Categories
ISH

ISH 62

1 Zan yi magana domin in ƙarfafa Urushalima,

Ba zan yi shiru ba,

Sai na ga adalcinta ya bayyana kamar haske,

Cetonta kuma ya haskaka kamar fitila da dare.

2 Ya Urushalima, al’ummai za su ganki mai gaskiya!

Dukan sarakunansu za su ga darajarki.

Za a kira ki da sabon suna,

Sunan da Ubangiji ya bayar da kansa.

3 Za ki zama kamar kyakkyawan rawani ga Ubangiji,

Wato kambin sarauta mai daraja gare shi.

4 Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba,

Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.”

Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.”

Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,”

Domin Ubangiji ya ji daɗinki,

Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.

5 Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa,

Za ku yi murna tare,

Kamar murnar amarya da ango.

6 Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki

Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana.

Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa,

Ba kuwa za su bari ya manta ba!

7 Ba za su bari ya huta ba, sai ya ceci Urushalima tukuna,

Ya sa ta zama birnin da dukan duniya za ta yaba wa.

8 Ubangiji ya yi alkawari mai ƙarfi,

Ta wurin ikonsa kuwa zai cika shi.

“Hatsinku ba zai ƙara zama abincin abokan gābanku ba,

Baƙi ba za su ƙara shanye ruwan inabinku ba.

9 Amma ku da kuka shuka hatsin kuka kuma girbe shi,

Za ku ci abinci, ku yi yabon Ubangiji!

Ku da kuka lura da itatuwan inabi kuka tara su,

Za ku sha ruwan inabi a filayen Haikalina.”

10 Ku mutanen Urushalima, ku fita daga cikin birni,

Ku gyara hanyoyi domin jama’arku da suke komowa!

Ku shirya babbar hanya,

Ku kawar da duwatsu daga hanyar!

Ku sa alama domin al’ummai su sani,

11 Ubangiji yana sanarwa ga dukan duniya,

Cewa, “Ku ce wa jama’ar Urushalima,

Ubangiji Mai Cetonku yana zuwa,

Yana kawo mutanen da ya cece su.”

12 Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama’ar Allah,”

“Jama’ar da Ubangiji ya Fansa!”

Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,”

“Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”

Categories
ISH

ISH 63

Ranar Ramawa ta Ubangiji

1 Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa?

Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.

2 Me ya sa tufafinsa suke da ja haka, kamar na mutumin da ya tattake ‘ya’yan inabi domin ya sami ruwan inabi?

3 Ubangiji ya amsa ya ce, “Na tattake al’ummai kamar ‘ya’yan inabi, ba kuwa wanda ya taimake ni. Na tattake su cikin fushina, jininsu kuwa ya fantsamar wa dukan tufafina.

4 Na ga lokacin da zan fanshi mutanena ya yi, lokaci ne da zan hukunta wa abokan gābansu.

5 Na yi mamaki sa’ad da na duba, sai na ga ba wanda zai taimake ni. Amma fushina ya sa na sami ƙarfi, har ni kaina na ci nasara.

6 Da fushina na tattake dukan sauran al’umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”

Alherin Ubangiji ga Isra’ila

7 Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa,

Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana.

Ya sa wa jama’ar Isra’ila albarka mai yawa,

Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.

8 Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su

9 daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala’ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,

10 amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.

11 Amma suka tuna da zamanin dā, zamanin Musa bawan Ubangiji, suka yi tambaya suka ce, “Yanzu fa, ina Ubangiji yake wanda ya ceci shugabannin jama’arsa daga teku? Ina Ubangiji yake, wanda ya ba Musa iko musamman?

12 Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al’amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama’arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”

13 Sa’ad da Ubangiji ya bi da su ta ruwa mai zurfi, suka taka kamar ingarmun dawakai, ba su ko yi tuntuɓe ba.

14 Kamar yadda ake bi da shanu cikin kwari mai dausayi, haka Ubangiji ya ba mutanensa hutawa. Haka kuma Ubangiji ya bi da mutanensa, ya kuwa kawo ɗaukaka ga sunansa.

Addu’ar Neman Jinƙai da Taimako

15 Ya Ubangiji, ka dube mu daga Sama, wurin da kake cike da tsarki da ɗaukaka. Ina kulawan nan da kake yi mana? Ina ikon nan naka? Ina ƙaunan nan taka da juyayin nan naka? Kada ka watsar da mu.

16 Kai ne Ubanmu. Ko kakanninmu, wato su Ibrahim da Yakubu, ba za su iya taimakonmu ba, amma kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu. Kai ne Mai Fansarmu a koyaushe.

17 Don me ka bari muka ɓata daga al’amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.

18 Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka.

19 Mun zama kamar ba ka taɓa zama mai mulkinmu ba, kamar mu kuma ba mu taɓa zama mutanenka ba.

Categories
ISH

ISH 64

1 Don me ba za ka kware sararin sama, ka sauko ba? Duwatsu za su gan ka, su girgiza saboda tsoro!

2 Za su karkaɗu kamar ruwan da yake tafasa a wuta. Ka zo ka bayyana ikonka a kan abokan gābanka, ka sa al’ummai su yi rawar jiki a gabanka.

