Categories
1 TAR

1 TAR 13

Dawuda Ya Yi Niyyar Kawo Akwatin Alkawari a Urushalima

1 Sa’an nan Dawuda ya yi shawara da shugabannin sojoji na dubu dubu da na ɗari ɗari, da kowane shugaba.

2 Ya kuma yi magana da dukan taron Isra’ilawa, ya ce, “Idan kun ga ya yi kyau, idan kuma nufin Ubangiji Allahnmu ne, to, bari mu aika a ko’ina wurin ‘yan’uwanmu waɗanda aka rage a ƙasar Isra’ila, mu kuma aika wa firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a biranensu masu makiyaya domin su zo wurinmu.

3 Sa’an nan mu ɗauko akwatin alkawari na Allahnmu mu kawo shi wurinmu, gama mun ƙyale shi tun zamanin Saul.”

4 Jama’a kuwa suka amince da shawarar, suka yarda kuma a yi haka ɗin.

Dawuda Ya Tafi Ya Kawo Akwatin Alkawari

5 Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.

6 Sai Dawuda tare da dukan Isra’ilawa, suka haura zuwa Ba’al, wato Kiriyat-yeyarim ta Yahuza, domin su ɗauko akwatin alkawarin Allah daga can, inda ake kira bisa sunan Ubangiji, wanda kuma yake zaune a wurin kerubobi.

7 Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabon keken shanu daga gidan Abinadab. Uzza da Ahiyo suka kora keken shanun.

8 Sai Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi rawa da iyakar ƙarfinsu a gaban Allah, suna raira waƙoƙi suna kaɗa, garayu, da molaye, da ganguna, da kuge, suna busa ƙaho.

9 Sa’ad da suka kai masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa don ya riƙe akwatin alkawarin saboda gargada.

10 Sai Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take a gaban Allah, saboda ya miƙa hannunsa ya kama akwatin alkawari.

11 Sai Dawuda ya ɓata ransa saboda da Ubangiji ya hukunta Uzza da fushi, sai ya sa wa wannan wuri suna Feresa-uzza, wato hukuncin Uzza.

12 Sa’an nan Dawuda ya ji tsoron Allah, ya ce, “Ƙaƙa zan kawo akwatin alkawarin Allah a gidana?”

13 Don haka Dawuda bai kai akwatin alkawarin zuwa cikin birninsa ba, amma ya raɓa da shi zuwa gidan Obed-edom wanda yake daga Gat.

14 Akwatin alkawarin Allah kuwa ya kasance a gidan Obed-edom har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa iyalin Obed-edom da dukan abin da yake da shi albarka.

Categories
1 TAR

1 TAR 14

Hiram da Dawuda

1 Sai Hiram Sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda, su kai masa itatuwan al’ul, da magina, da massassaƙa domin a gina masa fāda.

2 Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya tabbatar masa da sarautar Isra’ila, mulkinsa kuwa ya ɗaukaka ƙwarai saboda jama’arsa, Isra’ila.

‘Ya’yan da aka Haifa wa Dawuda a Urushalima

3 Dawuda kuwa ya ƙara auren waɗansu mata a Urushalima, suka haifi ‘ya’ya mata da maza.

4 Ga sunayen ‘ya’yan da aka haifa masa a Urushalima, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,

5 da Ibhar, da Elishuwa, da Elifelet,

6 da Noga, da Nefeg, da Yafiya,

7 da Elishama, da Eliyada, da Elifelet.

Dawuda Ya Ci Filistiyawa da Yaƙi

8 Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra’ila duka, sai dukan Filistiyawa suka haura, suna neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya fita domin ya yi yaƙi da su.

9 Filistiyawa suka iso kwarin Refayawa suka fara fatali da shi.

10 Sai Dawuda ya roƙi Allah, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?”

Ubangiji kuwa ya amsa masa, ya ce, “Ka haura, gama zan bashe su a hannunka.”

11 Sai suka haura zuwa Ba’al-ferazim, Dawuda kuwa ya ci su da yaƙi a wurin. Sai ya ce, “Allah ya raraki maƙiyana ta hannuna, kamar yadda ruwa yakan rarake ƙasa.” Don haka aka sa wa wurin suna Ba’al-ferazim.

12 Filistiyawa suka gudu suka bar gumakansu a wurin. Dawuda kuwa ya yi umarni, aka ƙone su duka.

13 Filistiyawa kuma suka sāke kawo yaƙi a kwarin.

14 Dawuda ya sāke yin roƙo ga Allah, Allah kuwa ya ce masa, “Kada ka hau zuwa wurinsu, ka kewaye ka ɓullo musu ta baya daura da itatuwan tsamiya.

