Categories
FAR

FAR 21

Haihuwar Ishaku

1 Ubangiji ya yi wa Saratu alheri kamar yadda ya alkawarta.

2 Saratu kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Ibrahim ɗa cikin tsufansa a lokacin nan da Allah ya faɗa masa.

3 Sai Ibrahim ya raɗa wa ɗansa wanda Saratu ta haifa masa, suna, Ishaku.

4 Ibrahim ya yi wa Ishaku ɗansa kaciya yana da kwana takwas, kamar yadda Allah ya umarce shi.

5 Ibrahim kuwa yana da shekara ɗari sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.

6 Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, har dukan wanda ya ji zai yi dariya tare da ni.”

7 Ta kuma ce, “Dā wa zai iya ce wa Ibrahim Saratu za ta bai wa ‘ya’ya mama? Duk da haka cikin tsufansa na haifa masa ɗa.”

8 Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.

Korar Hajaratu da Isma’ilu

9 Amma Saratu ta ga ɗan Hajaratu Bamasariya wanda ta haifa wa Ibrahim yana wasa da ɗanta Ishaku.

10 Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.”

11 Abin ya ɓata wa Ibrahim zuciya ƙwarai sabili da ɗansa.

12 Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka.

13 Zan kuma yi al’umma daga ɗan baiwar, domin shi ma zuriyarka ne.”

14 Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.

15 Sa’ad da ruwan salkar ya ƙare, sai ta yar da yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.

16 Sai ta tafi, ta zauna ɗaura da shi da ‘yar rata, misalin nisan harbin baka, gama ta ce, “Don kada in ga mutuwar yaron.” Da ta zauna can daura da shi, sai yaron ya ta da muryarsa ya yi ta kuka.

17 Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala’ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me yake damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake.

18 Tashi, ki ɗauki yaron, ki rungume shi da hannunki gama zan maishe shi babbar al’umma.”

19 Sai Allah ya buɗe idanunta, ta ga rijiyar ruwa, ta kuwa tafi, ta cika salkar da ruwa ta ba yaron ya sha.

20 Allah kuwa yana tare da yaron, ya kuwa yi girma, ya zauna a jeji, ya zama riƙaƙƙen maharbi.

21 Ya zauna a jejin Faran. Sai mahaifiyarsa ta auro masa mata daga ƙasar Masar.

Ibrahim da Abimelek suka Ƙulla Yarjejeniya

22 A lokacin nan fa, ya zamana Abimelek, da Fikol shugaban sojojinsa ya zo ya ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai cikin sha’aninka duka,

23 don haka, yanzu sai ka rantse mini da Allah, cewa ba za ka ci amanata, ko ta ‘ya’yana, ko ta zuriyata ba, amma kamar yadda na riƙe ka cikin mutunci, haka za ka yi da ni da ƙasar da ka yi baƙunta a ciki.”

24 Sai Ibrahim ya amsa, “I, zan rantse.”

25 Sa’ad da Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek a kan rijiyar ruwa wadda barorin Abimelek suka ƙwace,

26 Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan abu ba, ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba sai yau.”

27 Ibrahim ya ɗibi tumaki da takarkarai ya bai wa Abimelek, su biyu ɗin kuwa suka yi alkawari.

28 Ibrahim ya ware ‘yan raguna bakwai daga cikin garke.

29 Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Ina ma’anar waɗannan ‘yan raguna bakwai da ka keɓe?”

30 Ya ce, “Waɗannan ‘yan raguna bakwai za ka karɓe su daga hannuna domin su zama shaida a gare ni, cewa ni na haƙa rijiyan nan.”

31 Don haka aka kira wannan wuri Biyer-sheba, domin a can ne su duka suka yi rantsuwa.

32 Saboda haka suka yi alkawari a Biyer-sheba. Sai Abimelek, tare da Fikol shugaban sojojinsa, ya tashi ya koma ƙasar Filistiyawa.

33 Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.

34 Ibrahim kuwa ya daɗe yana baƙunci a ƙasar Filistiyawa.

Categories
FAR

FAR 22

An Umarci Ibrahim ya yi Hadaya da Ishaku

1 Bayan waɗannan al’amura Allah ya jarraba Ibrahim ya ce masa, “Ibrahim!”

Sai ya ce, “Ga ni.”

2 Ya ce, “Ɗauki ɗanka, tilon ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi ƙasar Moriya, a can za ka miƙa shi hadayar ƙonawa a bisa kan ɗayan duwatsun da zan faɗa maka.”

3 Sai Ibrahim ya tashi tun da sassafe, ya ɗaura wa jakinsa shimfiɗa ya kuwa ɗauki biyu daga cikin samarinsa tare da shi, da kuma ɗansa Ishaku, ya faskara itace na yin hadayar ƙonawa. Ya kuwa tashi ya tafi inda Allah ya faɗa masa.

4 A rana ta uku Ibrahim ya ta da idanunsa ya hangi wurin daga nesa.

5 Ibrahim ya ce wa samarinsa, “Ku tsaya nan wurin jakin, ni da saurayin za mu yi gaba mu yi sujada, sa’an nan mu komo wurinku.”

6 Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare.

7 Ishaku ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba!”

Sai ya ce, “Ga ni, ɗana.”

Ya ce, “Ga wuta, ga itace, amma ina ragon hadayar ƙonawa?”

8 Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare.

9 Sa’ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden.

10 Sai Ibrahim ya miƙa hannu ya ɗauki wuƙar don ya yanka ɗansa.

11 Amma mala’ikan Ubangiji ya yi kiransa daga sama, ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!”

Sai ya ce, “Ga ni.”

12 Ya ce, “Kada ka sa hannunka a kan saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu, gama yanzu na sani kai mai tsoron Allah ne, da yake ba ka ƙi ba da ɗanka, tilonka, a gare ni ba.”

13 Ibrahim ya ta da idanunsa, ya duba, ga rago kuwa a bayansa, da ƙahoni a sarƙafe cikin kurmi. Ibrahim kuwa ya tafi ya kamo ragon, ya miƙa shi hadayar ƙonawa maimakon ɗansa.

