Categories
2 SAM

2 SAM 11

Dawuda da Bat-Sheba

1 Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra’ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.

2 Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.

3 Sai ya aika a bincika ko wace ce wannan mata, ashe, ‘yar Ammiyel ce, matar Uriya Bahitte.

4 Dawuda kuwa ya aiki waɗansu manzanni suka kawo masa ita, ya kwana da ita. (A lokacin kuwa ta gama wankan haila ke nan.) Sa’an nan ta koma gidanta.

5 Matar kuwa ta yi juna biyu, sai ta aika a faɗa wa Dawuda, cewa, tana da ciki.

6 Dawuda kuwa ya aika wurin Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya Bahitte.” Yowab kuwa ya aika da Uriya wurin Dawuda.

7 Da Uriya ya iso, sai Dawuda ya tambaye shi labarin Yowab, da lafiyar jama’ar, da labarin yaƙin.

8 Ya kuma ce masa, “Ka tafi gidanka, ka wanke ƙafafunka.” Da Uriya ya fita daga gidan sarki, sarki ya ba da kyauta a kai masa.

9 Amma Uriya bai tafi gidansa ba, sai ya kwana a ƙofar gidan sarki tare da sauran barorin sarki.

10 Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”

11 Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra’ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”

12 Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan.

13 Kashegari kuma Dawuda ya kira shi liyafa. Ya zo, ya ci ya sha tare da shi, har Dawuda ya sa shi ya bugu. Amma da dare, sai ya tafi ya kwanta a shimfiɗarsa tare da sauran barorin sarki, amma bai tafi gidansa ba.

14 Da safe Dawuda ya rubuta wasiƙa, ya ba Uriya ya kai wa Yowab.

15 A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa’an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.”

16 Sa’ad da Yowab yake kama garin da yaƙi, sai ya sa Uriya a inda ya sani akwai jarumawan gaske.

17 Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.

18 Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin.

19-20 Ya ce wa manzo, “Bayan da ka gama faɗa wa sarki labarin yaƙin duka, idan sarki ya husata, har ya ce maka, ‘Me ya sa kuka tafi yaƙi kurkusa da garin? Ba ku sani ba za su tsaya a gefen garu daga ciki su yi harbi?

21 Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubba’al? Ba mace ce a TebEze ta jefe shi da ɗan dutsen niƙa ta kan garu daga ciki ta kashe shi ba? Me ya sa kuka tafi kusa da garu?’ Sai ka faɗa masa cewa, ‘Baranka, Uriya Bahitte, shi ma an kashe shi.’ ”

22 Manzon kuwa ya tafi ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Yowab ya ce.

23 Ya ce, “Abokan gābanmu sun sami sa’a a kanmu. Sun fito su gabza da mu a karkara, amma muka kore su zuwa cikin ƙofar garin.

24 Sai maharba suka tsaya a kan garu daga ciki suka yi ta harbin barorinka. Waɗansu daga cikin barorin sarki sun mutu. Baranka Uriya Bahitte shi ma ya matu.”

25 Dawuda ya ce wa manzon, “Je ka ka faɗa wa Yowab kada wannan abu ya dame shi, ai, takobi ba ya tarar wanda zai kashe. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku faɗa masa har ku ragargaza shi. Ka ƙarfafa Yowab.”

26 Sa’ad da matar Uriya ta ji labarin mutuwar mijinta, ta yi makoki dominsa.

27 Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.

Categories
2 SAM

2 SAM 12

Natan Ya Tsauta wa Dawuda

1 Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.

2 Basaraken yana da garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu.

3 Amma talakan ba shi da kome sai ‘yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi renonta, ta yi girma a wurinsa, tare da ‘ya’yansa. Takan ci daga cikin ɗan abincinsa, ta kuma sha daga cikin abin shansa, ta kwanta a ƙirjinsa. Ta zama kamar ‘ya a gare shi.

4 Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo ‘yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”

5 Dawuda ya husata ƙwarai a kan mutumin, ya ce wa Natan, “Hakika mutumin da ya yi haka ya cancanci mutuwa.

6 Sai kuma ya biya diyyar ‘yar tunkiya riɓi huɗu, domin ya aikata mugun abu na rashin tausayi.”

7 Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra’ila, na cece ka daga hannun Saul.

8 Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra’ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka.

9 Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka.

10 Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka.

11 Na rantse zan sa wani daga cikin iyalinka ya far maka da tashin hankali. A idonka zan ba da matanka ga wani mutum. Zai kwana da su da rana katā.

12 Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra’ila da rana katā.’ ”

13 Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”

Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.

14 Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.”

15 Sa’an nan Natan ya tafi gida.

Ɗan Dawuda Ya Mutu, aka Haifi Sulemanu

Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda.

16 Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.

17 Sai fādawansa suka zo suka kewaye shi, don su tashe shi daga ƙasa, amma bai yarda ba, bai kuma ci abinci tare da su ba.

18 An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.”

19 Da Dawuda ya ga fādawansa suna raɗa da juna, sai ya gane lalle yaron ya rasu. Ya tambaye su, ya ce, “Yaron ya rasu ne?”

Suka amsa cewa, “I, ya rasu.”

20 Sai Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya sake tufafinsa, ya tafi ɗakin sujada, ya yi sujada, sa’an nan ya koma gidansa ya ce a kawo abinci. Suka kawo masa abinci ya ci.

21 Fādawansa suka ce masa, “Me ka yi ke nan? Ka yi azumi, ka yi kuka saboda yaron tun yana da rai, amma da yaron ya rasu ka tashi, ka ci abinci.”

22 Ya ce musu, “Tun yaron yana da rai, na yi azumi da kuka, ina cewa wa ya sani, ko Ubangiji zai yi mini jinƙai, ya bar yaron da rai?

23 Amma yanzu ya rasu, me zai sa kuma in yi azumi? Zan iya koma da shi ne? Ni zan tafi wurinsa, amma shi ba zai komo wurina ba.”

24 Sa’an nan Dawuda ya yi wa Batsheba, matarsa, ta’aziyya. Ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Ta haifa masa ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubangiji kuwa ya ƙaunace shi,

25 ya kuma umarci annabi Natan ya raɗa wa yaron suna Yedideya, wato ƙaunataccen Ubangiji.

Dawuda ya ci Rabba da Yaƙi

26 Yowab kuwa ya yi yaƙi da Rabba ta Ammonawa, yana kuwa gab da cin birnin.

27 Sai ya aiki manzanni wurin Dawuda ya ce, “Na yaƙi Rabba, na kama hanyar samun ruwansu.

28 Yanzu ka tara sauran sojoji ka fāɗa wa birnin, ka ci shi da kanka. Gama ba na so in yi suna da cin birnin.”

29 Saboda haka sai Dawuda ya tara sauran sojoji duka, ya tafi Rabba, ya yi yaƙi da ita, ya kuwa ci birnin.

30 Sarkinsu, wato Milkom, yana da kambi na zinariya a kansa, nauyinsa ya kai talanti ɗaya na zinariya yana kuma da duwatsu masu daraja cikinsa. Dawuda kuwa ya ɗauke kambin daga kan sarkin ya sa a nasa. Sa’an nan ya kwaso ganima mai ɗumbun yawa daga cikin birnin.

