Categories
1 SAR

1 SAR 1

Abishag ta Yi wa Dawuda Hidima

1 Sarki Dawuda ya tsufa ƙwarai, don haka ko an rufe shi da abin rufa ba ya jin ɗumi.

2 Saboda haka fādawansa suka ce masa, “Ranka ya daɗe bari mu nemo maka budurwa, wadda za ta zauna tare da kai, ta riƙa yin maka hidima, ta kwanta a ƙirjinka don ka riƙa jin ɗumi.”

3 Suka kuwa nemi kyakkyawar yarinya a dukan ƙasar Isra’ila. Sai suka sami Abishag a Shunem, suka kawo ta wurin sarki.

4 Ko da yake yarinyar kyakkyawa ce ƙwarai, ta zama mai lura da sarki, ta kuwa yi masa hidima, amma sarki bai yi jima’i da ita ba.

Adonija Ya Ci Sarauta

5 Adonija, dan da Haggit ta haifa wa Dawuda, ya ɗaukaka kansa cewa, “Zan zama sarki.” Ya kuwa shirya wa kansa karusai, da dakarai, da zagage hamsin a gabansa.

6 Tsohonsa bai taɓa tsawata masa ba. Shi kuma mutum ne kyakkyawa, an haife shi bayan Absalom.

7 Ya gama baki da Yowab ɗan Zeruya, da Abiyata, firist. Su kuwa suka yarda su goyi bayansa, su taimake shi.

8 Amma Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da annabi Natan, da Shimai, da Reyi, da masu tsaron lafiyar Dawuda, ba su goyi bayan Adonija ba.

9 Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan ‘yan’uwansa, ‘ya’yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza.

10 Amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benaiya, ko masu tsaron lafiyar sarki, ko Sulemanu ɗan’uwansa ba.

An Zaɓi Sulemanu Ya Zama Sarki

11 Natan kuwa ya ce wa Bat-sheba tsohuwar Sulemanu, “Ba ki ji cewa Adonija ɗan Haggit ya zama sarki ba? Sarki Dawuda kuma bai sani ba!

12 Yanzu sai ki zo in ba ki shawara domin ki tsira da ranki da na ɗanki Sulemanu.

13 Ki tafi wurin sarki Dawuda, ki ce masa, ‘Ran sarki ya daɗe, ashe, ba ka rantse mini ba cewa, Sulemanu ɗana zai yi mulki bayanka, shi ne kuma zai hau gadon sarautarka? Me ya sa Adonija ya zama sarki?’

14 Sa’ad da kike magana da sarki, ni ma zan shigo in tabbatar da maganarki.”

15 Bat-sheba kuwa ta tafi wurin sarki a ɗakinsa. Sarki dai ya tsufa ƙwarai, Abishag, yarinyar nan daga Shunem, tana yi masa hidima.

16 Bat-sheba ta rusuna, ta gai da sarki. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so?”

17 Ta ce masa, “Ranka ya daɗe, ka riga ka rantse mini da sunan Ubangiji Allahnka, ka ce, ‘Sulemanu ɗanki zai yi mulki bayana, shi ne zai hau gadon sarautata.’

18 To, ga shi Adonija ya zama sarki, ko da yake kai ba ka sani ba.

19 Ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan ‘ya’yan sarki, da Abiyata firist, da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Sulemanu ɗanka ba.

20 Ranka ya daɗe, yanzu idanun dukan jama’ar Isra’ila suna kallonka don su ga wanda za ka nuna musu ya gāji gadon sarauta a bayanka.

21 In ba haka ba, zai zama sa’ad da ka rasu za a ɗauka ni da ɗana, sulemanu, masu laifi ne.”

22 Tana cikin magana da sarki, sai annabi Natan ya zo.

23 Aka faɗa wa sarki cewa, ga annabi Natan. Da ya zo gaban sarki, sai ya rusuna ya gaishe shi.

24 Sa’an nan ya ce, “Ranka ya daɗe, ashe, ko ka sanar, cewa Adonija ne zai gaje ka?

25 Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan ‘ya’yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, ‘Ran sarki Adonija ya daɗe.’

26 Amma ni da Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da ɗanka Sulemanu, bai gayyace mu ba.

27 Ranka ya daɗe ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fādawanka, cewa ga wanda zai gāje ka ba?”

An Naɗa Sulemanu Sarki

28 Sai sarki Dawuda ya ce, “A kirawo mini Bat-sheba.” Ta kuwa zo gaban sarki.

29 Sa’an nan ya ce mata, “Na yi miki alkawari da Ubangiji mai rai wanda ya fanshe ni daga dukan wahala,

30 a yau ne kuma zan cika alkawarin da na yi miki da sunan Ubangiji Allah na Isra’ila, cewa Sulemanu, ɗanki, zai yi mulki a bayana, shi ne zai hau gadon sarautata ya gāje ni, haka kuwa zan yi yau.”

31 Bat-sheba kuwa ta rusuna har ƙasa, domin girmamawa, ta ce, “Ran ubangijina sarki ya daɗe har abada!”

32 Sarki Dawuda kuma ya ce, “Ku kirawo mini Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada.” Su kuwa suka zo gaban sarki,

33 ya ce musu, “Ku tafi tare da fādawana, ku sa Sulemanu, ɗana, ya hau alfadarina, ku kai shi Gihon,

34 a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra’ila, sa’an nan ku busa ƙaho, ku ce, ‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.’

35 Sa’an nan ku zo da shi ya hau gadon sarautata, gama shi ne zai zama sarki a maimakona. Na sa shi ya zama mai mulkin Isra’ila da Yahuza.”

36 Sai Benaiya ɗan Yehoyada ya ce wa sarki, “Za a yi haka, Ubangiji Allah na ubangijina, sarki, ya tabbatar da haka.

37 Kamar yadda Ubangiji ya kasance tare da ubangijina, sarki, haka kuma ya kasance tare da Sulemanu, ya fifita gadon sarautarsa fiye da na ubangijina, sarki Dawuda!”

38 Saboda haka sai Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki, suka tafi, suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki Dawuda. Suka kuma kai shi Gihon.

39 A can ne Zadok, firist, ya ɗauki ƙahon mai wanda ya kawo daga alfarwa ta sujada, ya zuba wa Sulemanu. Sa’an nan suka busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka ce, “Ran sarki Sulemanu ya daɗe.”

40 Mutane duka kuwa suka bi shi, suna bushe-bushe, suna murna da yawa, kamar ƙasa ta tsage saboda sowarsu.

41 Adonija da dukan baƙin da suke tare da shi suka ji amon sowa bayan da suka gama cin abinci. Da Yowab ya ji busar ƙaho, sai ya ce, “Mene ne dalilin wannan hargitsi a birni?”

42 Yana cikin magana ke nan sai ga Jonatan ɗan Abiyata, firist, ya zo. Adonija ya ce musu, “Shigo, gama kai nagarin mutum ne, ka kawo albishir.”

43 Jonatan kuwa ya ce wa Adonija, “A’a, gama ubangijinmu, sarki Dawuda, ya naɗa Sulemanu sarki.

44 Sarki ya aiki Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki. Su kuwa suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki.

45 Zadok firist, da annabi Natan kuma suka zuba masa mai a Gihon don ya zama sarki. Daga can suka tashi da murna don haka ake hayaniya a birnin. Wannan ita ce hayaniyar da kake ji.

46 Sulemanu ne sarki yanzu.

47 Banda wannan kuma, fādawa sun tafi su kai caffa ga sarki Dawuda, suna cewa, ‘Allahnka ya sa Sulemanu ya yi suna fiye da kai, ya kuma fīfita gadon sarautarsa fiye da naka.’ Sai sarki ya sunkuyar da kansa a gadonsa.

