Categories
1 TAR

1 TAR 21

Dawuda Ya Ƙidaya Mutane

1 Shaiɗan ya tashi gaba da Isra’ila, sai ya iza Dawuda ya ƙidaya Isra’ilawa.

2 Dawuda fa ya ce wa Yowab da sauran shugabannin jama’a, “Ku tafi, ku ƙidaya jama’ar Isra’ila tun daga Biyer-sheba har zuwa Dan, ku kawo mini labari don in san yawansu.”

3 Amma Yowab ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya yawan jama’arsa har sau ɗari bisa kan yadda suke a yanzu! Ranka ya daɗe, ya sarki, ashe, dukkansu ba naka ba ne? Me zai sa shugabana ya so a yi haka? Me zai sa ya zama sanadin tuntuɓe ga mutanen Isra’ila?”

4 Duk da haka, sarki ya sa Yowab ya bi umarninsa. Sai Yowab ya tashi, ya bibiya ƙasar Isra’ila duka, sa’an nan ya komo Urushalima.

5 Yowab ya kawo wa Dawuda adadin yawan mutanen. Jimillar dukan Isra’ila zambar dubu ne da dubu ɗari (1,100,000) waɗanda za su iya yaƙi. Jimillar mutanen Yahuza kuwa dubu ɗari huɗu da dubu saba’in ne (470,000) waɗanda suka isa zuwa yaƙi.

6 Amma bai ƙidaya Lawiyawa da mutanen Biliyaminu ba, domin Yowab bai ji daɗin umarnin sarki ba.

7 Allah bai ji daɗin wannan al’amari ba, don haka sai ya bugi Isra’ila.

8 Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai saboda abin nan da na aikata. Amma ina roƙonka ka gafarta mini laifina, gama na yi aikin wauta ƙwarai da gaske.”

9 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Gad, annabin Dawuda, ya ce,

10 “Je ka ka faɗa wa Dawuda, ka ce, ‘Ubangiji yana so ka zaɓi ɗaya daga cikin abu uku, wanda zai yi maka.’ ”

11 Gad kuwa ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka zaɓa,

12 ko shekara uku na yunwa, ko kuwa ka sha ɗibga a hannun maƙiyanka har wata uku, maƙiyanka su yi ta fafararka, ko kwana uku na takobin Ubangiji, wato annoba ke nan da zai aukar wa ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai yi ta hallakarwa ko’ina a ƙasar Isra’ila. Yanzu fa, sai ka yi tunani, ka ba ni amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”

13 Dawuda kuwa ya ce wa Gad, “Na shiga uku, gara in fāɗa a hannun Ubangiji, gama shi mai yawan jinƙai ne, kada ka bar ni in faɗa a hannun mutum.”

14 Saboda haka Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra’ila. Mutum dubu saba’in (70,000) na Isra’ila suka mutu.

15 Allah ya aiko mala’ikansa don ya hallaka Urushalima, amma sa’ad da yake gab da hallaka ta, sai Ubangiji ya gani, ya janye shirin annobar, ya ce wa mala’ikan hallakarwa, “Ya isa, janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa na tsaye kusa da masussukar Arauna Bayebuse.

16 Dawuda ya ɗaga idonsa, sai ya ga mala’ikan Ubangiji yana tsakanin sama da ƙasa, da takobinsa a zare a hannunsa a kan Urushalima. Sa’an nan Dawuda tare da dattawa suka fāɗi rubda ciki, suna saye da tufafin makoki.

17 Dawuda ya ce wa Allah, “Ai, ni ne na ba da umarni a ƙidaya jama’ar. Hakika, ni na yi zunubi, na kuwa aikata mummunan abu, amma waɗannan talakawa fa, me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, ka bar hannunka ya yi gāba da ni da gidan tsohona, amma kada ka yi gāba da jama’arka, har da za ka aukar musu da annoba.”

18 Mala’ikan Ubangiji ya umarci Gad ya faɗa wa Dawuda ya haura, ya gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna Bayebuse.

19 Dawuda kuwa ya haura kamar yadda Gad ya faɗa masa da sunan Ubangiji.

20 Arauna yana cikin sussukar alkama, sai ya waiwaya ya ga mala’ika. ‘Ya’yansa maza su huɗu kuwa, waɗanda suke tare da shi suka ɓuya.

21 Sa’ad da Dawuda ya tafi wurin Arauna, da Arauna ya ga Dawuda, sai ya fito daga masussukar ya tafi ya fāɗi rub da ciki a gaban Dawuda ya gaishe shi.

22 Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ba ni wannan masussuka don in gina wa Ubangiji bagade. Ka sayar mini da masussukar a bakin cikakken kuɗinta, domin a kawar wa jama’a da annobar.”

23 Arauna ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa, na ba ka, sai ka yi abin da kake so da ita, ranka ya daɗe. Zan kuma ba da bijimai domin hadayu na ƙonawa, in ba da keken sussuka domin itacen wuta, in kuma ba da alkama don hadaya ta gari. Zan ba ka waɗannan duka.”

