Categories
ZAK

ZAK 10

Alkawarin Mai Ceto

1 Ku roƙi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara,

Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri,

Shi ne yake bai wa mutane yayyafi.

Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.

2 Gama maganar shirme kan gida yake yi,

Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya,

Masu mafarkai suna faɗar ƙarya,

Ta’aziyyarsu ta banza ce.

Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki,

Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.

3 Ubangiji ya ce,

“Ina fushi ƙwarai da makiyayan,

Zan kuwa hukunta shugabannin,

Gama ni Ubangiji Mai Runduna zan lura da garkena,

Wato jama’ar Yahuza.

Zan mai da su dawakaina na yaƙi.

4 Daga cikinsu za a sami mafificin dutsen gini,

Daga cikinsu kuma za a sami turken alfarwa,

Daga cikinsu za a sami bakan yaƙi,

Daga cikinsu kuma kowane mai mulki zai fito.

5 Za su zama kamar ƙarfafan mutane cikin yaƙi,

Za su tattaka maƙiyi a cikin taɓon tituna.

Za su yi yaƙi, gama Ubangiji yana tare da su,

Za su kunyatar da sojojin doki.

6 “Zan sa jama’ar Yahuza ta yi ƙarfi,

Zan ceci jama’ar Yusufu.

Zan dawo da su domin ina jin tausayinsu.

Za su zama kamar waɗanda ban taɓa ƙyale su ba,

Gama ni Ubangiji Allahnsu ne,

Zan amsa musu.

7 Sa’an nan mutanen Ifraimu za su zama kamar ƙarfafan jarumawa,

Za su yi farin ciki kamar sun sha ruwan inabi,

‘Ya’yansu za su gani su yi murna,

Zukatansu za su yi murna da Ubangiji.

8 “Zan yafato su in tattaro su,

Gama zan fanshe su,

Zan sa su su yi yawa kamar yadda suke yi a dā.

9 Ko da yake na watsar da su cikin al’ummai,

Duk da haka za su riƙa tunawa da ni daga ƙasashe masu nisa.

Su da ‘ya’yansu za su rayu, su komo.

10 Zan dawo da su gida daga ƙasar Masar,

In tattaro su daga Assuriya,

Zan kawo su a ƙasar Gileyad da ta Lebanon,

Har su cika, ba sauran wuri.

11 Za su bi ta cikin tekun wahala,

Zan kwantar da raƙuman teku,

Kogin Nilu zai ƙafe duk da zurfinsa,

Za a ƙasƙantar da Assuriya,

Sandan sarautar Masar zai rabu da ita.

12 Zan ƙarfafa su,

Za su yi tafiya da sunansa,

Ni Ubangiji na faɗa.”

Categories
ZAK

ZAK 11

1 Ki buɗe ƙofofinki, ke Lebanon,

Don wuta ta cinye itatuwan al’ul naki.

2 Ka yi kuka, kai itacen kasharina,

Gama itacen al’ul ya riga ya fāɗi,

Itatuwa masu daraja sun lalace,

Ku yi kuka, ku itatuwan oak na Bashan,

Saboda an sassare itatuwan babban kurmi.

3 Ku ji kukan makiyaya,

Gama an ɓata musu darajarsu.

Ji rurin zakoki,

Gama an lalatar da jejin Urdun.

Makiyaya Marasa Amfani

4 Ga abin da Ubangiji Allah ya faɗa, “Ka zama makiyayin garken tumakin da za a yanka.

5 Masu sayensu za su yanyanka su, ba za a kuwa hukunta su ba. Masu sayar da su kuma za su yi hamdala gare ni, su ce sun sami dukiya. Makiyayansu kuwa ba su ji tausayinsu ba.

6 “Gama ba zan ƙara jin tausayin mazaunan ƙasan nan ba, ni Ubangiji na faɗa. Ga shi, zan sa su fāɗa a hannun junansu da a hannun sarkinsu. Za su lalatar da ƙasar, ba kuwa zan cece su daga hannunsu ba.”

7 Sai na zama makiyayi na masu tumakin kore. Na kuwa ɗauko sanda biyu, na ce da ɗaya “Alheri,” ɗaya kuma na ce da shi “Haɗa Kai.” Sai na yi kiwon tumakin.

8 A wata guda na hallaka makiyayan nan uku, gama ban jure da su ba, su ma sun gaji da ni.

9 Sai na ce wa tumakin, ba zan yi kiwonsu ba, “Waɗanda za su mutu sai su mutu, waɗanda kuma za su hallaka, to, sai su hallaka. Sauran da suka ragu kuma, su yi ta cin naman junansu!”

