Categories
1 SAR

1 SAR 11

Sulemanu Ya Ridda

1 Sarki Sulemanu ya ƙaunaci baƙin mata. Banda ‘yar Fir’auna, Sarkin Masar, ya auri matan Mowabawa, da na Ammonawa, da na Edomawa, da na Sidoniyawa, da na Hittiyawa.

2 Suna kuwa cikin al’umman da Ubangiji ya umarci jama’ar Isra’ila, ya ce, “Kada ku yi aurayya da su, gama hakika za su karkatar da zuciyarku zuwa gumakansu.” Sulemanu kuwa ya manne wa waɗannan mata da yake ƙauna.

3 Ya auri mata ɗari bakwai, dukansu kuwa gimbiyoyi ne. Yana kuma da ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa kuwa suka janye zuciyarsa daga bin Ubangiji,

4 sa’ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.

5 Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa.

6 Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.

7 Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima.

8 Ya kuma gina masujadai inda dukan matansa baƙi za su riƙa miƙa turare da hadayu ga gumakansu.

9 Ubangiji kuwa ya yi fushi da Sulemanu, domin zuciyar Sulemanu ta rabu da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana a gare shi sau biyu,

10 ya kuma umarce shi kada ya bi gumaka. Amma bai kiyaye umarnin da Ubangiji ya yi masa ba.

11 Saboda haka Ubangiji ya ce wa Sulemanu, “Tun da yake ka yi haka, ba ka kuwa kiyaye umarnina da dokokina waɗanda na umarce ka da su ba, to, hakika zan ƙwace mulki daga gare ka, in ba baranka.

12 Amma saboda tsohonka, Dawuda, ba zan ƙwace a zamaninka ba, amma zan ƙwace daga hannun ɗanka.

13 Duk da haka ba zan ƙwace mulkin duka ba, amma zan ba ɗanka kabila guda, saboda bawana Dawuda, saboda kuma Urushalima wadda na zaɓa.”

Abokan Gāban Sulemanu

14 Ubangiji kuwa ya sa Hadad Ba’edome, ya tayar wa Sulemanu. Shi Hadad daga jinin sarautar Edom ne.

15 Gama sa’ad da Dawuda ya ci Edom, Yowab, shugaban sojoji, ya tafi don ya binne kisassu, sun yi wata shida a can, shi da mutanensa, sai ya kashe kowane namijin da yake cikin Edom.

16 Gama Yowab da dukan Isra’ilawa sun tsaya a Edom wata shida, sai da ya gama kashe mazajen Edom duka.

17 Amma Hadad ya tsere zuwa Masar tare da waɗansu Edomawa, barorin tsohonsa. Hadad yana ɗan saurayi a lokacin.

18 Suka kama hanya daga Madayana suka zo Faran. Daga Faran suka kwashi mutane tare da su, suka tafi Masar zuwa wurin Fir’auna, Sarkin Masar, wanda ya ba shi gida, ya kuma riƙa ba shi abinci, ya kuma ba shi ƙasa.

19 Hadad kuwa ya sami farin jini ƙwarai a wurin Fir’auna, har ya aurar masa da ƙanwar matarsa, wato ƙanwar Tafenes, sarauniya.

20 Ita kuwa ta haifa masa ɗa, Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a gidan Fir’auna. Genubat kuwa ya zauna tare da ‘ya’yan Fir’auna, maza.

21 Amma sa’ad da Hadad ya ji labari Dawuda ya rasu, Yowab shugaban sojoji shi ma ya rasu, sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Ka yardar mini, in tashi, in koma ƙasata.”

22 Amma Fir’auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?”

Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.

23 Allah kuma ya sa Rezon ɗan Eliyada, ya tayar wa Sulemanu, shi Rezon ya gudu daga wurin maigidansa, Hadadezer Sarkin Zoba.

24 Ya tattara wa kansa mutane ya zama shugaban ‘yan hari bayan kashe-kashen da Dawuda ya yi. Sai suka tafi Dimashƙu, suka zauna a can, suka naɗa shi Sarkin Dimashƙu.

25 Ya zama abokin gāban Isra’ila a dukan zamanin Sulemanu. Ya yi ta ɓarna kamar yadda Hadad ya yi. Ya ƙi jinin mutane Isra’ila. Ya yi mulkin suriya.

Alkawarin Allah ga Yerobowam

26 Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba’ifraime na Zaretan, baran Sulemanu, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki.

27 Ga dalilin da ya sa ya tayar wa sarki.

Sulemanu ya gina Millo ya kuma faɗaɗa garun birnin Dawuda tsohonsa.

28 Yerobowam mutum ne mai fasaha. Da Sulemanu ya ga shi saurayi ne mai himma, sai ya shugabantar da shi kan aikin tilas na gidan Yusufu.

29 A sa’ad da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahija mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahija yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai,

30 sai Ahija ya kama sabuwar rigar da ya sa, ya kyakketa ta ƙyalle goma sha biyu,

31 ya ce wa Yerobowam, “Kwashi ƙyalle goma, gama haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Ga shi, ina gab da in kece sarauta daga hannun Sulemanu, zan ba ka kabila goma.

32 Amma Sulemanu, zai sami kabila ɗaya saboda bawana Dawuda, da kuma ɗaya saboda Urushalima, wato birnin da na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila duka.

33 Domin Sulemanu ya rabu da ni, ya bauta wa Ashtoret, gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh, gunkin Mowab, da Milkom, gunkin Ammonawa. Bai yi tafiya a cikin tafarkuna ba, bai yi abin da yake daidai a gare ni ba, bai kiyaye dokokina, da ka’idodina kamar yadda Dawuda, tsohonsa, ya yi ba.

34 Duk da haka ba zan karɓe sarauta duka daga hannunsa ba, amma zan bar shi ya yi mulki muddin ransa saboda bawana Dawuda, wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnaina da dokokina.

35 Amma zan karɓe mulki daga hannun ɗansa in ba ka, zan ba ka kabila goma.

36 Duk da haka zan ba ɗansa kabila guda, domin bawana Dawuda ya kasance da fitila kullum a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa sunana.

37 Zan sa ka yi mulki a kan duk abin da ranka yake bukata, za ka zama Sarkin Isra’ila.

38 Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra’ila.

39 Zan wahalar da zuriyar Dawuda, amma ba har abada ba.’ ”

40 Sulemanu kuwa ya nema ya kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tashi, ya tsere zuwa Masar, wurin Shishak Sarkin Masar, ya zauna a can har rasuwar Sulemanu.

