yawa daga cikinsu.

Akwatin Alkawari a Kiriyat-yeyarim

20 Mutanen Bet-shemesh suka ce, “Wa ya isa ya tsaya a gaban Ubangiji, Allahn nan mai tsarki? A wurin wa zai tafi don ya rabu da mu?”

21 Sai suka aiki manzanni wurin mutanen Kiriyat-yeyarim, suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawari na Ubangiji, sai ku zo, ku ɗauka, ku tafi da shi.”

Categories
1 SAM

1 SAM 7

1 Mutanen Kiriyat-yeyarim kuwa suka zo suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji suka kai shi gidan Abinadab a bisa tudu. Suka keɓe ɗansa, Ele’azara, ya lura da akwatin alkawarin Ubangiji.

Sama’ila Ya Shugabanci Isra’ila

2 Akwatin alkawarin Ubangiji ya daɗe a Kiriyat-yeyarim, ya kai har shekara ashirin. A wannan lokaci kuwa dukan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

3 Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”

4 Isra’ilawa kuwa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot, suka bauta wa Ubangiji shi kaɗai.

5 Sama’ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.”

6 Isra’ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.

7 Da Filistiyawa suka ji Isra’ilawa sun taru a Mizfa, sai sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka tafi, su yi yaƙi da Isra’ilawa. Sa’ad da Isra’ilawa suka ji labari, sai suka tsorata,

8 suka ce wa Sama’ila, “Ka yi ta roƙo ga Ubangiji Allahnmu don ya cece mu daga hannun Filistiyawa.”

9 Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya kuma yi roƙo ga Ubangiji ya taimaki Isra’ilawa, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.

10 A sa’ad da Sama’ila yake miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso don su yi yaƙi da Isra’ilawa, sai Ubangiji ya buge wa Filistiyawa tsawa mai ƙarfi daga sama, suka kuwa ruɗe suka juya a guje.

11 Isra’ilawa suka fito daga Mizfa suka runtumi Filistiyawa, suka yi ta karkashe su har zuwa kwarin Bet-kar.

12 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa shi a tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer, wato “Har wa yau Ubangiji yana taimakonmu.”

13 Ta haka aka ci Filistiyawa. Daga nan ba su ƙara shiga yankin ƙasar Isra’ilawa ba, gama Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa a dukan zamanin Sama’ila.

14 Aka mayar wa Isra’ilawa garuruwan da Filistiyawa suka ƙwace musu, tun daga Ekron har zuwa Gat. Isra’ilawa kuma suka ƙwato dukan yankin ƙasarsu daga hannun Filistiyawa. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Ƙan’aniyawa.

15 Sama’ila kuwa ya yi mulkin Isra’ilawa dukan kwanakin ransa.

16 A kowace shekara yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa, inda yakan yi musu shari’a.

17 Sa’an nan kuma ya koma gidansa a Rama inda kuma yakan yi wa Isra’ilawa shari’a. Ya kuma gina wa Ubangiji bagade a can Rama.

Categories
1 SAM

1 SAM 8

Isra’ilawa Sun Roƙa A Naɗa musu Sarki

1 Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ‘ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.

2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abaija. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba.

3 Amma ‘ya’yansa ba su bi gurbin mahaifinsu ba, amma suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi, suka yi ta cin hanci, suka danne gaskiya.

4 Dukan shugabannin Isra’ila kuwa suka tattaru, suka tafi wurin Sama’ila a Rama,

5 suka ce masa, “Ga shi, ka tsufa, ga kuma ‘ya’yanka ba su bi gurbinka ba, yanzu dai sai ka naɗa mana sarki wanda zai yi mulkinmu kamar sauran ƙasashe.”

6 Amma Sama’ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu’a ga Ubangiji.

7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu.

8 Irin abubuwan da suke yi maka, irinsu ne suka yi mini tun daga ranar da na fito da su daga Masar har wa yau, sun ƙi ni, suka yi ta bauta wa gumaka.

9 Yanzu dai sai ka saurari maganarsu kurum, amma ka faɗakar da su sosai da sosai, ka kuma nuna musu irin halin sarkin da zai sarauce su.”

10 Sama’ila kuwa ya faɗa wa mutanen da suke roƙo ya naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.

11 Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa ‘ya’yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman.

12 Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. ‘Ya’yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa.

