Categories
IRM

IRM 36

An Ƙone Littafi

1 A sa’ad da Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, yana shekara huɗu da sarauta, sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya, ya ce,

2 “Ka ɗauki takarda, ka rubuta dukan maganar da na yi maka a kan Isra’ila, da Yahuza, da dukan al’ummai, tun daga ran da na fara yi maka magana a zamanin Yosiya har ya zuwa yau.

3 Mai yiwuwa ne idan mutanen Yahuza suka ji dukan masifar da na yi niyya in aukar musu da ita, za su bar mugayen ayyukansu don in gafarta musu muguntarsu da zunubinsu.”

4 Sai Irmiya ya kirawo Baruk ɗan Neriya. Baruk kuwa ya rubuta maganar da Irmiya ya faɗa masa a takarda, wato dukan maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya.

5 Sai Irmiya ya umarci Baruk, ya ce, “An hana ni zuwa Haikali,

6 saboda haka kai za ka tafi. A ranar azumi za ka karanta wa mutane maganar Ubangiji, wadda take a takardar da ka rubuta ta wurin shibtar da na yi maka. Ka karanta ta a cikin Haikali, a gaban mutanen Yahuza waɗanda suka fito daga biranensu.

7 Mai yiwuwa ne za su roƙi Ubangiji, su tuba, su bar mugayen ayyukansu, gama Ubangiji yana fushi ƙwarai, Ubangiji ya hurta hasala a kan wannan jama’a.”

8 Sai Baruk ɗan Neriya ya yi dukan abin da annabi Irmiya ya umarce shi. Ya karanta takardan nan ta maganar Ubangiji a Haikalin Ubangiji.

9 A watan tara a shekara ta biyar ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, sai dukan jama’ar Urushalima da dukan jama’ar da suka zo Urushalima daga biranen Yahuza suka yi shela a yi azumi a gaban Ubangiji.

10 Sai Baruk ya karanta maganar Irmiya wadda take a takardar, kowa yana ji, a cikin Haikali a ɗakin Gemariya ɗan Shafan, magatakarda. Ɗakinsa yana a shirayi na bisa a hanyar shiga Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11 Sa’ad da Mikaiya ɗan Gemariya, ɗan Shafan, ya ji dukan maganar Ubangiji da take a littafin,

12 sai ya gangara gidan sarki, ya shiga ɗakin magatakarda, inda dukan shugabanni suke zaune, wato Elishama magatakarda, da Delaiya ɗan Shemaiya, da Elnatan ɗan Akbor, da Gemariya ɗan Shafan, da Zadakiya ɗan Hananiya, da dukan sarakuna.

13 Sai Mikaiya ya faɗa musu dukan maganar da ya ji sa’ad da Baruk ya karanta littafin a kunnuwan jama’a.

14 Sai dukan sarakunan suka aiki Yehudi ɗan Netaniya, ɗan Shelemiya, ɗan Kushi, ya faɗa wa Baruk ya kawo littafin nan da ya karanta wa jama’a. Sai Baruk ɗan Neriya ya ɗauki littafin ya je wurinsu.

15 Suka ce masa ya zauna, ya karanta musu littafin. Baruk kuwa ya karanta musu.

16 Da suka ji dukan maganar, suka dubi juna a firgice, suka ce wa Baruk, “Ai, sai mu faɗa wa sarki wannan magana.”

17 Suka kuma tambayi Baruk, suka ce, “Ka faɗa mana yadda ka yi ka rubuta wannan magana. Ya yi maka shibta ne?”

18 Sai Baruk ya ce musu, “Ya yi mini shibtar dukan wannan magana ne, na kuwa rubuta su da tawada a takarda.”

19 Sarakunan kuwa suka ce wa Baruk, “Ka tafi, da kai da Irmiya ku ɓuya kada ku bari kowa ya san wurin da kuke.”

20 Suka tafi zauren sarki bayan sun ajiye littafin a ɗakin Elishama, magatakarda, suka sanar da sarki dukan abin da yake cikin littafin.

21 Sarki ya aiki Yehudi ya je ya kawo littafin. Sai ya je ya ɗauko littafin daga ɗakin Elishama magatakarda. Yehudi kuwa ya karanta wa sarki tare da dukan sarakunan da suke tsaye kewaye da sarkin.