31 Ya kuma kamo mutanen da suke cikin birnin, ya sa su su yi aiki da zartuka, da faretani, da gatura. Ya kuma sa su yi tubula. Haka Dawuda ya yi da dukan biranen Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan sojojinsa suka koma Urushalima.

Categories
2 SAM

2 SAM 13

Amnon da Tamar

1 Absalom, ɗan Dawuda, yana da kyakkyawar ƙanwa, sunanta Tamar. Ana nan Amnon ɗaya daga cikin ‘ya’yan Dawuda, ya ƙaunace ta.

2 Amnon ya matsu har ya fara ciwo saboda Tamar ƙanwarsa. Ita kuwa budurwa ce, ba shi yiwuwa Amnon ya yi wani abu da ita.

3 Amma Amnon yana abuta da Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab kuwa yana da hila.

4 Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?”

Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan’uwana Absalom.”

5 Yonadab kuwa ya ce masa, “Kwanta a gadonka ka yi kamar kana ciwo, lokacin da mahaifinka ya zo domin ya duba ka, sai ka ce masa, ‘A bar ƙanwata Tamar ta zo ta ba ni abinci, ta riƙa shirya abincin a idona, don in gani in kuma riƙa ci daga hannunta.’ ”

6 Amnon kuwa ya kwanta, ya yi kamar yana ciwo.

Sa’ad da sarki ya zo duba shi, sai Amnon ya ce wa sarki, “Ina roƙo a sa ƙanwata, Tamar, ta zo ta toya mini waina a inda nake, ta riƙa ba ni da hannunta ina ci.”

7 Sai Dawuda ya aika gida, wurin Tamar, ya ce, “Tafi gidan Amnon wanki, ki shirya masa abinci.”

8 Tamar kuwa ta tafi gidan wanta Amnon, inda yake kwance. Sai ta ɗauki ƙullu, ta cuɗa, ta toya waina a idonsa.

9 Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.

10 Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana.

11 Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”

12 Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra’ila, kada ka yi halin dabba.

13 Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra’ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.”

14 Amma Amnon bai ji maganarta ba. Da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata faɗe.

15 Bayan haka sai Amnon ya ƙi ta da mummunar ƙiyayya, har ƙiyayyar ta fi yawan ƙaunar da ya yi mata. Ya ce mata, “Tashi, ki fita.”

16 Sai ta ce masa, “A’a wana, muguntar koran nan da kake yi mini, ta fi ta wadda ka riga ka yi mini.”

Amma bai kasa kunne gare ta ba.

17 Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”

18 Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar.

19 Tamar ta baɗe kanta da toka, ta keta doguwar rigarta mai hannuwa wadda ta sa, ta rufe fuska da hannu, ta tafi tana ta kuka da ƙarfi.

20 Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta.

21 Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.

22 Amma Absalom bai tanka wa Amnon da wata magana ta alheri ko ta mugunta ba, gama yana ƙin Amnon saboda ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.

Absalom Ya Rama Ya Gudu

23 Bayan shekara biyu cif, sai Absalom ya sa a yi masa sausayar tumaki a Ba’al-hazor, wadda take kusa da Ifraimu. Ya kuma gayyaci dukan ‘yan’uwansa, wato ‘yan sarki.

24 Ya kuma tafi wurin sarki, ya ce masa, “Ranka ya daɗe, ga shi, ina sausayar tumakina, ina roƙonka, ka zo, kai da fādawanka tare da ni.”

25 Amma sarki ya ce wa Absalom, “A’a ɗana, ba ma tafi duka ba, don kada mu nawaita maka.” Absalom ya dāge cewa, sai sarki ya je, amma duk da haka sarki bai tafi ba, sai dai ya sa masa albarka.

26 Sa’an nan Absalom ya ce, “Idan ba za ka tafi ba, ina roƙonka ka bar Amnon ɗan’uwana ya tafi tare da mu.”

Sarki ya ce, “Don me zai tafi tare da kai?”

27 Amma Absalom ya dāge har sarki ya yarda. Amnon da dukan ‘ya’yan sarki suka tafi tare da shi.

28 Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa’ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, ‘Bugi Amnon’, sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.”

29 Haka kuwa barorin Absalom suka kashe Amnon yadda Absalom ya umarta. Sauran ‘ya’yan sarki kuwa suka tashi, kowa ya hau alfadarinsa, ya gudu.

30 Sa’ad da suke kan hanya labari ya kai kunnen Dawuda. Aka ce, “Absalom ya kashe dukan ‘ya’yan sarki, ba wanda ya tsira daga cikinsu.”

31 Sai sarki ya tashi ya keta rigunansa, ya kwanta a ƙasa. Dukan barorinsa kuma da suke tsaye a wurin suka kyakketa rigunansu.

32 Amma Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda, ya ce, “Ranka ya daɗe, ba fa dukan ‘ya’yan sarki aka kashe ba. Amnon ne kaɗai aka kashe ta umarnin Absalom, gama ya ƙudura wannan tun daga ranar da Amnon ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.

33 Don haka, kada shugabana sarki ya damu, cewa, an kashe dukan ‘ya’yan sarki, gama Amnon ne kaɗai aka kashe.”

34 Absalom kuwa ya gudu.

Sa’an nan sojan da yake tsaro a wannan lokaci ya ga ɗumbun mutane suna tahowa daga hanyar Horonayim, wajen gefen dutse.

35 Sai Yonadab ya ce wa sarki, “Waɗannan ‘ya’yan sarki ne yake zuwa, kamar yadda na faɗa.”

36 Yana gama magana ke nan, sai ga ‘ya’yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.

37 Amma Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai, ɗan Ammihud, Sarkin Geshur. Dawuda kuwa ya yi makokin Amnon ɗansa kwana da kwanaki.

38 Absalom ya shekara uku a Geshur.

39 Sai zuciyar sarki ta koma kan Absalom, gama ya haƙura a kan Amnon da yake ya riga ya rasu.

Categories
2 SAM

2 SAM 14

Yowab Ya Shirya yadda Absalom zai Koma

1 Da Yowab ɗan Zeruya, ya gane zuciyar sarki ta koma kan Absalom,

2 sai ya aika zuwa Tekowa a kira masa wata mace mai hikima. Da ta zo, ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki, ki sa rigunan makoki, kada ki shafa mai. Ki yi kamar wadda ta yi kwanaki da yawa tana makokin rasuwar wani.

3 Sa’an nan ki tafi wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai ya faɗa mata abin da za ta faɗa.

4 Sa’ad da macen nan da ta zo daga Tekowa ta isa gaban sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma. Sa’an nan ta ce, “Ya sarki, ka yi taimako.”

