Categories
ISH

ISH 22

Annabci a kan Kwarin Wahayi

1 Wannan shi ne jawabi a kan kwarin wahayi.

Me yake faruwa? Me ya sa jama’ar birni duka suke biki a kan rufin gidaje?

2 Birnin duka ya ruguntsume, cike da hayaniya da tashin hankali.

Mutanenku da suka mutu ba su mutu suna yaƙi ba.

3 Dukan shugabanninku sun gudu, an kuwa kama su tun kafin su harba ko kibiya ɗaya. Dukanku da aka iske tare, aka kama ku, ko da yake kuka gudu da nisa.

4 Ni dai ƙyale ni kurum, in yi ta kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni, saboda yawancin mutanena sun mutu.

5 Wannan shi ne lokacin gigicewa, da shan ɗibga, da ruɗewa a cikin kwarin wahayi, Ubangiji Allah Mai Runduna shi ya aukar mana da shi. An ragargaza garukan birninmu har ƙasa, ana jin amsar kuwwar koke-kokenmu na neman taimako a cikin tsaunuka.

6 Sojojin ƙasar Elam sun zo kan dawakai suna rataye da kwari da baka. Sojojin ƙasar Kir sun shirya garkuwoyinsu.

7 Kwarurukansu masu dausayi na ƙasar Yahuza suna cike da karusai, sojoji kuma a kan dawakai suna tsattsaye a ƙofofin Urushalima.

8 Dukan kagaran Yahuza sun rushe.

Sa’ad da wannan ya faru kun kwaso makamai daga cikin taskar makamai.

9-10 Kun ga wuraren da suke bukatar gyara a garukan Urushalima. Ku ƙidaye dukan gidaje da suke cikin Urushalima, kuka rushe waɗansu gidaje don ku sami duwatsun da za ku gyara garukan Urushalima. Don ku tanada ruwa a cikin birnin,

11 kun gina matarar ruwa a jikin garuka don ta tare ruwan da yake gangarowa daga tsohon tafki. Amma ba ku kula da Allah ba, wanda ya shirya wannan tuntuni, wanda kuma ya sa wannan ya kasance.

12 Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki.

13 A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”

14 Ubangiji Mai Runduna ya ce mini, “Ko kusa ba za a gafarta musu wannan mugunta ba muddin ransu. Ni, Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

Eliyakim Zai Gāji Shebna

15 Ubangiji Mai Runduna ya faɗa mini in tafi wurin Shebna, mai hidimar iyalin gidan sarki, in ce masa,

16 “Kana tsammani kai wane ne? Wa ya ba ka ‘yancin sassaƙa wa kanka kabari a jikin duwatsu?

17 Yana yiwuwa kai wani abu ne, amma Ubangiji zai ɗauke ka, ya jefar.

18 Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!

19 Ubangiji zai fisshe ka daga maƙaminka, ya ƙasƙantar da kai daga babban matsayinka!”

20 Ubangiji ya ce wa Shebna, “Idan haka ya faru zan aika wa bawana Eliyakim ɗan Hilkiya.

21 Zan sa masa tufafin sarautarka, in ɗaura masa ɗamara, in kuma ba shi dukan ikon da kake da shi. Zai zama kamar uba ga jama’ar Urushalima da na Yahuza.

22 Zan sa shi ya zama sarki mai cikakken iko, na zuriyar Dawuda. Mabuɗan fāda suna hannunsa, abin da ya buɗe, ba mai ikon rufewa. Abin da ya rufe kuwa ba mai ikon buɗewa.

23 Zan kafa shi da ƙarfi a wurin kamar turke, zai kuwa zama sanadin daraja ga dukan iyalinsa.

24 “Amma dukan ‘yan’uwansa da masu dogara gare shi za su zama nawaya a gare shi. Za su rataya gare shi kamar tukwane da ƙoren da aka sa a ragaya!

25 Sa’ad da wannan ya faru ragayar da aka ɗaura tam za ta tsinke ta fāɗo. Wannan shi ne ƙarshen kowane abin da aka sa a cikin ragayar ke nan. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

Categories
ISH

ISH 23

Annabci a kan Taya da Sidon

1 Wannan shi ne jawabi a kan Taya.

Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa’ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin.