10 Sa’an nan na ɗauki sandana, wato “Alheri,” na karya shi, alama ke nan da ta nuna na keta alkawarin da na yi wa al’ummai duka.

11 Da haka aka karya alkawarina a wannan rana. Masu tumakin kore suna tsaye suna kallon abin da na yi, sai suka gane lalle wannan maganar Ubangiji ce.

12 Sai na ce musu, “Idan kun ga daidai ne sai ku biya ni hakkina, idan kuwa ba haka ba ne, to, ku riƙe abinku!” Sai suka biya ni tsabar azurfa talatin, ladana.

13 Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka zuba kuɗin a baitulmalin Haikali.” Sai na ɗauki kuɗin da suka kimanta shi ne tamanina, na zuba su a baitulmalin Haikalin Ubangiji.

14 Sa’an nan kuma na karya sandana na biyun mai suna “Haɗa Kai,” wato alama ke nan da ta nuna na kawar da ‘yan’uwancin da yake tsakanin Yahuza da Isra’ila.

15 Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ka sāke ɗaukar kayan aiki na makiyayi marar amfani.

16 Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.

17 Taka ta ƙare, kai makiyayi marar amfani,

Wanda yakan bar tumakin!

Da ma takobi ya sari dantsensa da idonsa na dama!

Da ma hannunsa ya shanye sarai,

Idonsa na dama kuma ya makance!”

Categories
ZAK

ZAK 12

Za a Ceci Urushalima nan Gaba

1 Ga maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji wanda ya shimfiɗa sammai, ya kirkiro duniya, ya kuma sa rai a cikin mutum, ya ce,

2 “Ga shi, ina gab da sa Urushalima ta zama ƙoƙon sa tangaɗi ga dukan al’ummai da yake kewaye. Yaƙin da zai kewaye Urushalima zai shafi Yahuza ita ma.

3 A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al’ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al’umman duniya za su taru su kewaye ta.

4 A wannan rana zan firgita kowane doki, in sa mahayinsa ya haukace. Zan lura da mutanen Yahuza, amma zan makantar da dawakan abokan gābansu.

5 Sa’an nan iyalan Yahuza za su ce wa kansu, ‘Ubangiji Allah Maɗaukaki yana ƙarfafa mutanensa waɗanda suke zaune a Urushalima.’

6 “A ranan nan zan sa iyalan Yahuza su zama kamar wuta a kurmi, ko kuwa a gonar da hatsi ya nuna. Za su halaka dukan al’umman da suke kewaye da su. Amma mutanen Urushalima za su yi zamansu lami lafiya.

7 “Ubangiji zai fara ba mutanen Yahuza nasara, domin kada darajar jama’ar Dawuda da ta mazaunan Urushalima ta fi ta mutanen Yahuza.

8 A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama’ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala’ikan Ubangiji a gabansu.

9 A ranar kuma zan hallaka dukan al’umman da suka zo su yi yaƙi da Urushalima.

10 “Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu’a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.

11 A ran nan za a yi babban makoki a Urushalima kamar mutane suka yi wa Hadadrimmon a filin Magiddo.

12 Kowane iyali a ƙasar za su yi makokinsu a keɓe, iyalin gidan Dawuda kuma za su yi nasu a keɓe, matansu za su yi nasu a keɓe. Iyalin gidan Natan su ma za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.

13 Iyalin gidan Lawi za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe. Iyalin gidan mutanen Shimai za su yi makokinsu a keɓe, matansu kuma a keɓe.

14 Sauran dukan iyalan da suka ragu za su yi nasu makoki a keɓe, matansu kuma a keɓe.”

Categories
ZAK

ZAK 13

1 “A ran nan za a buɗe maɓuɓɓuga don wanke zuriyar Dawuda da mazaunan Urushalima daga zunubi da rashin tsarki.

2 A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.

3 Idan har yanzu wani ya ci gaba da yin annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’an nan mahaifinsa da mahaifiyarsa su soke shi sa’ad da yake annabcin.

4 A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa’ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama’a ba.

5 Amma zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne, ni manomi ne, gama ƙasa abar mallakata ce tun ina yaro.’

6 Idan wani ya tambaye shi cewa, ‘Waɗannan raunukan da suke a hannuwanka fa?’ Zai ce, ‘Ai, raunuka ne da aka yi mini a gidan abokaina.’ ”

Za a Kashe Makiyayi na Ubangiji

7 “Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina,

Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni,

Ka sari makiyayin domin tumakin su watse.