3 Ka taɓa zuwa ka yi abubuwan banrazana waɗanda ba mu sa tsammani ba, duwatsu suka ganka suka kaɗu domin tsoro.

4 Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.

5 Ka amince da waɗanda suke murna su aikata abin da yake daidai, su waɗanda suka tuna da yadda kake so su yi zamansu. Ka yi fushi da mu, amma muka ci gaba da yin zunubi, har da fushin da ka yi ƙwarai, muka ci gaba da aikata abin da ba daidai ba, tun daga zamanan dā.

6 Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.

7 Ba wanda ya juyo gare ka ya yi addu’a, ba wanda ya je gare ka neman taimako. Ka ɓuya mana, ka kuwa yashe mu saboda zunubanmu.

8 Amma kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu,

9 saboda haka kada ka yi fushi da mu ainun, ko ka riƙe da zunubanmu har abada, mu dai mutanenka ne, ka yi mana jinƙai.

10 Keɓaɓɓun biranenka suna kama da hamada, aka kuma ƙaurace wa kufan Urushalima.

11 Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su.

12 Ya Ubangiji, dukan wannan bai sa ka yi wani abu ba? Ba za ka yi kome ba, kana kuwa sa mu yi ta shan wuya, har fiye da yadda muke iya daurewa?

Categories
ISH

ISH 65

Hukuncin Allah a kan Masu Tawaye

1 Ubangiji ya ce, “Na shirya in amsa addu’o’in mutanena, amma ba su yi addu’a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al’ummar ba ta yi addu’a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, ‘Ga ni nan, zan taimake ku.’

2 Kullum ina a shirye domin in marabci waɗannan mutane, waɗanda saboda taurinkansu suka yi ta aikata abin da ba daidai ba, suka bi hanyoyin kansu.

3 Suka yi ta ƙara sa ni fushi ta wurin rashin kunyarsu. Suka miƙa hadayu irin na arna a ɗakunan tsafi da suke a lambu, suka kuma ƙona turare a kan bagadan arna.

4 Da dare sukan tafi cikin kogwanni da kaburbura, suna neman shawarar kurwar matattu. Waɗannan mutane sukan ci naman alade, su kuma sha romon naman da aka miƙa hadaya irin ta arna.

5 Sa’an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.

6 “Na riga na ƙudura hukuncinsu, shari’ar da aka yanke kuwa an rubuta ta. Ba zan ƙyale abin da suka aikata ba, amma zan sāka musu

7 saboda zunubansu da zunuban kakanninsu. Gama suka ƙona turare a ɗakunan tsafin arna na kan tuddai, suka kuwa faɗi mugun abu a kaina. Saboda haka zan hukunta su yadda ya cancance su.”

8 Ubangiji ya ce, “Ba wanda ya lalatar da ‘ya’yan inabi, maimakon haka sai suka yi ruwan inabi da su. Ni kuwa ba zan hallakar da dukan mutanena ba, zan ceci waɗanda suke bauta mini.

9 Zan sa wa Isra’ilawa waɗanda suke na kabilar Yahuza albarka, zuriyarsu kuma za su mallaki ƙasata da duwatsuna. Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda suke bauta mini za su zauna a can.

10 Za su yi mini sujada, za su kai tumakinsu da shanunsu wurin kiwo a kwarin Sharon a wajen yamma, da kuma a kwarin Akor a wajen gabas.

11 “Amma ba haka zai zama ba, ga ku da kuka rabu da ni, ku waɗanda kuka yi watsi da Sihiyona, tsattsarkan dutsena, kuka yi sujada ga Gad da Meni, wato allolin sa’a da na ƙaddara.

12 Mutuwa ta ƙarfi da yaji za ku yi, gama sa’ad da na yi kiranku ba ku amsa ba, ba ku kasa kunne ba kuwa sa’ad da nake magana da ku. Kuka zaɓa ku yi mini rashin biyayya, ku kuma aikata mugunta.

13 Saboda haka ina faɗa muku, cewa su waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yi mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya.

14 Za su raira waƙa don farin ciki, amma ku za ku yi kuka da karayar zuci.

15 Zaɓaɓɓun mutane ne za su mori sunayenku wajen la’antarwa. Ni, Ubangiji, zan kashe ku. Amma zan ba da sabon suna ga waɗanda suke yi mini biyayya.

16 Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”

Sabuwar Sama da Sabuwar Duniya

17 Ubangiji ya ce, “Ina yin sabuwar duniya da sabon sararin sama. Abubuwa na dā za a manta da su ɗungum.

18 Ku yi murna da farin ciki a kan abin da na halitta. Sabuwar Urushalima da nake halittawa za ta cika da murna, jama’arta kuma za su yi farin ciki.

19 Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama’arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako.

20 Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.

21-22 Mutane za su gina gidaje su kuwa zauna a cikinsu, ba waɗansu dabam za su mori gidajen ba. Za su dasa gonakin inabi su kuwa ji daɗin ruwan inabi, ba waɗansu dabam za su sha shi ba. Mutanena za su yi tsawon rai kamar itatuwa. Za su ci cikakkiyar moriyar abubuwan da suka yi aikinsu.

