Categories
ISH

ISH 42

Bawan Ubangiji

1 Ubangiji ya ce,

“Ga bawana, wanda na ƙarfafa,

Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa.

Na cika shi da ikona,

Zai kuwa kawo shari’ar gaskiya ga dukan al’ummai.

2 Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba,

Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.

3 Zai lallaɓi marasa ƙarfi,

Ya nuna alheri ga tafkakku.

Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.

4 Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba,

Zai kuma kafa gaskiya a duniya,

Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”

5 Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su,

Ya yi duniya, da dukan masu rai nata,

Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta.

Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,

6 “Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka iko

Domin ka ga ana aikata gaskiya a duniya.

Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari,

Ta wurinka zan kawo haske ga al’ummai.

7 Za ka buɗe idanun makafi,

Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.

8 “Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka.

Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata,

Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.

9 Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika.

Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa,

Tun kafin ma su soma faruwa.”

Yabo ga Ubangiji domin Cetonsa

10 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,

Ku raira yabo ku dukan duniya!

Ku yabe shi, ku da kuke tafiya ta teku,

Ku yabe shi, ku dukan halitta a teku!

Ku raira, ku manisantan ƙasashe, da dukan waɗanda suke a can!

11 Bari hamada da garuruwanta su yabi Allah,

Bari mutanen Kedar su yabe shi!

Bari su da suke zaune a birnin Sela

Su yi sowa don murna daga ƙwanƙolin duwatsu!

12 Bari waɗanda suke a manisantan ƙasashe su yi yabo,

Su kuma girmama Ubangiji!

13 Ubangiji ya fita domin ya yi yaƙi kamar jarumi,

Ya shirya, ya kuma ƙosa domin yaƙi.

Ya yi gunzar yaƙi da tsawar yaƙi,

Ya nuna ikonsa a kan abokan gābansa.

Allah Ya Yi wa Mutanensa Alkawarin Taimako

14 Allah ya ce,

“Na daɗe na yi shiru,

Ban amsa wa jama’ata ba.

Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu,

Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.

15 Zan lalatar da tuddai da duwatsu,

In kuma busar da ciyawa da itatuwa,

Zan mai da kwaruruka inda akwai rafi hamada,

In kuma busar da kududdufan ruwa.

16 “Zan yi wa mutanena makafi jagora

A hanyar da ba su taɓa bi ba.

Zan sa duhunsu ya zama haske,

In kuma sa ƙasa mai kururrumai ta zama sumul a gabansu.

Ba zan kasa yin waɗannan abu ba.

17 Dukan waɗanda suke dogara ga gumaka,

Masu kiran siffofi allolinsu,

Za a ƙasƙantar da su, su kuma sha kunya.”

Isra’ila Suka Kāsa Koyo

18 Ubangiji ya ce,

“Ku kasa kunne, ya ku kurame!

Ku duba da kyau sosai, ku makafi!

19 Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta,

Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko?

20 Isra’ila, kun ga abu da yawa,

Amma bai zama da ma’ana a gare ku ba ko kaɗan.

Kuna da kunnuwan da za ku ji,

Amma a ainihi me kuka ji?”

21 Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa,

Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,

22 Amma yanzu an washe mutanensa,

Aka kukkulle su a kurkuku,

Aka ɓoye su a rami.

Aka yi musu fashi, aka washe su,

Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su.

23 Ko akwai wanda zai kasa kunne ga wannan?

Ko za ku kasa kunne ku yi lura daga yanzu?

24 Wane ne ya ba da Isra’ila ga masu waso?

Ubangiji ne kansa, shi wanda muka yi wa zunubi!

Ba mu iya zama kamar yadda yake so mu yi ba,

Ko mu yi biyayya da koyarwarsa da ya ba mu.

25 Domin haka ya sa mu ji zafin fushinsa,

Mu kuma sha wahalar da yaƙi ya kawo.

Fushinsa ya yi ƙuna cikin dukan Isra’ila kamar wuta,

Amma ba mu taɓa sanin abin da yake faruwa ba,

Ba mu koyi kome daga wannan ba ko kaɗan.

Categories
ISH

ISH 43

Ubangiji kaɗai ne Mai Fansa

1 Ya Isra’ila, Ubangiji wanda ya halicce ku ya ce,

“Kada ku ji tsoro, na fanshe ku.

Na kira ku da sunanku, ku nawa ne.

2 Sa’ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi,

Zan kasance tare da ku,

Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba.

Sa’ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba,

Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.

3 Gama ni ne Ubangiji Allahnku,

Allah Mai Tsarki na Isra’ila, wanda ya cece ku.

Zan ba da Masar, da Habasha, da Seba

Ga Sairus domin fansarku.

4 Zan ba da dukan al’ummai don in ceci ranku,

Gama kuna da daraja a gare ni,

Gama na ba ku girma, ina kuma ƙaunarku.

5 Kada ku ji tsoro, ina tare da ku!

“Daga gabas mafi nisa, da kuma yamma mafi nisa,

Zan kawo jama’arku zuwa gida.

