Categories
1 TAR

1 TAR 1

Zuriyar Nuhu

1 Adamu ya haifi Shitu, Shitu ya haifi Enosh,

2 Enosh ya haifi Kenan, Kenan ya haifi Mahalalel, Mahalalel ya haifi Yared,

3 Yared ya haifi Anuhu, Anuhu ya haifi Metusela, Metusela ya haifi Lamek.

4 Lamek ya haifi Nuhu, Nuhu ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.

Zuriyar Yafet Nuhu

5 ‘Ya’yan Yafet, maza ke nan, Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras.

6 ‘Ya’yan Gomer, maza, su ne Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.

7 ‘Ya’yan Yawan, maza, su ne Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim.

Zuriyar Ham

8 ‘Ya’yan Ham, maza, su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan’ana.

9 ‘Ya’yan Kush, maza, su ne Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra’ama, da Sabteka. ‘Ya’yan Ra’ama, maza, su ne Sheba da Dedan.

10 Kush shi ne mahaifin Lamirudu wanda shi ne ya fara ƙasaita a duniya.

11 Mizrayim shi ne mahaifin jama’ar Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Naftuhawa,

12 da Fatrusawa, da Kasluhawa tushen Filistiyawa ke nan, da Kaftorawa.

13 Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Het,

14 da Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,

15 da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa,

16 da Arwadiyawa, da Zemariyawa, da Hamatiyawa.

Zuriyar Shem

17 ‘Ya’yan Shem, maza, su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram, da Uz, da Hul, da Geter, da Meshek.

18 Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuma shi ne mahaifin Eber.

19 ‘Ya’ya biyu maza ne aka haifa wa Eber. Sunan ɗayan Feleg, saboda a lokacinsa ne aka karkasa duniya, sunan ɗan’uwansa kuwa Yokatan.

20 Yokatan shi ne mahaifin Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera,

21 da Adoniram, da Uzal, da Dikla,

22 da Ebal, da Abimayel, da Sheba,

23 da Ofir, da Hawila, da Yobab. Waɗannan duka su ne ‘ya’yan Yokatan, maza.

24 Shem ya haifi Arfakshad, Arfakshad ya haifi Shela,

25 Shela ya haifi Eber, Eber ya haifi Feleg, Feleg ya haifi Reyu,

26 Reyu ya haifi Serug, Serug ya haifi Nahor, Nahor ya haifi Tera,

27 Tera ya haifi Abram, wato Ibrahim ke nan.

Zuriyar Isma’ilu da Ketura

28 ‘Ya’yan Ibrahim, maza, su ne Ishaku da Isma’ilu.

29 Ga zuriyarsu. Nabayot shi ne ɗan farin Isma’ilu, sa’an nan sai Kedar, da Abdeyel, da Mibsam,

30 da Mishma, da Duma, da Massa, da Hadad, da Tema,

31 da Yetur, da Nafish, da Kedema. Waɗannan su ne ‘ya’yan Isma’ilu, maza.

32 ‘Ya’ya maza na Ketura, wato ƙwarƙwarar Ibrahim, su ne Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. ‘Ya’yan Yokshan, maza, su ne Sheba, da Dedan.

33 ‘Ya’yan Madayana, maza, su ne Efa, da Efer, da Hanok, da Abida, da Eldaya. Waɗannan duka su ne ‘ya’yan Ketura, maza.

Zuriyar Isuwa

34 Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ‘Ya’yan Ishaku, maza, su ne Isuwa da Isra’ila.

35 ‘Ya’yan Isuwa, maza, su ne Elifaz, da Reyuwel, da Yewush, da Yalam da Kora.

36 ‘Ya’yan Elifaz, maza, su ne Teman, da Omar, da Zeho, da Gatam, da Kenaz, da Tima, da Amalek.

37 ‘Ya’yan Reyuwel, maza kuwa, su ne Nahat, da Zera, da Shamma, da Mizza.

38 ‘Ya’yan Seyir, maza kuma, su ne Lotan, da Shobal, da Zibeyon, da Ana, da Dishon, da Ezer, da kuma Dishan.

39 ‘Ya’yan Lotan, maza, su ne Hori, da Hemam. Timna ce ‘yar’uwar Lotan.

40 ‘Ya’yan Shobal, maza, su ne Alwan, da Manahat, da Ebal, da Sheho, da Onam.

‘Ya’yan Zibeyon, maza su ne Aiya da Ana.

41 Dishon shi ne ɗan Ana. ‘Ya’yan Dishon, maza kuwa, su ne Hemdan, da Eshban, da Yitran, da Keran.

42 ‘Ya’yan Ezer, maza, su ne Bilhan, da Zayawan, da Akan. ‘Ya’yan Dishan, maza, su ne Uz da Aran.

43-50 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a ƙasar Edom kafin wani Sarkin Isra’ila ya ci sarauta.

Bela ɗan Beyor, sunan birninsa kuwa Dinhaba

Yobab ɗan Zera na Bozara

Husham na ƙasar Teman

Hadad ɗan Bedad na Awit, wanda ya kori Madayanawa a filin Mowab

Samla na Masrek

Shawul na Rehobot wadda take bakin Kogin Yufiretis

Ba’al-hanan ɗan Akbor

Hadad na Fau, sunan matarsa kuma Mehetabel ‘yar Matred, wato jikar Mezahab

51 Hadad kuwa ya rasu. Sarakunan Edom su ne Timna, da Alwa, da Yetet,

52 da Oholibama, da Ila, da Finon,

53 da Kenaz, da Teman, da Mibzar,

54 da Magdiyel, da Iram.

Categories
1 TAR

1 TAR 2

‘Ya’yan Isra’ila

1 Waɗannan su ne ‘ya’yan Isra’ila, maza, Ra’ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza, da Issaka, da Zabaluna,

2 da Dan, da Yusufu, da Biliyaminu, da Naftali, da Gad, da Ashiru.

Zuriya Yahuza

3 ‘Ya’yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela. Waɗannan uku Batshuwa Bakan’aniya, ita ce ta haifa masa su. Amma Er, ɗan farin Yahuza, mugu ne a gaban Ubangiji, don haka Ubangiji ya kashe shi.

4 Surukarsa Tamar, matar ɗansa kuma ta haifa masa Feresa da Zera. Yahuza yana da ‘ya’ya maza biyar.

5 ‘Ya’yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.

6 ‘Ya’yan Zera, maza, su ne Zabdi da Etan, da Heman, da Kalkol, da Darda. Su biyar ke nan.

7 Karmi shi ne mahaifin Akan wanda ya jawo wa Isra’ila wahala a kan abin da aka haramta.

8 Etan yana da ɗa guda ɗaya, shi ne Azariya.

9 ‘Ya’yan Hesruna, maza, waɗanda aka haifa masa, su ne Yerameyel, da Arama, da kuma Kalibu.

