Categories
2 SAR

2 SAR 11

Sarauniya Ataliya ta Yahuza

1 Sa’ad da Ataliya, uwar Ahaziya, ta ga ɗanta ya rasu, sai ta tashi ta hallaka dukan ‘ya’yan sarauta.

2 Amma Yehosheba ‘yar sarki Yoram, ‘yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ‘ya’yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba.

3 Ya zauna tare da ita shekara shida a ɓoye, a cikin Haikalin Ubangiji sa’ad da Ataliya take mulkin ƙasar.

Yehoyada Ya Tayar

4 A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya aika ya kawo shugabannin Keretiyawa da na masu tsaro a Haikalin Ubangiji. Ya yi alkawari da su, ya sa suka yi rantsuwa a Haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.

5 Ya kuma umarce su cewa, “Abin da za ku yi ke nan, sai sulusinku da sukan zo aiki a ranar Asabar, su yi tsaron gidan sarki.

6 Sulusinku kuma zai kasance a ƙofar Sur. Ɗaya sulusin kuma zai kasance a bayan masu tsaro, haka za ku yi tsaron gidan, ku tsare shi.

7 Ƙungiyarku biyu kuma waɗanda sukan tashi aiki ran Asabar, za su yi tsaron Haikalin Ubangiji da kuma sarki.

8 Za ku kewaye sarki, kowane mutum ya riƙe makaminsa. Duk wanda ya yi ƙoƙari ya zo kusa, sai a kashe shi. Sai ku kasance tare da sarki duk lokacin da zai fita da duk lokacin da zai shiga.”

9 Shugabannin fa suka aikata bisa ga dukan abin da Yehoyada firist ya umarta. Kowa ya zo duk da mutanensa waɗanda za su huta aiki ran Asabar tare da waɗanda za su yi aiki ran Asabar, suka zo wurin Yehoyada.

10 Firist kuwa ya ba shugabannin māsu da garkuwoyin Dawuda waɗanda suke cikin Haikalin Ubangiji.

11 Matsara suka tsaya, kowa da makaminsa a hannu, daga wajen kudu na Haikalin zuwa wajen arewa. Suka kewaye bagade da Haikali.

12 Sa’an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kuma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa’an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”

13 Da Ataliya ta ji muryoyin matsara da na jama’a, sai ta zo wurin mutane a Haikalin Ubangiji.

14 Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al’ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!”

15 Yehoyada, firist kuwa, ya umarci shugabannin sojoji, ya ce, “Ku fitar da ita daga nan, duk kuma wanda yake son kāre ta, ku sa takobi ku kashe shi.” Ya kuma ce, “Kada a kashe ta a Haikalin Ubangiji.”

16 Suka kama ta, suka fitar da ita ta ƙofar dawakai zuwa gidan sarki, can suka kashe ta.

Gyare-gyaren Yehoyada

17 Yehoyada kuwa ya yi alkawari tsakanin Ubangiji, da sarki, da jama’a, yadda za su zama jama’ar Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da jama’a.

18 Sai dukan jama’ar ƙasa suka tafi haikalin Ba’al suka farfashe shi, da bagadensa da siffofinsa. Suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagaden.

Yehoyada kuwa ya sa matsara su yi tsaron Haikalin Ubangiji,

19 ya kuma sa shugabanni, da Keretiyawa, da matsara, da dukan jama’ar ƙasar, su fito da sarki daga Haikalin Ubangiji, suka rufa masa baya ta ƙofar matsara zuwa gidan sarki. Suka sa shi a gadon sarautar sarakuna.

20 Dukan jama’ar ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya huta bayan da an kashe Ataliya a gidan sarki.

Sarki Yowash na Yahuza

21 Jowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya ci sarauta.

Categories
2 SAR

2 SAR 12

1 A shekara ta bakwai ta sarautar Yehu, Yowash ya ci sarautar. Ya yi shekara arba’in yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya ta Biyer-sheba.

2 Yowash kuwa ya yi abin da yake daidai ga Ubangiji dukan kwanakinsa, domin Yehoyaka, firist, ya koya masa.

3 Duk da haka ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba, mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a kan tuddan.

4 Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali,

5 sai ku karɓa daga junanku, don a gyara duk inda ake bukatar gyara a Haikalin.”

6 Amma har a shekara ta ashirin da uku ta sarautar sarki Yowash, firistocin ba su yi wani gyara a Haikalin ba.

7 Saboda haka Yowash ya kirawo Yehoyada, firist, da sauran firistoci, ya ce musu, “Me ya sa ba ku gyara Haikalin? Daga yanzu kada ku karɓi kuɗi daga wurin abokanku, sai in za ku ba da shi domin gyaran Haikalin.”

8 Firistocin kuwa suka yarda, ba za su karɓi kuɗi daga wurin jama’a ba, ba su kuwa gyara Haikalin ba.

9 Sa’an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa’an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji.

10 Sa’ad da suka gani akwai kuɗi da yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki, da babban firist suka zo, suka ƙirga kuɗin da yake a Haikalin Ubangiji suka ƙunsa shi a babbar jaka.

11 Sa’an nan suka ba da kuɗin da aka ƙirga a hannun waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji, domin su biya masassaƙan katakai, da masu haɗawa da suke aikin Haikalin Ubangiji,

12 da masu gini, da masu sassaƙa duwatsu, a kuma sayi katako da sassaƙaƙƙun duwatsu don gyaran Haikalin Ubangiji, da kowane irin abu da ake bukata domin gyaran Haikalin.

13 Amma ba a mori kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji domin yin kwanonin azurfa, da abin katse fitila, da tasoshi, da ƙahoni, da kwanonin zinariya ko na azurfa ba.