13 Zai sa ‘ya’yanku mata yin aikin turare, da dafe-dafe, da toye-toye.

14 Zai ƙwace gonakinku mafi kyau, da gonakinku na inabi, da gonakinku na zaitun, ya ba fādawansa.

15 Zai kuma karɓi ushirin hatsinku da na inabinku ya ba shugabannin fādarsa da sauran fādawansa.

16 Zai ƙwace bayinku mata da maza, da mafi kyau na shanunku da jakunanku, domin su riƙa yi masa aiki.

17 Zai kuma karɓi ushirin dabbobinku. Za ku zama barorinsa.

18 A lokacin za ku yi kuka saboda sarkin da kuka zaɓar wa kanku, amma Ubangiji ba zai kasa kunne ga kukanku ba.”

19 Amma mutane suka ƙi jin abin da Sama’ila ya faɗa musu, sai suka ce, “Duk da haka dai, muna so sarki ya sarauce mu,

20 don mu ma mu zama kamar sauran ƙasashe, mu sami sarki wanda zai sarauce mu, ya shugabance mu zuwa yaƙe-yaƙe.”

21 Sa’ad da Sama’ila ya ji dukan abin da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.

22 Ubangiji kuwa ya ce wa Sama’ila, “Ka yarda da abin da suka ce, ka naɗa musu sarki.”

Sai Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa ya koma gida.”

Categories
1 SAM

1 SAM 9

Aka Zaɓi Saul Ya Zama Sarki

1 Akwai wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror, na iyalin Bekorat, dangin Afinya, shi attajiri ne.

2 Yana da wani ɗa, sunansa Saul, kyakkyawan saurayi ne. A cikin jama’ar Isra’ila ba wanda ya fi shi kyau, ya fi kowa tsayi a cikin Isra’ilawa duka.

3 Ana nan sai jakunan Kish, mahaifin Saul suka ɓace, Kish kuwa ya ce wa Saul, ɗansa, “Tashi, kai da ɗaya daga cikin barorin ku tafi, ku nemo jakunan.”

4 Suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, suka ratsa ta ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Suka kuma bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba. Sai suka bi ta ƙasar Biliyaminu, amma ba su same su ba.

5 Da suka kai ƙasar Zuf, sai Saul ya ce wa baransa da yake tare da shi, “Zo mu koma gida, kada babana ya bar damuwa a kan jakunan ya yi ta damuwa a kanmu.”

6 Amma baran ya ce masa, “Ai, akwai wani mutumin Allah a garin nan, ana kuwa ganin girmansa, domin duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa, watakila ya iya faɗa mana inda jakunanmu suke.”

7 Saul ya ce wa baransa, “Idan muka tafi, me za mu ba shi? Gama guzurin da yake tare da mu ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu ba shi.”

8 Baran kuma ya ce wa Saul, “Ina da ‘yar azurfa tsaba da zan ba shi domin ya faɗa mana inda za mu same su.”

9 (A dā a Isra’ila, idan wani yana so ya yi tambaya ga Allah, sai ya ce, “Zo, mu tafi wurin maigani.” Gama wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani.)

10 Sai Saul ya ce wa baransa, “Maganarka daidai ce, zo, mu tafi.” Suka kuwa tafi garin da mutumin Allah yake.

11 Sa’ad da suka haura zuwa garin, suka gamu da waɗansu ‘yan mata za su ɗebo ruwa, suka ce musu, “Maigani yana nan?”

12 ‘Yan matan suka amsa, suka ce, “I, yana nan, ai, ga shi nan ma a gabanku, ku hanzarta. Shigowarsa ke nan a garin, domin yau mutane za su ba da sadaka a bagade a kan tudu.

13 Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama’a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa’an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”

14 Suka kuwa haura zuwa cikin garin. Da shigarsu suka ga Sama’ila ya nufo wajen da suke, za shi wurin da ake yin sujadar.

15 Ana gobe Saul zai tafi wurin Sama’ila, Ubangiji ya bayyana wa Sama’ila.

16 Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama’ata Isra’ila. Zai ceci jama’ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama’ata suke sha, gama na ji kukansu.”

17 Da Sama’ila ya ga Saul, sai Ubangiji ya ce masa, “To, ga mutumin da na faɗa maka! Shi ne wanda zai sarauci jama’ata.”

18 Sa’an nan Saul ya tafi wurin Sama’ila a ƙofar gari, ya tambaye shi, “Ina gidan maigani?”

19 Sama’ila ya amsa ya ce, “Ni ne maiganin, wuce gaba, mu tafi wurin yin sujada a kan tudu, gama yau dukanku za ku ci abinci tare da ni. Gobe da safe zan amsa muku dukan tambayoyinku, sa’an nan in sallame ku.

