Categories
2 TAR

2 TAR 1

Addu’ar Sulemanu ta Neman Hikima

1 Sulemanu ɗan Dawuda ya kahu sosai cikin mulkinsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, Ubangiji kuwa ya sa shi ya zama mashahuri.

2 Sulemanu ya yi magana da dukan manya, wato shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da alƙalai, da dukan shugabanni na Isra’ila, wato shugabannin gidajen kakanni.

3 Sa’an nan Sulemanu da dukan waɗanda suke tare da shi, suka tafi masujadar da take a Gibeyon, gama alfarwar sujada ta Allah, wadda Musa, bawan Ubangiji ya yi a jeji, tana can.

4 Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.

5 Amma bagaden tagulla wanda Bezalel ɗan Uri daga dangin Hur, ya yi, yana a gaban Wuri Mai Tsarki na Ubangiji, sai Sulemanu da taron jama’a suka yi sujada ga Ubangiji a can.

6 Sulemanu kuwa ya haura, ya tafi wurin da bagaden tagulla yake a gaban Ubangiji, a cikin alfarwa ta sujada, ya miƙa hadayun ƙonawa dubu a kansa.

7 A wannan dare Allah ya bayyana ga Sulemanu, ya ce masa, “Ka roƙe ni abin da kake so in ba ka.”

8 Sai Sulemanu ya ce wa Allah, “Ka nuna wa tsohona Dawuda madawwamiyar ƙaunarka, har ka naɗa ni sarki a matsayinsa.

9 Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama’a mai yawa kamar turɓaya.

10 Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama’a, gama wa zai iya mulkin wannan jama’a taka mai yawa haka?”

11 Allah kuwa ya amsa wa Sulemanu ya ce, “Tun da kana da irin wannan tunani a zuciyarka, ba ka kuwa roƙi dukiya, ko wadata, ko girma, ko ran maƙiyanka ba, ba ka kuma roƙi tsawon rai ba, amma ka roƙa wa kanka hikima da sani domin ka iya yin mulkin jama’ata wadda na naɗa ka sarki a kanta,

12 to, na ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka dukiya, da wadata, da girma, waɗanda ba wani sarkin da ya taɓa samun irinsu, ba kuma wani sarkin da zai taɓa samun irinsu.”

13 Daga nan sai Sulemanu ya taso daga masujadar da take Gibeyon inda alfarwa ta sujada take, ya zo Urushalima inda ya zauna yana mulkin Isra’ila.

Sulemanu Ya Tara Dawakai da Karusai

14 Sai Sulemanu ya tara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), sai ya sa su a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da shi.

15 Sarki ya yawaita azurfa da zinariya har suka zama kamar duwatsu a Urushalima. Haka kuma ya yi da itatuwan al’ul, suka yawaita kamar itatuwan ɓaure a fadama.

16 Wakilan sarki suka ɗauki nauyin shigo da dawakai daga Masar da Kilikiya,

17 suka kuma shigo da karusai daga Masar. Suka riƙa sayar wa sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa karusai a kan azurfa ɗari shida shida, kowane doki kuma a kan azurfa ɗari da hamsin.

Categories
2 TAR

2 TAR 2

Shirye-shiryen Ginin Haikali

1 Sai Sulemanu ya yi niyya a ransa zai gina Haikali saboda sunan Ubangiji, ya kuma gina wa kansa fāda.

2 Don haka, sai ya sa mutane dubu saba’in (70,000) don ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) su haƙo duwatsu a tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuma su ne shugabanni.

3 Sulemanu fa ya aika wurin Hiram Sarkin Taya ya ce, “Yadda ka yi wa tsohona Dawuda, wato ka aiko masa da itatuwan al’ul domin ya gina gida inda zai zauna, ni ma ina so ka yi mini haka.

4 Ga shi dai, na yi niyyar gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe masa shi, domin a riƙa ƙona masa turare mai daɗin ƙanshi, inda kuma za a riƙa ajiye gurasar ajiyewa dukan lokaci, don kuma a riƙa miƙa hadayun ƙonawa safe da yamma, da ranakun Asabar, da na amarya wata, da kuma a lokatan ƙayyadaddun idodin Ubangiji Allahnmu, yadda dai aka faralta a riƙa yi a cikin Isra’ila.

5 Haikalin nan kuwa da nake niyyar ginawa babba ne, gama Allahnmu ya fi dukan alloli.

6 Amma wa ya isa ya gina masa Haikali, shi wanda sama da saman sammai ba su iya ɗaukarsa ba. Ni wane ne da zan gina masa Haikali, sai dai wurin da za a riƙa ƙona turare a gabansa?

7 Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanance a kan aiki da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanance da aikin sassaƙa, domin ya yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuza da Urushalima, waɗanda tsohona Dawuda ya kawo.

8 Ka kuma aiko mini da itacen al’ul, da na fir, da katakon algum daga Lebanon, gama na sani barorinka sun san yadda ake yanyanka katakan Lebanon. Barorina za su yi aiki tare da barorinka,

9 domin su shirya mini katako mai yawa. Gama Haikalin da zan gina mai girma ne ƙwarai, mai banmamaki.