23 Aikin da suka yi zai yi nasara, ‘ya’yansu ba za su gamu da bala’i ba, zan sa musu albarka duk da zuriyarsu har dukan zamanai.

24 Zan amsa addu’o’insu tun ma kafin su gama yin addu’a gare ni.

25 Kyarketai da ‘yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci budu kamar yadda shanu suke yi. Maciji ba zai ƙara zama abu mai hatsari ba. A kan Sihiyona tsattsarkan dutsena, ba za a sami wani abu da zai cutar ba, ko wani mugun abu.”

Categories
ISH

ISH 66

Hukuncin Ubangiji da Wadatar Sihiyona

1 Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?

2 Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali’u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.

3 “Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu’a ga gumaka. Suna jin daɗin al’amuran banƙyama a lokacin yin sujada.

4 Saboda haka zan aukar musu da masifa, ainihin abin da suke jin tsoro, gama ba wanda ya amsa sa’ad da na yi kira, ko ya kasa kunne sa’ad da na yi magana. Suka zaɓa su yi mini rashin biyayya, su kuma aikata mugunta.”

5 Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga ‘yan’uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba’a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya!

6 Ku kasa kunne! Waccan babbar hayaniya cikin birni, wancan amo a Haikali, amon Ubangiji ne da yake hukunta abokan gābansa!

7 “Tsattsarkan birnina yana kama da uwa wadda ta haifi ɗa, ba tare da naƙuda ba.

8 Ko akwai wanda ya taɓa gani ko ya ji labari irin wannan abu? Ko an taɓa haihuwar al’umma rana ɗaya? Sihiyona ba za ta sha wahala ba kafin a haifi al’umma.

9 Kada ku zaci zan kawo jama’ata a wurin haihuwa in kuma hana ta haihuwa.” Ubangiji ne ya faɗa.

10 Ku yi murna tare da Urushalima

Ku yi farin ciki tare da ita,

Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan!

Ku yi murna tare da ita yanzu,

Dukanku da kuka yi makoki dominta!

11 Za ku ji daɗin wadatarta,

Kamar yaro a ƙirjin mamarsa.

12 Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al’ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna.

13 Zan ta’azantar da ku a Urushalima, kamar yadda uwa take ta’azantar da ɗanta.

14 Sa’ad da kuka ga wannan ya faru, za ku yi murna, wannan zai ba ku ƙarfi da lafiya. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji, mai taimakon masu biyayya gare ni, ina kuwa nuna fushina a kan abokan gābana.”

15 Ubangiji zai zo da wuta. Zai hau a kan fikafikan hadiri, domin ya hukunta waɗanda yake fushi da su.

16 Zai hukunta dukan mutanen duniya da wuta da takobi, waɗanda ya same su da laifi, za su kuwa mutu.

17 Ubangiji ya ce, “Ƙarshe ya kusa ga waɗanda suka tsabtace kansu domin sujadar arna, suka kuma yi jerin gwano zuwa ɗakin tsafi a lambu, inda suka ci naman alade da na ɓera, da waɗansu abinci masu banƙyama.

18 Na san tunaninsu da ayyukansu. Ina zuwa domin in tattara jama’ar dukan al’ummai. Sa’ad da suka tattaru, za su ga abin da ikona zai yi,

19 su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu.

“Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al’ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al’ummai.

20 Za su taho da ‘yan ƙasarku daga al’ummai, su kawo mini su kyauta. Za su zo da su a tsattsarkan dutsena, wato Urushalima, za su kawo su a kan dawakai, da alfadarai, da raƙuma, da cikin karusai, kamar dai yadda Isra’ilawa suke kawo hadaya ta hatsi a Haikali cikin tsabtatattun ƙore.

21 Zan sa waɗansu su zama firistoci da Lawiyawa.”

22 Ubangiji ya ce, “Kamar yadda sabuwar duniya da sabon sararin sama za su tabbata ta wurin ikona, haka zuriyarku da sunanku za su tabbata.

23 A kowane bikin amaryar wata, da kowace ranar Asabar, jama’ar kowace al’umma za su zo su yi mini sujada a nan cikin Urushalima.

24 Sa’ad da suke tafiya, za su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa. Tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, wutar da take ƙona su kuma ba za ta taɓa mutuwa ba. Dukan mutane za su ji ƙyamarsu.”

Categories
IRM

IRM 1

Kiran Irmiya da Keɓewarsa

1 Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,

2 wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa,

3 da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.

4 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

5 “Na san ka tun kafin a yi cikinka,

Na keɓe ka tun kafin a haife ka,

Na sa ka ka zama annabi ga

al’ummai.”

6 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah!

Ban san abin da zan faɗa ba,

Gama ni yaro ne.”

7 Amma Ubangiji ya ce mini,

“Kada ka ce kai yaro ne,

Kai dai ka tafi wurin mutanen da zan

aike ka,

8 Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da

kai,

Zan kiyaye ka.

Ni Ubangiji na faɗa.”

9 Sa’an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini,

“Ga shi, na sa maganata a bakinka.