48 Sa’an nan ya ce, ‘Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra’ila wanda ya sa ɗaya daga cikin zuriyata ya hau gadon sarautata yau, idona kuwa ya gani.’ ”

49 Sai baƙin Adonija duka suka tashi suna rawar jiki, kowa ya kama hanyarsa.

50 Adonija kuwa ya ji tsoron Sulemanu, sai ya tashi, ya tafi, ya kama zankayen bagade.

51 Aka faɗa wa Sulemanu cewa ga Adonija yana jin tsoron sarki Sulemanu, gama, ga shi, ya kama zankayen bagade, yana cewa, “Bari sarki Sulemanu ya rantse mini tukuna, cewa ba zai kashe ni ba.”

52 Sulemanu kuwa ya ce, “Idan ya nuna kansa nagarin mutum ne, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba, amma idan aka iske shi da mugunta, to, lalle kashe shi za a yi.”

53 Sarki Sulemanu kuwa ya aika aka kawo shi daga bagaden. Da ya zo, sai ya rusuna, ya gai da sarki Sulemanu. Sulemanu ya ce masa, “Tafi gidanka.”

Categories
1 SAR

1 SAR 2

Gargaɗin da Dawuda Ya Yi wa Sulemanu

1 Sa’ad da lokacin rasuwar Dawuda ya gabato, sai ya yi wa ɗansa Sulemanu gargaɗi na ƙarshe, ya ce,

2 “Ina gab da rasuwa yanzu. Saboda haka, ka ƙarfafa, ka yi jaruntaka.

3 Ka yi abin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka. Ka yi biyayya da dokokinsa, da umarnansa, kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, domin ka yi nasara da dukan abin da kake yi da inda ka nufa duka,

4 domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan ‘ya’yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba.’

5 “Ka kuma san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi mini, yadda ya kashe shugabannin sojoji na Isra’ila su biyu, wato Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya zubar da jinin yaƙi a lokacin salama. Ya sa jinin yaƙi a kan ɗamararsa wadda take gindinsa, da kuma kan takalmansa da yake ƙafafunsa.

6 Ka san abin da za ka yi, kada ka bar shi ya mutu ta hanyar lafiya.

7 “Amma ka nuna alheri ga ‘ya’yan Barzillai daga Gileyad, ka lura da su da kyau, gama sun nuna mini alheri sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka, Absalom.

8 “Ga kuma Shimai ɗan Gera, daga garin Bahurim ta Biliyaminu. Shi ne ya yi mini mugun zagi sa’ad da na tafi Mahanayim, amma sa’ad da ya zo taryata a Urdun, sai na rantse masa da Ubangiji, na ce ba zan kashe shi ba.

9 Don haka dole ka hukunta shim, ka dai san abin da za ka yi da shi, lalle ne kuma za ka ga an kashe shi.”

Rasuwar Dawuda

10 Sa’an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.

11 Ya yi shekara arba’in yana sarautar Isra’ila. Ya yi mulki shekara bakwai a Hebron, sa’an nan ya yi shekara talatin da uku yana mulki a Urushalima.

12 Sulemanu kuwa ya hau gadon sarautar ubansa, Dawuda. Mulkinsa kuma ya kahu sosai.

Mutuwar Adonija

13 Sa’an nan Adonija ɗan Haggit ya tafi wurin Bat-sheba, tsohuwar Sulemanu. Ta ce masa, “Ka zo lafiya?”

Ya ce, “Lafiya lau.”

14 Sa’an nan ya ce, “Ina da wani abin da zan faɗa miki.”

Ta ce, “To, sai ka faɗa.”

15 Ya amsa ya ce, “Kin sani dai sarauta tawa ce. Ni ne kuwa mutanen Isra’ila duka suka sa zuciya zan ci sarautar, amma al’amarin ya sāke, sai sarautar ta zama ta ƙanena , gama tasa ce bisa ga nufin Allah.

16 Yanzu dai ina da roƙo guda zuwa gare ki, kada ki hana mini.”

17 Ta ce masa, “To, sai ka faɗa.”

Sai ya ce, “In kin yarda ki yi magana da sarki Sulemanu, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce ya ba ni yarinyar nan, Abishag, daga Shunem, ta zama matata.”

18 Bat-sheba kuwa ta ce, “Da kyau, zan yi wa sarki magana dominka.”

19 Sa’an nan Bat-sheba ta tafi wurin sarki Sulemanu don ta yi magana da shi a kan Adonija. Sarki ya tashi domin ya tarye ta. Ya rusuna mata, sa’an nan ya zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo mata kujera, ta kuwa zauna a wajen damansa.

20 Sai ta ce, “Ina da wani ɗan roƙo a gare ka, kada ka hana mini shi.”

Sarki ya ce mata, “Ya tsohuwata, sai ki faɗi abin da kike so, gama ba zan hana miki ba.”

21 Ta ce, “Bari a ba Adonija, ɗan’uwanka, Abishag daga Shunem, ta zama matarsa.”

22 Sai sarki Sulemanu ya amsa wa tsohuwarsa, ya ce, “Don me kika roƙar wa Adonija Abishag? Ki roƙar masa sarautar mana, gama shi wana ne, Abiyata, firist kuma, da Yowab ɗan Zeruya suna goyon bayansa.”

23 Sai sarki Sulemanu ya rantse da Ubangiji ya ce, “Allah ya kashe ni nan take idan ban sa Adonija ya biya wannan roƙo da ransa ba.

24 Ubangiji ya kafa ni sosai a gadon sarautar tsohona, Dawuda, ya kuma cika alkawarinsa, ya ba ni mulki da zuriyata. Na rantse za a kashe Adonija yau.”

25 Sai Sarki Sulemanu ya aiki Benaiya ɗan Yehoyada, ya kashe Adonija.

An Kori Abiyata an Kashe Yowab

26 Sarki kuma ya ce wa Abiyata, firist, “Ka koma ƙasarka ta gādo a Anatot, gama ka cancanci mutuwa, amma yanzu ba zan kashe ka ba domin ka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji Allah a gaban Dawuda, tsohona, domin kuma ka sha wahala duka tare da tsohona.”

27 Saboda haka Sulemanu ya kori Abiyata daga aikin firist na Ubangiji, ta haka aka cika maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Eli a Shilo.

28 Da Yowab ya ji labari, gama har shi ya goyi bayan Adonija, ko da yake bai goyi bayan Absalom ba, sai ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ya kama zankayen bagade.

29 Sa’ad da aka faɗa wa sarki Sulemanu, Yowab ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ga shi, yana wajen bagade, sai Sulemanu ya aiki Benaiya, ɗan Yehoyada, ya je ya kashe shi.

30 Benaiya kuwa ya tafi alfarwa ta Ubangiji, ya ce masa, “Sarki ya ce ka fito.”

Amma Yowab ya ce, “A’a, a nan zan mutu.”

Benaiya kuma ya je ya faɗa wa sarki abin da Yowab ya ce.

31 Sarki kuwa ya ce masa, “Ka yi yadda ya ce, ka kashe shi, ka binne shi, ta haka za ka kawar mana da hakkin jinin da Yowab ya zubar ba dalili.

32 Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.

33 Don haka alhakin jininsu zai koma a kan zuriyar Yowab har abada, amma da Dawuda da zuriyarsa, da gidansa, da gadon sarautarsa, albarkar Ubangiji za ta zauna a kansu har abada.”

34 Benaiya ɗan Yehoyada kuwa ya shiga alfarwar ya kashe shi. Aka binne shi a gidansa a karkara.

35 Sa’an nan sarki ya naɗa Benaiya ɗan Yehoyada, shugaban sojoji a maimakon Yowab, ya kuma naɗa Zadok, firist, a maimakon Abiyata.