14 Gama an ba da kuɗin ga ma’aikatan da suke gyaran Haikalin ubangiji.

15 Ba a nemi lissafin kuɗin a wurin mutanen da aka ba su kuɗin don su biya ma’aikatan ba, gama su amintattu ne.

16 Ba a kawo kuɗi na hadaya don laifi da hadaya don zunubi a cikin Haikalin Ubangiji ba, ya zama na firistoci.

17 Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Gat har ya cinye ta, ya kuma shirya zai yi yaƙi da Urushalima.

18 Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa’an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.

19 Sauran ayyukan Yowash da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

20 Fādawansa suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidan da yake Millo, a kan hanyar da ta nufi Silla.

21 Yozakar ɗan Shimeyat, da Yehozabad ɗan Shemer su ne fādawansa da suka kashe shi. Aka binne shi a makabartar kakanninsa cikin birnin Dawuda. Amaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.

Categories
2 SAR

2 SAR 13

Sarki Yehowahaz na Isra’ila

1 A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra’ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai.

2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, gama ya aikata irin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ilawa su yi zunubi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ba.

3 Ubangiji kuwa ya husata da jama’ar Isra’ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel.

4 Sai Yehowahaz ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji shi, gama ya ga wahalar da Isra’ilawa suke ciki, wato yadda Sarkin Suriya yake musguna musu.

5 Saboda haka Ubangiji ya ba jama’ar Isra’ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā.

6 Duk da haka ba su rabu da zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi. Sun aikata irin zunuban Yerobowam. Gunkiyan nan mai suna Ashtoret tana nan a Samariya.

7 Rundunar Yehowahaz kuwa ba ta fi mahaya hamsin, da karusai goma, da dakarai dubu goma (10,000) ba, gama Sarkin Suriya ya hallaka rundunar, ya yi kaca kaca da ita kamar ƙura a masussuka.

8 Sauran ayyukan Yehowahaz da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

9 Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.

Sarki Yehowash na Isra’ila

10 A shekara ta talatin da bakwai ta sarautar Yowash Sarkin Yahuza, Yehowash ɗan Yehowahaz ya ci sarautar Isra’ila a Samariya. Ya yi shekara goma sha shida yana sarauta.

11 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa jama’ar Isra’ila su yi zunubi. Ya bi halin Yerobowam ɗan Nebat.

12 Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfin da ya yi yaƙi da Amaziya Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.2Sar 14.15; 1Sar 15.31

13 Yehowash kuwa ya mutu, aka binne shi a Samariya, inda ake binne sarakunan Isra’ila, sai Yerobowam na biyu ya gāji gadon sarautarsa.

Annabi Elisha Ya Rasu

14 Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra’ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra’ila da mahayan dawakanta!”

15 Elisha kuwa ya ce masa, “Ka ɗauki baka da kibau.” Shi kuwa ya ɗauka.

16-17 Sa’an nan ya ce, “Ka buɗe tagar da take wajen gabas.” Sai ya buɗe. Elisha ya kuma ce masa, “Ka ja bakan.” Ya kuwa ja. Sai Elisha ya ɗora hannuwansa a bisa hannuwan sarki. Sa’an nan Elisha ya ce, “Harba.” Sai ya harba. Elisha kuwa ya ce, “Kibiyar Ubangiji ta nasara, kibiyar nasara a kan Suriya. Gama za ka yi yaƙi da Suriyawa a Afek har ka ci su.”

18 Sa’an nan ya ce, “Ka ɗauki kibau.” Shi kuwa ya ɗauka. Sai ya ce wa Sarkin Isra’ila, “Ka caki ƙasa da su.” Sai ya caka har sau uku, sa’an nan ya tsaya.

19 Elisha kuwa ya husata, ya ce, “Da ma ka caka sau biyar ko shida da za ka yi nasara a kan Suriyawa har ka ci su sarai, amma yanzu za ka yi nasara da su sau uku kawai.”

20 Elisha kuwa ya rasu, aka binne shi.

Maharan Mowabawa sukan kawo yaƙi a ƙasar da bazara.

21 Wata rana ana binne gawa, sai aka ga mahara, aka jefar da gawar a cikin kabarin Elisha. Da gawar ta taɓi ƙasusuwan Elisha, sai ya farko ya tashi ya miƙe tsaye.

Yaƙi tsakanin Isra’ila da Suriya

22 Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya musguna wa jama’ar Isra’ila a dukan zamanin Yehowahaz.

23 Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, bai ba su baya ba saboda alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Bai yarda ya hallaka su ba, bai kuma yi watsi da su ba har wa yau.

24 Da Hazayel Sarkin Suriya ya rasu, sai Ben-hadad ɗansa ya gāji sarautarsa.

25 Sai Yehowash ɗan Yehowahaz ya ƙwace daga hannun Ben-hadad, ɗan Hazayel, biranen da Ben-hadad ya ci da yaƙi daga hannun Yehowahaz, tsohonsa. Sau uku Yehowash ya ci shi da yaƙi, sa’an nan ya karɓe biranen Isra’ila.

Categories
2 SAR

2 SAR 14

Sarki Amaziya na Yahuza

1 A shekara ta biyu ta sarautar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra’ila, Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza ya ci sarauta.

2 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Yehowaddin ta Urushalima.

3 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma bai kai kamar kakansa Dawuda ba. Ya yi kamar yadda tsohonsa, Yowash ya yi.

4 Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadaya, da ƙona turare a matsafai na kan tuddai.

5 Sa’ad da mulkin ya kahu sosai a hannun Amaziya, sai ya kashe fādawan da suka kashe tsohonsa.

6 Amma bai kashe ‘ya’yan masu kisankai ɗin ba, don ya bi abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, inda Ubangiji ya umarta cewa, “Kada a kashe iyaye saboda ‘ya’ya, kada kuma a kashe ‘ya’ya saboda iyaye, amma kowa zai mutu saboda laifin kansa.”