10 Arama shi ne mahaifin Amminadab. Amminadab kuma shi ne mahaifin Nashon, shugaban ‘ya’yan Yahuza.

11 Nashon shi ne mahaifin Salmon. Salmon kuwa shi ne mahaifin Bo’aza.

12 Bo’aza kuma shi ne mahaifin Obida. Obida shi ne mahaifin Yesse.

13 Yesse shi ne mahaifin Eliyab ɗan farinsa, sa’an nan sai Abinadab da Shimeya,

14 da Netanel, da Raddai,

15 da Ozem, da Dawuda. Su ‘ya’ya maza bakwai ke nan.

16 ‘Yan’uwansu mata kuwa su ne Zeruya da Abigail.

‘Ya’yan Zeruya, maza, su ne Abishai, da Yowab, da Asahel, su uku ke nan.

17 Abigail ta haifi Amasa. Mahaifin Amasa shi ne Yeter daga zuriyar Isma’ilu.

18 Azuba, matar Kalibu ɗan Hesruna ta haifa masa ‘ya’ya maza. Matarsa Yeriyot kuma ta haifi ‘ya’ya maza, su ne Yesher, da Shobab, da Ardon.

19 Sa’ad da Azuba ta rasu sai Kalibu ya auri Efrata wadda ta haifa masa Hur.

20 Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuwa shi ne mahaifin Bezalel.

21 Bayan haka sai Hesruna ya shiga wurin ‘yar Makir mahaifin Gileyad, wadda ya aura sa’ad da yake da shekara sittin da haihuwa. Ta haifa masa Segub.

22 Segub shi ne mahaifin Yayir wanda yake da birane ashirin da uku a ƙasar Gileyad.

23 Amma sai Geshur da Aram suka ƙwace garuruwan Hawwotyayir ɗin daga gare su, har da Kenat da ƙauyukanta, garuruwa sittin. Duk waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.

24 Bayan rasuwar Hesruna, Abaija, matarsa, ta haifa masa Ashur, mahaifin Tekowa.

25 ‘Ya’yan Yerameyel ɗan farin Hesruna, su ne Arama ɗan fari, sa’an nan Buna, da Oren, da Ozem, da Ahaija.

26 Sai Yerameyel ya auro wata mace, sunanta Atara. Ita ce mahaifiyar Onam.

27 ‘Ya’yan Arama, ɗan farin Yerameyel, su ne Ma’az, da Yamin, da Eker.

28 ‘Ya’yan Onam, maza, su ne Shammai da Yada. ‘Ya’yan Shammai, maza, su ne Nadab da Abishur.

29 Sunan matar Abishur Abihail, ta haifa masa Aban da Molid.

30 ‘Ya’yan Nadab, maza, su ne Seled da Affayim, amma Seled ya rasu bai bar ‘ya’ya ba.

31 Ɗan Affayim shi ne Ishi. Ɗan Ishi kuwa shi ne Sheshan. Ɗan Sheshan shi ne Alai.

32 ‘Ya’yan Yada, maza, ɗan’uwan Shammai, su ne Yeter da Jonatan. Amma Yeter ya rasu bai bar ‘ya’ya ba.

33 ‘Ya’yan Jonatan su ne Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.

34 Sheshan ba shi da ‘ya’ya maza, sai dai ‘ya’ya mata. Amma yana da wani bara Bamasare mai suna Yarha.

35 Sai Sheshan ya aurar wa Yarha baransa da ‘yarsa, ita kuwa ta haifar masa Attai.

36 Attai shi ne mahaifin Natan, Natan kuma shi ne mahaifin Zabad.

37 Zabad kuwa shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne ya haifi Obida.

38 Obida shi ne mahaifin Yehu, Yehu kuma shi ne mahaifin Azariya.

39 Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa.

40 Eleyasa shi ne mahaifin Sisamai, Sisamai shi ne mahaifin Shallum.

41 Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya shi ne mahaifin Elishama.

42 Ɗan Kalibu, ɗan’uwan Yerameyel, shi ne Mesha ɗan farinsa wanda ya haifi Zif. Zif ya haifi Maresha wanda ya haifi Hebron.

43 ‘Ya’yan Hebron, maza, su ne Kora, da Taffuwa, da Rekem, da Shema.

44 Shema shi ne mahaifin Raham wanda ya kafa Yorkeyam. Rekem kuwa shi ne mahaifin Shammai.

45 Shammai shi ne mahaifin Mayon, Mayon kuwa shi ne mahaifin Bet-zur.

46 Efra ƙwarƙwarar Kalibu, ta haifi Haran, da Moza, da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.

47 ‘Ya’yan Yadai, maza, su ne Regem, da Yotam, da Geshan, da Felet, da Efa, da Sha’af.

48 Ma’aka, ƙwarƙwarar Kalibu, ta haifi Sheber da Tirhana.

49 Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna, da Shewa mahaifin Makbena, da mahaifin Gibeya.

‘Yar Kalibu ita ce Aksa.

50 Waɗannan su ne zuriyar Kalibu, maza.

‘Ya’yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, su ne Shobal wanda ya kafa Kiriyat-yeyarim,

51 da Salma, shi kuwa ya kafa Baitalami, da Haref ɗansa kuma wanda ya kafa Bet-gader.

52 Shobal yana da waɗansu ‘ya’ya maza, su ne Rewaiya da wanda yake kakan rabin Manahatiyawa,

53 da iyalan da suke a Kiriyat-yeyarim, da na Itiriyawa, da na Futiyawa, da na Shumatiyawa, da na Mishraiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.

54 Salma, wanda ya kafa Baitalami, shi ne kakan mutanen Netofa, da na Atarot-bet-yowab, da rabin Manahatiyawa, da Zoratiyawa.

55 Iyalan gwanayen rubutu waɗanda suka zauna a Yabez, su ne Tiratiyawa, da Shimeyatiyawa, da Sukatiyawa. Su ne Keniyawa na Hammat, Hammat kuwa shi ne mahaifin mutanen Rekab.

Categories
1 TAR

1 TAR 3

‘Ya’yan Dawuda

1-3 Waɗannan su ne ‘ya’yan Dawuda, maza, waɗanda aka haifa masa a Hebron.

Amnon wanda Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa.

Kileyab wanda Abigail Bakarmeliya ta haifa masa.

Absalom ɗan Ma’aka ‘yar Talmai, Sarkin Geshur.

Adonaija ɗan Haggit.

Shefatiya wanda Abital ta haifa.

Itireyam wanda Egla ta haifa.

4 Dukansu shida an haife su ne a Hebron inda ya yi sarauta shekara bakwai da wata shida.

Ya yi sarauta a Urushalima shekara talatin da uku.

5 Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba ‘yar Ammiyel ta haifa masa.

6 Yana da waɗansu ‘ya’ya kuma, su ne Ibhar, da Elishuwa da Elifelet,

7 da Noga, da Nefeg, da Yafiya,

8 da Elishama, da Eliyada, da kuma Elifelet, su tara ke nan.

9 Waɗannan duka su ne ‘ya’yan Dawuda, maza, banda ‘ya’yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce ‘yar’uwarsu.