Rasuwar Sulemanu

41 Sauran ayyukan Sulemanu, da dukan abin da ya yi, da hikimarsa an rubuta su a littafin tarihin Sulemanu.

42 Sulemanu ya yi shekara arba’in yana sarauta a Urushalima a kan Isra’ila duka.

43 Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima. ‘Dansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.

Categories
1 SAR

1 SAR 12

Mulki ya Rabu Biyu

1 Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan mutanen Isra’ila sun tafi Shekem don su naɗa shi sarki.

2 Sa’ad da Yerobowam, ɗan Nebat, ya ji labari, gama a lokacin yana Masar inda ya gudu saboda sarki Sulemanu, sai ya komo daga Masar.

3 Suka aika a kirawo shi, sai Yerobowam da dukan taron jama’ar Isra’ila suka zo suka ce wa Rehobowam,

4 “Tsohonka ya nawaita mana, yanzu sai ka rage mana wahalar aikin tsohonka da nawayarsa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”

5 Sai ya ce musu, “Ku tafi, ku sāke zuwa bayan kwana uku.” Sai suka tafi.

6 Sarki Rehobowam kuwa ya nemi shawara daga wurin dattawa, waɗanda suka bauta wa tsohonsa, Sulemanu, lokacin da yake da rai. Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?”

7 Suka ce masa, “Idan za ka zama mai lura da jama’an nan yau, ka bauta musu, sai ka yi musu magana da kyau, su kuwa za su zama talakawanka har abada.”

8 Amma ya yi watsi da shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawara daga wurin matasa, tsararsa.

9 Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka roƙe ni wai in rage musu nawayar da tsohona ya aza musu?”

10 Matasa da suke tsara ɗaya da shi kuwa suka ce masa, “Haka za ka faɗa wa mutanen nan da suka yi magana da kai, cewa tsohonka ya nawaita musu, amma sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri.

11 Zan ƙara a kan nawayar da tsohona ya aza muku. Shi ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”

12 Yerobowam da dukan mutane suka zo wurin Rehobowam a rana ta uku kamar yadda ya faɗa musu su zo wurinsa bayan kwana uku.

13 Da suka zo, sai sarki ya yi musu magana da zafi, ya kuma yi watsi da shawarar da dattawa suka ba shi.

14 Ya yi musu magana bisa ga shawarar matasa ya ce, “Tsohona ya nawaita muku, ni kuwa zan ƙara nawaita muku. Tsohona ya yi muku horo da bulala, amma ni zan yi muku da kunamai.”

15 Haka kuwa sarki ya ƙi jin roƙon da jama’a suka yi masa, gama Ubangiji ne ya sa al’amarin ya zama haka domin ya cika maganarsa, wadda ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta bakin Ahija mutumin Shilo.

16 Da mutanen Isra’ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra’ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!”

Jama’ar Isra’ila fa suka tayar,

17 suka bar Rehobowam ya sarauci jama’ar da take zaune a yankin ƙasar Yahuza.

18 Sa’an nan sarki Rehobowam ya aiki Adoniram, shugaban aikin tilas, sai mutanen Isra’ila suka jajjefe shi da duwatsu har lahira. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta, ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima.

19 Da haka mutanen Isra’ila suka tayar wa gidan Dawuda har wa yau.

20 Da dukan mutane suka ji, cewa Yerobowam ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron jama’a. Suka naɗa shi Sarkin Isra’ila duka. Ba wanda ya bi gidan Dawuda, sai dai kabilar Yahuza.

21 Da Rehobowam ya komo Urushalima, sai ya tara dukan jama’ar gidan Yahuza, da na kabilar Biliyaminu. Aka sami mayaƙa dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) waɗanda za su yi yaƙi da gidan Isra’ila, don su komar da su a ƙarƙashin mulkin Rehobowam, ɗan Sulemanu.

22 Amma Ubangiji Allah ya yi magana da annabi Shemaiya,

23 ya faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen gidan Yahuza da na Biliyaminu, da sauran jama’a,

24 Ubangiji ya ce, “Kada ku haura zuwa yaƙi da ‘yan’uwanku, mutanen Isra’ila, sai kowa ya koma gidansa, gama wannan al’amari daga wurina ne.” Su kuwa suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka koma gida.

Yerobowam Ya bar Bin Tafarkin Allah

25 Sa’an nan sarki Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu, ya zauna can. Daga can kuma ya tafi ya gina Feniyel.

26 Yerobowam kuwa ya ce a zuciyarsa, “Mulkin fa zai koma gidan Dawuda.

27 Idan mutanen nan sun ci gaba da zuwa Urushalima don miƙa wa Ubangiji hadayu, zuciyarsu za ta koma kan sarki Rehobowam, na Yahuza, za su kashe ni, su koma wurinsa.”

28 Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata ‘yan maruƙa biyu da zinariya. Sa’an nan ya ce wa jama’arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra’ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”

29 Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.

30 Wannan abu ya zama zunubi, gama mutane sun tafi wurin siffofin maruƙan nan a Betel da Dan.

31 Ya kuma gina masujadai a tuddai, sa’an nan ya sa waɗansu daga cikin mutane waɗanda ba Lawiyawa ba, su zama firistoci.

An Soki Sujada a Betel

32 Yerobowam kuma ya sa a yi idi ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel. Ya yi ta miƙa hadayu ga siffofin maruƙan da ya yi. Ya kuma sa firistoci a masujadan da ya gina a Betel.

33 Ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, wato watan da ya zaɓa don kansa. Ya kafa wa jama’ar Isra’ila idi. Sai ya tafi don ya ƙona turare a kan bagaden.

Categories
1 SAR

1 SAR 13

Annabi Ya Faɗakar da Yerobowam

1 Bisa ga umarnin Ubangiji, sai ga annabi ya fito daga Yahuza zuwa Betel. Yerobowam kuwa yana tsaye kusa da bagaden don ya ƙona turare.

2 Bisa ga umarnin Ubangiji, sai annabin ya ta da murya, ya ce, “Ya bagade, bagade, Ubangiji ya ce za a haifi ɗa a gidan Dawuda, sunansa Yosiya wanda zai miƙa firistoci na masujadan tuddai hadaya a kanka, wato firistoci waɗanda suke ƙona turare. Za a ƙone ƙasusuwan mutane a bisa kanka.”

3 Ya kuma ba da alama a wannan rana cewa, “Wannan ita ce alamar da Ubangiji ya faɗa, za a rushe bagaden, a zubar da tokar da take bisansa.”

4 Da sarki ya ji maganar annabin, wato wadda ya yi a kan bagaden da yake Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden, ya ce, “Ku kama shi.” Hannun da ya miƙa kuwa ya sage, bai iya komo da shi ba.

