Categories
1 SAM

1 SAM 1

Haihuwar Sama’ila

1 Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf.

2 Yana da mata biyu, sunayensu Hannatu da Feninna. Feninna tana da ‘ya’ya, amma Hannatu ba ta haihuwa.

3 A kowace shekara Elkana yakan haura daga garinsu zuwa Shilo domin ya miƙa wa Ubangiji Mai Runduna hadaya, ya kuma yi masa sujada. ‘Ya’yan Eli, maza biyu, Hofni da Finehas, su ne firistoci na Ubangiji a can.

4 Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da ‘ya’yanta mata da maza nasu rabo.

5 Amma Hannatu, sai ya ba ta babban rabo guda ɗaya, gama yana ƙaunarta, amma Ubangiji ya kulle mahaifarta.

6 Kishiyarta takan tsokane ta don ta ji haushi, gama Ubangiji ya hana mata haihuwa.

7 Haka aka yi ta yi kowace shekara, duk lokacin da suka tafi domin yin sujada, sai Feninna ta tsokane ta. Don haka Hannatu ta yi ta kuka, ta ƙi cin abinci.

8 Elkana mijinta kuwa, ya ce mata, “Hannatu, me ya sa kike kuka? Me ya sa kike ƙin cin abinci? Me ya sa zuciyarki ta ɓaci? Ni ban fi ‘ya’ya maza goma a gare ki ba?”

Hannatu da Eli

9 Wata rana a Shilo bayan da sun gama cin abinci, sai Hannatu ta tashi. Eli, firist, kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar masujadar Ubangiji.

10 Hannatu tana fama da baƙin ciki ƙwarai, sai ta yi addu’a, tana kuka da ƙarfi ga Ubangiji.

11 Ta yi wa’adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”

12 Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa’ad da take yin addu’a.

13 Gama ta yi addu’ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓun motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne,

14 ya kuwa ce mata, “Sai yaushe za ki daina maye? Ki daina shan ruwan inabi.”

15 Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.

16 Kada ka zaci ni ‘yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”

17 Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra’ila ya amsa miki roƙonki.”

18 Ita kuma ta amsa, ta ce, “Bari baiwarka ta sami tagomashi a gare ka.” Sa’an nan ta tafi, ta ci abinci. Ba ta ƙara ɓata ranta ba.

Haihuwar Sama’ila da Miƙawarsa

19 Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa’an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.

20 Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama’ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.”

21 Elkana da iyalinsa duka suka tafi Shilo domin su miƙa wa Ubangiji hadaya ta shekara shekara, ya kuma cika wa’adinsa.

22 Amma Hannatu ba ta tafi ba, sai ta ce wa mijinta, “Da zarar an yaye yaron, zan kai shi domin ya zauna a gidan Ubangiji muddin ransa.”

23 Elkana ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi kyau, ki jira har ki yaye shi, Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Hannatu ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta.

24 Sa’ad da ta yaye yaron, sai ta ɗauke shi, ta kuma ɗauki bijimi bana uku, da mudun gari, da salkar ruwan inabi, ta kai shi ɗakin Ubangiji a Shilo, yaron kuwa yana ɗan ƙarami.

25 Sai suka yanka bijimin, suka kuma kai yaron wurin Eli.

26 Sa’an nan Hannatu ta ce, “Gafara dai, ba ka tuna da ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana roƙon Ubangiji.

27 Na roƙi Ubangiji wannan yaro, Ubangiji kuwa ya biya mini bukatata da na roƙa a gare shi.

28 Saboda haka nake miƙa shi ga Ubangiji muddin ransa. Ya zama na Ubangiji.”

A can ya yi wa Ubangiji sujada.

Categories
1 SAM

1 SAM 2

Waƙar Hannatu

1 Hannatu kuwa ta yi addu’a ta ce,

“Ubangiji ya cika zuciyata da murna.

Ina farin ciki da abin da ya yi.

Ina yi wa maƙiyana dariya,

Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni.

2 “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji,

Babu wani mai kama da shi,

Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu.

3 Kada ku ƙara yin magana ta girmankai,

Ku daina maganganunku na fariya,

Gama Ubangiji Allah shi ne masani,

Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi.

4 An kakkarya bakunan ƙarfafan sojoji,

Amma rarrauna ya zama mai ƙarfi.

5 Ƙosassun mutane suna ƙodago saboda abinci,

Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa.

Bakarariya ta haifi ‘ya’ya bakwai,

Wadda ta haifi ‘ya’ya da yawa kuwa

ta rasa su duka.

6 Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar,

Yana kai mutane kabari,

Ya kuma tā da su.

7 Yakan sa waɗansu mutane su zama

matalauta,

Waɗansu kuwa attajirai.

Yakan ƙasƙantar da waɗansu,

Ya kuma ɗaukaka waɗansu.