Zuriyar Sulemanu

10 Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat,

11 da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,

12 da Amaziya, da Azariya, da Yotam,

13 da Ahaz, da Hezekiya da Manassa,

14 da Amon, da Yosiya.

15 ‘Ya’yan Yosiya, maza, su ne Yohenan ɗan farinsa, na biyu shi ne Eliyakim, na uku shi ne Zadakiya, na huɗu shi ne Yehowahaz,

16 Eliyakim yana da ‘ya’ya biyu maza, su ne Yekoniya, da Zadakiya.

17 ‘Ya’yan Yekoniya wanda aka kama, su ne Sheyaltiyel,

18 da Malkiram, da Fedaiya, da Shenazzar, da Yekamiya, da Hoshama, da Nedabiya.

19 Fedaiya yana da ‘ya’ya biyu maza, su ne Zarubabel da Shimai. ‘Ya’yan Zarubabel, maza, su ne Meshullam, da Hananiya, da Shelomit ‘yar’uwarsu,

20 da Hashuba, da Ohel, da Berikiya, da Hasadiya, da Yushab-hesed, su biyar ke nan.

21 ‘Ya’yan Hananiya, maza, su ne Felatiya, da Yeshaya, da ‘ya’yan Refaya, maza, da ‘ya’yan Arnan, maza, da ‘ya’yan Obadiya, maza, da ‘ya’yan Shekaniya, maza.

22 Ɗan Shekaniya shi ne Shemaiya. ‘Ya’yan Shemaiya, maza, su ne Hattush, da Igal, da Bariya da Neyariya, da Shafat, su shida ke nan.

23 ‘Ya’yan Neyariya, maza, su ne Eliyehoyenai, da Hezekiya, da Azrikam, su uku ne nan.

24 ‘Ya’yan Eliyehoyenai, maza, su ne Hodawiya, da Eliyashib, da Felaya, da Akkub, da Yohenan, da Dalaya, da Anani, su bakwai ke nan.

Categories
1 TAR

1 TAR 4

Zuriyar Yahuza

1 ‘Ya’yan Yahuza, maza, su ne Feresa, da Hesruna, da Karmi, da Hur, da Shobal.

2 Rewaiya ɗan Shobal, shi ne mahaifin Yahat. Yahat shi ya haifi Ahumai, da Lahad. Waɗannan su ne iyalin Zoratiyawa.

3 Waɗannan kuma su ne ‘ya’yan Itam, Yezreyel, da Ishma, da Idbasha, da ‘ya ɗaya, ita ce Hazzelelfoni.

4 Feniyel shi ne mahaifin Gedor, Ezer kuwa shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne ‘ya’yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, zuriyarsa ne suka kafa Baitalami.

5 Ashur, wanda ya kafa Tekowa, yana da mata biyu, su ne Hela, da Nayara.

6 Nayara ta haifa masa Ahuzzam, da Hefer, da Temeni, da Hayahashtari. Waɗannan su ne ‘ya’yan Nayara, maza.

7 ‘Ya’yan Hela, maza, su ne Zeret, da Izhara, da Etnan.

8 Hakkoz shi ne mahaifin Anub, da Zobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.

9 Yabez ya fi sauran ‘yan’uwansa kwarjini saboda haka mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, wato da wahala ta haife shi.

10 Yabez ya roƙi Allah na Isra’ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.

11 Kalibu ɗan’uwan Shuwa, shi ne mahaifin Mehir wanda ya haifi Eshton.

12 Eshton kuwa shi ne ya haifi Bet-rafa, da Faseya, da Tehinna wanda ya kafa birnin Ir-nahash, zuriyar waɗannan mutane kuwa su suka zauna a Reka.

13 ‘Ya’yan Kenaz, maza, su ne Otniyel da Seraiya. Yana kuma da waɗansu ‘ya’ya maza, su ne Hatata da Meyonotai.

14 Meyonotai kuwa shi ne mahaifin Ofra.

Seraiya shi ne ya haifi Yowab, Yowab ya kafa kwarin Ge-harashim, saboda su masu sana’a ne.

15 ‘Ya’yan Kalibu, maza, ɗan Yefunne, su ne Airu, da Ila, da Na’am. Ila shi ya haifi Kenaz.

16 ‘Ya’yan Yehallelel, maza, su ne Zif, da Zifa, da Tiriya, da Asarel.

17-18 ‘Ya’yan Ezra, maza, su ne Yeter, da Mered, da Efer, da Yalon. Bitiya ‘yar Fir’auna, wadda Mered ya aura, ta haifi waɗannan, Maryamu, da Shammai, da Ishaba wanda ya haifi Eshtemowa. Mered kuma ya auri wata daga kabilar Yahuza, ta haifi Yered wanda ya kafa garin Gedor. Eber kuma ya kafa garin Soko, Yekutiyel kuwa ya kafa garin Zanowa.

19 ‘Ya’ya maza na matar Hodiya ‘yar’uwar Naham, su ne suka zama kakannin Kaila, Bagarme, da Eshtemowa da suke zaune a Ma’aka.

20 ‘Ya’yan Shimon, maza, su ne Amnon, da Rinna, da Ben-hanan, da Tilon.

‘Ya’yan Ishi, maza kuwa, su ne Zohet da Ben-zohet.

21 ‘Ya’yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La’ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,

22 da Yokim, da mutanen da suke zaune a Kozeba, da Yowash, da Saraf, waɗanda suka yi sarauta a Mowab, sa’an nan suka zauna a Baitalami. (Waɗannan labaru na tun dā ne.)

23 Su ne maginan tukwane, waɗanda suke zaune a Netayim da Gedera. Sun zauna tare da sarki don su yi masa aiki.

Zuriyar Saminu

24 ‘Ya’yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, da Zohar, da Shawul,

25 da Shallum ɗansa, da Mibsam jīkansa, da Mishma jīkan ɗansa.

26 ‘Ya’yan Mishma, maza, su ne Hammuwel, da Zakkur, da Shimai.

27 Shimai yana da ‘ya’ya maza goma sha shida, da ‘ya’ya mata shida, amma ‘yan’uwansa ba su da ‘ya’ya da yawa kamarsa. Iyalin Saminu ba su kai yawan na Yahuza ba.

28 Suka zauna a waɗannan garuruwa, wato Biyer-sheba, da Molada, da Hazar-shuwal,

29 da Bilha, da Ezem, da Eltola,

30 da Betuwel, da Horma, da Ziklag,

31 da Bet-markabot, da Hazarsusa, da Bet-biri, da Shayarim. Waɗannan su ne biranensu tun kafin Dawuda ya yi sarauta.

32-33 Sun kuwa zauna a waɗansu wurare guda biyar, wato Itam, da Ayin, da Rimmon, da Token, da Ashan, da ƙauyukan da suke kewaye, har zuwa kudu maso gabas da garin Ba’al: Ga lissafin iyalansu da wuraren da suka zauna.