5 Sai sarki ya tambaye ta, “Me ya dame ki?”

Ta ce, “Ni mace ce wadda mijinta ya rasu.

6 Baranyarka tana da ‘ya’ya biyu maza, sai suka yi faɗa a gona, inda ba wanda zai raba su, ɗayan kuwa ya bugi ɗayan ya kashe shi.

7 Yanzu kuwa dukan dangi sun tasar mini, suna cewa, in ba da ɗayan wanda ya kashe ɗan’uwansa domin su kashe shi saboda ran ɗan’uwansa da ya kashe. Wato za su hallaka magāji ke nan, ta haka za a yi biyu babu ke nan, su bar mijina ba suna ko zuriya a duniya.”

8 Sarki kuwa ya ce mata, “Ki tafi gidanki, zan daidaita maganarki.”

9 Sai ta ce wa sarki, “Ya ubangijina, sarki, bari laifin ya zauna a kaina da gidan mahaifina, sarki kuwa da gadon sarautarsa ya barata.”

10 Sarki ya ce mata, “In wani ya ƙara ce miki wani abu, ki kawo shi wurina, ba zai ƙara yi miki fitina ba.”

11 Sai ta ce, “Ina roƙonka, ya sarki, ka rantse da Ubangiji Allahnka, kada a bar masu bin hakkin jini su yi ramako, don kada su kashe ɗana.”

Ya ce mata, “Na rantse miki da zatin Ubangiji, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba.”

12 Ta kuma ce, “Ina roƙonka, ya ubangijina sarki, ka bar ni in yi magana.”

Sai ya ce, “Yi maganarki.”

13 Sa’an nan ta ce, “To, me ya sa ka yi wa jama’ar Allah irin wannan abu? Gama bisa ga maganar bakinka, ya sarki, ka hukunta kanka tun da yake sarki bai yarda ɗansa ya komo gida ba.

14 Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.

15 Saboda mutane sun tsorata ni shi ya sa na zo in faɗa wa ubanjijina, sarki. Na kuwa yi tunani na ce, ‘Zan tafi in faɗa wa sarki, watakila sarki zai amsa roƙona.

16 Gama sarki zai ji, ya cece ni daga hannun mutumin nan da zai hallaka ni tare da ɗana daga cikin jama’ar Allah.’

17 Na kuma yi tunani a kan maganar ubangijina, sarki, za ta kwantar da zuciyata, gama ubangijina, sarki, kamar mala’ikan Allah yake, yana rarrabe tsakanin nagarta da mugunta. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da kai!”

18 Sai sarki ya ce mata, “Kada ki rufe mini duk abin da zan tambaye ki.”

Ta ce, “To, ka yi tambayarka.”

19 Sa’an nan ya ce mata, “Ko akwai hannun Yowab cikin dukan sha’anin nan naki?”

Ita kuwa ta amsa, “Na rantse da kai, ya ubangijina, sarki, ba dama a yi maka ƙumbiya-ƙumbiya. Haka ne, Yowab baranka ne ya sa ni. Shi ya sa dukan waɗannan magana a bakin baranyarka.

20 Yowab baranka ya yi wannan don ya daidaita al’amarin. Amma ubangijina yana da hikima irin ta mala’ikan Allah domin ya san dukan al’amuran da suke a duniya.”

21 Sa’an nan sarki ya ce wa Yowab, “To, na yarda, sai ka tafi ka komo da saurayin nan, Absalom.”

22 Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.”

23 Sa’an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.

24 Sarki ya ce a sa shi ya koma gidansa, kada ya zo gabansa. Absalom kuwa ya yi zamansa can gidansa, bai je gaban sarki ba.

Absalom Ya Sulhunta da Dawuda

25 A cikin Isra’ila duka ba wanda ake yaba kyansa kamar Absalom. Tun daga tafin sawunsa har zuwa bisa kansa ba shi da makusa.

26 Sa’ad da ya yi aski yakan auna nauyin gashin kansa, nauyin yakan kai wajen shekel ɗari biyu. Gama a ƙarshen kowace shekara yake aski, sa’ad da gashin ya yi masa nauyi.

27 Aka haifa wa Absalom ‘ya’ya uku maza da ‘ya mace guda, sunanta Tamar, ita kuwa kyakkyawa ce.

28 Absalom ya yi shekara biyu cif a Urushalima, amma bai sami izinin ganin sarki ba.

29 Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don ya aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Ya kuma sāke aikawa, Yowab kuwa ya ƙi zuwa.

30 Sai ya ce wa barorinsa, “Ga Yowab yana da gonar sha’ir kusa da tawa, ku tafi, ku sa mata wuta.” Barorin Absalom kuwa suka tafi suka sa wa gonar wuta.

31 Yowab kuwa ya tashi ya tafi wurin Absalom har gidansa, ya ce masa, “Don me barorinka suka sa wa gonata wuta?”

32 Absalom ya ce wa Yowab, “Har sau biyu na aika maka domin ka zo in aike ka wurin sarki, ka tambaya mini, ‘Ko me ya sa na komo daga Geshur?’ Da ma ina can har yanzu, ai, da ya fi mini. Yanzu har ni in tafi wurin sarki, idan ina da laifi, to, ya kashe ni.”

33 Sai Yowab ya tafi wurin sarki, ya faɗa masa. Sarki ya sa a kira Absalom. Absalom kuwa ya zo gaban sarki, ya rusuna har ƙasa. Sarki kuwa ya marabce shi, ya yi masa sumba.

Categories
2 SAM

2 SAM 15

Absalom ya Tayar wa Dawuda

1 Bayan wannan Absalom ya samo wa kansa karusa, da dawakai, da zagage mutum hamsin.

2 Absalom yakan tashi da wuri, ya tsaya a kan hanyar da take shiga ƙofar garin. Idan wani mai kai ƙara ya zo wurin sarki don shari’a, Absalom yakan kira shi, ya ce, “Daga ina kake?” Idan mutumin ya faɗa masa garin da ya fito daga cikin Isra’ila,

3 sai Absalom ya ce masa, “Ƙararka tana da kyau, tana kuma da gaskiya, amma sarki ba zai yi maka shari’a ba.”

4 Yakan kuma ƙara da cewa, “Kai, in da a ce ni ne alƙali a ƙasar, zan yi wa duk wanda ya zo wurina da ƙara, shari’ar gaskiya.”

5 Sa’ad da mutum ya je kusa da shi ya rusuna don ya gaishe shi, Absalom kuwa yakan rungume mutumin ya sumbace shi.

6 Haka Absalom ya riƙa yi wa dukan Isra’ilawan da suka zo wurin sarki don shari’a. Da haka ya saci zukatan mutanen Isra’ila.

7 Bayan shekara huɗu sai Absalom ya ce wa sarki, “Ina roƙonka, ka yardar mini in je Hebron in cika wa’adina wanda na yi wa Ubangiji.