Zan bugi ƙanana da hannuna,

Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

8 Ni Ubangiji na ce sulusi biyu na ƙasar za su hallaka,

Sulusi ɗaya ne kawai zai ragu.

9 Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta,

Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa,

Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya.

Za su kira gare ni,

Zan kuwa amsa musu,

Zan ce, ‘Su jama’ata ne,’

Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”

Categories
ZAK

ZAK 14

Urushalima da Sauran Al’umma

1 Ga ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba ganimar da aka ƙwace daga gare ku a kan idonku.

2 Gama zan tattara dukan al’ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.

3 Sa’an nan Ubangiji zai tafi ya yi yaƙi da waɗannan al’ummai kamar yadda ya yi a dā.

4 A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.

5 Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa!

6 A wannan rana ba haske. Masu ba da haske za su dushe.

7 Ubangiji ne ya san wannan rana. Ba rana ba dare. Da maraice ma akwai haske.

8 A wannan rana ruwa mai rai zai gudano daga Urushalima. Rabinsa zai nufi tekun Gishiri, rabi kuma zai nufi Bahar Rum. Zai riƙa malalowa rani da damuna.

9 A ranar, Ubangiji zai zama Sarkin Duniya duka, zai kuma zama shi ne Ubangiji shi kaɗai, ba wani suna kuma sai nasa.

10 Ƙasa dukka za ta zama fili, daga Geba zuwa Rimmon a kudancin Urushalima. Amma Urushalima za ta kasance a kan tudu, za ta miƙe daga Ƙofar Biliyaminu, zuwa wurin da ƙofa ta fari take a dā, har zuwa Ƙofar Kusurwa, sa’an nan ta miƙe daga Hasumiyar Hananel zuwa wuraren matsewar ruwan inabin sarki.

11 Za a zauna cikin Urushalima lami lafiya, ba sauran la’ana.

12 Ga annobar da Ubangiji zai bugi dukan al’ummai da ita, wato su da suka tafi su yi yaƙi da Urushalima. Naman jikunansu zai ruɓe lokacin da suke a tsaye. Idanunsu kuma za su ruɓe cikin kwarminsu. Harsunansu za su ruɓe a bakunansu.

13 A wannan rana babbar gigicewa daga wurin Ubangiji za ta faɗo musu, har kowa zai kama hannun ɗan’uwansa, ya kai masa dūka.

14 Mutanen Yahuza za su yi yaƙi don su kāre Urushalima. Za a kuma tattara dukan dukiyar al’umman da suke kewaye, su zinariya, da azurfa, da riguna tuli.

15 Annoba irin wannan kuma za ta faɗo wa dawakai da alfadarai, da raƙuma, da jakuna, da dukan dabbobin da suke cikin sansaninsu.

16 Sa’an nan wanda ya ragu daga cikin dukan al’umman da suka kai wa Urushalima yaƙi zai riƙa haurawa zuwa Urushalima kowace shekara, domin yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarkin sujada a lokacin kiyaye Idin Bukkoki.

17 Idan kuwa wata al’umma a duniya ba ta haura zuwa Urushalima domin ta yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarki sujada ba, ba za a yi mata ruwan sama ba.

18 Idan al’ummar Masar ba ta halarci Idin Bukkoki ba, ba za a yi mata ruwan sama ba. Ubangiji kuma zai kawo mata irin annobar da ya kawo wa al’umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

19 Wannan shi ne hukuncin da za a yi wa Masar da dukan al’umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

20 A wannan rana za a zāna waɗannan kalmomi, wato “Mai Tsarki ga Ubangiji” a kan ƙararrawar dawakai. Tukwanen da suke Haikalin Ubangiji za su zama kamar kwanonin da suke a gaban bagade.

21 Kowace tukunya da take a Urushalima da Yahuza za ta zama tsattsarka ga Ubangiji Mai Runduna domin dukan masu miƙa hadaya su ɗauka su dafa naman hadaya a cikinsu. A wannan rana ba za a ƙara samun mai ciniki a Haikalin Ubangiji Mai Runduna ba.

Categories
MAL

MAL 1

Ubangiji Yana Ƙaunar Yakubu

1 Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya ba Malakai ya faɗa wa jama’ar Isra’ila.

2 Ubangiji ya ce, “Ina ƙaunarku.”

Amma ku kuka amsa kuka ce, “Ta yaya kake ƙaunarmu?”

Ubangiji ya amsa, ya ce, “Ashe, Isuwa da Yakubu ba ‘yan’uwan juna ba ne? Amma zuriyar Yakubu nake ƙauna.