Mutuwar Shimai

36 Sai kuma sarki ya aika a kirawo Shimai. Sa’an nan ya ce masa, “Ka gina wa kanka gida a Urushalima, ka zauna a nan, kada ka fita ko kaɗan zuwa wani wuri.

37 Gama ran da ka fita, ka haye rafin Kidron, ka tabbata fa za ka mutu, alhakin jininka kuwa zai koma kanka.”

38 Shimai kuwa ya ce wa sarki, “Abin da ka faɗa daidai ne, abin da ka ce in yi, zan yi, ranka ya daɗe.” Sai Shimai ya zauna a Urushalima kwanaki da yawa.

39 Amma bayan shekara uku, sai biyu daga cikin bayin Shimai suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, Sarkin Gat. Da aka faɗa wa Shimai, cewa bayinsa suna a Gat,

40 sai ya tashi, ya yi wa jakinsa shimfiɗa, ya tafi Gat wurin Akish don neman bayinsa. Ya kuwa komo da bayinsa daga Gat.

41 Da aka faɗa wa Sulemanu, cewa Shimai ya fita Urushalima, ya tafi Gat, ya komo

42 sai ya aika a kirawo Shimai, ya ce masa, “Ashe, ban sa ka ka rantse da Ubangiji ba, na kuma dokace ka da ƙarfi, cewa ka tabbata ran da ka fita zuwa ko’ina za ka mutu? Kai kuma ka ce mini, ‘Abin da ka ce daidai ne, zan yi biyayya.’

43 To, me ya sa ka karya rantsuwar da ka yi da sunan Ubangiji, da kuma umarnin da na umarce ka?”

44 Sarki kuma ya ce masa, “Ka sani sarai irin duk muguntar da ka yi wa tsohona, Dawuda. Haka kuma Ubangiji zai sāka maka bisa ga muguntarka.

45 Amma Ubangiji zai sa mini albarka, ya kuma tabbatar da gadon sarautar Dawuda har abada.”

46 Sa’an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.

Categories
1 SAR

1 SAR 3

Sulemanu ya Auri ‘Yar Fir’auna

1 Sulemanu ya gama kai da Fir’auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri ‘yar Fir’auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.

2 Mutane suka yi ta miƙa hadayu a al’amudai dabam dabam, domin ba a gina haikalin Ubangiji ba tukuna.

3 Sulemanu ya ƙaunaci Ubangiji, ya yi tafiya bisa ga koyarwar tsohonsa, Dawuda, amma ya miƙa sadakoki da hadayu da yawa a al’amudai dabam dabam.

Addu’ar Sulemanu don Samun Hikima

4 Sarki kuwa ya tafi Gibeyon don ya miƙa hadaya, gama a can ne akwai babban al’amudi. Ya miƙa hadayu na ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.

5 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

6 Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona,domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali’u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.

7 Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.

8 Ga ni kuwa a tsakiyar jama’arka wadda ka zaɓa, jama’a mai yawa wadda ba ta ƙidayuwa saboda yawansu.

9 Domin haka ka ba ni hikima ta yi wa jama’arka shari’a, domin in rarrabe tsakanin nagarta da mugunta, gama wane ni in iya mallakar jama’arka mai yawa haka?”

10 Ubangiji kuwa ya ji daɗin abin da Sulemanu ya roƙa.

11 Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama’a,

12 to, zan yi maka yadda ka roƙa, zan ba ka zuciya ta hikima da ganewa har ba wanda ya kai kamarka, ba kuwa wanda zai kai kamarka.

13 Na kuma ba ka abin da ba ka roƙa ba, wato wadata da girma. Domin haka a zamaninka ba za a sami wani sarki kamarka ba.

14 Idan za ka yi mini biyayya ka kuma kiyaye dokokina, da umarnaina kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, to, zan ba ka tsawon rai.”

15 Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa’an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.

Sulemanu Ya Shara’anta Mawuyaciyar Matsala

16 Wata rana waɗansu mata masu zaman kansu, su biyu, suka zo gaban sarki.

17 Sai ɗayar ta ce, “Ran sarki ya daɗe, ni da wannan mata a gida ɗaya muke zaune, sai na haifi ɗa namiji, ita kuwa tana nan a gidan.

18 Bayan kwana uku da haihuwata, ita ma sai ta haihu. Mu kaɗai ne, ba kowa tare da mu a gidan.

19 Ana nan sai ɗan wannan mata ya mutu da dare, domin ta kwanta a kansa.

20 Da tsakar daren sai ta tashi, ta ɗauke ɗana daga wurina, sa’ad da nake barci, ta kai shi gadonta, sa’an nan ta kwantar da mataccen ɗanta a wurina.

21 Sa’ad da na tashi da safe don in ba ɗana mama, sai ga shi, matacce. Da na duba sosai, sai na ga ba nawa ba ne, wanda na haifa.”

22 Amma ɗaya matar ta ce, “A’a, mai ran shi ne nawa, mataccen kuwa shi ne naki!”

Sai ta fari ta ce, “A’a, mataccen shi ne naki, mai rai ne nawa!”

Haka suka yi ta gardama a gaban sarki.

23 Sa’an nan sarki ya ce, “To, kowaccenku ta ce mai ran shi ne nata, mataccen kuwa shi ne na waccan.”

24 Sai ya umarta a kawo takobi. Da aka kawo takobin,

25 sai ya ce, “A raba ɗan nan mai rai kashi biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”

26 Saboda zuciyar mahaifiyar ta ainihi ta cika da juyayin ɗanta, ta ce wa sarki, “Ranka ya daɗe kada a kashe yaron! A ba ta!”

Amma ɗayar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu, a ci gaba a raba shi.”

27 Sa’an nan Sulemanu ya ce, “Kada ku kashe yaron! Ku miƙa wa ta farin, ita ce mahaifiyarsa ta ainihi.”

28 Sa’ad da dukan mutanen Isra’ila suka ji shari’ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.

Categories
1 SAR

1 SAR 4

Fādawan Sulemanu

1 Sarki Sulemanu shi ne sarkin dukan Isra’ila,

2-6 waɗannan kuma su ne manyan fādawansa,

Azariya ɗan Zadok shi ne firist.

Elihoref da Ahija ‘ya’yan Seraiya,

maza, su ne magatakarda.

Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne mai

lura da takardu.

Benaiya ɗan Yehoyada shi ne

shugaban sojoji.

Zadok da Abiyata su ne firistoci.

Azariya ɗan Natan shi ne shugaban

hakimai.

Zabud ɗan Natan shi ne mashawarcin

sarki da abokinsa.

Ahishar shi ne mai lura da bayin fāda.

Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura

da aikin gandu.

7 Sulemanu kuma ya naɗa mutum goma sha biyu a lardunan Isra’ila. Su ne za su tanaji abinci daga lardunansu domin sarki da iyalinsa. Kowane hakimi yakan kawo abinci wata guda a shekara.

8-19 Waɗannan su ne hakimai, da kuma lardunan da suke aiki.

Ben-hur yana a ƙasar tudu ta Ifraimu.

Ben-deker shi ne mai lura da biranen

Makaz, da Shalim, da Bet-shemesh,

da Elon-bet-hanan.

Ben-hesed shi ne mai lura da Arubot,

da Soko, da dukan ƙasar Hefer.

Ben-abinadab shi ne mai lura da

dukan jihar Dor, ya auri Tafat

‘yar Sulemanu.

Ba’ana ɗan Ahilud shi ne mai lura da

biranen Ta’anak da Magiddo, da

dukan jihar Bet-sheyan, kusa da

garin Zaretan, kudu da garin

Yezreyel, har zuwa birnin Abel

mehola da birnin Yokmeyam.