8 Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura,

Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki.

Ya sa su zama abokan ‘ya’yan sarki,

Ya ɗora su a wurare masu maƙami.

Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne,

A kansu ya kafa duniya.

9 “Zai kiyaye rayukan amintattun

mutanensa,

Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu,

Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.

10 Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji,

Zai yi musu tsawa daga Sama.

Ubangiji zai hukunta dukan duniya,

Zai ba sarkinsa iko,

Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama

mai nasara.”

11 Sa’an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.

‘Ya’yan Eli Maza

12 ‘Ya’yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba,

13 Ko ka’idodi game da abin da firistoci za su karɓa a hannun jama’a. A maimakon haka, lokacin da mutum ya je domin ya miƙa hadayarsa, sai baran firist ya zo da rino a hannunsa a sa’ad da ake dafa naman.

14 Sai ya caka rinon a cikin tukunyar, to, duk abin da ya cako wannan ya zama na firist. Haka suka yi ta yi wa dukan Isra’ilawa da suka zo miƙa hadaya a Shilo.

15 Tun kuma kafin a ƙona kitse, baran firist ɗin yakan zo ya ce wa wanda yake yin hadayar. “Ka ba ni wanda firist zai gasa, gama ba zai karɓi dafaffen nama daga gare ka ba, sai dai ɗanye.”

16 Idan mutumin ya ce, “To, bari a ƙona kitsen tukuna, sa’an nan ka ɗibi iyakar abin da kake bukata,” sai baran firist ɗin ya ce, “A’a, tilas ne ka ba ni yanzu, idan kuwa ba haka ba, zan ɗiba ƙarfi da yaji!”

17 Zunubin ‘ya’yan nan maza na Eli ya yi yawa a gaban Ubangiji, gama sun wulakanta hadayar Ubangiji ƙwarai da gaske.

Sama’ila a Shilo

18 Yaron nan Sama’ila yana ta aiki gaban Ubangiji, yana sāye da falmaran.

19 A kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka ‘yar rigar ado, ta kai masa a sa’ad da ita da mijinta sukan tafi miƙa hadayarsu ta shekara shekara.

20 Eli kuwa yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, ya ce, “Ubangiji ya ba ka waɗansu ‘ya’ya ta wurin matan nan a maimakon wanda kuka ba Ubangiji.”

Bayan wannan sai su koma gida.

21 Ubangiji ya sa wa Hannatu albarka, ta haifi ‘ya’ya maza uku da mata biyu. Yaron nan Sama’ila kuwa ya girma a gaban Ubangiji.

Eli da ‘Ya’yansa Maza

22 Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin dukan abin da ‘ya’yansa maza suke yi wa Isra’ilawa, da yadda suke kwana da matan da suke aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.

23 Sai ya ce musu, “Me ya sa kuke irin waɗannan abubuwa? Gama kowa yana faɗa mini irin mugayen abubuwan da kuke aikatawa.

24 Haba ‘ya’yana, ku bari! Jama’ar Ubangiji suna ta magana a kan wannan mugun abu.

25 Idan mutum ya yi wa wani laifi, Allah yakan kāre shi, amma idan mutum ya yi wa Ubangiji zunubi, wa zai kāre shi?”

Amma ba su ji maganar mahaifinsu ba, gama Ubangiji ya riga ya yi shirin kashe su.

Annabci a kan Gidan Eli

26 Yaron nan Sama’ila ya yi ta girma da samun tagomashi a gaban Ubangiji da kuma mutane.

27 Wani annabi ya zo wurin Eli da saƙo daga wurin Ubangiji ya ce, “Sa’ad da kakanka Haruna da iyalinsa suke bauta wa Fir’auna a Masar, na bayyana kaina gare shi.

28 Na zaɓi iyalinsa daga dukan kabilan Isra’ila domin su zama firistocina, su riƙa aiki a bagade, suna ƙona turare, su riƙa ɗaukar keɓaɓɓen akwatina cikin yi mini aiki. Na kuma yardar musu su sami rabonsu daga hadayun da aka ƙona a kan bagade.

29 Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama ‘ya’yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama’ata Isra’ila?

30 Ni Ubangiji Allah na Isra’ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.

31 Ga shi, lokaci yana zuwa da zan karkashe samari cikin iyalinka da danginka, har da ba za a sami wanda zai rayu har ya tsufa a gidanka ba.

32 Za ka kasance da damuwa da jin kishi, za ka duba dukan albarkun da zan sa wa Isra’ila, amma a gidanka ba za a taɓa samun wanda zai rayu har ya tsufa ba.

33 Zan dai bar ɗaya daga zuriyarka da rai, zai yi mini aikin firist, amma zai makance ya fid da zuciya ga kome. Dukan sauran zuriyarka kuwa za su yi mutuwa ƙarfi da yaji.