10 Zan ba barorinka masu aikin katako misalin mudu dubu ashirin (20,000) ta sussukakkiyar alkama, da mudu dubu ashirin (20,000) ta sha’ir, da misalin garwar ruwan inabi dubu ashirin (20,000), da ta mai dubu ashirin (20,000).”

11 Hiram, Sarkin Taya kuwa, ya ba Sulemanu amsar takardarsa, ya ce, “Saboda Ubangiji yana ƙaunar jama’arsa, ya naɗa ka sarkinsu.”

12 Hiram ya ci gaba da cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa, ya ba sarki Dawuda ɗa mai hikima, mai hankali, mai ganewa, wanda zai gina Haikali dominsa, ya gina fāda kuma domin kansa.

13 Yanzu zan aika maka da Huram mutum mai gwaninta, mai ganewa.

14 Shi ɗan wata mace mutuniyar Dan, mahaifinsa kuwa mutumin Taya ne. Huram ya gwanance a kan aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da dutse, da itace, da kuma shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau. Shi kuma zai iya sassaƙa kowane irin abu da aka sa shi ya sassaƙa, tare da gwanayenka, da na tsohonka, ubangidana, wato Dawuda.

15 To, yanzu, sai ka aiko wa barorinka da alkama, da sha’ir, da mai, da ruwan inabi kamar yadda ka alkawarta.

16 Mu kuwa za mu yanko maka dukan katakan da kake bukata a Lebanon, mu kawo maka su a kan gadajen fito ta hanyar teku, zuwa Yafa, domin ka kwashe ka kai Urushalima.”

An Fara Ginin Haikali

17 Sarki Sulemanu ya ƙidaya dukan baƙin da suke a ƙasar Isra’ila, kamar yadda tsohonsa Dawuda ya yi. Yawan baƙin da aka samu sun kai dubu ɗari da dubu hamsin da uku, da ɗari shida (153,600).

18 Sai ya zaɓi mutum dubu saba’in (70,000) daga cikinsu su zama masu ɗaukar kaya, dubu tamanin (80,000) kuma don su riƙa haƙo duwatsu daga tsaunuka, dubu uku da ɗari shida (3,600) kuwa don su zama shugabanni.

Categories
2 TAR

2 TAR 3

Sulemanu Ya Gina Ɗakin Sujada domin Ubangiji

1 Sulemanu kuwa ya fara ginin Haikalin Ubangiji a Urushalima a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga tsohonsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Arauna Bayebuse.

2 Ya fara ginin a ran biyu ga watan biyu a shekara ta huɗu ta sarautarsa.

3 Ga awon harsashin da Sulemanu ya kafa domin ginin Haikalin Ubangiji. Tsawonsa bisa ga tsohon magwajin, kamu sittin ne, fāɗin kuwa kamu ashirin.

4 Tsawon shirayi daga gaban Haikalin ya yi daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, sa’an nan tsayinsa kamu ɗari da ashirin. Aka shafe ciki da zinariya tsantsa.

5 Ya jera itatuwan fir a cikin babban ɗakin, sa’an nan ya shafe su da zinariya tsantsa, ya kuma zana siffofin itatuwan dabino da na sarƙoƙi.

6 Banda wannan kuma ya ƙawata Haikalin da duwatsu masu daraja da zinariya irin ta Farwayim.

7 Ya kuma shafe Haikalin duk da ginshiƙansa, da bakin ƙofofinsa, da bangayensa, da ƙyamarensa da zinariya, ya kuma zana siffofin kerubobi a jikin bangaye.

8 Sai ya gina Wuri Mafi Tsarki. Tsawonsa daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu ashirin. Ya shafe shi da zinariya tsantsa, wadda jimillar nauyinta ta yi talanti ɗari shida.

9 Nauyin ƙusoshin ya kai shekel hamsin na zinariya. Ya kuma shafe benaye da zinariya tsantsa.

10 Ya sassaƙa siffofin kerubobi biyu na itace, a Wuri Mafi Tsarki, ya shafe su da Zinariya.

11 Tsawon fikafikan kerubobin duka kamu ashirin ne, fiffike ɗaya, kamu biyar, ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken kuma wanda shi ma kamu biyar ne, ya taɓo fiffiken kerub ɗaya ɗin.

12 Guda kerub ɗin kuma, fiffikensa guda ya taɓo bangon ɗakin, ɗaya fiffiken shi ma ya taɓo fiffiken kerub na farko.

13 Tsawon fikafikan kerubobin ya kai kamu ashirin. Su kerubobin a tsaye suke, suna fuskantar babban ɗakin.

14 Sai ya yi labule mai launin shuɗi, da shunayya, da garura, da lilin mai kyau, sa’an nan ya zana siffofin kerubobin a jikin labulen.

Kayan Haikali

15 Ya kuma yi ginshiƙai biyu domin ƙofar Haikalin, tsayinsu kamu talatin da biyar ne, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.