20 A kan zancen jakunanku da suka ɓace yau kwana uku ke nan da suka wuce, kada ka damu, gama an same su. Banda wannan ma, ga wa Isra’ilawa duka suke sa zuciya? Ba kai ba ne da gidan mahaifinka?”

21 Saul ya ce, “Ni mutumin kabilar Biliyaminu ne, kabilar da ta fi ƙanƙanta a Isra’ila. Iyalina kuma su ne mafi ƙanƙanta a iyalan kabilar Biliyaminu. Me ya sa ka faɗa mini irin wannan magana?”

22 Sa’an nan Sama’ila ya shigar da Saul da baransa a babban ɗakin taruwa, ya sa su zauna gaba inda baƙi suke, wajen mutum talatin aka gayyata.

23 Sama’ila kuwa ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman nan da na ba ka, wanda na ce ka ajiye shi dabam.”

24 Sai mai dahuwa ya kawo cinya da gadon baya ya ajiye a gaban Saul. Sa’an nan Sama’ila ya ce, “Sai ka ci naman da aka ajiye a gabanka, gama dominka aka ajiye shi don ka ci a wannan lokaci tare da waɗanda na gayyata.”

A wannan rana kuwa Saul ya ci tare da Sama’ila.

25 Sa’ad da suka gangaro daga wurin yin sujadar zuwa cikin gari, sai aka shirya wa Saul gado a kan bene.

26 Ya kwanta, ya yi barci.

Sama’ila Ya Keɓe Saul Ya Zama Sarki

Da asuba, Sama’ila ya kira Saul ya ce, “Tashi, in sallame ka.” Saul kuwa ya tashi, shi da Sama’ila suka fita waje zuwa kan titi.

27 Sa’ad da suka kai bayan gari, sai Sama’ila ya ce wa Saul, “Ka sa baranka ya yi gaba, kai ka tsaya nan tukuna domin in faɗa maka abin da Allah ya ce.”

Categories
1 SAM

1 SAM 10

1 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki ‘yar kwalabar mai, ya zuba wa Saul a kā, ya yi masa sumba, ya ce, “Ubangjiji ne ya keɓe ka, ya naɗa ka sarki a kan jama’arsa.

2 Yau, sa’ad da ka rabu da ni, za ka gamu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a karkarar Biliyaminu a Zelza. Za su ce maka, jakunan da ka tafi nema an same su, yanzu mahaifinka ya daina damuwa saboda jakunan, sai a kanku, yana cewa, ‘Ina zan gane ɗana?’

3 Sa’ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da ‘yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.

4 Za su gaishe ka, su ba ka malmala biyu, kai kuwa sai ka karɓa.

5 Sa’ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa’ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa.

6 Sa’an nan Ruhun Ubangiji zai sauko maka, za ka kuwa yi rawa da sowa tare da su, za ka zama wani mutum dabam.

7 Sa’ad da waɗannan alamu suka cika, sai ka yi abin da hali ya nuna maka, gama Ubangiji yana tare da kai.

8 Za ka riga ni zuwa Gilgal inda zan zo in miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai, har in zo in sanar da kai abin da za ka yi.”

9 Da Saul ya juya zai tashi daga wurin Sama’ila, sai Ubangiji ya ba shi sabuwar zuciya. Alamun nan kuma suka cika a ranar.

10 Sa’ad da suka iso Gileyad, sai suka tarar da ƙungiyar annabawa. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga rawa da sowa tare da su.

11 Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi, suka gan shi yana yin wannan tare da annabawa, suka ce wa junansu, “Me ya faru da ɗan Kish? Saul kuma yana cikin annabawa ne?”

12 Sai wani mutumin da yake wurin ya ce, “Sauran fa, su ma, iyayensu annabawa ne?” Wannan kuwa ya zama karin magana, “Har Saul kuma yana cikin annabawa?”

13 Da ya gama rawa da sowa sai ya tafi wurin bagaden a kan tudu.

14 Kawun Saul kuwa ya tambaye shi, shi da baransa, “Ina ne kuka tafi?”

Saul ya ce, “Mun je neman jakuna, da ba mu same su ba, sai muka tafi wurin Sama’ila.”

