Categories
LUK

LUK 8

Waɗansu Mata sun Tafi tare da Yesu

1 Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa’azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,

2 da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. Cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai,

3 da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.

Misali na Mai Shuka

4 Da jama’a masu yawa suka taru, mutane suna ta zuwa gare shi gari da gari, sai ya yi musu misali ya ce.

5 “Wani mai shuka ya tafi shuka. Yana cikin yafa iri sai waɗansu suka fāɗi a hanya, aka tattake su, tsuntsaye suka tsince su.

6 Waɗansu kuma suka fāɗi a dutse. Da suka tsiro sai suka bushe, don ba danshi.

7 Waɗansu kuma suka fāɗi cikin ƙaya, suka tashi tare, har ƙayar ta sarƙe su.

8 Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Manufar Misalin

9 Almajiransa suka tambaye shi ma’anar misalin.

10 Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.

Yesu Ya Ba da Bayanin Misalin Mai Shuka

11 “To, misalin shi ne, irin Maganar Allah ne.

12 Waɗanda suka fāɗi a hanya su ne kwatancin waɗanda suka ji Maganar Allah, sa’an nan Iblis ya zo ya ɗauke Maganar daga zuciyarsu, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.

13 Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya ‘yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.

14 Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.

15 Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.

Fitila a Rufe da Masaki

16 “Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki, ko ya ajiye ta a ƙarƙashin gado. A’a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.

17 Ba abin da yake a ɓoye da ba za a bayyana ba. Ba kuma asirin da ba zai tonu ya zama bayyananne ba.

18 Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”

Uwar Yesu da ‘Yan’uwansa

19 Uwa tasa da ‘yan’uwansa suka zo wurinsa, amma suka kasa isa gunsa saboda taro.

20 Sai aka ce masa, “Tsohuwarka da ‘yan’uwanka suna tsaye a waje, suna son ganinka.”

21 Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma ‘yan’uwana.”

Yesu Ya Tsawata wa Hadiri

22 Wata rana ya shiga jirgi tare da almajiransa. Ya ce musu, “Mu haye wancan hayin teku.” Sai suka tashi.

23 Suna cikin tafiya sai barci ya kwashe shi. Hadiri mai iska ya taso a tekun, jirginsu ya tasar wa cika da ruwa, har suna cikin hatsari.

24 Suka je suka tashe shi, suka ce, “Maigida, Maigida, mun hallaka!” Ya farka, ya tsawata wa iskar da kuma haukan ruwa. Sai suka kwanta, wurin ya yi tsit.

25 Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”

Warkar da Mai Aljan na Garasinawa

26 Sai suka iso ƙasar Garasinawa wadda take hannun riga da ƙasar Galili.

27 Da saukarsa a gaci sai wani mai aljannu ya fito daga cikin gari ya tarye shi. Ya daɗe bai sa tufa ba, ba ya zama a gida kuwa, sai a makabarta.

28 Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”

29 Ya faɗi haka ne domin Yesu ya umarci baƙin aljanin ya rabu da mutumin. Gama sau da yawa aljanin yakan buge shi, akan kuma tsare shi, a ɗaure shi da sarƙa da mari, amma ya tsintsinka ɗaurin, aljanin ya kora shi jeji.

30 Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa.

31 Sai suka yi ta roƙansa kada ya umarce su su fāɗa a mahalaka.

32 To, wurin nan kuwa akwai wani babban garkin alade na kiwo a gangaren dutse, suka roƙe shi ya yardar musu su shiga cikinsu. Ya kuwa yardar musu.

33 Sai aljannun suka rabu da mutumin, suka shiga aladun. Garken kuwa suka rungungunta ta gangaren, suka faɗa tekun, suka halaka a ruwa.

34 Da ‘yan kiwon aladen nan suka ga abin da ya faru, suka gudu, suka ba da labari a birni da ƙauye.

35 Sai jama’a suka firfito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suka tarar da mutumin da aljannun suka rabu da shi, zaune gaban Yesu, saye da tufa, yana cikin hankalinsa. Sai suka tsorata.

36 Waɗanda aka yi abin a idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkar da mai aljannun nan.

37 Dukan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya kama su. Sai ya shiga jirgi ya koma.

38 Mutumin da aljannun suka rabu da shi kuwa, ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma ya sallame shi ya ce,

39 “Koma gida, ka faɗi irin manyan abubuwan da Allah ya yi maka.” Sai ya tafi ko’ina a cikin birnin yana sanar da manyan abubuwan da Yesu ya yi masa.

Warkar da ‘Yar Yayirus da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu

40 To, da Yesu ya komo, taron suka yi masa maraba domin ko a dā ma duk suna jiransa ne.

41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, wani shugaban majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya roƙe shi ya je gidansa.

42 Yana da ‘ya ɗaya tilo, mai shekara misalin goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa.

Yana tafiya, taro masu yawa na matsa tasa,

43 sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda ya iya warkar da ita.

44 Ta raɓo ta bayansa, ta taɓa gezar mayafinsa. Nan take zubar jininta ta tsaya.

45 Sai Yesu ya ce, “Wa ya taɓa ni?” Da kowa ya yi mūsū, Bitrus da waɗanda suke tare da shi suka ce, “Maigida, ai, taro masu yawa ne suke tutturarka, suna matsarka.”

