Categories
2 SAM

2 SAM 21

Ramuwa don Gibeyonawa

1 A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.”

2 (Gibeyonawa dai ba mutanen Isra’ila ba ne, su Amoriyawan da suka ragu ne, waɗanda Isra’ilawa suka rantse musu, cewa, ba za su kashe su ba. Amma Saul, saboda kishin da yake yi domin mutanen Isra’ila da Yahuza, ya nema ya kashe su duk.)

3 Dawuda kuwa ya kira Gibeyonawa ya ce musu, “Me zan yi muku, da me zan yi kafara, domin ku sa wa mutanen Ubangiji albarka?”

4 Gibeyonawa suka amsa suka ce, “Ba zancen azurfa ko zinariya yake tsakaninmu da Saul ko da gidansa ba. Ba kuma wani mutum muke so mu kashe daga cikin Isra’ila ba.”

Dawuda kuma ya tambaye su ya ce, “To, me kuke so in yi muku?”

5 Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya karkashe mu, ya yi niyyar hallakar da mu, don kada mu kasance tare da Isra’ilawa ko’ina a cikin karkararsu.

6 Sai ka ba mu ‘ya’yansa maza bakwai domin mu rataye su a gaban Ubangiji a Gibeya a kan dutsen Ubangiji.”

Sarki kuwa ya ce, “To, zan bayar.”

7 Amma sarki ya ware Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, saboda rantsuwar da yake tsakaninsa da Jonatan, ɗan Saul.

8 Sai sarki ya sa aka kamo masa Armoni da Mefiboshet, ‘ya’yan Saul waɗanda Rizfa, ‘yar Aiya, ta haifa masa, da ‘ya’ya maza biyar na Adriyel, ɗan Barzillai, mutumin Abelmehola, waɗanda matarsa Merab ‘yar Saul ta haifa masa.

9 Sarki kuwa ya bai wa Gibeyonawa su. Sai suka rataye su a kan dutse a gaban Ubangiji. Su bakwai ɗin nan suka hallaka gaba ɗaya. An kashe su a farkon kakar sha’ir.

10 Rizfa kuwa, ‘yar Aiya, ta ɗauki algarara ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutsen. Ta zauna a wurin tun daga farkon kaka har zubar ruwan damuna da ya bugi gawawwakin. Ba ta bar tsuntsaye su sauka a kansu da rana ba, ko namomin jeji da dare.

11 Sa’ad da aka sanar wa Dawuda abin da Rizfa, ‘yar Aiya, ƙwarƙwarar Saul ta yi,

12 Dawuda ya tafi ya kwaso ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan daga wurin mutanen Yabesh a Gileyad. (Gama suka sace su daga dandalin Bet-sheyan, a inda Filistiyawa suka rataye su, a ranar da suka kashe Saul a Gilbowa.)

13 Daga can ne ya kwaso ƙasusuwan Saul da na Jonatan, suka kuma tattara ƙasusuwan waɗanda aka rataye.

14 Aka binne ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan a kabarin Kish, tsohon Saul, a Zela a ƙasar Biliyaminu. Aka aikata dukan abin da sarki ya umarta. Bayan haka Allah ya ji addu’arsu a kan ƙasar.

Abishai Ya Ceci Dawuda daga Ƙaton Mutum

15 Ana nan sai Filistiyawa suka kai wa Isra’ilawa yaƙi. Dawuda kuwa ya gangara tare da jama’arsa, suka yi yaƙi da Filistiyawa. Dawuda kuwa ya gaji.

16 Sai Ishbi-benob, ɗaya daga cikin Refayawa, gwarzayen nan, wanda nauyin mashinsa ya yi shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma rataye da sabon takobi, ya zaci zai iya kashe Dawuda.

17 Abishai ɗan Zeruya kuwa, ya kawo wa Dawuda gudunmawa. Ya faɗa wa Bafilisten, ya kashe shi. Jama’ar Dawuda kuwa suka sa ya yi musu alkawari ba zai ƙara binsu zuwa wurin yaƙi ba. Suka ce, “Kai ne begen Isra’ila, ba mu so mu rasa ka.”

Jarumawan Dawuda sun Kashe Ƙattin Mutane

18 Bayan wannan kuma suka sāke yin yaƙi da Filistiyawa a Gab. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin gwarzayen.