15 Kawunsa kuma ya ce, “In ka yarda ka faɗa mini abin da Sama’ila ya faɗa maka.”

16 Saul kuwa ya ce wa kawunsa, “Ya faɗa mana a fili an gane jakunan.” Amma bai faɗa wa kawunsa zancen sarautar da Sama’ila ya faɗa masa ba.

An yi Na’am da Zaman Saul Sarki

17 Sama’ila kuwa ya tara mutanen Isra’ila a gaban Ubangiji a Mizfa.

18 Ya ce musu, “In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, ‘Ni na fito da Isra’ilawa daga Masar, na cece ku daga Masarawa da kuma daga hannun mulkokin da suka wahalshe ku.

19 Ni ne Allahnku wanda yake cetonku daga dukan masifu da wahalai, amma ga shi yau, kun ƙi ni kuna roƙona in ba ku sarki. To, da kyau, yanzu fa sai ku kusato gaban Ubangiji kabila kabila da iyali iyali.’ ”

20 Sa’an nan Sama’ila ya ce wa kabilan Isra’ila su guso, kuri’a kuwa ta faɗa a kan kabilar Biliyaminu.

21 Sai kuma ya sa kabilar Biliyaminu ta guso iyali iyali, kuri’a kuwa ta faɗa a kan iyalin Matri. Sa’an nan kuma ya guso da iyalin Matri mutum mutum, kuri’a ta faɗa a kan Saul, ɗan Kish. Amma sa’ad da suka neme shi, ba a same shi ba.

22 Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?”

Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”

23 Sai suka sheƙa, suka fito da shi daga wurin da ya ɓuya, ya tsaya cikin mutane, ya fi kowa tsayi da misalin ƙafa guda.

24 Sama’ila ya ce wa dukan jama’a, “Kun gan shi? Shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa, babu wani kamarsa a cikin dukan jama’a.”

Jama’a duka kuwa suka yi sowa suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”

25 Sa’an nan Sama’ila ya faɗa wa jama’a ka’idodin sarautar. Ya rubuta su cikin littafi, ya ajiye a wuri mai tsarki. Sa’an nan ya sallami jama’a duka kowa ya koma gidansa.

26 Saul kuma ya koma gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawa da Allah ya taɓa zuciyarsu.

27 Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.

Categories
1 SAM

1 SAM 11

Saul Ya Ci Ammonawa

1 Sai Nahash Ba’ammone ya kewaye Yabesh da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”

2 Nahash Ba’ammone kuwa ya ce, “Zan ƙulla amana da ku a kan wannan sharaɗi, wato in ƙwaƙule idanunku na dama don ku zama abin raini ga Isra’ilawa.”

3 Dattawan Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ba mu zarafi kwana bakwai domin mu aika da manzanni a dukan ƙasar Isra’ila, idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, to, sai mu ba da kanmu gare ku.”

4 Da manzannin suka zo Gibeya inda Saul yake, suka ba mutane labarin abin da ya faru. Sai jama’a duka suka yi kuka.

5 Saul kuwa yana dawowa daga gona ke nan, tare da shanunsa na huɗa. Sai ya ce, “Me ya sami jama’a suke kuka haka?” Suka faɗa masa labarin mutanen Yabesh.

6 Da Saul ya ji, sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.

7 Ya kwance shanun, ya yanka gunduwa gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta hannun manzanni, yana cewa, “Duk wanda bai fito ya bi Saul da Sama’ila ba, to, haka za a yi da shanun nomansa!”

Jama’a suka ji tsoron abin da Ubangiji zai yi, suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.

8 Sa’ad da Saul ya tara mutane a Bezek, aka sami mutum dubu ɗari uku (300,000) daga Isra’ila, dubu talatin (30,000) kuma daga Yahuza.

9 Suka faɗa wa manzannin da suka zo. “Ga abin da za ku faɗa wa mutanen Yabesh, ‘Gobe, kafin rana ta yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa’ad da manzannin suka je, suka faɗa wa mutanen Yabesh saƙon, suka yi murna.

10 Saboda haka mutanen Yabesh suka ce wa Nahash Ba’ammone, “Gobe za mu zo wurinku, ka yi mana yadda ka ga dama.”

11 Gari na wayewa, sai Saul ya raba mutanen kashi uku, suka fāɗa wa sansanin Ammonawa da kisa tun da sassafe har rana tsaka, aka warwatsa waɗanda suka tsira ɗaya ɗaya.