22 A watan tara ne, sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, ga wuta tana ci cikin kasko a gabansa.

23 Da Yehudi ya karanta sakin layi uku ko huɗu sai sarki ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone littafin duka.

24 Duk da haka da sarkin da barorinsa suka ji maganar, ba wanda ya ji tsoro, balle su keta rigunansu don baƙin ciki.

25 Ko da yake Elnatan, da Delaiya, da Gemariya, sun faɗa wa sarki kada ya ƙone littafin, amma ya yi biris da su.

26 Sarki ya umarci Yerameyel ɗan sarki, da Seraiya ɗan Azriyel da Shelemiya ɗan Abdeyel, su kamo Baruk magatakarda da annabi Irmiya, amma Ubangiji ya ɓoye su!

27 Bayan da sarki ya ƙone littafin da Baruk ya rubuta ta wurin shibtar da Irmiya ya yi masa, sai Ubangiji ya yi wa Irmiya magana, ya ce,

28 ya ɗauki wata takarda ya rubuta dukan maganar da take cikin littafin da Yehoyakim Sarkin Yahuza, ya ƙone.

29 Zai kuma ce wa Yehoyakim Sarkin Yahuza, “Haka Ubangiji ya ce maka, ka ƙone littafin, kana cewa, ‘Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle Sarkin Babila zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?’

30 Saboda haka Ubangiji ya ce Yehoyakim, Sarkin Yahuza, ba zai sami magāji wanda zai zauna a gadon sarautar Dawuda ba. Za a jefar da gawarsa a waje ta sha zafin rana, da dare kuma za ta sha matsanancin sanyi.

31 Zan hukunta shi, shi da zuriyarsa, da barorinsa saboda muguntarsu. Zan kawo dukan masifar da na hurta a kansu, da a kan mazaunan Urushalima, da a kan mutanen Yahuza, amma sun ƙi ji.”

32 Sai Irmiya ya ɗauko wata takarda ya ba Baruk, magatakarda, ɗan Neriya. Shi kuwa ta wurin shibtar Irmiya, ya rubuta dukan maganar da take a wancan littafi, wanda Yehoyakim Sarkin Yahuza ya ƙone a wuta. An ƙara magana da yawa kamar ta dā.

Categories
IRM

IRM 37

An Sa Irmiya a Kurkuku

1 Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim.

2 Amma shi da barorinsa, da mutanen ƙasar, ba wanda ya kasa kunne ga maganar Ubangiji wadda ya yi musu ta bakin annabi Irmiya.

3 Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma’aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allah dominmu.”

4 A lokacin nan Irmiya yana kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a tsare shi a kurkuku ba tukuna.

5 Rundunar sojojin Fir’auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.

6 Sai Ubangiji ya yi magana da annabi Irmiya, ya ce,

7 “Ni Ubangiji Allah na Isra’ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir’auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.

8 Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta.

9 Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo.

10 Ko da a ce za ku ci dukan rundunar sojojin Kaldiyawa wadda take yaƙi da ku, sauran waɗanda kuka yi wa rauni da suke kwance a alfarwai za su tashi su ƙone birnin da wuta.’ ”

11 Da rundunar sojojin Kaldiyawa ta janye daga Urushalima saboda zuwan rundunar sojojin Fir’auna,

12 sai Irmiya ya tashi daga Urushalima zai tafi can ƙasar Biliyaminu, don ya karɓi nasa rabo tare da dangi.

13 A sa’ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”

14 Sai Irmiya ya ce, “Ƙarya ce, ni ba gudu zuwa wurin Kaldiyawa nake yi ba.” Amma Irija bai yarda ba, sai ya kai shi wurin shugabanni.

15 Shugabanni suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka tsare shi a gidan Jonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.

16 Irmiya ya yi kwanaki da yawa can cikin kurkukun.

Zadakiya Ya Nemi Shawara ga Irmiya

17 Sarki Zadakiya ya aika a kawo masa Irmiya. Sarki kuwa ya shigar da shi gidansa, ya tambaye shi a asirce, ya ce, “Ko akwai wata magana daga wurin Ubangiji?”

Sai Irmiya ya ce, “Akwai kuwa!” Ya ci gaba ya ce, “Za a ba da kai a hannun Sarkin Babila.”

18 Sai kuma ya tambayi sarki Zadakiya ya ce, “Wane laifi na yi maka, ko barorinka, ko wannan jama’a da ka sa ni a kurkuku?