3 Na ƙi Isuwa da zuriyarsa, na hallaka ƙasarsa ta kan tudu, wurin zamansa kuwa na ba namomin jeji.”

4 Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.”

Sa’an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, ‘Ƙasar mugaye, da al’ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.’ ”

5 “Da idanunku za ku ga wannan, za ku kuwa ce, Allah mai girma ne yake a ƙasar da ba ta Isra’ila ba ce!”

Ubangiji Ya Tsauta wa Firistoci

6 Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’

7 Yadda kuka yi ke nan. Kun miƙa haramtacciyar hadaya ta abinci a kan bagadena, sa’an nan kuna cewa, ‘Ta ƙaƙa muka raina ka?’ To, zan faɗa muku, don kun ƙazantar da bagadena.

8 Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, kuna tsammani wannan daidai ne? Ko kuwa sa’ad da kuka kawo gurguwar dabba ko marar lafiya wannan daidai ne? Ku ba mai mulkinku irin wannan ku gani. Zai yi murna? Ko za ku sami tagomashi, a wurinsa? Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

9 To, firistoci ku gwada, ku roƙi Allah domin ya yi mana alheri. Ai, ba zai amsa addu’arku ba, wannan kuwa laifinku ne. Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.

10 “Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

11 “Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko’ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

12 “Amma ku kun raina ni da yake kuka ce bagadena ba kome ba ne, kuna raina abincin da kuke ajiyewa a kai.

13 Kuka kuma ce, ‘Mun gaji da wannan irin abu fa!’ Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku?

14 La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyun dabbobi da ya alkawarta zai ba ni daga cikin garkensa ya kuwa miƙa mini hadaya ta haramtacciyar dabba. Gama ni babban Sarki ne, dukan al’ummai kuwa suna jin tsoron sunana, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

Categories
MAL

MAL 2

1 “Yanzu firistoci, ga umarni dominku.

2 Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la’ana, zan la’antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la’antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

3 Ga shi, zan tsauta wa ‘ya ‘yanku, in watsa kāshin dabbobin hadayunku a fuskokinku, sa’an nan zan kore ku daga gabana.

4 Ta haka za ku sani ni na ba ku wannan umarni domin alkawarin da na yi wa Lawi ya tabbata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

5 “Alkawarin da na yi masa na rai ne da salama. Na yi masa alkawaran kuma domin ya ji tsorona, yana kuwa tsorona. Yana kuma tsoron sunana ƙwarai.

6 Koyarwar gaskiya tana cikin bakinsa, ba a sami kuskure a bakinsa ba. Ya yi tafiya tare da ni da salama da gaskiya. Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta.

7 Gama ya kamata bakin firist ya kiyaye ilimi, wajibi ne firistoci su koyar da ilimin gaskiya na Allah, a gare su mutane za su tafi su koyi nufina, domin su manzannina ne, ni Ubangiji Mai Runduna.

8 “Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

9 Saboda haka, ni ma zan sa jama’ar Isra’ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa’ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”

Rashin Amincin Isra’ilawa

10 Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu?

11 Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra’ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka.

12 Ubangiji zai lalatar da dukan wanda ya aikata wannan, wato wanda ya farka da wanda ya amsa, ko wanda yake kawo hadayu ga Ubangiji Mai Runduna.

13 Ga kuma abin da kuke yi. Kuna cika bagaden Ubangiji da hawaye, da kuka, da kururuwa domin ba zai ƙara karɓar hadayun da kuke kawo masa ba.

14 Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka.

15 Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so ‘ya’yanmu su zama ‘yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.

16 “Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, na ce ina ƙin kisan aure, ina ƙinsa sa’ad da waninku ya yi wa matarsa haka nan. Domin haka sai ku kula da kanku kada ku keta alkawari, mutum ya zama mai aminci ga matarsa.”

Ranar Hukunci Ta Gabato

17 Kun gajiyar da Ubangiji Mai Runduna da maganganunku, amma kun ce, “Ƙaƙa muka gajiyar da shi?” Kuna cewa, “Ubangiji yana ganinsu, dukan masu aikata mugunta mutanen kirki ne, yana kuwa ƙaunarsu.” Kuna kuma cewa, “Ina Allah yake wanda yake shi adali ne?”

Categories
MAL

MAL 3

1 A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa’an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”

2 Amma wa zai iya jurewa da ranar zuwansa? Wa kuma zai tsira sa’ad da ya bayyana? Zai zama kamar wutar da suke bauta ƙarfe, kamar kuma sabulu salo.