34-37 Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya,

Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya, wato jīkan Seraiya, ɗan Asiyel,

Eliyehoyenai, da Ya’akoba, da Yeshohaya, da Asaya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benaiya,

Ziza ɗan Shifi, wato jīkan Allon, zuriyar Yedaiya, da Shimri ɗan Shemaiya.

38 Waɗannan da aka jera sunayensu, su ne shugabannin iyalansu da gidajen kakanninsu.

Sun ƙaru ƙwarai.

39 Suka yi tafiya har zuwa mashigin Gedor, zuwa gabashin kwarin don nemar wa garkunansu makiyaya.

40 A can suka sami makiyaya mai kyau mai dausayi. Ƙasar kuwa tana da faɗi, babu fitina, sai salama, gama mazaunan wurin a dā Hamawa ne.

41 Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa’an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.

42 Waɗansu daga cikinsu, mutum ɗari biyar daga zuriyar Saminu, suka tafi wajen gabashin Edom. Waɗanda suka shugabance su kuwa, su ne ‘ya’yan Ishi, wato Felatiya, da Neyariya, da Refaya, da Uzziyel.

43 A can suka karkashe sauran Amalekawan da suka ragu, sa’an nan suka zauna a can har wa yau.

Categories
1 TAR

1 TAR 5

Zuriyar Ra’ubainu

1 Ra’ubainu shi ne ɗan farin Isra’ila, amma saboda ya ƙazantar da gadon mahaifinsa aka ba ‘ya’yan Yusufu, maza, ɗan Isra’ila, gādonsa na ɗan fari. Don haka ba a lasafta shi a kan matsayin ɗan fari ba.

2 Ko da yake Yahuza ya rinjayi ‘yan’uwansa, har daga gare shi aka sami shugaba, duk da haka matsayin ɗan farin na Yusufu ne.

3 ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza, wato ɗan farin Isra’ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.

4 ‘Ya’yan Yowel, maza, su ne Shemaiya, da Gog, da Shimai,

5 da Mika, da Rewaiya, da Ba’al,

6 da Biyera wanda Tiglat-filesar Sarkin Assuriya ya kai bauta. Shi ne shugaban Ra’ubainawa.

7 Danginsa bisa ga iyalansu da asalinsu a zamaninsu, su ne sarki Yehiyel, da Zakariya,

8 da Bela ɗan Azaz, wato jīkan Shema, ɗan Yowel, wanda ya zauna a Arower har zuwa Nebo da Ba’al-meyon.

9 Ya kuma zauna wajen gabas, har zuwa goshin jejin da yake wajen Kogin Yufiretis, saboda shanunsu sun ƙaru a ƙasar Gileyad.

10 Zuriyar Ra’ubainu suka yi yaƙi da Hagarawa a kwanakin Saul. Suka ci Hagarawa, saboda haka suka zauna a ƙasar da take gabashin Gileyad.

Zuriyar Gad

11 ‘Ya’yan Gad, maza, suka zauna a ƙasar Bashan, daura da Ra’ubainawa har zuwa Salka.

12 Yowel ne sarki, Shafam kuwa shi ne na biyun, da Yanai, da Shafat, su ne tushen Bashan.

13 Danginsu bisa ga gidajen kakanninsu, su ne Maikel, da Meshullam, da Sheba, da Yorai, da Jakan, da Ziya, da Eber, su bakwai ke nan.

14 Waɗannan su ne ‘ya’ya maza na Abihail ɗan Huri. Ga yadda kakanninsu suke, wato Abihail, ɗan Huri ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Maikel, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.

15 Ahi ɗan Abdiyel, wato jīkan Guni, shi ne shugaban gidan kakanninsu.

16 Suka zauna a Gileyad, da Bashan, da garuruwanta, da dukan iyakar makiyayar Sharon.

17 (An rubuta waɗannan duka bisa ga asalinsu a zamanin Yotam, Sarkin Yahuza, da Yerobowam Sarkin Isra’ila.)

Tarihin Kabilai Biyu da Rabi

18 ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa suna da jarumawa masu riƙon garkuwa da takobi, masu harbi kuma da baka. Gwanayen yaƙi ne, su dubu arba’in da huɗu, da ɗari bakwai da sittin ne (44,760).

19 Suka yi yaƙi da Hagarawa, da Yetur, da Nafish, da Nodab.

20 Aka taimake su yin yaƙi da abokan gābansu, sai aka ba da Hagarawa da duk waɗanda suke tare da su a hannunsu, saboda suka yi roƙo ga Allah a cikin yaƙin, Allah kuwa ya amsa musu roƙonsu saboda sun dogara gare shi.

21 Sai suka kwashe dabbobinsu, raƙuma dubu hamsin (50,000), da tumaki dubu ɗari biyu da dubu hamsin (250,000), da jakuna dubu biyu (2,000), da kuma mutane dubu ɗari (100,000).

22 Aka karkashe mutane da yawa, domin yaƙin na Allah ne. Sai suka gāje wurin zamansu, har lokacin da aka kai su bauta.

23 Mutanen rabin kabilar Manassa suna da yawa, sun zauna a ƙasar, daga Bashan har zuwa Ba’al-harmon, da Senir, da Dutsen Harmon.

24 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Efer, da Ishi, da Eliyel, da Azriyel, da Irmiya, da Hodawiya, da Yadiyel. Su jarumawa ne na gaske, masu suna, su ne shugabannin gidajen kakanninsu.

25 Amma mutanen suka yi rashin gaskiya ga Allah na kakanninsu, suka bi gumakan mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu.

26 Don haka Allah na Isra’ila ya zuga Ful, Sarkin Assuriya, wato Tiglat-filesar, ya zo ya kwashe su, ya kai su bauta, wato su Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa. Ya kai su Hala, da Habor, da Hara, har zuwa kogin Gozan, can suke har yau.

Categories
1 TAR

1 TAR 6

Zuriyar Manyan Firistoci

1 ‘Ya’yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.

2 ‘Ya’yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.

3 ‘Ya’yan Amram kuwa, su ne Haruna, da Musa, da Maryamu.

‘Ya’yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar.

4 Zuriyar Ele’azara daga tsara zuwa tsara, su ne Finehas, da Abishuwa,

5 da Bukki, da Uzzi,

6 da Zarahiya, da Merayot,

7 da Amariya, da Ahitub,

8 da Zadok, da Ahimawaz,

9 da Azariya, da Yohenan,

10 da Azariya wanda ya yi hidimar firist a Haikalin da Sulemanu ya gina a Urushalima.

11 Ga Amariya kuma da Ahitub,

12 da Zakok, da Meshullam,

13 da Hilkiya, da Azariya,

14 da Seraiya, da Yehozadak.

15 Sarki Nebukadnezzar ya kama Yehozadak, ya tafi da shi tare da sauran jama’a zuwa zaman talala, sa’ad da Ubangiji ya ba da su a hannun Nebukadnezzar don su yi zaman talala.