7 Ya kuma kashe Edomawa dubu goma (10,000) a Kwarin Gishiri, sa’an nan ya ƙwace Sela, ya ba ta suna Yokteyel, haka ake kiranta har wa yau.

8 Amaziya kuwa ya aiki manzanni wurin Yehowash, ɗan Yehowahaz, ɗan Yehu, Sarkin Isra’ila, yana nemansa da yaƙi.

9 Yehowash Sarkin Isra’ila ya mayar wa Amaziya Sarkin Yahuza da amsa cewa, “A dutsen Lebanon ƙaya ta aika wurin itacen al’ul ta ce, ‘Ka ba ɗana ‘yarka ya aura.’ Sai mugun naman jeji na Lebanon ya wuce, ya tattake ƙayar.

10 Yanzu kai, Amaziya, ka bugi Edomawa don haka zuciyarka ta kumbura. To ka gode da darajar da ka samu, ka tsaya a gida, gama don me kake tonon rikici da zai jawo maka fāduwa, kai da mutanen Yahuza?”

11 Amma Amaziya bai ji ba. Sai Yehowash Sarkin Isra’ila ya tafi, ya shiga yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza a Bet-shemesh ta Yahuza.

12 Mutanen Isra’ila suka ci na Yahuza. Sai kowane mutum ya gudu gida.

13 Yehowash Sarkin Isra’ila kuwa ya kama Amaziya, Sarkin Yahuza, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-shemesh. Ya kuma zo Urushalima ya rushe garun Urushalima kamu ɗari huɗu daga Ƙofar Ifraimu zuwa Ƙofar Kusurwa.

14 Ya kwashe dukan zinariya, da azurfa, da dukan kwanonin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na baitulmalin gidan sarki, da mutanen da aka ba da su jingina, sa’an nan ya koma Samariya.

15 Sauran ayyukan Yehowash da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yadda ya yi yaƙi da Amaziya, Sarkin Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

16 Yehowash ya mutu, aka binne shi a Samariya a makabartar sarakunan Isra’ila, Ɗansa Yerobowam na biyu ya gāji sarautarsa.

Mutuwar Sarki Amaziya na Yahuza

17 Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, ya yi shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra’ila.

18 Sauran ayyukan da Amaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

19 Aka ƙulla makirci a kansa a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma aka aika zuwa Lakish, aka kashe shi a can.

20 Aka kawo gawar a kan dawakai, aka binne a Urushalima a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda.

21 Sai dukan mutanen Yahuza suka ɗauki Azariya mai shekara goma sha shida, suka sarautar da shi don ya gāji tsohonsa Amaziya.

22 Shi ne ya gina Elat, ya mai da ita ta Yahuza bayan rasuwar tsohonsa.

Sarki Yerobowam na biyu na Isra’ila

23 A shekara goma sha biyar ta sarautar Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash Sarkin Isra’ila, ya ci sarauta a Samariya. Ya yi mulki shekara arba’in da ɗaya.

24 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

25 Ya kafa iyakar Isra’ila daga ƙofar Hamat har zuwa tekun Araba. Wannan kuwa shi ne abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa ta bakin bawansa annabi Yunana, ɗan amittai, daga Gathefer.

26 Gama Ubangiji ya ga Isra’ila tana shan azaba mai tsanani, gama ba bawa ko ɗa wanda zai taimaki Isra’ila.

27 Ubangiji kuwa bai ce zai shafe sunan Isra’ila daga duniya ba, saboda haka ya cece su ta hannun Yerobowam na biyu.

28 Sauran ayyukan Yerobowam na biyu, da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yaƙi da ya yi, da yadda ya ƙwato wa Isra’ila Dimashƙu da Hamat waɗanda suke na Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

29 Yerobowam na biyu kuwa ya mutu, kamar kakanninsa, sarakunan Isra’ila. Zakariya ɗansa ya gaji sarautarsa.

Categories
2 SAR

2 SAR 15

Sarki Azariya na Yahuza

1 A shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Yerobowam na biyu Sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

2 Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara hamsin da biyu a Urushalima. Sunan tsohuwarsa, Yekoliya ta Urushalima.

3 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda Amaziya, tsohonsa, ya yi.

4 Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a wuraren tsafi na kan tuddai.

5 Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama’ar ƙasar.

6 Sauran ayyukan Azariya, da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

7 Azariya ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Yotam ɗansa ya gāji sarautarsa.

Sarki Zakariya na Isra’ila

8 A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Zakariya ɗan Yerobowam na biyu, ya ci sarautar Isra’ila a Samariya wata shida.

9 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar yadda kakanninsa suka yi. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

10 Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa’an nan ya hau gadon sarautarsa.

11 Sauran ayyukan da Zakariya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

12 Wannan shi ne alkawarin da Ubangiji ya yi wa Yehu, cewa ‘ya’yansa maza za su zauna a gadon sarautar Isra’ila har tsara ta huɗu. Haka kuwa ya zama.

Sarki Shallum na Isra’ila

13 Shallum ɗan Yabesh ya ci sarauta a shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza. Ya yi mulki wata ɗaya a Samariya.

14 Menahem ɗan Gadi daga Tirza ya zo Samariya ya bugi Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya hau gadon sarautarsa.

15 Sauran ayyukan Shallum duk da makircin da ya ƙulla, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

16 A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.

Sarki Menahem na Isra’ila

17 A shekara ta talatin da tara ta sarautar Azariya, Sarkin Yahuza, Menahem ɗan Gadi, ya ci sarautar. Ya yi shekara goma a Samariya.

18 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A dukan kwanakinsa bai rabu da zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

19 Tiglatfilesar, mai mulkin Assuriya, ya kawo wa ƙasar yaƙi, Menahem kuwa ya ba Tiglat-filesar talanti dubu (1,000) na azurfa, don dai ya taimake shi yadda sarautarsa za ta kahu sosai.