6 Zan faɗa wa kudu su bar su su tafi,

Arewa kuma kada su riƙe su a can.

Bari mutanena su komo daga manisantan ƙasashe,

Daga kowane sashi na duniya.

7 Su mutanena ne, na kaina,

Na kuwa halicce su don su girmama ni.”

8 Allah ya ce,

“Kirawo mutanena a ɗakin shari’a.

Suna da idanu, amma makafi ne,

Suna da kunnuwa, amma kurame ne!

9 Kirawo sauran al’umma, su zo ga shari’a.

A cikin allolinsu wane zai iya faɗar abin da yake a gaba?

A cikinsu wa ya yi hurci a kan abin da yake faruwa yanzu?

Bari waɗannan alloli su kawo shaidunsu

Don su tabbatar daidai suke,

Su shaida gaskiyar maganganunsu.

10 “Ya jama’ar Isra’ila, ku ne shaiduna,

Na zaɓe ku al’umma, baiwata,

Domin ku san ni, ku gaskata ni,

Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah.

In banda ni ba wani Allah,

Ba a taɓa yin wani ba,

Ba kuwa za a yi ba.

11 “Ni kaɗai ne Ubangiji,

Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.

12 Na faɗi abin da zai faru

Sa’an nan na zo domin taimakonku.

Ba wani gunkin da ya taɓa yin haka,

Ku ne shaiduna.

13 Ni ne Allah, haka kuwa nake tutur,

Ba wanda zai iya tserewa daga ikona,

Ba mai iya sāke abin da na riga na yi.”

Za a Hallaka Babila

14 Allah Mai Tsarki na Isra’ila, Ubangiji wanda ya fanshe ku ya ce,

“Domin in cece ku zan aiko sojoji gāba da Babila,

Zan rushe ƙofofin birni,

Sowar mutanen birnin za ta zama kuka.

15 Ni ne Ubangiji, Allahnku Mai Tsarki na Isra’ila,

Ni na halicce ku, ni ne kuma sarkinku.”

16 Tuntuni Ubangiji ya shirya hanya ta cikin teku,

Da turba kuma a cikin ruwa.

17 Ya bi da manyan sojoji zuwa hallaka,

Sojojin karusai da na dawakai.

Sun faɗi warwar, ba za su ƙara tashi ba,

An hure su kamar ‘yar wutar fitila!

18 Amma Ubangiji ya ce,

“Kada ku maƙale wa abubuwan da suka wuce,

Ko ku riƙa tunanin abin da ya faru tuntuni.

19 Ku duba abin da nake shirin yi.

Yana ta faruwa ma, kuna iya ganinsa yanzu!

Zan yi hanya a cikin jeji,

In kuma ba ku rafuffukan ruwa a can.

20 Har da namomin jeji za su girmama ni,

Diloli da jiminai za su yi yabona

Sa’ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada,

Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena.

21 Su ne mutanen da na yi domin kaina,

Za su raira yabbaina!”

22 Ubangiji ya ce,

“Amma ba ni kuka yi wa sujada ba,

Kun gaji da ni, ya Isra’ila.

23 Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba,

Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba.

Ban nawaita muku da neman hadayu ba,

Ko in gajiyar da ku da roƙon turare.

24 Ba ku sayi turare domina ba,

Ko ku gamshe ni da kitsen dabbobinku.

Maimakon haka, sai kuka nawaita mini da zunubanku,

Kuka gajiyar da ni da abubuwan da kuke aikatawa da ba daidai ba.

25 Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku,

Na kuwa yi haka saboda yadda nake.

Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.

26 “Bari mu tafi ɗakin shari’a, ku kawo ƙararrakinku.

Ku gabatar da matsalarku don a tabbatar kuna da gaskiya!

27 Kakanninku na farko sun yi zunubi,

Manyanku sun yi mini laifi.

28 Zan musunci masu mulkin tsattsarkan masujadai,

Saboda haka zan jawo wa Isra’ila hallaka,

Zan bari a la’anta mutanena su sha zagi!”

Categories
ISH

ISH 44

Ubangiji Shi Kaɗai ne Allah

1 Ubangiji ya ce,

“Ka saurara yanzu, ya Isra’ila, bawana,

Zaɓaɓɓun mutanena, zuriyar Yakubu,

2 Ni ne Ubangiji wanda ya halicce ku,

Tun farko, na taimake ku.

Kada ku ji tsoro, ku bayina ne,

Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda nake ƙaunarsu.

3 “Zan ba da ruwa ga ƙasa mai ƙishi,

In kuma sa rafuffuka su yi gudu a hamada.

Zan kwararo da albarka a kan ‘ya’yanku,

In sa albarkata kuma a kan zuriyarku.

4 Za su yi kumari kamar ciyawar da ta sami ruwa sosai,

Kamar itatuwan wardi a gefen rafuffukan ruwa mai gudu.

5 “Da ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya mutane za su ce, ‘Ni na Ubangiji ne!’

Za su zo su haɗa kai da jama’ar Isra’ila.