8 Gama na yi wa’adi sa’ad da nake zaune a Geshur ta Suriya. Na yi wa’adi cewa, ‘Idan dai Ubangiji ya komar da ni Urushalima zan bauta masa.’ ”

9 Sarki ya ce masa, “To, ka sauka lafiya.” Sai ya tashi ya tafi Hebron.

10 Amma Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra’ila a faɗa musu haka, “Da zarar kun ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom shi ne sarki, yana Hebron.’ ”

11 Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba.

12 Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.

Dawuda Ya Gudu daga Urushalima

13 Ana nan sai wani manzo ya zo wurin Dawuda, ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra’ila suna wajen Absalom.”

14 Sa’an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”

15 Fādawan suka ce, “Mu a shirye muke mu yi dukan abin da ubangijinmu sarki ya faɗa.”

16 Sarki ya fita, iyalinsa suka bi shi, amma ya bar ƙwaraƙwarai goma su lura da gidan.

17 Sarki ya fita yana tafiya da ƙafa, dukan mutane kuwa suna biye da shi. Da suka zo Bet-Merhak, wato gida na ƙarshe sai suka tsaya.

18 Dukan fādawansa, da matsaransa, wato dukan Keretiyawa, da dukan Feletiyawa, da dukan Gittiyawa, sojoji ɗari shida waɗanda suka bi Dawuda tun daga Gat suka wuce a gabansa.

19 Sarki kuwa ya ce wa Ittayi, shugabansu, “Don me kai kuma za ka tafi tare da mu? Koma ka zauna wurin sabon sarki, gama kai baƙo ne, ɗan gudun hijira kuma daga ƙasarku.

20 Jiya jiya ka zo, ba daidai ba ne in sa ka ka yi ta ragaita tare da mu, ga shi, ban san inda zan tafi ba. Koma tare da ‘yan’uwanka. Ubangiji ya nuna maka alherinsa, da amincinsa.”

21 Amma Ittayi ya amsa wa sarki, ya ce, “Na rantse da zatin Ubangiji da darajar ubangijina, sarki, duk inda za ka tafi ko a mutu ko a yi rai zan tafi.”

22 Sai Dawuda ya ce masa, “To, wuce gaba.” Ittayi Bagitte kuwa ya wuce gaba tare da dukan mutanensa da ‘yan yaransu.

23 Dukan ƙasar ta yi ta kururuwa sa’ad da mutane suka tashi. Sarki ya haye rafin Kidron, mutane kuma suka haye, suka nufi jeji.

24 Sai ga Abiyata ya zo, sai kuma ga Zadok ya zo tare da dukan Lawiyawa, ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka ajiye akwatin har dukan mutane suka gama fita daga birnin.

25 Sa’an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka koma da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a wurin Ubangiji zai komo da ni, zan sāke ganin akwatin da mazaunin zatinsa.

26 Amma idan Ubangiji bai ji daɗina ba, to, ga ni, sai ya yi yadda ya ga dama da ni.”

27 Sa’an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da ‘ya’yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata.

28 Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”

29 Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.

30 Dawuda yana tafe ba takalmi a ƙafarsa, ya rufe kansa, yana ta kuka, sa’ad da yake hawan Dutsen Zaitun, dukan mutane kuma da suke tare da shi suka rufe kawunansu, suna hawa, suna kuka.

31 Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin ‘yan maƙarƙashiya tare da Absalom.”

Sai Dawuda ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”

32 Da Dawuda ya hau kan dutse inda ake yi wa Allah sujada, sai ga amininsa Hushai Ba’arkite, da ketacciyar riga, da ƙura a kansa, ya zo ya taryi Dawuda.

33 Dawuda kuwa ya ce masa, “Idan ka tafi tare da ni za ka zama mini nawaya.

34 Amma in za ka koma cikin birnin, ka ce wa Absalom, ‘Ya sarki, zan zama baranka kamar yadda na zama baran mahaifinka a dā. Haka zan zama baranka.’ Ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.

35 Ga shi, Zadok da Abiyata, firistoci, suna tare da kai. Duk abin da ka ji daga gidan sabon sarki, sai ka faɗa wa Zadok da Abiyata, firistoci.

36 Ga ‘ya’yansu biyu suna tare da su a can, wato Ahimawaz, ɗan Zadok, da Jonatan, ɗan Abiyata. Duk abin da ka ji, ka aiko su, su zo su faɗa mini.”

37 Hushai, abokin Dawuda kuwa, ya isa Urushalima daidai lokacin da Absalom yake shiga.

Categories
2 SAM

2 SAM 16

Dawuda da Ziba

1 Sa’ad da Dawuda ya wuce ƙwanƙolin dutsen kaɗan, sai ga Ziba baran Mefiboshet ya sadu da shi. Ya zo da jaki biyu ya yi musu labtu da gurasa dunƙule ɗari biyu, da zabibi ɗari, da sababbin ‘ya’yan itace guda ɗari, da salkar ruwan inabi.

2 Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?”

Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da ‘ya’yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”

3 Sarki kuma ya tambaye shi, “Ina ɗan ubangijinka?”

Sai Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima, yana cewa, ‘Yanzu dai mutanen gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar tsohona.’ ”

4 Da jin haka sai sarki ya ce wa Ziba, “Dukan abin da yake na Mefiboshet ya zama naka.”

Ziba kuma ya rusuna ya yi godiya ya ce, “Bari in zama majidaɗin ubangijina, sarki.”

Dawuda da Shimai

5 Sa’ad da Dawuda ya kai Bahurim, sai ga wani mutum sunansa Shimai, ɗan Gera, daga iyalin gidan Saul, ya fito yana ta zagi.

6 Ya jajjefi Dawuda da fādawansa da duwatsu, da sauran jama’a, da dukan jarumawan da suke kewaye da shi.

7 Shimai ya yi ta zagi, yana cewa, “Tafi, tafi, kai mai kisankai, sakarai.

8 Ubangiji ya sāka maka saboda alhakin jinin gidan Saul, wanda ka hau gadon sarautarsa. Yanzu Ubangiji ya ba da sarautar ga Absalom, ɗanka. Duba, masifa ta auko maka, gama kai mai kisankai ne.”

9 Sai Abishai, ɗan Zeruya, ya ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, don me za ka bar wannan kare yana ta zaginka? Bari in tafi in fille masa kai.”

10 Amma sarki ya ce masa, “Ba ruwanku, ku ‘ya’yan Zeruya. Idan yana zagi saboda Ubangiji ya sa shi, to, wa ya isa ya ce, ‘Don me kake yin haka?’ ”

11 Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.

12 Watakila Ubangiji zai dubi azabata, ya sāka mini da alheri saboda wannan zagin da aka yi mini yau.”

13 Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu. Shimai kuwa yana biye da su ta gefen dutse, yana tafe, yana ta zagi, yana jifarsa da duwatsu, yana masa ature.