15 Sa’ad da ka ji motsi kamar na tafiyar sojoji a bisa itatuwan tsamiya, sai ka fita ka yi yaƙi, gama Allah ya wuce ta gabanka don ya bugi sojojin Filistiyawa.”

16 Dawuda fa ya yi daidai yadda Ubangiji ya umarce shi. Suka bugi sojojin Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.

17 Sunan Dawuda kuma ya kai ko’ina cikin dukan ƙasashe. Ubangiji kuwa ya sa dukan al’ummai su ji tsoron Dawuda.

Categories
1 TAR

1 TAR 15

An Kawo Akwatin Alkawari a Urushalima

1 Dawuda kuwa ya gina wa kansa gidaje a birninsa, ya kuma kafa alfarwa domin akwatin alkawari na Allah.

2 Sai Dawuda ya ce, “Kada wani ya ɗauki akwatin alkawari na Allah sai Lawiyawa kaɗai, gama su ne Ubangiji ya zaɓa domin su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su kuma yi masa hidima har abada.”

3 Saboda haka Dawuda ya tattara Isra’ilawa duka a Urushalima don a kawo akwatin alkawarin Ubangiji a wurinsa, inda aka riga aka shirya masa.

4 Dawuda kuma ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya, tare kuma da Lawiyawa.

5 Waɗanda aka tattaro ke nan, daga iyalin Kohat su ɗari da shirin ne. Uriyel shi ne shugabansu.

6 Daga iyalin Merari su ɗari biyu da ashirin, Asaya ne shugabansu.

7 Daga iyalin Gershon ɗari da talatin, Yowel ne shugabansu.

8 Daga iyalin Elizafan ɗari biyu, Shemaiya ne shugabansu.

9 Daga iyalin Hebron su tamanin, Eliyel ne shugabansu.

10 Daga iyalin Uzziyel ɗari da goma sha biyu, Amminadab ne shugabansu.

11 Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyata firistoci, da Lawiyawa, wato Uriyel, da Asaya, da Yowel, da Shemaiya, da Eliyel, da Amminadab,

12 ya ce musu, “Ku ne shugabanni na gidajen kakanninku, Lawiyawa. Sai ku tsarkake kanku da ‘yan’uwanku domin ku iya kawo akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a inda na shirya masa.

13 Gama Ubangiji Allahnmu ya fashe fushinsa a kanmu saboda ba ku ne kuka ɗauke shi a karo na farko ba, saboda kuma ba mu yi masa sujada kamar yadda aka umarta ba.”

14 Sa’an nan firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji Allah na Isra’ila.

15 Lawiyawa fa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah a bisa sandunansa a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.

16 Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa ‘yan’uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske.

17 Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berikiya daga cikin ‘yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kishi.

18 Daga cikin ‘yan’uwansu, har yanzu aka zaɓi mataimakansu, wato Zakariya, da Ben, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Benaiya, da Ma’aseya, da Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da masu tsaron ƙofofi.

19 Haka aka zaɓi mawaƙa, wato Heman, da Asaf, da Etan don su buga kuge na tagulla.

20 Su Zakariya, da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Unno, da Eliyab, da Ma’aseya, da Benaiya, su ne masu kaɗa molaye da murya a sama.

21 Su Mattitiya, da Elifelehu, da Mikneya, da Obed-edom, da Yehiyel, da Azaziya suke ja da garayu da murya ƙasa-ƙasa.

22 Kenaniya shugaban Lawiyawa shi ne yake bi da waƙoƙi domin shi gwani ne.

23 Berikiya da Elkana su ne masu tsaron ƙofa ta akwatin alkawari.

24 Sai Shebaniya, da Yehoshafat, da Netanel, da Amasai, da Zakariya, da Benaiya, da Eliyezer, firistoci, suka yi ta busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-edom da Yehiya su ne kuma masu tsaron ƙofar akwatin alkawari.

25 Haka Dawuda, da dattawan Isra’ilawa, da shugabannin dubu dubu, suka tafi da murna domin su ɗauko akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-edom.

26 Saboda Allah ya taimaki Lawiyawa waɗanda suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi hadaya da bijimai bakwai da raguna bakwai.

27 Dawuda yana saye da kyakkyawar taguwa ta lilin tare da Lawiyawa duka waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, da mawaƙa, da Kenaniya shugaban mawaƙan. Dawuda kuma ya sa falmaran ta lilin.

28 Da haka fa Isra’ilawa duka suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suna ta sowa, suna ta busa ƙaho, suna kaɗa kuge da molaye, da garayu.

29 Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shigo birnin Dawuda, sai Mikal ‘yar Saul ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana ta rawa, yana murna, sai ta ji ya saƙale mata a zuci.

Categories
1 TAR

1 TAR 16

1 Suka fa shigo da akwatin alkawarin Allah, suka ajiye shi a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa masa, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama a gaban Allah.