46 Amma Yesu ya ce, “An dai taɓa ni, domin na ji iko ya fita daga gare ni.”

47 Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama’a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take.

48 Sai ya ce mata, “’Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

49 Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami’ar, ya ce, “Ai, ‘yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.”

50 Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami’ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.”

51 Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da kuma uban yarinyar da uwa tata,

52 Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.”

53 Sai suka yi masa dariyar raini, don sun sani ta mutu.

54 Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”

55 Ruhunta kuwa ya dawo, nan take ta tashi. Sai ya yi umarni a ba ta abinci.

56 Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.

Categories
LUK

LUK 9

Yesu ya Aiki Goma Sha Biyu ɗin Nan

1 Sai ya tara goma sha biyun nan ya ba su iko da izini kan dukan aljannu, su kuma warkar da cuce-cuce,

2 ya kuma aike su su yi wa’azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.

3 Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu.

4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.

5 Duk waɗanda ba su yi na’am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”

6 Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko’ina.

Mutuwar Yahaya Maibaftisma

7 To, sarki Hirudus ya ji duk abin da ake yi, ya kuwa damu ƙwarai, don waɗansu suna cewa Yahaya ne aka tasa daga matattu.

8 Waɗansu kuwa suka ce wai Iliya ne ya bayyana. Waɗansu kuma suka ce ɗaya daga annabawan dā ne ya tashi.

9 Sai Hirudus ya ce, “Yahaya kam na fille masa kai. Wa ke nan kuma da nake jin irin waɗannan abubuwa game da shi?” Sai ya nemi ganinsa.

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

10 Da manzanni suka dawo, suka gaya wa Yesu abin da suka yi. Sai ya tafi da su a keɓe zuwa wani gari wai shi Betsaida.

11 Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa.

12 Da rana ta fara sunkuyawa, sha biyun suka matso, suka ce masa, “Sai ka sallami taron, su shiga ƙauyuka da karkara na kurkusa, su sauka, su nemi abinci, don inda muke ba mutane.”

13 Amma ya ce musu, “Ku ku ba su abinci mana.” Suka ce, “Ai, abin da muke da shi bai fi gurasa biyar da kifi biyu ba, sai dai in za mu je mu sayo wa dukkan jama’an nan abinci ne.”

14 Maza sun yi wajen dubu biyar. Sai ya ce wa almajiransa, “Ku ce musu su zazzauna ƙungiya ƙungiya, kowace ƙungiya misali hamsin hamsin.”

15 Haka kuwa suka yi, suka sa dukkansu su zazzauna.

16 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama’a.

17 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har aka kwashe ragowar gutsattsarin, kwando goma sha biyu.

Hurcin Bitrus a kan Yesu

18 Wata rana yana addu’a shi kaɗai, almajiransa kuwa suka zo wurinsa. Sai ya tambaye su, ya ce, “Wa mutane suke cewa nake?”

19 Suka amsa suka ce, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, ɗaya daga cikin annabawan dā ne ya tashi.”

20 Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Almasihu na Allah.”

Yesu Ya Faɗi irin Mutuwar da zai Yi

21 Sai ya kwaɓe su gaya matuƙa kada su gaya wa kowa wannan magana.

22 Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”

23 Sai ya ce wa dukansu, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, yă bi ni.

24 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, tattalinsa ya yi.

25 Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a kan hasarar ransa, ko a bakin ransa?

26 Duk wanda sai ya ji kunyar shaida ni da maganata, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi sa’ad da ya zo da ɗaukaka tasa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala’iku tsarkaka.

27 Amma hakika ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Mulkin Allah.”

Sākewar Kamanninsa

28 Bayan misalin kwana takwas da yin maganan nan, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, ya hau wani dutse domin yin addu’a.

29 Yana yin addu’a, sai kama tasa ta sāke, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido.

30 Sai ga mutum biyu na magana da shi, wato Musa da Iliya.

31 Sun bayyana da ɗaukaka, suna zancen ƙaura tasa ne, wadda yake gabannin yi a Urushalima.

32 Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi.

33 Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Maigida, ya kyautu da muke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba.

34 Yana faɗar haka sai wani gajimare ya zo ya rufe su. Da kuma gajimaren ya lulluɓe su suka tsorata.

35 Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana zaɓanɓɓena. Ku saurare shi!”

36 Bayan muryar ta yi magana, aka ga Yesu shi kaɗai. Suka yi shiru. A kwanakin nan kuwa ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.

Yesu Ya Warkar da Yaro Mai Farfadiya

37 Kashegari da suka gangaro daga kan dutsen, wani babban taro ya tarye shi.

38 Sai ga wani daga cikin taron ya yi kira, ya ce, “Malam, ina roƙonka ka dubi ɗana da idon rahama, shi ne ke nan gare ni.

39 Ga shi, aljani yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai.

40 Na kuwa roƙi almajiranka su fitar da shi, amma sun kasa.”

41 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗa naka nan.”