12 Jama’ar Isra’ila kuwa suka ce wa Sama’ila, “Su wa suka ce Saul ba zai sarauce mu ba? Ka kawo su, mu kashe su.”

13 Amma Saul ya ce, “Ba wanda za a kashe a yau, gama Ubangiji ya yi wa Isra’ila ceto a yau.”

14 Sai Sama’ila ya ce wa jama’a, “Ku zo, mu tafi Gilgal a yi wankan sarautar a can.”

15 Jama’a duka kuwa suka nufi Gilgal, suka yi wa Saul wankan sarauta a gaban Ubangiji. Suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama. A can kuwa Saul tare da dukan mutanen Isra’ila suka yi murna ƙwarai.

Categories
1 SAM

1 SAM 12

Sama’ila Ya Yi Jawabin Bankwana

1 Sama’ila ya ce wa jama’ar Isra’ila, “Ga shi, na kasa kunne gare ku, na kuwa yi muku abin da kuka ce mini, na naɗa muku sarki.

2 Yanzu ga sarki a gabanku, ‘ya’yana maza kuma suna tare da ku. Ni na tsufa, na yi furfura, amma na yi ta kai da kawowa a cikinku tun ina yaro har zuwa yau.

3 To, ga ni nan, ku shaida a kaina a gaban Ubangiji da gaban wanda Ubangiji ya naɗa sarki. Takarkari ko jakin wa na ƙwace? Wa kuma na zalunta, ko na wulakanta? A wurin wa na karɓi hanci don in danne gaskiya? Sai ku shaida, ni kuwa zan mayar masa.”

4 Jama’a suka amsa, suka ce, “Ba ka zalunci kowa ba, ba ka wulakanta kowa ba, ba ka kuma yi wa kowa ƙwace ba.”

5 Sa’an nan ya ce musu, “Ubangiji shi ne shaida, wanda kuma ya naɗa, shi ma shaida ne a yau, cewa ba ku iske ni da laifin kome ba.”

Jama’ar suka ce, “Ubangiji ne shaida.”

6 Sama’ila kuma ya ce wa jama’a, “Ubangiji ne ya sa Musa da Haruna su fito da kakanninku daga ƙasar Masar.

7 Yanzu fa ku tsaya shiru don in yi muku magana a kan ayyuka masu adalci na Ubangiji waɗanda ya aikata dominku da kakanninku.

8 Sa’ad da Yakubu da ‘ya’yansa suka tafi Masar, Masarawa suka wulakanta su, sai suka kai kuka ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiki Musa da Haruna waɗanda suka fito da kakanninku daga ƙasar Masar, suka kawo su su zauna a wannan wuri.

9 Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su.

10 Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba’al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.

11 Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba’al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa’an nan kuka yi zamanku lafiya.

12 Amma da kuka ga Nahash Sarkin Ammonawa ya zo don ya yi yaƙi da ku, sai kuka ce mini, ‘Mu dai a yi mana sarki da zai sarauce mu,’ alhali kuwa Ubangiji Allahnku ne Sarkinku.

13 To, ga sarkin da kuka zaɓa nan, kuka roƙa. Ga shi, Ubangiji ya naɗa muku shi.

14 Idan za ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku yi biyayya da maganarsa, ba za ku karya umarnin Ubangiji ba, idan kuma ku da sarkin da yake sarautarku za ku bi Ubangiji Allahnku, kome zai zamar muku daidai.

15 Amma idan kun ƙi yin biyayya da maganar Ubangiji, kuka kuma karya umarnin Ubangiji, to, Ubangiji zai yi gāba da ku da sarkinku.

16 Yanzu fa ku tsaya shiru ku ga babban al’amarin da Ubangiji zai yi a idanunku.

17 Yanzu dai rani ne, ko ba haka ba? Zan roƙi Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama, da haka za ku sani, ku kuma ga babbar muguntar da kuka yi wa Ubangiji da kuka roƙa a yi muku sarki.”

18 Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa aka yi tsawa da ruwan sama a wannan rana. Dukan jama’a kuwa suka ji tsoron Ubangiji da Sama’ila ƙwarai.

19 Suka ce wa Sama’ila, “Ka yi wa bayinka roƙo ga Ubangiji Allahnka don kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”

20 Sama’ila kuwa ya ce musu, “Kada ku razana, gama kun riga kun aikata wannan mugunta, duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta masa da zuciya ɗaya.