10 Ga shi, a wannan rana na ba ka iko a

kan al’ummai da mulkoki,

Don ka tumɓuke, ka rusar,

Ka hallakar, ka kaɓantar,

Ka gina, ka dasa.”

11 Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?”

Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”

12 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”

13 Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce, “Me kuma ka gani?”

Na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, daga wajen arewa kamar za ta jirkice wajen kudu.”

14 Sai Ubangiji ya ce mini, “Daga wajen arewa masifa za ta fito ta auka wa dukan mazaunan ƙasar.

15 Ga shi kuwa, ina kiran dukan kabilan mulkokin arewa, za su kuwa zo su kafa gadajen sarautarsu a ƙofofin Urushalima, su kewaye dukan garukanta da dukan sauran biranen Yahuza.

16 Zan hurta hukuncin da zan yi musu saboda dukan muguntarsu, da suka bar bina, suka ƙona turare ga gumaka, suka kuma bauta wa gumakan da suka yi.

17 Amma kai, ka tashi ka sha ɗamara, ka faɗa musu dukan abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu domin kada in tsoratar da kai a gabansu.

18 Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar.

19 Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”

Categories
IRM

IRM 2

Ubangiji Ya Ji da Isra’ila da Masu Ridda

1 Ubangiji ya ce mini,

2 in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce,

“Na tuna da amincinki a lokacin

ƙuruciyarki,

Da ƙaunarki kamar ta amarya da

ango.

Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a

ƙasar da ba a shuka ba.

3 Isra’ila tsattsarka ce ta Ubangiji,

Nunar fari ta girbina.

Dukan waɗanda suka ci daga cikinki

sun yi laifi,

Masifa za ta auko miki.

Ni Ubangiji, na faɗa.”

4 Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra’ila.

5 Ubangiji ya ce,

“Wane laifi ne na yi wa kakanninku,

Da suka bar bina?

Suka bauta wa gumaka marasa

amfani,

Su kuma suka zama marasa amfani.

6 Ba su kula da ni ba,

Ko da yake na cece su daga ƙasar

Masar.

Na bi da su a cikin hamada,

A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai,

Busasshiya mai yawan hatsari,

Ba a bi ta cikinta,

Ba wanda yake zama cikinta kuma.

7 Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi,

Don su more ta su ci amfaninta,

Amma da suka shiga, sun ƙazantar

mini da ita,

Suka sa ƙasar da na gādar musu ta

zama abar ƙyama.

8 Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji

Yake?’ ba.

Masanan shari’a ba su san ni ba.

Masu mulki sun yi mini laifi,

Annabawa sun yi annabci da sunan

Ba’al,

Sun bi waɗansu abubuwa marasa

amfani.”

Shari’ar da Ubangiji yake Yi wa Mutanensa

9 “Domin haka, ni Ubangiji zan

gabatar da ku gaban shari’a,

Ku da ‘ya’yanku, da ‘ya’yan

‘ya’yanku, wato jikokinku.

10 Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajen

yamma, ku gani,

Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, ku

duba da kyau,

A dā an taɓa yin wani abu haka?

11 Akwai wata al’umma da ta taɓa

sāke gumakanta

Ko da yake su ba kome ba ne?

Amma mutanena sun sauya darajarsu

da abin da ba shi da rai.

12 Sammai, ku girgiza saboda wannan,

ku razana,

Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.

13 Mutanena sun yi zunubi iri biyu,

Sun rabu da ni, ni da nake

maɓuɓɓugar ruwan rai,

Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa,

hudaddu,

Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.

14 “Isra’ila ba bawa ba ne, ba a kuma

haife shi bawa ba,

Amma me ya sa ya zama ganima?

15 Zakuna suna ruri a kansa,

Suna ruri da babbar murya.

Sun lalatar da ƙasarsa,

Garuruwansa sun lalace,

Ba wanda yake zaune cikinsu.

16 Mutanen Memfis kuma da na

Tafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.

17 Ya Isra’ila, kai ne ka jawo wa kanka

wannan,

Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,

Sa’ad da ya bishe ka a hanya.

18 Wace riba ka samu, har da ka tafi

Masar,

Don ka sha ruwan Kogin Nilu?

Wace riba ka samu, har da ka tafi

Assuriya,

Don ka sha ruwan Kogin

Yufiretis?

19 Muguntarka za ta hore ka,

Riddarka kuma za ta hukunta ka.

Sa’an nan za ka sani, ka kuma

gane,

Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare

ka

Ka rabu da Ubangiji Allahnka,

Ba ka tsorona a zuciyarka.

Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na

faɗa.”

Isra’ila Ya Ƙi Yi wa Ubangiji Biyayya

20 “Ya Isra’ila, tun da daɗewa, ka ƙi

yarda

Ubangiji ya mallake ka,

Ka ƙi yin biyayya da ni,

Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’

Amma ka yi karuwanci a kan

kowane tudu,

Da kowane ɗanyen itace.

21 Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyar

kurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafi

kyau.

Ta yaya ka lalace haka ka zama

rassan kurangar inabi ta jeji,

Waɗanda ba zan yarda da su ba?