42 Yana zuwa, sai aljanin ya buge shi ƙwarai, jikinsa na rawa. Amma Yesu ya tsawata wa baƙin aljanin, ya warkar da yaron, ya kuma mayar wa ubansa da shi.

43 Duk aka yi mamakin girman ikon Allah.

Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi

Tun dukansu suna mamakin duk abubuwan da yake yi, sai ya ce wa almajiransa,

44 “Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.”

45 Amma ba su fahimci maganan nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane. Su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana.

Wane ne Mafi Girma?

46 Sai musu ya tashi a tsakaninsu a kan ko wane ne babbansu.

47 Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi.

48 Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”

Wanda ba ya Gāba da ku, Naku Ne

49 Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Maigida, mun ga wani yana fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.”

50 Amma Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

Samariyawan wani Ƙauye sun Ƙi Karɓar Yesu

51 Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.

52 Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa.

53 Amma Samariyawa suka ƙi karɓarsa, domin niyyarsa duk a kan Urushalima take.

54 Da almajiransa Yakubu da Yahaya suka ga haka suka ce, “Ya Ubangiji, ko kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama ta lashe su?”

55 Amma ya juya, ya tsawata musu.

56 Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.

Masu Cewa za su Bi Yesu

57 Suna tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka.”

58 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

59 Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”

60 Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne ‘yan’uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”

61 Wani kuma ya ce, “Ya Ubangiji, zan bi ka, amma ka bar ni tukuna in yi wa mutanen gida bankwana.”

62 Yesu ya ce masa “Wanda ya fara huɗa da keken noma, yana duban baya, bai dace da Mulkin Allah ba.”

Categories
LUK

LUK 10

Yesu Ya Aiki Saba’in Ɗin

1 Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba’in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.

2 Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi.

3 To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar ‘yan tumaki a tsakiyar kyarketai.

4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya.

5 Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikun mutanen gidan nan!’

6 In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku.

7 Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma’aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa sāke masauki.

8 Duk garin da kuka shiga, in an yi na’am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku.

9 Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’

10 Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na’am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa,

11 ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’

12 Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”

Tsawata wa Garuruwan da ba su Tuba Ba

13 “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu’ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka.

14 Amma a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.

15 Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A’a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.

16 “Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”

Komowar Saba’in Ɗin

17 Sai kuma saba’in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!”

18 Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.

19 Ga shi, na ba ku ikon taka macizai da kunamai, ku kuma rinjaye a kan dukan ikon Maƙiyi, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan.

20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”

Yesu Ya Yi Farin Ciki

21 A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.

22 Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”

23 Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a keɓance, “Albarka tā tabbata ga idanun da suka ga abin da kuka gani.

24 Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa suna son ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, suna kuma so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

Basamariyen da Ya Nuna Jinƙai

25 Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?”

26 Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?”

27 Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.”

28 Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, za ka rayu.”

29 Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan’uwa nawa?”

30 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai ‘yan fashi suka fāɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun dūka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah.

31 Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

32 Haka kuma wani Balawe, da ya iso wurin ya gan shi, shi ma ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa.

33 Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi,

34 ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa’an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauki, ya yi ta jiyyarsa.

35 Kashegari ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, ‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai in biya ka.’

36 To, a cikin ukun nan, wa kake tsammani ya zama ɗan’uwa ga wanda ‘yan fashin suka faɗa wa?”

37 Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”

Yesu Ya Ziyarci Marta da Maryamu

38 Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke da shi a gidanta.

39 Tana kuwa da ‘yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron magana tasa.

40 Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, ‘yar’uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.”

41 Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa.

42 Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”

Categories
LUK

LUK 11

Koyarwar Yesu a kan Addu’a

1 Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Bayan da ya gama, sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka koya mana addu’a, kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”

2 Sai ya ce musu, “In kuna addu’a ku ce,

‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki,

Mulkinka yă zo,

3 Ka ba mu abincin yau da na kullum.

4 Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi.

Kada ka kai mu wurin jaraba.’ ”

5 Ya kuma gaya musu, “Misali, idan waninku yana da amini, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ‘Wāne, ranta mini gurasa uku mana,

6 ga shi, wani abokina matafiyi ya sauka a wurina yanzu, ba ni kuwa da abincin da zan ba shi,’

7 sa’an nan aminin ya amsa masa daga ciki ya ce, ‘Kada ka dame ni, ai, an kulle ƙofa, da ni da ‘ya’yana duk mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka wani abu ba.’

8 Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata.

9 Ina dai gaya muku, ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

10 Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.

11 Wane uba ne a cikinku, da ɗansa zai roƙe shi [gurasa, ya ba shi dutse? Ko ya roƙe shi] kifi, ya ba shi maciji?

12 Ko kuwa ya roƙe shi ƙwai, ya ba shi kunama?

13 To, ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba ‘ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu roƙonsa.”

Yesu da Ba’alzabul

14 Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.

15 Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba’alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”

16 Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama.