14 Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, “Ubangiji zai tanada,” kamar yadda ake faɗa har yau, “A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada.”

15 Mala’ikan Ubangiji kuma ya sāke kiran Ibrahim, kira na biyu daga sama,

16 ya ce, “Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba,

17 hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,

18 ta wurin zuriyarka kuma al’umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.”

19 Sai Ibrahim ya koma wurin samarinsa. Suka tashi suka tafi Biyer-sheba tare. Ibrahim ya yi zamansa a Biyer-sheba.

Zuriyar Nahor

20 Ana nan bayan waɗannan al’amura, aka faɗa wa Ibrahim, “Ga shi, Milka ta haifa wa ɗan’uwanka Nahor, ‘ya’ya.

21 Uz ɗan fari, da Buz ɗan’uwansa, da Kemuwel mahaifin Aram,

22 da Kesed, da Hazo, da Fildash, da Yidlaf, da Betuwel.”

23 Betuwel kuwa ya haifi Rifkatu, su takwas ɗin nan Milka ta haifa wa Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.

24 Banda haka, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifi Teba, da Gaham, da Tahash, da Ma’aka.

Categories
FAR

FAR 23

Ibrahim Ya Sayi Makabarta a Rasuwar Saratu

1 Saratu ta yi shekara ɗari da ashirin da bakwai a duniya,

2 sa an nan ta rasu a Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar Kan’ana. Ibrahim kuwa ya tafi ya yi makoki, yana baƙin ciki domin Saratu.

3 Ibrahim ya bar gawar matarsa, ya je ya ce wa Hittiyawa,

4 “Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!”

5 Hittiyawa suka amsa wa Ibrahim suka ce,

6 “Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.”

7 Ibrahim ya tashi ya sunkuya wa Hittiyawa, mutanen ƙasar.

8 Sai ya ce musu, “Idan kun yarda in binne matata in daina ganinta, to, ku ji ni, ku roƙar mini Efron Bahitte ɗan Zohar,

9 ya ba ni kogon Makfela nasa na can ƙarshen saurarsa. Bari ya sallama mini wurin a gabanku a cikakken kuɗinsa, ya zama mallakata domin makabarta.”

10 A sa’an nan Efron yana tare da Hittiyawa. Sai Efron Bahitte ya amsa wa Ibrahim a kunnuwan Hittiyawa, da gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsa, ya ce,

11 “Ba haka ba ne, ya shugaba, ka ji ni. Na ba ka saurar, da kogon da yake cikinta. A gaban jama’ata na ba ka ita, ka binne matarka.”

12 Ibrahim kuwa ya sunkuya a gaban jama’ar ƙasar.

13 Ya ce wa Efron, a kunnuwan jama’ar ƙasar, “In dai ka yarda, ka ji ni. Zan ba da kuɗin saurar. Ka karɓa daga gare ni don in binne matata a can.”

14 Efron ya amsa wa Ibrahim,

15 “Ya shugabana, ka ji ni, don ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu, a bakin me yake, a tsakaninmu? Binne matarka.”

16 Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da ‘yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci.

17 Don haka saurar Efron da yake cikin Makfela wadda take gabashin Mamre, da saurar, da kogon da yake ciki, da dukan itatuwan da suke cikin saurar, iyakar girmanta duka

18 an tabbatar wa Ibrahim, cewa mallakarsa ce a gaban Hittiyawa, a gaban dukan waɗanda suke shiga ta ƙofar birninsu.

19 Bayan wannan, Ibrahim ya binne Saratu matarsa a kogon da yake a saurar Makfela a gabashin Mamre, wato Hebron, cikin ƙasar Kan’ana.

20 Da saurar, da kogon da yake cikinta, aka tabbatar wa Ibrahim mallakarsa ce don makabarta da iznin Hittiyawa.

Categories
FAR

FAR 24

Aka Auro wa Ishaku Mata

1 Yanzu Ibrahim ya tsufa, ya kuwa kwana biyu. Ubangiji kuma ya sa wa Ibrahim albarka a cikin abu duka.

2 Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata,

3 ka rantse da Ubangiji na sama da duniya, cewa ba za ka auro wa ɗana mata daga ‘yan matan Kan’aniyawa waɗanda nake zaune a tsakaninsu ba.

4 Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”

5 Sai baransa ya ce masa, “Watakila matar ba za ta yarda ta biyo ni zuwa wannan ƙasa ba, tilas ke nan, in koma da ɗanka ƙasar da ka fito?”

6 Ibrahim ya ce masa, “Ka kiyaye wannan fa, kada ka kuskura ka koma da ɗana can.

7 Ubangiji Allah na Sama wanda ya ɗauke ni daga gidan mahaifina daga ƙasar haihuwata, wanda ya yi magana da ni ya kuma rantse mini, ‘Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa,’ shi zai aiki mala’ikansa a gabanka. Za ka kuwa auro wa ɗana mata daga can.

8 Amma idan matar ba ta yarda ta biyo ka ba, ka kuɓuta daga rantsuwan nan tawa. Kai dai kada ka koma da ɗana can.”

9 Sai baran ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar Ibrahim maigidansa, ya kuwa rantse masa zai yi.

10 Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.

11 Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa.

12 Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim.

13 Ga shi kuwa, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ga kuma ‘yan matan mutanen birnin suna fitowa garin ɗibar ruwa.

14 Bari budurwar da zan ce wa, ‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,’ wadda za ta ce, ‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,’ bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.”

15 Kafin ya rufe baki, sai ga Rifkatu wadda aka haifa wa Betuwel ɗan Milka, matar Nahor ɗan’uwan Ibrahim, ta fito da tulun ruwanta a bisa kafaɗarta.

16 Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro.