22 Ko da za ka yi wanka da sabulun

salo,

Ka yi amfani da sabulu mai yawa,

Duk da haka zan ga tabban

zunubanka.

Ni Ubangiji Allah na faɗa.

23 Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da

kanka ba,

Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba’al ba?

Ka duba hanyarka ta zuwa cikin

kwari, ka san abin da ka yi.

Kana kama da taguwa, mai yawon

neman barbara.

24 Kamar jakar jeji kake, wadda take

son barbara,

Wadda take busar iska,

Sa’ad da take son barbara, wa zai iya

hana ta?

Jakin da take sonta, ba ya bukatar

wahalar da kansa

Gama a watan barbararta za a same

ta.

25 Kai Isra’ila, kada ka bar ƙafafunka

ba takalma,

Kada kuma ka bar maƙogwaronka

ya bushe.

Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,

Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwa

zan bi.’

26 “Kamar yadda ɓarawo yakan sha

kunya sa’ad da aka kama shi,

Haka nan mutanen Isra’ila za su sha

kunya,

Da su, da sarakunansu, da

shugabanninsu,

Da firistocinsu, da annabawansu.

27 Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne

mahaifinmu.’

Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka

haife mu.’

Gama sun ba ni baya, ba su fuskance

ni ba.

Amma sa’ad da suke shan wahala,

sukan ce,

‘Ka zo ka taimake mu.’

28 Ina gumakan da kuka yi wa

kanku?

Bari su tashi in sun iya cetonku

lokacin wahalarku.

Yahuza, yawan gumakanku sun kai

Yawan garuruwanku.

29 Ni Ubangiji, ina tambayarku, ‘Wace

ƙara kuke da ita game da ni?’

Kun yi mini tawaye dukanku.

30 Na hori ‘ya’yanku, amma a banza, ba

su horu ba,

Kun kashe annabawanku da takobi

kamar mayunwacin zaki.

31 Ya ku mutanen zamanin nan, ku

saurari maganata.

Na zamar wa Isra’ila jeji? Ko ƙasar

da take da kurama?

Don me fa mutanena suke cewa,

‘Mu ‘yantattu ne,

Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?

32 Budurwa ta manta da kayan

kwalliyarta?

Ko kuwa amarya ta manta da kayan

adonta?

Amma mutanena sun manta da ni

kwanaki ba iyaka.

33 Kun sani sarai yadda za ku yi ku

farauci masoya,

Har mugayen mata ma, kun koya

musu hanyoyinku.

34 Tufafinku sun ƙasantu da jinin

marasa laifi,

Waɗanda ba ku same su suna fasa

gidajenku ba.

Amma duk da haka kuna cewa,

35 ‘Ba mu da laifi, hakika kuwa,

Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’

Amma ni Ubangiji zan hukunta ku,

Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.

36 Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya,

Sai ku yi nan ku yi can?

Masar za ta kunyata ku kamar yadda

Assuriya ta yi.

37 Da hannuwanku a kā za ku komo

daga Masar don kunya.

Gama waɗanda kuke dogara gare su,

ni Ubangiji, na ƙi su,

Ba za ku yi arziki tare da su ba.”

Categories
IRM

IRM 3

1 Ubangiji ya ce,

“Idan mutum ya saki matarsa,

Ta kuwa rabu da shi, har ta auri

wani,

Ya iya ya komo da ita?

Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da

ƙasar ba?

Ya Isra’ila, kin yi karuwanci,

Abokan sha’anin karuwancinki, suna

da yawa.

Za ki sāke komowa wurina?

Ni, Ubangiji, na faɗa.

2 Ki ta da idonki, ki duba filayen

tuddai ki gani,

Akwai wurin da ba ki laɓe kin yi

karuwanci ba?

Kin yi ta jiran abokan sha’anin

karuwancinki a kan hanya,

Kamar Balaraben da yake fako a

hamada.

Kin ƙazantar da ƙasar da mugun

karuwancinki.

3 Saboda haka aka ƙi yin ruwa,

Ruwan bazara bai samu ba.

Goshinki irin na karuwa ne, ba ki jin

kunya.

4 “Yanzu kin ce, ‘Kai ne mahaifina,

Ka ƙaunace ni tun ina cikin

ƙuruciyata.

5 Za ka dinga yin fushi da ni?

Za ka husata da ni har abada?’

Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi,

kin aikata dukan muguntar da

kika iya yi.”

Dole Isra’ila da Yahuza su Tuba

6 A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da take yi, ita marar amincin nan, wato Isra’ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta.

7 Na yi zaton bayan da ta aikata wannan duka, za ta komo wurina. Amma ba ta komo ba, maƙaryaciyar ‘yar’uwarta, wato Yahuza, ta gani.

8 Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar ‘yar’uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.

9 Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa.

10 Duk da haka maƙaryaciyar ‘yar’uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.”

11 Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra’ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba.

12 Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce,

“Ki komo ya Isra’ila, marar aminci,

Ni Ubangiji, na faɗa.

Domin ni mai jinƙai ne,

Ba zan yi fushi da ke ba.

Ba zan yi fushi da ke har abada ba,

Ni, Ubangiji na faɗa.