Ko wanne zai ɗaura sunan Ubangiji a dantsensa,

Ya ce da kansa ɗaya daga cikin mutanen Allah.”

6 Ubangiji, wanda yake mulkin Isra’ila, ya kuma fanshe su,

Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan,

“Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici,

Ba wani Allah sai ni.

7 Ko akwai wanda zai iya yin abin da na yi,

Ya kuma fito fili ya faɗi abin da zai faru

Tun daga farko, har zuwa ƙarshe?

8 Ya jama’ata, kada ku ji tsoro!

Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu,

Na faɗa tun da wuri abin da zai faru.

Ku ne kuwa shaiduna!

Ko akwai wani Allah?

Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”

Wautar Bautar Gumaka

9 Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya.

10 Wannan aikin banza ne, mutum ya yi siffa da ƙarfe don ya yi mata sujada!

11 Dukan wanda ya yi mata sujada za a ƙasƙantar da shi. Mutanen da suka ƙera gumakan, ‘yan adam ne, ba wani abu ba. Bari su zo su tsaya gaban shari’a, za su razana, su kuma sha kunya.

12 Maƙeri yakan ɗauki guntun ƙarfe ya sa shi a wuta ya yi aiki. Da hannunsa mai ƙarfi yana ɗaukar guduma yana bugun ƙarfen, yana mai da shi siffa. Yakan ji yunwa, da ƙishi, yakan kuma ji gajiya.

13 Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa’an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu.

14 Zai yiwu ya sare itacen al’ul ya yi da shi, ko kuwa ya zaɓi itacen oak, ko na kasharina daga jeji. Ko kuwa ya dasa wani itace, ya jira ruwan sama don ya sa itacen ya yi girma.

15 Mutum yakan yi abin wuta da wani sashi na itacen, wani sashi kuma ya yi gunki da shi. Yakan hura wuta da wani sashi don ya ji ɗumi, yakan kuma toya gurasa. Yakan yi gunki da wani sashi, ya riƙa yi masa sujada!

16 Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!”

17 Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu’a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”

18 Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.

19 Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”

20 Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.

Ubangiji Mai Fansar Isra’ila

21 Ubangiji ya ce,

“Ka tuna da waɗannan abu, ya Isra’ila,

Ka tuna kai bawana ne.

Na halicce ka domin ka zama bawana,

Ba zan taɓa mantawa da kai ba.

22 Na shafe zunubanka kamar baƙin girgije,

Da girgije kuma zan rufe laifofinka

Ka komo wurina, ni ne na fanshe ka.”

23 Ku yi sowa ta farin ciki ya ku sammai!

Ku yi sowa ku zurfafan wurare na duniya!

Ku yi sowa ta murna, ku duwatsu, da kowane itace na jeji!

Ubangiji ya fanshi mutanensa, Isra’ila,

Saboda haka ya nuna girmansa.

24 “Ni ne Ubangiji, Mahaliccinku, Mai Fansarku.

Ni ne Ubangiji, Mahaliccin dukkan abu.

Ni kaɗai na shimfiɗa sammai,

Ba wanda ya taimake ni sa’ad da na yi duniya.

25 Na sa masu duba su zama wawaye,

Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari.

Na bayyana kuskuren maganar masu hikima,

Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.

26 Amma sa’ad da bawana ya yi annabci,

Sa’ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena,

Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika.

Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can,

Za a kuma sāke gina biranen Yahuza.

Waɗannan birane za su daina zama kufai.

27 Na yi umarni na sa teku ta ƙafe.

28 Na ce wa Sairus, ‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina,

Za ka yi abin da nake so ka yi,

Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima,

A kuma kafa harsashin ginin Haikali.’ ”

Categories
ISH

ISH 45

Ubangiji ya Mori Sairus

1 Sairus shi ne zaɓaɓɓen sarki na Ubangiji!

Ubangiji ya sa shi ya ci al’ummai,

Ya aike shi ya tuɓe ikon sarakuna,

Ubangiji zai buɗe masa ƙofofin birni.

Ubangiji ya ce wa Sairus,

2 “Ni kaina zan shirya hanya dominka,

Ina baji duwatsu da tuddai.

Zan kakkarye ƙyamaren tagulla,

In kuma daddatse gagara badau na baƙin ƙarfe.

3 Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare,

Sa’an nan za ka sani ni ne Ubangiji,

Allah na Isra’ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.

4 Na sa ka domin ka taimaki bawana Isra’ila,

Jama’ar da ni na zaɓa.

Na ba ka girma mai yawa,

Ko da yake kai ba ka san ni ba.

5 “Ni ne Ubangiji, ba wani Allah sai ni.

Zan ba ka irin ƙarfin da kake bukata,

Ko da yake kai ba ka san ni ba.

6 Na yi wannan domin dukan waɗanda suke daga wannan bangon duniya zuwa wancan

Su sani ni ne Ubangiji,

Ba kuwa wani Allah sai ni.

7 Ni na halicci haske duk da duhu,

Ni ne na kawo albarka duk da la’ana.

Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.