17 Sai baran ya tarye ta a guje, ya ce, “Roƙo nake, ki ba ni ruwa kaɗan daga cikin tulunki in sha.”

18 Ta ce, “Sha, ya shugabana.” Nan da nan ta sauke tulunta ta riƙe a hannunta, ta ba shi ya sha.

19 Sa’ad da ta gama shayar da shi, ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka kuma, har su gama sha.”

20 Sai nan da nan ta bulbule tulunta a cikin kwami, ta sāke sheƙawa a guje zuwa rijiyar, ta kuwa ɗebo wa raƙumansa duka.

21 Mutumin kuwa ya zura mata ido, shiru, yana so ya sani ko Allah ya arzuta tafiyarsa, ko kuwa babu?

22 Sa’ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,

23 ya ce, “Ki faɗa mini ke ‘yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?”

24 Sai ta ce masa, “Ni ‘yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.”

25 Ta ƙara da cewa, “Muna da isasshen baro da harawa duka, da kuma masauki.”

26 Mutumin ya yi ruku’u ya yi wa Ubangiji sujada,

27 ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan’uwan maigidana.”

28 Budurwar ta sheƙa a guje zuwa gida wurin mahaifiyarta ta faɗi waɗannan abubuwa.

29 Rifkatu kuwa tana da ɗan’uwa sunansa Laban. Sai Laban ya sheƙo zuwa wurin mutumin a bakin rijiya.

30 Sa’ad da ya ga zoben da mundaye da suke hannuwan ‘yar’uwarsa, sa’ad da kuma ya ji maganar Rifkatu ‘yar’uwarsa cewa, “Ga abin da mutumin ya faɗa mini,” sai ya je wurin. Ya kuwa same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar.

31 Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”

32 Mutumin ya shiga gidan, Laban kuwa ya sauke raƙuman, ya ba shi baro da harawa domin raƙuma, da ruwa ya wanke ƙafafunsa da ƙafafun waɗanda suke tare da shi.

33 Aka sa abinci a gabansa domin ya ci, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.”

Laban ya ce, “Faɗi maganarka.”

34 Ya ce, “Ni baran Ibrahim ne.

35 Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.

36 Saratu ta haifa wa maigidana ɗa cikin tsufanta, a gare shi kuma ya ba da dukan abin da yake da shi.

37 Maigidana ya rantsar da ni da cewa, ‘Ba za ka auro wa ɗana mace daga cikin ‘ya’yan Kan’aniyawa waɗanda nake zaune a ƙasarsu ba,

38 amma ka tafi gidan mahaifina da dangina, ka auro wa ɗana mace.’

39 Sai na ce wa maigidana, ‘Watakila matar ba za ta biyo ni ba.’

40 Amma ya amsa mini ya ce, ‘Ubangiji wanda nake tafiya a gabansa zai aiki mala’ikansa tare da kai, ya arzuta hanyarka, za ka kuwa auro wa ɗana mace daga cikin dangina daga gidan mahaifina.

41 Sa’an nan za ka kuɓuta daga rantsuwata. Sa’ad da ka zo wurin dangina, idan kuwa ba su ba ka ita ba, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’

42 “Yau kuwa da na iso bakin rijiyar, sai na ce a raina, ‘Ya Ubangiji, Allah na shugabana Ibrahim, in nufinka ne ka arzuta tafiyata.

43 Ga ni, ina tsaye a bakin rijiyar kuwa, bari budurwar da za ta fito ɗibar ruwa, wadda in na ce mata, “Roƙo nake, ba ni ruwa kaɗan daga ruwan tulunki in sha,”

44 in ta amsa mini, “To, sha, zan ɗebo wa raƙumanka kuma,” bari ta zama ita ce wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’

45 Kafin in gama tunani a zuciyata, sai ga Rifkatu ta fito ɗauke da tulun ruwa a kafaɗarta, ta gangara zuwa rijiya ta ɗebo. Na ce mata, ‘Roƙo nake, ki ba ni, in sha.’

46 Nan da nan ta sauke tulunta daga kafaɗarta, ta ce, ‘To, sha, zan kuma shayar da raƙumanka.’ Na sha, ta kuma shayar da raƙuman.

47 Na kuwa tambaye ta, ‘’Yar gidan wane ne ke?’ Ta ce, ‘Ni ‘yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ Sai na sa mata zobe a hanci, mundaye kuma a hannu.

48 Sa’an nan na yi ruku’u, na yi wa Ubangiji sujada, na yabi Ubangiji Allah na maigidana, Ibrahim, wanda ya bishe ni a hanya sosai, in auro wa ɗansa ‘yar danginsa.

49 Yanzu fa, idan za ku amince ku gaskata da maigidana, ku faɗa mini, in ba haka ba, sai ku faɗa mini, domin in san abin yi, in juya dama ko hagu.”

50 Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al’amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a’a.

51 Ga Rifkatu nan gabanka, ka ɗauke ta ku tafi, ta zama matar ɗan maigidanka, bisa ga faɗar Ubangiji.”

52 Sa’ad da baran Ibrahim ya ji wannan, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada a gaban Ubangiji.

53 Sai baran ya kawo kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, ya bai wa Rifkatu, ya kuma ba ɗan’uwanta da mahaifiyarta kayan ado masu tsada.

54 Shi da mutanen da suke tare da shi suka ci suka sha, suka kwana wurin. Da suka tashi da safe, sai ya ce, “A sallame ni, in koma wurin maigidana.”

55 Ɗan’uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Ka bar budurwar tare da mu har ɗan lokaci, kada ya gaza kwana goma, bayan wannan ta tafi.”

56 Amma ya ce musu, “Kada ku makarar da ni, tun da yake Allah ya arzuta tafiyata, a sallame ni domin in koma wurin maigidana.”

57 Suka ce, “Za mu kira budurwar mu tambaye ta.”

58 Suka kirawo Rifkatu suka ce mata, “Za ki tafi tare da wannan mutum?”

Sai ta ce, “Zan tafi.”

59 Suka kuwa sallami Rifkatu ‘yar’uwarsu da uwar goyonta, da baran Ibrahim da mutanensa.

60 Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata,

“’Yar’uwarmu, ki zama mahaifiyar

dubbai,

Har dubbai goma,

Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofin

maƙiyansu!”