20 Menahem ya karɓi kuɗin daga mutanen Isra’ila, wato daga attajirai. Ya tilasta wa kowannensu ya ba da azurfa hamsin. Saboda haka Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya ya koma ƙasarsa.

21 Sauran ayyukan Menahem, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

22 Menahem ya mutu, ɗansa Fekahiya ya gaji sarautarsa.

Sarki Fekahiya na Isra’ila

23 A shekara ta hamsin ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Fekahiya ɗan Menahem, ya ci sarautar Isra’ila a Samariya. Ya yi mulki shekara biyu.

24 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

25 Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.

26 Sauran ayyukan Fekahiya, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

Sarki Feka na Isra’ila

27 A shekara ta hamsin da biyu ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Feka ɗan Remaliya ya ci sarautar Isra’ila a Samariya. Ya yi mulki shekara ashirin.

28 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa mutanen Isra’ila su yi zunubi.

29 A zamanin Feka Sarkin Isra’ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma’aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa’an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.

30 Hosheya ɗan Ila kuwa ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya, ya buge shi ya kashe shi, sa’an nan ya ci sarauta a shekara ta ashirin ta sarautar Yotam ɗan Azariya.

31 Sauran ayyukan Feka da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

Sarki Yotam na Yahuza

32 A shekara ta biyu ta sarautar Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Azariya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

33 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha, ‘yar Zadok.

34 Yotam ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda tsohonsa, Azariya, ya yi.

35 Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.

36 Sauran ayyukan Yotam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

37 A kwanakin nan Ubangiji ya fara aiken Rezin Sarkin Suriya da Feka ɗan Remaliya su yi yaƙi da Yahuza.

38 Yotam ya rasu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.

Categories
2 SAR

2 SAR 16

Sarki Ahaz na Yahuza

1 A shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.

2 Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya ci sarautar, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Bai yi abin da yake da kyau a gaban Ubangiji Allahnsa ba, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.

3 Ya bi halin sarakunan Isra’ila. Har ma ya yi hadaya ta ƙonawa da ɗansa, kamar mugayen ayyukan al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban mutanen Isra’ila.

4 Ya kuma miƙa hadaya da turaren ƙonawa a wuraren tsafi na kan tuddai da ƙarƙashin itatuwa masu duhuwa.

5 Rezin Sarkin Suriya kuwa, da Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra’ila, suka kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye Ahaz da yaƙi, amma ba su ci shi ba.

6 A lokacin nan kuma Sarkin Edom ya sāke ƙwace Elat, ya kori Yahudawa daga cikinta, Edomawa suka zo suka zauna a ciki har wa yau.

7 Ahaz kuwa ya aiki manzanni wurin Tiglat-filesar, mai mulkin Assuriya, ya ce, “Ni baranka ne, ɗanka kuma, ka zo ka cece ni daga hannun Sarkin Suriya da Sarkin Isra’ila, waɗanda suke yaƙi da ni.”

8 Ahaz kuma ya kwashe azurfa da zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, da wadda take cikin baitulmalin sarki, ya aika wa mai mulkin Assuriya kyauta.

9 Tiglat-filesar ya ji roƙonsa, sai ya zo ya faɗa wa Dimashƙu da yaƙi, ya ci ta. Sa’an nan ya kwashe mutane zuwa Kir. Ya kuma kashe sarki Rezin.

10 Sa’ad da sarki Ahaz ya tafi Dimashƙu don ya sadu da Tiglat-filesar, Sarkin Assuriya, ya ga bagaden da yake a Dimashƙu, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayaninsa.

11 Uriya firist kuwa, ya gina bagaden bisa ga yadda sarki Ahaz ya aika masa daga Dimashƙu. Uriya firist, ya gina bagaden kafin sarki Ahaz ya komo daga Dimashƙu.

12 Da sarki ya komo daga Dimashƙu, ya hango bagaden, sai ya tafi kusa da shi.

13 Sa’an nan ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayarsa ta gari, da hadayarsa ta sha, ya yayyafa jinin hadayarsa ta salama a bisa bagaden.

14 Sai ya kawar da bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi arewacin sabon bagadensa.

15 Sarki Ahaz ya umarci Uriya firist cewa, “Sai ka miƙa hadaya ta ƙonawa ta safe, da hadaya ta gari ta maraice, da hadaya ta ƙonawa ta sarki, da hadayarsa ta gari, da hadaya ta ƙonawa ta dukan jama’ar ƙasar, da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, ka yayyafa dukan jinin hadaya ta ƙonawa, da dukan jinin hadayu a bisa babban bagaden. Amma bagaden tagulla zai zama nawa don yin ibada.”

16 Uriya firist kuwa, ya yi dukan abin da sarki Ahaz ya umarta.

17 Sarki Ahaz kuwa ya yanke sassan dakalan, ya ɗauke daruna da suke bisansu, ya kuma ɗauke kwatarniya da take bisa bijimai na tagulla, ya ajiye kwatarniya a daɓen dutse.

18 Hanyar da aka killace ta Asabar, wadda suka yi a cikin gidan, da ƙofar waje ta shigar sarki, Ahaz ya kawar da su daga Haikalin Ubangiji saboda Sarkin Assuriya.

19 Sauran ayyukan Ahaz waɗanda ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

20 Ahaz ya mutu, aka binne shi a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda. Sai ɗansa, Hezekiya, ya gaji sarautarsa.

Categories
2 SAR

2 SAR 17

Faɗuwar Samariya da Bautar Isra’ila

1 A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Ahaz Samariya Yahuza, Hosheya ɗan Ila ya ci sarautar Isra’ila a Samariya. Ya yi mulki shekara tara.

2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar sauran sarakunan Isra’ila da suka riga shi ba.