19 Suka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gab, sai Elhanan, ɗan Yayir, mutumin Baitalami, ya kashe ɗan’uwan Goliyat na Gat, wanda girman gorar māshinsa ta yi kama da dirkar masaƙa.

20 An kuma yi wani yaƙi a Gat, inda aka sami wani ƙaton mutum wanda shi cindo ne, hannuwa da ƙafafu, wato yana da yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi kuma daga cikin zuriyar gwarzayen mutanen ne.

21 Sa’ad da ya nuna wa Isra’ilawa raini, Jonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda, ya kashe shi.

22 Waɗannan gwarzaye huɗu sun fito daga zuriyar gwarzayen Gat ne. Dawuda da mutanensa suka kashe su.

Categories
2 SAM

2 SAM 22

Waƙar Nasarar Dawuda

1 Wannan waƙa Dawuda ya raira wa Ubangiji sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun Saul da dukan sauran abokan gābansa, ya ce,

2 “Ubangiji ne mai cetona,

Shi ne ƙaƙƙarfar kagarata.

3 Allahna, shi ne kāriyata,

Ina zaune lafiya tare da shi.

Yana kāre ni kamar garkuwa,

Yana tsare ni, ya kiyaye ni.

Shi ne mai cetona.

4 Na yi kira ga Ubangiji,

Ya cece ni daga abokan gābana.

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

5 Gama raƙuman ruwa na mutuwa sun kewaye ni,

Raƙuman ruwa na hallaka suna gangarawa ta kaina.

6 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi,

Kabari kuma ya ɗana mini tarko.

7 A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji,

Na yi kira ga Allah domin taimako.

Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata,

Ya kasa kunne ga kukana na neman taimako.

8 “Sa’an nan duniya ta yi tangaɗi, ta girgiza,

Harsashin sararin sama ya yi makyarkyata, ya raurawa, saboda fushin Allah.

9 Hayaƙi ya fito daga kafafen hancinsa,

Harshen wuta mai cinyewa da garwashi mai ƙuna daga bakinsa.

10 Ya jā sararin sama baya ya sauko,

Da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.

11 Ya hau kerub, ya tashi sama,

Ya yi tafiya ta fikafikan iska.

12 Ya rufe kansa da duhu,

Gizagizai masu kauri cike da ruwa suna kewaye da shi,

13 Garwashi mai ci daga tsawar walƙiya a gabansa.

14 “Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama

Aka kuma ji muryar Maɗaukaki.

15 Ya harharba kibau, ya warwatsa magabtansa,

Da walƙiyoyin tsawa ya sa su gudu.

16 An bayyana ƙarƙashin teku a fili,

An tone tussan duniya,

Lokacin da Ubangiji ya yi wa abokan gāba tsautawa,

Ya yi musu ruri cikin fushi.

17 Daga Sama Ubangiji ya miƙo ya ɗauke ni,

Ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.

18 Ya kuɓutar da ni daga waɗanda suke ƙina,

Daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina!

19 Sa’ad da nake cikin wahala sun auka mini,

Amma Ubangiji ya kiyaye ni.

20 Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari,

Ya cece ni domin yana jin daɗina.

21 “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina,

Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.

22 Gama na kiyaye dokar Ubangiji,

Ban yi wa Allahna tayarwa ba.

23 Na kiyaye dukan dokokinsa,

Ban yi rashin biyayya ga umarnansa ba.

24 Ya sani ni marar laifi ne,

Na kiyaye kaina daga aikata mugunta.

25 Domin haka ya sāka mini bisa ga adalcina,

Gama ya sani ba ni da laifi.

26 “Kai, ya Ubangiji, amintacce ne ga waɗanda suke da aminci,

Nagari ne kuma ga waɗanda suke cikakku.

27 Mai Tsarki ne kai ga waɗanda suke tsarkaka,

Amma kana gāba da waɗanda suke mugaye.

28 Kakan ceci masu tawali’u,

Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.

29 “Ya Ubangiji, kai ne haskena,

Kana haskaka duhuna.

30 Ka ba ni ƙarfi don in auka wa abokan gābana,

Da iko domin in murƙushe tsaronsu.

31 “Allahn nan cikakke ne ƙwarai,

Maganarsa tabbatacciya ce!