17 Shi kuwa da ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Haka kuma, in gida ya rabu a kan gāba, zai baje.

18 In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba’alzabul nake fitar da aljannu.

19 In kuwa da ikon Ba’alzabul nake fitar da aljannu, to, ‘ya’yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.

20 Ni kuwa in da ikon Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.

21 In ƙaƙƙarfan mutum ya yi ɗamara sosai, yana tsaron gidansa, kayan gidansa lafiya suke.

22 In kuwa wanda ya fi shi ƙarfi ya fāɗa masa, ya kuma rinjaye shi, sai ya ƙwace duk makaman da ya dogara da su, ya kuma rarraba kayansa ganima,

23 Wanda ba nawa ba ne, gāba yake yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.”

Komawar Baƙin Aljan

24 “Baƙin aljan, in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa, yana neman hutawa. In ya rasa, sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’

25 Sa’ad da kuwa ya komo gidan ya tarar da shi shararre, ƙawatacce,

26 Daga nan sai ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum kuwa ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa.”

Tabbatacciyar Albarka

27 Yana faɗar haka, sai wata mace a taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Albarka tā tabbata ga wadda ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”

28 Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”

‘Yan Zamani Mugaye suna Neman Alama

29 Da taro ya riƙa ƙaruwa a wurinsa, sai ya fara cewa, “Wannan zamani mugun zamani ne. Suna neman ganin wata alama, amma ba wata alamar da za a nuna musu sai dai ta Yunusa.

30 Wato, kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Nineba, haka kuma, Ɗan Mutum zai zamar wa zamanin nan.

31 A Ranar Shari’a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta kā da su. Don ta zo ne daga bangon duniya tă ga hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.

32 A Ranar Shari’a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan su kā da su. Don sun tuba saboda wa’azin Yunusa. To, ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.”

Fitilar Jiki

33 “Ba mai kunna fitila ya ɓoye ta a rami, ko ya rufe ta da masaki. A’a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.

34 Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka zai cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu.

35 Saboda haka, sai ka lura ko hasken da yake a gare ka duhu ne.

36 In kuwa duk jikinka ya cika da haske, ba inda ke da duhu, ai, duk sai ya haskaka gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila take haskaka maka.”

Yesu Ya Fallashi Farisiyawa da Masanan Attaura

37 Yesu yana magana, sai wani Bafarisiye ya kira shi cin abinci. Ya shiga cin abincin.

38 Sai Bafarisiyen ya yi mamakin ganin yadda Yesu zai ci abinci ba da fara wanke hannu ba.

39 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ku Farisiyawa kam, kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike kuke da zalunci da mugunta.

40 Ku marasa azanci! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ya yi cikin ba?

41 Gara ku tsarkake cikin, sa’an nan kome zai tsarkaka a gare ku.

42 “Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na’ana’a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba.

43 Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna son mafifitan mazaunai a majami’u, da kuma gaisuwa a kasuwa.

44 Kaitonku! Kuna kama da kaburburan da ba a gani, waɗanda mutane suke takawa da rashin sani.”

45 Sai wani a cikin masanan Attaura ya amsa masa ya ce, “Malam, faɗar haka fa, mu ma, ai, ka ci mutuncinmu.”

46 Sai Yesu ya ce, “Ku kuma kaitonku, masanan Attaura! Don kuna jibga wa mutane kaya masu wuyar ɗauka, ku da kanku ko ɗan yatsa ba kwa sawa ku tallafa musu!

47 Kaitonku! Don kuna gina gubbobin annabawan da kakanninku suka kashe.

48 Wato, ku shaidu ne a kan kun yarda da ayyukan kakanninku, ga shi, su ne fa suka kashe su, ku kuwa wai har kuka gina musu gubbobin!

49 Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’

50 don alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani,

51 wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani.

52 Kaitonku, masanan Attaura! Don kun ɗauke mabuɗin ilimi, ku kanku ba ku shiga ba, kun kuma hana masu son shiga su shiga.”

53 Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa,

54 suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.

Categories
LUK

LUK 12

Faɗaka a kan Makirci

1 Sa’an nan kuwa da dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, da farko ya yi magana da almajiransa. Ya fara cewa, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, makirci.

2 Ba abin da yake rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.

3 Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a loloki, za a yi shelarsa daga kan soraye

Wanda za a Ji Tsoro

4 “Ya ku masoyana, ina dai gaya muku, kada ku ji tsoron masu kisan mutum, bayan sun kashe kuwa, ba abin da za su iya yi.

5 Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro!

6 Ashe, ba gwara biyar ne kobo biyu ba? Ko ɗayarsu kuwa Allah bai manta da ita ba.

7 Kai! ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”

Bayyana Yarda da Almasihu a gaban Mutane

8 “Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai bayyana yarda a gare shi a gaban mala’ikun Allah.

9 Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala’ikun Allah.

10 Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.

11 Sa’ad da suka kai ku gaban majami’u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,

12 domin Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya kamata ku faɗa a lokacin.”

Misali na Mai Arziki Marar Azanci

13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, kă ce wa ɗan’uwana ya raba gādo da ni.”

14 Amma Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zama muku alƙali, ko in raba muku gādo?”

15 Ya kuma ce musu, “Ku kula fa, ku yi nesa da kowane irin kwaɗayi, don yawan kaya ba shi ne rai ba.”

16 Sai ya ba su misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta yi albarka ƙwarai.

17 Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’

18 Ya kuma ce, ‘To, ga abin da zan yi. Sai in rushe rumbunana, in gina waɗansu manya, in zuba duk amfanin gonata da kayana a ciki.