16 Ya yi sarƙoƙi, ya rataya wa ginshiƙan, ya kuma yi siffofin rumman guda ɗari, ya maƙala wa sarƙoƙin.

17 Sai ya kafa ginshiƙin a ƙofar Haikali, ɗaya a wajen kudu, ɗaya kuma a wajen arewa. Ya sa wa na wajen kudu suna Yakin, na wajen arewa kuwa Bo’aza.

Categories
2 TAR

2 TAR 4

1 Ya yi bagade na tagulla, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin, tsayinsa kuwa kamu goma.

2 Ya yi kwatarniya kewayayyiya ta zubi, kamu goma daga gāɓa zuwa gāɓa, tsayinsa kuwa kamu biyar ne, da’irarsa kuwa kamu talatin.

3 A ƙashiyar kwatarniya akwai siffofin bijimai kamu goma kewaye da ita har jeji biyu. Gaba ɗaya aka yi zubinsu da na kwatarniya.

4 Kwatarniya tana bisa bijimai goma sha biyu, uku suna fuskantar gabas, uku suna fuskantar yamma, uku suna fuskantar kudu, uku kuma suna fuskantar arewa. Kwatarniya tana bisa bijiman, gindin kowannensu yana daga ciki.

5 Kaurin kwatarniya taƙi guda ne, bakinsa kamar bakin finjali ne, kamar kuma siffar furen bi-rana. Kwatarniya kuwa tana iya ɗaukar fiye da garwa dubu uku na ruwa.

6 Ya kuma yi daro goma na wanki, ya ajiye biyar a wajen kudu, biyar kuma a wajen arewa, don a riƙa ɗauraye abubuwan da ake hadayar ƙonawa da su. Amma kwatarniya don firistoci su riƙa wanka a ciki ne.

7 Sa’an nan ya yi alkuki goma na zinariya kamar yadda aka tsara. Ya sa su cikin Haikali, biyar a sashen dama, biyar kuma a hagu.

8 Ya kuma yi tebur goma, ya ajiye a cikin Haikalin, biyar a dama, biyar kuma a hagu. Ya kuma yi kwanonin zinariya guda ɗari.

9 Sa’an nan ya yi wani shirayi domin firistoci, ya kuma yi wani babban shirayi, ya yi ƙofofi domin shirayun. Ya dalaye ƙyamaren ƙofofin da tagulla.

10 Ya girka kwatarniya a kusurwar kudu maso gabas daura da Haikalin.

11-16 Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah:

ginshiƙi biyu

dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu

siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi

Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan

dakali goma

daro goma

kwatarniya

bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya

kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin haikalin Ubangiji

17 Sarki ya yi zubinsu a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zaretan a wuri mai yumɓu.

18 Haka Sulemanu ya yi kayayyakin nan da yawa ƙwarai, har ba a iya lissafin yawan nauyin tagullar da aka yi amfani da ita ba.

19-22 Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su.

bagade na zinariya

tebur don ajiye gurasar ajiyewa

alkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsara

furanni

fitilu

arautaki

hantsuka

daruna

cokula

farantan wuta

ƙofofi na can ciki

ƙofofi na waje

Categories
2 TAR

2 TAR 5

1 Sulemanu ya kammala dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sa’an nan ya kawo kayayyakin da tsohonsa Dawuda ya riga ya keɓe, wato azurfa da zinariya, da dukan kayan girke-girke, da tasoshi, ya ajiye su a taskokin Haikalin Allah.

Sulemanu Ya Kawo Akwatin Alkawari a Haikali

2 Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra’ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama’ar Isra’ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.

3 Sai dukan mutanen Isra’ila suka hallara a gaban sarki, a wurin bikin, a wata na bakwai ke nan.

4 Sa’an nan dukan dattawan Isra’ila suka zo, Lawiyawa kuwa suka ɗauko akwatin.

5 Suka kuma kawo akwatin, da alfarwa ta taruwa, da dukan tsarkakakkun kayayyakin da suke cikin alfarwar. Lawiyawa da firistoci ne suka kawo su.

6 Sarki Sulemanu da dukan taron mutanen Isra’ila waɗanda suka hallara a gaban akwatin suka yi ta miƙa hadayun tumaki da bijimai masu yawan gaske, har ba su ƙidayuwa.

7 Sa’an nan firistoci suka shigar da akwatin alkawari na Ubangiji a wurinsa, wato a Wuri Mafi Tsarki na cikin Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.

8 Gama kerubobin sun miƙe fikafikansu bisa a daidai wurin da akwatin yake, wato kerubobin sun yi wa akwatin da sandunansa kamar rumfa ke nan.

9 Sandunan akwatin dogaye ne ƙwarai, har ana ganin kawunansu a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki. Amma daga waje ba a iya ganinsu. Suna a wannan wuri har yau.

10 Ba kome cikin akwatin sai alluna biyu waɗanda Musa ya sa a ciki sa’ad da suke a Horeb. A Horeb ne Ubangiji ya ƙulla alkawarin da mutanen Isra’ila, sa’ad da suka fito daga Masar.