61 Sai Rifkatu da kuyanginta suka tashi suka hau raƙuman, suka bi mutumin. Haka nan kuwa baran ya ɗauki Rifkatu ya koma.

62 A lokacin kuwa Ishaku ya riga ya zo daga Biyer-lahai-royi yana zaune a Negeb.

63 A gabatowar maraice, sai Ishaku ya fita saura ya yi tunani, ya ɗaga idanunsa ya duba, ya ga raƙuma suna zuwa.

64 Da Rifkatu ta ɗaga idanunta, ta hangi Ishaku, sai ta sauka daga raƙumi,

65 ta ce wa baran, “Wane ne mutumin can da yake zuwa daga saura garin ya tarye mu?”

Sai baran ya ce, “Ai, maigidana ne.” Ta ɗauki mayafinta ta yi lulluɓi.

66 Sai baran ya faɗa wa Ishaku dukan abin da ya yi.

67 Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Categories
FAR

FAR 25

Sauran Zuriyar Ibrahim

1 Ibrahim ya auro wata mace kuma, sunanta Ketura.

2 Ta haifa masa Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa.

3 Yokshan ya haifi Sheba da Dedan. ‘Ya’yan Dedan su ne Asshurim, da Letushim, da Le’umomim.

4 ‘Ya’yan Madayana su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka ‘ya’yan Ketura ne.

5 Ibrahim ya ba Ishaku dukan abin da yake da shi.

6 Amma ga ‘ya’yan ƙwaraƙwarai Ibrahim ya ba da kyautai, ya sallame su tun yana da rai, su tafi nesa da Ishaku zuwa can cikin ƙasar gabas.

Rasuwar Ibrahim da Jana’izarsa

7 Waɗannan su ne kwanakin shekarun Ibrahim a duniya, shekara ɗari da saba’in da biyar.

8 Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama’arsa, waɗanda suka riga shi.

9 Ishaku da Isma’ilu ‘ya’yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre,

10 wato saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa.

11 Bayan rasuwa Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.

Zuriyar Isma’ilu

12 Waɗannan su ne zuriyar Isma’ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.

13 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Isma’ilu, maza, bisa ga haihuwarsu. Nebayot ɗan farin Isma’ilu, da Kedar, da Adbeyel, da Mibsam,

14 da Mishma, da Duma, da Massa,

15 da Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema.

16 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Isma’ilu, bisa ga ƙauyukansu da zangonsu, hakimai goma sha biyu, bisa ga kabilansu.

17 Waɗannan su ne shekarun Isma’ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama’arsa waɗanda suka riga shi.

18 Mazauninsa a tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake ɗaura da Masar wajen Assuriya. Suka ware daga danginsu suka yi zamansu.

Haihuwar Isuwa da Yakubu

19 Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ya haifi Ishaku.

20 Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rifkatu, ‘yar Betuwel Ba’aramiye daga Fadan-aram ‘yar’uwar Laban Ba’aramiye.

21 Ishaku kuwa ya yi addu’a sai matarsa Rifkatu ta yi ciki.

22 ‘Ya’yan kuwa suka kama kokawa da juna a cikinta, har ta ce, “In haka ne don me zan rayu?” Sai ta je ta tambayi Ubangiji.

23 Sai Ubangiji ya ce mata, “Al’umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”

24 Sa’ad da kwanakin haihuwarta suka cika, sai ga shi, ashe, tagwaye ne suke a cikin mahaifarta.

25 Na farin ya fito ja wur kamar riga mai gashi, saboda haka suka raɗa masa suna Isuwa.

26 Daga baya kuma ɗan’uwansa ya fito, hannunsa na riƙe da diddigen Isuwa, saboda haka aka raɗa masa suna Yakubu. Ishaku yana da shekara sittin sa’ad da ya haife su.

Isuwa ya Sayar da Matsayinsa na Ɗan Fari

27 Sa’ad da yaran suka yi girma, Isuwa ya zama ƙwararren maharbi, ya zama mutumin jeji, Yakubu kuwa kintsattse ne mai son zaman gida.

28 Ishaku ya ƙaunaci Isuwa saboda yakan ci naman da ya farauto, amma Rifkatu ta ƙaunaci Yakubu.

29 Wata rana, sa’ad da Yakubu yake dafa fate, Isuwa ya komo daga jeji, yana jin yunwa ƙwarai.

30 Sai Isuwa ya ce wa Yakubu, “Ka ɗibar mini jan fatenka in sha, gama ina fama da yunwa!” Saboda haka aka kira sunansa Edom.

31 Yakubu ya ce, “Sai dai ko in yau za ka sayar mini da matsayinka na ɗan fari.”

32 Sai Isuwa ya ce, “Ni da nake bakin mutuwa, wane amfani matsayina na ɗan fari zai yi mini?”

33 Yakubu ya ce, “Yau sai ka rantse mini.” Sai ya rantse masa ya kuwa sayar wa Yakubu da matsayinsa na ɗan fari.

34 Sa’an nan Yakubu ya ba Isuwa gurasa da faten wake, ya ci ya sha, ya tashi ya yi tafiyarsa. Ta haka Isuwa ya banzatar da matsayinsa na ɗan fari.

Categories
FAR

FAR 26

Ishaku a Gerar da Biyer-sheba

1 Aka sāke yin yunwa a ƙasar, banda wadda aka yi a zamanin Ibrahim. Sai Ishaku ya tafi Gerar wurin Abimelek, Sarkin Filistiyawa.

2 Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar, ka zauna a ƙasar da zan faɗa maka.

3 Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.

4 Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al’umman duniya duka za su sami albarka,

5 saboda Ibrahim ya yi biyayya da muryata, ya kuma kiyaye umarnina, da dokokina, da ka’idodina, da shari’una.”

6 Ishaku ya yi zamansa a Gerar.

7 Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi matarsa, ya ce, “Ita ‘yar’uwata ce,” gama yana jin tsoro ya ce, “Ita matata ce,” don kada mutanen wurin su kashe shi saboda Rifkatu, da yake ita kyakkyawa ce.

8 Sa’ad da ya dakata ‘yan kwanaki a can, sai Abimelek, Sarkin Filistiyawa ya duba ta taga, ya ga Ishaku ya rungumi Rifkatu.