5 Aka rushe bagaden, aka kuma zubar da tokar daga bagaden bisa ga alamar da annabin ya faɗa da sunan Ubangiji.

6 Sarki Yerobowam ya ce wa annabin, “In ka yarda ka yi roƙo ga Ubangiji Allahnka domina, ka yi mini addu’a don ya warkar da hannuna.”

Annabi ya roƙi Ubangiji, sai hannun sarki ya komo daidai.

7 Sa’an nan sarkin ya ce wa annabin, “Zo mu tafi gida don ka shaƙata, zan ba ka lada.”

8 Annabin kuwa ya ce wa sarki, “Ko da za ka ba ni rabin gidanka, ba zan tafi tare da kai ba, ba kuma zan ci abinci ko in sha ruwa a wurin nan ba.

9 Gama Ubangiji ya umarce ni da cewa kada in ci abinci, ko in sha ruwa, ko in koma ta hanyar da na zo.”

10 Haka kuwa ya koma ta wata hanya dabam bai koma ta hanyar da ya bi zuwa Betel ba.

Tsohon Annabi na Betel

11 Akwai wani tsohon annabi a Betel. ‘Ya’yansa maza kuwa suka tafi suka faɗa masa dukan abin da annabin Allah ya yi a Betel a wannan rana. Suka faɗa wa mahaifinsu maganar da annabin Allah ya faɗa wa sarki.

12 Tsohon annabin ya tambaye su, “Wace hanya ya bi?” Su kuwa suka nuna masa hanyar.

13 Ya ce musu su ɗaura wa jakinsa shimfiɗa. Sai suka ɗaura wa jakin shimfiɗa, shi kuwa ya hau,

14 ya bi bayan annabin nan da ya fito daga Yahuza, ya same shi yana zaune a gindin itace oak. Ya tambaye shi, “Ko kai ne annabin da ya zo daga Yahuza?”

Mutumin ya amsa, “I, ni ne,”

15 Sa’an nan ya ce masa, “Zo mu tafi gida ka ci abinci.”

16 Amma annabin ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba, ba kuwa zan shiga gida ba, ko in ci abinci, ko in sha ruwa tare da kai a wannan wuri,

17 gama Ubangiji ya ce mini kada in ci abinci, ko in sha ruwa a can, ko in koma ta hanyar da na zo.”

18 Sa,an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala’ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.

19 Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin.

20 Sa’ad da suke zaune wurin ci, sai maganar Ubangiji ta zo ga tsohon annabin da ya komar da annabin Allah,

21 sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba,

22 amma ka komo, ka ci abinci, ka sha ruwa a wurin da ya ce maka, kada ka ci abinci, ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a binne gawarka a kabarin kakanninka ba.’ ”

23 Bayan da ya ci abinci, ya sha sai tsohon annabin ya ɗaura wa jaki shimfiɗa don annabin da ya komo da shi.

24 Sa’ad da annabin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya, ya kashe shi, ya jefar da gawarsa a kan hanya. Sai jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar.

25 Mutane suka wuce, suka ga gawar a kan hanya, da zaki a tsaye kusa da gawar. Suka tafi suka faɗa a birni, inda tsohon annabin nan yake.

26 Sa’ad da tsohon annabin nan ya ji, sai ya ce, “Wannan annabin Allah ne, wanda bai yi biyayya da maganar Ubangiji ba, saboda haka Ubangiji ya bashe shi ga zaki ya yayyage shi, ya kashe shi, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.”

27 Sa’an nan ya ce wa ‘ya’yansa maza, “Ku ɗaura mini shimfiɗa.” Su kuwa suka ɗaura,

28 ya hau ya tafi, ya iske gawar a hanya. Jakin da zakin suna tsaye kusa da gawar. Zakin bai ci gawar ba, bai kuma fāɗa wa jakin ba.

29 Tsohon annabin kuwa ya ɗauki gawar ya ɗora bisa jakin, ya kawo ta cikin birni, wato Betel, don yin makoki da binnewa.

30 Ya binne gawar a kabarinsa, sa’an nan suka yi makoki suna cewa, “Kaito, dan’uwana!”

31 Bayan da ya binne shi, sai ya ce wa ‘ya’yansa, “Sa’ad da na rasu, sai ku binne ni a kabarin da aka binne annabin nan. Ku ajiye gawata kusa da tasa.

32 Gama maganar Ubangiji da ya faɗa game da bagaden da yake cikin Betel, da masujadai na kan tuddai waɗanda suke a garuruwan Samariya, za ta cika.”

Zunubin Yerobowam zai Kai shi Hallaka

33 Bayan wannan al’amari Yerobowam bai bar muguwar hanyarsa ba, amma ya naɗa firistoci daga cikin mutane don masujadai da suke kan tuddai. Duk mutumin da yake so, sai ya keɓe shi don ya zama firist na masujada da take kan tudu.

34 Wannan zunubi ya zama sanadi ga gidan Yerobowam, har ya isa a shafe gidan, a hallaka shi ƙaƙaf.

Categories
1 SAR

1 SAR 14

Annabcin Ahija

1 A lokacin nan Abaija ɗan Yerobowam ya kwanta ciwo.

2 Yerobowam kuwa ya ce wa matarsa, “Ki tashi, ki ɓad da kama don kada a sani ke matata ce, sa’an nan ki tafi Shilo wurin Ahija, annabin nan wanda ya ce mini zan sarauci jama’an nan.

3 Ki ɗauki malmalar abinci guda goma, da waina, da kurtun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.”

4 Matar kuwa ta yi haka. Ta tashi ta tafi Shilo a gidan Ahija. Ahija ba ya gani, saboda tsufa.

5 Ubangiji ya ce wa Ahija, “Ga matar Yerobowam tana zuwa don ta tambaye ka abin da zai faru da ɗanta, gama ɗan yana ciwo. To, da haka za ka amsa mata, gama sa’ad da ta zo, za ta nuna kamar ita wata mace ce dabam.”

6 Da Ahija ya ji motsin takawarta a bakin ƙofa, sai ya ce mata, “Ki shigo, matar Yerobowam, me ya sa kike yi kamar ke wata ce dabam? Gama an umarce ni in faɗa miki labari marar daɗi.

7 Ki koma, ki faɗa wa Yerobowam, Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na ɗaukaka ka daga cikin mutane, na sa ka zama shugaban mutanena, Isra’ilawa.

8 Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba ka, duk da haka ba ka zama kamar bawana Dawuda ba, wanda ya kiyaye umarnaina, ya bi ni da zuciya ɗaya, yana yin abin da yake daidai a gare ni.

9 Amma ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka riga ka, ka yi wa kanka gumaka, da siffofi na zubi, ka tsokane ni in yi fushi, ka yi watsi da ni.