2 Ku yi kuka ku fataken Sidon! Kun aika da mutane

3 a hayin teku don su yi muku saye da sayarwa na hatsin da ake nomawa a Masar, su yi hulɗa da dukan sauran al’umma.

4 Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar ‘ya’ya ba, ban taɓa goyon ‘ya’ya mata ko maza ba.”

5 Har Masarawa ma za su firgita su razana, sa’ad da suka ji, cewa an hallakar da Taya.

6 Ku yi ruri da baƙin ciki, ku jama’ar bakin teku, ku yi ƙoƙari ku tsere zuwa Tarshish!

7 Ya yiwu kuwa a ce wannan Taya ce birnin farin ciki, wadda aka kafa ta tuntuni? Wannan kuwa ita ce birnin da yake aikawa da mutane hayin teku su kafa nahiyoyi?

8 Wane ne wannan wanda ya shirya ya aukar wa Taya da wannan duka, wannan muhimmiyar alkarya, wadda fatakenta hakimai ne, waɗanda ake ɗaukaka su fiye da sauran mutane a duniya?

9 Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.

10 Ku je ku nomi ƙasarku jama’ar nahiyoyin Tarshish! Ba wanda zai ƙara kiyaye ku.

11 Ubangiji ya miƙa dantsensa a kan tekun, ya hamɓarar da mulkoki. Ya umarta a lalatar da manyan biranen ciniki na Taya.

12 Birnin Sidon, farin cikinki ya ƙare. Ana zaluntar jama’arki, ko da za su tsere zuwa Kubrus duk da haka ba za su zauna lafiya ba.

13 (Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)

14 Ku yi hargowar baƙin ciki ku matuƙan jiragen teku! An hallaka birnin da kuke dogara gare shi.

15 Lokaci yana zuwa da za a manta da Taya har shekara saba’in, gwargwadon kwanakin sarki. Bayan waɗannan shekaru kuma, Taya za ta yi waƙa irin ta karuwa, cewa

16 “Ɗauki garayarki, kewaya cikin gari,

Ayya, an manta da karuwa!

Yi kiɗa, sāke raira waƙoƙinki,

Don ki komo da masoyanki.”

17 Bayan shekara saba’in ɗin, Ubangiji zai bar Taya ta koma a kan cinikinta na dā, za ta ba da kanta ijara ga dukan mulkokin duniya.

18 Kuɗin da ta samu ta kasuwanci za a keɓe wa Ubangiji. Ba za ta tara wa kanta ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada su za su yi amfani da kuɗinta don su saya wa kansu abinci da sutura da suke bukata.

Categories
ISH

ISH 24

Ubangiji Zai Hukunta Duniya

1 Ubangiji zai hallaka duniya ya bar ta kufai. Zai kaɓantar da duniya ya watsar da jama’ar da take cikinta.

2 Bala’i ɗaya ne zai sami kowa da kowa, firistoci da sauran jama’a, bayi da iyayengijinsu, masu saye da masu sayarwa, masu ba da rance da masu karɓa, attajirai da matalauta.

3 Duniya za ta ragargaje ta zama kufai. Ubangiji ne ya faɗa, haka kuwa za a yi.

4 Duniya za ta bushe ta ƙeƙashe, duniya duka za ta raunana, duniya da sararin sama za su ruɓe.

5 Jama’ar sun ƙazantar da duniya da suka keta dokokin Allah, suka ta da alkawarin da ya yi don ya dawwama.

6 Saboda haka Allah ya aiko da la’ana ta hallaka duniya. Jama’arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. ‘Yan kalilan ne suka ragu da rai.

7 Kurangun inabi sun bushe, ruwan inabi ya yi kaɗan. Dukan wanda yake farin ciki a dā, yanzu sai baƙin ciki yake yi,

8 kaɗe-kaɗen garayunsu da gangunansu na farin ciki sun ƙare.

