Categories
ISH

ISH 32

Sarki Mai Adalci

1 Wata rana za a yi wani sarki mai adalci, da kuma shugabannin ƙasa waɗanda za su yi mulki da gaskiya.

2 Ko wannensu zai zama kamar wurin fakewa daga iska da kuma wurin ɓuya saboda hadiri, za su zama kamar rafuffukan da suke gudu cikin hamada, kamar inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

3 Idanunsu da kunnuwansu za su kasance a buɗe domin sauraron jama’a.

4 Za su zama masu haƙuri sosai, za su yi kome da haziƙanci, za su kuma faɗi abin da suke nufi.

5 Ba wanda zai girmama wawayen mutane, ko kuma ya ce da mazambata suna da aminci.

6 Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha.

7 Mugu ne shi, yana kuwa yin mugayen abubuwa, yakan yi shiri don ya lalatar da matalauta da ƙarya, ya kuma hana su samun hakkinsu.

8 Amma mutum mai aminci yakan yi aikin aminci ya kuwa tsaya da ƙarfi a kan abin da yake daidai.

An Yi wa Matan Urushalima Faɗaka

9 Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ba ku da damuwar kome, ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

10 Zai yiwu ku wadatu yanzu, amma baɗi war haka za ku fid da zuciya, gama ba inabin da za ku tattara.

11 Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

12 Ku bugi ƙirjinku don baƙin ciki, gama an lalatar da gonaki masu dausayi da kuma gonakin inabi,

13 ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ne suke girma a ƙasar jama’ata. Ku yi kuka domin dukan gidajen da mutane suke murna a cikinsu dā, domin kuma birnin da yake cike da jin daɗi a dā.

14 Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.

15 Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa.

16 A ko’ina a ƙasar za a aikata adalci da gaskiya.

17 Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.

18 Gidajen jama’ar Allah za su zama da salama da zaman lafiya, ba abin da zai dame su.

19 (Amma ƙanƙara za ta faɗo a jeji, za a kuma rurrushe birni.)

20 Kowa zai yi murna da ruwan sama mai yawa domin amfanin gona, da kuma lafiyayyiyar makiyaya domin jakuna da shanu.

Categories
ISH

ISH 33

Ubangiji Zai Kawo Ceto

1 Magabtanmu sun shiga uku! Sun yi fashi sun ci amana, ko da yake ba wanda ya yi musu fashi ko cin amana. Amma lokacinsu na fashi da na cin amana zai ƙare, su ne kuma za a yi wa fashi da cin amana.

2 Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai. Muna sa zuciyarmu gare ka. Ka dinga kiyaye mu yau da gobe, ka kuma cece mu a lokatan wahala.

3 Lokacin da kake yaƙi dominmu, al’ummai sukan gudu daga bakin dāga.

4 Akan tsirga a bisa abubuwan da suke da su, a kwashe su ganima.

5 Ubangiji da girma yake! Yana mulki a kan kome. Zai cika Urushalima da adalci da mutunci,

6 zai kuma sa aminci cikin al’ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama’arsa ya kuma ba su hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji.

7 Mutane masu jaruntaka suna kira don a taimake su! Jakadu waɗanda suke ƙoƙarin kawo salama suna kuka mai zafi.

8 Manyan karauku suna da hatsari har ba mai iya binsu. Aka keta yarjejeniya, aka ta da sharuɗa. Ba a kuma ganin girman kowa.

9 Ƙasar na zaman banza, an gudu an bar ta. Jejin Lebanon ya bushe, kwarin Sharon mai dausayi ya zama kamar hamada, a Bashan kuma da a kan Dutsen Karmel sai ganyaye suke karkaɗewa daga itatuwa.

10 Ubangiji ya ce wa al’ummai, “Yanzu zan tashi! Zan nuna irin ikon da nake da shi.

11 Kuka yi shirye-shiryen banza, kowane abu da kuke yi kuma ba shi da amfani. Kuna hallakar da kanku!

12 Za ku marmashe kamar duwatsun da aka ƙona don a yi farar ƙasa, kamar ƙayayuwan da aka ƙone suka zama toka.

13 Bari kowa da yake kusa da na nesa ya ji abin da na yi, ya kuma san ikona.”

14 Jama’ar Sihiyona cike da zunubi suke, suna ta rawar jiki don tsoro. Suka ce, “Hukuncin Allah kamar wuta ce mai ci har abada. Akwai wani daga cikinmu da zai iya tsira daga irin wannan wuta?”

15 Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa.