19 Ina annabawanku waɗanda suka yi maka annabci cewa, ‘Sarkin Babila ba zai kawo wa ƙasarku yaƙi ba?’

20 Yanzu ya maigirma sarki, ina roƙonka ka ji wannan roƙo da nake yi maka, kada ka mai da ni a gidan Jonatan magatakarda, domin kada in mutu a can.”

21 Sai sarki Zadakiya ya ba da umarni, suka sa Irmiya a gidan waƙafi. Aka riƙa ba shi malmalar abinci daga unguwar masu tuya kowace rana, har lokacin da abinci ya ƙare duka a birnin. Haka kuwa Irmiya ya zauna a gidan waƙafi.

Categories
IRM

IRM 38

An Fitar da Irmiya daga Rijiya Marar Ruwa

1 Shefatiya ɗan Mattan, da Gedaliya ɗan Fashur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da Fashur ɗan Malkiya, suka ji maganar da Irmiya yake faɗa wa dukan mutane cewa,

2 “Ubangiji ya ce wanda ya zauna a wannan birni zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma wanda ya fita ya je wurin Kaldiyawa zai rayu, zai sami ransa kamar ganimar yaƙi.

3 Gama Ubangiji ya ce, hakika za a ba da wannan birni a hannun rundunar sojojin Sarkin Babila su ci shi.”

4 Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama’a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama’a sai dai wahala yake nemar musu.”

5 Sarki Zadakiya ya ce, “Ai, ga shi nan a hannunku, gama sarki ba zai yi abin da ba ku so ba.”

6 Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.

7 Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda yake a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu.

8 Sai Ebed-melek ya fita, ya tafi gaban sarki, ya ce masa,

9 “Ya maigirma sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu da suka saka annabi Irmiya cikin fijiya, Zai mutu can da yunwa, gama ba sauran abinci a birnin.”

10 Sa’an nan sarki ya umarci Ebedmelek, mutumin Habasha, ya tafi da mutum talatin su tsamo annabi Irmiya daga cikin rijiyar kafin ya mutu.

11 Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a ɗakin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar.

12 Ebedmelek, mutumin Habasha, ya ce wa Irmiya ya sa tsummokin da tsofaffin tufafin a hammatarsa, ya zarga igiya, Irmiya kuwa ya yi yadda aka ce masa.

13 Suka jawo Irmiya da igiyoyi, suka fito da shi daga rijiya. Irmiya kuwa ya zauna a gidan waƙafi.

Zadakiya Ya Nemi Shawarar Irmiya

14 Sarki Zadakiya ya aika a kirawo annabi Irmiya. Ya tafi ya sadu da Irmiya a ƙofa ta uku ta Haikalin Ubangiji. Sarki kuwa ya ce wa Irmiya, “Zan yi maka tambaya, kada kuwa ka ɓoye mini kome.”

15 Irmiya kuwa ya ce wa Zadakiya, “Idan na faɗa maka gaskiya za ka kashe ni, idan kuma na ba ka shawara, ba za ka karɓi shawarata ba.”

16 Sarki Zadakiya ya rantse wa Irmiya a ɓoye, ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda yake ba mu rai, ba zan kashe ka ko in bashe ka a hannun waɗannan mutane da suke neman ranka ba.”

17 Irmiya ya ce wa Zadakiya, “Haka Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, idan ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila, za ka tsira, ba kuwa za a ƙone birnin da wuta ba, kai da gidanka za ku tsira.

18 Amma idan ba ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila ba, to, za a ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa, za su ƙone shi da wuta. Kai kuma ba za ka tsira daga hannunsu ba.”

19 Sarki Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawa waɗanda suka gudu zuwa wurin Kaldiyawa. Kila a bashe ni a hannunsu, su ci mutuncina.”

20 Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.

21 Amma idan ka ƙi miƙa wuya, to, ga abin da Ubangiji ya nuna mini a wahayi.

22 Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa,

‘Aminanka sun ruɗe ka,

Sun rinjaye ka.

Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutse

cikin laka,

Sai suka rabu da kai.’

23 “Dukan matanka da ‘ya’yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”

24 Sai Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan magana, kai kuwa ba za a kashe ka ba.

25 Idan sarakuna suka ji, wai na yi magana da kai, in suka zo wurinka, suka ce, ‘Ka faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da abin da sarki ya faɗa maka, kada ka ɓoye mana kome mu kuwa ba za mu kashe ka ba.’