9 Babu sauran waƙar farin ciki ga mashayan ruwan inabi, ba kuma wanda zai ƙara jin daɗin ɗanɗanar ruwan inabi.

10 A cikin birni kome ya birkice, an kulle kowane gida don a hana mutane shiga.

11 Mutane za su tsaya a tituna, suna ihu, suna neman ruwan inabi. Farin ciki ya ƙare har abada, ya ƙare a ƙasar.

12 Birnin ya zama kango, an farfashe ƙofofinsa.

13 Wannan shi ne abin da zai sami kowace al’umma ko’ina a duniya. Zai zama kamar ƙarshen kaka sa’ad da aka karkaɗe zaitun daga kowane itace, aka kuma gama tsinke ‘ya’yan inabi daga kurangar inabi.

14 Waɗanda suka tsira za su raira waƙa don farin ciki. Waɗanda suke wajen yamma za su ba da labarin girman Allah,

15 waɗanda suke wajen gabas kuma za su yabe shi. Jama’ar da take zaune a gefen teku za su yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.

16 Daga manisantan wurare na duniya za mu ji waƙoƙin yabon Isra’ila, al’umma adala.

Amma ba ni da sauran sa zuciya! Lalacewa nake yi! Maciya amana suna ta cin amana, cin amanarsu sai gaba gaba yake yi.

17 Ya jama’ar duniya, razana, da wushefe, da tarkuna suna jiranku.

18 Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga razana zai fāɗa cikin wushefe, wanda kuma ya tsere daga wushefe za a kama shi a tarko. Za a kwararo ruwa daga sama kamar da bakin ƙwarya, harsashin ginin duniya zai jijjigu.

19 Duniya za ta tsage, ta farfashe ta wage.

20 Duniya kanta za ta yi tangaɗi kamar mashayi, ta yi ta yin lau kamar rumfa a lokacin hadiri. Nauyin zunuban duniya ya rinjaye ta har ƙasa, za ta fāɗi, ba za ta ƙara tashi ba.

21 A wannan rana Ubangiji zai hukunta wa ikoki na sama, da sarakunan da suke a duniya.

22 Allah zai tattara sarakuna wuri ɗaya kamar ɗaurarru a rami, zai kulle su a kurkuku kafin lokacin da zai hukunta su ya yi.

23 Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama’a za su dubi ɗaukakarsa.

Categories
ISH

ISH 25

Waƙar Yabo saboda Alherin Ubangiji

1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka.

Ka aikata al’amura masu banmamaki,

Ka tafiyar da su da aminci,

Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.

2 Ka mai da birane kufai

Ka lalatar da kagaransu,

Wuraren da maƙiya suka gina kuwa,

An shafe su har abada.

3 Jama’ar al’ummai masu iko za su yabe ka,

Za a ji tsoronka a biranen mugayen al’ummai.

4 Matalauta da ‘yan ƙaƙa naka yi sun sheƙa zuwa wurinka,

Sun sami zaman lafiya a lokatan wahala.

Ka ba su mafaka daga hadura,

Ka inuwantar da su daga matsanancin zafi.

Mugaye sukan tasar musu kamar hadirin ƙanƙara,

5 Kamar fari a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

Amma kai, ya Ubangiji, ka rufe bakin abokan gābanmu,

Ka sa hayaniyar mugaye ta yi tsit,

Kamar yadda girgije yake sanyaya zafin rana.

Allah Ya Shirya Biki

6 A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al’umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau.

7 A can ne zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan sauran al’umma.

8 Ubangiji zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum, ya kawar da kunyar da jama’arsa suke sha a duniya duka. Ubangiji ne da kansa ya faɗa!

9 Sa’ad da wannan ya faru, kowa zai ce, “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”

10 Ubangiji zai kiyaye Dutsen Sihiyona, amma za a tattake jama’ar Mowab a ƙasa, kamar yadda ake tattake tattaka cikin taki.

11 Za su miƙa hannuwansu kamar suna ƙoƙarin yin ninƙaya, amma girmankansu zai jā hannuwansu ƙasa a duk sa’ad da suka ɗaga.

12 Allah zai lalatar da kagaran Mowab da dogayen garukansu, ya rushe su ƙasa su zama ƙura.

Categories
ISH

ISH 26

Waƙar Dogara ga Kiyayewar Ubangiji

1 Rana tana zuwa da jama’a za su raira wannan waƙa a ƙasar Yahuza.

Birni ƙaƙƙarfa ne,

Allah kansa yake tsare garukansa!