24 Amma sarki Dawuda ya ce wa Arauna, “A’a, zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai in ba Ubangiji ba, ba kuwa zan miƙa masa hadayu na ƙonawa da abin da ban biya ba.”

25 Sai Dawuda ya biya Arauna shekel ɗari shida na zinariya domin masussukar.

26 Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ya yi roƙo ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wutar da ta sauko daga sama a bisa bagaden hadayar ta ƙonawa.

27 Sa’an nan Ubangiji ya umarci mala’ikan, shi kuwa ya mai da takobinsa a kube.

Inda Za a Yi Haikalin

28 Da Dawuda ya ga Ubangiji ya amsa masa a masussukar Arauna Bayebuse, sai ya miƙa hadaya a wurin.

29 Gama wurin zama na Ubangiji wanda Musa ya yi a jeji, da bagaden hadaya ta ƙonawa sun cikin masujada a Gibeyon.

30 Dawuda bai iya zuwa wurin don ya yi tambaya ga Allah ba, saboda yana jin tsoron takobin mala’ikan Ubangiji.

Categories
1 TAR

1 TAR 22

1 Sa’an nan sai Dawuda ya ce, “A nan Haikalin Ubangiji Allah zai kasance, da kuma bagaden ƙona hadaya domin Isra’ila.”

Shirye-shiryen da Dawuda Ya Yi domin Gina Haikali

2 Dawuda kuwa ya umarta a tattaro dukan baƙin da suke a ƙasar Isra’ila. Ya sa waɗansu su farfasa duwatsu, su sassaƙe duwatsun domin ginin Haikalin Allah.

3 Dawuda kuma ya cika manyan ɗakunan ajiya da ƙarafa don yin ƙusoshi na ƙyamaren ƙofofi, da mahaɗai, ya kuma tara tagulla mai yawa wanda ta fi ƙarfin awo,

4 da katakan al’ul da ba a san adadinsu ba, gama Sidoniyawa da mutanen Taya sun kawo wa Dawuda itacen al’ul mai ɗumbun yawa.

5 Dawuda kuwa ya ce, “Ɗana Sulemanu yaro ne, bai gogu da duniya ba. Ga shi, Haikalin da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, zai zama sananne mai daraja cikin dukan ƙasashe, saboda haka sai in tanada masa.” Domin haka Dawuda ya tara kayayyakin gini masu ɗumbun yawa kafin rasuwarsa.

6 Sai Dawuda ya kira Sulemanu ɗansa, ya yi masa wasiyyar gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila.

7 Dawuda kuwa ya ce wa Sulemanu, “Ɗana, na ƙudura a zuciyata in gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allah.

8 Amma Ubangiji ya ce mini, ‘Ka zubar da jini da yawa, ka yi manyan yaƙe-yaƙe, don haka ba za ka gina Haikali saboda sunana ba, gama a gabana ka zubar da jini mai yawa a duniya.

9 Za a haifa maka ɗa, zai zama mutumin salama. Zan kuwa ba shi zaman lafiya da abokan gāba da suke kewaye da shi, gama za a ce da shi Sulemanu, wato salama. Zan kawo wa Isra’ila salama, da natsuwa a zamaninsa.

10 Shi zai gina Haikali saboda sunana. Zai zama ɗana, ni kuwa zan zama uba a gare shi, zan kafa gadon sarautarsa a Isra’ila har abada.’

11 “To, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, domin ka yi nasara ka gina Haikalin Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya faɗa a kanka.

12 Ubangiji dai ya ba ka basira da haziƙanci domin sa’ad da ya sa ka ka lura da Isra’ila ka kiyaye dokokinsa.

13 Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka’idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra’ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.

14 Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.

15 Kana da ma’aikata jingim, su masu fasa duwatsu, da magina, da masassaƙa, da gwanayen masu sana’o’i iri dabam dabam, masu yawan gaske.

16 Za su yi aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da ƙarfe. Tashi, ka kama aiki, Ubangiji ya kasance tare da kai!”

17 Dawuda kuma ya umarci dukan shugabannin Isra’ila su taimaki ɗansa Sulemanu.

18 Ya ce, “Ubangiji Allahnku yana tare da ku, ya ba ku zaman lafiya a kowane sashi. Gama ya ba da mazaunan ƙasar a hannuna, an murƙushe ƙasar a gaban Ubangiji da jama’arsa.

19 Yanzu fa sai ku sa hankalinku da zuciyarku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku tashi, ku gina wa Ubangiji Allah tsattsarkan wuri domin a kawo akwatin alkawari na Ubangiji, da tsarkakakkun tasoshin Allah a cikin Haikalin da aka gina saboda sunan Ubangiji.”