8 Zan aiko da nasara daga sararin sama kamar ruwan sama.

Ƙasa za ta buɗe ta karɓe ta,

Za ta kuwa hudo da ‘yanci da gaskiya.

Ni Ubangiji, ni zan sa haka ya faru.”

Ubangiji Mahalicci Ne

9 Ko tukunyar yumɓu tana iya gardama da magininta,

Tukunyar da take daidai da sauran tukwane?

Ko yumɓu ya iya tambayar abin da maginin yake yi?

Ko tukunya tana iya gunaguni a kan magininta?

10 Ko akwai wanda zai iya ce wa iyayensa,

“Don me kuka haife ni kamar haka?”

11 Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra’ila,

Shi wanda ya halicce su, ya ce,

“Ba ka da iko ka yi mini tambaya game da ‘ya’yana,

Ko ka faɗa mini abin da ya kamata in yi!

12 Ni ne wanda ya halicci duniya,

Na kuma halicci mutum don ya zauna cikinta.

Da ikona na shimfiɗa sammai,

Ina kuwa mallakar rana, da wata, da taurari.

13 Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu,

Don ya cika nufina ya daidaita al’amura.

Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai.

Zai sāke gina birnina, wato Urushalima,

Ya kuma ‘yantar da mutanena da suke bautar talala.

Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.”

Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.

14 Ubangiji ya ce wa Isra’ila,

“Dukiyar Masar da ta Habasha za ta zama taku,

Dogayen mutanen Seba kuma za su zama bayinku,

Za su bi ku suna a ɗaure da sarƙoƙi.

Za su rusuna a gabanku su tuba, su ce,

‘Allah yana tare da ku, shi kaɗai ne Allah.’ ”

15 Allah na Isra’ila, wanda ya ceci mutanensa,

Shi ne yakan ɓoye kansa.

16 Su waɗanda suka yi gumaka, dukansu za su sha kunya,

Dukansu za su zama abin kunya.

17 Amma Ubangiji ya ceci Isra’ila,

Nasararsa kuwa za ta tabbata har abada,

Mutanensa ba za su taɓa shan kunya ba.

18 Ubangiji ne ya halicci sammai,

Shi ne wanda yake Allah!

Shi ne ya shata duniya ya kuma yi ta,

Ya kafa ta, ta kahu da ƙarfi, za ta yi ƙarƙo!

Bai halicce ta hamada da ba kome a ciki ba,

Amma wurin zaman mutane.

Shi ne wanda ya ce, “Ni ne Ubangiji,

Ba kuwa wani Allah, sai ni.

19 Ba a ɓoye na yi magana ba,

Ban kuwa ɓoye nufina ba.

Ban ce jama’ar Isra’ila

Su neme ni a kowace hanyar ruɗami ba.

Ni ne Ubangiji, gaskiya kuwa nake faɗa,

Ina sanar da abin da yake daidai.”

Ubangiji da Gumakan Babila

20 Ubangiji ya ce,

“Ku taru wuri ɗaya ku jama’ar al’ummai,

Dukanku da kuka tsira daga faɗuwar mulki,

Ku gabatar da kanku domin shari’a!

Waɗancan da suka ɗauka gumakansu na itace,

Suna kuma addu’a ga allolin da ba su iya cetonsu,

Waɗannan mutane ba su san kome ba ko kaɗan!

21 Ku zo ku gabatar da matsalarku a ɗakin shari’a,

Bari waɗanda aka kai ƙara su yi shawara da juna.

Wane ne ya faɗi abin da zai faru,

Ya kuma yi annabci tuntuni?

Ashe, ba ni ba ne, Ubangiji, Allah wanda ya ceci mutanensa?

Ba wani Allah sai ni.

22 “Ku juyo wurina a cece ku,

Ku mutane ko’ina a duniya!

Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.

23 Abin da na faɗa gaskiya ne,

Ba kuwa zai sāke ba.

Ni, a dukkan yadda nake, na yi alkawari mai ƙarfi,

Kowa da kowa zai zo ya durƙusa a gabana,

Ya yi wa’adin zama mai biyayya a gare ni.

24 “Za su ce ta wurina kaɗai

Za a iya samun nasara da ƙarfi,

Amma dukan waɗanda suka raina ni za su sha kunya.

25 Ni Ubangiji, zan kuɓutar da dukan zuriyar Yakubu,

Za su kuwa yi yabona.”

Categories
ISH

ISH 46

1 “Wannan ne ƙarshen allolin Babila!

Dā ana yi wa Bel da Nebo sujada,

Amma yanzu ana labtunsu a kan jakuna,

Sun zama nawaya a kan dabbobin da suka gaji!

2 Wannan ne ƙarshen waɗannan alloli,

Gumaka ba su iya ceton kansu,

Aka kame su aka tafi da su.

3 “Ku kasa kunne gare ni ku zuriyar Yakubu,

Dukanku, mutanena da kuka ragu.

Ina ta lura da ku tun daga lokacin da aka haife ku.

4 Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku,

Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura.

Ni na halice ku zan kuwa lura da ku,

Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”

5 Ubangiji ya ce, “Da wane ne za ku kwatanta ni?

Akwai wani mai kama da ni?

6 Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya,

Suna auna azurfa a kan ma’auni.

Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki,

Sa’an nan suka rusuna suka yi masa sujada!

7 Suka ɗauke shi a kafaɗunsu su tafi da shi,

Suna ajiyewa a wani wuri, ya yi ta tsayawa a can,

Ba ya iya motsawa daga inda yake.

Idan wani ya yi addu’a gare shi, ba zai iya amsawa ba,

Ko ya cece shi daga bala’i.

8 “Ku tuna da wannan, ku masu zunubi,

Ku dubi irin abin da na yi.

9 Ku tuna da abin da ya faru tuntuni,

Ku sani, ni kaɗai ne Allah,

Ba kuwa wani mai kama da ni.

10 Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama,

Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru.

Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba,

Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.

11 Ina kiran wani mutum ya zo daga gabas,

Zai kawo sura kamar shaho,

Zai kammala abin da na shirya.

Na yi faɗi, zai kuwa cika.

12 “Ku kasa kunne gare ni, ku mutane masu taurinkai,

Ku da kuke tsammani nasara tana can da nisa.

13 Ina kawo ranar nasara kusa,

Ba ta da nisa ko kaɗan.

Nasarata ba za ta yi jinkiri ba.

Zan ceci Urushalima,

Zan kuma kawo ɗaukaka ga Isra’ila a can.”

Categories
ISH

ISH 47

Hukunci a kan Babila

1 Ubangiji ya ce,

“Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki,

Ki zauna a ƙasa cikin ƙura.

Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba!

Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi!

Ke baiwa ce yanzu!

2 Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari!

Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!

3 Mutane za su gan ki a ƙasƙance, a kunyace kuma,

A tuɓe ki tsirara kamar yarinyar da take baiwa.

Zan ɗauki fansa, ba kuwa wanda zai hana ni.”

4 Allah Mai Tsarki na Isra’ila ya fanshe mu,

Sunansa Ubangiji Mai Runduna ne!

5 Ubangiji ya ce wa Babila,

“Ki zauna shiru a cikin duhu,

Ba za su ƙara kiranki sarauniyar al’ummai ba!

6 Na yi fushi da mutanena,

Na maishe su kamar su ba nawa ba ne.

Na sa su a ƙarƙashin ikonki,

Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba,

Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.

7 Kina tsammani za ki yi ta zama sarauniya kullayaumin,

Ba ki ɗauki waɗannan al’amura a zuci ba,

Ko ki yi tunanin yadda za su ƙare.

8 “Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi,

Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya.

Kin ɗauka kina da girma kamar Allah,

Har kina ganin ba wani kamarki.

Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba,

Ko ki sha hasarar ‘ya’yanki.

9 Amma ba da jimawa ba, a rana ɗaya

Dukan waɗannan al’amura za su faru.

Kome sihirin da za ki yi,

Za ki rasa ‘ya’yanki, ki kuwa zama gwauruwa.

10 “Kin amince da kanki cikin muguntarki,

Kina tsammani ba wanda yake ganinki.

Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata,

Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah,

Ba mai kama da ni!’

11 Duk da haka bala’i zai auko miki,

Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba,

Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya,

Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!

12 Ki riƙe dukan sihirinki, da makarunki, da layunki,

Kina amfani da su tun kina ƙarama.

Watakila za su yi miki wani taimako,

Watakila kya iya tsoratar da abokan gāba.

13 Kome shawarar da kika samu ba ki da ƙarfi.

Bari mashawartanki su fito su cece ki,

Waɗancan mutane masu binciken taurari

Waɗanda suka zana taswirar sammai,

Su kuma faɗa miki

Dukan abin da zai faru da yake wata wata.

14 “Za su zama kamar budu,

Wuta kuwa za ta ƙone su ƙurmus!

Ba ma za su ko iya ceton kansu ba.

Harshen wuta zai fi ƙarfinsu,

Ba wutar da za su zauna, su ji ɗumi!

15 Nan ne inda shawararsu za ta kai ki,

Waɗannan masanan taurari da kika yi ta neman shawararsu dukan kwanakin ranki.

Dukansu za su bar ki, kowa ya tafi inda ya nufa,

Ba wanda zai ragu da zai cece ki.”

Categories
ISH

ISH 48

Annabci a kan Sababbin Abubuwa

1 Ku kasa kunne, ya jama’ar Isra’ila,

Ku da kuke zuriyar Yahuza.

Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji,

Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra’ila,

Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.

2 Amma duk da haka kuna fāriya, da cewa

Ku ne mazaunan birni mai tsarki,

Kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila,

Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.

3 Ubangiji ya ce wa Isra’ila,

“Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru,

Sa’an nan na sa ya faru ba labari!

4 Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne,

Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.

5 Tuntuni na yi faɗi a kan makomarku,

Na hurta abubuwa tun kafin su faru,

Domin kada ku ɗauka cewa gumakanku ne suka yi su,

Siffofinku ne kuma suka sa abin ya zama haka.

6 “Dukan abin da na faɗa yana cika yanzu,

Sai ku yarda, faɗata gaskiya ce.

Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwan da za su zo,

Abubuwan da ban bayyana su a dā ba.

7 Yanzu ne kaɗai nake sawa su faru,

Ba wani abu makamancin wannan da ya faru a baya.

Da ya faru, da za ku ɗauka cewa kun san kome a kansa.

8 Na sani ba za a iya gaskata ku ba,

Tun daga haihuwarku kuma an san ku da tayarwa.

Shi ya sa ba ku taɓa jin wannan ba ko kaɗan,

Ko kalma ɗaya ba ta taɓa shiga kunnenku ba.

9 “Saboda mutane su yi yabon sunana

Shi ya sa nake danne fushina,

Ina kuma ɓoye shi, kada in hallaka ku.

10 Na gwada ku da wutar wahala,

Kamar yadda ake tace azurfa a tanda,

Amma na tarar ba ku da amfani.

11 Abin da na yi, na yi shi don kaina ne,

Ba zan bari a rasa girmama sunana ba,

Ko kuwa wani dabam ya sami ɗaukaka

Wadda take tawa ce, ni kaɗai.”

Ubangiji Zai Fanshi Isra’ila

12 “Ku kasa kunne gare ni, ya Isra’ila, jama’ar da na kira!

Ni ne Allah, farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici!

13 Dantsena ne ya kafa harsashin ginin duniya,

Ya kuma shimfiɗa sammai.

Lokacin da na kira duniya da sararin sama,

Sukan zo nan da nan, su gabatar da kansu!

14 “Ku tattaru, ku duka, ku kasa kunne!

Ba ko ɗaya cikin alloli da zai iya yin annabci ba,

Cewa mutumin da na zaɓa, shi zai iya fāɗa wa Babila,

Zai yi abin da na umarce shi.

15 Ni ne na yi magana, na kuwa kira shi,

Na yi masa jagora na kuwa ba shi nasara.

16 “Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni,

Ku ji abin da nake faɗa.

Tun da farko na yi magana da ku a fili,

A koyaushe nakan cika maganata.”

(Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)

17 Allah Mai Tsarki na Isra’ila,

Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce,

“Ni ne Ubangiji Allahnku,

Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku,

Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.

18 “Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum!

Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku

Kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba!

Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa

Da suke bugowa zuwa gāɓa.

19 Zuriyarku za su yi yawa kamar tsabar yashi,

Zan kuma tabbatar, cewa ba za a hallaka su ba.”

20 Ku fita daga Babila, ku tafi a sake!

Ku yi sowar albishir da farin ciki, ku sa a sani a ko’ina,

“Ubangiji ya fanshi bawansa Isra’ila!”

21 Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi,

Ba su sha wahalar ƙishi ba.

Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu,

Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.

22 Ubangiji ya ce, “Ba mafaka domin masu zunubi.”

Categories
ISH

ISH 49

Bawan Ubangiji Zai Zama Haske ga Al’ummai

1 Ku kasa kunne gare ni, ku al’ummai manisanta,

Ku mutanen da suke zaune a can nesa!

Ubangiji ya zaɓe ni, tun kafin a haife ni,

Ya kuwa sa ni in zama bawansa.

2 Ya sa maganata ta yi kaifi kamar takobi,

Ya kiyaye ni da ikonsa.

Ya sa na zama kamar kibiya

Mai tsini shirayayyiya domin harbi.

3 Ya ce mini, “Isra’ila, kai bawana ne.

Mutane za su yabe ni saboda kai.”

4 Na ce, “Na yi aiki, amma a banza ne.

Na mori ƙarfina, amma ban ƙulla kome ba.”

Duk da haka na dogara ga Ubangiji, ya daidaita al’amura,

Shi zai sāka mini abin da na yi.

5 Ubangiji ya zaɓe ni tun kafin a haife ni.

Ya maishe ni bawansa domin in komo da mutanensa,

In komo da jama’ar Isra’ilan da aka warwatsar.

Ubangiji ya ba ni daraja,

Shi ne tushen ƙarfina.

6 Ubangiji ya ce mini,

“Bawana, ina da aiki mai girma dominka,

Ba komo da girman jama’ar Isra’ila da suka ragu kaɗai ba,

Amma zan sa ka zama haske ga al’ummai,

Domin dukan duniya ta tsira.”

7 Allah Mai Tsarki na Isra’ila, Mai Fansa,

Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai,

Al’ummai suka ƙi shi,

Bawa na masu mulki kuma,

“Sarakuna za su gan ka a sake,

Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma,

Shugabanni su kuma za su gani,

Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.”

Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji,

Allah Mai Tsarki na Isra’ila, ya zaɓi bawansa,

Ya kuwa cika alkawaransa.

Alkawarin Maido Urushalima

8 Ubangiji ya ce wa jama’arsa,

“Idan lokacin da zan cece ku ya yi, zan nuna muku alheri.

Zan ji kukanku in taimake ku.

Zan tsare ku in kiyaye ku,

Zan kuwa yi wa dukan mutane alkawari ta wurinku.

Zan bar ku ku sāke zama a ƙasarku wadda take kufai a yanzu.

9 Zan ce wa ‘yan kurkuku, ‘Ku tafi na sake ku!’

Waɗanda suke cikin duhu kuwa, in ce musu,

‘Ku fito zuwa wurin haske!’

Za su zama kamar tumakin da suke kiwo a tuddai,

10 Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba.

Ba za su sha zafin rana da na hamada ba,

Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su.

Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.

11 “Zan yi babbar hanya ta kan duwatsu,

In kuma shirya hanya domin mutanena su bi.

12 Mutanena za su zo daga can nesa,

Daga Birnin Sin a kudu,

Daga yamma, da arewa.”

13 Ku raira, ku sammai! Ki yi sowar murna, ke duniya!

Bari duwatsu su ɓarke da waƙa!

Ubangiji zai ta’azantar da mutanensa,

Zai ji juyayin mutanensa da suke shan wahala.

14 Amma mutanen Urushalima suka ce,

“Ubangiji ya yashe mu!

Ya manta da mu.”

15 Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce,

“Mace za ta iya mantawa da jaririnta,

Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa?

Ya yiwu mace ta manta da ɗanta,

To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.

16 Ya Urushalima, ba zan taɓa mantawa da ke ba,

Na rubuta sunanki a gabana.

17 “Su waɗanda za su sāke gina ki suna tafe yanzu,

Waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su tashi.

18 Ki dudduba, ki ɗaga idonki, ki ga abin da yake faruwa!

Mutanenki suna tattaruwa suna komowa gida!

Hakika, da yake ni ne Allah Mai Rai,

Za ki yi fāriya da mutanenki,

Kamar yadda amarya take fāriya da kayan adonta!

19 “Aka lalatar da ƙasar, ta zama kufai,

Amma yanzu za ta yi wa waɗanda suke komowa domin su zauna cikinta kaɗan.

Waɗanda suka lalatar da ke kuwa,

Za a kawar da su daga gare ki.

20 Mutanenki da aka haifa a lokacin zaman talala,

Wata rana za su ce miki,

‘Wannan ƙasa ta yi kaɗan ƙwarai,

Muna bukatar ƙarin wurin zama!’

21 Sa’an nan za ki ce wa kanki,

‘Wa ya haifa mini waɗannan ‘ya’ya?

Na rasa ‘ya’yana, ba kuwa zan iya haifar waɗansu ba.

Aka kore ni, aka yi mini ɗaurin talala,

Wane ne ya haifi waɗannan ‘ya’ya?

Aka bar ni, ni kaɗai,

Daga ina waɗannan ‘ya’ya suka fito?’ ”

22 Ubangiji Allah ya ce wa jama’arsa,

“Zan nuna alama ga al’ummai,

Za su kuwa kawo ‘ya’yanku gida.

23 Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku,

Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye.

Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma,

Da tawali’u za su nuna muku bangirma.

Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji,

Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.”

24 Kuna iya ku ƙwace wa sojoji wason da suka yi?

Kuna iya kuɓutar da ‘yan kurkuku daga ɗaurin masu baƙin mulki?

25 Ubangiji ya amsa ya ce,

“Wannan shi ne ainihin abin da zai faru.

Za a ƙwace kamammun yaƙi,

Za a kuma ƙwace wason da masu baƙin mulki ya yi.

Zan yi yaƙi da dukan wanda yake yaƙi da ku,

Zan kuwa kuɓutar da ‘ya’yanku.

26 Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna,

Za su yi māye, da kisankai, da fushi.

Sa’an nan dukan ‘yan adam za su sani, ni ne Ubangiji,

Wanda ya cece ku, ya fanshe ku.

Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra’ila.”

Categories
ISH

ISH 50

1 Ubangiji ya ce,

“Kuna tsammani na kori mutanena

Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa?

To, in haka ne ina takardar kisan auren?

Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta

Kamar mutumin da ya sayar da ‘ya’yansa?

A’a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku,

Aka tafi da ku saboda da laifofinku.

2 “Don me mutanena ba su amsa ba

Sa’ad da na je wurinsu domin in cece su?

Don me ba su amsa ba sa’ad da na yi kiransu?

Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne?

Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina,

Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada,

Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.

3 Ina da iko in sa sararin sama ya yi duhu,

In sa ya zama makoki domin matattu.”

Biyayyar Bawan Ubangiji

4 Ubangiji ya koya mini abin da zan faɗa,

Domin in iya ƙarfafa marar ƙarfi.

A kowace safiya yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya mini.

5 Ubangiji ya ba ni fahimi,

Ban kuwa yi masa tayarwa ba

Ko in juya in rabu da shi.

6 Na tsiraita ga masu dūkana.

Ban hana su sa’ad da suke zagina ba,

Suna tsittsige gemuna,

Suna tofa yau a fuskata.