2 Da Dawuda ya gama miƙa hadayar ƙonawa da ta salama, sai ya sa wa jama’a albarka da sunan Ubangiji.

3 Ya kuma rarraba wa Isra’ilawa mata da maza, gurasa, da gunduwar nama, da kauɗar zabibi.

4 Ya kuma sa waɗansu Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka Ubangiji Allah na Isra’ila, su gode masa, su kuma yabe shi.

5 Asaf shi ne shugaba, na biye da shi su ne Zakariya da Aziyel, da Shemiramot, da Yehiyel, da Mattitiya, da Eliyab, da Benaiya, da Obed-edom, da Yehiyel, waɗanda za su kaɗa molaye da garayu. Asaf kuwa shi ne mai kaɗa kuge.

6 Benaiya da Yahaziyel firistoci, su ne za su riƙa busa ƙaho a gaban akwatin alkawarin Allah.

Waƙar Yabo ta Dawuda

7 A wannan lokaci ne Dawuda ya fara sa Asaf da ‘yan’uwansa su riƙa raira waƙoƙin yabo ga Ubangiji.

8 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,

Ku sanar wa sauran al’umma abubuwan da ya yi!

9 Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,

Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!

10 Ku yi murna saboda mu nasa ne,

Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!

11 Ku je wurin Ubangiji neman taimako,

Ku tsaya a gabansa koyaushe.

12 Ku tuna da mu’ujizansa masu girma, masu banmamaki,

Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.

13 Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,

Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu.

14 Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,

Umarnansa domin dukan duniya ne.

15 Zai cika alkawarinsa har abada,

Alkawaransa kuma don dubban zamanai,

16 Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,

Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.

17 Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra’ila,

Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa’ad da ya ce,

18 “Zan ba ka ƙasar Kan’ana,

Za ta zama mallakarka.”

19 Jama’ar Ubangiji kima ne,

Baƙi ne kuwa a ƙasar.

20 Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,

Daga wannan mulki zuwa wancan.

21 Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,

Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.

22 Ya ce, “Kada ku taɓa bayina, zaɓaɓɓu,

Kada ku cuci annabawana!”

23 Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku dukan duniya,

Ku yi shelar albishir na ceton da ya yi mana kowace rana.

24 Ku yi shelar ɗaukakarsa ga al’ummai,

Da ayyukansa masu girma ga dukan mutane,

25 Ubangiji da girma yake, wajibi ne mu yabe shi,

Dole mu yi tsoronsa fiye da dukan alloli.

26 Gama allolin dukan sauran al’umma gumaka ne,

Amma Ubangiji shi ne ya halitta sammai.

27 Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,

Iko da farin ciki sun cika haikalinsa.

28 Ku yi yabon Ubangiji, ku dukan mutanen duniya,

Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!

29 Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,

Kuna kawo sadaka, kuna zuwa Haikalinsa.

Ku rusuna a gaban Mai Tsarki da sahihiyar zuciya,

30 Ku yi rawar jiki a gabansa, ku dukan duniya!

Hakika duniya ta kahu sosai, ba za ta jijjigu ba.

31 Duniya da sararin sama, ku yi farin ciki!

Ku faɗa wa al’ummai, Ubangiji shi ne sarki.

32 Ki yi ruri, ke teku, da dukan abin da yake cikinki,

Ka yi farin ciki, kai saura da dukan abin da yake cikinka.

33 Itatuwa a jeji za su yi sowa domin murna

Sa’ad da Ubangiji zai zo ya yi mulki a duniya.

34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne,

Ƙaunarsa madawwamiya ce!

35 Ku ce masa, “Ka cece mu, ya Allah Mai Cetonmu,

Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga al’ummai,

Domin mu gode maka,

Mu kuma yabi sunanka mai tsarki.”

36 Ku yabi Ubangiji Allah na Isra’ila!

Ku yi ta yabonsa har abada abadin!

Sa’an nan dukan jama’a suka ce, “Amin, Amin,” suka yabi Ubangiji.

An Zaɓi Lawiyawa domin Akwatin Alkawari

37 Dawuda ya sa Asaf tare da ‘yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji domin a yi hidima kullayaumin a gaban akwatin alkawarin kamar yadda aka bukaci a yi kowace rana.

38 Akwai kuma masu tsaron ƙofofi, wato Obed-edom ɗan Yedutun tare da ‘yan’uwansa, su sittin da takwas, da Hosa.

39 Sai ya bar Zadok firist da ‘yan’uwansa firistoci a wurin zama na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon.

40 Kowace safiya da maraice suna miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a bisa bagaden ƙona hadaya, kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, waɗanda ya ba Isra’ilawa.