Categories
1 TAR

1 TAR 23

1 Sa’ad da Dawuda ya tsufa, yana da shekaru da yawa, sai ya naɗa ɗansa Sulemanu ya zama Sarkin Isra’ila.

Ayyukan Lawiyawa

2 Dawuda kuwa ya tattara dukan shugabannin Isra’ila, da firistoci, da Lawiyawa.

3 Aka ƙidaya Lawiyawa maza tun daga mai shekara talatin har sama, jimillarsu dubu talatin da dubu takwas (38,000).

4 Sai Dawuda ya ce dubu ashirin da dubu huɗu (24,000) daga cikinsu za su yi hidimar Haikalin Ubangiji, dubu shida (6,000) kuma su zama manyan ma’aikata da alƙalai,

5 dubu huɗu (4,000) su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu (4,000) kuma za su zama masu raira yabbai ga Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda ya yi.

6 Dawuda kuwa ya kasa su kashi kashi bisa ga ‘ya’yan Lawi maza, wato Gershon, da Kohat, da Merari.

7 ‘Ya’yan Gershon maza, su ne Libni da Shimai.

8 ‘Ya’yan Libni, maza, su ne Yehiyel, shi ne babba, da Zetam, da Yowel, su uku.

9 ‘Ya’yan Shimai, maza kuwa, su ne Shelomit, da Heziyel, da Haran, su uku. Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu, Libni.

10 ‘Ya’yan Shimai, maza, su ne Yahat, da Zaina, da Yewush, da Beriya. ‘Ya’yan Shimai, maza, ke nan, su huɗu.

11 Yahat shi ne babba, Zaina shi ne na biyu, amma Yewush, da Beriya ba su da ‘ya’ya da yawa, saboda haka ana lasafta su a haɗe gida ɗaya.

12 ‘Ya’yan Kohat, maza, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel, su huɗu ke nan.

13 ‘Ya’yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da ‘ya’yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.

14 Amma ‘ya’yan Musa mutumin Allah, an lasafta su tare da kabilar Lawi.

15 ‘Ya’yan Musa, maza, ke nan, Gershom da Eliyezer.

16 Ɗan Gershom babba shi ne Shebuwel.

17 Ɗan Eliyezer shi ne Rehabiya, shugaba, shi Eliyezer ba shi da waɗansu ‘ya’ya, amma Rehabiya yana da ‘ya’ya da yawa.

18 Ɗan Izhara shi ne Shelomit, shugaba.

19 ‘Ya’yan Hebron, maza, su ne Yeriya, shi ne babba, da Amariya na biyu, da Yahaziyel na uku, da kuma Yekameyam na huɗu.

20 ‘Ya’yan Uzziyel, maza, su ne Mika, da Isshiya.

21 ‘Ya’yan Merari, su ne Mali da Mushi. ‘Ya’yan Mali su ne Ele’azara da Kish.

22 Ele’azara kuwa ya rasu ba shi da ‘ya’ya maza, sai ‘yan mata kaɗai, sai ‘yan’uwansu, ‘ya’yan Kish, maza, suka aure su.

23 ‘Ya’yan Mushi, maza, su uku ne, wato Mali, da Eder, da Yerimot.

24 Waɗannan su ne ‘ya’yan Lawi, maza, bisa ga gidajen kakanninsu, wato su ne shugabannin da aka rubuta sunayensu ɗaya ɗaya daga mai shekara ashirin da haihuwa zuwa sama. Su ne za su yi hidima a cikin Haikalin Ubangiji.

25 Gama Dawuda ya ce, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya hutar da jama’arsa, yana kuwa zama a Urushalima har abada.

26 Yanzu Lawiyawa ba za su riƙa ɗaukar alfarwar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta ba.”

27 Bisa ga maganar Dawuda ta ƙarshe aka ƙidaya ‘ya’yan Lawiyawa, maza, daga mai shekara ashirin zuwa sama.

28 Aikinsu shi ne su taimaki ‘ya’yan Haruna, maza, gudanar da aiki cikin Haikalin Ubangiji, wato lura da farfajiyoyi da ɗakuna, da tsabtace tsarkakan abubuwa, da yin taimako cikin kowace hidimar Haikalin Ubangiji.

29 Za su kuma taimaka wajen gurasar ajiyewa, da lallausan gari na hadaya ta gari, da waina marar yisti, da abin da akan toya, da abin da akan kwaɓa, da ma’aunan nauyi da na girma.

30 Za su kuma riƙa tsayawa kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Haka kuma za su riƙa yi da maraice,

31 da kuma lokacin miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa a ranakun Asabar, da lokacin tsayawar amaryar wata, da lokacin ƙayyadaddun idodi, za su tsaya a gaban Ubangiji bisa ga yawansu da ake bukata.

32 Su ne za su riƙa lura da alfarwa ta sujada, da Wuri Mai Tsarki, za su kuma taimaki ‘ya’yan Haruna, maza, ‘yan’uwansu, da yin hidimar Haikalin Ubangiji.

Categories
1 TAR

1 TAR 24

Ayyukan da aka Raba wa Firistoci

1 Ga yadda ‘ya’yan Haruna, maza, suka karkasu. ‘Ya’yan Haruna, maza, su ne Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar.