2 A buɗe ƙofofin birnin,

A bar amintacciyar al’umma ta shiga,

Al’ummar da jama’arta take aikata abin da yake daidai.

3 Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji,

Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi,

Waɗanda suke dogara gare ka.

4 Ku dogara ga Ubangiji har abada.

Zai kiyaye mu kullayaumin.

5 Ya ƙasƙantar da masu girmankai,

Ya hallaka ƙaƙƙarfan birnin da suke zaune ciki,

Ya rusa garunsa ƙasa.

6 Waɗanda aka zalunta, a kansa suke tafiya yanzu,

Suna tattaka shi da ƙafafunsu.

7 Ka sa hanyar mutanen kirki ta yi sumul,

Hanyar da suke bi ta yi bai ɗaya,

8 Muna bin nufinka, muna sa zuciya gare ka.

Kai kaɗai ne bukatarmu.

9 Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya.

Sa’ad da kake yi wa duniya da jama’arta shari’a

Dukansu za su san yadda adalci yake.

10 Ko da yake kana yi wa mugaye alheri,

Duk da haka ba su taɓa koyon abin da yake na kirki ba.

Har a nan ma, a ƙasar adalai,

Suna ta aikata kuskure,

Sun ƙi ganin girmanka.

11 Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba.

Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala,

Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya.

Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama’arka.

12 Kai za ka wadata mu, ya Ubangiji,

Duk abin da muka iya yi daga gare ka ne.

13 Ya Ubangiji Allahnmu, waɗansu sun mallake mu,

Amma kai kaɗai ne Ubangijinmu.

14 Yanzu kuwa sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba,

Kurwarsu ba za ta tashi ba,

Domin ka hukunta su, ka hallaka su.

Ba wanda zai ƙara tunawa da su.

15 Ya Ubangiji, ka sa al’ummarmu ta yi ƙarfi,

Ka faɗaɗa karkararta a kowane gefe,

Wannan kuwa ya sa ana girmama ka.

16 Ka hukunta jama’arka, ya Ubangiji,

A cikin azaba sun yi addu’a gare ka.

17 Kai ne, ya Ubangiji, ka sa muka yi kuka,

Kamar macen da take naƙuda tana kuka da azaba.

18 Muna shan azaba da wahala,

Amma ba abin da muka haifa.

Ba mu ciwo wa ƙasarmu nasara ba,

Ba abin da muka kammala!

19 Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa!

Jikunansu za su sāke rayuwa!

Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu

Za su farka, su yi waƙa don farin ciki!

Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya,

Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.

20 Jama’ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa.

21 Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama’arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.

Categories
ISH

ISH 27

Ceton Isra’ila da Tarawarta

1 A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da yake cikin teku.

2 A wannan rana Ubangiji zai yi magana a kan kyakkyawar gonar inabinsa,

3 ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.

4 Ba zan ƙara yin fushi da gonar inabin ba. Da ma a ce akwai ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya in yi faɗa da su, da na ƙone su ƙurmus.

5 Amma idan maƙiyan jama’ata suna so in cece su, sai su yi sulhu da ni, i, bari su yi sulhu da ni.”

6 A wannan rana jama’ar Isra’ila, zuriyar Yakubu, za su yi saiwa kamar itace, za su yi toho, su yi fure. ‘Ya’yan da suka yi za su cika duniya.

7 Ubangiji bai hukunta Isra’ila da tsanani kamar yadda ya yi wa maƙiyanta ba, ba za su yi hasarar mutane da yawa ba.

8 Ubangiji ya hukunta jama’arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su.

9 Ba za a gafarta zunuban Isra’ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.

10 Birni mai garu ya zama kufai. An bar shi kamar jejin da ba kowa ciki. Ya zama wurin kiwon shanu, inda za su huta su yi kiwo.

11 Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama’a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.

12 A wannan rana Ubangiji kansa zai hukunta jama’arsa, Isra’ila, daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, tun daga Yufiretis har zuwa iyakar Masar. Zai raba tsakanin nagari da mugu.