34 Lokacin da ‘ya’yanka biyu, Hofni da Finehas, za su mutu rana ɗaya wannan zai nuna maka abin da na faɗa sai ya cika.

35 Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da ko yaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.

36 Dukan wanda ya ragu daga zuriyarka zai je wurin sarki ya roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa ya taimaki firistoci da aiki domin ya sami abin da zai ci.”

Categories
1 SAM

1 SAM 3

Ubangiji Ya Kira Sama’ila

1 Yaron nan Sama’ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba.

2 Wata rana da dare Eli wanda ya kusa makancewa har ba ya iya gani sosai, yana kwance a masujada.

3 Fitilar Ubangiji kuwa tana ci. Sama’ila kuma yana kwance a masujada inda akwatin alkawarin Allah yake.

4 Ubangiji kuwa ya kira Sama’ila. Sama’ila ya ce, “Na’am.”

5 Ya sheƙa zuwa wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”

Amma Eli ya ce masa, “Ban kira ka ba, koma ka kwanta.” Sai Sama’ila ya koma ya kwanta.

6 Ubangiji ya sāke kiran Sama’ila. Sama’ila ya tashi ya tafi wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”

Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”

7 (Sama’ila dai bai san Ubangiji ba tukuna, gama Ubangiji bai riga ya fara magana da shi ba.)

8 Ubangiji kuma ya kira Sama’ila sau na uku. Sai kuma Sama’ila ya tashi ya nufi Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”

Sa’an nan Eli ya gane Ubangiji ne yake kiran yaron,

9 saboda haka Eli ya ce wa Sama’ila ya koma ya kwanta, idan an sāke kiransa sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.” Sama’ila kuwa ya koma ya kwanta.

10 Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama’ila! Sama’ila!”

Sama’ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.”

11 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Zan yi wa Isra’ilawa wani abu, duk wanda ya ji kuwa zai razana.

12 A ranar zan cika abin da na faɗa game da Eli da iyalinsa daga farko har zuwa ƙarshe.

13 Na fāɗa masa zan hukunta gidansa har abada saboda ‘ya’yansa sun faɗi mugayen maganganu a kaina. Eli kuwa ya sani, amma bai kwaɓe su ba.

14 Domin haka na faɗa da ƙarfi, cewa laifin gidan Eli ba za a yi kafararsa da sadaka, ko da hadaya ba har abada.”

15 Sama’ila ya kwanta har safiya, sa’an nan ya buɗe ƙofofi. Amma ya ji tsoron faɗa wa Eli wahayin.

16 Amma Eli ya kira shi, ya ce, “Ya ɗana, Sama’ila.”

Sama’ila ya ce, “Ga ni.”

17 Eli ya tambaye shi, ya ce, “Me Ubangiji ya faɗa maka? Kada ka ɓoye mini. Allah zai hukunta ka idan ka ɓoye mini abin da ya faɗa maka.”

18 Sama’ila kuwa ya faɗa masa kome da kome, bai ɓoye masa kome ba. Sai Eli ya ce, “Ai, Ubangiji ne, bari ya yi abin da ya yi masa daidai.”

19 Sama’ila fa ya yi girma, Ubangiji yana tare da shi. Dukan maganarsa kuwa Ubangiji yana cika ta.

20 Dukan mutanen Isra’ila fa daga wannan kusurwar ƙasa zuwa wancan, sun tabbata Sama’ila annabin Ubangiji ne.

21 Ubangiji kuma ya yi ta bayyana a Shilo inda ya bayyana kansa ga Sama’ila, ya kuma yi magana da shi. Duk lokacin da Sama’ila ya yi magana dukan mutanen Isra’ila suna kasa kunne.

Categories
1 SAM

1 SAM 4

Filistiyawa Sun Ƙwace Akwatin Alkawari

1 A wannan lokaci Isra’ilawa suka yi shiri su yi yaƙi da Filistiyawa, Isra’ilawa suka kafa sansaninsu a Ebenezer, Filistiyawa kuma suka kafa nasu a Afek.

2 Filistiyawa suka shirya su fara yaƙi. Bayan yaƙi mai zafi, sai Filistiyawa suka ci Isra’ilawa, suka kashe mutane wajen dubu huɗu (4,000) a bakin dāga.

3 Da sojojin da suka ragu suka koma sansani, sai shugabannin Isra’ila suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa Filistiyawa suka ci mu yau? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo ya kasance tare da mu, ya cece mu daga ikon abokan gābanmu.”

4 Sai suka aika zuwa Shilo aka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Mai Runduna, wanda yake zaune a tsakanin kerubobi. ‘Ya’yan nan na Eli, maza guda biyu, wato Hofni da Finehas, suna tare da akwatin alkawarin.