Sauran Zuriyar Lawi

16 ‘Ya’yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.

17 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Gershon, maza, Libni da Shimai.

18 ‘Ya’yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.

19 ‘Ya’yan Merari, maza kuwa, su ne Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawiyawa bisa ga gidajen kakanninsu.

20 Zuriyar Gershon bi da bi, su ne Libni, da Yahat, da Zimma,

21 da Yowa, da Iddo, da Zera, da Yewaterai.

22 Zuriyar Kohat bi da bi, su ne Izhara, da Kora, da Assir,

23 da Elkana, da Ebiyasaf, da Assir,

24 da Tahat, da Uriyel, da Azariya, da Shawul.

25 ‘Ya’yan Elkana, maza, su ne Amasai da Ahimot.

26 Zuriyar Ahimot bi da bi, su ne Elkana, da Zofai, da Nahat,

27 da Eliyab, da Yeroham, da Elkana.

28 ‘Ya’yan Sama’ila, maza, su ne Yowel ɗan farinsa, na biyun shi ne Abaija.

29 Zuriyar Merari bi da bi, su ne Mali, da Libni, da Shimai, da Uzza,

30 da Shimeya, da Haggiya, da Asaya.

Masu Bushe-bushe a Haikali da Dawuda Ya Zaɓa

31 Waɗannan su ne waɗanda Dawuda ya sa su su zama mawaƙa a Haikalin Ubangiji, sa’ad da aka kawo akwatin alkawari a cikin Haikalin.

32 Suka yi ta raira waƙoƙi a gaban wurin zama na alfarwa ta taruwa tun kafin Sulemanu ya gina Haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi hidima bisa ga matsayinsu ta yadda aka tsara.

33 Waɗannan su ne waɗanda suka yi ta raira waƙoƙin, su da ‘ya’yansu maza.

Daga iyalin Kohat, Heman shi ne shugaban ƙungiyar farko ta mawaƙa, shi ɗan Yowel ne, ɗan Sama’ila,

34 ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyab, ɗan Mahat,

35 ɗan Zafai, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,

36 ɗan Elkana, ɗan Shawul, ɗan Azariya, ɗan Uriyel,

37 ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,

38 ɗan Izhara, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila.

39 Asaf kuma shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta biyu. Shi ɗan Berikiya ne, ɗan Shimeya,

40 ɗan Maikel, ɗan Ba’aseya, ɗan Malkiya,

41 ɗan Yewaterai, ɗan Zera, ɗan Iddo,

42 ɗan Yowa, ɗan Zimma, ɗan Shimai,

43 ɗan Yahat, ɗan Gershon, ɗan Lawi.

44 Etan na zuriyar Merari, shi ne shugaban ƙungiyar mawaƙa ta uku, asalinsa shi ɗan Kishi ne, ɗan Abdi, ɗan Malluki,

45 ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,

46 ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,

47 ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.

48 Aka sa ‘yan’uwansu, Lawiyawa, su yi dukan hidimomi a cikin Haikalin Ubangiji.

Zuriyar Haruna

49 Amma Haruna da ‘ya’yansa maza suka miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa, da kan bagaden ƙona turare, domin dukan aikin Wuri Mafi Tsarki, da kuma yin kafara domin Isra’ila bisa ga dukan abin da Musa, bawan Allah, ya umarta.

50 Waɗannan su ne zuriyar Haruna, maza, bi da bi, Ele’azara, da Finehas, da Abishuwa,

51 da Bukki, da Uzzi, da Zerahiya,

52 da Merayot, da Amariya, da Ahitub,

53 da Zadok da Ahimawaz.

Inda Zuriyar Haruna Suka Zauna

54 Ga wuraren da aka ba zuriyar Haruna, na iyalin Kohat. Sun karɓi rabo na farko a ƙasar.

55 Rabonsu ya haɗu da Hebron ta yankin ƙasar Yahuza, da makiyayar da suke kewaye da ita.

56 Amma an ba Kalibu ɗan Yefunne saurukan birnin, tare da ƙauyukansa.

57 Suka ba ‘ya’yan Haruna, maza, biranen mafaka, wato Hebron, da Libna tare da makiyayarta, da Yattir, da Eshtemowa tare da makiyayarta,

58 da Holon tare da makiyayarta, da Debir tare da makiyayarta,

59 da Ayin tare da makiyayarta, da Bet-shemesh tare da makiyayarta.

60 Daga kabilar Biliyaminu aka ba su Geba tare da makiyayarta, da Allemet tare da makiyayarta, da Anatot tare da makiyayarta. Dukan biranen iyalansu guda goma sha uku ne.

Inda Sauran Lawiyawa Suka Zauna

61 Aka ba sauran ‘ya’yan Kohat, maza, garuruwa goma daga na rabin kabilar Manassa, ta hanyar kuri’a.

62 Aka kuma ba Gershonawa bisa ga iyalansu, birane goma sha uku daga na kabilar Issaka, da na kabilar Ashiru, da na kabilar Naftali, da na kabilar Manassa da take nan a Bashan.

63 Haka kuma aka ba ‘ya’yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga na kabilar Ra’ubainu, da na kabilar Gad, da na kabilar Zabaluna.

64 Haka fa, jama’ar Isra’ila suka ba Lawiyawa garuruwa duk da makiyayansu.

65 Daga na kabilar Yahuza, da na kabilar Saminu, da na kabilar Biliyaminu kuma aka ba da waɗannan garuruwan da aka ambaci sunayensu ta hanyar kuri’a.

66 Waɗansu daga cikin iyalan ‘ya’yan Kohat, maza, sun sami garuruwa na yankinsu daga cikin kabilar Ifraimu.

67 Sai suka ba su waɗannan biranen mafaka, wato Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu duk da makiyayarta, da Gezer tare da makiyayarta,

68 da Yokmeyam duk da makiyayarta, da Bet-horon duk da makiyayarta,

69 da Ayalon duk da makiyayarta, da Gatrimmon duk da makiyayarta.

70 Daga cikin rabin kabilar Manassa kuma an ba su Ta’anak duk da makiyayarta, da Bileyam duk da makiyayarta. An ba da waɗannan ga sauran iyalai na ‘ya’yan Kohat, maza.

71 Daga na rabin kabilar Manassa na gabas, an ba ‘ya’yan Gershon, maza, Golan ta Bashan tare da makiyayarta, da Ashtarot duk da makiyayarta.

72 Daga na kabilar Issaka kuma an ba su Kishiyon duk da makiyayarta, da Daberat duk da makiyayarta,

73 da Ramot duk da makiyayarta, da Enganin duk da makiyayarta.

74 Daga cikin kabilar Ashiru kuma an ba da Mishal duk da makiyayarta, da Abdon duk da makiyayarta,

75 da Helkat duk da makiyayarta, da Rehob duk da makiyayarta.

76 Daga na kabilar Naftali kuma an ba da Kedesh ta Galili duk da makiyayarta, da Hammon duk da makiyayarta, da Kartan duk da makiyayarta.