16 Sa’an nan za ku yi nasara, ku kuma zauna lafiya kamar kuna cikin kagara mai ƙarfi. Za ku sami abincin da za ku ci da ruwan da za ku sha.

Gaba Mai Daraja

17 Wata rana za ku ga sarki mai ɗaukaka yana mulki a dukan ƙasar da take shimfiɗe zuwa kowace kusurwa.

18 Tsoronku na dā game da baƙi masu tara haraji, magewaya, zai ƙare.

19 Ba za ku ƙara ganin baƙin nan masu girmankai, masu magana da harshen da ba ku fahimta ba!

20 Ku duba Sihiyona, birni inda muke idodinmu. Ku duba Urushalima! Za ta zama wurin zama mai lafiya! Za ta zama kamar alfarwar da ba ta taɓa gusawa ba, wadda ba a taɓa tumɓuke turakunta ba, igiyoyinta kuma ba su taɓa tsinkewa ba.

21 Ubangiji zai nuna mana ɗaukakarsa. Za mu zauna a gefen koguna da rafuffuka masu faɗi, amma ba kuwa jirgin ruwan abokan gāba da zai bi ta cikinsu.

22-23 Dukan kayayyakin waɗannan jiragen ruwa ba su da amfani, tafiyarsu ba za ta yi nisa ba! Za a kwashe dukan dukiyar sojojin abokan gāba. Za ta yi yawa har sauran jama’a za su sami rabonsu. Ubangiji kansa shi zai zama sarkinmu, zai mallake mu, ya kiyaye mu.

24 Ba wanda zai zauna a ƙasarmu har ya ƙara yin kukan yana ciwo, za a kuma gafarta dukan zunubai.

Categories
ISH

ISH 34

Ubangiji Zai Hukunta Edom

1 Ku zo, ku jama’ar dukan al’ummai! Ku tattaru ku kasa kunne. Bari dukan duniya, da kowane mai zama cikinta, ya zo nan ya kasa kunne.

2 Ubangiji yana fushi da al’ummai duka, da kuma dukan sojojinsu. Ya zartar musu da hukuncin hallaka.

3 Ba za a binne gawawwakinsu ba, amma za a bar su can, su ruɓe, su yi ɗoyi, duwatsu kuma za su yi ja wur da jini.

4 Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.

5 Ubangiji ya shirya takobinsa a can Sama, yanzu kuwa zai buga Edom, wato mutanen can da ya zartar musu da hukuncin hallaka.

6 Jininsu da kitsensu za su rufe takobinsa, kamar jini da kitsen raguna, da na awaki, da aka miƙa hadaya. Ubangiji zai yi wannan hadaya a birnin Bozara, zai sa wannan ya zama babban kisa a ƙasar Edom.

7 Mutane za su fāɗi kamar bijiman jeji da ‘yan bijimai, ƙasar za ta yi ja wur da jini, kitse kuma zai rufe ta.

8 Wannan shi ne lokacin da Ubangiji zai kuɓutar da Sihiyona, ya kuma ɗauki fansa a kan abokan gābanta.

9 Kogunan Edom za su zama kalo, wato kwalta, ƙasar za ta zama kibritu, wato farar wuta. Dukan ƙasar za ta ƙone kamar kalo.

10 Za ta yi ta ci dare da rana, hayaƙi zai yi ta tashi sama har abada. Ƙasar za ta zama marar amfani shekara da shekaru, ba wanda zai iya ƙara bi ta cikinta.

11 Mujiyoyi da hankaki su ne za su gāji ƙasar. Ubangiji zai maishe ta marar amfani, kamar yadda take tun kafin halitta.

12 Ba sarkin da zai yi mulkin ƙasar, dukan shugabanni kuma za su ƙare.

13 Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su tsiro su yi girma a cikin dukan fādodi da garuruwa masu garuka, diloli da mujiyoyi za su zauna a cikinsu.

14 Namomin jeji za su yi ta kaiwa da komowa a can suna kiran juna. Mugun naman jeji zai je can ya nemi wurin hutawa.

15 Mujiyoyi za su yi sheƙarsu a can, su nasa ƙwayaye, su ƙyanƙyashe ‘ya’yansu, su kuma lura da su a can. Ungulai za su tattaru a can a kai a kai.

16 Bincika cikin Littafin Ubangiji ka karanta abin da yake faɗa. Ba ko ɗaya cikin halittattun nan da zai ɓata ba, ba kuwa wanda zai rasa ɗan’uwansa. Ubangiji ne ya umarta ya zama haka, shi kansa zai kawo su tare.