2 Amma Nadab da Abihu sun riga mahaifinsu mutuwa, ba su kuma da ‘ya’ya. Saboda haka Ele’azara da Itamar suka shiga aikin firistoci.

3 Sai Dawuda da Zadok daga zuriyar Ele’azara, da Ahimelek daga zuriyar Itamar suka karkasa su bisa ga ƙayyadaddun lokatansu na yin aiki.

4 Tun da yake akwai manyan mutane da yawa a zuriyar Ele’azara fiye da zuriyar Itamar, sai suka karkasa su haka, shugabannin gidajen kakannin zuriyar Ele’azara mutum goma sha shida, na zuriyar Itamar kuwa su takwas, bisa ga gidajen kakanninsu.

5 Da haka aka karkasa su ta hanyar kuri’a gama akwai ma’aikatan Wuri Mai Tsarki da kuma ma’aikata na Allah daga zuriyar Ele’azara da zuriyar Itamar.

6 Shemaiya, ɗan Netanel marubuci, Balawe, ya rubuta su a gaban sarki da shugabanni, da Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin gidajen kakannin firistoci, da Lawiyawa. Aka ɗauki gida guda daga gidajen kakannin Ele’azara, aka kuma ɗauki ɗaya daga gidajen kakannin Itamar.

7-18 Ga yadda aka shirya ƙungiyoyin iyali ashirin da huɗu su sami aikinsu, 1) Yehoyarib, 2) Yedaiya, 3) Harim, 4) Seyorim, 5) Malkiya, 6) Mijamin, 7) Hakkoz, 8) Abaija, 9) Yeshuwa, 10) Shekaniya, 11) Eliyashib, 12) Yakim, 13) Huffa, 14) Yeshebeyab, 15) Bilga, 16) Immer, 17) Hezir, 18) Haffizzez, 19) Fetahiya, 20) Yehezkel, 21) Yakin, 22) Gamul, 23) Delaiya, 24) Ma’aziya.

19 Waɗannan suna da aikin da aka ba su na hidimar Haikalin Ubangiji bisa ga ka’idar da kakansu Haruna ya kafa musu, kamar yadda Ubangiji Allah na Isra’ila ya umarce shi.

20 Sauran ‘ya’yan Lawi, maza, na wajen Amram, shi ne Shebuwel.

Na wajen Shebuwel, shi ne Yedaiya.

21 Na wajen Rehabiya, shi ne Isshiya,

22 Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.

23 Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.

24 Na wajen Uzziyel, shi ne Mika, na wajen Mika, shi ne Shamir.

25 Ɗan’uwan Mika, shi ne Isshiya. Na wajen Isshiya, shi ne Zakariya.

26 Na wajen Merari, Mali da Mushi, da Yayaziya. Na wajen Yayaziya, shi ne Beno.

27 Na wajen Merari, wato na wajen Yayaziya, su ne Beno, da Shoham, da Zakkur, da Ibri.

28 Na wajen Mali, shi ne Ele’azara wanda ba shi da ‘ya’ya maza.

29 Na wajen Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel.

30 ‘Ya’yan Mushi, maza, su ne Mali, da Eder, da Yerimot.

Waɗannan su ne ‘ya’yan Lawiyawa, maza, bisa ga gidajen kakanninsu.

31 Su ma suka jefa kuri’a kamar yadda ‘yan’uwansu, ‘ya’yan Haruna, maza, suka yi a gaban sarki Dawuda, da Zadok, da Ahimelek, da shugabannin gidajen kakanni na firistoci da na Lawiyawa. Shugaban gidan kakanni ya jefa kuri’a daidai da ƙanensa.

Categories
1 TAR

1 TAR 25

Ƙungiyoyin Mawaƙa

1 Dawuda fa da shugabannin Lawiyawa suka zaɓi waɗansu daga cikin ‘ya’yan Asaf, maza, da na Heman, da na Yedutun domin su raira waƙa da garayu, da molaye, da kuge. Ga waɗanda suka yi wannan hidima.

2 Daga cikin ‘ya’yan Asaf, maza, Zakkur, da Yusufu, da Netaniya, da Asharela, Asaf mahaifinsu ne yake bi da su, shi ne kuma mawaƙin sarki.

3 Na wajen Yedutun, su ne ‘ya’yan Yedutun, maza, wato Gedaliya, da Zeri, da Yeshaya, da Shimai, da Hashabiya, da Mattitiya, su shida ne. Mahaifinsu Yedutun shi ne yake bi da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya domin godiya da yabon Ubangiji.

4 Na wajen Heman, su ne ‘ya’yan Heman, maza, wato Bukkiya, da Mattaniya, da Uzziyel, da Shebuwel, da Yerimot, da Hananiya, da Hanani, da Eliyata, da Giddalti, da Romamti-yezer, da Yoshbekasha, da Malloti, da Hotir, da Mahaziyot.