26 Sai ka ce musu, ‘Na roƙi sarki da ladabi don kada ya mai da ni a gidan Jonatan, don kada in mutu a can.’ ”

27 Dukan sarakuna suka tafi wurin Irmiya suka tambaye shi. Shi kuwa ya amsa musu yadda sarki ya umarce shi. Sai suka daina magana da shi, tun da yake ba wanda ya ji maganar da ya yi da sarki.

28 Irmiya kuwa ya yi zamansa a gidan waƙafi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi.

Categories
IRM

IRM 39

Faɗuwar Urushalima

1 A watan goma a na shekara ta tara ta sarautar sarki Zadikiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, da dukan sojojinsa suka zo, suka kewaye Urushalima da yaƙi.

2 A rana ta tara ga watan huɗu, a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya, sai aka huda garun birnin.

3 Sa’an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.

4 Sa’ad da Zadakiya, Sarkin Yahuza, da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu, suka fita daga birnin da dare, ta hanyar gonar sarki a ƙofar da take a tsakanin garu biyu. Suka nufi zuwa wajen Araba.

5 Amma sojojin Kaldiyawa suka bi su, suka ci wa Zadakiya a filayen Yariko. Suka kama shi, suka kawo shi gaban Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a can Nebukadnezzar ya yanka masa hukunci.

6 Sarkin Babila ya kashe ‘ya’yan Zadakiya, maza, a Ribla a kan idon Zadakiya. Ya kashe dukan shugabannin Yahuza.

7 Ya kuma ƙwaƙule idanun Zadakiya, ya buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babila.

8 Sai Kaldiyawa suka ƙone gidan sarki, da gidajen jama’a. Suka kuma rushe garun Urushalima.

9 Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashi sauran mutane da suka ragu a birnin zuwa babila, wato mutanen da suka gudu zuwa wurinsa.

10 Amma ya bar matalauta waɗanda ba su da kome a ƙasar. Ya ba su gonakin inabi da waɗansu gonaki a ran nan.

Nebukadnezzar Ya Lura da Irmiya

11 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya yi wa Nebuzaradan shugaban matsara umarni a kan Irmiya ya ce,

12 “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.”

13 Sai Nebuzaradan shugaban matsara, da Nebushazban, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan shugabannin Sarkin Babila,

14 suka aika aka kawo Irmiya daga gidan waƙafi, suka ba da Irmiya amana ga Gedaliya, ɗan Ahikam ɗan Shafan, don ya kai shi gida. Da haka Irmiya ya zauna tare da mutane.

Ebed-melek yana Sa Zuciya ga Kuɓuta

15 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a lokacin da aka kulle shi a gidan waƙafi, ya ce,

16 “Ka tafi ka faɗa wa Ebedmelek mutumin Habasha, cewa Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan sa masifa, ba alheri ba, ta auko wa wannan birni. Wannan kuwa zai faru a kan idanunka a wannan rana.

17 Amma a ranan nan, ni Ubangiji zan cece ka, ba za a ba da kai a hannun mutanen da kake jin tsoronsu ba.

18 Gama hakika zan cece ka, ba za ka mutu ta takobi ba. Za ka sami ranka kamar ganimar yaƙi, domin ka dogara gare ni, ni Ubangiji na faɗa.’ ”

Categories
IRM

IRM 40

Irmiya da waɗanda Suka Ragu Sun Zauna tare da Gedaliya

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya bayan da Nebuzaradan shugaban matsara ya sake shi daga Rama, sa’ad da ya yi masa ƙuƙumi tare da waɗanda aka kwaso daga Urushalima da Yahuza, za su Babila.

2 Shugaban matsara ya ware Irmiya, sa’an nan ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ne ya hurta wannan masifa a kan wurin nan.

3 Ga shi kuwa, ya yi kamar yadda ya faɗa, domin kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, don haka wannan masifa ta auko muku.

4 Yau na kwance ƙuƙumin da yake a wuyanka, idan ka ga ya fi maka kyau, ka zo mu tafi tare zuwa Babila, to, sai ka zo, zan lura da kai da kyau, amma idan ba ka ga haka ya yi maka daidai ba, to, kada ka bi ni. Ga dukan ƙasa shimfiɗe a gabanka, ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.”

5 Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa’an nan ya sallame shi.