19 Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’

20 Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’

21 Haka, wanda ya tanada wa kansa dukiya yake, ba shi kuwa da wani tanadi a gun Allah.”

Damuwa da Alhini

22 Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura.

23 Domin rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.

24 Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!”

25 Wane ne a cikinku don damuwarsa zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?

26 To, in ba za ku iya yin ƙaramin abu irin wannan ba, don me kuke damuwa da sauran?

27 Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba.

28 To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!

29 Ku ma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini.

30 Ai, al’umman duniya suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu.

31 Ku ƙwallafa rai ga al’amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwa kuma.

Tara Dukiya a Sama

32 “Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.

33 Ku sayar da mallakarku, ku bayar taimako. Ku samar wa kanku jakar kuɗi da ba ta tsufa, wato, dukiya marar yankewa ke nan a Sama, inda ba ɓarawon da zai gabato, ba kuma asun da zai ɓāta,

34 don kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Bayin da suke a Faɗake

35 “Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne.

36 Ku dai zama kamar mutane masu jiran ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya ƙwanƙwasa su buɗe masa.

37 Albarka tā tabbata ga bayin nan waɗanda ubangijinsu da zuwansa zai same su a faɗake. Hakika, ina gaya muku, zai yi ɗamara, ya ce su zauna cin abinci, sa’an nan ya bi ta kan kowannensu yana yi masa hidima.

38 In kuwa ya zo da tsakar dare ne, ko kuwa bayan tsakar dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne.

39 Amma dai ku sani, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida.

40 Ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba Ɗan Mutum zai zo.”

Amintaccen Bawa ko Marar Aminci

41 Sai Bitrus ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa na kowa da kowa ne?”

42 Ubangiji ya ce, “Wane ne amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangidansa zai ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?

43 Albarka tā tabbata ga bawan da, in ubangidansa ya dawo, zai samu yana yin haka.

44 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallaka tasa.

45 In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa’an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa,

46 ai, ubangijin wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a lokacin kuma da bai sani ba, yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da marasa riƙon amana.

47 Bawan nan kuma wanda ya san nufin ubangijinsa, bai yi shiri ba, bai kuma bi nufinsa ba, za a yi masa matsanancin dūka,

48 Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”

Yesu Ya Kawo Rabuwa

49 “Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru!

50 Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita!

51 Kuna tsammani na zo ne in kawo salama a duniya? A’a, ina gaya muku, sai dai rabuwa.

52 Nan gaba, a gida guda mutum biyar za su kasu biyu, uku na gāba da biyu, biyu kuma na gāba da uku.

53 Ta haka, za su rabu. Uba yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da ubansa, uwa tana gāba da ‘ya tata, ‘yar kuma tana gāba da uwa tata, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da suruka tata.”

Gane Yanayin Lokatai

54 Ya kuma ce wa taron, “In kun ga girgije yana tasowa daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwa.’ Sai kuwa a yi.

55 In kuwa kun ga iskar kudu tana busowa, kukan ce, ‘Za a yi matsanancin zafi.’ Sai kuwa a yi.

56 Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamun zamanin ba?”

Yi Jiyayya da Mai Ƙararka

57 “Me ya sa ku da kanku ma ba kwa iya rarrabewa da abin da yake daidai?

58 Misali, in kuna tafiya zuwa gaban shari’a da mai ƙararku, sai ku yi ƙoƙari ku yi jiyayya da shi tun a hanya, don kada ya ja ku zuwa gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa wa ɗan doka, ɗan doka kuma ya jefa ku a kurkuku.

59 Ina gaya muku, lalle ba za ku fita ba, sai kun biya duka, ba sauran ko anini.”

Categories
LUK

LUK 13

Tuba ko Halaka

1 Nan take waɗansu da suke a wurin suka ba shi labarin Galilawan da Bilatus ya sa aka kashe, har jininsu ya gauraya da na yankan da suka yi na hadaya.

2 Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawa zunubi ne, don sun sha wannan azaba?

3 Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku halaka kamarsu.

4 Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?

5 Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku hallaka kamarsu.”

Misali na Ɓaure Marar ‘Ya’ya

6 Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman ‘ya’ya, amma bai samu ba.

7 Sai ya ce wa mai kula da garkar, ‘Ka ga, yau shekara uku ke nan nake zuwa neman ‘ya’yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?’

8 Sai ya amsa masa ya ce, ‘Ubangijina, bar shi dai bana ma, in yi masa kaftu, in zuba masa taki.

9 In ya yi ‘ya’ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”

Warkar da Tanƙwararriyar Mace a Ran Asabar

10 Wata rana yana koyarwa a wata majami’a ran Asabar,

11 sai ga wata mace wadda inna ta shanye tun shekara goma sha takwas, duk ta tanƙware, ko kaɗan ba ta iya miƙewa.

12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!”

13 Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah.

14 Amma shugaban majami’a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama’a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.”

15 Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi banruwa ran Asabar?