14 Sarki da dukan jama’ar da suke tare da shi suka isa Urdun a rafke. Sai suka shaƙata.

Absalom a Urushalima

15 Absalom kuwa ya zo Urushalima tare da dukan mutanen Isra’ila da suke tare da shi. Ahitofel kuma yana tare da shi.

16 Sa’ad da Hushai Ba’arkite, aminin Dawuda ya zo wurin Absalom, ya ce masa, “Ran sarki ya daɗe!”

17 Sai Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake yi wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”

18 Hushai ya amsa, ya ce, “Ba haka ba, ni dai zan zama na wanda Ubangiji, da wannan jama’a, dukan mutanen Isra’ila suka zaɓa. Zan zauna tare da mutumin da aka zaɓa.

19 Banda haka ma, wane ne ya kamata in bauta wa, in ba ɗan ubangidana ba? Kamar yadda na bauta wa tsohonka, haka kuma zan bauta maka.”

20 Sa’an nan Absalom ya juya wajen Ahitofel, ya ce, “To, ka kawo shawararka a kan abin da ya kamata mu yi?”

21 Ahitofel kuwa ya ce wa Absalom, “Ka shiga ka kwana, da ƙwarakwaran tsohonka waɗanda ya bar su su lura da gidan. Dukan Isra’ilawa za su sani ba shiri kuma tsakaninka da tsohonka. Dukan masu goyon bayanka kuma za su ƙara ƙarfafa.”

22 Sai suka kafa wa Absalom alfarwa a bisa kan soro, ya shiga ya kwana da ƙwaraƙwaran tsohonsa, a idon mutanen Isra’ila duka.

23 Shawarar da Ahitofel yake bayarwa a lokacin nan ta zama kamar faɗar Allah ce. Absalom duk da Dawuda, shawarar Ahitofel suke bi.

Categories
2 SAM

2 SAM 17

Hushai Ya Wofintar da Shawarar Ahitofel

1 Ahitofel ya kuma ce wa Absalom, “Bari in zaɓi mutum dubu goma sha biyu (12,000), mu tafi mu bi Dawuda da daren nan.

2 Zan fāɗa masa sa’ad da yake cikin gajiya da karayar zuciya, in firgitar da shi. Dukan mutanen da suke tare da shi za su gudu. Shi kaɗai zan kashe.

3 Zan kawo maka dukan jama’a kamar yadda akan kawo amarya a gidan angonta. Ran mutum guda kaɗai kake nema, sauran mutane duka kuwa su yi zamansu lafiya.”

4 Wannan shawara ta gamshi Absalom da dattawan Isra’ila.

5 Sa’an nan Absalom ya ce, “A kirawo Hushai Ba’arkite don mu ji abin da shi kuma zai faɗa.”

6 Da Hushai ya zo, sai Absalom ya ce masa, “Ga shawarar da Ahitofel ya bayar, mu bi ta? Ko kuwa? Kai, me ka ce?”

7 Sai Hushai ya ce wa Absalom, “A wannan lokaci dai shawarar da Ahitofel ya bayar ba ta da kyau.”

8 Hushai ya ci gaba da cewa, “Ka san tsohonka da jama’arsa jarumawa ne, yanzu a husace suke kamar damisar da aka kwashe wa ‘ya’ya a jeji. Tsohonka kuma ya ƙware da sha’anin yaƙi, ba tare da mutanensa zai kwana ba.

9 Yanzu haka yana cikin rami ko dai a wani wuri a ɓoye. Idan an kashe waɗansu daga cikin mutanenka a karo na farko, duk wanda ya ji zai ce, ‘An kashe mutane da yawa daga cikin mutanen Absalom.’

10 Wannan zai sa jarumi wanda yake da zuciya kamar ta zaki ya karaya don tsoro, gama dukan mutanen Isra’ila sun sani tsohonka jarumi ne, su kuma waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.

11 Shawarata ita ce a tattara maka dukan Isra’ilawa tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, yawansu kamar yashi a bakin teku. Kai kuma da kanka ka tafi wurin yaƙin.

12 Da haka za mu tafi mu neme shi duk inda yake, mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo bisa ƙasa. Da shi da mutanensa, ba wanda za a bari da rai.

13 Idan ya gudu zuwa cikin gari, sai dukan jama’armu su zarge garin da igiya, su jā har duk ya watse, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”

14 Sai Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba’arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.

An Yi wa Dawuda Sanarwa ya Tsere

15 Sa’an nan Hushai ya ce wa Zadok da Abiyata, firistoci, “Ga irin shawarar da Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Isra’ila, ga kuma irin wadda ni na bayar.

16 Yanzu sai ka aika da sauri a faɗa wa Dawuda, kada ya kwana a bakin jeji a daren yau, amma ya haye don kada a hallaka shi tare da mutanensa.”

17 Jonatan da Ahimawaz suna jira a En-rogel. Wata baranya takan tafi ta faɗa musu saƙo, su kuma sai su tafi su faɗa wa sarki Dawuda, don kada a gan su suna shiga birnin.

18 Amma wani saurayi ya gan su, sai ya faɗa wa Absalom. Sai su biyu ɗin suka gudu nan da nan. Suka shiga gidan wani mutum a Bahurim, akwai rijiya a filin gidan. Sai suka shiga rijiyar.

19 Matar gidan kuwa ta yi shimfiɗa a bakin rijiyar, ta baza tsaba a kai, ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.

20 Sa’ad da fādawan Absalom suka zo gidan, suka tambayi matar, “Ina Ahimawaz da Jonatan suke?”

Sai ta ce musu, “Ai, tuni sun haye kogi.”

Sa’ad da suka neme su ba su same su ba, sai suka koma Urushalima.

21 Bayan da fādawan sun tafi, sai mutanen suka fito daga rijiyar. Suka tafi suka ce wa sarki Dawuda, “Ka tashi ka haye kogin nan da nan, gama ka ji irin muguwar shawarar da Ahitofel ya bayar a kanka.”

22 Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka haye Urdun. Kafin wayewar gari ko wannensu ya haye Urdun.

23 Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.

Dawuda a Mahanayim

24 Dawuda kuwa ya zo Mahanayim. Absalom kuma da dukan mutanen Isra’ila suka haye Urdun.

25 Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba’isma’ile, wanda ya auri Abigail ‘yar Nahash, ‘yar’uwar Zeruya mahaifiyar Yowab.

26 Absalom da mutanen Isra’ila suka kafa sansaninsu a ƙasar Gileyad.

27 Sa’ad da Dawuda ya kai Mahanayim, sai Shobi ɗan Nahash daga Rabba ta Ammonawa, da Makir ɗan Ammiyel daga Lodebar, da Barzillai Bagileyade daga Rogelim,

28 suka kawo wa Dawuda da jama’arsa waɗannan kaya da abinci, wato gadaje, da tasoshi, da tukwane, da alkama, da sha’ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa,

29 da zuma, da kindirmo, da tumaki, da cukun madarar shanu. Gama sun sani Dawuda da mutanensa suna jin yunwa, da gajiya, da kishi, a cikin jeji.