21 Kada kuma ku ratse ku bi abubuwa marasa amfani da ba za su amfane ku, ko su cece ku ba, gama ba su da wani amfani.

22 Gama Ubangiji ya yi ƙaƙƙarfan alkawari, ba zai yashe ku ba, gama ya ɗauri aniya ya maishe ku jama’arsa.

23 Amma ni kaina, Allah ya sawwaƙa in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin fasa yin addu’a ga Ubangiji dominku. Zan riƙa koya muku kyawawan abubuwan da suke daidai.

24 Ku dai ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aminci, da zuciya ɗaya. Ku tuna da manyan al’amuran da ya yi muku.

25 Amma idan kuka ci gaba da aikata mugunta, za a shafe ku, ku da sarkinku.”

Categories
1 SAM

1 SAM 13

Yaƙi da Filistiyawa

1 Saul yana da shekara talatin sa’ad da ya ci sarauta, ya yi shekara arba’in da biyu yana sarautar Isra’ila.

2 Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga Isra’ila, dubu biyu (2,000) su zauna tare da shi a Mikmash da ƙasar tuddai ta Betel, dubu ɗaya (1,000) kuma su zauna tare da Jonatan a Gibeya ta Biliyaminu, sauran jama’a kuwa ya sallame su, su koma gida, kowa zuwa alfarwarsa.

3 Jonatan kuwa ya kashe wani shugaban yaƙi na Filistiyawa a Geba, Filistiyawa kuwa suka ji labarin abin da ya faru. Sai Saul ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar, na kiran Ibraniyawa su zo yaƙi.

4 Isra’ilawa duka kuwa suka ji wai Saul ya kashe shugaban yaƙi na Filistiyawa, da kuma, Isra’ilawa sun zama abin ƙi ga Filistiyawa, sai jama’a suka amsa kiran, suka tafi wurin Saul a Gilgal.

5 Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000), da mahayan dawakai dubu shida (6,000), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen.

6 Sa’ad da Isra’ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai.

7 Waɗansu kuwa suka haye Kogin Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad.

Saul kuwa yana can a Gilgal. Dukan mutanen da suka bi shi suka yi ta rawar jiki.

8 Ya dakata kwana bakwai bisa ga adadin lokacin da Sama’ila ya ɗibar masa, amma Sama’ila bai iso Gilgal ba. Mutane suka yi ta watsewa suna barin Saul.

9 Sai Saul ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadayun salama.” Ya kuwa miƙa hadaya ta ƙonawa.

10 Yana gama miƙa hadayar ke nan, sai ga Sama’ila ya iso.

Saul kuwa ya fita don ya tarye shi, ya gaishe shi.

11 Sai Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?”

Saul ya amsa ya ce, “Don na ga mutane suna watsewa, suna barina, kai kuma ba ka zo daidai lokacin ba, ga kuma Filistiyawa sun tattaru a Mikmash.

12 Sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ni kuwa ban riga na roƙi Ubangiji ba,’ don haka ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa!”

13 Sama’ila kuwa ya ce wa Saul, “Ka yi wauta, ba ka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba. Dā Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada.

14 Amma yanzu sarautarka ba za ta tabbata ba, gama Ubangiji ya riga ya sami mutum wanda yake so. Ubangiji ya riga ya naɗa shi ya zama sarkin jama’arsa, domin ba ka kiyaye umarnin Ubangiji ba.”

15 Sama’ila ya tashi daga Gilgal zuwa Gibeya ta Biliyaminu. Da Saul ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, ya tarar wajen mutum ɗari shida ne.

16 Sai Saul da ɗansa, Jonatan, da mutanen da suke tare da su suka zauna a Geba ta Biliyaminu. Filistiyawa kuwa suka kafa sansaninsu a Mikmash.

17 Sai runduna uku na mahara suka fito daga sansanin Filistiyawa. Runduna ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal.

18 Runduna guda kuma ta nufi Bet-horon, guda kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar kwarin Zeboyim wajen jeji.

19 A wannan lokaci ba maƙeri a ƙasar Isra’ila duka, domin Filistiyawa sun hana Ibraniyawa su ƙera wa kansu takuba ko māsu.

20 Saboda haka kowane Ba’isra’ile yakan gangara zuwa Filistiyawa domin ya koɗa bakin garmarsa, da fartanyasa, da gatarinsa, da laujensa,

21 duk lokacin da za su koɗar bakin garma da fartanya sai su biya sulusin shekel ne, ladan koɗar gatari da shirya abin korar shanun noma sulusin shekel ne.

22 A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko mashi ba a cikin mutanen da suke tare da Saul da Jonatan. Amma Saul da ɗansa, Jonatan, suna da su.