13 A wannan rana za a busa ƙaho don a kirawo Isra’ilawan da suke zaman baƙunci a Assuriya da Masar. Za su zo su yi wa Ubangiji sujada a Urushalima a tsattsarkan dutsensa.

Categories
ISH

ISH 28

Faɗakarwa game da Ifraimu

1 Mulkin Isra’ila ya ƙare, darajarsa tana dushewa kamar rawanin furanni a kan shugabanninsa da suka bugu da giya. Sun bulbula turare a kawunansu na girmankai, amma ga su nan a kwance bugaggu.

2 Ubangiji yana da wani ƙaƙƙarfa mai iko a shirye don ya fāɗa musu da yaƙi. Zai zo kamar hadirin ƙanƙara, kamar kwararowar ruwan sama, kamar kuma rigyawa mai kirmewa wadda ta shafe ƙasa.

3 Za a tattake girmankan bugaggun shugabannin nan.

4 Darajan nan mai dushewa ta shugabanni masu girmankai za ta shuɗe kamar ‘ya’yan ɓaure, nunan fari, da aka tsinke aka cinye nan da nan da nunarsu.

5 Rana tana zuwa da Ubangiji Mai Runduna zai zama kamar rawanin furanni mai daraja ga jama’arsa da suka ragu.

6 Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.

Faɗaka da Alkawari ga Urushalima

7 Har da annabawa da firistoci, tangaɗi suke yi, mashaya ne. Sun sha ruwan inabi da barasa da yawa, suna ta tuntuɓe barkatai. Annabawan sun bugu ƙwarai, har ba su iya fahimtar wahayin da Allah ya aiko musu ba, firistoci su ma sun bugu, har sun kāsa yanke shari’un da aka kawo musu.

8 Duk sun cika teburorin da suke zaune da amai, ba inda ba su amaye ba.

9 Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga ‘yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani!

10 Yana ƙoƙari ya koya mana baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi.”

11 Idan ba za ku saurare ni ba, to, Allah zai yi amfani da baƙi masu magana da harshen da ba ku sani ba, su koya muku darasi.

12 Ya miƙa muku hutawa da wartsakewa, amma kun ƙi saurarawa gare shi.

13 Saboda haka ne Ubangiji zai koya muku baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi. Sa’an nan kowane ɗaga ƙafar da kuka yi, za ku yi tuntuɓe, za a yi muku rauni, a kama ku a tarko, a kai ku kurkuku.

14 Yanzu fa ku mutane masu girmankai, da kuke mulki a nan a Urushalima a kan wannan jama’a, ku saurara ga abin da Ubangiji yake faɗa.

15 Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa’ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku.

16 Yanzu fa ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan kafa ƙaƙƙarfan harsashin gini a Sihiyona. A kansa zan sa ƙaƙƙarfan dutsen kusurwa. A kansa an rubuta wannan magana, ‘Amincin da yake kafaffe mai haƙuri ne kuma.’

17 Adalci ne zai zama igiyar gwajin tushen ginin, aminci kuma zai zama shacin dirin ginin.

Hadirin ƙanƙara zai share dukan ƙarairayin da kuke dogara gare su, rigyawa za ta hallakar da zaman lafiyarku.”

18 Alkawarin da kuka ƙulla da mutuwa ya tashi, yarjejeniyar da kuka yi da lahira, an soke ta. Sa’ad da masifa ta auko za a hallaka ku.

19 Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!

20 Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana, wanda ya yi ƙoƙari ya kwanta a gajeren gado, ya kuma rufa da ɗan siririn bargo.

21 Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al’ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al’ajabi ne.

22 Kada ku yi dariya saboda faɗakarwar da nake yi muku! Idan kuwa kun yi, zai ƙara yi muku wuya ku tsira. Na ji niyyar da Ubangiji Mai Runduna ya yi, ta ya hallaka dukan ƙasar.