5 Allah ya ba Heman, wato annabin sarki, ‘ya’ya maza su goma sha huɗu, da ‘ya’ya mata su uku, kamar yadda ya yi alkawari, domin ya ba Heman iko.

6 Dukansu tsohonsu ne yake bi da su da raira waƙoƙi, da kaɗa kuge, da molaye da garayu, cikin Haikalin Ubangiji, domin yin sujada. Asaf, da Yedutun, da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki.

7 Jimillar horarrun mawaƙa don raira waƙa ga Ubangiji, su da ‘yan’uwansu, duka waɗanda suke ƙwararru, su ɗari biyu da tamanin da takwas ne.

8 Sai suka jefa kuri’a domin su ba kowa aikin da zai yi, yaro da babba, malami da almajiri.

9-31 Waɗannan su ne shugabannin ƙungiyoyi ashirin da huɗu, na goma sha biyu biyu, bisa ga yadda aka tsara su ga aikin. 1) Yusufu daga iyalin Asaf, 2) Gedaliya, 3) Zakkur, 4) Zeri, 5) Netaniya, 6) Bukkiya, 7) Asharela, 8) Yeshaya, 9) Mattaniya, 10) Shimai, 11) Uzziyel, 12) Hashabiya, 13) Shebuwel, 14) Mattitiya, 15) Yeremot, 16) Hananiya, 17) Yoshbekasha, 18) Hanani, 19) Malloti, 20) Eliyata, 21) Hotir, 22) Giddalti, 23) Mahaziyot, 24) Romamtiyezer.

Categories
1 TAR

1 TAR 26

Masu Tsaron Haikali da Shugabanni

1 Ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi ke nan. Na wajen Kora shi ne Shallum ɗan Kore, daga cikin iyalin Ebiyasaf.

2 Shallum kuwa yana da ‘ya’ya maza, su ne Zakariya, da Yediyayel, da Zabadiya, da Yatniyel,

3 da Elam, da Yehohanan, da Eliyehoyenai, su bakwai ke nan.

4 Obed-edom kuma Allah ya ba shi ‘ya’ya maza, su ne Shemaiya, da Yehozabad, da Yowa, da Sakar, da Netanel,

5 da Ammiyel, da Issaka, da Fauletai, da su Allah ya sa masa albarka.

6 Ɗan farin Obed-edom, wato Shemaiya ya haifi ‘ya’ya maza waɗanda suka yi shugabanci a gidan kakansu, gama su jarumawa ne.

7 ‘Ya’yan Shemaiya, su ne Otni, da Refayel, da Obida, da Elzabad, waɗanda ‘yan’uwansu, Elihu, da Semakiya jarumawa ne.

8 Waɗannan duka iyalin Obed-edom ne. Su da ‘ya’yansu maza da ‘yan’uwansu suna da ƙarfi da gwaninta na yin aiki. Su sittin da biyu ne daga wajen Obed-edom.

9 Shallum yana da ‘ya’ya maza da ‘yan’uwa, su goma sha takwas jarumawa.

10 Hosa kuma na wajen ‘ya’yan Merari, maza, yana da ‘ya’ya maza, Shimri shi ne babba, ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka mahaifinsa ya maishe shi babba.

11 Hilkiya shi ne na biyu, da Tebaliya na uku, da Zakariya na huɗu. Dukan ‘ya’yan Hosa, maza, da ‘yan’uwansa, su goma sha uku ne.

12 Aka rarraba masu tsaron Haikali ƙungiya ƙungiya, bisa ga iyali, aka raba musu ayyuka a Haikali kamar dai sauran Lawiyawa.

13 Sai suka jefa kuri’a bisa ga gidajen kakanninsu, ba a damu da yawan jama’a a iyali ba, a kan kowace ƙofar.

14 Kuri’a ta ƙofar gabas ta faɗo a kan Shallum. Sai aka jefa kuri’a don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai kuri’a ta ƙofar arewa ta faɗo a kansa.

15 Kuri’a ta ƙofar kudu ta faɗo a kan Obed-edom. Aka sa ‘ya’yansa maza su lura da ɗakunan ajiya.

16 Kuri’a ta ƙofar yamma kusa da Ƙofar Shalleket, a kan hanyar da ta haura, ta faɗo a kan Shuffim da Hosa. Aka raba aikin tsaro bisa ga lokatan da aka tsara bi da bi.

17 A kowace rana Lawiyawa shida suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.

18 A ɗan ɗakin da take wajen yamma, akwai masu tsaro huɗu a hanyar, biyu kuma a ɗan ɗakin.

19 Waɗannan su ne ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi daga zuriyar Kora da ta Merari.

Sauran Ayyukan Haikali

20 Sauran Lawiyawa, ‘yan’uwansu kuwa, suke lura da baitulmalin Haikalin Allah, da ɗakin ajiyar kayan da aka keɓe ga Allah.