3 Sai Shalmanesar Sarkin Assuriya, ya kawo masa yaƙi, Hosheya kuwa ya zama talakansa, yana kai masa haraji.

4 Amma Sarkin Assuriya ya gane Hosheya ya tayar masa, gama ya aiki manzanni wurin So, wato Sarkin Masar, ya kuma ƙi ya kai wa Sarkin Assuriya haraji kamar yadda ya saba yi kowace shekara, Saboda haka sai Sarkin Assuriya ya kama shi ya sa shi a kurkuku.

5 Sa’an nan Sarkin Assuriya ya kai wa dukan ƙasar yaƙi, har ya kai Samariya. Ya kewaye Samariya da yaƙi shekara uku.

6 A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.

7 Wannan abu ya sami Isra’ila saboda sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fito da su daga ƙasar Masar, daga hannun Fir’auna, Sarkin Masar. Suka bauta wa gumaka.

8 Suka bi al’adun al’ummai waɗanda Ubangiji ya kora a gabansu, da al’adun da sarakunan Isra’ila suka kawo.

9 Jama’ar Isra’ila kuma suka yi wa Ubangiji Allahnsu abubuwan da ba daidai ba, daga ɓoye. Sun gina wa kansu matsafai a dukan garuruwansu daga hasumiya zuwa birni mai garu.

10 Suka kuma kafa wa kansu ginshiƙai da siffofin gumakan Ashtarot a kowane tudu da a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.

11 Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al’ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi.

12 Suka bauta wa gumaka waɗanda Ubangiji ya ce musu kada su bauta musu.

13 Amma Ubangiji ya faɗakar da jama’ar Isra’ila da jama’ar Yahuza ta bakin annabawa da kowane maigani, cewa su bar mugayen hanyoyinsu, su kiyaye umarnansa da dukan dokokinsa waɗanda ya umarci kakanninsu da su, waɗanda kuma ya aiko musu ta wurin bayinsa annabawa.

14 Duk da haka suka ƙi kasa kunne, suka taurare zuciyarsu kamar yadda kakanninsu suka yi, waɗanda ba su yi imani da Ubangiji Allahnsu ba.

15 Suka yi watsi da dokokinsa, da alkawarinsa da ya yi wa kakanninsu, da kuma faɗakarwar da ya yi musu. Suka bi gumakan banza, suka zama banza, suka bi halin al’ummai da suke kewaye da su, waɗanda Ubangiji ya umarce su kada su yi kamarsu.

16 Suka bar dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu siffofin zubi na ‘yan maruƙa biyu, suka yi gunkiyan nan, Ashtoret, suka yi wa taurari sujada, suka bauta wa Ba’al.

17 Suka yi hadaya ta ƙonawa da ‘ya’yansu mata da maza. Suka yi duba, suka yi sihiri, suka duƙufa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji, suka sa shi ya yi fushi.

18 Saboda wannan Ubangiji ya husata da jama’ar Isra’ila, ya kawar da su daga gabansa, ba wanda aka rage, sai dai kabilar Yahuza.

19 Jama’ar Yahuza kuma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba, sai suka bi al’adun da mutanen Isra’ila suka kawo.

20 Ubangiji kuwa ya ƙi dukan zuriyar Isra’ila, ya wahalshe su, ya kuma bashe su a hannun mugayen abokan gāba, ta haka ya kawar da su daga gabansa.

21 Sa’ad da Ubangiji ya ɓalle Isra’ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat ya zama sarki. Yerobowam kuwa ya karkatar da jama’ar Isra’ila daga bin Ubangiji. Ya sa su suka aikata babban zunubi.

22 Jama’ar Isra’ila suka yi ta aikata dukan zunuban da Yerobowam ya yi, ba su daina aikata su ba.

23 har lokacin da Ubangiji ya kawar da su daga gabansa kamar yadda ya faɗa ta bakin bayinsa, annabawa. Saboda haka aka fitar da jama’ar Isra’ila daga ƙasarsu zuwa Assuriya har wa yau.

An Zaunar da Assuriyawa cikin Isra’ilawa

24 Sarkin Assuriya kuwa ya kawo mutane daga Babila, da Kuta, da Awwa, da Hamat, da Sefarwayim, ya zaunar da su a garuruwan Samariya a maimakon jama’ar Isra’ila. Sai suka mallaki Samariya, suka zauna a garuruwanta.

25 A farkon zamansu a can, ba su yi tsoron Ubangiji ba saboda haka Ubangiji ya aika da zakoki a cikinsu, suka karkashe waɗansu daga cikinsu.

26 Sai aka faɗa wa Sarkin Assuriya cewa, “Al’umman da ka kwashe ka zaunar da su a garuruwan Samariya ba su san shari’ar Allahn ƙasar ba, domin haka ya aiki zakoki a cikinsu, suna ta karkashe su.”

27 Sa’an nan Sarkin Assuriya ya umarta a aiki firist ɗaya daga cikin firistocin da aka kwashe daga can, ya tafi, ya zauna can domin ya koya musu shari’ar Allahn ƙasar.

28 Sai firist ɗaya daga cikin firistocin da suka kwashe daga Samariya, ya zo, ya zauna a Betel. Shi kuwa ya koya musu yadda za su yi tsoron Ubangiji.

29 Amma duk da haka kowace al’umma ta riƙa yin gumakanta, tana ajiye su a wuraren yin tsafin na kan tuddai waɗanda Samariyawa suka gina. Kowace al’umma kuma ta yi haka a garin da ta zauna.

30 Mutanen Babila suka yi Sukkot-benot, mutanen Kuta suka yi Nergal, mutanen Hamat suka yi Ashima.

31 Awwiyawa suka yi Nibhaz da Tartak, mutanen Sefarwayim suka miƙa ‘ya’yansu hadaya ta ƙonawa ga Adrammelek da Anammelek, gumakansu.