9 Sai Abimelek ya kira Ishaku, ya ce, “Ashe lalle ita matarka ce, ƙaƙa fa ka ce, ‘Ita ‘yar’uwata ce’?”

Ishaku ya amsa masa ya ce, “Don na yi tsammani zan rasa raina saboda ita.”

10 Abimelek ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ai, da wani daga jama’a ya kwana da matarka a sawwaƙe, da ka jawo laifi a bisanmu.”

11 Abimelek ya umarci dukan mutane ya ce, “Duk wanda ya taɓa mutumin nan ko matarsa, za a kashe shi.”

12 Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekaran nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka,

13 har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.

14 Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa.

15 Saboda haka, Filistiyawa don kishi sai suka ciccike rijiyoyin da ƙasa, waɗanda barorin mahaifinsa, Ibrahim, suka haƙa tun Ibrahim yana da rai.

16 Abimelek kuwa ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu, gama ka fi ƙarfinmu.”

17 Don haka Ishaku ya bar wurin, ya yi zango cikin kwarin Gerar, ya yi zamansa a can.

18 Sai Ishaku ya sāke haƙa rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa sun tattoshe su bayan rasuwar Ibrahim. Ishaku kuma ya sa wa rijiyoyin sunayen da mahaifinsa ya sa musu.

19 Amma sa’ad da barorin Ishaku suka haƙa rijiya a kwarin, sai suka tarar da idon ruwa.

20 Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa,“Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta.

21 Suka haƙa wata rijiya, suka yi jayayya a kan wannan kuma, ya sa mata suna Sitna.

22 Sai ya zakuɗa daga nan ya haƙa wata rijiya kuma, amma ba su yi jayayya a kan wannan ba, don haka ya sa mata suna Rehobot, yana cewa, “Gama yanzu Ubangiji ya yalwata mana, za mu hayayyafa a ƙasa.”

23 Daga nan ya haura zuwa Biyer-sheba.

24 Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”

25 Ishaku ya gina bagade a wurin ya kira bisa sunan Ubangiji, a can kuwa ya kafa alfarwarsa. A can ne kuma barorin Ishaku suka haƙa rijiya.

Yarjejeniya Tsakanin Ishaku da Abimelek

26 Abimelek ya zo daga Gerar tare da Ahuzat mashawarcinsa da Fikol shugaban sojojinsa, don ya ga Ishaku.

27 Sai Ishaku ya ce musu, “Me yake tafe da ku zuwa gare ni, ga shi kun ƙi ni, kun kuma kore ni nesa da ku?”

28 Suka ce, “Lalle, mun gani a fili Ubangiji yana tare da kai, saboda haka muke cewa bari rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai, bari kuma mu ƙulla alkawari da kai,

29 cewa ba za ka cuce mu ba, daidai kamar yadda ba mu taɓe ka ba, ba mu yi maka kome ba sai alheri, muka kuwa sallame ka cikin salama. Yanzu, kai albarkatacce ne na Ubangiji.”

30 Sai ya shirya musu liyafa, suka ci suka sha.

31 Suka tashi tun da sassafe suka rantse wa juna, Ishaku ya sallame su, suka tafi cikin salama.

32 Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.”

33 Ya sa mata suna Sheba, domin haka har yau sunan birnin Biyer-sheba.

34 Sa’ad da Isuwa yake da shekara arba’in, ya auro Judit, ‘yar Biyeri Bahitte, da Basemat ‘yar Elon Bahitte,

35 suka baƙanta wa Ishaku da Rifkatu rai.

Categories
FAR

FAR 27

Yakubu Ya Karɓi Albarka daga wurin Ishaku

1 Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!”

Sai ya amsa, “Ga ni nan.”

2 Ishaku ya ce, “Ga shi, na tsufa, ban san ranar rasuwata ba.

3 Yanzu fa, ka ɗauki makamanka, da kwarinka da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama,

4 ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.”

5 Rifkatu kuwa tana ji lokacin da Ishaku yake magana da ɗansa Isuwa. Don haka, sa’ad da Isuwa ya tafi jeji garin ya farauto nama ya kawo,

6 sai Rifkatu ta ce wa ɗanta Yakubu, “Na ji mahaifinka ya yi magana da ɗan’uwanka Isuwa, ya ce,

7 ‘Kawo mini nama, ka shirya mini abinci mai daɗi in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in rasu.’

8 Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka.

9 Je ka garke, ka kamo ‘yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so.

10 Kai kuwa ka kai wa mahaifinka, ya ci, domin ya sa maka albarka kafin ya rasu.”

11 Amma Yakubu ya ce wa Rifkatu mahaifiyarsa, “Ga shi fa, ɗan’uwana Isuwa gargasa ne, ni kuwa mai sulɓi ne.

12 Watakila, baba zai lallaluba ni, zai kuwa ce, ruɗinsa nake yi, in kuwa jawo wa kaina la’ana maimakon albarka.”

13 Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La’anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.”

14 Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so.

15 Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su,

16 fatun ‘yan awakin kuwa ta naɗe wa hannuwansa, da sashen dokin wuyansa mai sulɓi.

17 Sai ta bai wa ɗanta, Yakubu, abinci mai daɗin ci da gurasar da ta shirya.

18 Ya kuwa shiga wurin mahaifinsa, ya ce, “Baba.”

Mahaifin ya ce, “Ga ni, wane ne kai, ya ɗana?”

19 Yakubu ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini, in ka yarda ka tashi ka ci naman da na harbo, domin ka sa mini albarka.”

20 Amma Ishaku ya ce wa ɗansa, “Ƙaƙa aka yi ka same shi da sauri haka, ɗana?”

Sai ya amsa, “Domin Ubangiji, Allahnka, ya ba ni sa’a.”

21 Ishaku kuwa ya ce wa Yakubu, “Matso kusa in ka yarda, don in lallaluba ka, ɗana, domin in hakikance ko kai ne ɗana Isuwa, ko babu.”

22 Saboda haka Yakubu ya matsa kusa da Ishaku mahaifinsa, sai ya lallaluba shi, ya ce, “Murya, muryar Yakubu ce, amma hannuwa, hannuwan Isuwa ne.”