10 Saboda haka zan kawo masifa a gidanka. Zan datse maka kowane ɗa namiji, ko bawa, ko ‘yantacce, daga cikin Isra’ila. Zan ƙone gidanka kamar yadda akan ƙone juji ƙurmus.

11 Duk wanda yake naka wanda zai mutu a birni, karnuka za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura tsuntsaye za su cinye shi, ni Ubangiji, ni ne na faɗa.’

12 “Ki tashi, ki koma gida. Da shigarki birni, yaron zai mutu.

13 Dukan jama’ar Isra’ila za su yi makoki dominsa, su binne shi, gama shi kaɗai zai sami binnewa daga cikin gidan Yerobowam, domin a gare shi kaɗai aka iske abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yake murna da shi.

14 Ubangiji kuma zai ta da wani wanda zai sarauci Isra’ila, wanda kuma zai rushe gidan Yerobowam daga yanzu har zuwa nan gaba.

15 Ubangiji zai hukunta Isra’ila kamar yadda akan girgiza iwa a baƙin rafi, zai tumɓuke Isra’ila daga wannan ƙasa mai albarka wadda ya ba kakanninsu, ya kuma watsar da su a hayin Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu gumaka don sun tsokani Ubangiji ya yi fushi.

16 Ubangiji zai rabu da Isra’ila saboda zunuban Yerobowam waɗanda ya yi, da kuma waɗanda ya sa mutanen Isra’ila su yi.”

17 Sa’an nan matar Yerobowam ta tashi, ta tafi Tirza. Amma tana shiga gidan ke nan, sai yaron ya mutu.

18 Jama’ar Isra’ila duka suka binne shi, suka yi makoki dominsa, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa, annabi Ahija.

Mutuwar Yerobowam

19 Sauran ayyukan Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

20 Yerobowam ya yi mulki shekara ashirin da biyu sa’an nan ya rasu, aka binne shi. Ɗansa Nadab ya gāji sarautarsa.

Mulkin Rehobowam

21 Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi mulki a Yahuza. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi shekara goma sha bakwai yana sarauta a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila duka, domin ya sa sunansa ya kasance a wurin. Sunan tsohuwarsa Na’ama, ita kuwa Ba’ammoniya ce.

22 Mutanen Yahuza suka yi wa Ubangiji zunubi. Suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata fiye da abin da kakanninsu suka yi.

23 Gama su ma sun gina wa kansu wuraren tsafi a tuddai, da ginshiƙai, da gumaka a tuddai, da cikin duhuwar itatuwa.

24 Fiye da haka kuma akwai mata da maza da suke aikin karuwanci a wuraren da suke tsafin a wurin al’ummai. Mutanen Yahuza sun yi dukan abubuwan ƙazanta na al’ummai waɗanda Ubangiji ya kora sa’ad da Isra’ilawa suke gab da shigar ƙasar.

25 A cikin shekara ta biyar ta sarautar sarki Rehobowam, sai Shishak Sarkin Masar ya kai wa Urushalima yaƙi.

26 Ya kwashe dukiyar Haikalin Ubangiji, da dukiyar gidan sarki duka. Ya kuma kwashe garkuwoyin zinariya waɗanda Sulemanu ya yi.

27 A maimakonsu kuwa sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla, ya sa a hannun shugabannin masu tsaro waɗanda suke tsaron ƙofar gidan sarki.

28 Duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su ɗauki garkuwoyin, su kuma mayar da su a ɗakin tsaro.

29 Sauran ayyukan Rehobowam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

30 Kullum akan yi ta yin yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam,

31 Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na’ama, ita kuwa Ba’ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.

Categories
1 SAR

1 SAR 15

Sarki Abaija na Yahuza

1 A shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yerobowam ɗan Nebat, Abaija ya sarauci mutanen Yahuza.

2 Ya yi mulki shekara uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma’aka, ‘yar Absalom, wato kakarsa.

3 Shi kuma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa sosai, kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi ba.

4 Amma duk da haka, saboda Dawuda, Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima da ya sa ɗansa ya gāje shi, ya kuma kafa Urushalima,

5 domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.

6 Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa.

7 Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

8 Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.

Sarki Asa na Yahuza

9 A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowam Sarkin Isra’ila, Asa ya sarauci jama’ar Yahuza.

10 Ya yi shekara arba’in da ɗaya yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma’aka, ‘yar Absalom, wato kakarsa.

11 Asa kuwa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.

12 Ya kori mata da maza da suke karuwanci a wuraren tsafi na arna a ƙasar, ya kuma kawar da gumakan da kakanninsa suka yi.

13 Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma’aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron.

14 Amma ba a kawar da wuraren tsafi na tuddai ba, duk da haka Asa ya yi aminci sosai ga Ubangiji dukan kwanakinsa.

15 Ya kawo dukan tsarkakakkun abubuwan da tsohonsa ya keɓe, da kuma azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda shi kansa ya yi, a cikin Haikalin Ubangiji.

Alkawari Tsakanin Asa da Ben-hadad

16 Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha, Sarkin Isra’ila a dukan kwanakin mulkinsu.

17 Ba’asha, Sarkin Isra’ila, ya kai wa Yahuza yaƙi. Sai ya gina Rama don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.

18 Sa’an nan Asa ya kwashe dukan azurfa da zinariya da suka ragu a ɗakunan ajiya na Haikalin Ubangiji, da na gidan sarki, ya ba barorinsa su kai wa Ben-hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, ya ce,

19 “Bari mu ƙulla alkawari da juna kamar yadda tsohona da tsohonka suka yi, ga shi, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Sai ka tafi, ka warware alkawarinka da Ba’asha, Sarkin Isra’ila, domin ya tashi ya bar ni.”

20 Ben-hadad kuwa ya yarda da maganar sarki Asa. Ya kuwa aiki shugabannin sojojinsa su yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Su kuwa suka tafi, suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma’aka, da dukan Kinneret, da dukan ƙasar Naftali.

21 Da Ba’asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.

22 Sa’an nan sarki Asa ya gayyaci dukan jama’ar Yahuza, ba wanda aka ɗauke wa. Suka tafi suka kwashe duwatsu da katakai waɗanda Ba’asha yake ginin Rama da su. Da su sarki Asa ya gina Geba ta Biliyaminu, da Mizfa.

23 Sauran dukan ayyukan Asa, da dukan ƙarfinsa, da dukan abin da ya yi, da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza. Amma da ya tsufa, sai ya sami ciwo a ƙafafunsa.

24 Asa kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima, Ɗansa Yehoshafat ya gāji sarautarsa.

Sarki Nadab na Isra’ila

25 Nadab ɗan Yerobowam ya ci sarautar Isra’ila a shekara ta biyu ta sarautar Asa Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra’ila shekara biyu.