21 Libni daga cikin iyalin Gershon, shi ne kakan ƙungiyoyin iyali da dama, iyalin Yehiyel ne ɗaya daga cikinsu.

22 Biyu daga cikin wannan iyali, wato Zetam da Yowel, suke lura da baitulmalin Haikali da ɗakin ajiyar kaya.

23 Aka raba aiki kuma ga zuriyar Amram, da ta Izhara, da ta Hebron, da kuma ta Uzziyel.

24 Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’in baitulmalin.

25 Ta wurin ɗan’uwan Gershom, wato Eliyezer ya sami dangantaka da Shelomit. Eliyezer shi ne mahaifin Rehabiya, wanda ya haifi Yeshaya, uban Yoram, da Zikri, da Shelomit.

26 Shi wannan Shelomit da ‘yan’uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah.

27 Daga cikin ganimar yaƙi suka keɓe wani sashi domin gyaran Haikalin Ubangiji.

28 Dukan kuma abin da Sama’ila annabi, da Saul ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruya, suka keɓe an sa su a hannun Shelomit da ‘yan’uwansa.

Ayyukan Sauran Lawiyawa

29 Kenaniya da ‘ya’yansa maza na wajen Izhara su ne aka danƙa wa al’amuran sasantawa na Isra’ilawa, wato sun zama shugabanni da alƙalai.

30 Hashabiya da ‘yan’uwansu, su dubu da ɗari bakwai (1,700), gwanaye ne, daga zuriyar Hebron, su ne suke lura da Isra’ilawan yamma da Urdun a kan aikin Ubangiji da na sarki.

31 Yeriya shi ne shugaban zuriyar Hebron bisa ga asalinsu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a cikinsu, a Yazar ta Gileyad.

32 Sarki Dawuda ya sa shi, shi da ‘yan’uwansu su dubu biyu da ɗari bakwai (2,700) gwanaye, waɗanda suke shugabancin gidajen kakanni, su lura da kabilar Ra’ubainu, da ta Gad, da rabin kabilar Manassa a kan dukan ayyukan Allah da na sarki.

Categories
1 TAR

1 TAR 27

Manyan Ma’aikatan Mulki

1 Ga lissafin kawunan iyalin Isra’ilawa, da shugabannin dangi, da jama’a masu gudanar da ayyukan mulki. A kowane wata akan sauya aikin ƙungiyar mutum dubu ashirin da dubu huɗu (24,000), a ƙarƙashin shugaban aiki na wannan wata. Kowane wata akan sauya, wata ƙungiya ta kama aiki.

2-15 Waɗannan su ne shugabanni don kowane wata.

Wata na 1, Yashobeyam, ɗan Zabdiyel. (Shi daga dangin Feresa na kabilar Yahuza ne.)

Wata na 2, Dodai, ɗan Ahowa. (Miklot yake bi masa a shugabancin.)

Wata na 3, Benaiya, ɗan Yehoyada firist. Shugaba ne daga cikin sanannun nan “talatin.” (Ɗansa Ammizzabad ya gāje shi a shugabancin ƙungiya.)

Wata na 4, Asahel, ƙanen Yowab. (Ɗansa Zabadiya ya gāje shi.)

Wata na 5, Shimeya, daga zuriyar Izhara.

Wata na 6, Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa.

Wata na 7, Helez, mutumin Ifraimu, daga Felet.

Wata na 8, Sibbekai, daga garin Husha. (Shi daga dangin Zera ne, na kabilar Yahuza.)

Wata na 9, Abiyezer, daga Anatot na kabilar Biliyaminu.

Wata na 10, Maharai, daga Netofa. (Shi ma daga dangin Zera ya fito.)

Wata na 11, Benaiya, daga Firaton na kabilar Ifraimu.

Wata na 12, Heled, daga Netofa. (Shi daga zuriyar Otniyel ne.)

Aikin Mulkin Kabilan Isra’ila

16-22 Ga jerin sunayen masu mulkin kabilan Isra’ila.

Ra’ubainu: Eliyezer ɗan Zikri,
Saminu: Shefatiya ɗan Ma’aka,
Lawi: Hashabiya ɗan Kemuwel,
Haruna: Zadok,
Yahuza: Eliyab ɗaya daga cikin ‘yan’uwan sarki Dawuda,
Issaka: Omri ɗan Maikel,
Zabaluna: Ishmaiya ɗan Obadiya,
Naftali: Yerimot ɗan Azriyel,
Ifraimu: Hosheya ɗan Azaziya,
Manassa ta Yamma: Yowel ɗan Fedaiya,
Manassa ta Gabas: Iddo ɗan Zakariya,
Biliyaminu: Yawasiyel ɗan Abner,
Dan: Azarel ɗan Yeroham.

Waɗannan su ne shugabannin kabilai.

23 Sarki Dawuda bai ƙidaya waɗanda shekarunsu suka kasa ashirin ba, gama Ubangiji ya yi alkawari zai sa mutanen Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.

24 Yowab ɗan Zeruya ne ya fara ƙidayar, amma bai gama ba. Allah ya hukunta wa Isra’ila saboda wannan ƙidaya, saboda haka ba za a taɓa samun cikakken adadi a lissafin da suke a ajiye na fādawan sarki Dawuda ba.