16 Ashe, bai kamata matar nan ‘yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?”

17 Da ya faɗi haka, sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwan al’ajabi da yake yi.

Misali na Ƙwayar Mastad

18 Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah yake kama? Da me kuma zan kwatanta shi?

19 Kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa, ta kuma girma ta zama itace, har tsuntsaye suka yi sheƙarsu a rassanta.”

Misali na Yisti

20 Ya sāke cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Allah?

21 Kamar yisti yake wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗa da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya gama da yistin.”

Ƙunƙuntar Ƙofa

22 Sai ya ɗauki hanyarsa ta zuwa birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima.

23 Sai wani ya ce masa, “Ya Ubangiji, waɗanda za su sami ceto kam, kaɗan ne?” Sai ya ce musu,

24 “Ku yi famar shiga ta ƙunƙuntar ƙofa. Don ina gaya muku, mutane da yawa za su nemi shiga, amma ba su iya ba.

25 In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.’

26 Sa’an nan za ku fara cewa, ‘Ai, mun ci mun sha a gabanka, har ka koyar a kan titi-titinmu.’

27 Shi kuwa sai ya ce, ‘Ina dai gaya muku, ku kam, ban san daga inda kuke ba. Ku tafi daga wurina, dukanku ku masu aikata mugunta!’

28 Sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon baki.

29 Za a zo daga gabas da yamma, kudu da arewa, a zauna cin abinci a Mulkin Allah.

30 Ga shi fa, waɗansu da suke na ƙarshe za su zama na farko, waɗansu kuwa da suke na farko za su koma na ƙarshe.”

Yesu Ya Ji Juyayin Urushalima

31 Nan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.”

32 Sai ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, ‘Ka ga, yau ina fitar da aljannu, ina warkarwa, gobe ma haka, a rana ta uku kuwa zan gama aikina.

33 Duk da haka, lalle ne in ci gaba da tafiyata yau da gobe, da kuma jibi, don kuwa bai dace a kashe annabi ba, in ba a Urushalima ba.’

34 “Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gare ku! Sau nawa ne ina so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara ‘yan tsakinta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi!

35 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”

Categories
LUK

LUK 14

Warkar da Mai Ciwon Fara

1 Wata ranar Asabar, ya shiga gidan wani shugaba Farisiyawa garin cin abinci, mutane kuwa suna haƙwansa.

2 Sai ga wani mai ciwon fara a gabansa.

3 Yesu ya amsa ya ce wa masanan Attaura da Farisiyawa, “Ya halatta a warkar ran Asabar ko kuwa?”

4 Sai suka yi shiru, Yesu kuwa ya riƙe shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi.

5 Sa’an nan ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya faɗa a rijiya ran Asabar, ba zai fitar da shi nan da nan ba?”

6 Sai suka kasa ba da amsar waɗannan abubuwa.

Aya ga Waɗanda aka Gayyato Biki da Mai Gayyar

7 To, ganin yadda waɗanda aka gayyato sun zaɓi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali ya ce,

8 “In an gayyace ka zuwa biki, kada ka zauna a mazaunin alfarma, kada ya zamana an gayyato wani wanda ya fi ka daraja,

9 wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa’an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci.

10 Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce maka, ‘Aboki, hawo nan mana.’ Za ka sami girma ke nan a gaban dukan waɗanda kuke zaune tare.

11 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”

12 Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutum cin abinci ko biki, kada ka riƙa kiran abokanka kawai, ko ‘yan’uwanka, ko danginka ko maƙwabtanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka.

13 Amma in za ka kira biki, sai ka gayyayo gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi,

14 za ka kuwa sami albarka, da yake ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka ranar tashin masu adalci.”

Misali na Babban Biki

15 Da jin haka, sai ɗaya daga cikin abokan cinsa ya ce masa, “Albarka tā tabbata ga wanda zai ci abinci a Mulkin Allah.”

16 Amma ya ce masa, “Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa.

17 Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa yă ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, duk an shirya kome,’

18 Sai dukansu baki ɗaya suka fara kawo hanzari. Na farko ya ce masa, ‘Na sayi gona, lalle ne in je in gano ta. Ina roƙonka ka ɗauke mini,’

19 Sai wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma, za ni in gwada su. Ina roƙonka ka ɗauke mini.’

20 Wani kuma ya ce, ‘Na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.’

21 Bawan ya dawo ya ba ubangijinsa labari. Sai maigidan ya yi fushi, ya ce wa bawansa, ‘Fita maza, ka bi titi-titin birni da kwararo-kwararo, ka ɗebo gajiyayyu, da musakai, da makafi, da guragu.’

22 Sai bawan ya ce, ‘Ya ubangiji, abin da ka umarta duk an gama, amma har yanzu da sauran wuri.’

23 Sai ubangijin biki ya ce wa bawan, ‘Fita, ka bi gwadabe-gwadabe da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana.

24 Ina gaya muku, ba ko ɗaya daga cikin mutanen da na gayyata a dā da zai ɗanɗana bikina ba.’ ”

Wuyar Zama Almajiri

25 To, taro masu yawan gaske binsa. Sai ya juya ya ce musu,

26 “Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da ‘ya’yansa, da ‘yan’uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.