41 Tare da su kuma akwai Heman, da Yedutun, da sauran waɗanda aka zaɓa musamman domin su yi godiya ga Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa.

42 Heman da Yedutun suna lura da ƙaho, da kuge, da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin raira waƙoƙin yabo ga Allah. ‘Ya’yan Yedutun, maza, su aka ba aikin tsaron ƙofa.

43 Sa’an nan dukan jama’a suka watse, kowa ya koma gidansa, Dawuda kuma ya koma gidansa, ya sa wa iyalinsa albarka.

Categories
1 TAR

1 TAR 17

Alkawarin da Allah Ya Yi wa Dawuda

1 Sa’ad da Dawuda yake zaune a fādarsa, sai ya ce, wa annabi Natan, “Ga shi, ni ina zaune a cikin gidan da aka yi da itacen al’ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana cikin alfarwa.”

2 Natan ya amsa masa ya ce, “Ka yi duk abin da zuciyarka ta ɗauka, gama Allah yana tare da kai.”

3 Amma a wannan dare Ubangiji ya yi magana da Natan, ya ce,

4 “Ka tafi, ka faɗa wa bawana, Dawuda, cewa ni Ubangiji na ce, ‘Ba za ka gina mini ɗakin da zan zauna a ciki ba.

5 Gama tun ranar da na fito da Isra’ilawa ban taɓa zama a cikin ɗaki ba, amma daga alfarwa zuwa alfarwa, daga wannan mazauni kuma zuwa wancan.

6 A dukan wuraren da na tafi tare da Isra’ilawa, ban taɓa faɗa wa wani daga cikin hakiman Isra’ila, waɗanda na ba da umarni su yi kiwon jama’ata, cewa su gina mini ɗaki da itacen al’ul ba.’

7 “Saboda haka fa sai ka faɗa wa bawana Dawuda cewa, ‘Ni Ubangiji Mai Runduna, na ɗauko ka daga kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama’ata Isra’ila.

8 Na kuwa kasance tare da kai a duk inda ka tafi, na kuma hallaka maƙiyanka a gabanka. Zan sa ka shahara kamar waɗanda suka shahara a duniya.

9 Zan zaɓo wa jama’ata, wato Isra’ila, wuri, zan dasa su, su zauna a wuri na kansu, don kada a sāke damunsu, kada kuma masu mugunta su ƙara lalata su kamar dā,

10 tun lokacin da na sa hakimai su shugabanci jama’ata Isra’ila. Zan rinjayi dukan maƙiyanka. Banda wannan kuma na yi alkawari zan ci dukan maƙiyanka, in mallakar da su ga zuriyarka.

11 Sa’ad da lokacinka ya yi da za ka mutu, zan ta da ɗaya daga cikin zuriyarka, ɗaya daga cikin ‘ya’yanka maza, zan kafa mulkinsa.

12 Shi ne zai gina mini Haikali, zan kafa gadon sarautarsa har abada.

13 Ni zan zama uba a gare shi, shi kuwa ya zama ɗa a gare ni, ba zan kawar masa da madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na kawar da ita daga wanda ya riga ka sarauta.

14 Zan zauna da shi a gidana da mulkina har abada. Gadon sarautarsa kuwa zai kahu har abada.’ ”

15 Natan kuwa ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.

Addu’ar Dawuda ta Godiya

16 Sarki Dawuda kuwa ya shiga alfarwa, ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, mene kuma gidana da za ka yi mini haka?

17 Amma wannan ƙanƙanen abu ne a gare ka, ya Allah. Ka kuma yi alkawari, cewa za ka tsawaita kwanakin zuriyar bawanka, ka ɗauke ni kamar ni wani babban mutum ne, ya Ubangiji Allah.

18 Me kuma ni Dawuda zan ƙara ce maka, a kan girman da ka ba bawanka? Gama ka san bawanka.

19 Ya Ubangiji, saboda bawanka ne, da kuma bisa ga yardar ranka, ka aikata wannan babban al’amari, domin ka bayyana waɗannan manyan abubuwa.

20 Ya Ubangiji, ba wani kamarka, ba kuma wani Allah sai kai, bisa ga duk abin da muka ji da kunnuwanmu.

21 Wace al’umma ce take a duniyar nan kamar jama’arka, Isra’ila, wadda kai, Allah, ka je ka fanshe ta, ta zama jama’arka, domin ka yi suna ta wurin manyan abubuwa masu banmamaki, kamar yadda ka kori al’ummai a gaban jama’arka, wadda ka fansa daga Masar?

22 Gama ka mai da jama’ar Isra’ila ta zama taka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

23 “Yanzu dai, ya Ubangiji, bari maganar da ka yi wa bawanka da gidansa ta tabbata har abada, ka kuma aikata yadda ka faɗa.