Ɗaukakar Ubangiji

11 Firistocin suka fito daga Wuri Mai Tsarki na Haikalin Allah, gama dukan firistocin da suka hallara, sun tsarkake kansu ba tare da kula da bambancin matsayi ba.

12 Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da ‘ya’yansu maza da ‘yan’uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su.

13 Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa’ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa,

“Yabo ya tabbata ga Ubangiji

Gama shi nagari ne,

Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.”

Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije,

14 har ma firistoci ba su iya tsayawa su ci gaba da hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Allah.

Categories
2 TAR

2 TAR 6

Maganar Sulemanu ga Mutane

1 Sulemanu ya ce,

“Ubangiji ya riga ya faɗa zai zauna a cikin girgije mai duhu.

2 Yanzu kuwa na gina maka ƙasaitaccen ɗaki,

Na gina maka wurin da za ka zauna har abada.”

3 Sa’an nan sarki ya juya, ya dudduba, ya sa wa dukan taron jama’ar Isra’ila albarka, dukansu kuwa suka tsaya.

4 Sai ya ce, “Ubangiji Maɗaukaki ne, Allah na Isra’ila wanda ya yi wa tsohona Dawuda alkawari, ga shi kuwa ya cika shi, gama ya ce,

5 ‘Tun daga ranar da na fito da jama’ata daga ƙasar Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin dukan kabilan Isra’ila ba, inda zan gina wurin da sunana zai kasance, ban kuma zaɓi wani mutum da zai shugabanci jama’ata Isra’ila ba.

6 Amma na zaɓi Urushalima domin sunana ya kasance a wurin, na kuma zaɓi Dawuda ya zama shugaban jama’ata Isra’ila.’

7 “Ya zama kuwa tsohona Dawuda ya yi niyyar gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

8 Amma Ubangiji ya ce wa ubana Dawuda, ya kyauta, tun da yake ya yi niyya a zuciyarsa zai gina ɗaki saboda sunansa.

9 Duk da haka, ba shi zai gina Haikalin ba, ɗansa wanda za a haifa masa, shi ne zai gina Haikalin domin sunansa.

10 “Yanzu fa Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na gāji matsayin ubana Dawuda, na kuwa hau gadon sarautar Isra’ila, yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuwa gina Haikali domin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

11 A can na ajiye akwati inda aka sa alkawarin da Ubangiji ya yi wa jama’ar Isra’ila.”

Addu’ar Sulemanu

12 Sulemanu ya miƙe a gaban bagaden Ubangiji a idon dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa.

13 Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama’ar Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama,

14 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ba wani Allah kamarka a sama ko a duniya, wanda yake cika alkawari, kana nuna madawwamiyar ƙauna ga bayinka masu tafiya a gabanka da zuciya ɗaya.

15 Kai ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka, tsohona Dawuda. Abin da ka faɗa ka kuma aikata.

16 Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra’ila ba, in dai ‘ya’yanka maza za su lura da al’amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari’ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’

17 Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.

18 “Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.

19 Duk da haka ka kula da addu’ar bawanka da roƙe-roƙensa. Ya Ubangiji Allahna, ka kasa kunne ga kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka.

20 Ka dubi wajen Haikalin nan dare da rana, wurin da ka yi alkawari za ka sa sunanka, ka kasa kunne ga addu’ar da bawanka zai yi wajen wannan wuri,

21 ka ji roƙe-roƙen bawanka da na jama’ar Isra’ila, sa’ad da suke addu’a suna fuskantar wannan wuri, ka ji daga wurin da kake zaune a Sama, sa’ad da ka ji, ka gafarta.

22 “Idan wani ya yi wa maƙwabcinsa laifi, har aka sa shi ya rantse, ya kuwa zo ya rantse a gaban bagaden a wannan Haikali,

23 sai ka ji ka yi wa bayinka shari’a daga Sama, ka hukunta wa mugun, ka ɗora masa alhakinsa, ka baratar da adalin, ka ba shi sakayyar adalcinsa.

24 “Idan abokan gāba sun kori jama’arka, wato Isra’ila, saboda laifin da suka yi maka, sa’an nan suka juyo suka shaida sunanka, suka yi addu’a, suka yi roƙo a gabanka a wannan Haikali,

25 sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin jama’arka Isra’ila, ka komo da su ƙasar da ka ba su, su da kakanninsu.

26 “Sa’ad da aka kulle sammai, ba ruwan sama saboda sun yi maka zunubi, sa’an nan suka fuskanci wurin nan suka yi addu’a, suka shaida sunanka, suka juyo suka daina zunubinsu a sa’ad da ka hukunta su,

27 sai ka ji daga Sama ka gafarta zunubin bayinka, wato jama’arka Isra’ila, lokacin da ka koya musu kyakkyawar hanya da za su bi. Sai ka sa a yi ruwa a ƙasarka, wadda ka ba jama’arka gādo.