6 Irmiya kuwa ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa, ya zauna tare da shi da mutanen da suka ragu a ƙasar.

7 Sa’ad da shugabannin sojoji waɗanda suke a karkarar Yahudiya tare da mutanensu, suka ji labari Sarkin Babila ya sa Gedaliya ɗan Ahikam ya zama mai mulkin ƙasar, a kan matalauta, wato mata da maza, da yara na ƙasar, waɗanda ba a kwashe su zuwa bautar talala a Babila ba,

8 sai shugabannin, wato Isma’ilu ɗan Netaniya, da Yohenan da Jonatan, ‘ya’yan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, da ‘ya’yan Efai, mutumin Netofa, da Yazaniya ɗan mutumin Ma’aka suka tafi tare da mutanensu zuwa wurin Gedaliya a Mizfa.

9 Gedaliya ɗan Ahikam, jikan shafan ya rantse musu da mutanensu, ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Kaldiyawa, ku yi zamanku a ƙasar, ku bauta wa Sarkin Babila, za ku kuwa zauna lafiya.

10 Amma ni zan zauna a Mizfa, in zama wakilinku a wurin Kaldiyawa waɗanda za su zo wurinmu. Ku tattara inabi, da ‘ya’yan itatuwa na kaka, da man zaitun, ku tanada su a gidajenku, ku zauna a garuruwan da kuka ci.”

11 Haka kuma Yahudawan da suke a Mowab, da Ammon, da Edom, da kuma sauran ƙasashe suka ji, cewa Sarkin Babila ya bar waɗansu mutane a Yahuza, ya kuma shugabantar da Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan a kansu,

12 sai dukan Yahudawa suka koma daga inda aka kora su zuwa ƙasar Yahuza. Suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Suka tattara ruwan inabi da ‘ya’yan itatuwa na kaka da yawa.

Maƙarƙashiyar Isma’ilu gāba da Gedaliya

13 Yohenan ɗan Kareya kuwa, tare da dukan shugabannin sojojin da suke cikin sansani a karkara, suka zo wurin Gedaliya a Mizfa.

14 Suka ce masa, “Ko ka sani Ba’alis Sarkin Ammonawa ya aiko Isma’ilu ɗan Netaniya ya kashe ka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam, bai gaskata su ba.

15 Sai Yohenan ɗan Kareya ya yi magana da Gedaliya a Mizfa a asirce ya ce, “Ka bar ni in tafi in kashe Isma’ilu ɗan Netaniya, ba wanda zai sani. Don me shi zai kashe ka, ya watsa dukan Yahudawan da suke tare da kai, har sauran Yahudawan da suka ragu su halaka.”

16 Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohenan ɗan Kareya, “Kada ka kuskura ka yi wannan abu, gama ƙarya ce kake yi wa Isma’ilu.”

Categories
IRM

IRM 41

1 A watan bakwai sai Isma’ilu ɗan Netaniya, ɗan Elishama, na cikin zuriyar sarauta, ɗaya daga cikin ma’aikatan sarki, ya zo a wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa tare da mutum goma. Sa’ad da suke cin abinci tare a Mizfa,

2 Isma’ilu ɗan Netaniya, da mutanen nan goma da take tare da shi, suka tashi suka sare Gedaliya ɗan Ahikam ɗan shafan, da takobi, suka kashe shi, wato Gedaliya wanda Sarkin Babila ya naɗa ya zama mai mulkin ƙasar.

3 Isma’ilu kuma ya kashe dukan Yahudawa da suke tare da Gedaliya a Mizfa da waɗansu sojojin Kaldiyawa da suke a wurin.

4 Kashegari bayan da an kashe Gedaliya, tun kafin wani ya sani,

5 sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji.

6 Sai Isma’ilu ɗan Netaniya ya fito daga cikin Mizfa yana kuka, don ya tarye su. Da ya sadu da su, sai ya ce musu, “Ku zo mu tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam!”

7 Sa’ad da suka shiga birnin, sai Isma’ila ɗan Nataniya da mutanen da suke tare da shi suka kashe su, suka jefa su a wata rijiya.

8 Amma waɗansu mutum goma daga cikinsu suka ce wa Isma’ila, “Kada ka kashe mu, gama muna da rumbunan alkama, da na sha’ir, da kuma man zaitun da zuma a ɓoye a cikin gonaki.” Sai ya bar su, bai kashe su tare da abokansu ba.