77 Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato ‘ya’yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.

78 Daga na kabilar Ra’ubainu a hayin Urdun a Yariko, wato gabashin Urdun, an ba da Bezer ta cikin jeji duk da makiyayarta, da Yahaza duk da makiyayarta,

79 da Kedemot duk da makiyayarta, da Mefayat duk da makiyayarta.

80 Daga na kabilar Gad kuma an ba da Ramot ta Gileyad duk da makiyayarta, da Mahanayim duk da makiyayarta,

81 da Heshbon duk da makiyayarta, da Yazar duk da makiyayarta.

Categories
1 TAR

1 TAR 7

Zuriyar Issaka

1 ‘Ya’yan Issaka, maza, su huɗu ne, wato Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron.

2 ‘Ya’yan Tola, maza, su ne Uzzi, da Refaya, da Yeriyel, da Yamai, da Ibsam, da Sama’ila, su ne shugabannin gidajen kakanninsu. ‘Ya’yan Tola kuwa manyan mayaƙa ne a zamaninsu. Yawansu a zamanin Dawuda, su dubu ashirin da biyu ne da ɗari shida (22,600).

3 Ɗan Uzzi, shi ne Izrahiya. ‘Ya’yan Izrahiya, maza, su ne Maikel, da Obadiya, da Yowel, da Isshiya. Su biyar duka manyan mutane ne.

4 A zamaninsu, bisa ga gidajen kakanninsu suna da sojoji dubu talatin da dubu shida (36,000) gama suna da mata da yara da yawa.

5 Mayaƙan da aka lasafta bisa ga asalinsu na dukan iyalan Issaka, su dubu tamanin da dubu bakwai ne (87,000), jarumawa ne sosai.

Zuriyar Biliyaminu

6 ‘Ya’yan Biliyaminu su uku ne, wato Bela, da Beker, da Yediyayel.

7 ‘Ya’yan Bela, maza, su biyar ne, wato Ezbon, da Uzzi, da Uzziyel, da Yerimot, da Iri. Su ne shugabannin gidajen kakanninsu, jarumawa ne su. An lasafta su bisa ga asalinsu, su dubu ashirin da biyu ne da talatin da huɗu (22,034).

8 ‘Ya’yan Beker, maza, su ne Zemira, da Yowash, da Eliyezer, da Eliyehoyenai, da Omri, da Yerimot, da Abaija da Anatot, da Alamet. Waɗannan duka ‘ya’yan Beker ne, maza.

9 An lasafta su bisa ga asalinsu a zamaninsu, su dubu ashirin ne da ɗari biyu (20,200), jarumawa ne su sosai. Su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu.

10 Ɗan Yediyayel shi ne Bilhan. ‘Ya’yan Bilhan, maza, su ne Yewush, da Biliyaminu, da Ehud, da Kena’ana, da Zetan, da Tarshish, da Ahishahar.

11 Duk waɗannan ‘ya’yan Yediyayel, maza ne, bisa ga shugabannin gidajen kakanninsu. Su dubu goma sha bakwai ne da ɗari biyu (17,200), jarumawa ne sosai, shiryayyu don yaƙi.

12 Shuffim da Huffim su ne ‘ya’yan Iri, maza.

Hushim shi ne ɗan Ahiram.

Zuriyar Naftali

13 Naftali yana da ‘ya’ya huɗu, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum. Su ne zuriya daga Bilha.

Zuriyar Manassa

14 ‘Ya’yan Manassa, maza, su ne Asriyel, wanda ƙwarƙwararsa Ba’aramiya ta haifa masa. Ta kuma haifi Makir mahaifin Gileyad.

15 Makir ya auro wa Huffim da Shuffim mata. Sunan ‘yar’uwarsa Ma’aka, sunan ɗan’uwansa kuwa Zelofehad, Zelofehad yana da ‘ya’ya mata kaɗai.

16 Sai Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa, ta sa masa suna Feres, sunan ɗan’uwansa kuwa Sheres. ‘Ya’yan Feres maza, su ne Ulam da Rakem.

17 Ɗan Ulam shi ne Bedan. Waɗannan su ne ‘ya’ya maza na Gileyad ɗan Makir, jīkan Manassa.

18 ‘Yar’uwarsa, Hammoleket ta haifi Ishodi, da Abiyezer, da Mala.

19 ‘Ya’yan Shemida, maza, su ne Ahiyan, da Shekem, da Liki, da Aniyam.

Zuriyar Ifraimu

20 ‘Ya’yan Ifraimu, maza, daga tsara zuwa tsara, su ne Shutela, da Bered, da Tahat, da Eleyada, da Tahat,

21 da Zabad, da Shutela, da Ezer, da Eleyad waɗanda mutanen Gat, haifaffun ƙasar, suka kashe sa’ad da suka kai hari don su kwashe dabbobinsu.

22 Sai mahaifinsu, Ifraimu, ya yi ta makoki kwanaki da yawa. ‘Yan’uwansu kuwa suka zo don su yi masa ta’aziyya.

23 Sa’an nan ya shiga wurin matarsa, ta kuwa sami juna biyu, ta haifi ɗa, ya raɗa masa suna Beriya saboda masifar da ta auko wa gidansa.

24 ‘Yarsa kuma ita ce Sheyera, wadda ta gina garin Bet-horon na kwari da na tudu, ta kuma gina Uzzen-sheyera.

25 Waɗansu zuriyarsa bi da bi, su ne Refa, da Reshe, da Tela, da Tahan,

26 da Ladan, da Ammihud, da Elishama,

27 da Nun, da Joshuwa.

28 Mallakarsu da wuraren zamansu, su ne Betel duk da garuruwanta, da Nayaran wajen gabas, da Gezer wajen yamma duk da garuruwanta, da Shekem duk da garuruwanta, har zuwa Ayya duk da garuruwanta.

29 Zuriyar Manassa sun mallaki Bet-sheyan, da Ta’anak, da Magiddo, da Dor duk da garuruwan da suke kewaye da su. A nan ne zuriyar Yusufu, ɗan Isra’ila, suka zauna.

Zuriyar Ashiru

30 ‘Ya’yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da ‘yar’uwarsu Sera.

31 ‘Ya’yan Beriya, maza, su ne Eber, da Malkiyel wanda ya kafa garin Birzayit.

32 Eber shi ne mahaifin Yaflet, da Shemer, da Helem, da ‘yar’uwarsu Shuwa.

33 ‘Ya’yan Yaflet, maza, su ne Fasak, da Bimhal, da Ashewat.

34 ‘Ya’yan Shemer maza, su ne Ahi, da Roga, da Yehubba, da Aram.

35 ‘Ya’ya maza na ɗan’uwansa Helem, su ne Zofa, da Imna, da Sheles da Amal.

36 ‘Ya’yan Zofa, su ne Suwa, da Harnefer, da Shuwal, da Beri, da Imra,

37 da Bezer, da Hod, da Shamma, da Shilsha, da Yeter, da Biyera.