28 “Idan ana yunwa a ƙasar, ko annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fārā, ko gamzari, ko da maƙiyansu za su kewaye biranensu da yaƙi, ko kowace irin annoba, da kowace irin cuta da take akwai,

29 kowace irin addu’a, kowane irin roƙo da kowane mutum, ko jama’ar Isra’ila suka yi, ko wannensu yana sane da irin wahalarsa, da baƙin cikinsa, ya kuwa ɗaga hannunsa wajen wannan Haikali,

30 sa’an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al’amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane,

31 don su yi tsoronka su yi tafiya bisa ga dokokinka muddin ransu, a ƙasar da ka ba kakanninmu.

32 “Haka kuma baƙo wanda ba cikin jama’arka Isra’ila yake ba, idan ya taho daga wata ƙasa mai nisa saboda girman sunanka da ƙarfin ikonka, in ya zo ya yi sujada, yana fuskantar Haikalin nan,

33 ka ji daga Sama wurin zamanka, ka kuwa aikata bisa ga dukan irin roƙon da baƙon ya yi gare ka. Domin ta haka sauran al’umman duniya za su san sunanka, su kuma yi tsoronka, yadda jama’arka Isra’ila suke yi, za su kuma sani cewa wannan Haikali da na gina, ana kiransa da sunanka.

34 “Sa’ad da jama’arka za su fita don yin yaƙi da magabtansu, duk dai ko ta ina ne za ka aike su, in sun yi addu’a gare ka, suna fuskantar wannan birni wanda kai ka zaɓa, da Haikalin nan da na gina saboda sunanka,

35 sai ka ji addu’arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, ka biya muradinsu.

36 “Sa’ad da suka yi maka zunubi (gama ba wani ɗan adam da ba ya yin zunubi), ka kuwa yi fushi da su, har ka bashe su a hannun magabtansu, magabtansu suka kakkama su suka kai wata ƙasa ta nesa ko ta kusa,

37 duk da haka idan sun yi niyya a ransu a can ƙasar da aka kai su baƙunta, suka tuba, suka roƙe ka a can ƙasar baƙunci tasu, suna cewa, ‘Mun yi zunubi, mun aikata laifi, mun kuma yi mugunta,’

38 in sun tuba da zuciya ɗaya, a ƙasar da aka kai su, in sun fuskanci ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, suka yi addu’a, suna kuma fuskantar Haikalin nan da na gina domin sunanka,

39 sai ka ji addu’arsu da roƙe-roƙensu, daga wurin zamanka a Sama, ka sa su yi nasara, ka biya musu muradinsu, ka gafarta wa jama’arka waɗanda suka yi maka zunubi.

40 “Yanzu fa, ya Allahna, ina roƙonka, ka buɗe idanunka, ka kasa kunnuwanka, ka saurari addu’ar da ake yi a wannan wuri.

41 Yanzu fa, ya Ubangiji ka tashi ka tafi wurin hutawarka, kai da akwatin ikonka. Ya Ubangiji Allah ka yi wa firistocinka sutura da cetonka, adalanka kuma su yi farin ciki da nagartarka.

42 Ya Ubangiji Allah kada ka juya baya ga keɓaɓɓenka, ka tuna da madawwamiyar ƙaunarka ga bawanka Dawuda.”

Categories
2 TAR

2 TAR 7

Ƙeɓewar Haikali

1 Sa’ad da Sulemanu ya gama yin addu’arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin.

2 Firistoci ba su iya shiga Haikalin Ubangiji ba saboda darajar Ubangiji ta cika Haikalin.

3 Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wuta ta sauko daga sama, ɗaukakar Ubangiji kuma na cike da Haikalin, sai suka sunkuyar da kansu ƙasa, suka yi sujada, suka yabi Ubangiji, saboda nagarinsa da madawwamiyar ƙaunarsa.

4 Sa’an nan sarki da dukan jama’a suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji.

5 Sarki Sulemanu kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000), da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki tare da dukan jama’a suka keɓe Haikalin Allah.

6 Sai firistoci suka tsaya a matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a nasu matsayi riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji, gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce har abada. A duk lokacin da Dawuda zai yabi Ubangiji tare da su, sai firistoci waɗanda suke daura da su su busa ƙaho, sa’an nan sai dukan Isra’ilawa su miƙe tsaye.

7 Sa’an nan Sulemanu ya tsarkake tsakiyar filin da yake a gaban Haikalin Ubangiji, gama a wurin ne ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayu domin salama, saboda bagaden tagulla wanda Sulemanu ya yi bai iya ɗaukar hadayu domin ƙonawa, da ta gari, da ta kitse ba.

8 A wannan lokaci, Sulemanu ya yi biki a wurin har kwana bakwai, tare da dukan Isra’ilawa, da waɗanda suka zo tun daga ƙofar Hamat, har zuwa rafin Masar, taron kuwa mai girma ne ƙwarai.