9 Rijiyar da Isma’ilu ya zuba dukan gawawwakin mutanen da ya kashe mai zurfi ce, sarki Asa ne ya haƙa saboda tsoron Ba’asha Sarkin Isra’ila. Isma’ilu ɗan Netaniya kuwa ya cika ta da gawawwakin mutanen da ya kashe.

10 Sai Isma’ilu ya kwashe dukan sauran mutanen da suke Mizfa, gimbiyoyi da dukan jama’ar da aka bari a Mizfa, waɗanda Nebuzaradan, shugaban matsara, ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Isma’ilu ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya haye da su zuwa yankin Ammonawa.

11 Amma sa’ad da Yohenan ɗan Kareya, tare da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi suka ji irin wannan mugun aiki wanda Isma’ilu ɗan Netaniya ya yi,

12 sai suka kwashe mutanensu duka, suka tafi su yi yaƙi da Isma’ilu ɗan Netaniya. Suka iske shi a babban tafkin da take a Gibeyon.

13 Sa’ad da dukan jama’ar da Isma’ilu ya kwashe suka ga Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji tare da shi, sai suka yi murna.

14 Dukan mutanen nan da Isma’ilu ya kwashe su ganima daga Mizfa, suka juya, suka koma wurin Yohenan ɗan Kareya.

15 Amma Isma’ilu ɗan Netaniya tare da mutum takwas suka tsere suka gudu zuwa wurin Ammonawa.

16 Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama’a, waɗanda Isma’ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon.

17 Suka fa tafi suka zauna a wurin Kimham kusa da Baitalami. Suna nufin su tafi Masar,

18 don gudun Kaldiyawa, gama suna jin tsoronsu, domin Isma’ilu ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam wanda Sarkin Babila ya naɗa shi mai mulkin ƙasa.

Categories
IRM

IRM 42

Jawabin Irmiya ga Yohenan

1 Shugabannin sojoji, da Yohenan ɗan Kareya, da Yazaniya ɗan Hoshaiya, da jama’a duka, daga ƙarami zuwa babba, suka zo,

2 suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka.

3 Ka yi mana addu’a domin Ubangiji Allahnka ya nuna mana hanyar da za mu bi, da kuma abin da za mu yi.”

4 Annabi Irmiya kuwa ya ce musu, “Na ji abin da kuka ce. Ga shi kuwa, zan yi addu’a ga Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka roƙa. Kowace irin amsa da Ubangiji ya bayar, zan faɗa muku, ba zan ɓoye muku kome ba.”

5 Sa’an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji mai gaskiya, mai aminci ya zama shaida a tsakaninmu, idan ba mu yi duk yadda Ubangiji Allahnka ya aiko ka gare mu ba.

6 Ko nagari ne ko mugu ne, za mu yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu wanda muka aike ka wurinsa, gama zai zama alheri a gare mu idan mun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnmu.”

7 Bayan kwana goma sai Ubangiji ya yi magana da Irmiya.

8 Sai Irmiya ya kira Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi, da dukan jama’a tun daga ƙarami har zuwa babba.

9 Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni da koke-kokenku wurinsa ya ce,

10 ‘Idan za ku zauna a ƙasan nan, to, zan gina ku, ba zan rushe ku ba. Zan dasa ku, ba zan tumɓuke ku ba, gama zan janye masifar da na aukar muku.

11 Kada ku ji tsoron Sarkin Babila, shi wanda kuke jin tsoronsa. Kada ku ji tsoronsa,’ in ji Ubangiji, ‘gama ina tare da ku, zan cece ku, in kuɓutar da ku daga hannunsa.

12 Zan yi muku jinƙai in sa sarkin ya ji ƙanku, ya bar ku ku zauna a ƙasarku.’

13 “Amma idan kuka ce ba za ku zauna a wannan ƙasa ba, kuka ƙi yin biyayya da muryar Ubangiji Allahnku,

14 kuna cewa, ‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.’

15 To, sai ku ji maganar Ubangiji, ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Idan zuwa Masar kuka sa gaba don ku tafi ku zauna a can,

16 to, takobin nan da kuke jin tsoro, zai ci muku can a ƙasar Masar, yunwan nan kuma da kuke jin tsoro za ta bi ku zuwa Masar ta tsananta muku, a can za ku mutu.