38 ‘Ya’yan Yeter, su ne Yefunne, da Fisfa, da Ara.

39 ‘Ya’yan Ulla, maza, su ne Ara, da Haniyel, da Riziya.

40 Waɗannan duka su ne zuriyar Ashiru, su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu. Zaɓaɓɓun jarumawa ne su, manyan sarakuni. Yawansu da aka lasafta bisa ga asalinsu don yaƙi su dubu ashirin da dubu shida ne (26,000).

Categories
1 TAR

1 TAR 8

Zuriyar Biliyaminu

1 Biliyaminu yana da ‘ya’ya biyar, su ne Bela, da Ashbel, da Ahiram,

2 da Noha, da Rafa.

3 Bela kuma yana da ‘ya’ya maza, su ne Adar, da Gera da Abihud,

4 da Abishuwa, da Na’aman, da Ahowa,

5 da Gera, da Shuffim, da Huram.

6 Waɗannan kuma su ne ‘ya’yan Ehud, maza. Su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Geba, waɗanda aka kai su bauta a Manahat.

7 Ga sunayensu, Na’aman, da Ahaija, da Gera wanda yake shugabansu lokacin da aka kai su bauta. Shi ne kuma mahaifin Uzza da Ahihud.

8 Shaharayim kuma yana da ‘ya’ya maza a ƙasar Mowab bayan da ya saki matansa biyu, wato Hushim da Ba’ara.

9 Matarsa Hodesh ta haifa masa ‘ya’ya maza, su ne Yobab, da Zibiya, da Mesha, da Malkam,

10 da Yuz, da Sakiya, da Mirma. Waɗannan su ne ‘ya’yansa maza, shugabannin gidajen kakanninsu.

11 Hushim kuma ta haifa masa waɗansu ‘ya’ya maza, su ne Abitub da Elfayal.

12 ‘Ya’yan Elfayal, su ne Eber, da Misham, da Shemed wanda ya gina Ono da Lod da ƙauyukansu, da

13 Beriya, da Shimai, su ne shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Ayalon waɗanda suka kori mazaunan Gat,

14 da Ahiyo, da Shashak, da Yeremot.

15 Zabadiya, da Arad, da Eder,

16 da Maikel, da Ishfa, da Yoha, su ne ‘ya’yan Beriya, maza.

17 Zabadiya, da Meshullam, da Hizki, da Eber,

18 da Ishmerai, da Izliya, da Yobab, su ne zuriyar Elfayal.

19 Zuriyar Shimai, su ne Yakim, da Zikri, da Zabdi,

20 da Eliyenai, da Zilletai, da Eliyel,

21 da Adaya, da Beraiya, da Shimrat.

22 Zuriyar Shashak, su ne Isfan, da Eber, da Eliyel,

23 da Abdon, da Zikri, da Hanan,

24 da Hananiya, da Elam, da Antotiya,

25 da Ifediya, da Feniyel.

26 Zuriyar Yeroham, su ne Shemsherai, da Shehariya, da Ataliya,

27 da Yawareshiya, da Eliya, da Zikri.

28 Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakanninsu a zamaninsu, waɗanda suka zauna a Urushalima.

Zuriyar Saul

29 Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a can. Sunan matarsa Ma’aka.

30 Abdon ne ɗansa na fari, sa’an nan Zur, da Kish, da Ba’al, da Nadab,

31 da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya,

32 da Miklot, mahaifin Shimeya. Waɗannan su ne suka zauna daura da ‘yan’uwansu a Urushalima.

33 Ner shi ne mahaifin Kish, Kish kuma shi ne mahaifin Saul, Saul shi ne mahaifin Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.

34 Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika.

35 ‘Ya’yan Mika, maza, su ne Fiton, da Melek, da Tareya, da Ahaz.

36 Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Allemet, da Azmawet, da Zimri. Zimri ya haifi Moza.

37 Moza ya haifi Bineya, da Refaya, da Eleyasa, da Azel.

38 Azel ya haifi ‘ya’ya maza su shida, su ne Azrikam, da Bokeru, da Ismayel, da Sheyariya, da Obadiya, da Hanan.

39 ‘Ya’ya maza na Esheke ɗan’uwansa su ne, Ulam, da Yewush, da Elifelet.

40 ‘Ya’yan Ulam, maza, jarumawa ne sosai, ‘yan baka, suna da ‘ya’ya maza, da jikoki maza da yawa. Su ɗari da hamsin ne. Waɗannan duka mutanen Biliyaminu ne.

Categories
1 TAR

1 TAR 9

Waɗanda Suka Komo daga Babila

1 Haka kuwa aka lasafta Isra’ilawa bisa ga asalinsu. An rubuta su a littafin sarakunan Isra’ila.

Sai aka kai mutanen Yahuza zaman talala a Babila saboda rashin amincinsu ga Ubangiji.

2 Waɗanda suka fara zama a biranen mallakarsu, su ne Isra’ilawa da firistoci, da Lawiyawa, da kuma ma’aikatan Haikali.

3 Waɗansu mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na Ifraimu, da na Manassa suka zauna a Urushalima.

4-6 Iyalin Yahuza guda ɗari shida da tasa’in suka zauna a Urushalima, shugabansu kuwa shi ne Utai ɗan Ammihud, jīkan Omri daga wajen Feresa. Waɗansu kakanninsu kuwa su ne Imri da Bani. Zuriyar Shela ɗan Yahuza suna da shugaba mai suna Asaya. Zuriyar Zera ɗan Yahuza kuwa, shugabansu Yuwel.

7 Ga zuriyar Biliyaminu a Urushalima bi da bi, da Sallai ɗan Meshullam, da Hodawiya, da Hassenuwa,

8 da kuma Ibneya ɗan Yeroham, da Ila ɗan Uzzi, wato jīkan Mikri, da Meshullam ɗan Shefatiya, da Reyuwel, da Ibnija.

9 Tare da danginsu a zamaninsu, sun kai ɗari tara da hamsin da shida ne. Duk waɗannan shugabannin gidajen kakanninsu ne.

Firistocin da Suke a Urushalima

10 Daga cikin firistoci masu zama a Urushalima su ne Yedaiya, da Yehoyarib, da Yakin,

11 da Azariya ɗan Hilkiya, shi ne jami’in Haikalin Ubangiji, kakanninsa sun haɗu da Shallum ɗan Zadok, da Merayot, da Ahitub,

12 da Adaya ɗan Yeroham, kakanninsa sun haɗu da Fashur, da Malkiya, da Ma’asai ɗan Adiyel, kakanninsa sun haɗu da Yazera, da Meshullam, da Meshillemot, da Immer.

13 Firistacin da suke shugabannin gidajen kakanninsu, sun kai mutum dubu da ɗari bakwai da sittin (1,760). Ƙwararru ne cikin hidimar Haikalin Ubangiji.