17 Ubangiji ne zai rarraba musu ƙasar, ya kuma ba ko wannensu nasa rabo. Za su zauna a ƙasar shekara da shekaru, za ta kuwa zama tasu har abada.

Categories
ISH

ISH 35

Mayarwar Mutanen Allah

1 Hamada za ta yi farin ciki.

Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani.

2 Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna,

Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon,

Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon.

Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah,

Ya ga girmansa da ikonsa.

3 Ku ƙarfafa hannuwan da suka gaji,

Da gwiwoyin da suke fama da rashin ƙarfi.

4 Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce,

“Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro!

Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai,

Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”

5 Makaho zai iya ganin gari,

Kurma kuma zai iya ji.

6 Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa,

Waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna.

Rafuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada,

7 Yashi mai ƙuna kuma zai zama tafki,

Ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za ta cika da maɓuɓɓugai.

Inda diloli suka yi zama,

Ciyawar fadama da iwa za su tsiro.

8 Za a yi babbar karauka a can,

Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.”

Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya,

Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.

9 Ba za a sami zakoki a can ba,

Mugayen namomin jeji ba za su bi ta can ba.

Waɗancan da Ubangiji ya fansar

Su za su zo gida ta wannan hanya.

10 Za su kai Urushalima da murna,

Suna raira waƙa suna sowa don murna.

Za su yi farin ciki har abada,

Ba damuwa da ɓacin rai har abada.

Categories
ISH

ISH 36

Assuriyawa Sun Kai Hari a Urushalima

1 A shekara ta goma sha huɗu da Hezekiya yake sarautar Yahuza, sai Sennakerib Sarkin Assuriya ya tasar wa birane masu kagara na Yahuza, ya kame su.

2 Sa’an nan ya umarci babban shugaban yaƙinsa ya tashi daga Lakish ya tafi Urushalima tare da babbar rundunar mayaƙa don su sa sarki Hezekiya ya ba da kai. Sai shugaban ya mamaye hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a daidai magudanar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake daga can bisa.

3 Mutanen Yahuza su uku suka fito don su tarye shi, shugaba mai lura da fāda, wato Eliyakim ɗan Hilkiya, da marubucin ɗakin shari’a, wato Shebna, da shugaban da yake kula da tarihin da aka rubuta, wato Yowa ɗan Asaf.

4 Sai shugaban Assuriyawa ya faɗa musu, cewa babban sarki yana so ya san ko me ya sa sarki Hezekiya yake dogara ga kansa.

5 Ya ce, “Kana tsammani magana da baki kawai ta isa ta yi aiki da gwanayen sojoji, da kuma masu ƙarfi? Wa kake tsammani zai taimake ka, har da za ka yi mini tawaye?

6 Kana sa zuciya Masar za ta taimake ka, to, wannan ya zama kamar ka ɗauki kyauro ya zama sandan dogarawa, zai karye, ya yi wa hannunka sartse. Haka Sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara gare shi.”

7 Ya ci gaba ya ce, “Ko za ka ce mini kana dogara ga Ubangiji Allahnka? Shi ne wannan da Hezekiya ya lalatar masa da wuraren sujada da bagadai, sa’an nan ya faɗa wa jama’ar Yahuza da na Urushalima su yi sujada ga bagade ɗaya kurum.

8 Zan yi ciniki da kai da sunan babban sarki, wato Sennakerib. Zan ba ka dawakai dubu biyu idan za ka iya samun yawan mutanen da za su hau su!

9 Ba ka yi daidai da ka ƙi ko wani marar maƙami a shugabannin Assuriya ba, duk da haka kana sa rai ga Masarawa su aiko maka da karusai, da mahayan dawakai!

10 Kana tsammani na tasar wa ƙasarka na kuma lalatar da ita ba tare da taimakon Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya faɗa mini in tasar wa ƙasarka in lalatar da ita.”

11 Sa’an nan sai Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka ce wa shugaba na Assuriya, “Ka yi mana magana da harshen Aramiyanci, muna jinsa. Kada ka yi da Ibrananci, dukan jama’ar da suke a kan garu suna saurare.”

12 Ya amsa ya ce, “Kuna tsammani babban sarki ya aiko ni don in daɗa wa ku da sarki kurum dukan magana? Sam, ina magana ne da jama’ar da suke a kan garu, waɗanda za su ci kāshinsu su kuma sha fitsarinsu, kamar yadda ku kanku za ku yi.”