Kamar garkuwa yake

Ga dukan masu neman kiyayewarsa.

32 Ubangiji shi kaɗai ne Allah,

Allah ne kaɗai madogararmu.

33 Allahn nan shi ne mafaka, mai ƙarfi ne a gare ni,

Ya sa hanyata ta zama lafiyayyiya.

34 Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa,

Ya kiyaye ni a kan duwatsu.

35 Ya horar da ni domin yaƙi,

Domin in iya tausa baka mafi ƙarfi.

36 “Ya Ubangiji, ka kiyaye ni, ka cece ni,

Taimakonka ya sa na zama babba.

37 Ka hana a kama ni,

Ban kuwa taɓa faɗuwa ba.

38 Na runtumi abokan gābana, na kuwa hallaka su,

Ban tsaya ba sai da na kore su.

39 Na fyaɗa su ƙasa, ba su iya tashi ba,

Suna kwance warwar a ƙafafuna.

40 Ka ba ni ƙarfi domin yin yaƙi,

Nasara kuma a kan abokan gābana.

41 Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana,

Na hallaka waɗanda suke ƙina.

42 Suka nemi taimako, amma ba wanda zai cece su,

Suka yi kira ga Ubangiji, amma bai amsa musu ba.

43 Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura,

Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.

44 “Ka cece ni daga jama’ata mai tawaye,

Ka sa in yi mulkin al’ummai,

Mutanen da ban san su ba sun zama bayina.

45 Baƙi sun zo suna rusuna mini,

Sa’ad da suka ji ni suka yi mini biyayya.

46 Zuciyarsu ta karai,

Suka fito daga kagararsu suna rawar jiki.

47 “Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai tsaronsa!

Allah ne ƙaƙƙarfan Mai Cetona! Ku yi shelar girmansa!

48 Ya ba ni nasara a kan abokan gabana,

Ya sa mutane a ƙarƙashin mulkina,

49 Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiya.

Kai, ya Ubangiji, ka ba ni nasara a kan maƙiyana,

Ka tsare ni daga mutane masu zafin hali.

50 Domin wannan zan yi yabonka cikin al’ummai,

Zan raira yabbai gare ka.

51 Allah ya ba sarkinsa manya manyan nasarori,

Ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shi wanda ya zaɓa,

Wato ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”

Categories
2 SAM

2 SAM 23

Maganar Dawuda ta Ƙarshe

1 Wannan ita ce maganar Dawuda ta ƙarshe. Dawuda ɗan Yesse, shi ne mutumin da Allah ya ɗaukaka, wanda Allah na Yakubu ya zaɓa ya zama sarki, wanda kuma ya shirya waƙoƙin Isra’ila. Dawuda ya ce,

2 “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina,

Saƙonsa yana kan leɓunana.

3 Allah na Isra’ila ya yi magana,

Matsaron Isra’ila ya ce mini,

‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci,

Wanda yake mulki da tsoron Allah,

4 Yana kama da hasken rana a kan girgijen alfijir,

Rana da take sa ciyawa ta yi ƙyalƙyali bayan an gama ruwan sama.’

5 “Haka Allah zai sa wa zuriyata albarka,

Gama ya yi mini madawwamin alkawari,

Duka kuwa a shirye yake, zai kuwa kiyaye.

Abin da nake bukata ke nan,

Wannan ne nasarata,

Na tabbata kuwa Allah zai kammala shi.

6 Amma marasa Allah suna kama da ƙayayuwan da aka zubar,

7 Amma wanda zai taɓa su, sai da wani ƙarfe ko da māshi,

Za a ƙone su ƙurmus.”

Jarumawan Dawuda

8 Ga sunayen jarumawan Dawuda, Yosheb-basshebet, daga Takemon, shi ne ɗaya daga cikin shugabanni uku. Ya girgiza māshinsa, ya kashe mutum ɗari takwas baki ɗaya.

9 Wanda yake biye da shi a cikin su uku ɗin shi ne Ele’azara, ɗan Dodo, ɗan Ahowa. Yana tare da Dawuda sa’ad da suka raina Filistiyawan da suka taru don yaƙi. Mutanen Isra’ila kuwa suka jā baya,

10 shi kuwa ya tsaya, ya yi ta yaƙi da Filistiyawa, har hannunsa ya ƙage, har bai iya ɓanɓaruwa daga takobinsa ba. Ubangiji ya ba da babbar nasara a wannan rana. Bayan an gama sai Isra’ilawa suka koma wurin Ele’azara don su kwashi ganima kawai.