23 Amma bai gane shi ba, gama hannuwansa gargasa ne kamar hannuwan ɗan’uwansa Isuwa, saboda haka ya sa masa albarka.

24 Ya ce, “Hakika, kai ne ɗana Isuwa?”

Ya amsa, “Ni ne.”

25 Ya ce, “Kawo mini naman da ka harbo, in ci in sa maka albarka.” Sai ya kawo masa, ya kuwa ci, ya kawo masa ruwan inabi, ya sha.

26 Mahaifinsa Ishaku kuwa ya ce masa, “Zo kusa ka sumbace ni, ɗana.”

27 Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce,

“Duba, ƙanshin ɗana

Yana kama da ƙanshin jeji

Wanda Ubangiji ya sa wa albarka!

28 Allah ya ba ka daga cikin raɓar

sama,

Daga cikin ni’imar ƙasa,

Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.

29 Bari jama’a su bauta maka,

Al’ummai kuma su sunkuya maka.

Za ka yi shugabancin ‘yan’uwanka,

Allah ya sa ‘ya’yan mahaifiyarka su

sunkuya maka.

La’ananne ne dukan wanda ya

la’anta ka,

Albarkatacce ne dukan wanda ya sa

maka albarka.”

30 Ishaku yana gama sa wa Yakubu albarka, Yakubu yana fita daga gaban mahaifinsa ke nan sai ga Isuwa ɗan’uwansa ya komo daga farauta.

31 Shi kuma ya shirya abinci mai daɗin ci, ya kawo wa mahaifinsa. Sai ya ce wa mahaifinsa, “In ka yarda baba, ka tashi, ka ci naman da na harbo don ka sa mini albarka.”

32 Mahaifinsa Ishaku ya ce masa, “Wane ne kai?”

Ya amsa, “Ni ne ɗanka, ɗan farinka, Isuwa.”

33 Ishaku kuwa ya yi makyarkyata ƙwarai, ya ce, “Wane ne wannan fa, da ya farauto naman ya kawo mini, na kuwa cinye kafin ka zo, har na sa masa albarka? – i, albarkatacce zai zama.”

34 Da Isuwa ya ji kalmomin mahaifinsa, sai ya yi kūwwa da kuka mai tsananin gaske, ya ce wa mahaifinsa, “Ka sa mini albarka, har da ni ma, ya babana.”

35 Amma ya ce, “Ɗan’uwanka ya zo cikin makirci, ya karɓe albarkarka.”

36 Isuwa ya ce, “Ba saboda haka ne aka raɗa masa suna Yakubu ba? Gama sau biyu ke nan yake yi mini ƙwace. Ya ƙwace mini matsayina na ɗan fari, ga shi kuma, yanzu ya ƙwace mini albarkata.” Sa’an nan ya ce, “Ba sauran albarkar da ka rage mini?”

37 Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan ‘yan’uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?”

38 Sai Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Har da ni ma ka sa mini albarka, babana.” Isuwa ya ta da murya ya yi kuka.

39 Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce,

“Ga shi, ni’imar ƙasar za ta nisanci

mazauninka,

Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za

ta nisance ka.

40 Ta wurin takobinka za ka rayu

Za ka yi wa ɗan’uwanka barantaka,

Amma sa’ad da ka ɓalle,

Za ka kakkarye karkiyarsa daga

wuyanka.”

41 Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa’an nan zan kashe Yakubu ɗan’uwana.”

42 Amma maganganun Isuwa babban ɗanta suka kai a kunnen Rifkatu. Saboda haka, sai ta aika aka kirawo Yakubu ƙaramin ɗanta. Ta ce masa, “Ga shi, ɗan’uwanka Isuwa, yana ta’azantar da kansa da nufin ya kashe ka, ya ɗau fansa.

43 Domin haka, ɗana, ka ji muryata, ka tashi ka gudu zuwa wurin Laban ɗan’uwana a Haran,

44 ka zauna tare da shi ‘yan kwanaki, har zafin fushin ɗan’uwanka ya huce,

45 ya manta da abin da ka yi masa, sa’an nan zan aika in komo da kai daga can. Don me zan rasa ku, ku biyu a rana ɗaya?”

Ishaku Ya Aika da Yakubu wurin Laban

46 Rifkatu kuwa ta ce wa Ishaku, “Na gaji da raina saboda matan Hittiyawa. Idan Yakubu zai auri ɗaya daga cikin waɗannan mata na Hittiyawa, wato daga matan ƙasar, wane amfani raina zai daɗa mini?”

Categories
FAR

FAR 28

1 Ishaku ya kira Yakubu ya sa masa albarka, ya umarce shi da cewa, “Ba za ka auri ɗaya daga cikin ‘ya’yan matan Kan’aniyawa ba.

2 Tashi, ka tafi Fadan-aram, zuwa gidan Betuwel kakanka na wajen uwa, ka zaɓo wa kanka mata daga cikin ‘ya’ya mata na Laban ɗan’uwan mahaifiyarka a can.

3 Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama’o’i,

4 ya kuma sa ka sami albarkar Ibrahim da zuriyarka tare da kai, har da za ka amshe ƙasar baƙuncinka wadda Allah ya bai wa Ibrahim!”

5 Da haka, Ishaku ya sallami Yakubu, ya kuwa tafi Fadan-aram wurin Laban, ɗan Betuwel Ba’aramiye ɗan’uwan Rifkatu, mahaifiyar Yakubu da Isuwa.

Isuwa Ya Ƙara Auro Wata

6 Yanzu Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka, ya kuwa sallame shi zuwa Fadan-aram domin ya auro mace daga can. Da Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka ya kuma umarce shi da cewa, “Ba za ka auro wata daga cikin ‘yan matan Kan’aniyawa ba,”

7 ya kuma ga Yakubu ya biye wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, har ya tafi Fadan-aram,

8 sai Isuwa ya gane ‘yan matan Kan’aniyawa ba su gamshi Ishaku mahaifinsa ba.