26 Ya yi wa Ubangiji zunubi kamar yadda tsohonsa ya yi, ya kuma sa Isra’ila su yi zunubi.

27 Ba’asha ɗan Ahija kuwa daga gidan Issaka ya yi wa Nadab maƙarƙashiya, ya kashe shi a Gibbeton ta Filistiyawa, gama Nadab da mutanen Isra’ila sun kewaye Gibbeton da yaƙi.

28 Haka Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, ya kuwa ci sarautar a maimakonsa.

29 Nan da nan da ya zama sarki, sai ya kashe dukan mutanen gidan Yerobowam, bai bar wani na gidan Yerobowam da rai ba, ya hallaka su sarai, bisa ga maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa bawansa Ahija mutumin Shilo.

30 Wannan abu ya faru saboda zunubin Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra’ila su yi, ya tsokani fushin Ubangiji Allah na Isra’ila.

31 Sauran ayyukan Nadab, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

32 Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba’asha Sarkin Isra’ila dukan kwanakin sarautarsu.

Sarki Ba’asha na Isra’ila

33 A cikin shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ba’asha ɗan Ahija ya yi sarautar Isra’ila a Tirza. Ya yi shekara ashirin da huɗu yana sarauta.

34 Ya aikata zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi hanyar Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra’ila su yi.

Categories
1 SAR

1 SAR 16

1 Ubangiji ya yi magana da Yehu, ɗan Hanani a kan Ba’asha, ya ce,

2 “Tun da yake na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaban jama’ata Isra’ila, kai kuwa ka bi hanyar Yerobowam, ka sa jama’ata, wato Isra’ila, su yi zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu,

3 to, zan shafe ka da gidansa, in mai da gidanka kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat.

4 Duk mutumin da yake naka da zai mutu a cikin birni, karnuka ne za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura, tsuntsaye ne za su cinye shi.”

5 Sauran ayyukan Ba’asha, da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

6 Ba’asha kuwa ya rasu, aka binne shi a Tirza. Sai Ila, ɗansa ya gāji sarautarsa.

7 Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba’asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.

Sarki Ila na Isra’ila

8 A shekara ta ashirin da shida ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ila ɗan Ba’asha, ya ci sarautar Isra’ila a Tirza. Ya yi sarauta shekara biyu.

9 Amma Zimri, shugaban rabin karusan Ila, ya yi masa maƙarƙashiya. Sa’ad da Ila yake Tirza, ya sha, ya bugu a gidan Arza wanda yake lura da fāda,

10 sai Zimri ya shiga gidan, ya buge shi ya kashe shi. Wannan ya faru a shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza.

11 Da Zimri ya zama sarki, nan da nan sai ya kashe dukan mutanen gidan Ba’asha, bai bar masa wani namiji, ko dangi, ko aboki ba.

12 Haka Zimri ya hallaka gidan Ba’asha bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa a kansa ta bakin annabi Yehu.

13 Wannan kuwa ya faru saboda zunuban Ba’asha da na ɗansa Ila, da zunuban da suka sa jama’ar Isra’ila su yi, har suka sa Ubangiji Allah na Isra’ila ya yi fushi saboda gumakansu.

14 Sauran ayyukan Ila da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

Sarki Zimri na Isra’ila

15 A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Zimri ya yi sarauta kwana bakwai a Tirza. A lokacin nan sojoji suka kai wa Gibbeton ta Filistiyawa yaƙi.

16 Da sojojin da suke bakin dāga suka ji an ce Zimri ya shirya makirci, ya kashe sarki, sai dukan Isra’ilawa suka naɗa Omri, shugaban sojojin, can a sansani. A wannan rana ya zama Sarkin Isra’ila.

17 Omri kuwa ya tashi daga Gibbeton tare da dukan Isra’ila, suka kai wa Tirza yaƙi.

18 Da Zimri ya ga an ci birnin, sai ya tafi ya shiga hasumiyar da take a fāda, ya sa wa fādar wuta, wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu.

19 Wannan ya faru saboda zunuban da ya aikata, ya yi mugun abu a gaban Ubangiji, ya bi hanyar Yerobowam da zunubinsa da ya aikata, har ya sa Isra’ilawa su yi zunubi.

20 Sauran ayyukan Zimri da makircin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

Sarki Omri na Isra’ila

21 Jama’ar Isra’ila suka rabu biyu. Rabi suka bi Tibni ɗan Ginat don su naɗa shi sarki. Rabin kuwa suka bi Omri.

22 Amma jama’ar da suka bi Omri suka rinjayi waɗanda suka bi Tibni ɗan Ginat. Sai Tibni ya mutu, Omri kuwa ya zama sarki.

23 A shekara ta talatin da ɗaya ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Omri ya ci sarautar Isra’ila. Ya yi shekara goma sha biyu yana sarauta. Ya yi shekara shida yana mulki a Tirza.

24 Sa’an nan ya sayi tudun Samariya daga Shemer a bakin azurfa dubu shida (6,000), a wurin Shemer, ya kuwa yi gini a kan tudun, ya sa masa suna Samariya saboda sunan Shemer mai tudun.

25 Omri kuwa ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi.

26 Ya bi duk irin hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, da irin zunuban da ya sa jama’ar Isra’ila su yi. Suka sa Ubangiji Allah na Isra’ila ya yi fushi saboda gumakansu.

27 Sauran ayyukan da Omri ya yi, da kama-karyar da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

28 Omri kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Ɗansa Ahab ya gāji sarautarsa.

Sarki Ahab na Isra’ila

29 A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ahab ɗan Omri ya yi sarautar Isra’ila. Ahab ɗan Omri kuwa ya yi sarautar Isra’ila a Samariya shekara ashirin da biyu.

30 Shi kuma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji fiye da dukan waɗanda suka riga shi.

31 Da yake abu ne mai sauƙi a gare shi ya bi hanyar zunuban Yerobowam ɗan Nebat, sai ya auro Yezebel ‘yar Etba’al, Sarkin Sidon, ya kuma bauta wa gunkin nan Ba’al, ya yi masa sujada.

32 Ya gina wa Ba’al bagade a matsafar Ba’al ɗin, da ya gina a Samariya.

33 Ahab kuma ya yi gunkiyan nan Ashtoret. Ahab dai ya yi abin da ya sa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra’ila waɗanda suka riga shi.

34 A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa’ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa’ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.

Categories
1 SAR

1 SAR 17

Iliya Ya yi Annabci Za a yi Fari

1 Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”

2 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Iliya,

3 “Ka tashi daga nan ka nufi wajen gabas, ka ɓuya a rafin Kerit, a gabashin Urdun.