11 Biye da Ele’azara kuma, sai Shamma, ɗan Agi, daga Harod. Filistiyawa suka taru a Lihai, inda akwai wata gonar wake. Isra’ilawa kuwa suka guji wa Filistiyawa.

12 Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar gonar, ya kāre ta. Ya kuma kashe Filistiyawa. Ubangiji ya ba da babbar nasara.

13 Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa.

14 Dawuda yana cikin kagara, ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuwa tana a Baitalami.

15 Dawuda ya ji marmari, ya ce, “Kai, da ma wani zai ba ni ruwan rijiyar ƙofar garin Baitalami in sha!”

16 Shahararrun jarumawan nan uku kuwa suka sheƙa a guje, suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka tafi, suka ɗebo ruwa daga rijiyar ƙofar garin Baitalami, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda bai sha ba, ya zuba shi hadaya a gaban Ubangiji.

17 Sa’an nan ya ce, “Ya Ubangiji, ka tsare ni daga shan jinin mutanen da suka sadaukar da ransu.” Saboda haka bai sha ruwan ba.

Abubuwan da jarumawan nan uku suka yi ke nan.

18 Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban jarumawan nan talatin. Sa’ad da ya girgiza mashinsa, sai da ya kashe mutum ɗari uku. Da haka ya samar wa kansa sūna tare da mutanen nan uku.

19 Shi ya fi shahara daga cikin su talatin ɗin, don haka ya zama shugabansu, amma bai kai su uku ɗin can ba.

20 Benaiya ɗan Yehoyada, mutumin Kabzeyel, jarumi ne. Ya yi manyan ayyuka. Ya kashe ƙwararrun jarumawa biyu na Mowab. Wata rana kuma da aka yi dusar ƙanƙara, sai ya tafi ya kashe zaki a kogo.

21 Ya kuma kashe wani Bamasare mai cika fuska. Bamasaren yana da māshi a hannunsa, amma Benaiya ya tafi wurinsa da sanda, ya fizge mashin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da māshin.

22 Abubuwan da Benaiya, ɗan Yehoyada ya yi ke nan. Da haka ya samar wa kansa suna tare da jarumawan nan talatin.

23 Ya shahara cikin jarumawan nan talatin, amma bai kai su uku ɗin can ba. Dawuda kuwa ya maishe shi ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

24-39 Sauran jarumawan da suka zama talatin sun haɗu da waɗannan,

Asahel, ɗan’uwan Yowab,

Elhanan, ɗan Dodo, daga Baitalami,

Shamma da Elika, daga Harod,

Helez, daga Felet,

Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa,

Abiyezer, daga Anatot,

Sibbekai, daga Husha,

Zalmon, daga Aho,

Maharai, da Heled, ɗan Ba’ana, daga Netofa,

Ittayi, ɗan Ribai, daga Gibeya ta Biliyaminu,

Benaiya, daga Firaton,

Hurai, daga kwaruruka kusa da Ga’ash,

Abiyel, daga Araba,

Azmawet, daga Bahurim,

Eliyaba, daga Shalim,

Yashen, daga Gimzo,

Jonatan, ɗan Shamma, daga Harod,

Ahiyam, ɗan Sharar, daga Harod,

Elifelet, ɗan Ahasbai, daga Ma’aka,

Eliyam, ɗan Ahitofel, daga Gilo,

Hezro, daga Karmel,

Nayarai, daga Arabiya,

Igal, ɗan Natan, daga Zoba,

Bani, daga Gad,

Zelek, daga Ammon,

Naharai, (mai ɗaukar wa Yowab, ɗan Zeruya makamai) daga Biyerot,

Aira daga Gareb, daga Yattir,

Uriya, Bahitte.

Dukansu su talatin da bakwai ne shahararrun sojoji.

Categories
2 SAM

2 SAM 24

Dawuda Ya Ƙidaya dukan Jama’a

1 Ubangiji kuwa ya husata da Isra’ilawa. Ya kuwa zuga Dawuda a kansu, ya ce, “Tafi ka ƙidaya jama’ar Isra’ila da ta Yahuza.”