Categories
2 SAM

2 SAM 18

An Ci Absalom

1 Dawuda kuwa ya shirya sojojin da suke tare da shi, sa’an nan ya naɗa musu shugabanni na dubu dubu da na ɗari ɗari.

2 Ya aiki runduna zuwa yaƙi. Ya sa Yowab ya shugabanci sulusi ɗaya na rundunar, sulusi na biyu kuma ya sa a hannun Abishai, ɗan Zeruya, ɗan’uwan Yowab. Sulusi na uku kuwa ya sa a hannun Ittayi Bagitte. Sa’an nan sarki ya ce wa sojojin, “Ni ma da kaina zan tafi tare da ku.”

3 Amma sojojin suka ce, “Ba za ka tafi tare da mu ba, gama idan muka gudu, ba za su kula da mu ba. Ko rabinmu sun mutu, ba za su kula ba, gama kai kana bakin mutum dubu goma (10,000) na mutanenmu. Zai fi kyau kuma ka zauna cikin gari ka riƙa aika mana da taimako.”

4 Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa’ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu.

5 Ya kuma umarci Yowab, da Abishai, da Ittayi ya ce, “Ku lurar mini da saurayin nan, Absalom.” Dukan sojojin suka ji umarnin da sarki ya yi wa shugabanninsu a kan Absalom.

6 Sojojin suka tafi zuwa karkara don su yi yaƙi da mutanen Isra’ila. Suka yi yaƙin a kurmin Ifraimu.

7 Mutanen Isra’ila suka sha kashi a hannun jarumawan Dawuda. A wannan rana aka kashe mutane da yawa, har mutum dubu ashirin (20,000).

8 Yaƙin ya bazu ko’ina a ƙasar. A ranar abin da kurmin ya ci ya fi abin da aka kashe da takobi.

9 Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa’ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo.

10 Da wani mutum ya gani, sai ya tafi ya faɗa wa Yowab, ya ce, “Na ga Absalom yana reto a itacen oak.”

11 Yowab ya ce wa mutumin da ya faɗa masa, “Kai! Ka gan shi! Me ya sa ba ka buge shi har ƙasa ba? Ai, da na ba ka azurfa goma da abin ɗamara.”

12 Sai mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a ba ni azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba, gama a kunnuwanmu sarki ya umarce ka, kai da Abishai, da Ittayi cewa, ‘Ku lura mini da saurayin nan, Absalom.’

13 In da na ci amana har na kashe shi, ba yadda abin zai ɓoyu ga sarki, sa’an nan kai da kanka ka zame, ka bar ni.”

14 Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci haka da kai ba.” Sai ya ɗibi mashi uku ya soki Absalom a ƙahon zuciya, tun yana da sauran rai, a maƙale cikin itacen oak.

15 Sa’an nan samari goma masu ɗaukar wa Yowab makamai, suka kewaye Absalom, suka yi ta dūkansa har ya mutu.

16 Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, sojoji suka komo daga runtumar Isra’ilawa. Yowab ya tsai da su.

17 Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra’ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.

18 Tun Absalom yana da rai ya gina wa kansa al’amudi a kwarin sarki, gama ya ce, “Ba ni da ɗa wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Ya kira al’amudin da sunansa. Ana kuwa kiransa al’amudin Absalom har wa yau.

An faɗa wa Dawuda Mutuwar Absalom

19 Ahimawaz ɗan Zadok ya ce wa Yowab, “Ka yarda mini in sheƙa a guje in kai wa sarki labari yadda Ubangiji ya cece shi daga hannun magabtansa.”

20 Yowab ya ce masa, “Ba za ka kai labari yau ba, sai wata rana ka kai, amma yau ba za ka kai labari ba, domin ɗan sarki ya mutu.”

21 Sa’an nan Yowab ya ce wa wani mutumin Habasha, “Tafi ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Sai Bahabashen ya rusuna wa Yowab, sa’an nan ya sheƙa a guje.

22 Ahimawaz ɗan Zadok kuma ya ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru dai, ka bar ni in bi bayan Bahabashen a guje.”

Yowab ya ce masa, “Don me za ka tafi, ɗana, tun da yake ba za ka sami lada saboda labarin da za ka kai ba?”

23 Ahimawaz ya ce, “Duk dai abin da zai faru, zan tafi.”

Sai Yowab ya yardar masa ya tafi. Sa’an nan Ahimawaz ya sheƙa, ya bi ta hanyar fili, ya wuce Bahabashen.

24 Dawuda kuwa yana zaune a tsakanin ƙofofi biyu na garin. Mai tsaro ya hau kan soron da yake kan bangon garu. Da ya ɗaga kai ya duba, sai ya ga mutum yana gudu shi kaɗai.

25 Ya ta da murya, ya faɗa wa sarki. Sai sarki ya ce, “Idan shi kaɗai ne, yana kawo labari ne.” Mutumin ya yi ta ƙara zuwa kusa.

26 Mai tsaron kuma ya ga wani mutum yana zuwa shi ma a guje, sai ya ta da murya wajen mai ƙofar garin, ya ce, “Ga wani mutum kuma yana zuwa a guje!”

Sai sarki ya ce, “Shi ma labari yake kawowa.”

27 Mai tsaron ya ce, “Na ga gudun na farin kamar gudun Ahimawaz ɗan Zadok.”

Sai sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana kawo kyakkyawan labari ne.”

28 Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa’an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”

29 Sai sarki ya ce, “Na ce dai, saurayin nan, Absalom, yana nan lafiya?”

Ahimawaz ya amsa, ya ce, “A sa’ad da Yowab ya aiko ni na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba.”

30 Sarki kuwa ya ce, “Koma waje ɗaya, ka tsaya.” Sai ya koma waje ɗaya ya tsaya cik.

31 Sai ga Bahabashe ya iso, ya ce, “Abishirinka, ya ubangijina, sarki, gama a wannan rana ta yau Ubangiji ya cece ka daga hannun waɗanda suka tayar maka.”

32 Sarki ya tambaye shi, “Na ce dai, saurayin nan Absalom, yana lafiya?”

Bahabashen ya amsa, “Allah ya sa abokan gāban ubangijina, sarki, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”

33 Sai zuciyar sarki ta tsinke, ya hau cikin ɗakin da yake kan garun ƙofar garin yana ta kuka, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ɗana! Wayyo, ɗana Absalom! Da ma ni ne na mutu, ba kai ba. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”

Categories
2 SAM

2 SAM 19

Yowab Ya Tsauta wa Dawuda

1 Aka faɗa wa Yowab, cewa, sarki yana kuka, yana makoki domin Absalom.

2 Saboda haka sai nasarar da aka ya a ranar ta zama makoki ga jama’a duka, gama jama’a suka ji an ce sarki yana baƙin ciki domin ɗansa.