9 Saboda haka Isuwa ya tafi wurin Isma’ilu ya auro Mahalat ‘yar’uwar Nebayot, ‘yar Isma’ilu ɗan Ibrahim, banda matan da yake da su.

Mafarkin Yakubu a Betel

10 Yakubu ya bar Biyer-sheba ya kama hanya zuwa Haran.

11 Da ya isa wani wuri, sai ya kwana can a wannan dare, don rana ta riga ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun da suke wurin, ya yi matashin kai da shi, ya kwanta, ya yi barci.

12 Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala’ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa!

13 Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.

14 Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka.

15 Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”

16 Yakubu ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika, Ubangiji yana wurin nan, ni kuwa ban sani ba.”

17 Ya tsorata, sai ya ce, “Wane irin wuri ne wannan mai banrazana haka! Ba shakka wannan wurin Allah ne, nan ne kuma ƙofar Sama.”

18 Sai Yakubu ya tashi tun da sassafe, ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuwa zuba mai a kan al’amudin.

19 Ya kira sunan wurin nan Betel, amma da farko, sunan birnin, Luz.

20 Yakubu ya yi wa’adi da cewa, “Idan Allah zai kasance tare da ni, ya kiyaye ni cikin tafiyan nan da nake yi, ya kuma ba ni abincin da zan ci, da suturar da zan sa,

21 har kuma in sāke komowa gidan mahaifina da salama, da Ubangiji ya zama Allahna,

22 wannan dutse kuwa wanda na kafa shi al’amudi zai zama wurin sujada ga Allah. Daga cikin dukan abin da ya ba ni, zan ba shi ushirinsa.”

Categories
FAR

FAR 29

Yakubu Ya Isa Gidan Laban

1 Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya.

2 Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba.

3 A sa’ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa’an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya.

4 Yakubu ya ce musu, “’Yan’uwana, daga ina kuka fito?”

Suka ce, “Daga Haran muke.”

5 Sai ya ce musu, “Kun san Laban ɗan Nahor?”

Suka ce, “Mun san shi.”

6 Ya ce musu, “Lafiyarsa ƙalau?”

Suka ce, “I, lafiya ƙalau yake, ga ma Rahila ‘yarsa, tana zuwa da bisashensa!”

7 Ya ce, “Ga shi kuwa, da sauran rana da yawa, lokacin tattaruwar dabbobi bai yi ba, me zai hana ku shayar da tumakin, ku sāke kai su wurin kiwo?”

8 Amma suka ce, “Ba za mu iya ba, sai sauran garkunan duka sun taru, sa’an nan a kawar da dutsen daga bakin rijiyar, sa’an nan mu shayar da garkuna.”

9 Kafin ya rufe baki, sai ga Rahila ta zo da bisashen mahaifinta, gama ita take kiwonsu.

10 Sa’ad da Yakubu ya ga Rahila, ‘yar Laban kawunsa, da bisashen, sai Yakubu ya hau ya kawar da dutsen daga bakin rijiyar, ya shayar da garken Laban, kawunsa.

11 Yakubu kuwa ya sumbaci Rahila, ya fara kuka da ƙarfi.

12 Ya faɗa mata shi dangin mahaifinta ne, shi kuma ɗan Rifkatu ne, sai ta sheƙa ta faɗa wa mahaifinta.

13 Sa’ad da Laban ya sami labari a kan Yakubu ɗan ‘yar’uwarsa, sai ya sheƙo ya tarye shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kawo shi a gidansa. Yakubu ya labarta wa Laban al’amura duka.

14 Laban ya ce masa, “Hakika, kai ƙashina ne da namana!” Yakubu ya zauna wata guda tara da Laban.

Yakubu Ya Yi wa Laban Barantaka domin Rahila da Lai’atu

15 Laban kuwa ya ce wa Yakubu, “Don kana dangina, za ka yi mini barantaka a banza? Ka faɗa mini, nawa zan biya ka?”

16 Laban dai yana da ‘ya’ya mata biyu, sunan babbar Lai’atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.

17 Lai’atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.

18 Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin ‘yarka Rahila.”

19 Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.”

20 Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar ‘yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.

21 Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.”

22 Sai Laban ya tattara mutanen wurin duka, ya yi biki.

23 Amma da maraice, ya ɗauki ‘yarsa Lai’atu ya kawo ta wurin Yakubu, Yakubu ya shiga a wurinta.

24 (Laban ya ba ‘yarsa Lai’atu Zilfa ta zama kuyangarta).

25 Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai’atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”

26 Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin ‘yar fari.

27 Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa’an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.”

28 Yakubu kuwa ya yi haka ɗin, ya cikasa makon, sa’an nan Laban ya aurar masa da ‘yarsa Rahila.

29 (Laban ya ba ‘yarsa Rahila Bilha, kuyangarsa, ta zama kuyangarta).

30 Sai Yakubu ya shiga wurin Rahila, amma ya fi ƙaunar Rahila da Lai’atu. Ya yi wa Laban barantaka waɗansu shekara bakwai kuma.

An Haifa wa Yakubu ‘Ya’ya

31 Sa’ad da Ubangiji ya ga ana ƙin Lai’atu, ya buɗe mahaifarta, amma Rahila bakarariya ce.

32 Lai’atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra’ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”

33 Ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Saboda Ubangiji ya ji ana ƙina ya ba ni wannan ɗa kuma,” ta kuwa raɗa masa suna Saminu.

34 Sai kuma ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Yanzu, a wannan karo mijina zai shaƙu da ni , domin na haifa masa ‘ya’ya uku maza.” Saboda haka ta raɗa masa suna Lawi.

35 Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.

Categories
FAR

FAR 30

1 Sa’ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin ‘yar’uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni ‘ya’ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”

2 Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”

3 Sai ta ce, “Ga kuyangata Bilha, ka shiga wurinta, domin ta haihu bisa gwiwoyina, domin ni ma in sami ‘ya’ya ta wurinta.”

4 Don haka ta ba shi Bilha ta zama matarsa. Yakubu kuwa ya shiga wurinta.

5 Bilha kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa.

6 Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan.