4 Za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”

5 Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa, ya tafi ya zauna a rafin Kerit wanda yake gabashin Urdun.

6 Hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da maraice. Yakan kuma sha ruwa daga rafin.

7 Da aka jima sai rafin ya ƙafe saboda ba a yin ruwan sama a ƙasar.

Iliya da Mace Gwauruwa a Zarefat

8 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Iliya.

9 “Tashi ka tafi Zarefat ta Sidon, ka zauna a can. Ga shi, na umarci wata mace wadda mijinta ya rasu ta ciyar da kai.”

10 Sai ya tashi, ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar garin, sai ga wata wadda mijinta ya rasu tana tattara itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa in sha.”

11 Ta juya ta tafi don ta kawo masa ruwan sha ke nan, sai ya sāke kiranta, ya ce, “Ki kuma kawo mini ɗan abinci.”

12 Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan farin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da yake cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.”

13 Amma Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, ki tafi, ki yi yadda kika ce, amma ki fara yi mini ‘yar waina, ki kawo mini, sa’an nan ki yi wa kanki da ɗanki.

14 Gama Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Garin da yake a tukunyarki ba zai ƙare ba, man da yake a kurtunki kuma ba zai ƙare ba, sai ran da Ubangiji ya sa aka yi ruwan sama a ƙasar.’ ”

15 Ta tafi, ta yi yadda Iliya ya ce, dukansu kuwa suka sami isasshen abinci har kwanaki da yawa.

16 Garin da yake cikin tukunyar bai ƙare ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.

17 Bayan wannan sai ɗan macen, wato ɗan uwargijiyar gidan, ya yi ciwo. Ciwon kuwa ya tsananta har ransa ya fita.

18 Sai macen ta ce wa Iliya, “Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo don ka nuna wa Allah zunubina, ka zama sanadin mutuwar ɗana?”

19 Iliya ya ce mata, “Ki kawo mini ɗanki.” Ya karɓe shi daga wurinta, ya kai shi a bene inda yake kwana. Ya kwantar da shi a gadonsa.

20 Sa’an nan ya yi addu’a da gaske ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wa gwauruwan nan da nake zaune wurinta masifa, ka aukar wa ɗanta da ajali?”

21 Sa’an nan ya kwanta ya miƙe a kan yaron sau uku, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka sa ran yaron nan ya komo cikinsa.”

22 Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo.

23 Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga soro, ya kai shi cikin gida, ya ba uwar. Ya ce mata, “Ki gani, ɗanki yana da rai.”

24 Sai macen ta ce wa Iliya, “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuwa yana magana ta wurinka.”

Categories
1 SAR

1 SAR 18

Iliya ya Koma gun Ahab

1 Bayan ‘yan kwanaki, sai Ubangiji ya yi magana da Iliya a shekara ta uku, ya ce, “Tafi, ka nuna kanka ga Ahab, ni kuwa zan sa a yi ruwan sama.”

2 Sai Iliya ya tafi.

A lokacin kuwa yunwa ta tsananta a Samariya.

3 Ahab kuwa ya kira Obadiya, shugaban gidansa. Obadiya kuwa mai tsoron Ubangiji ne sosai.

4 A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.

5 Sai Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka tafi ko’ina a ƙasar duk inda maɓuɓɓugan ruwa suke, da inda fadamu suke duka, watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa waɗansu.”

6 Saboda haka suka rabu biyu don su zagaya. Ahab ya bi waje guda, shi kuma ya bi ɗaya wajen.

7 Sa’ad da Obadiya yake tafiya a hanya suka yi kaciɓis da Iliya, Obadiya kuwa ya rabe da shi, sai ya rusuna ya ce, “Shugabana Iliya, kai ne kuwa?”

8 Iliya ya amsa masa ya ce, “Ni ne. Tafi, ka faɗa wa shugabanka, sarki, cewa ga ni nan.”

9 Obadiya ya ce, “Wane laifi na yi, har da za ka ba da ni a hannun Ahab ya kashe ni?

10 Na rantse da Ubangiji Allahnka mai rai, ba al’umma ko mulki da shugabana sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka nan, sai ya sa mulkin ko al’ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.

11 Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa masa, cewa ga ka a nan?

12 Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji.

13 Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa’ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su.

14 Yanzu kuwa ka ce, in tafi in faɗa wa sarki Ahab, cewa ga ka nan, ai, zai kashe ni.”

15 Iliya kuwa ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji Mai Runduna, wanda nake tsaye a gabansa, hakika zan nuna kaina gare shi yau.”

16 Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.

17 Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne, wanda kake wahalar da Isra’ila?”

18 Iliya kuwa ya amsa ya ce, “Ban wahalar da Isra’ila ba, kai ne da tsohonka, gama kuna ƙin bin umarnan Ubangiji, kuna yi wa Ba’al sujada.

19 Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra’ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba’al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtarot kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel take kula da su.”

Iliya da Annabawan Ba’al

20 Sai Ahab ya aika wa dukan jama’ar Isra’ila, ya tattara annabawa ɗin tare da su a dutsen Karmel.

21 Iliya kuwa ya zo kusa da jama’a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba’al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba.

22 Sa’an nan ya ce wa jama’a, “Ni kaɗai ne annabin Ubangiji da ya ragu, amma annabawan Ba’al ɗari huɗu ne da hamsin.

23 To, a ba mu bijimi biyu, su su zaɓi guda su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa a kan itacen wuta, amma kada su kunna masa wuta. Ni kuma zan shirya ɗaya bijimin, in shimfiɗa bisa itacen wuta ba kuwa zan kunna masa wuta ba.

24 Za ku yi kira ga sunan Ba’al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.”

Jama’a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.

25 Sa’an nan Iliya ya ce wa annabawan Ba’al, “Ku zaɓi bijimi guda, ku shirya shi da farko, gama kuna da yawa, sa’an nan ku yi kira ga sunan Ba’al ɗinku, amma fa kada ku kunna wuta. ”

26 Suka kuwa kama bijimin da aka ba su, suka gyara shi suka yi ta kira ga sunan Ba’al tun da safe, har tsakar ranar suna ta cewa, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma ba murya, ba kuwa wanda ya amsa. Suka yi ta tsalle a wajen bagaden da suka gina.

27 Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi musu ba’a, ya ce musu, “Ku kira da babbar murya, gama shi wani allah ne, watakila yana tunani ne, ko kuwa ya zagaya ne, ko kuma ya yi tafiya. Watakila kuma yana barci ne, sai a tashe shi.”