13 Sa’an nan ya tsaya ya ta da murya da harshen Ibrananci, ya ce, “Ku saurara ga abin da Sarkin Assuriya yake faɗa muku.

14 Yana muku kashedi, cewa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, Hezekiya ba zai iya cetonku ba.

15 Kada kuma ku bari ya rinjaye ku ku dogara ga Ubangiji, har ku sa tsammani Ubangiji zai cece ku, ya hana sojojinmu na Assuriya su cinye birninku.

16 Kada ku kasa kunne ga Hezekiya. Sarkin Assuriya yana umartarku ku fito daga cikin birni ku sallama. Za a yardar muku duka ku ci ‘ya’yan inabi daga gonakinku, da ‘ya’yan ɓaure na itatuwan ɓaurenku, ku kuma sha ruwa daga rijiyoyinku na kanku,

17 har babban sarki ya sāke zaunar da ku a wata ƙasa mai kama da taku, inda akwai gonakin inabi da za su ba da ruwan inabi, da hatsi don yin gurasa.

18 Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, da cewa Ubangiji zai kuɓutar da ku. Ko gumakan waɗansu al’ummai sun ceci ƙasashensu daga Sarkin Assuriya?

19 Ina suke yanzu, wato gumakan Hamat da na Arfad? Ina gumakan Sefarwayim? Ba ko ɗaya da ya ceci Samariya, ko ba haka ba?

20 A yaushe ko gunki ɗaya na dukan waɗannan ƙasashe ya taɓa ceton ƙasarsa daga babban sarkinmu? To, yanzu me ya sa kuke tsammani Ubangiji zai ceci Urushalima?”

21 Jama’a suka yi tsit, kamar dai yadda sarki Hezekiya ya faɗa musu, ba su amsa da kome ba.

22 Sa’an nan Eliyakim, da Shebna, da Yowa suka kyakkece tufafinsu don baƙin ciki, suka tafi, suka faɗa wa sarki abin da shugaban mayaƙan Assuriya ya yi ta farfaɗa.

Categories
ISH

ISH 37

An Ceci Yahuza daga Sennakerib

1 Da sai sarki Hezekiya ya ji abin da suka faɗa, sai ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki, ya sa tsummoki a jiki, ya shiga Haikalin Ubangiji.

2 Ya aiki Eliyakim mai kula da fāda, da Shebna marubucin ɗakin shari’a, da manyan firistoci zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. Su kuma suna saye da tsummoki.

3 Ga saƙon da ya aike su su faɗa wa Ishaya, “Yau rana ce ta wahala, muna shan hukunci da wulakanci. Mun zama daidai da mace wadda take naƙuda, amma ba ta da ƙarfin da za ta haihu.

4 Sarkin Assuriya ya aiko babban shugaban mayaƙansa don ya zagi Allah mai rai. Da ma Ubangiji Allahnka ya ji waɗannan zage-zage ya kuma hukunta waɗanda suka yi su. Don haka sai ka yi addu’a ga Allah saboda mutanenmu waɗanda suka ragu.”

5 Sa’ad da Ishaya ya karɓi saƙon sarki Hezekiya,

6 sai ya aika masa da amsa cewa, “Ubangiji ya ce kada ka damu da irin zargin da Assuriyawa suke ta yi a kansa.

7 Ubangiji zai sa Sarkin Assuriya ya ji jita-jitar da za ta sa ya koma ƙasarsa, Ubangiji kuwa zai kashe shi a can.”

8 Shugaban mayaƙan Assuriya ya ji labari sarkin ya bar Lakish, yana can yana yaƙi da birnin Libna sai ya janye.

9 Sai Assuriyawa suka ji, cewa mayaƙan Masarawa, waɗanda sarki Tirhaka na Habasha take yi wa jagora, suna zuwa su far musu da yaƙi. Sa’ad da sarkin ya ji haka sai ya aika wa sarki Hezekiya da wasiƙa,

10 ya ce masa, “Allahn da kake dogara gare shi ya faɗa maka, ba za ka faɗa a hannuna ba, amma kada ka yarda wannan ya ruɗe ka.

11 Ka dai ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa duk ƙasar da ya yi niyyar hallakarwa. Kana tsammani za ka kuɓuta?

12 Kakannina sun hallakar da biranen Gozan, da Haran, da Rezef, suka kuma kashe mutanen Eden, mazaunan Telassar, ba ko ɗaya daga cikin gumakansu da ya iya cetonsu.