23 Sai ƙungiyar sojojin Filistiyawa ta fita zuwa mashigin Mikmash.

Categories
1 SAM

1 SAM 14

Karfin Zuciyar Jonatan

1 Wata rana Jonatan, ɗan Saul, ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye mu je sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai faɗa wa mahaifinsa ba.

2 Saul kuwa yana zaune a karkarar Gibeya a gindin itacen rumman a Migron. Mutum wajen ɗari shida suna tare da shi.

3 Ahaija ɗan Ahitub kuma, ɗan’uwan Ikabod, wato jikan Eli, firist na Ubangiji, yana Shilo, yana sāye da falmaran. Mutane kuma ba su sani ba, ashe Jonatan ya tafi wani wuri.

4 A tsakanin mashigin dutse inda Jonatan yake so ya bi zuwa sansanin Filistiyawa, akwai dutse mai tsayi a kowane gefe. Sunan ɗaya Bozer, ɗayan kuma Sene.

5 Ɗaya dutsen yana wajen arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma yana daga kudu a gaban Geba.

6 Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin ‘yan kaɗan.”

7 Sai mai ɗaukar masa makamai ya ce, “Ka yi abin da yake a zuciyarka, ga shi, ina tare da kai, gama ina goyon bayanka, kamar yadda zuciyarka take haka kuma tawa.”

8 Sa’an nan Jonatan ya ce, “Za mu haye zuwa wurin mutanen, mu nuna kanmu gare su.

9 Idan sun ce mana, ‘Ku dakata har mu zo wurinku,’ to, sai mu tsaya cik, ba za mu tafi wurinsu ba.

10 Amma idan sun ce, ‘Ku haura zuwa wurinmu,’ to, sai mu haura, gama wannan alama ce, wato Ubangiji ya bashe su a hannunmu.”

11 Sai su biyu suka tafi suka nuna kansu ga sansanin Filistiyawa. Da Filistiyawa suka gan su, sai suka ce, “Ku duba, Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.”

12 Sai suka kira Jonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce, “Ku hauro zuwa wurinmu, mu faɗa muku wani abu.”

Jonatan kuwa ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Ka biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra’ilawa.”

13 Sa’an nan Jonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukar makamansa kuwa yana biye da shi. Jonatan ya fāɗa wa Filistiyawa, ya yi ta kā da su, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa yana ta karkashe su.

14 A wannan karo na farko Jonatan da mai ɗaukar makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi kamar rabin kadada.

15 Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.

16 Da matsara na Saul a Gibeya ta Biliyaminu suka duba, sai ga taron Filistiyawa ya watse, kowa ya nufi wajensa, suna tafiya barkatai.

17 Saul ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ƙidaya mutane yanzu don ku ga wanda ya fita daga cikinmu.” Da aka ƙirga mutanen sai aka tarar Jonatan da mai ɗaukar makamansa ba su nan.

18 Sai Saul ya ce wa Ahaija, “Kawo akwatin alkawarin Allah a nan.” Gama a wannan lokaci akwatin Allah yana hannun Isra’ilawa.

19 Sa’ad da Saul yake magana da firist ɗin, sai hargowa a sansanin Filistiyawa ta yi ta ƙaruwa, Saul kuwa ya ce wa firist, “Janye hannunka.”

20 Sa’an nan Saul da mutanen da suke tare da shi suka taru, suka tafi su yi yaƙi. Sai suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna ta yaƙi da junansu. Aka yi babbar yamutsewa.

21 Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi su zuwa sansani, suka koma wajen Isra’ilawan da suke tare da Saul da Jonatan.

22 Waɗanda kuma suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, da suka ji labari Filistiyawa suna gudu, suka fito suka fafare su.

23 Haka Ubangiji ya ceci Isra’ilawa a ranan nan. Yaƙin kuwa ya kai har gaba da Bet-awen.

Abin da Ya Faru bayan Yaƙin

24 A ran nan kuwa Isra’ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.

25-26 Da dukan mutane suka shiga kurmi, sai ga zuma ko’ina, amma ba wanda ya lakata da yatsa ya sa a baka, domin mutane suna tsoron la’anar Saul.

27 Amma Jonatan bai ji barazanar da mahaifinsa ya yi wa jama’a ba, sai ya lakaci saƙar zuma da kan sandansa ya sa a hannu ya kai baka, sa’an nan idanunsa suka buɗe.