24 Bari sunanka ya kahu, ya ɗaukaka har abada, a riƙa cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna, shi ne Allah na Isra’ilawa.’ Gidan bawanka Dawuda kuma ya kahu a gabanka.

25 Gama kai, ya Allahna, ka riga ka bayyana wa bawanka, cewa za ka sa zuriyata su zama sarakuna, don haka ne, ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu’a gare ka.

26 Yanzu dai ya Ubangiji, kai Allah ne, ka riga ka yi alkawarin wannan kyakkyawan abu gare ni, bawanka.

27 Ina roƙonka, ka sa wa gidan bawanka albarka, domin ya dawwama a gabanka, gama ya Ubangiji, abin da ka sa wa albarka, ya albarkatu ke nan har abada.”

Categories
1 TAR

1 TAR 18

Dawuda Ya Faɗaɗa Mulkinsa

1 Bayan haka kuma Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya mallake su, ya ƙwace Gat da garuruwanta daga hannunsu.

2 Ya kuma ci Mowab da yaƙi, Mowabawa suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji.

3 Dawuda kuma ya ci Hadadezer, Sarkin Zoba, da yaƙi a Hamat, sa’ad da ya tafi ya kafa mulkinsa a Kogin Yufiretis.

4 Sai Dawuda ya ƙwace karusai dubu (1,000), da mahayan dawakai dubu bakwai (7,000), da sojojin ƙasa dubu ashirin (20,000) daga gare shi. Dawuda kuma ya yanyanke agarar dawakan da suke jan karusai, amma ya bar waɗansu dawakai daga cikinsu waɗanda suka isa jan karusai ɗari.

5 Sa’ad da Suriyawa daga Dimashƙu suka zo don su taimaki Hadadezer Sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe mutum dubu ashirin da dubu biyu (22,000) daga cikin Suriyawan.

6 Sa’an nan Dawuda ya sa ƙungiyoyin sojoji a Suriya ta Dimashƙu, Suriyawa kuma suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.

7 Dawuda kuma ya ƙwato garkuwoyi na zinariya waɗanda barorin Hadadezer suke ɗauke da su, ya kawo su Urushalima.

8 Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali.

9 Sa’ad da Toyi, Sarkin Hamat, ya ji an ce Dawuda ya riga ya ci nasara a kan sojojin Hadadezer, Sarkin Zoba,

10 sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda, don ya gaishe shi, ya kuma yabe shi saboda ya yi yaƙi da Hadadezer, har ya ci shi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi. Adoniram kuwa ya kawo kayayyaki iri iri na zinariya, da na azurfa, da na tagulla.

11 Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan ga Ubangiji, tare da azurfa da zinariya waɗanda ya kwaso daga al’umman da ya ci, wato Edom, da Mowab, da mutanen Ammon, da na Filistiya, da na Amalek.

12 Abishai ɗan Zeruya kuma ya ci nasara a kan Edomawa, mutum dubu goma sha takwas (18,000) a Kwarin Gishiri.

13 Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan Edomawa kuma suka zama bayin Dawuda. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.

Manyan Ma’aikatan Dawuda

14 Da haka Dawuda ya yi mulki bisa dukan Isra’ila. Ya yi wa dukan jama’arsa adalci da gaskiya.

15 Yowab ɗan Zeruya shi ne shugaban sojoji, Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci.

16 Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyata su ne firistoci, Seraiya kuwa shi ne magatakarda.

17 Benaiya ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. ‘Ya’yan Dawuda, maza, su ne manyan ma’aikata na kusa da shi.

Categories
1 TAR

1 TAR 19

Dawuda ya Ci Ammonawa da Suriyawa

1 Bayan haka kuma Nahash Sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa kuma ya gāji sarautarsa.

2 Sa’an nan Dawuda ya ce, “Zan nuna alheri ga Hanun ɗan Nahash, gama tsohonsa ya nuna mini alheri.” Don haka Dawuda ya aiki manzanni su yi wa Hanun ta’aziyyar rasuwar tsohonsa.

Fādawan Dawuda suka zo ƙasar Ammon wurin Hanun, domin su yi masa ta’aziyya.

3 Amma hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne da ya aiko manzanni su yi maka ta’aziyya? Fādawansa sun zo wurinka ne don su leƙi asirin ƙasar, su bincike ta, su ci ta da yaƙi.”

4 Hanun kuwa ya kama fādawan Dawuda, ya aske gyammansu, ya yanyanke rigunansu a tsaka daga wajen kwankwaso, sa’an nan ya sallame su.

5 Waɗansu mutane kuwa suka je suka faɗa wa Dawuda abin da ya sami mutanen. Sai ya aiko a tarye su, gama an ƙasƙanta mutanen nan da gaske. Sai sarki ya ce, “Ku zauna a Yariko, har lokacin da gyammanku suka tohu sa’an nan ku iso.”