32 Su ma suka yi tsoron Ubangiji, suka sa mutane iri dabam dabam su zama firistocin wuraren tsafinsu na kan tuddai. Firistocin nan suka miƙa hadayu dominsu a ɗakunan tsafinsu na kan tuddai.

33 Waɗannan mutane su ma suka yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka bauta wa gumakansu ta hanyar da al’umman da aka kwaso su daga cikinsu suke yi.

34 Har wa yau suna yin yadda suka yi a dā. Ba su yi tsoron Ubangiji ba, ba su bi dokoki, ko ka’idodi, ko shari’a, ko umarnan Ubangiji ba, waɗanda ya umarci ‘ya’yan Yakubu, wanda ya sa wa suna Isra’ila.

35 Ubangiji ya yi alkawari da ‘ya’yan Yakubu, ya kuma umarce su kada su yi wa gumaka sujada ko su durƙusa musu, ko su bauta musu, ko su miƙa musu hadayu.

36 Amma su yi tsoron Ubangiji, wanda ya fisshe su daga ƙasar Masar da iko mai girma da ƙarfi, shi za su yi wa sujada, shi kuma za su miƙa wa hadayu.

37 Sai su yi biyayya da dokokinsa da umarnansa da ya rubuta musu. Kada su ji tsoron waɗansu alloli.

38 Kada su manta da alkawarin da ya yi da su, kada kuma su ji tsoron gumaka.

39 Amma su yi tsoron Ubangiji Allahnsu, shi kuwa zai cece su daga hannun dukan abokan gābansu.

40 Duk da haka ba su kasa kunne ba, amma suka yi kamar yadda suka saba yi tun dā.

41 Waɗannan al’ummai suka yi wa Ubangiji sujada, amma suka kuma yi ta bauta wa gumakansu. Haka kuma ‘ya’yansu da jikokinsu suka yi kamar yadda kakanninsu suka yi. Haka suke yi har wa yau.

Categories
2 SAR

2 SAR 18

Sarki Hezekiya na Yahuza

1 A shekara ta uku ta sarautar Hosheya ɗan Ila Sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz Sarkin Yahuza ya ci sarautar.

2 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarautar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abi, ‘yar Zakariya.

3 Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.

4 Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama’ar Isra’ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan.

5 Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa.

6 Ya manne wa Ubangiji, bai bar binsa ba, ya kuma kiyaye umarnan da Ubangiji ya ba Musa.

7 Ubangiji kuwa ya kasance tare da shi, duk inda ya nufa sai ya sami albarka. Ya tayar wa Sarkin Assuriya, ya ƙi bautar masa.

8 Ya kuma bugi Filistiyawa har zuwa Gaza da iyakarta daga hasumiya zuwa birni mai garu.

Faɗuwar Samariya

9 A shekara ta huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, a lokacin Hosheya ɗan Ila, Sarkin Isra’ila, yana da shekara bakwai da sarauta, sai Shalmanesar Sarkin Assuriya ya kawo wa Samariya yaƙi, ya kewaye ta.

10 A ƙarshen shekara ta uku, ya ci ta da yaƙi. A lokacin Hezekiya yana da shekara shida da sarauta, Hosheya kuwa yana da shekara tara da tasa sarauta.

11 Sarkin Assuriya kuwa ya kwashi Isra’ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.

12 Ba su yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsa har da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su kasa kunne ba, balle su aikata. Domin wannan Samariya ta faɗi.

Assuriyawa Sun Yi wa Urushalima Barazana

13 A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa dukan birane masu garu na Yahuza yaƙi, ya kuwa ci su.

14 Sai Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya aika zuwa wurin Sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka ƙyale ni, duk abin da ka ɗora mini zan ɗauka.” Sai Sarkin Assuriya ya ce wa Hezekiya Sarkin Yahuza ya ba shi talanti ɗari uku na azurfa, da talanti talatin na zinariya.

15 Hezekiya kuwa ya ba shi dukan azurfar da take cikin Haikalin Ubangiji, da wanda yake cikin baitulmali na gidan sarki.

16 A lokacin sai Hezekiya ya kankare zinariyar da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin Haikalin Ubangiji da ita, ya ba Sarkin Assuriya.

17 Sai Sarkin Assuriya ya aiki Tartan, da Rabsaris, da Rabshake, tare da sojoji da yawa daga Lakish zuwa ga sarki Hezekiya a Urushalima. Suka haura zuwa Urushalima, suka tsaya kusa da wuriyar ruwan kududdufi wanda yake kan tudu, wanda yake a kan karauka zuwa wurin wanki.

18 Sa’ad da suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka fito.

19 Sa’an nan Rabshake ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya, cewa mai girma, Sarkin Assuriya ya ce, ‘Ga wa kake dogara?

20 Kana tsammani maganganu kurum su ne dabara da ƙarfin yin yaƙi? To, ga wa ka dogara har da ka tayar mini?

21 Ga shi yanzu, kana dogara ga Masar, wannan karyayyen sandan kyauro, wanda yakan yi wa hannun mutumin da yake tokarawa da shi sartse. Haka Fir’auna Sarkin Masar, yake ga dukan waɗanda suke dogara gare shi.’

22 “Amma idan ka ce mini, ‘Ina dogara ga Ubangiji Allahnmu,’ to, ba masujadansa na kan tuddai da bagadansa ne Hezekiya ya rurrushe ba? Yana ce wa mutanen Yahuza da Urushalima, ‘Za ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima?’

23 Sai ka zo, ku daidaita da ubangidana, Sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu (2,000), idan za ka iya samun mahayansu.

24 Ba ka isa ka kara da ko mafi ƙanƙanta na shugabannin sojojin maigidana ba, amma har kana dogara ga Masar don samun karusai da mahaya?