9 A rana ta takwas kuwa suka yi wani muhimmin taro, domin su keɓe bagaden. Sun yi kwana bakwai suna yin bikin.

10 A ran ashirin da uku ga watan bakwai, sai sarki ya sallami jama’a su koma gidajensu, suna ta murna da farin ciki a zuciyarsu saboda alherin da Ubangiji ya nuna wa Dawuda, da Sulemanu, da kuma jama’arsa Isra’ila.

Ubangiji Ya Sāke Bayyana ga Sulemanu

11 Haka kuwa Sulemanu ya gama Haikalin Ubangiji da fādar sarki. Ya fa yi nasara cikin dukan irin abin da ya yi niyya game da Haikalin Ubangiji da fādarsa.

12 Sa’an nan Ubangiji ya bayyana ga Sulemanu da dare, ya ce masa, “Na ji addu’arka, na kuwa zaɓi wannan wuri domin kaina, domin ya zama Haikalin miƙa hadaya.

13 Har idan na kulle sammai yadda ba za a yi ruwan sama ba, ko kuma in umarci fara su cinye ƙasar, ko kuwa in aiko da annoba cikin jama’ata,

14 in jama’ata waɗanda ake kiransu da sunana za su yi tawali’u, su yi addu’a, su nemi fuskata, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa’an nan sai in ji su daga Sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da ƙasarsu.

15 Yanzu idanuna za su kasance a buɗe, kunnuwana kuma za su saurari addu’ar da za a yi a wannan wuri.

16 Yanzu fa na riga na zaɓi wannan Haikali, na kuwa keɓe shi domin sunana ya kasance a wurin har abada. Idanuna da zuciyata kuma za su kasance a wurin kullayaumin.

17 Amma kai, idan za ka yi zamanka a gabana kamar yadda tsohonka Dawuda ya yi, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da na umarce ka, ka kiyaye dokokina da farillaina,

18 to, zan kafa gadon sarautarka, yadda na alkawarta wa tsohonka Dawuda, cewa ba za a rasa mutumin da zai yi mulkin Isra’ila ba.

19 Amma idan ka juya, ka bar dokokina da umarnaina waɗanda na sa a gabanka, har ka shiga bautar gumaka kana musu sujada,

20 to, sai in tumɓuke ka daga ƙasata wadda na ba ka, wannan Haikali kuma wanda na riga na keɓe domin sunana, zan kawar da shi daga fuskata, zan kuwa maishe shi abin karin magana, abin raini ga dukan sauran al’umma.

21 “Haikali kuwa, wanda aka ɗaukaka, duk mai wucewa zai yi mamaki ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa wannan ƙasa da wannan Haikali haka?’

22 “Sa’an nan kuma za su ce, ‘Saboda sun rabu da Ubangiji, Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga ƙasar Masar, amma suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, saboda haka ne ya aukar musu da duk wannan bala’i.’ ”

Categories
2 TAR

2 TAR 8

Waɗansu Ayyukan Sulemanu

1 A ƙarshen shekara ashirin waɗanda Sulemanu ya yi yana gina Haikalin Ubangiji da fādarsa,

2 sa’an nan ya sāke giggina biranen da Hiram ya ba shi, ya zaunar da Isra’ilawa a cikinsu.

3 Sai Sulemanu ya tafi ya ci Hamat-zoba da yaƙi.

4 Sa’an nan ya gina Tadmor a jeji, a Hamat kuwa ya gina biranen ajiya.

5 Ya kuma gina Bet-horon ta kan tudu da Bet-horon ta kwari, birane masu kagara kuwa ya gina musu garu, da ƙofofi, da ƙyamare,

6 da kuma Ba’alat da dukan biranen ajiya waɗanda yake da su, da birane don karusansa, da birane don mahayan dawakansa, ya gina dukan abin da yake bukata a Urushalima, da Lebanon, da a dukan ƙasashen da suke cikin mulkinsa.

7 Dukan jama’ar da suka ragu a ƙasar, wato Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, waɗanda Isra’ilawa ba su hallaka ba,

8 daga cikin zuriyarsu waɗanda suka ragu a ƙasar a bayansu, waɗanda Isra’ilawa ba su hallaka ba, su ne Sulemanu ya tilasta su biya gandu, haka kuwa suke har wa yau.

9 Amma Sulemanu bai bautar da kowa daga cikin mutanen Isra’ila ba, su ne mayaƙansa, da shugabannin yaƙi, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.

10 Manyan shugabanni na sarki Sulemanu, mutum ɗari biyu ne da hamsin waɗanda suke iko da jama’a.

11 Sulemanu kuwa ya kawo ‘yar Fir’auna daga birnin Dawuda zuwa gidan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za ta zauna a gidan Dawuda, Sarkin Isra’ilawa ba, saboda duk wuraren da akwatin Ubangiji ya shiga sun tsarkaka.”

12 Sai Sulemanu ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji a gaban shirayi.

13 Sulemanu ya yi bisa ga abin da aka wajabta a yi kowace rana, bisa ga umarnin Musa a miƙa hadayu domin ranakun Asabar, da na amaryar wata, da kuma lokatan idodi uku na shekara, wato idin abinci marar yisti, da idin makonni, da na bukkoki.