28 Suka yi ta kira da ƙarfi bisa ga al’adarsu, suna kuma tsattsaga jikunansu da wuƙaƙe, jini yana ta zuba.

29 Suka yi ta sambatu har azahar, lokacin ba da hadaya, amma ba muryar kowa, ba amsa, ba wanda ya kula.

30 Sa’an nan Iliya ya ce wa jama’a duka su zo kusa da shi. Jama’a duka kuwa suka zo kusa da shi. Sai ya gyara bagaden Ubangiji wanda aka lalatar.

31 Ya ɗibi duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan kabilan ‘ya’yan Yakubu, wanda Ubangiji ya ce masa, “Za a kira sunanka Isra’ila.”

32 Ya kuwa gina bagade da duwatsun da sunan Ubangiji. Ya kuma haƙa wuriya kewaye da bagaden, za ta ci kamar misalin garwar ruwa guda.

33 Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Sa’an nan ya ce a cika tuluna huɗu da ruwa, a kwarara a kan hadaya ta ƙonawar da kan itacen.

34 Ya kuma sa a kwarara sau na biyu, suka kwarara sau na biyun. Ya ce kuma a kwarara sau na uku, sai suka kwarara sau na ukun.

35 Ruwa kuwa ya malale bagaden, ya cika wuriyar da aka haƙa.

36 A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra’ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra’ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka.

37 Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”

38 Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.

39 Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka rusuna suka sunkuyar da kai suka ce, “Ubangiji shi ne Allah, Ubangiji shi ne Allah.”

40 Iliya kuma ya ce musu, “Ku kama annabawan Ba’al, kada ku bar ko ɗaya ya tsere.” Iliya kuwa ya kai su rafin Kishon, ya karkashe su a can.

Ƙarshen Fari

41 Iliya kuwa ya ce wa Ahab, “Sai ka haura ka ci ka sha, gama akwai motsin sakowar ruwan sama.”

42 Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha, Iliya kuwa ya hau can ƙwanƙolin Karmel, ya zauna ƙasa, ya haɗa kai da gwiwa.

43 Sa’an nan ya ce wa baransa, “Ka tafi ka duba wajen teku.”

Baran kuwa ya tafi ya duba, ya komo ya ce, “Ban ga kome ba.”

Sai ya ce, “Ka yi tafiya kana dubawa, har sau bakwai.”

44 A zuwa na bakwai sai ya ce, “Na ga wani ɗan girgije kamar tafin hannu yana tasowa daga teku.”

Iliya kuma ya ce, “Tafi, ka faɗa wa Ahab ya shirya karusarsa ya sauka don kada ruwan sama ya hana shi sauka.”

45 Jim kaɗan sai sararin sama ya yi baƙi ƙirin da gizagizai da iska, aka yi ruwan sama mai yawan gaske. Ahab kuwa ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel.

46 Ubangiji kuwa ya saukar wa Iliya da iko, ya sha ɗamara, ya sheka a guje, ya riga Ahab isa Yezreyel.

Categories
1 SAR

1 SAR 19

Iliya a Dutsen Sinai

1 Ahab kuwa ya faɗa wa Yezebel dukan abin da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe annabawan Ba’al duka.

2 Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”

3 Sai Iliya ya ji tsoro, ya tashi, ya tsere zuwa Biyer-sheba ta Yahuza.

Ya bar baransa a can.

4 Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”

5 Iliya kuwa ya kwanta, ya yi ta barci a gindin itacen. Farat sai mala’ika ya taba shi, ya ce masa, “Tashi, ka ci abinci.”

6 Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa.

7 Mala’ikan Ubangiji kuma ya sake zuwa sau na biyu, ya taɓa shi, ya ce, “Tashi, ka ci abinci, in ba haka ba kuwa tafiya za ta gagare ka.”

8 Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa’an nan ya kama tafiya kwana arba’in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.

9 A can ya shiga wani kogo domin ya kwana.

Ba labari sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”

10 Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama’ar Isra’ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”

11 Ubangiji ya ce masa, “Tafi, ka tsaya a kan dutse, a gabana.” Sai ga Ubangiji yana wucewa, babbar iska mai ƙarfi ta tsage dutsen, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasar.

12 Bayan girgizar kuma, sai wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wutar. Bayan wutar sai ƙaramar murya.

13 Sa’ad da Iliya ya ji muryar, sai ya rufe fuskarsa da alkyabbarsa, ya fita, ya tsaya a bakin kogon. Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”

14 Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama’ar Isra’ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”

15 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka juya zuwa jeji kusa da Dimashƙu, idan ka isa can, sai ka zuba wa Hazayel mai, ka keɓe shi, ya sama Sarkin Suriya,

16 da Yehu ɗan Nimshi, ka keɓe shi, ya zama Sarkin Isra’ila. Ka kuma zuba wa Elisha, ɗan Shafat na Abel-mehola, mai, ka keɓe shi, ya zama annabi a maimakonka.

17 Duk wanda zai tsere wa Hazayel, Yehu zai kashe shi. Wanda kuma ya tsere wa Yehu. Elisha zai kashe shi.

18 Duk da haka zan rage mutum dubu bakwai(7,000) na Isra’ila waɗanda ba su rusuna wa Ba’al da gwiwoyinsu ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”

An Kira Elisha

19 Iliya fa ya tashi daga wurin nan, ya tarar da Elisha ɗan Shafat, yana tare da shanu, garma goma sha biyu. Yana tare da na sha biyun, sai Iliya ya bi ta kusa da shi, ya jefa masa alkyabbarsa.

20 Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa’an nan in zo in bi ka.”

Sa’an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”

21 Elisha kuwa ya koma, ya kama shanun noman, ya yanka, ya dafa su da karkiyoyinsu. Ya raba wa mutane, suka ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya zama mai taimakonsa.

Categories
1 SAR

1 SAR 20

Ahab Ya Ci Suriyawa

1 Ben-hadad Sarkin Suriya kuwa ya tara dukan sojojinsa. Sarakuna talatin da biyu kuma suna tare da shi, da dawakai, da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya yaƙi. Ya kuwa yi yaƙi da ita.

2 Sai ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin sarki Ahab na Isra’ila, ya ce masa, “In ji Ben-hadad,

3 ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne, matanka kuma mafi kyau da ‘ya’yanka nawa ne!’ ”

4 Ahab Sarkin Isra’ila kuwa ya amsa, ya ce, “Ya maigirma sarki, kamar yadda ka faɗa, ni naka ne da dukan abin da nake da shi.”

5 Jakadun kuwa suka sāke komawa suka ce wa Ahab, “Ben-hadad ya ce, ‘Na aika maka ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka, da ‘ya’yanka.