25 Kana tsammani, ba da yardar Ubangiji ba ne na kawo wa wurin nan yaƙi don a hallaka shi? Gama Ubangiji ya ce mini, ‘Ka kai wa wannan ƙasa yaƙi don ka hallaka ta.’ ”

26 Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa, suka ce wa Rabshake, “Muna roƙonka, ka yi magana da mu barorinka da harshen Aramiya gama muna jinsa, kada ka yi magana da mu da harshen Yahudanci, har mutanen da suke kan garu su ji.”

27 Amma Rabshake ya ce musu, “Ai, ubangidana bai aike ni in yi wannan magana ga ubangidanku da ku kaɗai ba, amma ga dukan mutanen da suke zaune a kan garu, waɗanda aka ƙaddara su tare da ku don su ci najasarsu su sha fitsarinsu.”

28 Sa’an nan Rabshake ya tsaya, ya yi kira da ƙarfi da harshen Yahudanci, ya ce, “Ku ji maganar mai girma, Sarkin Assuriya!

29 Sarki ya ce, ‘Kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, gama ba zai iya cetonku daga hannuna ba.

30 Kada kuma ku yarda Hezekiya ya sa ku dogara ga Ubangiji da cewa lalle Ubangiji zai cece ku, ba za a kuma ba da wannan birni a hannun Assuriya ba.’

31 Kada ku kasa kunne ga Hezekiya, gama Sarkin Assuriya ya ce, ‘Ku yi amana da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ‘ya’yan inabinsa da ‘ya’yan ɓaurensa, ya kuma sha ruwa daga cikin randarsa,

32 har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi,da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! Kada kuma ku yarda Hezekiya ya yaudare ku da cewa Ubangiji zai cece ku.

33 Ko akwai wani allah daga cikin allolin al’ummai, wanda ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun Sarkin Assuriya?

34 Ina allolin Hamat, da na Arfad, da na Sefarwayim, da na Hena, da na Iwwa? Sun ceci Samariya daga hannuna ne?

35 Daga cikin dukan allolin ƙasashe, wane ne ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannuna har da Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?’ ”

36 Sai mutanen suka yi tsit, ba wanda ya ce masa uffan, gama sarki ya umarta cewa kada a tanka masa.

37 Sa’an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.

Categories
2 SAR

2 SAR 19

An Ceci Yahuza daga Sennakerib

1 Da sarki Hezekiya ya ji wannan magana, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa rigar makoki, sa’an nan ya shiga Haikalin Ubangiji.

2 Sai ya aiki Eliyakim wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da manyan firistoci, saye da tufafin makoki zuwa wurin annabi Ishaya, ɗan Amoz,

3 su ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ‘ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.

4 Mai yiwuwa ne Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun da Rabshake ya yi wanda ubangidansa, Sarkin Assuriya, ya aiko don yi wa Allah mai rai ba’a. Bari Ubangiji Allahnka ya hukunta masa saboda maganganunsa, sai ka yi addu’a saboda sauran da suka ragu.”

5 Sa’ad da fādawan sarki Hezekiya suka iso wurin Ishaya,

6 sai ya aike da amsa, ya ce musu, “Ku faɗa wa ubangidanku, Ubangiji ya ce, ‘Kada ka ji tsoron maganganun da ka ji daga bakin barorin Sarkin Assuriya, waɗanda suka saɓe ni.

7 Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa da zai ji jita-jita, har ya koma ƙasarsa, zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”

8 Rabshake kuwa ya koma, ya tarar Sarkin Assuriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji labari sarki ya riga ya bar Lakish.

9 Da sarki ya ji labari Tirhaka, Sarkin Habasha, ya fito don ya yi yaƙi da shi, sai ya sāke aikar manzanni wurin Hezekiya, ya ce,

10 “Ku faɗa wa Hezekiya Sarkin Yahuza, kada ya yarda Allahnsa wanda yake dogara gare shi ya yaudare shi da yi masa alkawari, cewa Sarkin Assuriya ba zai ci Urushalima ba.

11 Ya ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa dukan ƙasashe yadda ya hallaka su sarai. To, shi zai kuɓuta?

12 Allolin al’ummai sun cece su ne? Wato al’umman da kakannina suka hallaka, wato Gozan, da Haran, da Rezef, da mutanen Eden da suke Telassar.

13 Ina Sarkin Hamat, da Sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarwayim, da Sarkin Hena, da Sarkin Iwwa?”

14 Hezekiya ya karɓi wasiƙa daga hannun manzannin ya karanta ta, sa’an nan ya shiga Haikalin Ubangiji, ya buɗe ta, ya ajiye ta a gaban Ubangiji.

15 Sa’an nan ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.

16 Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka yi. Ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka gani, ka kuma ji irin maganar Sennakerib wadda ya aiko don a yi wa Allah mai rai ba’a.

17 A gaskiya kam, ya Ubangiji, sarakunan Assuriya sun lalatar da al’ummai da ƙasashensu.

18 Sun jefar da gumakansu cikin wuta, gama su ba Allah ba ne, amma ayyukan hannuwan mutane ne, waɗanda aka yi da itace da dutse, saboda haka an iya a hallaka su.

19 Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”

20 Sa’an nan Ishaya, ɗan Amoz, ya aika wa Hezekiya cewa, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ji addu’arka, ya kuma amsa.”

21 Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima ya yi maka dariya, kai Sennakerib, yana yi maka ba’a.

22 Wa kake tsammani ka yi wa ba’a har da zagi? Ba ka ga girmana ba, ni Allah Mai Tsarki na Isra’ila?

23 Ka aiki manzanninka su nuna mini girmankai saboda ka ci duwatsu mafi tsayi da karusanka, har ma ka ci duwatsun Lebanon. Ka yi fariyar a kan ka datse itatuwan al’ul mafi tsayi da na fir, har kuma ka shiga har can tsakiyar kurmi.

24 Ka yi fariya a kan gina rijiyoyi, ka sha ruwan baƙuwar ƙasa, ƙafafun sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu, ya ƙafe.