3 Sojojin suka shiga birni sururu kamar waɗanda sukan shiga birni a ɓoye da kunya saboda sun gudu daga wurin yaƙi.

4 Sarki ya rufe fuskarsa, ya yi kuka da ƙarfi, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ya Absalom, ɗana, ɗana!”

5 Yowab kuwa ya tafi wurin sarki a gidansa ya ce, “Yau ka kunyatar da mutanenka duka waɗanda suka ceci ranka, da rayukan ‘ya’yanka mata da maza, da rayukan matanka, da rayukan ƙwaraƙwaranka.

6 Gama kana ƙaunar maƙiyanka, amma kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Gama yau ka bayyana a fili, shugabannin sojojinka da fādawanka ba a bakin kome suke a gare ka ba. Gama yau na gane da a ce Absalom yana da rai, mu kuwa muka mutu duka, da daɗi za ka ji.

7 Don haka sai ka tashi yanzu, ka fita ka yi wa mutanenka magana mai daɗi. Gama na rantse da Ubangiji idan ba ka fita ba, ba wanda zai zauna tare da kai da daren nan. Wannan kuwa zai fi muni fiye da kowane irin mugun abin da ya taɓa samunka tun daga ƙuruciyarka har zuwa yanzu.”

8 Sa’an nan sarki ya tashi, ya zauna a dandalin ƙofar garu. Aka faɗa wa mutanensa duka, cewa, ga sarki yana zaune a dandalin ƙofar garu. Mutanensa duka kuwa suka zo suka kewaya sarki.

Dawuda Ya Tashi za shi Urushalima

Bayan wannan sai dukan Isra’ilawa suka gudu, kowa ya tafi gidansa.

9 Dukan mutanen ƙasar Isra’ila suna ta jayayya, suna cewa, “Sarki Dawuda ne ya cece mu daga hannun abokan gabanmu, ya cece mu daga hannun Filistiyawa, to, ga shi, ya gudu daga ƙasar don ya tsere wa Absalom.

10 Ga shi kuma, Absalom ɗin da muka naɗa ya zama sarkinmu, an kashe shi a yaƙi. Yanzu fa, me ya sa muka yi shiru ba mu komo da sarki ba?”

11 Da labarin abin da Isra’ilawa suke cewa, ya zo gun sarki Dawuda, sai ya aika zuwa wurin firistoci, wato Zadok da Abiyata, a faɗa musu su tambayi dattawan Yahuza abin da ya sa suka zama na ƙarshe a kan komar da sarki a gidansa.

12 Ya ce, “Ai, ku ‘yan’uwana ne, da ƙasusuwana, da namana. To, me ya sa za ku zama na ƙarshe a kan komar da sarki?

13 Ku ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”

14 Da haka Dawuda ya rinjayi zukatan mutanen Yahuza, suka zama ɗaya, kamar mutum guda. Sai suka aika wurin sarki, cewa, ya komo tare da dukan fādawansa.

15 Sa’ad da sarki ya iso Urdun. Mutanen Yahuza suka tafi Gilgal suka taryi sarki, domin su hawo da shi Urdun.

16 Shimai ɗan Gera kuma, mutumin Biliyaminu daga Bahurim, ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuza don ya taryi sarki Dawuda.

17 Ya zo tare da mutum dubu (1,000) daga kabilar Biliyaminu. Ziba kuma, baran gidan Saul, ya zo a gaggauce a gaban sarki a Urdun tare da ‘ya’yansa maza, su goma sha biyar, da barorinsa guda ashirin.

18 Suka haye zuwa wancan hayi don su hawo da iyalin sarki, su kuma yi masa abin da zai ji daɗi.

Sa’ad da sarki yake shirin hayewa, sai Shimai ɗan Gera ya zo ya fāɗi a gābansa.

19 Ya ce wa sarki, “Ina roƙon Ubangijina, sarki, in ka yarda kada ka riƙe baranka da laifi, kada ka tuna da laifin da baranka ya yi a ranar da Ubangijina sarki yake gudu daga Urushalima. Kada sarki ya riƙe wannan a zuci.

20 Gama na sani, ranka ya daɗe, na yi laifi, shi ya sa na zama na farko daga gidan Yusufu yau da na fito domin in taryi ubangijina sarki.”

21 Abishai ɗan Zeruya kuwa ya ce, “Ya kamata a kashe Shimai gama ya zagi wanda Ubangiji ya zaɓa ya zama sarki.”

22 Amma Dawuda ya ce wa Abishai da ɗan’uwansa Yowab, “Ina ruwana da ku, ku ‘ya’yan Zeruya? Kuna so ku jawo mini wahala? Ni ne Sarkin Isra’ila yanzu, don haka ba Ba’isra’ilen da za a kashe a yau.”

23 Sa’an nan ya ce wa Shimai, “Ina tabbatar maka, cewa, ba za a kashe ka ba.”

24 Sa’an nan Mefiboshet jikan Saul ya gangara ya taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har zuwa ranar da ya komo da nasara Mefiboshet bai wanke ƙafafunsa ba, bai kuma yi gyaran fuska ba, bai ma wanke tufafinsa ba.

25 Sa’ad da ya iso daga Urushalima don ya taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba, Mefiboshet?”

26 Mefiboshet ya amsa ya ce, “Ya ubangijina, sarki, barana ya ruɗe ni, gama na ce masa ya yi wa jaki shimfiɗa don in hau in tafi wurin sarki, gama ka sani ni gurgu ne, ranka ya daɗe.

27 Barana ya ɓata sunana a gaban ubangijina, sarki. Amma ranka ya daɗe, ya sarki, kai kamar mala’ikan Allah kake, sai ka yi abin da ya yi maka daidai.

28 Gama dukan mutanen gidan kakana sun cancanci mutuwa a gabanka, ranka ya daɗe, amma ga shi, ka sa na zama ɗaya daga cikin waɗanda suke ci a teburinka. Ba ni da dalilin da zai sa in yi wa sarki wani kuka kuma.”

29 Sai sarki ya ce masa, “Me ya kawo wannan magana a kan harkokinka? Ai, na riga na zartar, cewa, kai da Ziba za ku raba mallakar Saul.”

30 Mefiboshet ya ce wa sarki, “A ma bar masa duka ya mallaka, ni dai tun da ubangijina, sarki, ya komo gida lafiya, to, alhamdu lillahi.”

31 Barzillai Bagileyade kuma ya gangara daga Rogelim zuwa wurin sarki domin ya yi wa sarki rakiya zuwa hayin Urdun.

32 Barzillai kuwa tsoho ne, yana da shekara tamanin. Ya taimaki sarki da abinci sa’ad da sarki yake a Mahanayim, gama shi attajiri ne.