6 Sa’ad da Ammonawa suka ga sun mai da kansu abin ƙi ga Dawuda, sai Hanun da Ammonawa suka aika da talanti dubu (1,000) na azurfa don su yi ijara da karusai da mahayan dawakai daga Mesofotamiya, da jihohin Ma’aka ta Suriya, da Zoba.

7 Suka yi ijarar karusai dubu talatin da dubu biyu (32,000), da Sarkin Ma’aka, tare da jama’arsa. Suka zo suka kafa sansani a gaban Medeba. Ammonawa kuwa suka tattaru daga biranensu don su yi yaƙi.

8 Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab tare da dukan sojoji, ƙarfafan mutane.

9 Sai Ammonawa suka fito suka jā dāga a ƙofar birninsu. Sarakunan da suka zo suka ware suka zauna a saura.

10 Da Yowab ya ga an kafa masa yaƙi gaba da baya, sai ya zaɓi waɗansu jarumawa na gaske a Isra’ila, ya sa su su kara da Suriyawa.

11 Sa’an nan ya sa sauran sojoji a hannun Abishai ɗan’uwansa. Suka jā dāgar yaƙi da Ammonawa.

12 Yowab ya ce wa Abishai, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, to, sai ka taimake ni, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinka, to, sai in taimake ka.

13 Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama’armu da biranen Allahnmu. Bari Ubangiji ya yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”

14 Yowab da jama’ar da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Suriyawa, sai Suriyawa suka gudu daga gabansu.

15 Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai, ɗan’uwan Yowab, suka shiga birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima.

16 Da Suriyawa suka ga Isra’ilawa sun ci su da yaƙi sai suka aiki manzanni suka kira Suriyawa waɗanda suke hayin kogi. Shobak shugaban sojojin Hadadezer ne yake shugabantarsu.

17 Sa’ad da aka faɗa wa Dawuda, sai ya tattara Isra’ilawa duka ya haye Urdun, ya zo wurinsu, ya jā dāga don ya yi yaƙi da su. Aka fara gabza yaƙi,

18 sai Suriyawa suka gudu a gaban Isra’ilawa, Dawuda ya karkashe Suriyawa, mutum dubu bakwai (7,000) masu karusai, da sojojin ƙasa dubu arba’in (40,000). Ya kuma kashe Shobak shugaban sojojin.

19 Da barorin Hadadezer suka ga Isra’ilawa sun ci su da yaƙi, sai suka ƙulla zumunci da Dawuda, suka bauta masa. Saboda haka Suriyawa ba su ƙara yarda su taimaki Ammonawa ba.

Categories
1 TAR

1 TAR 20

Dawuda Ya Ci Rabba

1 Da bazara, lokacin da sarakuna sukan fita su yi yaƙi, sai Yowab ya tafi da sojoji suka lalatar da ƙasar Ammonawa. Suka tafi, suka kewaye Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima. Yowab ya bugi Rabba ya yi nasara da ita.

2 Sai Dawuda ya ciro kambi daga kan sarkinsu, sai ya iske nauyinsa talanti ɗaya na zinariya ne, akwai kuma duwatsu masu daraja a cikinsa. Dawuda ya sa kambin a kansa. Ya kwaso ganima da yawa a birnin.

3 Ya kuma fito da mutanen da suke ciki, ya yanyanka su da zartuna da makamai masu kaifi, da gatura. Haka Dawuda ya yi wa dukan biranen Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan jama’a suka koma Urushalima.

Yaƙi da Gwarzayen Filistiyawa

4 Bayan wannan kuma, sai yaƙi ya tashi a Gat tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar ƙattin nan. Aka ci Filistiyawa.

5 Yaƙi kuma ya sake tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, sai Elhanan ɗan Yayir, ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat daga Gat, wanda yake gorar mashinsa ta yi ya dirkar masaƙa.

6 Yaƙi ya sāke tashi a Gat, inda wani cindo, ƙaton mutum yake. Yana da yatsotsi ashirin da huɗu, wato a kowane hannu yana da yatsa shida, haka nan kuma a kowace ƙafarsa. Shi kuma daga zuriyar ƙattin nan ne.

7 Sa’ad da ya yi wa mutanen Isra’ila ba’a, sai Jonatan ɗan Shimeya, wato ɗan’uwan Dawuda, ya kashe shi.

8 Waɗannan uku ne Dawuda da jama’arsa suka kashe daga zuriyar ƙattin na Gat.

Categories
1 TAR

1 TAR 21

Dawuda Ya Ƙidaya Mutane

1 Shaiɗan ya tashi gaba da Isra’ila, sai ya iza Dawuda ya ƙidaya Isra’ilawa.

2 Dawuda fa ya ce wa Yowab da sauran shugabannin jama’a, “Ku tafi, ku ƙidaya jama’ar Isra’ila tun daga Biyer-sheba har zuwa Dan, ku kawo mini labari don in san yawansu.”