13 Ina sarakunan biranen Hamat da Arfad, da Sefarwayim, da Hena, da Iwwa?”

14 Sarki Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga hannun manzannin, ya karanta ta. Sa’an nan ya shiga Haikali, ya ajiye wasiƙar a gaban Ubangiji,

15 ya yi addu’a,

16 ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, kana kan kursiyinka, kai kaɗai ne Allah, kana mulkin dukan mulkokin duniya. Ka halicci duniya da sararin sama.

17 Yanzu, ya Ubangiji, ka ji mu, ka kuma dube mu. Ka kasa kunne ga dukan abubuwan da Senakerib yake ta faɗa, yana zaginka, ya Allah mai rai.

18 Dukanmu mun sani, ya Ubangiji, yadda sarakunan Assuriya suka hallakar da al’ummai masu yawa, suka mai da ƙasashensu kufai, marasa amfani,

19 suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.

20 Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al’umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”

21 Sa’an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu’ar sarki.

22 Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba’a.

23 Wa kake tsammani kana raina, kana yi masa ba’a? Ba ka ba ni girma ba, ni Allah mai tsarki na Isra’ila.

24 Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al’ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji.

25 Ka kuma yi fāriya da cewa ka haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa, ka kuma sha ruwansu, sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu da ƙafafunsu, har ya ƙafe.

26 “Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.

27 Mutanen da suke zaune a can marasa ƙarfi ne. Sun firgita, sun suma. Sun zama kamar ciyawa a saura, ko hakukuwan da suka tsiro a kan rufi, waɗanda zafin iskar gabas ta buga su.

28 “Amma na san kome game da kai, abin da kake yi da inda kake tafiya. Na san yadda ka harzuƙa gāba da ni.

29 Na sami labarin irin harzuƙarka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai.”

30 Sa’an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci ‘ya’yan.

31 Su da suka tsira daga al’ummar Yahuza za su yi lafiya kamar dashe-dashen da saiwoyinsu suka shiga da zurfi cikin ƙasa, suka kuma ba da amfani.

32 Mutanen da za su tsira su ne na cikin Urushalima da na kan Dutsen Sihiyona, gama Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyya ya sa haka ya faru.

33 “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya ce a kan Sarkin Assuriya, ‘Ba zai shiga wannan birni ba, ko kuwa ya harba ko da kibiya ɗaya a cikinsa. Sojoji masu garkuwoyi ba za su zo ko kusa da birnin ba, ba kuma za su yi mahaurai kewaye da birnin ba.

34 Zai koma ta kan hanyar da ya zo, ba kuwa zai taɓa shiga wannan birni ba. Ni, Ubangiji, ni na faɗa.

35 Zan kāre wannan birni in kiyaye shi, saboda girmana, domin kuma alkawarin da na yi wa bawana Dawuda.’ ”

36 Mala’ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu!

37 Sa’an nan sai Sarkin Assuriya, wato Sennakerib, ya janye ya koma Nineba.

38 Wata rana ya je yana sujada a gidan gunkinsa Nisrok, sai biyu daga cikin ‘ya’yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takubansu, sa’an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Wani daga cikin sauran ‘ya’yansa, wato Esar-haddon, ya gāje shi ya zama sarki.

Categories
ISH

ISH 38

Ciwon Sarki Hezekiya da Warkewarsa

1 A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”

2 Hezekiya kuwa ya juya wajen bango ya yi addu’a, ya ce,

3 “Ya Ubangiji, ka tuna, na bauta maka da aminci da biyayya, na kuma yi ƙoƙarin aikata abin da kake so in yi.” Sai ya fara kuka mai zafi.

4 Sa’an nan Ubangiji ya umarci Ishaya,

5 cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu’arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba.

6 Zan cece ka, da wannan birni na Urushalima, daga Sarkin Assuriya, zan ci gaba da kiyaye birnin.”

7 Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ubangiji zai nuna maka alama da za ta tabbatar maka zai cika alkawarinsa.

8 Ubangiji zai komar da inuwa baya da taki goma, bisa ga ma’aunin rana na sarki Ahaz.” Inuwa kuwa ta koma da baya daga fuskar rana har mataki goma.

9 Bayan da Hezekiya ya warke daga rashin lafiyarsa, sai ya rubuta wannan waƙar yabo.

10 Na zaci a gaɓar ƙarfina

Zan tafi lahira,

Ba zan ƙara rayuwa ba.

11 Na zaci ba zan ƙara ganin Ubangiji ba

A wannan duniya ta masu rai,

Ko kuwa in ga wani mutum mai rai.