Ben-geber shi ne mai fura da birnin

Ramot-gileyad, da ƙauyukan

Yayir da Manassa, waɗanda suke a

Gileyad, da kuma yankin Argob,

wanda yake a Bashan, duka dai

akwai manyan garuruwa sittin

masu garu da ƙyamare na tagulla.

Abinadab ɗan Iddo shi ne mai lura

da birnin Mahanayim.

Ahimawaz shi ne mai lura da Naftali,

ya auri Basemat ‘yar Sulemanu.

Ba’ana ɗan Hushai shi ne mai lura

da Ashiru da garin Beyalot.

Jehoshafat ɗan Faruwa shi ne mai

lura da Issaka.

Shimai ɗan Ila shi ne mai lura da

ƙasar Biliyaminu.

Geber ɗan Uri shi ne mai lura da

jihar Gileyad wadda Sihon Sarkin

Amoriyawa, da Og Sarkin Bashan,

suka mallaka.

Bayan waɗannan sha biyu akwai hakimi ɗaya da yake kan ƙasar Yahuza.

Hikimar Sulemanu da Wadatarsa

20 Mutanen Yahuza da na Isra’ila suka yi yawa kamar yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka yi murna.

21 Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.

22 Abincin gidan Sulemanu na rana ɗaya garwa talatin na lallausan gari ne, da garwa sittin na gari,

23 da turkakkun bijimai goma, da shanu ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari banda kishimai, da bareyi, da batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.

24 Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da yake yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko’ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta.

25 Mutanen Yahuza da na Isra’ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.

26 Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba’in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000).

27 Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waɗanda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba.

28 Suka kuma kawo sha’ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.

29 Allah ya ba Sulemanu hikima, da fahimi, da sani, har ba su misaltuwa.

30 Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar.

31 Gama ya fi dukan mutane hikima, ya fi Etan Ba’ezrahe, da Heman, da Kalkol, da Darda, ‘ya’yan Mahol. Ya shahara a ƙasashen da suke kewaye da shi.

32 Ya yi karin magana dubu uku, ya kuma yi waƙoƙi fiye da dubu.

33 Ya yi magana a kan itatuwa da tsire-tsire tun daga itacen al’ul da yake a Lebanon har zuwa ɗaɗɗoya da take tsirowa a jikin bango. Ya kuma yi magana a kan dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kifaye.

34 Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.

Categories
1 SAR

1 SAR 5

Yarjejeniya Tsakanin Sulemanu da Hiram

1 Hiram, Sarkin Taya, ya aiki jakadunsa zuwa wurin Sulemanu, sa’ad da ya ji ya gāji tsohonsa, gama Hiram abokin Dawuda ne ƙwarai dukan kwanakinsa.

2 Sai Sulemanu ya aika wurin Hiram, ya ce,

3 “Ka sani tsohona, Dawuda, bai iya gina Haikalin yin sujada ga Ubangiji Allahnsa ba saboda fama da yaƙe-yaƙe da maƙiyan da suke kewaye da shi, kafin Ubangiji ya mallakar masa da su.

4 Amma yanzu Ubangiji Allahna ya hutasshe ni ta kowace fuska, ba fitina ko masifa.

5 Ubangiji kuma ya yi wa tsohona Dawuda alkawari ya ce, ‘Ɗanka, wanda zai gāje ka, shi zai gina mini Haikali.’ Yanzu kuwa na yi niyyar gina wannan haikali domin sujada ga Ubangiji Allahna.

6 Saboda haka sai ka sa a saro mini itatuwan al’ul na Lebanon. Barorina za su haɗu da barorinka, ni kuwa zan biya ka aikin da barorinka za su yi bisa ga yadda ka ce, gama ka sani ba wani daga cikin mutanena da ya iya saran katako kamar mutanenka.”

7 Da Hiram ya ji maganar Sulemanu, sai ya yi murna ƙwarai, ya ce, “Yabo ga Ubangiji saboda wannan rana, gama ya ba Dawuda ɗa mai hikima da zai shugabanci wannan babbar jama’a.”

8 Sa’an nan Hiram ya aika wurin Sulemanu, ya ce, “Na ji saƙonka da ka aiko mini, a shirye nake in yi maka dukan abin da kake bukata a kan katakan itacen al’ul, da na fir.

9 Barorina za su kawo su daga Lebanon zuwa teku. Zan sa a yi gadon fito da su, su bi teku zuwa inda kake so, a can mutanena za su warware su, sa’an nan naka mutane su kwashe su. Kai kuma ka ba da abinci ga mutanena.”

10 Sai Hiram ya ba Sulemanu dukan katakan itacen al’ul da na fir da yake bukata,

11 Sulemanu kuwa yakan ba Hiram alkama mudu dubu ashirin (20,000), da tattaccen man zaitun ma’auni dubu ashirin (20,000) kowace shekara domin ya ciyar da mutanensa.

12 Ubangiji kuwa ya ba Sulemanu hikima kamar yadda ya yi masa alkawari. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Hiram da Sulemanu, suka kuma ƙulla yarjejeniya da juna.

13 Sarki Sulemanu kuwa ya sa a yi aikin tilas daga cikin Isra’ila duka. Waɗanda aka samu da za su yi aikin tilas ɗin mutum dubu talatin (30,000) ne.

14 Ya riƙa aikawa da su zuwa Lebanon, ya raba su mutum dubu goma goma (10,000) su yi wata ɗaya ɗaya, sa’an nan su komo gida su yi wata biyu biyu. Adoniram shi ne shugaban aikin tilas ɗin.

15 Sulemanu kuma yana da mutum dubu saba’in (70,000) a ƙasar tuddai masu haƙar duwatsu, da dubu tamanin (80,000) masu ɗauko duwatsun.

16 Banda waɗannan kuma, Sulemanu ya sa shugabanni dubu uku da ɗari uku (3,300) waɗanda suke lura da aikin, da mutanen da suke yin aikin.

17 Bisa ga umarnin sarki Sulemanu suka sassaƙa manyan duwatsu kyawawa don kafa harsashin ginin Haikali.

18 Sai maginan Sulemanu, da na Hiram, da mutanen Gebal suka shirya duwatsu da katakai da za a gina Haikalin.

Categories
1 SAR

1 SAR 6

Sulemanu Ya Gina Haikalin Ubangiji

1 A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra’ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.

2 Haikalin da sarki Sulemanu ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kamu talatin ne.

3 Tsawon shirayin da yake a gaban Haikalin kamu ashirin ne, wato daidai da fāɗin Haikalin. Fāɗinsa kuma daga gaban Haikalin kamu goma ne.

4 Ya yi wa Haikalin tagogi, suna da fāɗi daga ciki fiye da waje.

5 Ya kuma gina bene mai ɗakuna a jikin bangon Haikalin daga gefe, da kuma bayan Haikalin, har hawa uku, kowanne kamu bakwai da rabi.

6 Fāɗin ɗakuna na ƙasa kamu biyar ne. Fāɗin ɗakunan hawa na biyu kamu shida ne. Fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa kamu bakwai ne. Bangaye a ƙasa sun fi na saman kauri, don ɗakunan su zauna sosai, ba tare da an kafa ginshiƙai a cikin ɗakunan ba.

7 An gina Haikalin da duwatsun da aka sassaka tun daga can wurin da aka haƙo su, don haka ba a ji amon guduma, ko na gatari, ko na wani kayan aiki irin na ƙarfe ba, sa’ad da ake ginin Haikalin.

8 Ƙofar domin ɗakuna na ƙasa tana wajen dama na Haikalin. Akwai matakai zuwa hawa na tsakiya da zuwa bene na uku.