3 Amma Yowab ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya yawan jama’arsa har sau ɗari bisa kan yadda suke a yanzu! Ranka ya daɗe, ya sarki, ashe, dukkansu ba naka ba ne? Me zai sa shugabana ya so a yi haka? Me zai sa ya zama sanadin tuntuɓe ga mutanen Isra’ila?”

4 Duk da haka, sarki ya sa Yowab ya bi umarninsa. Sai Yowab ya tashi, ya bibiya ƙasar Isra’ila duka, sa’an nan ya komo Urushalima.

5 Yowab ya kawo wa Dawuda adadin yawan mutanen. Jimillar dukan Isra’ila zambar dubu ne da dubu ɗari (1,100,000) waɗanda za su iya yaƙi. Jimillar mutanen Yahuza kuwa dubu ɗari huɗu da dubu saba’in ne (470,000) waɗanda suka isa zuwa yaƙi.

6 Amma bai ƙidaya Lawiyawa da mutanen Biliyaminu ba, domin Yowab bai ji daɗin umarnin sarki ba.

7 Allah bai ji daɗin wannan al’amari ba, don haka sai ya bugi Isra’ila.

8 Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai saboda abin nan da na aikata. Amma ina roƙonka ka gafarta mini laifina, gama na yi aikin wauta ƙwarai da gaske.”

9 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Gad, annabin Dawuda, ya ce,

10 “Je ka ka faɗa wa Dawuda, ka ce, ‘Ubangiji yana so ka zaɓi ɗaya daga cikin abu uku, wanda zai yi maka.’ ”

11 Gad kuwa ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka zaɓa,

12 ko shekara uku na yunwa, ko kuwa ka sha ɗibga a hannun maƙiyanka har wata uku, maƙiyanka su yi ta fafararka, ko kwana uku na takobin Ubangiji, wato annoba ke nan da zai aukar wa ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai yi ta hallakarwa ko’ina a ƙasar Isra’ila. Yanzu fa, sai ka yi tunani, ka ba ni amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”

13 Dawuda kuwa ya ce wa Gad, “Na shiga uku, gara in fāɗa a hannun Ubangiji, gama shi mai yawan jinƙai ne, kada ka bar ni in faɗa a hannun mutum.”

14 Saboda haka Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra’ila. Mutum dubu saba’in (70,000) na Isra’ila suka mutu.

15 Allah ya aiko mala’ikansa don ya hallaka Urushalima, amma sa’ad da yake gab da hallaka ta, sai Ubangiji ya gani, ya janye shirin annobar, ya ce wa mala’ikan hallakarwa, “Ya isa, janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa na tsaye kusa da masussukar Arauna Bayebuse.

16 Dawuda ya ɗaga idonsa, sai ya ga mala’ikan Ubangiji yana tsakanin sama da ƙasa, da takobinsa a zare a hannunsa a kan Urushalima. Sa’an nan Dawuda tare da dattawa suka fāɗi rubda ciki, suna saye da tufafin makoki.

17 Dawuda ya ce wa Allah, “Ai, ni ne na ba da umarni a ƙidaya jama’ar. Hakika, ni na yi zunubi, na kuwa aikata mummunan abu, amma waɗannan talakawa fa, me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, ka bar hannunka ya yi gāba da ni da gidan tsohona, amma kada ka yi gāba da jama’arka, har da za ka aukar musu da annoba.”

18 Mala’ikan Ubangiji ya umarci Gad ya faɗa wa Dawuda ya haura, ya gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna Bayebuse.

19 Dawuda kuwa ya haura kamar yadda Gad ya faɗa masa da sunan Ubangiji.

20 Arauna yana cikin sussukar alkama, sai ya waiwaya ya ga mala’ika. ‘Ya’yansa maza su huɗu kuwa, waɗanda suke tare da shi suka ɓuya.

21 Sa’ad da Dawuda ya tafi wurin Arauna, da Arauna ya ga Dawuda, sai ya fito daga masussukar ya tafi ya fāɗi rub da ciki a gaban Dawuda ya gaishe shi.

22 Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ba ni wannan masussuka don in gina wa Ubangiji bagade. Ka sayar mini da masussukar a bakin cikakken kuɗinta, domin a kawar wa jama’a da annobar.”

23 Arauna ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa, na ba ka, sai ka yi abin da kake so da ita, ranka ya daɗe. Zan kuma ba da bijimai domin hadayu na ƙonawa, in ba da keken sussuka domin itacen wuta, in kuma ba da alkama don hadaya ta gari. Zan ba ka waɗannan duka.”