5 Da akwatin alkawarin Ubangiji ya iso sansanin, sai dukan mutanen Isra’ila suka yi sowa da ƙarfi, har ƙasa ta amsa.

6 Da Filistiyawa suka ji amon sowar suka ce, “Ina ma’anar irin wannan babbar sowa a sansanin Ibraniyawa?” Da suka gane akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga sansanin,

7 sai Filistiyawa suka tsorata, suka ce, “Allah ya shiga sansanin, kaitonmu, gama ba a taɓa yin irin wannan abu ba.

8 Mun shiga uku, wa zai cece mu daga hannun allolin nan masu iko? Waɗannan suka karkashe Masarawa a hamada!

9 Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”

10 Filistiyawa kuwa suka yi yaƙi gadan-gadan, suka ci mutanen Isra’ila. Mutanen Isra’ila suka gudu, kowa ya nufi gidansa. Aka kashe Isra’ilawa da yawa, wato mutum dubu talatin (30,000).

11 Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji, ‘ya’yan Eli guda biyu, Hofni da Finehas kuma, aka kashe su.

Mutuwar Eli

12 Wani mutumin kabilar Biliyaminu ya gudu daga dāgar yaƙin ya zo Shilo da tufafinsa ketattu ga kuma ƙura a kansa.

13 Sa’ad da ya iso, Eli yana zaune a kujerarsa a bakin hanya, yana jira, gama zuciyarsa ta damu saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shiga gari ya ba da labari, dukan garin ya ruɗe da kuka.

14 Sa’ad da Eli ya ji kukan, sai ya tambaya ya ce, “Me ake wa kuka?” Mutumin kuwa ya gaggauta zuwa wurin Eli ya faɗa masa.

15 (Eli yana da shekara tasa’in da takwas, ya kuwa makance ɗungum.)

16 Mutumin ya ce wa Eli, “Yau daga wurin yaƙin na tsere, na gudo gida.”

Eli ya ce, “Dana, me ya faru?”

17 Sai wanda ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, an kashe mutane da yawa, har ma da ‘ya’yanka biyu, Hofni da Finehas, sun rasu, an kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

18 Da aka ambaci akwatin alkawari, sai Eli ya tuntsura da baya daga inda yake zaune a bakin ƙofar gari, wuyansa kuwa ya karye, ya mutu, gama shi tsoho ne, mai ƙiba. Ya shekara arba’in yana shugabancin Isra’ila.

Mutuwar Matar Finehas

19 Surukar Eli, matar Finehas, tana da juna biyu, ta kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari an ƙwace akwatin alkawarin Allah, surukinta kuma da mijinta sun rasu, sai ta kama naƙuda farat ɗaya, ta haihu.

20 Tana bakin mutuwa, matan kuwa da take taimakonta suka ce mata, “Ki yi ƙarfin hali, gama kin haifi ɗa namiji.” Amma ba ta amsa ba, ba ta kuma kula ba.

21 Sai ta sa wa yaron suna Ikabod, wato ɗaukaka ta rabu da Isra’ila domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma surukinta da mijinta sun rasu.

22 Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

Categories
1 SAM

1 SAM 5

Akwatin Alkawarin Allah a wurin Filistiyawa

1 Sa’ad da Filistiyawa suka ƙwace akwatin alkawarin Allah a Ebenezer, suka kai shi Ashdod.

2 Suka shigar da shi cikin haikalin gunkinsu, Dagon, suka ajiye shi kusa da gunkin.

3 Kashegari da safe sa’ad da mutanen Ashdod suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Suka ta da shi, suka ajiye a wurinsa.

4 Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu.

5 (Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba su taka dokin ƙafar Dagon a Ashdod ba har wa yau.)

6 Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.

7 Da mutanen Ashdod suka ga yadda abin yake, sai suka ce, “Kada a bar akwatin alkawarin Allah na Isra’ila tare da mu, gama ya tsananta mana, mu da Dagon, allahnmu.”

8 Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila?”

Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can.

9 Amma da suka kai shi can sai Ubangiji ya hukunta birnin, ya gigita su, ya yi musu azaba da marurai, yara da manya.

10 Sai suka kai akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Amma da aka kai shi Ekron, sai mutanen Ekron suka fashe da kuka, suka ce, “Sun kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila don ya kashe dukanmu.”

11 Suka kuma aika a kirawo sarakunan Filistiyawa, suka ce, “Ku aika da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila zuwa inda ya fito don kada ya kashe mu duk da iyalinmu.” Dukan birnin ya gigita ƙwarai, gama Ubangiji yana hukunta su da tsanani.

12 Marurai sun fito wa mutanen da ba su mutu ba, mutane suka yi kuka domin allolinsu su cece su.

Categories
1 SAM

1 SAM 6

Filistiyawa Sun Komar da Akwatin Alkawari

1 Akwatin alkawarin Ubangiji ya yi wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.

2 Filistiyawa suka kirawo firistocinsu da bokayensu, suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku sanar da mu yadda za mu komar da shi inda ya fito.”