27 Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.

28 Misali, in wani daga cikinku yana son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗi da za su ƙare aikin?

29 Kada ya zamana bayan da ya sa harsashin ginin, yă kasa gamawa, har duk waɗanda suka gani, su fara yi masa ba’a,

30 su riƙa cewa, ‘A! Ka ga mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa gamawa!’

31 “Ko kuwa wane sarki ne, in za shi yaƙi da wani sarki, da fari ba ya zauna ya yi shawara, ya ga ko shi mai mutum dubu goma zai iya karawa da mai dubu ashirin ba?

32 In kuwa ba zai iya ba, to, tun wancan yana nesa, sai ya aiki jakadu, su tambayo sharuɗan amana.

33 Haka ma, kowannenku in bai saki duk abin da ya mallaka ba, ba zai iya zama almajirina ba.”

Sānannen Gishiri

34 “Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi?

35 Ba shi da wani amfani a gona, ko a taki, sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, ya ji.”

Categories
LUK

LUK 15

Misali na Ɓatacciyar Tunkiya

1 To, sai duk masu karɓar haraji da masu zunubi suka yi ta matsowa wurinsa su saurare shi.

2 Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka riƙa gunaguni suna cewa, “Haba! Wannan mutum yana karɓar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci!”

3 Sai ya ba su wannan misali ya ce.

4 “In waninku yana da tumaki ɗari, ɗayarsu ta ɓace, to, ba sai ya bar tasa’in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta ɓata, har ya same ta ba?

5 In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafaɗa, yana farin ciki.

6 In ya dawo gida, sai ya tara abokansa da maƙwabta ya ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na samo tunkiyata da ta ɓata.’

7 Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa’in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”

Misali na Ɓataccen Kuɗi

8 “Ko kuwa wace mace ce, in tana da kuɗi azurfa guda goma, in ta yar da ɗaya, ba sai ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta nacin nemansa, har ta same shi ba?

9 In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’

10 Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala’ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”

Misali na Ɓataccen Ɗa

11 Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai ‘ya’ya biyu maza.

12 Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa.

13 Bayan ‘yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha’a.

14 Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara.

15 Ya je ya rāɓu da wani ɗan ƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyayar kiwon alade.

16 Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu

17 Amma da ya tara hankalinsa sai ya ce, ‘Kaitona! Nawa ne daga cikin barorin ubana da suke da abinci, da yake kamar ƙasa a gare su! Ga ni a nan kuwa, yunwa tana kisana!

18 Zan tashi, in tafi gun ubana, in ce masa, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka.

19 Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ’

20 Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa.

21 Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’

22 Amma uban ya ce wa bayinsa, ‘Maza ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma,

23 a kuma kawo kiwataccen ɗan maraƙin nan, a yanka, mu ci, mu yi murna.

24 Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma a yanzu an same shi.’ Sai suka yi ta farin ciki.

25 “A sa’an nan kuwa, babban ɗansa yana gona. Yana dawowa, ya yi kusa da gida ke nan, sai ya ji ana kaɗe-kaɗe da raye-raye.

26 Sai ya kira wani baran gidan, ya tambayi dalilin wannan abu.

27 Shi kuwa ya ce masa, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, tsohonku ya yanka kiwataccen ɗan maraƙin nan saboda ya sadu da shi lafiya ƙalau.’

28 Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa.

29 Amma ya amsa wa ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina.

30 Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!’

31 Sai uban ya ce masa, ‘Ya ɗana, ai, kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne.

32 Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan’uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.’ ”

Categories
LUK

LUK 16

Misali na Wakili Marar Gaskiya

1 Ya kuma ce wa almajiransa, “An yi wani mai arziki da yake da wakili. Sai aka sari wakilin a wurinsa a kan yana fallasar masa da dukiya.

2 Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’

3 Sai wakilin ya ce a ransa, ‘Ƙaƙa zan yi, da yake maigida zai karɓe wakilci daga hannuna? Ga shi, ba ni da ƙarfin noma, in yi roƙo kuwa, ina jin kunya.

4 Yauwa! Na san abin da zan yi, don in an fisshe ni daga wakilcin, mutane su karɓe ni a gidajensu.’

5 Sai ya kira mabartan maigidansa da ɗaya ɗaya, ya ce wa na farko, ‘Nawa maigida yake bin ka?’

6 Ya ce, ‘Garwa ɗari ta mai.’ Sai ya ce masa, ‘Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubutu hamsin,’

7 Ya kuma ce wa wani, ‘Kai fa, nawa ake binka?’ Sai ya ce, ‘Buhu ɗari na alkama.’ Ya ce masa, ‘Ga takardarka, ka rubuta tamanin.’

8 Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don ‘yan zamani a ma’ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.

9 Ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, ko da yake aba ce wadda take iya aikata mugunta, don sa’ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.

10 “Wanda yake da aminci a ƙaramin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, marar gaskiya ne a babban abu.

11 Idan fa ba ku yi aminci da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?

12 In kuma ba ku yi aminci da kayan wani ba, wa zai ba ku halaliyarku?

13 Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”

Shari’a da Mulkin Allah

14 Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.