9 Ta haka ya gina Haikalin, ya rufe shi da katakan itacen al’ul.

10 Benayen da ya gina kewaye da Haikalin, kowane bene tsayinsa kamu biyar. An haɗa su da Haikalin da katakan itacen al’ul.

11 Ubangiji ya ce wa Sulemanu,

12 “Idan ka yi biyayya da dokokina da umarnaina, to, zan cika maka alkawarin da na yi wa tsohonka Dawuda.

13 Zan zauna tare da mutanena, wato Isra’ila, a wannan Haikali da kake ginawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”

14 Haka fa Sulemanu ya gama gina Haikali.

Kayan Haikali

15 Ya yi bango na ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har sama, ya kuma rufe daɓen da itacen fir.

16 Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi can ƙuryar Haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne , an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har sama.

17 Tsawon sauran Wuri Mafi Tsarki kuwa kamu arba’in ne.

18 Katakan itacen al’ul na cikin Haikalin, an yi musu zāne mai fasalin gora da na furanni buɗaɗɗu. An rufe bangon daga ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.

19 Ya shirya Wuri Mafi Tsarki na can cikin Haikalin domin a ajiye akwatin alkawari na Ubangiji.

20 Tsawon Wuri Mafi Tsarki na can ciki kamu ashirin ne, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu ashirin. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa. Ya kuma yi bagadensa da itacen al’ul.

21 Sulemanu ya dalaye cikin Haikalin da zinariya tsantsa. Ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki, sa’an nan ya dalaye su da zinariya.

22 Ya dalaye dukan cikin Haikalin da zinariya, ya kuma dalaye bagaden da yake Wuri Mafi Tsarki na can ciki, da zinariya.

23 Ya yi kerubobi guda biyu da itacen zaitun, ya sa su cikin Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.

24-25 Dukan kerubobin irinsu ɗaya girmansu kuma ɗaya. Tsawon kowane fiffike na kerub ɗin kamu biyar, wato tsawon daga ƙarshen wannan fiffike zuwa ƙarshen wancan fiffike kamu goma ne.

26 Tsayin kowane kerub kamu goma ne.

27 Ya sa kerubobin daura da juna a can cikin Haikali domin fikafikan su taɓi juna a tsakiya kowane ɗayan kuma ya taɓi bango.

28 Ya dalaye kerubobin da zinariya.

29 Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.

30 Har daɓen ƙasa, ya dalaye shi da zinariya.

31 Ya yi ƙofa biyu na shiga Wuri Mafi Tsarki na can ciki da itacen zaitun. A saman ƙofar ya yi baka.

32 Sai ya zazzāna siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a kan ƙofofi duka biyu, sa’an nan ya dalaye duk ƙofofin da zinariya.

33 Ya yi wa Haikalin madogaran ƙofa masu ƙusurwa huɗu da itacen zaitun.

34 Ya kuma yi ƙyamare biyu a haɗe, ya yi su da itacen fir,

35 ya zazzāna ya adanta su da siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni. Sa’an nan ya dalaye su da zinariya bai ɗaya.

36 Ya gina shirayi na ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.

37 A shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu aka kafa harsashin ginin Haikalin Ubangiji a watan biyu, wato watan Zib.

38 A shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Sulemanu a watan Bul, wato watan takwas, aka gama ginin Haikalin, daidai yadda aka zayyana fasalinsa. Sulemanu ya yi shekara bakwai yana ginin Haikalin.

Categories
1 SAR

1 SAR 7

Fādar Sulemanu

1 Sulemanu ya yi shekara goma sha uku yana gina gidansa kafin ya gama shi duka.

2 Ya kuma gina wani ɗaki da katakai daga kurmin Lebanon, tsawonsa kamu ɗari, faɗinsa kuma kamu hamsin, tsayinsa kuwa kamu talatin, a bisa jeri huɗu na ginshiƙan itacen al’ul. Aka shimfiɗa katakan itacen al’ul a bisa ginshiƙan.

3 Aka rufe shi da katakan al’ul a bisa ɗakuna arba’in da biyar da suke gefe, waɗanda suke bisa ginshiƙai. Ɗakuna goma sha biyar a kowane jeri har jeri uku.

4 Aka kuma yi tagogi masu sandunan ƙarfe, jeri uku, kowace taga tana daura da ‘yar’uwarta, har jeri uku.

5 Dukan ƙofofin da madogaransu murabba’i ne, taga kuma tana daura da ‘yar’uwarta har jeri uku.

6 Ya yi babban shirayi mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, faɗinsa kamu talatin. Akwai kuma wani shirayi mai ginshiƙai a gabansa.

7 Ya kuma gina shirayi ta sarauta inda zai riƙa yin shari’a, ya rufe dukan daɓenta da itacen al’ul.

8 Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, ‘yar Fir’auna, gida irin wannan.

9 Aikin gine-ginen nan, an yi shi da duwatsu masu tamani tun daga tushen har zuwa rufin. Sai da aka auna duwatsun sa’an nan aka yanka su da zarto, ciki da baya daidai da juna.

10 An kafa harsashin ginin da manyan duwatsu masu tsada, waɗansu kamu takwas waɗansu goma.

11 Daga sama kuma akwai duwatsu masu tsada waɗanda aka yanka su bisa ga ma’auni, da kuma itacen al’ul.

12 Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al’ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.

Aikin Huram

13 Sarki Sulemanu kuwa ya aika a kawo Huram daga Taya, gwanin aikin tagulla ne.

14 Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.

15 Ya kuwa yi ginshiƙi biyu na zubi da tagulla. Kowane ginshiƙi tsayinsa kamu goma sha takwas ne, da guru mai kamu goma sha biyu kewaye da shi.

16 Ya kuma yi dajiya biyu ta zubi da tagulla don a sa a kan ginshiƙan. Tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.

17 Ya yi wa kowace dajiya da take kan ginshiƙan ragogi da tukakkun sarƙoƙi. Kowace dajiya tana da guda bakwai.

18 Ta haka ya yi ginshiƙai jeri biyu kewaye da raga don rufe dajiya wadda take da siffofin rumman, haka kuma ya yi wa ɗaya dajiyar.

19 Dajiyar da take kan ginshiƙai na cikin shirayin an yi su da fasalin bi-rana kamu huɗu huɗu.

20 Dajiyar tana kan ginshiƙan nan biyu kusa da wani abu mai kama da gammo, wanda yake kusa da ragar. Akwai jeri biyu na siffofin rumman guda ɗari biyu a kewaye da dajiyar.

21 Ya kafa ginshiƙan a shirayin Haikalin. Ya kafa ginshiƙi ɗaya a wajen dama, ya sa masa suna, Yakin, wato Allah ya kafa. Ya kafa ɗaya ginshiƙin a wajen hagu, ya sa masa suna Bo’aza, wato da ƙarfin Allah.

22 A bisa kawunan ginshiƙan akwai dajiya masu fasalin bi-rana. Haka aka gama aikin ginshiƙan.

23 Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da’irarta kuma kamu talatin ne.

24 Akwai goruna kewaye da gefensa. Gora goma a kowane kamu ɗaya. Suka kewaye kwatarniya. Gorunan jeri biyu ne, an yi zubinsu haɗe da kwatarniyar.

25 Aka ɗora ta a kan siffofin bijimai goma sha biyu. Siffofin bijimai uku suna fuskantar gabas, uku kuma suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. An ɗora kwatarniya a kansu. Gindinsu duka na wajen ciki.

26 Kaurin kwatarniya ya kai taƙin hannu guda. An yi gefenta kamar finjali, kamar kuma furen bi-rana. Takan ci garwa dubu biyu.