13 Ke dai ki yarda da laifinki,

Da kika yi wa Ubangiji Allahnki,

Kin kuma watsar da mutuncinki a

wurin baƙi

A gindin kowane itace mai duhuwa.

Kika ƙi yin biyayya da maganata,

Ni, Ubangiji, na faɗa.

14 “Ku komo, ya ku mutane marasa

aminci,

Gama ni ne Ubangijinku.

Zan ɗauki mutum guda daga kowane

gari,

In ɗauki mutum biyu daga kowane

iyali,

Zan komo da su zuwa Dutsen

Sihiyona.

15 Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi.

16 Sa’ad da kuka yawaita a ƙasar, mutane ba za su ƙara yin magana a kan akwatin alkawari na Ubangiji ba. Ba za su ƙara yin tunaninsa ko su tuna da shi, ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.

17 In lokacin nan ya yi, za a kira Urushalima gadon sarautar Ubangiji, dukan sauran a’umma za su taru a Urushalima da sunana. Ba za su ƙara bin tattaurar zuciyarsu mai mugunta ba.

18 A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra’ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.”

19 “Isra’ila, na yi niyya in karɓe ku

kamar ɗana,

In gādar muku da kyakkyawar

ƙasa

Mafi kyau a dukan duniya.

Na zaci za ku ce ni ne mahaifinku,

Ba za ku ƙara rabuwa da bina ba.

20 Hakika kamar yadda mace marar

aminci takan bar mijinta,

Haka kun zama marar aminci a gare

ni, ya jama’ar Isra’ila.

Ni Ubangiji, na faɗa.”

21 An ji murya a kan filayen tuddai,

Kūka da roƙo ne na ‘ya’yan

Isra’ila maza,

Domin sun rabu da hanyarsu,

Sun manta da Ubangiji Allahnsu.

22 “Ku juyo ku marasa aminci,

Zan warkar da rashin amincinku.”

“To, ga shi, mun zo gare ka,

Gama kai ne Ubangiji Allahnmu,

23 Daga kan tuddai ba mu da wani

taimako,

Ko daga hayaniyar da ake yi a kan

duwatsu,

Daga wurin Ubangiji Allahnmu ne

kaɗai taimakon Isra’ila yake

fitowa.

24 Amma yin sujada ga gunkin nan Ba’al ya cinye mana amfanin wahalar da kakanninmu suka sha tun muna yara, wato na garkunan tumakinsu, da na awakinsu, da na shanunsu, da ‘ya’yansu mata da maza.

25 Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.”

Categories
IRM

IRM 4

1 Ubangiji ya ce,

“Ya mutanen Isra’ila, idan za ku

juyo ku komo wurina,

Idan kuka kawar da abubuwan

banƙyama daga gabana,

Kuka kuma bar yin shakka,

2 Idan kun yi rantsuwa kuka ce,

‘Har da ran Ubangiji kuwa,‘

Da gaskiya, da aminci, da adalci,

Sa’an nan sauran al’umma za su so

in sa musu albarka,

Za su kuma yabe ni.”

3 Ubangiji ya ce wa mutanen Yahuza da na Urushalima,

“Ku kafce saurukanku,

Kada ku yi shuka cikin ƙayayuwa.

4 Ya ku mutanen Yahuza da na

Urushalima,

Ku yi wa kanku kaciya domin

Ubangiji,

Ku kawar da loɓar zukatanku

Don kada fushina ya fito kamar

wuta,

Ya cinye, ba mai iya kashewa,

Saboda mugayen ayyukan da kuka

aikata.”

Yahuza tana cikin Barazanar Yaƙi

5 “Ku yi shela a cikin Yahuza,

Ku ta da murya a Urushalima, ku

ce,

‘Ku busa ƙaho a dukan ƙasar!’

Ku ta da murya da ƙarfi, ku ce,

‘Ku tattaru, mu shiga birane masu

garu.’

6 Ku ta da tuta wajen Sihiyona!

Ku sheƙa a guje neman mafaka,

kada ku tsaya!

Gama zan kawo masifa da babbar

halaka daga arewa.

7 Zaki ya hauro daga cikin

ruƙuƙinsa,

Mai hallaka al’ummai ya kama

hanya,

Ya fito daga wurin zamansa don ya

mai da ƙasarku kufai,

Ya lalatar da biranenku, su zama

kango, ba kowa.

8 Domin haka sai ku sa tufafin

makoki,

Ku yi makoki ku yi kuka,

Gama fushin Ubangiji bai rabu da

mu ba.”

9 Ubangiji ya ce, “A ranan nan, sarki da sarakuna, za su rasa ƙarfin hali, firistoci za su firgita, annabawa kuwa za su yi mamaki.”

10 Sai na ce, “Kaito, kaito, ya Ubangiji Allah, ka ruɗi jama’an nan da Urushalima, da ka ce musu, ‘Za ku zauna lafiya,’ amma ga shi, takobi zai sassare su.”

11 Lokaci yana zuwa da za a faɗa wa mutanen Urushalima cewa, “Iska mai zafi za ta huro daga tuddan hamada zuwa wajen jama’ata, ba domin a sheƙe ta ko a rairaye ta ba!