25 “Ba ka taɓa ji ba, cewa na ƙaddara wannan tun dā? Abin da yake faruwa yanzu, na shirya shi tun tuni, yadda za ka mai da birane masu garu su zama kufai.

26 Mazauna cikinsu suka rasa ƙarfi, suka damu, suka ruɗe. Suka zama kamar ciyawar saura, ko kuma ciyawar da ta tsiro a rufin soro, da iskar gabas mai zafi ta busa, har ta bushe.

27 “Na san zamanka, da fitarka, da shigowarka, da fushin da kake yi da ni.

28 Na ji irin fushinka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai baya, ta hanyar da ka biyo.”

29 Sa’an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci ‘ya’yansu.

30 Ringin mutanen gidan Yahuza za su yi saiwa a ƙasa, sa’an nan su ba da ‘ya’ya a sama.

31 Gama daga Urushalima ringi zai fito, daga Dutsen Sihiyona kuma waɗanda suka tsira za su fito. Kishin Ubangiji ne zai yi wannan.”

32 Saboda haka Ubangiji ya ce, “Sarkin Assuriya ba zai zo birnin ba, ko ya harba kibiya, ko ya zo kusa da shi da garkuwa, ko ya tsiba masa tudu.

33 Zai koma ta hanyar da ya zo. Ba zai shiga wannan birni ba.

34 Gama zan tsare wannan birni, in cece shi don kaina, da kuma don bawana Dawuda.”

35 A daren nan, sai mala’ikan Ubangiji ya tafi ya kashe Assuriyawa a sansaninsu, mutum dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Sa’ad da mutanen Isra’ila suka tashi da sassafe, sai suka ga gawawwakin nan kwance.

36 Sennakerib Sarkin Assuriya, kuwa ya tashi, ya koma gida, ya zauna a Nineba.

37 Sa’ad da yake yin sujada a haikalin gunkinsa Nisrok, sai ‘ya’yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takobi, sa’an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai ɗansa guda, wato Esar-haddon ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 SAR

2 SAR 20

Ciwon Hezekiya da Warkewarsa

1 A waɗannan kwanaki sai Hezekiya ya yi rashin lafiya har yana gab da mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya zo wurinsa, ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka, gama mutuwa za ka yi, ba za ka warke ba.”

2 Hezekiya kuwa ya juya fuskarsa bango, ya yi roƙo ga Ubangiji, yana cewa,

3 “Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.

4 Kafin Ishaya ya fita daga filin tsakiyar fādar, sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce,

5 “Ka koma, ka faɗa wa Hezekiya sarkin jama’ata cewa, ‘Ni Ubangiji Allahn kakanka, Dawuda, na ji roƙonka, na kuma ga hawayenka, saboda haka zan warkar da kai, a rana ta uku kuwa za ka haura zuwa Haikalin Ubangiji.

6 Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuwa cece ka, kai da wannan birni daga hannun Sarkin Assuriya, zan tsare wannan birni don kaina da kuma don bawana, Dawuda.’ ”

7 Sai Ishaya ya ce, “Ku yi masa farsa da ɓaure, marurun zai warke.”

8 Hezekiya kuwa ya ce wa Ishaya, “Mece ce alama, cewa Ubangiji zai warkar da ni har in haura zuwa Haikalin Ubangiji a rana ta uku?”

9 Sai Ishaya ya ce, “Wannan ita ce alama daga wurin Ubangiji, Ubangiji zai cika alkawarin da ya yi. Ƙaƙa kake so, inuwa ta yi gaba da taki goma, ko kuwa ta yi baya da taki goma?”

10 Hezekiya ya amsa, ya ce, “Ai, ya fi sauƙi inuwa ta yi gaba da taki goma da ta yi baya da taki goma.”

11 Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya komar da inuwa baya da taki goma, bayan da ta riga ta wuce a matakin sarki Ahaz.

Hezekiya ya Karɓi Manzanni daga Babila

12 A lokacin nan sai Merodak-baladan, ɗan Baladan, Sarkin Babila, ya ji labarin rashin lafiyar Hezekiya, sai ya aiki manzanni da wasiƙa da kyautai su kai wa Hezekiya,

13 Hezekiya kuwa ya marabce su, ya kuma nuna musu dukan taskokin dukiyarsa na azurfa, da na zinariya, da na turare, da na mai mai daraja, da na makaman yaƙinsa, da dukan abin da yake akwai a cikin ɗakunan ajiyarsa. Ba abin da ya rage daga cikin gidansa, ko a mulkinsa wanda bai nuna musu ba.

14 Sai annabi Ishaya ya tafi wurin sarki Hezekiya ya ce masa, “Daga ina ne waɗannan mutane? Me suka ce maka?”

Hezekiya ya amsa, ya ce, “Sun zo daga ƙasa mai nisa, wato Babila.”

15 Ishaya ya ce, “Me suka gani a fādarka?”

Hezekiya ya ce, “Sun ga duk abin da yake ciki, ba wani abu kuma daga cikin taskokina da ban nuna musu ba.”

16 Sa’an nan Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji abin da Ubangiji ya ce,

17 ‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe duk abin da yake cikin gidanka, da abin da kakanninka suka tanada, zuwa Babila.

18 Za a kuma kwashe waɗansu ‘ya’yanka da ka haifa zuwa Babila, can za a maishe su babani a fādar Sarkin Babila.’ ”

19 Sarki Hezekiya kuwa ya fahimci za a yi zaman lafiya da salama a zamaninsa, don haka ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”

Rasuwar Hezekiya

20 Sauran ayyukan Hezekiya da dukan ƙarfinsa, da yadda ya yi tafki da wuriyar ruwa don ya kawo ruwa cikin birnin, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.

21 Hezekiya kuwa ya rasu. Sai ɗansa, Manassa, ya gāji gadon sarautarsa.