12 An datse raina, ya ƙare,

Kamar alfarwar da aka kwance,

Kamar saƙar da aka yanke,

Na zaci Allah zai kashe ni.

13 Dare farai na yi ta kuka saboda azaba,

Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana.

Na zaci Allah zai kashe ni.

14 Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi,

Na kuwa yi kuka kamar kurciya,

Idanuna sun gaji saboda duban sama.

Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.

15 Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan.

Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.

16 Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai.

Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.

17 Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama.

Ka ceci raina daga dukan hatsari,

Ka gafarta dukan zunubaina.

18 Ba wanda yake yabonka a lahira,

Matattu ba za su iya dogara ga amincinka ba.

19 Masu rai ne suke yabonka,

Kamar yadda nake yabonka yanzu.

Iyaye za su faɗa wa ‘ya’yansu irin amincinka.

20 Ya Ubangiji, ka riga ka warkar da ni!

Za mu kaɗa garayu mu kuma raira waƙar yabo,

Za mu raira yabo cikin Haikalinka muddin ranmu.

21 Haka ya faru bayan da Ishaya ya faɗa wa sarki ya sa curin da aka yi da ‘ya’yan ɓaure a kan marurun, ya kuwa warke.

22 Sarki Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan iya zuwa Haikali?”

Categories
ISH

ISH 39

Manzanni daga Ƙasar Babila

1 A wannan lokaci sai Sarkin Babila, wato Merodak Baladan, ɗan Baladan, ya ji labarin sarki Hezekiya ya yi rashin lafiya, saboda haka sai ya aika masa da wasiƙa da kuma kyautai.

2 Hezekiya kuwa ya marabci manzannin, ya kuma nunnuna musu dukiyarsa, wato azurfa da zinariya, da kayan yaji da na ƙanshi, da dukan kayayyakinsa na yaƙi. Ba abin da bai nuna musu ba a ɗakunan ajiya, da ko’ina a mulkinsa.

3 Sa’an nan annabi Ishaya ya je wurin sarki Hezekiya, ya tambaye shi ya ce, “Daga ina waɗannan mutane suka zo? Me kuma suka faɗa maka?”

Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa suka zo, wato daga ƙasar Babila.”

4 Ishaya ya ce, “Me suka gani a fāda?”

Hezekiya ya amsa ya ce, “Suka ga kome da kome. Ba abin da ban nuna musu ba a ɗakunan ajiya.”

5 Sa’an nan Ishaya ya faɗa wa sarki ya ce, “Ubangiji Mai Runduna ya faɗi haka,

6 ‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe dukan abin da yake a fādarka, da dukan abin da kakanninka suka tara har ya zuwa yau, zuwa ƙasar Babila. Ba abin da za a rage.

7 Waɗansu daga cikin zuriyarka ta kanka, za a tafi da su a maishe su babani domin su yi hidima a fādar Sarkin Babila.’ ”

8 Da sarki Hezekiya ya gane, wannan zai faru ne a bayansa, wato a zamaninsa ba kome sai lafiya, sai ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”

Categories
ISH

ISH 40

Jawabin Ubangiji na Ta’aziyya ga Isra’ila

1 Ubangiji ya ce,

“Ka ta’azantar da jama’ata.

Ka ta’azantar da su!

2 Ka ƙarfafa jama’ar Urushalima.

Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa,

Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu.

Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”

3 Murya tana kira tana cewa,

“Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji!

Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!

4 Za a cike kowane kwari,

Za a baje kowane dutse.

Tuddai za su zama fili,

Ƙasa mai kururrumai za ta zama sumul.

5 Sa’an nan za a bayyana ɗaukakar Ubangiji,

Dukan ‘yan adam kuwa za su gan ta.

Ubangiji ne kansa ya yi wannan alkawari.”

6 Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!”

Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?”

“Ka yi shela, cewa dukan ‘yan adam kamar ciyawa suke,

Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba.

7 Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushi

Sa’ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu.

Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!

8 Hakika ciyawa takan bushe, furanni kuwa su yi yaushi,

Amma maganar Allah ba za ta taɓa faɗuwa ba!”

9 Ki haura a kan dutse mai tsayi, ke Urushalima,

Ki faɗi albishir!

Ki yi kira da babbar murya, ya Sihiyona,

Ki faɗi albishir!

Yi magana da ƙarfi, kada kuwa ki ji tsoro.

Ki faɗa wa garuruwan Yahuza,

Cewa Allahnsu yana zuwa!