7 Amma zaginsu ba zai yi mini ƙari ba,

Gama Ubangiji Allah yana taimakona.

Na ƙarfafa kaina domin in jure da su.

Na sani ba zan kunyata ba,

8 Gama Allah yana kusa,

Zai tabbatar da ni, marar laifi ne,

Ko akwai wanda zai iya kawo ƙararraki game da ni?

Bari mu je ɗakin shari’a tare!

Bari ya kawo ƙararrakinsa!

9 Ubangiji kansa zai kāre ni,

Wa zai iya tabbatar da ni mai laifi ne?

Dukan waɗanda suke sarana za su shuɗe,

Za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!

10 Ku duka da kuke tsoron Ubangiji,

Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa,

Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai,

Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku.

11 Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka juna

Ƙulle-ƙullenku za su hallaka ku!

Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru,

Za ku gamu da mummunar ƙaddara.

Categories
ISH

ISH 51

Maganar Ta’aziyya ga Sihiyona

1 Ubangiji ya ce,

“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuke so a cece ku,

Ku da kuka zo gare ni neman taimako.

Ku yi tunanin dutse inda kuka fito,

Da mahaƙar duwatsu inda kuka fito.

2 Ku yi tunani a kan kakanku Ibrahim,

Da Saratu, wadda kuke zuriyarta.

Sa’ad da na kira Ibrahim ba shi da ɗa,

Amma na sa masa albarka, na ba shi ‘ya’ya,

Na sa zuriyarsa suka yi yawa.

3 “Zan ji juyayi a kan Sihiyona,

Da dukan masu zama a kufanta.

Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu,

Kamar lambun da na dasa a Aidan.

Murna da farin ciki za su kasance a can,

Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.

4 “Ku kasa kunne gare ni, ku mutanena,

Ku saurara ga abin da nake faɗa,

Na ba da koyarwata ga al’ummai,

Dokokina za su kawo musu haske.

5 Zan zo da sauri in cece su,

Lokacina na nasara ya yi kusa.

Ni kaina zan yi mulki a kan al’ummai.

Manisantan ƙasashe za su jira ni in zo,

Za su jira da sa zuciya, ni in cece su.

6 Ku duba sammai, ku duba duniya!

Sammai za su shuɗe kamar hayaƙi,

Duniya kuwa za ta yage kamar tsohuwar tufa,

Dukan mutanenta kuma za su mutu.

Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,

Nasarata, ita ce za ta zama ta har abada.

7 “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai,

Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku.

Kada ku ji tsoro sa’ad da mutane suke yi muku ba’a da zagi.

8 Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!

Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,

Nasarata za ta kasance har abada abadin.”

9 Ya Ubangiji, ka tashi, ka taimake mu!

Ka nuna ikonka, ka cece mu,

Ka nuna ikonka kamar yadda ka yi a dā.

Kai ne ka daddatse dodon ruwa, wato Rahab.

10 Kai ne ka sa teku ta ƙafe,

Ka kuma shirya hanya ta ruwa,

Domin waɗanda kake cetonsu su haye.

11 Su waɗanda ka fansa

Za su kai Urushalima da farin ciki,

Da waƙa, da sowa ta murna.

Za su yi ta murna har abada,

Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.

12 Ubangiji ya ce,

“Ni ne wanda yake ƙarfafa ku.

Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa,

Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?

13 Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku,

Wanda ya shimfiɗa sammai,

Ya kuma kafa harsashin ginin duniya?

Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku,

Da waɗanda suke shiri su hallaka ku?

Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!

14 ‘Yan sarƙa za su fita ba da jimawa ba

Za su yi tsawon rai,

Su kuma sami dukan abincin da suke bukata.

15 “Ni ne Ubangiji Allahnku,

Na dama teku

Na sa raƙumanta suka yi ruri.

Sunana Ubangiji Mai Iko Dukka!

16 Na shimfiɗa sammai,

Na kafa harsashin ginin duniya,

Na ce wa Sihiyona, ‘Ku jama’ata ne!

Na ba ku koyarwata,

Na kuwa kiyaye ku da ikona.’ ”

Ƙarshen Wahalar Urushalima

17 Ya Urushalima, ki farka!

Ki tashi da kanki, ki miƙe!

Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha,

Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!

18 Ba wanda zai yi miki jagora,

Ba wani daga cikin mutanenki

Da zai kama hannunki.

19 Masifa riɓi biyu ta auko miki,

Yaƙi ya lalatar da ƙasarki,

Mutanenki suka tagayyara da yunwa.

20 A kan kusurwar kowane titi

Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi,

Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama.

Suka ji ƙarfin fushin Allah.

21 Ku mutanen Urushalima, masu shan wahala,

Ku da kuke tangaɗi kamar waɗanda suka bugu,

22 Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce,

“Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina.

Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.

23 Zan ba da shi ga waɗanda suke zaluntarku,

Su waɗanda suka sa kuka kwanta a tituna

Suka tattake ku, sai ka ce kun zama ƙura.”