12 Wannan iska da za ta zo daga wurin Ubangiji, tana da mafificin ƙarfi. Yanzu fa zan yanke hukunci a kansu.”

Abokan Gāba sun Kewaye Yahuza da Yaƙi

13 Duba, ga abokin gāba yana zuwa

kamar gizagizai,

Karusan yaƙinsa suna kama da

guguwa,

Dawakansa sun fi gaggafa sauri.

Kaitonmu, mun shiga uku!

14 Ya Urushalima, ki wanke mugunta

daga zuciyarki,

Domin a cece ki,

Har yaushe mugayen tunaninki za su

yi ta zama a cikinki?

15 Gama wata murya daga Dan ta

faɗa,

Ta kuma yi shelar masifar da za ta

fito daga duwatsun Ifraimu.

16 “A faɗakar da al’ummai, yana zuwa,

A faɗa wa Urushalima cewa,

‘Masu kawo mata yaƙi suna zuwa

daga ƙasa mai nisa,

Suna yi wa biranen Yahuza ihu.

17 Za su kewaye Yahuza kamar masu

tsaron saura,

Saboda ta tayar wa Ubangiji.’ Ni

Ubangiji na faɗa.

18 “Al’amuranki da ayyukanki suka

jawo miki wannan halaka,

Tana da ɗaci kuwa,

Ta soki har can cikin zuciyarki.”

Irmiya ya yi Baƙin Ciki don Mutanensa

19 Azaba! Ba zan iya daurewa da azaba

ba!

Zuciyata! Gabana yana faɗuwa da

ƙarfi,

Ba zan iya yin shiru ba,

Gama na ji amon ƙaho da hargowar

yaƙi.

20 Bala’i a kan bala’i,

Ƙasa duka ta zama kufai,

An lalatar da alfarwaina, ba zato ba

tsammani,

Labulena kuwa farat ɗaya.

21 Har yaushe zan yi ta ganin tuta,

In yi ta jin amon ƙaho?

22 Ubangiji ya ce,

“Mutanena wawaye ne,

Ba su san ni ba,

Yara ne dakikai,

Ba su da ganewa.

Suna gwanance da aikin mugunta,

Amma ba su san yadda za su yi

nagarta ba.”

23 Da na duba duniya sai na ga kufai ce

kawai ba kome,

Na kuma dubi sammai sai na ga ba

haske.

24 Da na duba duwatsu, sai na ga suna

makyarkyata,

Dukan tuddai kuma suna rawar jiki,

su yi gaba su yi baya.

25 Na duba sai na ga ba ko mutum

ɗaya,

Dukan tsuntsaye kuma sun tsere.

26 Na duba, sai na ga ƙasa mai dausayi

ta zama hamada,

An mai da dukan biranenta

kangwaye

A gaban Ubangiji saboda zafin

fushinsa.

27 Gama Ubangiji ya ce, “Ƙasar duka za ta zama kufai, amma duk da haka, ba wannan ne zai zama ƙarshenta na har abada ba.

28 Duniya za ta yi makoki saboda

wannan,

Sammai za su duhunta,

Gama ni na faɗa, haka kuwa na nufa

in yi,

Ba zan ji tausayi ba,

Ba zan kuwa fāsa ba.”

29 Da jin motsin mahayan dawakai da

na maharba

Kowane gari zai fashe.

Waɗansu za su shiga kurama,

Waɗansu kuma su hau kan duwatsu.

Dukan birane za su fashe tas,

Ba wanda zai zauna a cikinsu.

30 Ya ke da kike kufai marar kowa,

Me kike nufi da kika ci ado da mulufi,

Kike caɓa ado da kayan zinariya,

Kika sa wa idanunki tozali ram?

Kin yi kwalliyarki a banza,

Abokan sha’anin karuwancinki sun

raina ki,

Ranki suke nema.

31 Na ji kuka kamar na mace wadda take

naƙuda,

Na ji nishi kamar na mace a lokacin

haihuwarta ta fari,

Na ji kukan ‘yar Sihiyona tana

kyakyari,

Tana miƙa hannuwanta tana cewa,

“Wayyo ni kaina, gama ina suma a

gaban masu kisankai!”

Categories
IRM

IRM 5

Zunubin Urushalima da Yahuza

1 “Ku bi titunan Urushalima ko’ina!

Ku dudduba ku lura!

Ku bincika kowane dandali, ku gani,

Ko za ku iya samun ko mutum ɗaya

Mai aikata adalci, mai son gaskiya,

Sai in gafarta mata.

2 Ko da yake suna cewa, ‘Na rantse da

ran Ubangiji,’

Duk da haka rantsuwar ƙarya suke

yi.”

3 Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya

kake so ba?

Ka buge su, amma ba su yi nishi ba,

Ka hore su, amma sun ƙi horuwa,

Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse,

Sun ƙi tuba.

4 Sai na ce,

“Waɗannan mutane ba su da kirki,

Ba su da hankali,

Ba su san hanyar Ubangiji,

Ko shari’ar Allahnsu ba.