17 Duk waɗanda suka sa gaba zuwa Masar domin su zauna can, da takobi, da yunwa, da annoba su ne ajalinsu. Ba wanda zai ragu, ba wanda zai tsira daga masifar da zan aukar musu.’

18 “Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama najasa, da abin ƙyama, da la’ana, da abin ba’a. Wannan wuri kuwa ba za ku ƙara ganinsa ba.’

19 “Ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji ya ce, ‘Kada ku tafi Masar.’ Ku tabbata fa na faɗakar da ku yau,

20 cewa in kun ratse, to, a bakin ranku. Gama kun aike ni wurin Ubangiji Allah cewa, ‘Ka roƙar mana Ubangiji Allahnmu. Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya ce ka faɗa mana kuma za mu aikata.’

21 A wannan rana kuwa na faɗa muku abin da ya ce, amma ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku a kan kowane abin da ya aiko ni in faɗa muku ba.

22 Domin haka yanzu fa ku sani takobi, da yunwa, da annoba, su ne ajalinku a wurin can da kuke sha’awar ku zauna.”

Categories
IRM

IRM 43

Tafiya zuwa Masar

1 Sa’ad da Irmiya ya gama faɗa wa dukan jama’a maganar da Ubangiji Allahnsu ya aiko musu da ita,

2 sai Yazaniya ɗan Hoshaiya, da Yohenan ɗan Kareya, da dukan ‘yan tsagera, suka ce wa Irmiya, “Ƙarya kake yi, Ubangiji Allahnmu bai aiko ka da cewa kada mu tafi, mu zauna a Masar ba!

3 Amma Baruk ɗan Neriya shi ne ya sa ka faɗi wannan magana gāba da mu, don ka bashe mu a hannun Kaldiyawa domin su kashe mu, ko kuwa su kai mu bauta a Babila.”

4 Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji, da dukan jama’a, ba su yi biyayya da umarnin Ubangiji, su zauna a ƙasar Yahuza ba.

5 Amma Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe sauran mutanen Yahuza duka waɗanda suka komo suka zauna a ƙasar Yahuza, daga wurin al’ummai, inda aka kora su,

6 mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya.

7 Suka zo ƙasar Masar, gama ba su yi biyayya da muryar Ubangiji ba. Suka sauka a Tafanes.

8 Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya a Tafanes ya ce,

9 “Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir’auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza,

10 ka kuma ce musu, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin.

11 Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi.

12 Zai cinna wa gidajen gumakan Masar wuta, zai ƙone su, ya tafi da waɗansu, zai tsabtace ƙasar Masar kamar yadda makiyayi yakan kakkaɓe ƙwarƙwata daga cikin tufafinsa, zai kuwa tashi daga wurin lafiya.

13 Zai kuma farfashe al’amudan duwatsu na On a ƙasar Masar. Zai ƙone gidajen gumakan Masar da wuta.’ ”

Categories
IRM

IRM 44

Jawabin Ubangiji zuwa ga Yahudawan da suke Masar

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan dukan Yahudawan da suke zaune a ƙasar Masar, a garin Migdol, da Tafanes, da Memfis, da dukan ƙasar Fatros, ya ce,

2 “Ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra’ila, na ce, ku da kanku kun ga masifar da na aukar wa Urushalima, da dukan garuruwan Yahuza. Yanzu sun zama kufai, ba wanda yake zaune a cikinsu,

3 domin mutanen da suke cikinsu sun aikata mugayen abubuwa da suka tsokane ni. Sun miƙa wa gumaka hadayu, suka kuma bauta musu, ko da yake su, ko ku, ko kakanninku, ba ku san su ba.

4 Na yi ta aika muku da dukan bayina annabawa waɗanda suka faɗa muku kada ku aikata wannan mugun abin banƙyama.

5 Amma ba su kasa kunne ba, ba su kuwa ji ba, da za su juyo daga mugayen ayyukansu na miƙa wa gumaka hadayu.

6 Saboda haka fushina ya yi zafi a kan garuruwan Yahuza da titunan Urushalima, don haka a yanzu sun lalace, suka zama kufai.

7 “Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?

8 Me ya sa kuke tsokanata da ayyukan hannuwanku, kuna miƙa wa gumaka hadayu a ƙasar Masar inda kuka zo don ku zauna? Yin haka zai sa a hallaka ku, ku zama abin la’ana da zargi a cikin dukan ƙasashen duniya.

9 Ko kun manta da mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakunan Yahuza da na matansu, da naku, da na matanku, waɗanda suka aikata a ƙasar Yahuza da kan titunan Urushalima?

10 Amma har wa yau ba ku ƙasƙantar da kanku ba, ba ku ji tsorona ba, ba ku kuwa kiyaye dokokina da umarnaina ba, waɗanda na ba ku ku da kakanninku.

11 “Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, zan aukar muku da masifa, in hallaka mutanen Yahuza duka.

12 Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la’antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya.

13 Zan hukunta dukan waɗanda suke zaune a Masar kamar yadda na hukunta wa Urushalima da takobi, da yunwa, da annoba.

14 Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai ‘yan gudun hijira.”

15 Sai dukan mazan da suka sani matansu sun miƙa wa gumaka hadayu, da dukan matan da suke tsaye a wurin, da dukan Yahudawan da suke zaune a Fatros, babban taron jama’a, suka ce wa Irmiya,

16 “Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba!

17 Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.

18 Amma tun da muka daina miƙa wa sarauniyar sama hadayu, da hadayu na sha, ba mu da kome, sai dai takobi da yunwa suke kashe mu.”

19 Mata kuma suka ce, “Sa’ad da muka toya waina ga siffar sarauniyar sama, muka miƙa mata hadayu, da hadayu na sha, ai, mazanmu sun goyi bayan abin da muka yi.”

20 Sa’an nan Irmiya ya ce wa dukan mutane, mata da maza, waɗanda suka ba shi irin amsan nan, ya ce,

21 “A kan turaren da ku da kakanninku, da sarakunanku, da shugabanninku, da mutanen ƙasar, kuka ƙona a garuruwan Yahuza da a titunan Urushalima, kuna tsammani Ubangiji bai san su ba, ko kuna tsammani ya manta?

22 Ubangiji ba zai yarda da mugayen ayyukanku ba, da ƙazantarku da kuka aikata, don haka ƙasarku a yau ta zama kufai ba mai zama a cikinta. Ta zama abin ƙyama da la’ana.

23 Saboda kun ƙona turare, kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, ba ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da sharuɗansa ba, shi ya sa wannan masifa ta auko muku a yau.”

24 Sai Irmiya ya ce wa dukan mutane duk da mata, “Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da suke a Masar.

25 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya ce, ‘Ku da matanku kun faɗa da bakinku, kun kuma aikata da hannuwanku, cewa za ku aikata wa’adodin da kuka yi na ƙona turare, da miƙa hadayu na sha ga sarauniyar sama.’ To, sai ku tabbatar da wa’adodinku, ku cika su!

26 Domin haka ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da yake zaune a ƙasar Masar. ‘Ni Ubangiji na rantse da sunana Maɗaukaki, cewa ba zan yarda kuma wani mutumin Yahuza da yake ƙasar Masar ya ambaci sunana da yin rantsuwa, cewa ya rantse da zatin Ubangiji ba.’

27 Ga shi, ina lura da su, ba domin alheri ba, amma domin in aukar musu da masifa. Takobi da yunwa za su hallaka dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a ƙasar Masar.

28 ‘Yan kaɗan ne za su tsere wa takobi, za su kuwa koma daga ƙasar Masar zuwa ƙasar Yahuza. Sauran mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, za su sani ko maganar wa za ta cika, tasu ko kuwa tawa.

29 Ni Ubangiji na ce, wannan zai zama muku alama, cewa zan hukunta ku a wannan wuri domin ku sani lalle maganata ta aukar muku da masifa za ta cika.

30 Zan kuma ba da Fir’auna Hofra, Sarkin Masar, a hannun abokan gabansa, da waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zadakiya, Sarkin Yahuza, a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila wanda ya zama abokin gābansa, ya kuwa nemi ransa.’ ”

Categories
IRM

IRM 45

Jawabin Irmiya ga Baruk

1 A shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Baruk ɗan Neriya ya rubuta abin da Irmiya ya faɗa masa.

2 “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce maka, kai Baruk,

3 kai ka ce, ‘Kaitona, gama Ubangiji ya ƙara baƙin ciki a kan wahalaina, na gaji da nishina, ba ni da hutu!’

4 “Sai ka faɗa wa Baruk cewa, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, abin da na gina zan rushe shi, abin da kuma na dasa zan tumɓuke shi, wato ƙasar ɗungum.

5 Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan ‘yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.’ ”