6 Banda haka kuma zan aiko barorina wurinka gobe war haka su bincike gidanka da gidajen fādawanka, su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi da su.’ ”

7 Ahab Sarkin Isra’ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da ‘ya’yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”

8 Dukan dattawan da mutane, suka ce masa, “Kada ka kula, balle ka yarda.”

9 Sai ya ce wa jakadun Ben-hadad, “Ku ce wa maigirma, sarki, dukan abin da ya nema a wurina da farko, zan yi, amma wannan na ƙarshe, ban zan iya yi ba.”

Jakadun kuwa suka koma da wannan labari.

10 Ben-hadad kuwa ya sāke aikawa wurinsa ya ce, “Bari alloli su kashe ni idan ban kai mutane da yawa da za su hallaka Samariya ba.”

11 Sarki Ahab ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa’an nan ya yi fāriya, amma ba tun kafin a fara ba.”

12 Da Ben-hadad ya ji wannan saƙo sa’ad da yake sha tare da sarakuna a sansani, sai ya ce wa mutanensa, “Kowa ya tsaya a wurinsa.” Sai kowa ya tsaya a wurinsa don yin yaƙi da birnin.

13 Ba da jimawa ba, sai ga annabi ya zo wurin sarki Ahab na Isra’ila, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan babban taron sojoji? Zan ba da su a hannunka yau, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”

14 Ahab ya ce, “Wane ne zai yi jagorar yaƙin?”

Annabin ya ce, “Ubangiji ya ce, sojoji matasa, wato na hakiman larduna, za su yi yaƙin.”

Sarki ya ce, “Wa zai yi jagorar babbar rundunar?”

Annabin ya ce, “Kai ne.”

15 Sai ya tara sojoji matasa na hakiman larduna, mutum ɗari biyu da talatin da biyu. Sa’an nan kuma, ya tara dukan mutanen Isra’ila dubu bakwai (7,000).

16 Suka tafi da tsakar rana sa’ad da Ben-hadad yake a buge da sha a sansani, shi da sarakuna talatin da biyu waɗanda suka taimake shi.

17 Samarin ne suka fara fita. Sai Ben-hadad ya aiki mutane, suka faɗa masa cewa, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”

18 Sai ya ce, “Ku kama su da rai, ko sun zo da nufin salama ko da na yaƙi.”

19 Waɗannan kuwa suka fita daga birnin, wato sojoji matasa, rundunar Isra’ilawa kuma tana biye da su,

20 kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra’ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.

21 Sarkin Isra’ila ya fita, ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Suriyawa da yawa.

22 Sa’an nan annabin ya je wurin Sarkin Isra’ila, ya ce masa, “Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka yi tunani sosai a kan abin da za ka yi, gama da juyawar shekara Sarkin Suriya zai kawo maka yaƙi.”

Suriyawa Sun Kai Yaƙi na Biyu

23 Fādawan Sarkin Suriya suka ce masa, “Allolinsu na tuddai ne, don haka suka fi mu ƙarfi, bari mu yi yaƙi da su a cikin kwari, ta haka za mu ci su ba shakka.

24 Yanzu abin da za ka yi ke nan, sai ka fitar da sarakuna daga matsayinsu, ka sa shugabannin sojoji maimakonsu.

25 Sa’an nan ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa, ka kuma tara dawakai a maimakon na dā, da karusai a maimakon karusai na dā. Mu kuwa za mu yi yaƙi da su a kwari. Ba shakka za mu ci su.”

Sarki Ben-hadad ya ji maganarsu, ya kuwa yi haka nan.

26 Da shekara ta juyo, sai Ben-hadad ya tara Suriyawa, suka haura zuwa Afek don su yi yaƙi da Isra’ilawa.

27 Aka tara mutanen Isra’ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar ‘yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.

28 Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra’ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama’a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.’ ”

29 Suka kafa sansani daura da juna kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin, suka kama yaƙi. Isra’ilawa suka kashe Suriyawa mutum dubu ɗari (100,000) a rana ɗaya.

30 Sauran kuwa suka gudu zuwa birnin Afek. Garun birnin kuma ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai (27,000) waɗanda suka ragu.

Ben-hadad kuwa ya gudu ya shiga ƙurewar ɗaki, a cikin birnin.

31 Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin Sarkin Isra’ila, watakila zai bar ka da rai.”

32 Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra’ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.”

Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan’uwana ne.”

33 Da ma abin da fādawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad.”

Sarki Ahab ya ce musu, “Ku je ku kawo shi.” Ben-hadad kuwa ya zo wurinsa. Ahab ya sa ya shiga tare da shi cikin karusarsa.

34 Ben-hadad ya ce masa, “Biranen da tsohona ya ƙwace daga wurin tsohonka, zan mayar maka. Kai kuma za ka yi karauku a Dimashƙu kamar yadda tsohonka ya yi a Samariya.”

Sai Ahab ya ce, “Zan bar ka, ka tafi a kan wannan sharaɗi.” Ya kuwa yi alkawari da shi, sa’an nan ya bar shi, ya tafi.

Annabi Ya Soki Ahab

35 Ubangiji ya umarci wani daga cikin annabawa ya ce wa abokinsa bisa ga umarnin Ubangiji, “Ina roƙonka ka buge ni.” Abokinsa kuwa ya ƙi ya buge shi.

36 Sai annabin ya ce wa wannan aboki, “Da yake ba ka yi biyayya da muryar Ubangiji ba, da tashinka daga wurina, zaki zai kashe ka.” Da ya tashi daga wurinsa, sai zaki ya gamu da shi, ya kashe shi.

37 Annabin kuma ya tarar da wani mutum, ya ce masa, “Ina roƙonka ka buge ni.” Mutumin kuwa ya buge shi da ƙarfi ya rotsa shi.

38 Sai annabin ya ɓad da kama, ya ɗaure fuskarsa da ƙyalle, ya tafi, ya jira sarki a hanya.

39 Sa’ad da sarki yake wucewa, sai ya kira sarki, ya ce, “Ni baranka na tafi yaƙi, sai ga shi, soja ya kawo mini mutum, ya ce mini, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi ya kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’

40 Da na shiga fama da kai da kawowa sai mutumin ya tsere.”

Sai Sarkin Isra’ila ya ce masa, “Haka shari’arka za ta zama, gama kai da kanka ka yanke shari’ar.”

41 Annabin ya yi saurim, ya kware ƙyallen a fuskarsa, sa’an nan sarki ya gane, ashe, ɗaya daga cikin annabawa ne.

42 Sa’an nan annabin ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ka bar mutumin da na ƙaddara ga mutuwa ya kuɓuta daga hannunka, haka ranka zai zama a maimakon nasa, mutanenka kuwa a maimakon mutanensa.’ ”

43 Sarkin Isra’ila kuwa ya tafi gidansa a Samariya da baƙin ciki.