33 Sarki ya ce wa Barzillai, “Ka zo mu tafi tare zuwa Urushalima, ni kuwa zan riƙa biya maka bukata.”

34 Amma Barzillai ya amsa, ya ce, “Shekaruna nawa suka ragu har da zan tafi Urushalima tare da sarki?

35 A yau ina da shekara tamanin cif. Ba zan iya in rarrabe abu mai daɗi da marar daɗi ba. Ba kuma zan iya ɗanɗana daɗin abin da nake ci ko abin da nake sha ba. Ba zan iya jin daɗin muryar mawaƙa ba. Zan zamar maka kaya kurum, ranka ya daɗe.

36 Ban cancanci wannan irin babban lada ba. Zan dai yi maka ‘yar rakiya zuwa hayin Urdun.

37 Ina roƙonka ka bar ni in koma domin in rasu a garinmu, kusa da kabarin mahaifina. Amma ga Kimham barana, bari ya tafi tare da kai, ranka ya daɗe. Ka yi masa yadda kake so.”

38 Sarki ya ce, “To, Kimham zai tafi tare da ni, zan kuwa yi masa abin da zai yi maka daɗi. Duk abin da kake so a gare ni, zan yi maka.”

39 Sa’an nan dukan jama’a suka haye Urdun, sarki kuma ya haye. Ya yi bankwana da Barzillai, ya sumbace shi, ya kuma sa masa albarka. Sai Barzillai ya koma gidansa.

40 Sarki kuwa ya yi tafiya zuwa Gilgal. Kimham kuma ya tafi tare da shi. Mutanen Yahuza duka, da rabin mutanen Isra’ila suna tafe tare da sarki.

41 Sai dukan mutanen Isra’ila suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Me ya sa mutanen Yahuza ‘yan’uwanmu, suka sace ka, suka kawo sarki da iyalinsa a wannan hayin Urdun, tare da dukan mutanensa?”

42 Dukan mutanen Yahuza suka amsa wa mutanen Isra’ila suka ce, “Domin sarki ɗan’uwanmu ne na kusa. Me ya sa kuke fushi a kan wannan al’amari? Me muka ci a jikin sarki, ko kun ji ya ba mu wani abu ne?”

43 Isra’ilawa kuma suka amsa wa mutanen Yahuza, suka ce, “Muna da rabo goma a wurin sarki Dawuda fiye da ku, don me kuka raina mu? Ba mu ne muka fara maganar komowar sarki ba?”

Amma maganar mutanen Yahuza ta fi ta mutanen Isra’ila zafi.

Categories
2 SAM

2 SAM 20

Tawayen Sheba

1 Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra’ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”

2 Sai dukan Isra’ilawa suka janye jiki daga wurin Dawuda, suka bi Sheba, ɗan Bikri, amma mutanen Yahuza suka manne wa sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.

3 Da Dawuda ya koma gidansa a Urushalima, kwarakwaran nan nasa guda goma waɗanda ya bar su tsaron gida ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya yi ta lura da su, amma bai shiga wurinsu ba. Haka suka zauna a keɓe, suna zaune kamar gwauraye.

4 Sa’an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mini mutanen Yahuza kafin kwana uku, kai kuma ka zo tare da su.”

5 Sai Amasa ya tafi ya kira mutanen Yahuza, amma ya makara, bai zo a lokacin da aka ƙayyade masa ba.

6 Dawuda kuma ya ce wa Abishai, “Sheba ɗan Bikri fa, zai ba mu wuya fiye da Absalom, sai ka ɗauki mutanena, ka bi sawunsa, don kada ya ci garuruwa masu garu har ya tsere mana.”

7 Sa’an nan mutanen Yowab, wato Keretiyawa da Feletiyawa, da dukan jarumawa, suka bi bayan Abishai. Suka fita daga Urushalima don su bi sawun Sheba, ɗan Bikri.

8 Sa’ad da suke a babban dutsen Gibeyon, Amasa ya zo ya tarye su. A lokacin nan Yowab yana saye da rigar yaƙi, ya sha ɗamara, yana kuma rataye da takobi a ɗamararsa. Da ya gabato, sai takobin ya faɗi.

9 Yowab ya ce wa Amasa, “Abokina kana lafiya?” Yowab kuma ya kama gemun Amasa da hannun dama don ya sumbace shi.

10 Amma Amasa bai lura Yowab yana da takobi a hannunsa ba. Yowab kuwa ya kirɓa masa takobin a ciki sau ɗaya, sai hanjin Amasa ya zuba ƙasa, ya mutu.

Sa’an nan Yowab da Abishai ɗan’uwansa suka bi sawun Sheba, ɗan Bikri.

11 Sai ɗaya daga cikin samarin Yowab ya tsaya kusa da gawar Amasa ya ce, “Duk wanda yake son Yowab da duk wanda yake goyon bayan Dawuda, ya bi Yowab.”

12 Gawar Amasa kuwa ta birkiɗe da jini tana a tsakiyar hanya. Da mutumin ya ga yadda dukan mutane suka tsaya, sai ya kawar da ita daga tsakiyar hanya zuwa cikin saura, ya rufe ta da tufa, gama dukan wanda ya ga gawar, sai ya ja, ya tsaya.

13 Sa’ad da aka kawar da ita daga kan hanya, dukan mutane kuwa suka bi Yowab domin su bi sawun Sheba ɗan Bikri.

14 Sai Sheba ya bibiya kabilan Isra’ila, har ya kai Abel-bet-ma’aka. Dukan dangin Beri kuwa suka taru suka bi shi zuwa cikin garin.

15 Dukan mutanen da suke tare da Yowab kuma suka zo suka kewaye shi cikin Abel-bet-ma’aka. Suka tula ƙasa a jikin garun garin, daidai da tsayinta, waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe garun.

16 Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.”

17 Da ya zo kusa da ita, sai macen ta ce, “Kai ne Yowab?”

Ya ce, “I, ni ne.”

Ta ce masa, “Ka kasa kunne gare ni.”

Ya ce, “Ina sauraronki.”

18 Ta ce, “A dā sukan ce, ‘A nemi shawara a Abel,’ gama a can ake raba gardama.

19 Garinmu lafiyayye ne, amintacce ne kuma a cikin Isra’ila. Me ya sa kake so ka hallaka garin? Kana so ka rushe abin da yake na Allah?”

20 Yowab ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Ba zan lalatar ko in hallakar da birninku ba.

21 Ba haka ba ne, ni dai ina neman mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu, wanda ake ce da shi Sheba, ɗan Bikri. Shi ne ya tayar wa sarki Dawuda. Shi kaɗai za ku ba ni, ni kuwa zan janye daga garin.”

Macen kuwa ta ce wa Yowab, “To, za a jefar maka kansa ta kan garu.”

22 Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.

Fādawan Dawuda

23 Yowab shi ne shugaban dukan sojojin Isra’ila, Benaiya, ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato masu tsaro.

24 Adoniram shi ne shugaban aikin gandu, Yehoshafat, ɗan Ahilud, shi ne marubuci.

25 Shewa shi ne magatakarda. Zadok da Abiyata su ne firistoci.

26 Aira mutumin Yayir shi ne mashawarcin Dawuda.