Hikimar Allah

23 Ku kasa kunne ga abin da nake cewa, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa muku.

24 Manomi ba zai dinga huɗar gonakinsa har abada ba, ya yi ta shirya su domin shuka.

25 Da zarar ya shirya ƙasar yakan shusshuka ganyayen ci, kamar su kanumfari da ɗaɗɗoya, yakan kuma dasa kunyoyin alkama da na sha’ir, a gyaffan gonakin kuwa yakan shuka hatsi.

26 Ya san yadda zai yi aikinsa, gama Allah ya koya masa.

27 Ba ya bugun kanumfari da ɗaɗɗoya da ƙaton kulki, a maimakon haka yakan yi da ‘yan sanduna sirara.

28 Ba zai yi ta bugun alkama, har ya ɓata tsabar ba, ya san yadda zai sussuke alkamarsa, ba tare da ya ɓata tsabarta ba.

29 Dukan wannan hikima daga wurin Ubangiji Mai Runduna ne. Shirye-shiryen da Allah ya yi na hikima ne kullum kuwa sukan yi nasara!

Categories
ISH

ISH 29

Urushalima da Maƙiyanta

1 Bagaden Allah, Urushalima kanta, ƙaddara ta auko mata! Birnin da Dawuda ya kafa zango, ƙaddara ta auko mata! Bari shekara ɗaya ko biyu su zo su wuce suna shagulgulansu, suna bukukuwansu,

2 sa’an nan Allah zai kawo wa birnin wanda ake ce da shi, “Bagaden Allah,” masifa. Za a yi kuka a yi kururuwa, birnin kansa za a maishe shi bagade inda za a ƙona hadayun ƙonawa!

3 Allah zai tasar wa birnin, ya kewaye shi da yaƙi.

4 Urushalima za ta zama kamar fatalwar da take ƙoƙarin yin magana daga ƙarƙashin ƙasa, guni yana fitowa daga turɓaya.

5 Ya Urushalima, dukan baƙin da suka auka miki da yaƙi za a hure su kamar yadda iska take hure ƙura, sojojinsu kuma masu firgitarwa za a hure su kamar yadda iska take hure tattaka. Farat ɗaya ba zato ba tsammani,

6 Ubangiji Mai Runduna zai cece ki da tsawar hadiri da girgizar ƙasa. Zai aiko da hadirin iska da gagarumar wuta.

7 Sa’an nan dukan sojojin sauran al’umman da suka fāɗa wa birni inda bagaden Allah yake da yaƙi, da dukan makamansu, da kayayyakin yaƙinsu, kome da kome za su shuɗe kamar mafarki, kamar tunanin dare.

8 Dukan al’ummai da suka tattaru don su yaƙi Urushalima, za su zama kamar mutum mayunwaci da ya yi mafarki yana cin abinci, ya farka yana a mayunwacinsa, kamar wanda yake mutuwa da ƙishi ya yi mafarki yana kwankwaɗar ruwa, ya farka da busasshen maƙogwaro.

Makantar Isra’ilawa da Riyarsu

9 Ku ci gaba da aikin wautarku! Ku ci gaba da makancewarku, ku yi ta zama a makance. Ku bugu ba tare da kun sha ruwan inabi ba! Ku yi ta tangaɗi, ba don kun sha ko ɗigon ruwan inabi ba!

10 Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama’a, amma Allah ya rufe idanunsu.

11 Za a ɓoye muku ma’anar kowane annabci na cikin wahayi. Zai zama kamar naɗaɗɗen littafin da aka liƙe. Ko kun kai wa wanda ya iya karatu, don ya karanta muku, zai ce ba zai iya ba saboda a liƙe yake.

12 In kuwa kun ba wanda bai iya karatu ba, kuka roƙe shi ya karanta muku, zai ce bai iya karatu ba.

13 Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma’ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka’idodin mutane da suka haddace.

14 Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”

Maƙaryatan Mashawarta

15 Waɗanda suke ƙoƙarin ɓoye wa Ubangiji shirye-shiryensu sun shiga uku! Suna gudanar da dabarunsu a ɓoye, suna tsammani ba wanda zai gan su ko ya san abin da suke yi.

16 Sun birkitar da kome! Wane ne ya fi muhimmanci, mai ginin tukwane ko yumɓun? Abin da mutum ya yi da hannunsa ya iya ce wa mutumin, “Ba kai ka yi ni ba”? Ko kuma zai iya ce masa, “Ai, ba ka san abin da kake yi ba”?