Masu Lura da Dukiyar Sarki

25-30 Ga lissafin masu sarrafa dukiyar sarki.

Ɗakin ajiya na sarki: Azmawet ɗan Adiyel,

Ƙaramin ɗakin ajiya: Jonatan ɗan Uzziya,

Aikin gona: Ezri ɗan Kabilu,

Kurangar Inabi: Shimai daga Rama,

Ɗakin ajiyar Inabi: Zabdi daga Shefam,

Itatuwan zaitun da na ɓaure (a gindin tsaunukan yamma): Ba’al-hanan daga Geder,

Ajiyar man zaitun: Yowash,

Garken shanu na filin Sharon: Shirtai daga Sharon,

Garken shanu na cikin kwari: Shafat ɗan Adlai,

Raƙuma: Obil Ba’isma’ile,

Jakuna: Yedaiya daga Meronot,

Tumaki: Yaziz Bahagire.

31 Dukan waɗannan su ne masu lura da dukiyar sarki Dawuda.

Ƙwararrun Mashawartan Dawuda

32 Jonatan, kawun Dawuda, shi ne mai ba da shawara, yana da ganewa, shi kuma magatakarda ne. Shi da Yehiyel ɗan Hakmoni su ne masu koya wa ‘ya’yan sarki, maza.

33 Ahitofel shi abokin shawarar sarki ne. Hushai Ba’arkite kuwa shi ne abokin sarki.

34 Sai Yehoyada ɗan Benaiya, da Abiyata suka gāji matsayin Ahitofel. Yowab shi ne babban shugaban sojojin sarki.

Categories
1 TAR

1 TAR 28

Dawuda Ya Danƙa Ginin Haikali ga Sulemanu

1 Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra’ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na ‘ya’yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.

2 Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku ‘yan’uwana, da jama’ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,

3 amma Allah bai yardar mini in yi da kaina ba, domin ni mayaƙi ne, na kuwa zubar da jini.

4 Duk da haka Ubangiji Allah na Isra’ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra’ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin ‘ya’yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra’ila.

5 Daga cikin dukan ‘ya’yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni ‘ya’ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra’ila, abin mulkin Ubangiji.

6 “Ya ce mini, ‘Ɗanka Sulemanu ne zai gina Haikalina da shirayuna, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa in zama uba a gare shi.

7 Zan tabbatar da mulkinsa har abada idan ya bi umarnaina da ka’idodina da himma kamar yadda ake yi a yau.’

8 “Saboda haka a gaban dukan Isra’ila, wato taron jama’ar Ubangiji, da kuma gaban Allahnmu, sai ku kiyaye, ku bi dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki ƙasan nan mai kyau, ku kuma bar wa ‘ya’yanku ita gādo har abada.

9 “Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.

10 Ka lura, gama Ubangiji ya zaɓe ka domin ka gina Haikali, wato Wuri Mai Tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama aiki.”

11 Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi.

12 Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.

13 Ya kuma ba shi tsarin ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, da na dukan hidimar da za a yi a Haikalin Ubangiji, da aikin lura da kayayyakin aiki na cikin Haikalin Ubangiji.

14 Ya kuma faɗa wa Sulemanu yawan zinariya da za a yi kwanoni da ita don yin aiki, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita don yin aiki,

15 da yawan zinariya da za a yi alkukan fitilu, da kuma fitilun, da yawan zinariya da za a yi kowane alkuki da fitilunsa, da yawan azurfa da za a yi alkuki bisa ga yadda za a yi amfani da kowane alkuki,

16 da yawan zinariya da za a yi teburorin gurasar ajiyewa, da azurfar da za a yi teburorin azurfa,

17 da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi cokula masu yatsotsi, da daruna, da finjalai, da kwanoni da ita, da yawan azurfa da za a yi kwanoni da ita,

18 da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita. Ya kuma ba shi tsarin zinariya ta kerubobin da za su miƙe fikafikansu su rufe akwatin alkawari na Ubangiji.

19 Sarki Dawuda ya ce, “Dukan wannan rubutacce ne daga wurin Ubangiji zuwa gare ni domin in fahimci fasalin aikin filla filla.”

20 Sarki Dawuda kuma ya ce wa ɗansa Sulemanu, “Ka yi ƙarfin hali, ka dāge sosai, ka kama aikin, kada ka ji tsoro, kada kuwa ka karai, gama Ubangiji Allah, wato Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ba, ba kuwa zai rabu da kai ba, har ka gama dukan aikin Haikalin.

21 Ga dai ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, suna nan domin yin hidima a Haikalin Allah, ga kuma gwanaye na kowace irin sana’a suna tare da kai don yin kowane irin aiki. Shugabanni da dukan jama’a suna ƙarƙashinka duka.”