10 Ubangiji yana zuwa ya yi mulki da iko,

Zai taho tare da mutanen da ya cece su.

Ga shi, zai kawo lada

Zai kuma yi wa mutane sakamako.

11 Zai lura da garkensa kamar yadda makiyayi suke yi,

Zai tattara ‘yan raguna wuri ɗaya,

Zai ɗauke su ya rungume su,

A hankali zai bi da iyayensu.

Allah na Isra’ila, Gagara Misali

12 Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu,

Ko sararin sama da tafin hannunsa?

Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali,

Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma’auni?

13 Akwai wanda zai iya umartar Ubangiji ya yi abu?

Wa zai iya koya wa Ubangiji, ko ya yi masa shawara?

14 Da wa Allah yake yin shawara

Domin ya sani, ya kuma fahimta,

Ya kuma koyi yadda za a yi abubuwa?

15 Al’ummai ba kome ba ne a wurin Ubangiji,

Ba su fi ɗigon ruwa ba,

Manisantan tsibirai ba su fi ƙura nauyi ba.

16 Dukan dabbobin da yake a jejin Lebanon

Ba su isa hadaya guda ga Allahnmu ba,

Itatuwan jejin kuma ba su isa a hura wuta da su ba.

17 Al’ummai ba kome ba ne ko kaɗan a gare shi.

18 Da wa za a iya kwatanta Allah?

Wa zai iya faɗar yadda yake?

19 Shi ba kamar gunki yake ba, wanda mutane suka yi,

Maƙera kuma suka dalaye da zinariya,

Suka sa shi cikin abin da suka yi da azurfa.

20 Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba,

Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba.

Yana neman gwanin sassaƙa

Domin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba.

21 Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?

Ashe, ba a faɗa maka ba tuntuni?

Ashe, ba ka ji yadda aka fara duniya ba?

22 Wanda yake zaune a kursiyi ne ya yi ta,

Can ƙwanƙolin duniya, gaba kuma da sararin sama,

Yana ganin mutane a ƙarƙas kamar ‘yan ƙananan ƙwari.

Ya miƙa sararin sama kamar labule,

Kamar kuma alfarwa domin mutane su zauna ciki.

23 Yakan kawo masu mulki masu iko ƙwarai,

Ya kuwa mai da su ba kome ba ne,

24 Suna kama da ƙaramin dashe

Wanda bai daɗe ba,

Bai yi ko saiwar kirki ba.

Sa’ad da Ubangiji ya aiko da iska,

Sai su bushe, iskar ta hure su kamar ƙaiƙayi.

25 Da wane ne za a kwatanta Allah Mai Tsarki?

Ko akwai wani mai kama da shi?

26 Ka dubi sararin sama a bisa!

Wane ne ya halicci taurarin da kake gani?

Shi wanda yake musu jagora kamar sojoji,

Ya sani ko su guda nawa ne,

Yana kiran dukansu, ko wanne da sunansa!

Ikonsa da girma yake,

Ba a taɓa rasa ko ɗayansu ba!

27 Isra’ila, me ya sa kake gunaguni,

Cewa Ubangiji bai san wahalarka ba,

Ko ya kula ya daidaita abubuwa dominka?

28 Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba?

Ubangiji Madawwamin Allah ne?

Ya halicci dukkan duniya.

Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba.

Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.

29 Yakan ƙarfafa masu kasala da masu jin gajiya.

30 Har da waɗanda suke yara ma, sukan ji kasala,

Samari sukan siƙe su fāɗi,

31 Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako

Za su ji an sabunta ƙarfinsu.

Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa,

Sa’ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba,

Sa’ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.

Categories
ISH

ISH 41

Alkawarin Allah ga Isra’ila

1 Allah ya ce,

“Ku yi shiru ku kasa kunne gare ni, ku manisantan ƙasashe!

Ku yi shiri ku gabatar da ƙararku a ɗakin shari’a.

Za ku sami zarafi ku yi magana.

Bari mu taru mu ga wanda yake da gaskiya.

2 “Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas,

Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi?

Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al’ummai?

Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura!

Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska!

3 Yana biye da kora, yana kuma tafiya lafiya,

Da sauri ƙwarai, da ƙyar yake taɓa ƙasa!

4 Wane ne ya sa wannan ya faru?

Wane ne ya ƙudurta labarun tarihi?

Ni Ubangiji, ina can tun da farko,

Ni kuma Ubangiji Allah,

Zan kasance a can har ƙarshe.

5 “Mutanen manisantan ƙasashe suka ga abin da na yi,

Suka tsorata, suka yi rawar jiki saboda tsoro.