14 Lawiyawa masu zama a Urushalima kuma, su ne Shemaiya ɗan Hasshub, wanda kakanninsa suka haɗu da Azrikam da Hashabiya daga ‘ya’yan Merari, maza,

15 da kuma Bakbakkar, da Heresh, da Galal, da Mattaniya ɗan Mika wanda kakanninsa su ne Zikri da Asaf,

16 da kuma Obadiya ɗan Shemaiya, kakanninsa su ne Galal da Yedutun, da Berikiya ɗan Asa, wato jīkan Elkana, wanda ya zauna a garin Netofa.

17 Masu tsaron Haikalin, su ne Shallum, da Akkub, da Talmon, da Ahiman, da ‘yan’uwansu. Shallum shi ne shugaba.

18 Har zuwa yau, iyalinsu suke tsaron ƙofar sarki a wajen gabas. A dā su ne suke tsaron sauran ƙofofin zangon Lawiyawa.

19 Shallum ɗan Kore, wato jīkan Ebiyasaf, tare da ‘yan’uwansa na zuriyar Kora, suke lura da masu tsaron ƙofofin alfarwa kamar dai yadda kakanninsu suka lura da zangon Ubangiji.

20 A dā Finehas ɗan Ele’azara shi ne shugabansu, Ubangiji kuwa yana tare da shi.

21 Zakariya ɗan Shallum yake tsaron ƙofar alfarwa ta sujada.

22 Dukan waɗanda aka zaɓa domin su zama masu tsaron ƙofofi, su ɗari biyu ne da goma sha biyu. An lasafta su bisa ga asalinsu da garuruwansu. Dawuda da Sama’ila annabi, su ne suka sa su a matsayinsu na riƙon amana.

23 Saboda haka su da ‘ya’yansu maza suke tsaron ƙofofin Ubangiji, wato alfarwa ta sujada.

24 Matsaran ƙofofi suka tsaya a kusurwoyi huɗu, wato gabas da yamma, kudu da arewa.

25 ‘Yan’uwansu waɗanda suke a ƙauyuka kuwa, ya zamar musu wajibi su zo wurinsu kowane kwana bakwai, domin su karɓe su tsaron.

26 Su shugabanni huɗu na matsaran ƙofar Lawiyawa ne waɗanda suke da matsayi na riƙon amana, su ne masu lura da ɗakunan Haikalin Allah da dukiyarsa.

27 Sukan kwana suna tsaro kewaye da Haikalin Allah, gama hakkin yana kansu. Su ne sukan buɗe shi kowace safiya.

28 Waɗansunsu suna lura da kayayyakin aiki na cikin Haikali. Sukan ƙidaya su sa’ad da aka shigo da su, da sa’ad da aka fitar da su.

29 Aka sa waɗansu su zama masu lura da kayayyakin Haikalin, da kayayyakin aiki na cikin Wuri Mai Tsarki, da lallausan gari, da ruwan inabi, da mai, da turare, da kayan yaji.

30 Waɗansu ‘ya’yan firistoci, maza, suke harhaɗa kayan yaji.

31 Mattitiya, ɗaya daga cikin Lawiyawa, ɗan farin Shallum na iyalin Kora, shi ne mai lura da toya waina.

32 Waɗansu ‘yan’uwansu Kohatawa suke lura da gurasar ajiyewa. Sukan shirya ta kowace Asabar.

33 Waɗannan su ne mawaƙa, da shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa, waɗanda suka zauna a ɗakunan Haikali, ba su yin wani aiki dabam, gama dare da rana suke yin aikinsu.

34 Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa a zamaninsu, wato waɗanda suka zauna a Urushalima.

Kakannin Sarki Saul da Zuriyarsa

35 Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a ciki, sunan matarsa Ma’aka,

36 ɗan farinsa kuma shi ne Abdon. Sa’an nan ga Zur, da Kish, da Ba’al, da Ner, da Nadab,

37 da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya, da Miklot,

38 mahaifin Shimeya. Zuriyarsu ne suka zauna a Urushalima daura da ‘yan’uwansu.

39 Ner ya haifi Kish, Kish kuma ya haifi Saul, Saul ya haifi Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.

40 Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika.

41 ‘Ya’yan Mika, maza, su ne Fiton, da Melek, da Tareya, da Ahaz.

42 Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Allemet, da Azmawet, da Zimri. Zimri ya haifi Moza,

43 Moza ya haifi Bineya, da Refaya, da Eleyasa, da Azel.

44 Azel yana da ‘ya’ya maza guda shida, su ne Azrikam, da Bokeru, da Isma’ilu, da Sheyariya, da Obadiya, da Hanan.

Categories
1 TAR

1 TAR 10

Mutuwar Sarki Saul da ta ‘Ya’yansa

1 Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa, Isra’ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa.

2 Filistiyawa suka kama Saul da ‘ya’yansa maza, suka kashe Jonatan da Yishwi, da Malkishuwa.

3 Yaƙin ya tsananta wa Saul, maharba suka rutsa Saul, suka yi masa rauni.

4 Sai Saul ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Zare takobinka, ka kashe ni, don kada marasa kaciyan nan su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar makamai nasa bai yarda ba, gama yana jin tsoro ƙwarai. Saboda haka sai Saul ya zare takobinsa ya fāɗi a kansa.

5 Sa’ad da mai ɗaukar makamansa ya ga Saul ya mutu, sai shi ma ya faɗi a kan takobinsa ya mutu.

6 Ta haka Saul ya mutu, shi da ‘ya’yansa maza guda uku tare da dukan gidansa.

7 Sa’ad da dukan Isra’ilawa waɗanda suke zaune a kwari suka ga sojojin sun gudu, Saul kuma da ‘ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa suka zo suka zauna a wurin.

8 Kashegari, sa’ad da Filistiyawa suka tafi su kwashe waɗanda aka kashe, sai suka tarar da Saul da ‘ya’yansa maza matattu a Dutsen Gilbowa.

9 Suka kuwa tuɓe tufafinsa, suka datse kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka aiki manzanni ko’ina a ƙasar Filistiyawa don su ba gumakansu da jama’arsu wannan albishir.

10 Sai suka ajiye kayan yaƙin Saul a gidan gumakansu, suka kuma rataye kansa a gidan gunkin nan, wato Dagon.

11 Sa’ad da mutanen Yabesh-gileyad suka ji irin abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,

12 sai dukan ƙarfafan mutanensu suka tafi suka ɗauki gawar Saul, da gawawwakin ‘ya’yansa, suka kawo a Yabesh suka binne ƙasusuwansu a ƙarƙashin itacen oak cikin Yabesh. Suka yi azumi har kwana bakwai.

13 Haka nan Saul ya mutu saboda laifin da ya yi wa Ubangiji, gama bai kiyaye maganar Ubangiji ba, saboda kuma ya nemi shawara wurin masu mabiya.

14 Amma bai nemi Ubangiji ba. Domin haka Ubangiji ya kashe shi, ya ɗauki sarautar, ya ba Dawuda ɗan Yesse.