3 Zai zo ya yi hukunci kamar wanda yake tace azurfa, ya tsarkake ta. Zai tsarkake firistoci, ya tace su kamar yadda ake yi wa azurfa da zinariya. A sa’an nan ne za su kawo wa Ubangiji hadayun da suka dace.

4 Sa’an nan kuma Ubangiji zai yarda da hadayun mutanen Yahuza da na Urushalima kamar yadda yake a zamanin dā.

5 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari’a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”

Ba da Zaka

6 “Ni ne Ubangiji, ba na sākewa, domin haka ku zuriyar Yakubu, ba ku ƙāre ɗungum ba.

7 Ku kamar kakanninku kuke, kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba. Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku,” in ji Ubangiji Mai Runduna. “Amma kun ce, ‘Ƙaƙa za mu yi, mu koma gare ka?’

8 Mutum zai iya zambatar Allah? Amma ku kuna zambatata, kuna kuwa cewa, ‘Ta ƙaƙa muka zambace ka?’ A wajen al’amarin zaka da hadayu, kuke zambatata.

9 Dukanku la’antattu ne gama al’ummar duka zamba take yi mini!

10 Ku kawo dukkan zaka a ɗakin ajiyata domin abinci ya samu a cikin Haikalina. Ku gwada ni, za ku gani, zan buɗe taskokin sama in zubo muku da albarka mai yawan gaske.

11 Ba zan bar ƙwari su lalatar da amfanin gonaki ba. Kurangar inabinku za ta cika da ‘ya’ya, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

12 Sa’an nan jama’ar dukan al’ummai za su ce ku masu farin ciki ne, gama ƙasarku za ta yi daɗin zama.”

Bambancin Adalai da Mugaye

13 “Kun faɗi mugun abu a kaina,” in ji Ubangiji, “Amma kun ce, ‘Me muka ce a kanka?’

14 Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna.

15 A ganinmu masu girmankai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suke yi ba, amma sukan jarraba Allah da mugayen ayyukansu su kuwa zauna lafiya.’ ”

16 Sa’an nan mutane waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi.

17 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, za su zama mutanena na ainihi, a ranar da na aikata. Zan ji ƙansu kamar yadda mahaifi yakan ji ƙan ɗansa wanda suke masa hidima.

18 Sa’an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”

Categories
MAL

MAL 4

Ranar Ubangiji Mai Zuwa

1 “Duba rana tana zuwa, sa’ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

2 Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar ‘yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.

3 Za ku tattake mugaye, gama za su zama kamar ƙura a ƙarƙashin ƙafafunku, a ranan nan da zan aikata, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

4 “Ku tuna da koyarwar bawana Musa, da dokoki, da umarnai waɗanda na ba shi a kan Dutsen Horeb, domin dukan jama’ar Isra’ila su kiyaye.

5 “Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.

6 Zai sāke kawo iyaye da ‘ya’ya wuri ɗaya, da ba don haka ba, da sai in zo in hallaka ƙasar.”

Categories
MAT

MAT 1

Asalin Yesu Almasihu

1 Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.

2 Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu ya haifi Yahuza da ‘yan’uwansa,

3 Yahuza kuwa ya haifi Feresa da Zera (uwa tasu Tamar ce), Feresa ya haifi Hesruna, Hesruna ya haifi Aram,

4 Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,

5 Salmon ya haifi Bo’aza (uwa tasa Rahab ce), Bo’aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,

6 Yesse ya haifi sarki Dawuda.

Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda uwa tasa dā matar Uriya ce),

7 Sulemanu ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,

8 Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Azariya,

9 Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,

10 Hezekiya ya haifi Manassa, Manassa ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya.

11 Yosiya ya haifi Yekoniya da ‘yan’uwansa, wato, a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila.

12 Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel,

13 Zarubabel ya haifi Abihudu, Abihudu ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azuro,

14 Azuro ya haifi Saduƙu, Saduƙu ya haifi Akimu, Akimu ya haifi Aliyudu,

15 Aliyudu ya haifi Ele’azara, Ele’azara ya haifi Matana, Matana ya haifi Yakubu,

16 Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu.

17 Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.

Haihuwar Yesu Almasihu

18 Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa’ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki.

19 Yusufu mijinta kuwa da yake shi mutumin kirki ne, ba ya kuma so ya ba ta kunya a gaban jama’a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce.

20 Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.

21 Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

22 An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,

23 “Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa,

Za a kuma sa masa suna Immanuwel.”

(Ma’anar Immanuwel kuwa itace Allah na tare da mu.)

24 Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki matarsa,

25 amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.