24 Amma sarki Dawuda ya ce wa Arauna, “A’a, zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai in ba Ubangiji ba, ba kuwa zan miƙa masa hadayu na ƙonawa da abin da ban biya ba.”

25 Sai Dawuda ya biya Arauna shekel ɗari shida na zinariya domin masussukar.

26 Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ya yi roƙo ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wutar da ta sauko daga sama a bisa bagaden hadayar ta ƙonawa.

27 Sa’an nan Ubangiji ya umarci mala’ikan, shi kuwa ya mai da takobinsa a kube.

Inda Za a Yi Haikalin

28 Da Dawuda ya ga Ubangiji ya amsa masa a masussukar Arauna Bayebuse, sai ya miƙa hadaya a wurin.

29 Gama wurin zama na Ubangiji wanda Musa ya yi a jeji, da bagaden hadaya ta ƙonawa sun cikin masujada a Gibeyon.

30 Dawuda bai iya zuwa wurin don ya yi tambaya ga Allah ba, saboda yana jin tsoron takobin mala’ikan Ubangiji.

Categories
1 TAR

1 TAR 22

1 Sa’an nan sai Dawuda ya ce, “A nan Haikalin Ubangiji Allah zai kasance, da kuma bagaden ƙona hadaya domin Isra’ila.”

Shirye-shiryen da Dawuda Ya Yi domin Gina Haikali

2 Dawuda kuwa ya umarta a tattaro dukan baƙin da suke a ƙasar Isra’ila. Ya sa waɗansu su farfasa duwatsu, su sassaƙe duwatsun domin ginin Haikalin Allah.

3 Dawuda kuma ya cika manyan ɗakunan ajiya da ƙarafa don yin ƙusoshi na ƙyamaren ƙofofi, da mahaɗai, ya kuma tara tagulla mai yawa wanda ta fi ƙarfin awo,

4 da katakan al’ul da ba a san adadinsu ba, gama Sidoniyawa da mutanen Taya sun kawo wa Dawuda itacen al’ul mai ɗumbun yawa.

5 Dawuda kuwa ya ce, “Ɗana Sulemanu yaro ne, bai gogu da duniya ba. Ga shi, Haikalin da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, zai zama sananne mai daraja cikin dukan ƙasashe, saboda haka sai in tanada masa.” Domin haka Dawuda ya tara kayayyakin gini masu ɗumbun yawa kafin rasuwarsa.

6 Sai Dawuda ya kira Sulemanu ɗansa, ya yi masa wasiyyar gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila.

7 Dawuda kuwa ya ce wa Sulemanu, “Ɗana, na ƙudura a zuciyata in gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allah.

8 Amma Ubangiji ya ce mini, ‘Ka zubar da jini da yawa, ka yi manyan yaƙe-yaƙe, don haka ba za ka gina Haikali saboda sunana ba, gama a gabana ka zubar da jini mai yawa a duniya.

9 Za a haifa maka ɗa, zai zama mutumin salama. Zan kuwa ba shi zaman lafiya da abokan gāba da suke kewaye da shi, gama za a ce da shi Sulemanu, wato salama. Zan kawo wa Isra’ila salama, da natsuwa a zamaninsa.

10 Shi zai gina Haikali saboda sunana. Zai zama ɗana, ni kuwa zan zama uba a gare shi, zan kafa gadon sarautarsa a Isra’ila har abada.’

11 “To, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, domin ka yi nasara ka gina Haikalin Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya faɗa a kanka.

12 Ubangiji dai ya ba ka basira da haziƙanci domin sa’ad da ya sa ka ka lura da Isra’ila ka kiyaye dokokinsa.

13 Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka’idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra’ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.

14 Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.

15 Kana da ma’aikata jingim, su masu fasa duwatsu, da magina, da masassaƙa, da gwanayen masu sana’o’i iri dabam dabam, masu yawan gaske.

16 Za su yi aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da ƙarfe. Tashi, ka kama aiki, Ubangiji ya kasance tare da kai!”

17 Dawuda kuma ya umarci dukan shugabannin Isra’ila su taimaki ɗansa Sulemanu.

18 Ya ce, “Ubangiji Allahnku yana tare da ku, ya ba ku zaman lafiya a kowane sashi. Gama ya ba da mazaunan ƙasar a hannuna, an murƙushe ƙasar a gaban Ubangiji da jama’arsa.

19 Yanzu fa sai ku sa hankalinku da zuciyarku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku tashi, ku gina wa Ubangiji Allah tsattsarkan wuri domin a kawo akwatin alkawari na Ubangiji, da tsarkakakkun tasoshin Allah a cikin Haikalin da aka gina saboda sunan Ubangiji.”