15 Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.

16 “Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki.

17 Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”

Koyarwar Yesu a kan Kisan Aure

18 “Kowa ya saki mata tasa ya auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya ya yi zina.”

Mai Arziki da Li’azaru

19 “An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana.

20 An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li’azaru, wanda duk jikinsa miki ne.

21 Shi kuwa yana marmarin ya ƙoshi da suɗin mai arzikin nan. Har ma karnuka sukan zo suna lasar miyakunsa.

22 Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala’iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin Ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.

23 Yana a cikin Hades yana shan azaba, sai ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li’azaru a wurinsa.

24 Sai ya yi kira ya ce, ‘Baba Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiko Li’azaru ya tsoma kan yatsarsa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.’

25 Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li’azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.

26 Banda wannan ma duka, tsakaninmu da ku akwai wani gawurtaccen rami mai zurfi, zaunanne, don waɗanda suke son ƙetarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ƙetaro zuwa wurinmu daga can.’

27 Sai mai arzikin ya ce, ‘To, ina roƙonka, Baba, ka aika shi zuwa gidan ubana,

28 don ina da ‘yan’uwa biyar maza, ya je ya yi musu gargaɗi, kada su ma su zo wurin azabar nan.’

29 Amma Ibrahim ya ce, ‘Ai, suna da littattafan Musa da na annabawa, su saurare su mana.’

30 Sai ya ce, ‘A’a, Baba Ibrahim, in dai wani daga cikin matattu ya je wurinsu sa tuba.’

31 Ibrahim ya ce masa, ‘In dai har ba su saurari littattafan Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga cikin matattu ma, ba za su rinjayu ba.’ ”

Categories
LUK

LUK 17

Sanadodin Yin Zunubi

1 Sai ya ce wa almajiransa, “Sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadinsu!

2 Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan ‘yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku.

3 Ku kula da kanku fa. In ɗan’uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi.

4 Ko ya yi maka laifi sau bakwai rana ɗaya, sa’an nan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, ‘Na tuba,’ sai ka yafe shi.”

Ƙara Mana Bangaskiya

5 Sai manzanni suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya.”

6 Ubangiji kuwa ya ce, “Da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da za ku ce wa wannan durumi, ‘Ka ciru, ka dasu cikin teku,’ sai kuwa ya bi umarninku.”

Wajibin Bawa

7 “Misali, wane ne a cikinku in yana da bawa mai yi masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, ‘Maza, zo ka zauna, ka ci abinci’?

8 Ashe, ba ce masa zai yi, ‘Shirya mini jibi, ka kuma yi ɗamara, ka yi mini hidima, har in gama ci da sha, daga baya kai kuma ka ci ka sha,’ ba?

9 Yā gode wa bawan nan don ya bi umarni?

10 Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibinmu kurum.’ ”

Yesu Ya Warkar da Kutare Goma

11 Wata rana yana tafiya Urushalima, sai ya bi iyakar ƙasar Samariya da Galili.

12 Yana shiga wani ƙauye ke nan, sai waɗansu kutare maza guda goma suka tarye shi, suna tsaye daga nesa.

13 Sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ka ji tausayinmu,”

14 Da ya gan su, ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna tafiya ke nan, sai suka tsarkaka.

15 Ɗayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi,

16 ya fāɗi a gaban Yesu, yana gode masa. Shi kuwa Basamariye ne.

17 Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran?

18 Ashe, ba wanda aka samu ya komo ya ɗaukaka Allah, sai baƙon nan kaɗai?”

19 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”

Bayyanar Mulkin Allah

20 Da Farisiyawa suka tambaye shi lokacin bayyanar Mulkin Allah, ya amsa musu ya ce, “Ai, bayyanar Mulkin Allah ba ganinta ake yi da ido ba.

21 Ba kuwa za a ce, ‘A! Ga shi nan,’ ko kuwa, ‘Ga shi can,’ ba. Ai, Mulkin Allah a tsakaninku yake.”

22 Ya kuma ce wa almajiran, “Lokaci na zuwa da za ku yi begen ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.

23 Za su ce muku, ‘A! ga shi nan,’ ko kuwa, ‘Ga shi can!’ Kada ku je, kada ku bi su.

24 Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan, haka ma, Ɗan Mutum zai zama a ranar bayyanarsa.

25 Amma lalle sai ya sha wuya iri iri tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ƙi shi.

26 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Ɗan Mutum.

27 Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka.

28 Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine,

29 amma a ranar da Lutu ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka hallaka su duka.

30 Haka kuma zai zama a ranar bayyanar Ɗan Mutum.

31 A ran nan fa wanda yake kan soro, kayansa kuma na cikin gida, kada ya sauko garin ɗaukarsu. Haka kuma wanda yake gona, kada ya juyo.

32 Ku tuna fa da matar Lutu.

33 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa, adana shi ya yi.

34 Ina gaya muku, a wannan dare za a ga mutum biyu a gado ɗaya, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

35 Za a ga mata biyu suna niƙa tare, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. [

36 Za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.]”

37 Sai suka amsa suka ce, “Ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “A inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.”