27 Ya kuma yi dakali goma da tagulla. Kowane dakali tsawonsa kamu huɗu, faɗinsa kuma kamu huɗu, tsayinsa kuwa kamu uku ne.

28 Yadda aka yi dakalan ke nan, dakalan suna da sassa, sassan kuma suna da mahaɗai.

29 Aka zana hotunan zakoki, da na bijimai, da na kerubobi a kan sassan. A kan mahaɗan kuma akwai gammo, aka zana hotunan furanni a ƙarƙashin zakokin da bijiman.

30 Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na karusa, da sandunan tagulla don sa kwatarniya. A kusurwoyin akwai abubuwa na zubi don tallabar kwatarniya. An zana furanni a kowane gefensu.

31 Bakinsa daga cikin dajiyar ya yi sama kamu guda. Bakin da’ira ne kamar fasalin gammo, kamu ɗaya da rabi. Akwai zāne-zāne a bakin. Sassan murabba’i ne, ba da’ira ba.

32 Ƙafafu huɗu ɗin, suna ƙarƙashin sassan. Sandunan ƙafafun a haɗe suke da dakalan. Tsayin kowace ƙafa kuwa kamu ɗaya da rabi ne.

33 Ƙafafun suna kama da ƙafafun karusa. Sandunan ƙafafun, da gyaffansu, da kome na ƙafafun duka na zubi ne.

34 Akwai ginshiƙi huɗu daga ƙarƙashin kowane dakali. Ginshiƙan suna haɗe da dakalan.

35 Akwai wani abu kamar gammo mai tsayi rabin kamu a kan dakalin. Ginshiƙan kuma da sassan a haɗe suke da dakalin.

36 Ya zana siffofin kerubobi, da na zakoki, da na itatuwan dabino a jikin ginshiƙan da sassan a duk inda ya ga akwai fili. Ya kuma zana furanni kewaye da su.

37 Haka aka yi dakalai, dukansu iri ɗaya ne, girmansu da fasalinsu kuma iri ɗaya ne.

38 Ya kuma yi daruna na tagulla guda goma. Kowane daro yana cin misalin garwa tamanin. Kowane daro kamu huɗu ne. Kowane dakali yana da daro ɗaya.

39 Ya kafa dakali biyar a gefen dama na Haikalin, ya kuma kafa biyar a gefen hagu na Haikalin. Ya kuma sa kwatarniya na zubi a gefen dama na Haikalin, wajen kusurwar gabas maso kudu.

Jerin Kayan Haikali

40-45 Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe da manyan cokula, da daruna. Haka Huram ya gama dukan aikin da ya yi wa Sulemanu a cikin Haikalin Ubangiji. Ga abin da ya yi.

ginshiƙai biyu

dajiya da take a kawunan ginshiƙan

raga biyu don rufe dajiyar da take a

kawunan ginshiƙai

siffofin rumman ɗari huɗu domin

raga biyu ɗin, da jeri biyu na

siffofin rumman domin kowace

raga don a rufe dajiyar da take a

kawunan ginshiƙan

dakalai goma

daruna goma a kan dakalan

kwatarniya ɗaya

siffofin bijimai guda goma sha biyu

da kwatarniya take zaune a kai,

tukwanen ƙarfe, da manyan cokula,

da kwanoni

Dukan kayayyakin aiki a cikin Haikalin Ubangiji waɗanda Huram ya yi wa sarki Sulemanu, an yi su ne da gogaggiyar tagulla.

46 Sarki ya sa a yi zubinsu a filin Urdun a ƙasar yumɓun da yake tsakanin Sukkot da Zaretan.

47 Sulemanu bai auna nauyin kayayyakin aikin ba domin sun cika yawa. Ba a kuma san nauyin tagullar ba.

48-50 Sulemanu ya yi dukan kayayyakin aikin da suke na Haikalin Ubangiji.

bagaden zinariya

teburin zinariya inda ake ajiye

gurasar ajiyewa

alkuki na zinariya guda biyar a gefen

dama, biyar kuma a gefen hagu a

gaban Wuri Mafi Tsarki na can

ciki

furanni

fitilu

arautaki

finjalai na zinariya

hantsuka

daruna

cokula

farantan wuta na zinariya tsantsa

almanani na zinariya domin ƙofofin

ɗaki na can cikin Haikali, wato

Wuri Mafi Tsarki, da ƙofofin

Haikalin

51 Haka sarki Sulemanu ya gama dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sai ya kawo abubuwan da tsohonsa Dawuda ya keɓe, wato azurfa, da zinariya, da kayayyakin aiki, ya ajiye su cikin taskokin Haikalin Ubangiji.

Categories
1 SAR

1 SAR 8

Sulemanu Ya Kawo Akwatin Alkawari cikin Haikali

1 Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra’ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra’ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.

2 Dukan jama’ar Isra’ila suka taru gaban sarki Sulemanu, wurin biki a watan Etanim, wato wata na bakwai.

3 Dukan dattawan Isra’ila suka zo, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin,

4 suka kawo tare da alfarwa ta sujada, da dukan tsarkakan tasoshin da suke cikin alfarwar. Firistoci da Lawiyawa suka kawo su.

5 Sarki Sulemanu kuwa tare da dukan taron jama’ar Isra’ila, waɗanda suka taru a gabansa, suna tare a gaban akwatin alkawari, suna ta miƙa sadakoki, da tumaki, da bijimai masu yawa, har ba su ƙidayuwa.

6 Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji suka sa a cikin Wuri Mai Tsarki na can ciki a Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.

7 Gama fikafikan kerubobin suna buɗe a bisa wurin da akwatin alkawarin yake domin su rufe akwatin alkawarin da sandunansa.

8 Sandunansa suna da tsawo har ana iya ganinsu daga ɗaki na can ciki daga Wuri Mai Tsarki, amma ba a iya ganinsu daga waje. Suna nan haka har wa yau.

9 Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da jama’ar Isra’ila sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar.

10 Sa’ad da firistoci suka fito daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya rufe Haikalin Ubangiji,

11 har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji.

12 Sa’an nan Sulemanu ya yi addu’a ya ce,

“Ubangiji ya ce zai zauna cikin

gizagizai masu duhu.

13 Yanzu na gina maka ɗaki mai

daraja,

Wurin da za ka zauna har abada.”

Jawabin Sulemanu ga Jama’a

14 Sa’an nan sarki Sulemanu ya juya, ya fuskanci jama’a suna tsaye, ya roƙi Allah ya sa musu albarka.

15 Ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya cika alkawarin da ya yi wa tsohona, Dawuda, da ya ce masa,

16 ‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra’ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra’ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra’ilawa.’ ”

17 Sulemanu ya ci gaba, ya ce, “Tsohona, Dawuda ya yi niyyar gina wa Ubangiji Allah na Isra’ila ɗaki,

18 amma Ubangiji ya ce wa tsohona, Dawuda, ya ji daɗin niyyar da ya yi ta gina Haikali,

19 amma duk da haka ba zai gina Haikalin ba, sai ɗansa wanda za a haifa masa shi ne zai gina Haikali domin sunan Ubangiji.

20 Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra’ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra’ila.

21 A cikin Haikalin kuma na shirya wa akwatin alkawari wuri, inda alkawarin Ubangiji yake, wato alkawarin da ya yi wa kakanninmu sa’ad da ya fito da su daga ƙasar Masar.”

Addu’ar Sulemanu

22 Sa’an nan Sulemanu ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron jama’ar Isra’ila. Ya ɗaga hannuwansa sama,

23 ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, ba wani Allah kamarka cikin Sama a bisa, da cikin duniya a ƙasa, wanda yake cika alkawari, ya nuna ƙauna ga bayinsa, waɗanda suke tafiya a gabansa da zuciya ɗaya.