Saboda haka duka suka tattaru wuri guda.

6 Masu aikin hannu suka taimaka suka ƙarfafa juna.

7 Masassaƙi yakan ce wa maƙerin zinariya, ‘A gaishe ka!’

Wanda yake gyara gumaka ya yi sumul

Yana ƙarfafa wanda yake harhaɗa su.

Wani yakan ce, ‘Haɗin ya yi kyau,’

Sukan kuma manne gumakan da ƙusoshi.

8 “Amma kai, Isra’ila bawana,

Kai ne jama’ar da na zaɓa,

Zuriyar Ibrahim, abokina,

9 Na kawo ka daga maƙurar duniya,

Na kira ka daga kusurwoyi mafi nisa.

Na ce maka, ‘Kai ne bawana.’

Ban ƙi ka ba, amma maimakon haka na zaɓe ka.

10 Kada ka ji tsoro, ina tare da kai,

Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka.

Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka,

Zan kiyaye ka, in cece ka.

11 “Su waɗanda suke fushi da ku, ku jama’ata,

Za a ƙasƙantar da su su ji kunya.

Waɗanda suke faɗa da ku kuwa za su mutu.

12 Za ku neme su, amma ba za ku same su ba,

Wato waɗanda suke gāba da ku.

Waɗanda suka kama yaƙi da ku,

Za su shuɗe daga duniya.

13 Ni ne Ubangiji Allahnku,

Na ƙarfafa ku, na kuwa faɗa muku,

‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.’ ”

14 Ubangiji ya ce,

“Isra’ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma,

Kada ku ji tsoro, zan taimake ku.

Ni Allah Mai Tsarki na Isra’ila, ni ne mai fansarku.

15 Zan sa ku zama kamar abin sussuka,

Wanda yake sabo, mai kaushi, mai tsini.

Za ku sussuke duwatsu ku lalatar da su,

Za a marmashe tuddai kamar ƙura.

16 Za ku watsa su sama cikin iska,

Iska za ta hure su, ta tafi da su,

Hadiri kuma zai warwatsar da su.

Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku,

Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra’ila.

17 “Sa’ad da jama’ata ta bukaci ruwa,

Sa’ad da maƙogwaronsu ya bushe da ƙishi,

Sa’an nan ni Ubangiji, zan amsa addu’arsu,

Ni Allah na Isra’ila, ba zan taɓa yashe su ba.

18 Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga ƙeƙasassun tuddai,

Maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a kwaruruka.

Zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa,

Busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.

19 Zan sa itatuwan al’ul su tsiro a hamada,

Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun.

Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi,

Jejin itatuwan fir.

20 Mutane za su ga wannan, su sani,

Ni Ubangiji, na yi shi.

Za su fahimta,

Allah Mai Tsarki na Isra’ila ya sa abin ya faru.”

Allah Ya Ce wa Allolin Ƙarya, Ƙalubalanku

21 Ubangiji, Sarki na Isra’ila, ya faɗi wannan,

“Ku allolin al’ummai ku gabatar da matsalarku.

Ku kawo dukan gardandamin da kuke da su!

22 Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba,

Ku bayyana wa ɗakin shari’a abubuwan da suka riga sun faru,

Ku faɗa mana yadda zai zama duka,

Domin lokacin da ya faru mu mu sani.

23 Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa.

Sa’an nan za mu sani, ku alloli ne!

Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala’i,

Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!

24 Ku da dukan abin da kuke yi ba kome ba ne,

Waɗanda suke yi muku sujada kuwa,

Abin ƙyama ne su!

25 “Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas,

Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa.

Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka,

Kamar yadda magini yake tattake yumɓu.

26 Wane ne a cikinku ya faɗa mana tun da wuri,

Ko ya yi annabci, cewa wannan zai faru,

Har da za mu ce kun yi daidai?

Ba ko ɗayanku da ya ce tak a kan wannan,

Ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu!

27 Ni Ubangiji, ni ne na farko da na faɗa wa Sihiyona albishir,

Na aiki manzo zuwa Urushalima don ya ce,

‘Jama’arki suna zuwa! Suna zuwa gida.’

28 Sa’ad da na duba alloli,

Ba wanda yake da abin da zai faɗa,

Ko ɗaya, ba wanda ya iya amsa tambayar da na yi.

29 Dukan waɗannan alloli ba su da amfani,

Ba su iya kome ba, ko kaɗan,

Gumakansu ba su da ƙarfi, ba su kuma da iko!”