3 Sai firistocin da bokayen suka ce, “Idan za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila, dole ku aika da kyauta tare da shi domin zunubinku. Ba dama a komar da akwatin alkawarin hannu wofi. Ta haka za ku sami lafiya, za ku kuma san dalilin da ya sa ya yi ta hukunta ku.”

4 Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?”

Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.

5 Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye waɗanda suka lalatar da ƙasar, ku ba da girma ga Allah na Isra’ila, watakila zai ɗauke hukuncinsa a kanku, da allolinku, da ƙasarku.

6 Don me za ku taurare zukatanku kamar yadda Masarawa da Fir’auna suka taurare zukatansu? Sai da Allah ya wahalshe su tukuna kafin su sallami Isra’ilawa su tafi.

7 Yanzu kuwa ku yi sabon keken shanu, ku sami shanun tatsa biyu waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba, ku ɗaura wa shanun keken, amma ku tsare ‘yan maruƙansu a gida.

8 Sa’an nan ku sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken shanun, ku kuma sa siffofin maruran da na ɓerayen a cikin wani akwati ku ajiye a gefen akwatin alkawarin. Ku aika da waɗannan abubuwa tare da shi don yin hadaya ta laifi. Sa’an nan ku sa shi a hanya, a bar shi, ya tafi.

9 Ku zuba ido, ku gani, idan ya kama hanya zuwa Bet-shemesh, to, shi ne ya kawo mana wannan babbar masifa, amma idan ba haka ba, za mu sani ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”

10 Suka yi yadda aka faɗa musu, suka sami shanun tatsa biyu, suka ɗaura musu karkiyar keken. Suka tsare ‘yan maruƙansu a gida.

11 Suka sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken, da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran.

12 Shanun kuwa suka kama hanya sosai wadda ta nufi wajen Bet-shemesh, suna tafe, suna ta kuka, ba su kauce zuwa dama ko hagu ba, sarakunan Filistiyawa suna biye da su, har zuwa iyakar Bet-shemesh.

13 Mutanen Bet-shemesh kuwa suna cikin yankan alkamarsu a kwari. Da suka ɗaga kai sai suka ga akwatin alkawari, sai suka yi murna matuƙa.

14 Keken shanun kuwa ya shiga gonar Joshuwa mutumin Bet-shemesh, ya tsaya a wurin, kusa da wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun, suka yanka shanun suka ƙone su hadaya ga Ubangiji.

15 Lawiyawa kuwa suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji da akwatin da yake gefensa wanda aka sa siffofin zinariya a ciki. Suka ajiye su a kan babban dutsen. Mutanen Bet-shemesh kuwa suka miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu kuma a wannan rana.

16 Sarakunan nan biyar na Filistiyawa sun ga an yi wannan, sa’an nan suka koma Ekron a ran nan.

17 Waɗannan su ne siffofin marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin yin hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.

18 Suka kai siffofin ɓerayen nan na zinariya kuwa domin garuruwa biyar masu garu da ƙauyuka marasa garu na sarakunan Filistiyawa. Babban dutse inda suka ajiye akwatin Ubangiji yana nan har wa yau a saurar Joshuwa Bet-shemesh.

19 Sai Ubangiji ya kashe mutum saba’in daga cikin mutanen Bet-shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawari na Ubangiji. Mutanen kuwa suka yi makoki ƙwarai domin Ubangiji ya kashe mutane da yawa daga cikinsu.

Akwatin Alkawari a Kiriyat-yeyarim

20 Mutanen Bet-shemesh suka ce, “Wa ya isa ya tsaya a gaban Ubangiji, Allahn nan mai tsarki? A wurin wa zai tafi don ya rabu da mu?”

21 Sai suka aiki manzanni wurin mutanen Kiriyat-yeyarim, suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawari na Ubangiji, sai ku zo, ku ɗauka, ku tafi da shi.”

Categories
1 SAM

1 SAM 7

1 Mutanen Kiriyat-yeyarim kuwa suka zo suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji suka kai shi gidan Abinadab a bisa tudu. Suka keɓe ɗansa, Ele’azara, ya lura da akwatin alkawarin Ubangiji.

Sama’ila Ya Shugabanci Isra’ila

2 Akwatin alkawarin Ubangiji ya daɗe a Kiriyat-yeyarim, ya kai har shekara ashirin. A wannan lokaci kuwa dukan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

3 Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”

4 Isra’ilawa kuwa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot, suka bauta wa Ubangiji shi kaɗai.

5 Sama’ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.”

6 Isra’ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.

7 Da Filistiyawa suka ji Isra’ilawa sun taru a Mizfa, sai sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka tafi, su yi yaƙi da Isra’ilawa. Sa’ad da Isra’ilawa suka ji labari, sai suka tsorata,

8 suka ce wa Sama’ila, “Ka yi ta roƙo ga Ubangiji Allahnmu don ya cece mu daga hannun Filistiyawa.”

9 Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya kuma yi roƙo ga Ubangiji ya taimaki Isra’ilawa, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.

10 A sa’ad da Sama’ila yake miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso don su yi yaƙi da Isra’ilawa, sai Ubangiji ya buge wa Filistiyawa tsawa mai ƙarfi daga sama, suka kuwa ruɗe suka juya a guje.

11 Isra’ilawa suka fito daga Mizfa suka runtumi Filistiyawa, suka yi ta karkashe su har zuwa kwarin Bet-kar.

12 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa shi a tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer, wato “Har wa yau Ubangiji yana taimakonmu.”

13 Ta haka aka ci Filistiyawa. Daga nan ba su ƙara shiga yankin ƙasar Isra’ilawa ba, gama Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa a dukan zamanin Sama’ila.

14 Aka mayar wa Isra’ilawa garuruwan da Filistiyawa suka ƙwace musu, tun daga Ekron har zuwa Gat. Isra’ilawa kuma suka ƙwato dukan yankin ƙasarsu daga hannun Filistiyawa. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Ƙan’aniyawa.

15 Sama’ila kuwa ya yi mulkin Isra’ilawa dukan kwanakin ransa.

16 A kowace shekara yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa, inda yakan yi musu shari’a.

17 Sa’an nan kuma ya koma gidansa a Rama inda kuma yakan yi wa Isra’ilawa shari’a. Ya kuma gina wa Ubangiji bagade a can Rama.

Categories
1 SAM

1 SAM 8

Isra’ilawa Sun Roƙa A Naɗa musu Sarki

1 Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ‘ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.

2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abaija. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba.

3 Amma ‘ya’yansa ba su bi gurbin mahaifinsu ba, amma suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi, suka yi ta cin hanci, suka danne gaskiya.

4 Dukan shugabannin Isra’ila kuwa suka tattaru, suka tafi wurin Sama’ila a Rama,

5 suka ce masa, “Ga shi, ka tsufa, ga kuma ‘ya’yanka ba su bi gurbinka ba, yanzu dai sai ka naɗa mana sarki wanda zai yi mulkinmu kamar sauran ƙasashe.”

6 Amma Sama’ila bai ji daɗin roƙonsu ba, na a naɗa musu sarki, saboda haka ya yi addu’a ga Ubangiji.

7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sai ka kasa kunne ga dukan abin da suka faɗa maka, gama ba kai suka ƙi ba, amma ni suka ƙi da zama sarkinsu.

8 Irin abubuwan da suke yi maka, irinsu ne suka yi mini tun daga ranar da na fito da su daga Masar har wa yau, sun ƙi ni, suka yi ta bauta wa gumaka.

9 Yanzu dai sai ka saurari maganarsu kurum, amma ka faɗakar da su sosai da sosai, ka kuma nuna musu irin halin sarkin da zai sarauce su.”

10 Sama’ila kuwa ya faɗa wa mutanen da suke roƙo ya naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.

11 Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa ‘ya’yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman.

12 Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. ‘Ya’yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa.

13 Zai sa ‘ya’yanku mata yin aikin turare, da dafe-dafe, da toye-toye.

14 Zai ƙwace gonakinku mafi kyau, da gonakinku na inabi, da gonakinku na zaitun, ya ba fādawansa.

15 Zai kuma karɓi ushirin hatsinku da na inabinku ya ba shugabannin fādarsa da sauran fādawansa.

16 Zai ƙwace bayinku mata da maza, da mafi kyau na shanunku da jakunanku, domin su riƙa yi masa aiki.

17 Zai kuma karɓi ushirin dabbobinku. Za ku zama barorinsa.

18 A lokacin za ku yi kuka saboda sarkin da kuka zaɓar wa kanku, amma Ubangiji ba zai kasa kunne ga kukanku ba.”

19 Amma mutane suka ƙi jin abin da Sama’ila ya faɗa musu, sai suka ce, “Duk da haka dai, muna so sarki ya sarauce mu,

20 don mu ma mu zama kamar sauran ƙasashe, mu sami sarki wanda zai sarauce mu, ya shugabance mu zuwa yaƙe-yaƙe.”

21 Sa’ad da Sama’ila ya ji dukan abin da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.

22 Ubangiji kuwa ya ce wa Sama’ila, “Ka yarda da abin da suka ce, ka naɗa musu sarki.”

Sai Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa ya koma gida.”

Categories
1 SAM

1 SAM 9

Aka Zaɓi Saul Ya Zama Sarki

1 Akwai wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror, na iyalin Bekorat, dangin Afinya, shi attajiri ne.

2 Yana da wani ɗa, sunansa Saul, kyakkyawan saurayi ne. A cikin jama’ar Isra’ila ba wanda ya fi shi kyau, ya fi kowa tsayi a cikin Isra’ilawa duka.

3 Ana nan sai jakunan Kish, mahaifin Saul suka ɓace, Kish kuwa ya ce wa Saul, ɗansa, “Tashi, kai da ɗaya daga cikin barorin ku tafi, ku nemo jakunan.”

4 Suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, suka ratsa ta ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Suka kuma bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba. Sai suka bi ta ƙasar Biliyaminu, amma ba su same su ba.

5 Da suka kai ƙasar Zuf, sai Saul ya ce wa baransa da yake tare da shi, “Zo mu koma gida, kada babana ya bar damuwa a kan jakunan ya yi ta damuwa a kanmu.”

6 Amma baran ya ce masa, “Ai, akwai wani mutumin Allah a garin nan, ana kuwa ganin girmansa, domin duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa, watakila ya iya faɗa mana inda jakunanmu suke.”

7 Saul ya ce wa baransa, “Idan muka tafi, me za mu ba shi? Gama guzurin da yake tare da mu ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu ba shi.”

8 Baran kuma ya ce wa Saul, “Ina da ‘yar azurfa tsaba da zan ba shi domin ya faɗa mana inda za mu same su.”

9 (A dā a Isra’ila, idan wani yana so ya yi tambaya ga Allah, sai ya ce, “Zo, mu tafi wurin maigani.” Gama wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani.)

10 Sai Saul ya ce wa baransa, “Maganarka daidai ce, zo, mu tafi.” Suka kuwa tafi garin da mutumin Allah yake.

11 Sa’ad da suka haura zuwa garin, suka gamu da waɗansu ‘yan mata za su ɗebo ruwa, suka ce musu, “Maigani yana nan?”

12 ‘Yan matan suka amsa, suka ce, “I, yana nan, ai, ga shi nan ma a gabanku, ku hanzarta. Shigowarsa ke nan a garin, domin yau mutane za su ba da sadaka a bagade a kan tudu.

13 Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama’a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa’an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”

14 Suka kuwa haura zuwa cikin garin. Da shigarsu suka ga Sama’ila ya nufo wajen da suke, za shi wurin da ake yin sujadar.

15 Ana gobe Saul zai tafi wurin Sama’ila, Ubangiji ya bayyana wa Sama’ila.

16 Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama’ata Isra’ila. Zai ceci jama’ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama’ata suke sha, gama na ji kukansu.”

17 Da Sama’ila ya ga Saul, sai Ubangiji ya ce masa, “To, ga mutumin da na faɗa maka! Shi ne wanda zai sarauci jama’ata.”

18 Sa’an nan Saul ya tafi wurin Sama’ila a ƙofar gari, ya tambaye shi, “Ina gidan maigani?”

19 Sama’ila ya amsa ya ce, “Ni ne maiganin, wuce gaba, mu tafi wurin yin sujada a kan tudu, gama yau dukanku za ku ci abinci tare da ni. Gobe da safe zan amsa muku dukan tambayoyinku, sa’an nan in sallame ku.

20 A kan zancen jakunanku da suka ɓace yau kwana uku ke nan da suka wuce, kada ka damu, gama an same su. Banda wannan ma, ga wa Isra’ilawa duka suke sa zuciya? Ba kai ba ne da gidan mahaifinka?”

21 Saul ya ce, “Ni mutumin kabilar Biliyaminu ne, kabilar da ta fi ƙanƙanta a Isra’ila. Iyalina kuma su ne mafi ƙanƙanta a iyalan kabilar Biliyaminu. Me ya sa ka faɗa mini irin wannan magana?”

22 Sa’an nan Sama’ila ya shigar da Saul da baransa a babban ɗakin taruwa, ya sa su zauna gaba inda baƙi suke, wajen mutum talatin aka gayyata.

23 Sama’ila kuwa ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman nan da na ba ka, wanda na ce ka ajiye shi dabam.”

24 Sai mai dahuwa ya kawo cinya da gadon baya ya ajiye a gaban Saul. Sa’an nan Sama’ila ya ce, “Sai ka ci naman da aka ajiye a gabanka, gama dominka aka ajiye shi don ka ci a wannan lokaci tare da waɗanda na gayyata.”

A wannan rana kuwa Saul ya ci tare da Sama’ila.

25 Sa’ad da suka gangaro daga wurin yin sujadar zuwa cikin gari, sai aka shirya wa Saul gado a kan bene.

26 Ya kwanta, ya yi barci.

Sama’ila Ya Keɓe Saul Ya Zama Sarki

Da asuba, Sama’ila ya kira Saul ya ce, “Tashi, in sallame ka.” Saul kuwa ya tashi, shi da Sama’ila suka fita waje zuwa kan titi.

27 Sa’ad da suka kai bayan gari, sai Sama’ila ya ce wa Saul, “Ka sa baranka ya yi gaba, kai ka tsaya nan tukuna domin in faɗa maka abin da Allah ya ce.”

Categories
1 SAM

1 SAM 10

1 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki ‘yar kwalabar mai, ya zuba wa Saul a kā, ya yi masa sumba, ya ce, “Ubangjiji ne ya keɓe ka, ya naɗa ka sarki a kan jama’arsa.

2 Yau, sa’ad da ka rabu da ni, za ka gamu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a karkarar Biliyaminu a Zelza. Za su ce maka, jakunan da ka tafi nema an same su, yanzu mahaifinka ya daina damuwa saboda jakunan, sai a kanku, yana cewa, ‘Ina zan gane ɗana?’

3 Sa’ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da ‘yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.

4 Za su gaishe ka, su ba ka malmala biyu, kai kuwa sai ka karɓa.

5 Sa’ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa’ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa.

6 Sa’an nan Ruhun Ubangiji zai sauko maka, za ka kuwa yi rawa da sowa tare da su, za ka zama wani mutum dabam.

7 Sa’ad da waɗannan alamu suka cika, sai ka yi abin da hali ya nuna maka, gama Ubangiji yana tare da kai.

8 Za ka riga ni zuwa Gilgal inda zan zo in miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai, har in zo in sanar da kai abin da za ka yi.”

9 Da Saul ya juya zai tashi daga wurin Sama’ila, sai Ubangiji ya ba shi sabuwar zuciya. Alamun nan kuma suka cika a ranar.

10 Sa’ad da suka iso Gileyad, sai suka tarar da ƙungiyar annabawa. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga rawa da sowa tare da su.

11 Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi, suka gan shi yana yin wannan tare da annabawa, suka ce wa junansu, “Me ya faru da ɗan Kish? Saul kuma yana cikin annabawa ne?”

12 Sai wani mutumin da yake wurin ya ce, “Sauran fa, su ma, iyayensu annabawa ne?” Wannan kuwa ya zama karin magana, “Har Saul kuma yana cikin annabawa?”

13 Da ya gama rawa da sowa sai ya tafi wurin bagaden a kan tudu.

14 Kawun Saul kuwa ya tambaye shi, shi da baransa, “Ina ne kuka tafi?”

Saul ya ce, “Mun je neman jakuna, da ba mu same su ba, sai muka tafi wurin Sama’ila.”

15 Kawunsa kuma ya ce, “In ka yarda ka faɗa mini abin da Sama’ila ya faɗa maka.”

16 Saul kuwa ya ce wa kawunsa, “Ya faɗa mana a fili an gane jakunan.” Amma bai faɗa wa kawunsa zancen sarautar da Sama’ila ya faɗa masa ba.

An yi Na’am da Zaman Saul Sarki

17 Sama’ila kuwa ya tara mutanen Isra’ila a gaban Ubangiji a Mizfa.

18 Ya ce musu, “In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, ‘Ni na fito da Isra’ilawa daga Masar, na cece ku daga Masarawa da kuma daga hannun mulkokin da suka wahalshe ku.

19 Ni ne Allahnku wanda yake cetonku daga dukan masifu da wahalai, amma ga shi yau, kun ƙi ni kuna roƙona in ba ku sarki. To, da kyau, yanzu fa sai ku kusato gaban Ubangiji kabila kabila da iyali iyali.’ ”

20 Sa’an nan Sama’ila ya ce wa kabilan Isra’ila su guso, kuri’a kuwa ta faɗa a kan kabilar Biliyaminu.

21 Sai kuma ya sa kabilar Biliyaminu ta guso iyali iyali, kuri’a kuwa ta faɗa a kan iyalin Matri. Sa’an nan kuma ya guso da iyalin Matri mutum mutum, kuri’a ta faɗa a kan Saul, ɗan Kish. Amma sa’ad da suka neme shi, ba a same shi ba.

22 Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?”

Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”

23 Sai suka sheƙa, suka fito da shi daga wurin da ya ɓuya, ya tsaya cikin mutane, ya fi kowa tsayi da misalin ƙafa guda.

24 Sama’ila ya ce wa dukan jama’a, “Kun gan shi? Shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa, babu wani kamarsa a cikin dukan jama’a.”

Jama’a duka kuwa suka yi sowa suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”

25 Sa’an nan Sama’ila ya faɗa wa jama’a ka’idodin sarautar. Ya rubuta su cikin littafi, ya ajiye a wuri mai tsarki. Sa’an nan ya sallami jama’a duka kowa ya koma gidansa.

26 Saul kuma ya koma gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawa da Allah ya taɓa zuciyarsu.

27 Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.