14 Bisa ga ka’idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.

15 Firistoci da Lawiyawa kuwa, ba su kauce wa umarnin sarki a kan kowane al’amari ba, ko a kan sha’anin taskoki.

16 Haka Sulemanu ya kammala aikinsa, da aka aza harsashin gina Haikalin Ubangiji, har zuwa ran da aka gama. Haka kuwa aka kammala aikin Haikalin Ubangiji.

17 Sai Sulemanu ya tafi Eziyon-geber da Elat da suke a gaɓar teku a ƙasar Edom.

18 Hiram kuwa ya aika wa Sulemanu jiragen ruwa tare da barori waɗanda suka saba da sha’ani a teku. Sai barorin tare da barorin Sulemanu, suka tafi Ofir, suka ɗauko zinariya talanti ɗari huɗu da hamsin, suka kawo wa sarki Sulemanu.

Categories
2 TAR

2 TAR 9

Sarauniyar Sheba ta Ziyarci Sulemanu

1 Sa’ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da ‘yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa’ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta.

2 Sulemanu kuwa ya amsa dukan tambayoyin da ta yi masa, ba wani abu da yake ɓoye ga Sulemanu wanda ya kāsa bayyana mata.

3 Sa’ad da Sarauniyar Sheba ta ga hikimar Sulemanu, da gidan da ya gina,

4 da irin abincin da yake kan tebur ɗinsa da irin zaman manyan mutanensa, da barorin da yake yi masa hidima, da irin tufafinsu, da masu ba da abin sha, da irin tufafinsu, ta kuma ga hadayun ƙonawa da yake miƙawa a Haikalin Ubangiji, sai ta ji ba ta da sauran kuzari.

5 Sarauniya ta ce wa sarkin, “Ashe, gaskiya ce, labarinka da na ji a ƙasata a kan al’amuranka da hikimarka.

6 Amma dā ban gaskata labarinsu ba, sai da na zo na gani da idona, ashe, ko rabin yawan hikimarka ma ba a faɗa mini ba. Ashe, duk labarin da aka faɗa mini, ka zarce haka ƙwarai.

7 Masu farin ciki ne mutanenka, da barorinka waɗanda suke yi maka hidima kullayaumin, gama kullum suna jin hikimarka.

8 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra’ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.”

9 Sa’an nan kuma ta ba sarki zinariya talanti ɗari da ashirin, da kayan yaji masu yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Irin kayan yajin da Sarauniyar Sheba ta ba sarki Sulemanu ba irinsa.

10 Bayan haka kuma barorin Hiram tare da barorin Sulemanu waɗanda suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itatuwan algum da duwatsu masu daraja.

11 Da itatuwan algum ɗin, sarki ya yi matakan Haikalin Ubangiji da na fādar sarki, ya kuma yi garayu, da molaye saboda mawaƙa. Ba a taɓa ganin irinsu a ƙasar Yahuza ba.

12 Sarki Sulemanu kuwa ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ranta take bukata, da iyakar abin da take so, banda abin da ta kawo wa sarki. Sa’an nan ta koma ƙasarta, ita da barorinta.

Dukiyar Sulemanu da Shahararsa

13 Yawan zinariya da Sulemanu yake samu a shekara guda, talanti ɗari shida da sittin da shida,

14 banda wadda ‘yan kasuwa da fatake sukan kawo masa. Dukan sarakunan Arabiya da masu mulkin ƙasar kuma sun kawo wa Sulemanu zinariya da azurfa.

15 Sai Sulemanu sarki ya ƙera manyan garkuwoyi guda ɗari biyu na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari shida ne na zinariya.

16 Ya kuma ƙera garkuwa ɗari uku ƙanana na zinariya, kowace garkuwa nauyinta shekel ɗari uku ne. Sarki fa ya ajiye su a gidan da aka gina da katakai daga Lebanon.

17 Sarki ya yi babban gadon sarauta na hauren giwa, ya dalaye shi da zinariya.

18 Gadon sarautar yana da matakai da ‘yar kujerar zinariya ta ɗora ƙafa haɗe da gadon. A kowane gefen gadon an yi wurin ɗora hannu, akwai kuma siffar zaki a tsaye kusa da kowane wurin ɗora hannun.

19 Akwai kuma siffofin zaki goma sha biyu, zaki biyu a kowane mataki, gefe da gefe. Ba ma sarautar da aka taɓa yi irin wannan.

20 Dukan tasoshi da finjalai na sarki Sulemanu, da zinariya tsantsa aka yi su. Haka nan kuma dukan tasoshi da finjalai da suke cikin gidan da aka gina da katakai daga Lebanon, na zinariya ne tsantsa. Ba a mai da azurfa a bakin kome ba a zamanin Sulemanu.

21 Sau ɗaya a shekaru uku, sarki yakan aika da jiragen ruwa zuwa Tarshish tare da barorin Hiram, su kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da manyan birai, da ɗawisu.