2 Sai sarki ya ce wa Yowab da shugabannin sojojin su tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, su ƙidaya mutanen don ya san yawansu.

3 Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mutanenka su ƙaru har sau ɗari fiye da yadda suke, har ubangijina sarki ya gani da idonsa, amma me ya sa sarki yake so ya yi wannan abu?”

4 Amma maganar sarki ta rinjayi ta Yowab da ta sauran shugabannin sojojin. Yowab kuwa da sauran shugabannin sojojin suka tashi daga gaban sarki suka tafi su ƙidaya mutanen Isra’ila.

5 Suka haye Urdun suka fara daga Arower, da garin da yake tsakiyar kwarin zuwa Gad, har zuwa Yazar.

6 Sa’an nan suka zo Gileyad da Kadesh cikin ƙasar Hittiyawa, daga nan suka tafi Dan-ja’an. Daga Dan-ja’an kuma suka ratsa zuwa Sidon.

7 Suka tafi kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa, da na Ƙan’aniyawa. Daga can suka tafi ƙasar kudu ta Yahuza a Biyer-sheba.

8 Da suka gama ratsa dukan ƙasar, sai suka komo Urushalima bayan wata tara da kwana ashirin.

9 Yowab kuwa ya ba sarki yawan jimillar mutanen da aka samu. A Isra’ila an sami mutanen da suka isa yin yaƙi, su dubu ɗari takwas (800,000). A Yahuza kuwa an sami mutum dubu ɗari biyar (500,000).

10 Bayan da Dawuda ya ƙidaya mutane, sai lamirinsa ya kā da shi, ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka gafarta mini, gama na yi wauta.”

11 Da Dawuda ya tashi da safe, sai Ubangiji ya yi magana da annabi Gad, wato annabin da yake tare da Dawuda, ya ce,

12 “Tafi ka faɗa wa Dawuda na ba shi abu uku don ya zaɓi ɗaya wanda za a yi masa daga cikinsu.”

13 Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kuwa kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gabanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu sai ka yi tunani, ka faɗi irin amsar da zan mayar wa Ubangiji da ya aiko ni.”

14 Dawuda kuwa ya ce, “Na shiga uku, gara in faɗa a ikon Ubangiji, gama shi mai rahama ne, da in faɗa a ikon mutum.”

15 Ubangiji kuwa ya aika da annoba a kan Isra’ila tun da safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade. Mutum dubu saba’in (70,000) suka mutu daga Dan zuwa Biyer-sheba.

16 Sa’ad da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima don ya hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake hallakar da mutanen, “Ya isa, ka janye hannunka.” Mala’ikan ya tsaya kusa da masussukar Arauna Bayebuse.

17 Da Dawuda ya ga mala’ika wanda yake hallakar da mutanen, sai ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi, na aikata mugunta, amma me waɗannan tumaki suka yi? Ina roƙonka, ka hukunta ni da gidan ubana.”

18 A ran nan Gad ya koma wurin Dawuda ya ce masa, “Ka haura ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna Bayebuse.”

19 Dawuda kuwa ya haura bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Gad.

20 Da Arauna ya waiga, ya ga sarki da fādawansa suna zuwa wurinsa, sai ya tafi ya tarye su. Ya tafi ya rusuna a gaban sarki har ƙasa,

21 ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, me ya kawo ka?”

Sai Dawuda ya ce, “Don in sayi masussukarka ne domin in gina wa Ubangiji bagade, domin a kawar wa mutanen da annobar.”

22 Arauna kuwa ya ce wa Dawuda, “Bari ubangijina, sarki, ya karɓa, ya yi abin da yake so. Ga shanun nan domin hadayar ƙonawa, ga kuma itacen sussuka da karkiya domin itacen hadayar.”

23 Dukan waɗannan Arauna ya ba sarki. Ya kuma ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya karɓa.”

24 Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, saye zan yi daga gare ka da tamani. Ba zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da abin da ban yi wahalarsa ba.” Dawuda ya sayi masussukar da shanu a bakin shekel hamsin na azurfa.

25 Sa’an nan ya gina wa Ubangiji bagade a wurin. Ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa masa addu’o’i saboda ƙasar. Aka kawar wa Isra’ila da annobar.