Fansar Isra’ila

17 Kamar yadda karin maganar ta ce, kafin a jima kurmi zai zama gona, gona kuma za ta zama kurmi.

18 A wannan rana, kurame za su ji sa’ad da aka karanta littafi da murya, makafi kuwa waɗanda suke zaune cikin duhu za su buɗe idanunsu su gani.

19 Matalauta da masu tawali’u za su sāke samun farin ciki wanda Allah Mai Tsarki na Isra’ila ya bayar.

20 Zai zama ƙarshen waɗanda suke zaluntar waɗansu, suna raina Allah. Za a hallakar da kowane mai zunubi.

21 Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari’ar adalci.

22 Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya fanshi Ibrahim daga wahala, ya ce, “Jama’ata, ba za a ƙara kunyatar da ku ba, fuskokinku ba za su ƙara yanƙwanewa don kunya ba.

23 Za ku ga ‘ya’yan da zan ba ku, sa’an nan ne za ku tabbatar, cewa ni ne Allah Mai Tsarki na Isra’ila. Za ku girmama ni, ku yi tsorona.

24 Wawaye za su koya su gane, waɗanda a kullum sai gunaguni suke yi, za su yi murna su koya.”

Categories
ISH

ISH 30

Rashin Amfanin Dogara ga Masar

1 Ubangiji ya yi magana, ya ce, “Waɗanda suke mulkin Yahuza sun shiga uku, domin sun tayar mini. Suna aiki da shirye-shiryen da ba ni ne na yi ba, suka sa hannu a kan yarjejeniya gāba da nufina. Suna ta aikata zunubi a kan zunubi.

2 Suna tafiya Masar neman taimako, ba su shawarce ni ba. Suna so Masar ta kāre su, saboda haka suka sa dogararsu ga Sarkin Masar.

3 Amma sarkin zai rasa ikon taimakonsu, kāriyar da Masar za ta yi musu ƙarshenta masifa.

4 Ko da yake jakadunsu sun riga sun isa Zowan da Hanes, biranen Masar,

5 duk da haka jama’ar Yahuza za su yi da na sani, da suka dogara ga al’ummar da ba abar dogara ba ce, al’ummar da ba ta daɗa musu kome a lokacin da suke sa zuciya ga taimako ba.”

6 Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al’ummar da ba za ta taimake su da kome ba.

7 Taimakon da Masar za ta yi marar amfani ne. Don haka na yi mata laƙabi, ‘Macijin da ba ya yin kome.’ ”

Jama’a Marar Biyayya

8 Allah ya faɗa mini in rubuta a littafi yadda mutane suke, saboda ya zama tabbatacciyar shaida a kansu.

9 A kullum suna tayar wa Allah, a kullum ƙarya suke yi, a kullum suna ƙin kasa kunne ga koyarwar Allah.

10 Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.

11 Tashi daga nan, kada ku toshe mana hanya. Ba ma so mu ji kome game da Allah Mai Tsarki na Isra’ila.”

12 Amma wannan shi ne abin da Allah Mai Tsarki na Isra’ila ya ce, “Kun yi banza da abin da nake faɗa muku, kuna dogara ga aikin kamakarya da yin zamba.

13 Kun yi laifi. Kuna kamar bango wanda ya tsage daga bisa har ƙasa. Za ku fāɗi ba zato ba tsammani.

14 Za a ragargaza ku kamar tukunyar yumɓu, da mummunar ragargazawa har da ba za a sami ‘yar katangar da za a ɗauki garwashin wuta ba, ko a ɗebo ruwa daga randa.”

15 Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra’ila, ya ce wa jama’a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa’an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!

16 A maimakon haka sai kuka shirya ku tsere wa maƙiyanku a kan dawakai masu gudu. Daidai ne, tilas ku tsere! Tsammani kuke saurin gudun dawakanku ya isa, amma waɗanda za su fafare ku sun fi ku gudu!