22 Sarki Sulemanu ya fi dukan sarakunan duniya dukiya da hikima.

23 Sarakunan duniya duka suna nema su sadu da Sulemanu, don su ji irin hikimar da Allah ya ba shi.

24 Kowannensu yakan kawo masa kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai, masu yawan gaske a kowace shekara.

25 Sulemanu kuwa yana da ɗakunan dawakai da na karusai dubu huɗu (4,000), yana da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000) waɗanda suke zaune a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da sarki.

26 Ya mallaki dukan sarakuna tun daga Yufiretis, har zuwa ƙasar Filistiyawa har kuma zuwa kan iyakar Masar.

27 Sarki ya sa azurfa ta gama gari, kamar duwatsu a Urushalima, ya kuma sa itatuwan al’ul su yalwata kamar itatuwan ɓaure a Shefela.

28 Dawakan Sulemanu, sayo su aka yi daga Masar, da dukan sauran ƙasashe.

Rasuwar Sulemanu

29 Sauran ayyukan Sulemanu daga farko har ƙarshe an rubuta su a tarihin annabi Natan. An kuma rubuta su a annabcin Ahaija Bashilone, da kuma a wahayin Iddo maigani, game da Yerobowam ɗan Nebat.

30 A Urushalima, Sulemanu ya yi shekara arba’in yana mulkin dukan Isra’ila.

31 Sulemanu ya rasu aka binne shi tare da kakanninsa a birnin tsohonsa Dawuda, Rehobowam ɗansa shi ya gāje shi.

Categories
2 TAR

2 TAR 10

Kabilan Arewa sun yi Tawaye

1 Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ilawa sun tafi don su naɗa shi sarki.

2 Da Yerobowam ɗan Nebat, ya ji wannan labari (gama a Masar yake sa’ad da ya guje wa sarki Sulemanu), Yerobowam kuwa ya komo daga Masar.

3 Aka aika a kira shi, sai Yerobowam da dukan Isra’ilawa, suka je wurin Rehobowam suka ce,

4 “Tsohonka ya tsananta mana, yanzu sai ka sawwaƙa mana irin tsananin da muka sha daga wurin tsohonka, da irin tilastawar da ya yi mana, sa’an nan sai mu bauta maka.”

5 Rehobowam kuwa ya ce musu, “Ku komo bayan kwana uku.” Sai jama’a suka tafi.

6 Rehobowam ya nemi shawara a gun dattawan da suke tare da tsohonsa Sulemanu, sa’ad da yake da rai, ya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa jama’ar nan?”

7 Su kuwa suka ce masa, “Idan za ka nuna wa jama’ar nan alheri, ka daɗaɗa musu rai, ka kuma yi musu magana mai daɗi, za su zama barorinka har abada.”

8 Amma ya ƙi yarda da shawarar da dattawan suka ba shi, ya nemi shawara daga wurin matasa waɗanda suka girma tare, masu yi masa hidima.

9 Ya ce musu, “Wace irin shawara za ku bayar wadda za mu amsa wa jama’an nan da suka ce mini, ‘Ka sawwaƙa mana wahalar da muka sha daga wurin tsohonka’?”

10 Sai matasa waɗanda suka girma tare da shi, suka ce masa, “Ga abin da za ka faɗa wa jama’an nan da suka ce maka, tsohonka ya tsananta musu, yanzu sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun ubana kauri!

11 Ubana ya tsananta muku ƙwarai, amma ni zan tsananta muku fiye da shi, ubana ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”

12 Sai Yerobowam tare da dukan jama’a suka koma wurin Rehobowam a rana ta uku, kamar yadda sarki ya faɗa, “Bayan kwana uku ku komo.”

13 Sarki Rehobowam ya amsa musu da kakkausan harshe, gama bai karɓi shawarar dattawan ba.

14 Sarki Rehobowam ya yi aiki da shawarar da matasa suka ba shi, ya ce, “Ubana ya tsananta muku fiye da shi, ya hore ku da bulala, amma ni, da kunama zan hore ku.”

15 Sarki bai kasa kunne ga jama’ar ba, gama wannan al’amari, Allah ne ya aukar da shi, domin ya cika maganar da ya faɗa wa Yerobowam ɗan Nebat, ta bakin Ahaija Bashilone.

16 Da Isra’ilawa duka suka ga sarki bai saurare su ba, jama’ar kuwa suka amsa wa sarkin, suka ce, “Wane rabo muke da shi a wurin Dawuda? Ba mu da gādo a wurin ɗan Yesse. Kowa ya tafi alfarwarsa, ya ku Isra’ilawa. Ku bar Rehobowam ya lura da gidansa.”

Isra’ilawa duka kowa ya tafi alfarwarsa.

17 Amma Rehobowam ya ci gaba da mulki bisa Isra’ilawan da suke a biranen Yahuza.

18 Sai sarki Rehobowam ya aiki Adoniram shugaban aikin dole, jama’ar Isra’ila kuwa suka jejjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sai sarki Rehobowam ya gaggauta ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima.

19 Tun daga wannan lokaci kuwa har zuwa yau, Isra’ilawa suka tayar wa gidan Dawuda.