7 Bilha, kuyangar Rahila, ta sāke yin ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu.

8 Sai Rahila ta ce, “Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa da ‘yar’uwata, har na yi rinjaye,” sai ta raɗa masa suna Naftali.

9 Sa’ad da Lai’atu ta ga ta daina haihuwa, sai ta ɗauki kuyangarta Zilfa, ta ba Yakubu ta zama matarsa.

10 Kuyangar Lai’atu, Zilfa, ta haifa wa Yakubu ɗa.

11 Lai’atu kuma ta ce, “Sa’a!” Saboda haka ta sa masa suna Gad.

12 Kuyangar Lai’atu ta sāke haifa wa Yakubu ɗa na biyu.

13 Lai’atu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Gama mata za su ce da ni mai farin ciki,” saboda haka ta raɗa masa suna Ashiru.

14 A kwanakin kakar alkama, Ra’ubainu ya fita ya samo manta uwa a saura, ya kawo wa mahaifiyarsa Lai’atu. Sai Rahila ta ce wa Lai’atu, “Ina roƙonki, ɗiba mini daga cikin manta uwar da ɗanki ya samo.”

15 Amma ta ce mata, “Kanƙanen abu ne da kika ƙwace mini mijina? Za ki kuma ƙwace manta uwar da ɗana ya samo kuma?”

Rahila ta ce, “To, in haka ne, bari ya kwana tare da ke a daren yau a maimakon manta uwar da ɗanki ya samo.”

16 Sa’ad da Yakubu ya komo daga saura da maraice, Lai’atu ta fita ta tarye shi, ta ce, “Sai ka shigo wurina, gama na riga na ijarar da kai da manta uwar da ɗana ya samo.” Saboda haka ya kwana tare da ita a daren nan.

17 Allah ya saurari Lai’atu, ta kuwa yi ciki ta haifa wa Yakubu ɗa na biyar.

18 Lai’atu ta ce, “Allah ya yi mini sakamako domin na ba da kuyangata ga mijina,” saboda haka ta raɗa masa suna Issaka.

19 Lai’atu ta sāke yin ciki ta kuwa haifa wa Yakubu ɗa na shida.

20 Sai Lai’atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa ‘ya’ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.

21 Daga baya ta haifi ‘ya mace, ta kuwa raɗa mata suna Dinatu.

22 Allah kuwa ya tuna da Rahila, ya saurare ta, ya buɗe mahaifarta.

23 Ta yi ciki ta haifa ɗa, ta ce, “Allah ya kawar da zargina,”

24 ta sa masa suna Yusufu, tana cewa, “Da ma a ce Ubangiji ya ƙara mini wani ɗa!”

Yakubu Ya Yi Jinga da Laban

25 Bayan da Rahila ta haifi Yusufu, Yakubu ya ce wa Laban, “Ka sallame mu, domin mu tafi gidanmu a ƙasarmu.

26 Ka ba ni matana da ‘ya’yana waɗanda na yi maka barantaka saboda su, ka bar mu mu tafi, ka dai san ɗawainiyar da na yi maka.”

27 Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai.

28 Ka faɗa mini ladanka in ba ka.”

29 Yakubu ya ce masa, “Kai da kanka ka san barantakar da na yi maka, yadda bisashenka suka yawaita a hannuna.

30 Gama kafin in zo, kana da ‘yan kima ne, ga shi, sun ƙaru da yawa, Ubangiji kuwa ya sa maka albarka duk inda na juya. Amma yanzu, sai yaushe zan hidimta wa nawa gidan?”

31 Ya ce, “Me zan ba ka?”

Yakubu ya ce, “Ba za ka ba ni kome ba, in da za ka yi mini wannan, sai in sāke kiwon garkenka in lura da shi,

32 bar ni, in ratsa garkenka duka yau, in keɓe dukan masu dabbare-dabbare da tumaki babare-babare, da kowane ɗan rago baƙi, da dabbare-dabbare da babare-babare na awaki, waɗannan ne za su zama ladana.

33 Ta haka amincina zai shaide ni a gabanka a sa’ad da ka zo bincike hakkina. Duk wanda aka iske ba dabbare-dabbare ba ne, kuma ba babare-babare ba ne cikin awaki, ba kuma baƙi ba ne a cikin raguna, in aka samu a wurina, sai a ɗauka, na sata ne.”

34 Laban ya ce, “Madalla! Bari ya kasance kamar yadda ka faɗa.”

35 Amma a ran nan Laban ya ware bunsuran da suke dabbare-dabbare da masu sofane, da dukan awakin da suke dabbare-dabbare da kyalloli, da dukan baƙaƙen tumaki, ya danƙa su a hannun ‘ya’yansa maza,

36 ya sa nisan tafiya ta kwana uku tsakaninsu da Yakubu, Yakubu kuma ya ci gaba da kiwon sauran garken Laban.

37 Yakubu ya samo ɗanyun tsabgogin aduruku, da na katambiri, da na durumi, ya ɓare ya bayyanar da fararen zane-zanensu a fili.

38 Ya kafa tsabgogin da ya ɓare a gaban garkuna a magudana, wato kwamame na banruwa, don sukan yi barbara a wurin sa’ad da suka zo shan ruwa.

39 Garkunan suka yi barbara a gaban tsabgogin, don haka garkunan sukan haifi masu zāne, dabbare-dabbare da masu sofane.

40 Yakubu kuwa ya keɓe ‘yan raguna, ya sa garkuna su fuskanci tsabgogin da ya shasshauta, da dukan baƙaƙen da suke cikin garken Laban. Sai ya ware waɗanda suke nasa, bai kuwa haɗa su da garken Laban ba.

41 A kowane lokacin da ƙarfafan yake barbara Yakubu yakan sa tsabgogin a magudana a gaban idanun garken, domin su yi barbara a tsakanin tsabgogin.

42 Amma ga marasa ƙarfi na garken, ba ya sa musu. Don haka marasa ƙarfin ne na Laban, ƙarfafan kuwa na Yakubu.

43 Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙen mai arziki, yana da manya manyan garkuna da barori mata da maza, da raƙuma, da jakuna.