5 Zan tafi wurin manyan mutane, in yi

musu magana,

Gama sun san nufin Ubangiji, da

shari’ar Allahnsu.”

Amma dukansu sun ƙi yarda

Ubangiji ya mallake su,

Suka ƙi yi masa biyayya.

6 Domin haka zaki daga kurmi zai

kashe su,

Kyarkeci kuma daga hamada zai

hallaka su.

Damisa tana yi wa biranensu

kwanto,

Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a

yayyage shi,

Domin laifofinsu sun yi yawa,

Karkacewarsu babba ce.

7 “Don me zan gafarce ki?

‘Ya’yanki sun rabu da ni,

Sun yi rantsuwa da gumaka,

Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai,

Suka yi karuwanci, suka ɗunguma

zuwa gidajen karuwai,

8 Kamar ƙosassun ingarmu suke,

masu jaraba,

Kowa yana haniniya, yana neman

matar maƙwabcinsa.

9 Ba zan hore su saboda waɗannan

abubuwa ba?

Ni Ubangiji na ce, ba zan ɗauka wa

kaina fansa a kan wannan

al’umma ba?

10 Ku haura, ku lalatar da gonar

kurangar inabinta,

Amma kada ku yi mata ƙarƙaf,

Ku sassare rassanta,

Gama su ba na Ubangiji ba ne.

11 Gama mutanen Isra’ila da mutanen

Yahuza

Sun zama marasa aminci a gare ni.

Ni Ubangiji na faɗa.”

12 Sun yi ƙarya a kan Ubangiji,

Suka ce, “Ba abin da zai yi,

Ba wata masifa da za ta same mu.

Ba kuwa za mu ga takobi ko yunwa

ba.

13 Annabawa holoƙo ne kawai,

Maganar ba ta cikinsu.

Haka za a yi da su!”

Urushalima tana gab da Faɗuwa

14 Saboda haka Ubangiji Allah Mai

Runduna ya ce,

“Domin sun hurta wannan magana,

Ga shi, zan sa maganata a bakinka ta

zama wuta,

Waɗannan mutane kuwa su zama

itace,

Wutar za ta cinye su.

15 “Ya ku mutanen Isra’ila, ga shi, ina

kawo muku

Wata al’umma daga nesa,” in ji

Ubangiji,

“Al’umma ce mai ƙarfin hali ta tun

zamanin dā.

Al’umma wadda ba ku san harshenta

ba,

Ba za ku fahimci abin da suke faɗa

ba.

16 Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari

ne,

Dukansu jarumawa ne.

17 Za su cinye amfanin gonakinku da

abincinku.

Za su ƙare ‘ya’yanku mata da maza.

Za su cinye garkunanku na tumaki,

da na awaki, da na shanu,

Za su kuma cinye ‘ya’yan inabinku

da na ɓaurenku.

Za su hallaka biranenku masu kagara

da takobi, waɗanda kuke fariya da

su.

18 “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki ba zan yi muku ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.

19 “Sa’ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”

20 “Ka sanar wa zuriyar Yakubu da

wannan,

Ka kuma yi shelarsa a Yahuza, ka

ce,

21 ‘Ku ji wannan, ya ku wawaye,

marasa hankali,

Kuna da idanu, amma ba ku gani,

Kuna da kunnuwa, amma ba ku

ji.’ ”

22 Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona

ba?

Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba?

Ni ne na sa yashi ya zama iyakar

teku,

Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta

hayuwa,

Ko da yake raƙuman ruwa za su yi

hauka, ba za su iya haye ta ba,

Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta

ba.

23 Amma mutanen nan suna da taurin

zuciya, masu halin tayarwa ne,

Sun rabu da ni, sun yi tafiyarsu.

24 A zuciya ba su cewa,

‘Bari mu ji tsoron Ubangiji

Allahnmu

Wanda yake ba mu ruwan sama a

kan kari,

Na kaka da na bazara,

Wanda yake ba mu lokacin girbi.’

25 Laifofinku sun raba ku da waɗannan

abubuwa.

Zunubanku kuma sun hana ku

samun alheri.

26 “Gama an sami mugaye, a cikin

jama’ata,

Suna kwanto kamar masu kafa

ashibta.

Sun ɗana tarko su kama mutane.

27 Kamar kwando cike da tsuntsaye,

Haka nan gidajensu suke cike da cin

amana,

Don haka suka zama manya, suka

sami dukiya.

28 Sun yi ƙiba, sun yi bul-bul,

Ba su da haram a kan aikata

mugunta,

Ba su yi wa marayu shari’ar adalci,

don kada su taimake su.

A wajen shari’a ba su bin hakkin

matalauta.

29 “Ba zan hukunta su saboda

waɗannan abubuwa ba?

Ba zan ɗaukar wa kaina fansa a kan

al’umma irin wannan ba?

30 “Abin banmamaki da bantsoro

Ya faru a ƙasar.

31 Annabawa sun yi annabcin ƙarya,

Firistoci kuma sun yi mulki da ikon

kansu,

Mutanena kuwa suna so haka!

Amma sa’ad da ƙarshe ya zo, me za

ku yi?”