Categories
1 TAR

1 TAR 29

Ba Da Kyautai domin Gina Haikali

1 Sarki Dawuda fa ya yi magana da dukan taron, ya ce, “Ga shi, ɗana Sulemanu, wanda Allah ya zaɓa, shi dai saurayi ne tukuna, bai gogu da duniya ba tukuna, aikin kuwa babba ne, gama Haikali ba na mutum ba ne, amma na Ubangiji Allah ne.

2 A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.

3 Saboda kuma ƙaunar Haikalin Allahna da nake yi, shi ya sa na ba da zinariyata da azurfata domin Haikalin Allahna, banda wanda na riga na tanada saboda Haikali mai tsarki.

4 Na ba da zinariya tsantsa, talanti dubu uku (3,000), da azurfa tsantsa, talanti dubu bakwai (7,000), domin yin ado a bangon Haikalin,

5 da kuma dukan kayayyakin da masu sana’a za su yi. Yanzu fa ko akwai mai niyyar ba da sadaka ta yardar rai ga Ubangiji?”

6 Sa’an nan shugabannin gidajen kakanni, da shugabannin kabilai, da shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da aikin sarki, suka bayar da yardar rai.

7 Sun ba da zinariya talanti dubu biyar (5,000), da darik dubu goma (10,000), da azurfa talanti dubu goma (10,000), da tagulla talanti goma sha takwas (18,000), da ƙarfe talanti dubu ɗari (100,000).

8 Dukan waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka bayar da su cikin taskar Haikalin Ubangiji, ta hannun Yehiyel Bagershone.

9 Sai jama’a suka yi murna da ganin yadda suka bayar hannu sake, gama sun kawo sadakokinsu a gaban Ubangiji da zuciya ɗaya, shi sarki Dawuda kuma ya yi murna ƙwarai.

Dawuda Ya Yabi Allah

10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanmu Yakubu, yabo ya tabbata gare ka har abada abadin!

11 Girma, da iko, da daraja, da nasara, da ɗaukaka duk naka ne, ya Ubangiji, gama dukan abin da yake cikin sammai da duniya naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji. Kai ne Maɗaukaki duka.

12 Dukan wadata da girma daga gare ka suke, kai kake mulki da dukan iko da ƙarfi. Kai ne kake da iko ka ba mutum iko da ƙarfi.

13 Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.

14 “Amma wane ni ko kuma jama’ata, da za mu iya kawo sadaka mai yawa haka? Gama dukan kome daga gare ka yake. Daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.

15 Gama mu kamar baƙi ne, masu yawo a gabanka kamar kakanninmu. Kwanakinmu a duniya kamar inuwa ne, ba za mu tsere wa mutuwa ba.

16 Ya Ubangiji Allahnmu, duk wannan da muka kawo domin mu gina maka Haikali saboda sunanka mai tsarki, daga gare ka ne muka samu, duka naka ne.

17 Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama’arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.

18 Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kakanninmu, ka tabbatar da yardar rai ɗin nan a rayukan jama’arka, ka bi da zukatansu zuwa gare ka.

19 Ka kuma ba ɗana Sulemanu cikakkiyar zuciya, har da zai kiyaye umarnanka, da shaidunka, da dokokinka, domin ya aikata su duka, ya kuma gina Haikali wanda na riga na yi tanadi dominsa.”

Sulemanu Ya Gāji Dawuda

20 Sa’an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama’a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.

21 Kashegari sai suka miƙa wa Ubangiji hadayu, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji, bijimai dubu ɗaya (1,000), da raguna dubu ɗaya (1,000), da ‘yan raguna dubu ɗaya (1,000), da hadayunsu na sha, da hadayu masu yawa domin Isra’ila duka.

22 Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana.

Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.

23 Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra’ilawa dukansu suka yi masa biyayya.

24 Dukan ma’aikatan hukuma kuwa, da manyan mutane, da kuma dukan ‘ya’yan sarki Dawuda, suka yi alkawari za su yi wa sarki Sulemanu biyayya.

25 Ubangiji kuwa ya ɗaukaka Sulemanu ƙwarai da gaske a gaban dukan Isra’ilawa, ya ɗaukaka sarautarsa fiye da ta waɗanda suka riga shi sarauta a Isra’ila.

Sarautar Dawuda a Taƙaice

26 Dawuda ɗan Yesse ya yi mulki bisa dukan Isra’ila,

27 har shekara arba’in. Ya yi mulki a Hebron shekara bakwai sa’an nan ya yi mulki shekara talatin da uku a Urushalima.

28 Sa’an nan ya rasu da kyakkyawan tsufa, cike da shekaru, da arziki, da daraja. Ɗansa Sulemanu kuma ya gāji sarautarsa.

29 An fa rubuta ayyukan sarki Dawuda daga farko har ƙarshe a tarihin Sama’ila, annabi, da na annabi Natan, da na annabi Gad.

30 An rubuta labarin mulkinsa, da ikonsa, da al’amuran da suka same shi, da Isra’ilawa, da dukan mulkokin ƙasashe na kewaye.