24 Kai wanda ka cika abin da ka faɗa wa bawanka, Dawuda, tsohona, i, abin da ka faɗa da bakinka ka cika shi yau.

25 Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra’ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’

26 Yanzu fa, ya Allah na Isra’ila, sai ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka, Dawuda, tsohona.

27 “Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!

28 Duk da haka, ya Ubangiji Allahna, ka ji addu’ata, ni bawanka, da roƙe-roƙena, ka ji kukana da addu’ata da nake yi a gabanka yau.

29 Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu’ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin.

30 Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra’ilawa, idan sun yi addu’a, suna fuskantar wurin nan, sa’ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.

31 “Idan mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi, aka ba shi rantsuwa, idan ya zo, ya rantse a gaban bagadenka a wannan Haikali,

32 ya Ubangiji ka ji daga Sama, ka shara’anta bayinka, ka hukunta mai laifin, ka ɗora masa hakkinsa a kansa, amma ka kuɓutar da mara laifin, ka sāka masa bisa ga adalcinsa.

33 “Lokacin da abokan gāba suka ci mutanenka Isra’ila da yaƙi, saboda sun yi maka zunubi, idan sun komo wurinka, suka yabe ka, suka yi addu’a, suka roƙe ka a wannan Haikali,

34 sai ka ji daga Sama, ka gafarta wa jama’ar Isra’ila zunubinsu, sa’an nan ka sāke komar da su zuwa ƙasar da ka ba kakanninsu.

35 “Idan an hore su da rashin ruwan sama, saboda sun yi maka zunubi, idan sun tuba, suna fuskantar wannan Haikali, suka yi addu’a, suka kuma yabe ka,

36 sai ka ji daga Sama, ka gafarta zunuban sarki, da na jama’arka Isra’ila. Ka koya musu kyakkyawar hanyar da za su bi, ka sa a yi ruwan sama a ƙasarka wadda ka ba jama’arka gādo.

37 “Idan akwai yunwa a ƙasar, ko kuma akwai annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, sun cinye amfanin gona, idan kuma abokan gāba sun kawo wa jama’arka yaƙi har ƙofar birninsu, duk dai irin annoba da ciwon da yake cikinsu,

38 sai ka kasa kunne ga addu’arsu. Idan ɗaya daga cikin jama’arka Isra’ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu’a wajen wannan Haikali,

39 sai ka ji addu’arsa. Ka kasa kunne gare shi, a wurin zamanka a Sama, ka gafarta masa. Kai kaɗai ka san tunanin dukan mutane. Ka yi da kowa bisa ga abin da ya yi,

40 domin mutanenka su yi tsoronka a dukan kwanakinsu a ƙasar da ka ba kakanninmu.

41 “Sa’ad da kuma baƙo wanda yake wata ƙasa mai nisa ya ji labarin sunanka,

42 da manyan al’amura da ka yi wa jama’arka, ya zo domin ya yi maka sujada, da kuma addu’a gare ka a wannan Haikali,

43 sai ka kasa kunne ga addu’arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama’arka, Isra’ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.

44 “Idan jama’arka sun tafi su yi yaƙi da abokan gābansu, idan sun yi addu’a a gare ka, suna fuskantar birnin nan da ka zaɓa, da Haikalin nan wanda na gina saboda sunanka,

45 sai ka kasa kunne ga addu’arsu. Ka ji daga sama, ka ba su nasara.

46 “Idan jama’arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,

47 idan sun koma cikin hankalinsu a ƙasar da aka kai su bauta, har suka tuba, suka roƙe ka a ƙasar, suna hurta zunubansu da irin muguntar da suka aikata, ka ji addu’arsu, ya Ubangiji.

48 Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu’a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,

49 sai ka ji addu’arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, wurin zamanka, ka amsa, ka ji ƙansu.

50 Ka gafarta dukan zunubansu, da tayarwar da suka yi maka. Ka sa abokan gabansu su ji tausayinsu.

51 Gama su jama’arka ne, mallakarka, waɗanda ka fito da su daga Masar, daga tsakiyar azaba.

52 “Ya Ubangiji Allah, ka dubi jama’arka Isra’ila da sarkinsu da idon rahama, ka kasa kunne gare su duk lokacin da suka yi roƙo a gare ka.

53 Gama ka keɓe su daga sauran dukan al’ummai domin su zama jama’arka kamar yadda ka faɗa ta bakin bawanka Musa, sa’ad da ka fito da kakanninmu daga Masar.”

Addu’a ta Ƙarshe

54 Da Sulemanu ya gama wannan addu’a da roƙo ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda yake a durƙushe da hannuwansa a miƙe zuwa sama.

55 Ya tsaya, ya sa wa taron jama’ar Isra’ila albarka da babbar murya, ya ce,

56 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama’arsa, Isra’ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.

57 Ya Ubangiji Allah, sai ka kasance tare da mu kamar yadda ka kasance tare da kakanninmu, kada ka rabu da mu, ko ka yashe mu.

58 Ka sa zukatanmu su juyo gare ka, mu yi tafiya cikin tafarkunka, mu kiyaye umarnanka, da ka’idodinka da dokokinka, waɗanda ka umarci kakanninmu.

59 Ya Ubangiji Allahnmu, ka sa wannan roƙo da na yi ya kasance a gabanka, dare da rana. Ka biya bukatar bawanka, da bukatar jama’arka, Isra’ila, ta kowace rana,

60 domin dukan al’umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani.

61 Ku kuma jama’arsa, sai ku amince da Ubangiji Allahnmu da zuciya ɗaya, ku kiyaye dokokinsa da umarnansa, kamar yadda kuke yi a yau.”

An Keɓe Haikali

62 Sa’an nan sarki Sulemanu, tare da Isra’ilawa duka, suka miƙa sadaka ga Ubangiji.

63 Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra’ila suka keɓe Haikalin Ubangiji.

64 A wannan rana kuma ya keɓe tsakiyar filin da yake gaban Haikalin Ubangiji, gama a nan ne ya miƙa hadaya ta ƙonawa, da ta gari, da kitsen sadake-sadake na salama, gama bagaden tagullar da yake gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta ƙwarai da za a yi dukan waɗannan hadayu a kansa.

65 Sa’an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama’ar Isra’ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.

66 A rana ta takwas ya sallami jama’ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa’an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama’arsa, Isra’ilawa.

Categories
1 SAR

1 SAR 9

Ubangiji Ya Sāke Bayyana ga Sulemanu

1 Da Sulemanu ya gama ginin Haikalin Ubangiji da na fāda, da dukan abin da ya so ya yi,

2 sai Ubangiji ya sāke bayyana gare shi, kamar yadda ya bayyana gare shi a Gibeyon.

3 Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da roƙe-rokenka da ka yi a gare ni, saboda haka na tsarkake Haikalin nan da ka gina, na kuma sa sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullum.

4 Amma kai, idan ka yi tafiya a gabana kamar yadda tsohonka, Dawuda, ya yi da aminci, da sahihanci, kana aikata dukan abin da na umarce ka, kana kuma kiyaye dokokina da ka’idodina,

5 sa’an nan zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa tsohonka, Dawuda, sa’ad da na ce masa ba za a rasa mutum daga zuriyarsa wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba.

6 Amma idan kai, ko ‘ya’yanka, kun bar bina, ba ku kiyaye umarnaina da dokokina ba, waɗanda na yi muku, amma kuka tafi, kuka bauta wa waɗansu gumaka, kuka yi musu sujada,

7 sai in raba jama’ar Isra’ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama’ar Isra’ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba’a a wurin dukan mutane.