28 Sai wani daga cikin jama’a ya ce, “Ai, mahaifinka ya yi wa mutane barazana da rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana.’ ” Mutane kuwa suka tafke.

29 Jonatan kuwa ya ce, “Lalle mahaifina ya wahalar da jama’a! Dubi yadda na wartsake sa’ad da na ɗanɗana ‘yar zuman nan.

30 Da yaya zai zama yau da a ce mutane sun ci abinci sosai daga ganimar abokan gābansu, wadda suka samo! Ai, da kisan da aka yi wa Filistiyawa ya fi haka.”

31 Filistiyawa sun sha ɗibga a wannan rana, tun daga Mikmash har zuwa Ayalon. Isra’ilawa suka tafke da yunwa.

32 Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yanyanka su, suka ci naman ɗanye.

33 Sai aka faɗa wa Saul, “Ga shi, mutane suna yi wa Ubangiji laifi, suna cin nama ɗanye.”

Saul kuwa ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse a nan wurina.”

34 Sa’an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama’a duka, su kawo takarkarai da tumaki a nan, su yanyanka su, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Sai dukansu suka kawo takarkaransu a wannan dare, suka yanyanka a wurin.

35 Saul kuwa ya gina wa Ubangiji bagade. Shi ne bagade na farko da ya gina wa Ubangiji.

36 Sa’an nan Saul ya ce, “Mu tafi, mu fallasa Filistiyawa da dare har wayewar gari, kada ko mutum ɗaya daga cikinsu ya tsira.”

Sai suka ce masa, “Ka yi abin da ka ga ya yi maka kyau.” Amma firist ɗin ya ce, “Bari mu yi tambaya ga Allah.”

37 Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, ya ce, “In runtumi Filistiyawa? Za ka bashe su ga Isra’ilawa?” Amma Ubangiji bai amsa masa a wannan rana ba.

38 Sai Saul ya ce wa shugabanni, “Ku zo nan dukanku don mu bincike, mu san zunubin da aka yi a yau.

39 Hakika, duk wanda ya yi laifin za a kashe shi, ko da Jonatan ne, ɗana.” Amma ba wanda ya ce kome.

40 Ya kuma ce, “Dukanku ku tsaya waje ɗaya, ni kuma da Jonatan, ɗana, mu tsaya waje ɗaya.”

Sai jama’ar suka ce wa Saul, “Ka yi abin da ya yi maka kyau.”

41 Sa’an nan Saul ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, me ya sa ba ka amsa mini ba a wannan rana? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Jonatan, ya Ubangiji Allah na Isra’ila, ka nuna mana.” Sai amsa ta nuna Jonatan da Saul ne, jama’a kuwa suka kuɓuta.

42 Sa’an nan Saul ya ce, “A jefa kuri’a tsakanina da ɗana Jonatan.” Kuri’a kuwa ta fāɗa a kan Jonatan.

43 Sa’an nan Saul ya ce wa Jonatan, “Ka faɗa mini abin da ka yi!” Jonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana ‘yar zuma ne da na lakata da kan sandan da yake hannuna, ga ni, a shirye nake in mutu.”

44 Sai Saul ya ce, “Allah ya yi mini abin da ya fi haka, idan ba a kashe ka ba, Jonatan.”

45 Amma jama’a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra’ila, a ce za a kashe shi? Kai, a’a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.

46 Sa’an nan Saul ya komo daga runtumar Filistiyawa, suka koma yankin ƙasarsu.

Mulkin Saul da Iyalinsa

47 Sa’ad da Saul ya ci sarautar Isra’ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara.

48 Ya yi aikin jaruntaka, ya bugi Amalekawa, ya ceci Isra’ilawa daga hannun dukan waɗanda suka taso musu.

49 ‘Ya’yan Saul, maza ke nan, Jonatan, da Yishwi, da Malkishuwa. Yana kuma da ‘ya’ya mata biyu, Merab, ‘yar fari, da Mikal.

50 Sunan matarsa kuwa Ahinowam ‘yar Ahimawaz. Sunan shugaban rundunansa kuwa Abner ne, ɗan Ner, kawunsa.

51 Kish mahaifin Saul, da Ner mahaifin Abner, ‘ya’yan Abiyel ne.

52 Saul ya yi ta yaƙi mai zafi da Filistiyawa dukan zamanin da yake sarauta. Idan Saul ya ga ƙaƙƙarfan mutum, ko jarumi, sai ya sa shi cikin sojansa.