17 Dubunku za su gudu da ganin abokin gābanku ɗaya, abokan gāba biyar sun isa su sa dukanku ku gudu. Ba abin da zai ragu daga cikin rundunar sojojinku, sai sandan tutarku kaɗai da take kan tudu.

18 Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.

Ubangiji Zai Sa wa Jama’arsa Albarka

19 Ku jama’ar da suke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa’ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku.

20 Ubangiji zai sa ku ku sha wahala, amma shi kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba.

21 Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.”

22 Za ku kwashe gumakanku waɗanda aka dalaye da azurfa, da waɗanda aka rufe da zinariya, ku jefar da su kamar abin ƙyama, kuna ihu, kuna cewa, “Ku ɓace mana da gani!”

23 Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya.

24 Takarkaranku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau duka.

25 A wannan rana sa’ad da aka kame kagaran abokan gābanku, aka kashe jama’arsu, rafuffukan ruwa za su malalo daga kowane tsauni da kowane tudu.

26 Wata zai yi haske kamar rana, hasken rana zai riɓanya har sau bakwai kamar a tattara hasken rana na kwana bakwai a maishe shi ɗaya! Dukan wannan zai faru sa’ad da Ubangiji zai ɗaure raunukan da ya yi musu, ya warkar da su.

Allah zai Hukunta Assuriya

27 Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta.

28 Ya aika da iska a gabansa kamar rigyawa wadda take kwashe kome, ta tafi da shi. Yakan gwada al’ummai ya kai su hallaka, yakan sa dukan shirye-shiryensu na mugunta su ƙare.

29 Amma ku, jama’ar Allah, za ku yi farin ciki, ku raira waƙa kamar yadda kukan yi a daren tsattsarkan idi. Za ku yi murna kamar waɗanda suke tafiya suna bushe-bushe a hanyarsu ta zuwa Haikalin Ubangiji Mai Tsarki, Mai Ceton Isra’ila.

30 Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

31 Assuriyawa za su firgita sa’ad da suka ji muryar Allah, suka kuma ji irin zafin hukuncinsa.

32 Sa’ad da Ubangiji ya miƙa sandan hukuncinsa ya yi ta bugun Assuriyawa, jama’arsa kuwa za su yi ta kaɗa ganguna da garayu, su yi murna!

33 An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.

Categories
ISH

ISH 31

Masarawa Mutane ne, ba Allah Ba

1 Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra’ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.

2 Ya san abin da yake yi! Zai aika da bala’i. Zai ci gaba da niyyarsa ta hukunta wa mugaye duk da masu kiyaye su.

3 Masarawa su ba Allah ba ne, mutane ne kurum! Dawakansu ba su wuce ikon ɗan adam ba! Sa’ad da Ubangiji zai matsa, ƙaƙƙarfar al’umma za ta marmashe, al’ummar da aka yi wa taimako kuma za ta fāɗi. Dukansu za su hallaka.

4 Ubangiji ya ce mini, “Kamar dai makiyaya ba za su iya tsoratar da zakin da ya kashe dabba ba, kome irin tsawa da ihun da suka yi, haka ni ma, ba abin da zai iya hana ni, ni Ubangiji Mai Runduna, in kiyaye Dutsen Sihiyona.

5 Kamar yadda tsuntsu yake shawagi a kan sheƙarsa don ya kiyaye ‘ya’yansa, haka ni, Ubangiji Mai Runduna, zan kiyaye Urushalima in kāre ta kuma.”

6 Allah ya ce, “Jama’ar Isra’ila, kun yi mini zunubi, kuna kuwa yin gāba da ni. Amma yanzu ku komo wurina!

7 Lokaci zai yi da dukanku za ku watsar da gumakan da kuka yi na azurfa da na zinariya.

8 Assuriya za ta hallaka cikin yaƙi, amma ba ta wurin ikon mutum ba. Assuriyawa za su gudu daga bakin dāga, za a mai da majiya ƙarfinsu bayi.

9 Sarkinsu zai tsere saboda razana, shugabannin sojojinsu kuwa za su firgita, har su watsar da tutocinsu na yaƙi.” Ubangiji ne ya faɗa, Ubangiji da ake yi wa sujada a Urushalima, wanda kuma wutarsa tana ci a can domin hadayu.