8 Wannan Haikali kuwa zai zama tsibin juji, duk wanda zai wuce ta wurin, zai yi mamaki, ya yi tsaki, ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa ƙasar nan da Haikalin nan haka?’

9 Waɗansu kuwa za su amsa su ce, ‘Saboda sun bar bin Ubangiji Allahnsu wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, domin haka Ubangiji ya ɗora musu wannan masifa.’ ”

Sauran Ayyukan Sulemanu

10 Sulemanu ya yi shekara ashirin kafin ya gama ginin Haikalin Ubangiji da fādarsa.

11 Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al’ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili.

12 Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya domin ya ga garuruwan da Sulemanu ya ba shi, sai ya ga ba su gamshe shi ba.

13 Don haka ya ce wa Sulemanu, “Dan’uwa, waɗanne irin garuruwa ke nan da ka ba ni?” Saboda haka har yanzu ana kiran ƙasar Kabul, wato marar amfani.

14 Hiram kuma ya aika wa Sulemanu da zinariya mai nauyin talanti ɗari da ashirin.

15 Wannan shi ne lissafin aikin tilas da sarki Sulemanu ya sa domin ginin Haikalin, da na fādarsa, da kuma Millo, a kuma gina garun birnin. Ya kuma sa tilas a sāke gina garuruwan Hazor, da Magiddo, da Gezer.

16 Gama Fir’auna ya haura, ya ci Gezer, ya ƙone ta da wuta, ya kuma kashe masu zama cikinta. Sa’an nan ya yi wa ‘yarsa, wato matar Sulemanu, kyauta da Gezer ɗin.

17 Sulemanu kuwa ya sāke gina Gezer. Ya kuma sa aka gina Bet-horon ta kwari ta aikin tilas,

18 da Ba’alat, da Tadmor a cikin jeji, a ƙasar Yahuza,

19 da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.

20-21 Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, da suka ragu a ƙasar, wato waɗanda ba mutanen Isra’ila ba, waɗanda mutanen Isra’ila ba su iya hallakarwa ba, Sulemanu ya sa zuriyarsu su yi aikin tilas na bauta, haka kuwa suke har wa yau.

22 Sulemanu bai mai da mutanen Isra’ila bayi ba, amma su ne sojojinsa da dogaransa, da shugabannin sojoji, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.

23 Sulemanu yana da masu lura da aiki su ɗari biyar da hamsin, suna lura da masu aikin tilas a wurare dabam dabam da ake wa Sulemanu gini.

24 Da ‘yar Fir’auna matar Sulemanu ta fita birnin Dawuda, zuwa gidan kanta wanda Sulemanu ya gina mata, sa’an nan ya gina birnin Millo.

25 Sau uku a shekara Sulemanu yakan miƙa hadayu na ƙonawa, da na salama, da hadayar turare, a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji. Ta haka aka gama ginin Haikali.

26 Sarki Sulemanu kuma ya yi jiragen ruwa a Eziyon-geber wadda take kusa da Elat, a bakin Bahar Maliya a ƙasar Edom.

27 Sarki Hiram ya aiki barorinsa, gogaggun matuƙan jiragen ruwa, da jiragen ruwa tare da barorin Sulemanu.

28 Sai suka tafi Ofir suka kawo wa sarki Sulemanu zinariya mai nauyin talanti ɗari huɗu da shirin.

Categories
1 SAR

1 SAR 10

Sarauniyar Sheba Ta Ziyarci Sulemanu

1 Sarauniyar Sheba ta ji labarin sunan da Sulemanu ya yi ta dalilin sunan Ubangiji, ta zo don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya.

2 Ta iso Urushalima da ‘yan rakiya da yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya da yawa, da duwatsu masu daraja. Sa’ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa duk abin da yake a ranta.

3 Sulemanu ya amsa tambayoyinta dukka, ba abin da ya gagare shi amsawa.

4-5 Sarauniyar Sheba ta yi mamaki sa’ad da ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina, da irin abincinsa, da irin zaman fādawansa, da yadda ma’aikatan gida suke hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da hadayu na ƙonawa waɗanda yakan miƙa cikin Haikalin Ubangiji.

6 Sai ta ce wa Sulemanu, “Labarin da na ji a ƙasata a kan al’amuranka da hikimarka, gaskiya ne.

7 Amma ban gaskata da labarin ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabi ma ba a faɗa mini ba, gama hikimarka da wadatarka sun fi abin da na ji.

8 Jama’arka, da fādawanka waɗanda suke tsaye a gabanka kullum, sun yi sa’a gama suna jin hikimarka.

9 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda ya yarda da kai, ya sa ka a kan gadon sarautar Isra’ila, domin Ubangiji yana ƙaunar Isra’ila har abada, ya naɗa ka sarki domin ka zartar da shari’a da adalci.”

10 Sa’an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya,da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.

11 Bayan wannan kuma jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itacen almug da yawa, da duwatsu masu daraja daga can.

12 Da itacen almug ne sarki ya yi ginshiƙai na Haikalin Ubangiji da gidan sarki, ya kuma yi molaye da garayu domin mawaƙa. Har wa yau ba a taɓa samu, ko ganin irin itacen almug kamar wannan ba.

13 Sarki Sulemanu ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ta nuna tana bukata, banda kyautar karamcin da ya yi mata. Sai ta koma ƙasarta tare da barorinta.

Dukiyar Sulemanu da Shahararsa

14 Yawan zinariya da akan kawo wa Sulemanu kowace shekara yakan kai talanti ɗari shida da sittin da shida na zinariya.

15 Banda wanda ya sa wa ‘yan kasuwa, da fatake, da harajin dukan sarakunan Arabiya, da na hakimai.

16 Sarki Sulemanu ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu da zinariya. Anyi kowace garkuwa da shekel ɗari shida na zinariya.

17 Ya kuma yi waɗansu garkuwoyi guda ɗari uku da zinariya. An yi kowace garkuwa da shekel dari uku na zinariya. Sarki kuwa ya ajiye su a ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon.

18 Ya kuma yi babban gadon sarauta na hauren giwa, sa’an nan ya dalaye shi da tattacciyar zinariya.

19 Gadon sarautar yana da matakai shida da siffar kan maraƙi a bayan gadon sarautar, a kowane gefen mazaunin kuma, akwai wurin ɗora hannu da siffofin zaki biyu suna tsaye a gefen wuraren ɗora hannun.

20 Akwai siffar zaki goma sha biyu suna tsaye a kowane gefen matakan nan shida. Ba a taɓa yin irinsu a kowace masarauta ba.

21 Dukan finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya aka yi su, haka kuma finjalan da suke cikin ɗakin da aka gina da katakai daga Lebanon, ba a yi wani finjali da azurfa ba, domin ba a mai da azurfa kome ba a kwanakin Sulemanu.

22 Gama sarki yana da rundunar jiragen ruwa a tekun Tarshish tare da na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku rundunar jiragen ruwa na Tarshish sukan kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai, da ɗawusu masu daraja.

23 Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.

24 Dukansu suna so su zo wurin Sulemanu don su ji hikimarsa wadda Allah ya ba shi.

25 Kowannensu yakan kawo masa yawan kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai kowace shekara.

Kasuwancin Sulemanu a kan Dawakai da Karusai

26 Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.

27 Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar dai duwatsu a Urushalima, itacen al’ul kuma ya zama kamar jumaiza na Shefela.

28 Sulemanu kuwa ya sayo dawakai daga Masar da Kuye. ‘Yan kasuwar sarki sukan sayo dawakai daga Kuye a kan tamaninsu.

29 Akan sayo karusa a Masar a bakin azurfa ɗari shida, doki kuwa a bakin ɗari da hamsin, ‘yan kasuwar sarki sukan sayar da su ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa.