Categories
2 TAR

2 TAR 11

Annabcin Shemaiya

1 Sa’ad da Rehobowam ya kai Urushalima, sai ya tattara zaɓaɓɓun mayaƙa, mutum dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) daga cikin jama’ar Yahuza da ta Biliyaminu don su yi yaƙi da Isra’ila, su komo wa Rehobowam da mulki.

2 Sai Ubangiji ya yi magana da Shemaiya, mutumin Allah, ya ce,

3 “Ka faɗa wa Rehobowam ɗan Sulemanu, Sarkin Yahuza, da dukan Isra’ilawa da suke a Yahuza da Biliyaminu, ka ce,

4 ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, kada ku yi yaƙi da ‘yan’uwanku, kowa ya komo alfarwarsa, gama wannan al’amari daga gare ni yake.’ ” Suka kuwa ji maganar Ubangiji, suka koma, ba su tafi yaƙi da Yerobowam ba.

Rehobowam Ya Arzuta

5 Rehobowam ya zauna a Urushalima, ya kuwa gina birane masu kagara a Yehuza.

6 Ya gina Baitalami, da Itam, da Tekowa,

7 da Bet-zur, da Soko, da Adullam,

8 da Gat, da Maresha, da Zif,

9 da Adorayim, da Lakish, da Azeka,

10 da Zora, da Ayalon, da Hebron. Waɗannan su ne birane masu kagara a Yahuza da Biliyaminu.

11 Ya kuma ƙara ƙarfin kagaran, ya sa sarakunan yaƙi a cikinsu. Ya tara abinci, da mai, da ruwan inabi a cikinsu.

12 Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen nan, ya ƙara musu ƙarfi ƙwarai. Haka ya riƙe Yahuza da Biliyaminu.

Firistoci da Lawiyawa sun Zo Yahuza

13 Firistoci da Lawiyawa da suke a dukan Isra’ila kuwa suka komo gare shi daga dukan wuraren da suke.

14 Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da ‘ya’yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji.

15 Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.

16 Amma su waɗanda zuciyarsu take ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga kowace kabilar Isra’ila, sukan bi Lawiyawa zuwa Urushalima domin su miƙa hadaya ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.

17 Sai suka ƙarfafa mulkin Yahuza, suka tsare mutuncin Rehobowam ɗan Sulemanu har shekara uku. Suka yi shekara uku suna tafiya a tafarkin Sulemanu.

Iyalin Rehobowam

18 Rehobowam kuwa ya auri Mahalat ‘yar Yeremot ɗan Dawuda, wadda Abihail ‘yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.

19 Mahalat ta haifa masa ‘ya’ya maza, su ne Yewush, da Shemariya, da Zaham.

20 Banda Mahalat kuma, sai ya auri Ma’aka ‘yar Absalom, wadda ta haifa masa Abaija, da Attai, da Ziza, da kuma Shelomit.

21 Rehobowam ya fi ƙaunar Ma’aka, ‘yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. ‘Ya’yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, ‘ya’ya mata kuwa sittin.

22 Sai Rehobowam ya zaɓi Abaija ɗan Ma’aka, ya zama shugaban ‘yan’uwansa, gama nufinsa ya zama sarki.

23 Sai ya yi hikima ya rarraba waɗansu ‘ya’yansa maza ko’ina cikin gundumomin ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, a dukan birane masu kagara, ya tanada musu abinci a yalwace. Ya kuma samo musu mata masu yawan gaske.

Categories
2 TAR

2 TAR 12

Shishak Ya Kai wa Yahuza Yaƙi

1 Da mulkin Rehobowam ya kahu, ya kuma yi ƙarfi, sai Rehobowam da dukan Isra’ilawa tare da shi suka bar bin shari’ar Ubangiji.

2 A shekara ta biyar ta mulkin sarki Rehobowam, Isra’ilawa ba su bi Ubangiji da aminci ba, saboda haka Shishak, Sarkin Masar, ya hauro don ya yi yaƙi da Urushalima.

3 Aka faɗo masa da karusai dubu da ɗari biyu (1,200), da mahayan dawakai mutum dubu sittin (60,000). Mutanen da suka taho tare da sarki Shishak daga Masar, ba a san adadinsu ba, akwai Libiyawa, da Sukkimiyawa, da kuma Habashawa.

4 Ya ci birane masu kagara na Yahuza, har ya dangana da Urushalima.

5 Sai annabi Shemaiya ya zo wurin Rehobowam da sarakunan Yahuza waɗanda suka tattaru a Urushalima saboda Shishak, ya ce musu, “Ubangiji ya ce kun yashe shi, don haka shi ma ya bashe ku a hannun Shishak.”

6 Sai sarakunan Isra’ila tare da sarki Rehobowam, suka ƙasƙantar da kansu, suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”

7 Da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai ya yi magana da Shemaiya cewa, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.

8 Duk da haka fa, za su zama bayin Shishak don su san bautata dabam take da wadda ake yi wa mulkokin ƙasashe.”

9 Sai Shishak Sarkin Masar ya zo ya fāɗa wa Urushalima da yaƙi, ya kuwa kwashe dukiyoyin da suke cikin Haikalin Ubangiji, da na fādar sarki, ya yi musu ƙaƙaf. Ya kuma kwashe garkuwoyi na zinariya, waɗanda Sulemanu ya yi.

10 Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara, masu tsaron gidan sarki.

11 A duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su kawo su, daga baya kuma su maishe su a ɗakin matsaran.

12 Da sarki Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, sai fushin Ubangiji ya huce, don haka bai sa aka hallaka shi ƙaƙaf ba, har ma halin zama a ƙasar Yahuza ya yi kyau.

Mulkin Rehobowam a Taƙaice

13 Sarki Rehobowam kuwa ya kafa mulkinsa sosai a Urushalima, yana da shekara arba’in da ɗaya da haihuwa ya ci sarauta, ya yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila domin ya sa sunansa a wurin. Sunan tsohuwar Rehobowam Na’ama, Ba’ammoniya.

14 Amma ya aikata mugunta domin bai nemi Ubangiji a zuciyarsa ba.

15 Ayyukan Rehobowam, daga farko har zuwa ƙarshe an rubuta su a littafin tarihin annabi Shemaiya, da na Iddo maigani. Kullum yaƙi ne tsakanin Rehobowam da Yerobowam.

16 Rehobowam fa ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda. Abaija ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 TAR

2 TAR 13

Sarki Abaija na Yahuza

1 A shekara ta goma sha takwas ta mulkin sarki Yerobowam, sai Abaija ya ci sarautar Yahuza.

2 Ya yi mulki shekara uku a Urushalima, sunan tsohuwarsa Ma’aka, ‘yar Uriyel na Gibeya.

Sai yaƙi ya ɓarke a tsakanin Abaija da Yerobowam.

3 Abaija ya tafi da rundunar jarumawansa, dubu ɗari huɗu (400,000) zaɓaɓɓun mutane. Yerobowam shi kuma ya jā dāgar yaƙi don ya kara da Abaija, yana da mutum dubu ɗari takwas (800,000), zaɓaɓɓun mayaƙa ƙarfafa.

4 Sai Abaija ya hau kan Dutsen Zemarayim, wanda yake a ƙasar Ifraimu mai tuddai, ya ce, “Ku kasa kunne gare ni, ya Yerobowam da dukanku Isra’ilawa.

5 Ashe, ba ku sani ba, Ubangiji Allah na Isra’ila, ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda, da ‘ya’yansa maza har abada, ta wurin alkawarin gishiri?

6 Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, baran Sulemanu ɗan Dawuda, ya tashi, ya yi wa ɗan ubangidansa tawaye,

7 waɗansu marasa amfani, ‘yan iska, suka taru suka goyi bayansa, suka raina Rehobowam ɗan Sulemanu, saboda a lokacin shi yaro ne, ba shi da ƙarfin zuciya, bai iya tsayayya da su ba.

8 Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun ‘ya’yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku.

9 Ashe, ba ku kori firistocin Ubangiji, ‘ya’yan Haruna, maza, da Lawiyawa ba, kuka yi wa kanku firistoci kamar na al’umman sauran ƙasashe? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don ya tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.

10 “Amma a gare mu, Ubangiji shi ne Allahnmu, ba mu kuwa rabu da shi ba. Muna da firistoci, ‘ya’yan Haruna, maza, masu yi wa Ubangiji hidima, da Lawiyawa masu yi musu hidima.

11 Safe da yamma suna miƙa wa Ubangiji hadayun ƙonawa, da turare mai daɗin ƙanshi, sukan ajiye gurasar ajiyewa a kan tebur ɗin zinariya tsantsa, sukan lura da alkukin zinariya, da kuma fitilunsa kowane maraice, gama muna riƙe da umarnin Ubangiji Allahnmu, amma ku kun rabu da shi.

12 Ga shi kuwa, Allah yana tare da mu, shi ne shugabanmu, firistocinsa kuwa suna da ƙahon da akan busa lokacin yaƙi, don su busa kira na yin yaƙi. Ya ku Isra’ilawa, kada ku yi yaƙi da Ubangiji, Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”

13 Ashe, Yerobowam ya riga ya sa ‘yan kwanto, su yi musu yankan baya. Ƙungiyar mayaƙan Isra’ila tana fuskantar ta Yahuza, ‘yan kwanto kuma suna bayansu.

14 Da Yahuza suka duba, sai ga yaƙi a gabansu da bayansu. Sai suka yi kuka ga Ubangiji, firistoci kuma suka busa ƙaho.

15 Mutanen Yahuza suka yi kūwwar yaƙi. Da suka yi kuwwar yaƙin sai Ubangiji ya sa Yerobowam da dukan jama’ar Isra’ila su gudu a gaban Abaija da Yahuza.

16 Mutanen Isra’ila kuwa suka gudu a gaban Yahuza, Allah ya bashe su a hannunsa.

17 Abaija fa, da jama’arsa suka karkashe su, mugun kisa. Mutum dubu ɗari biyar (500,000) zaɓaɓɓu na Isra’ila, aka karkashe.

18 Haka kuwa aka ci nasara a kan mutanen Isra’ila a wannan lokaci. Mutanen Yahuza sun yi rinjaye saboda sun dogara ga Ubangiji, Allah na kakanninsu.

19 Abaija ya runtumi Yerobowam, ya ƙwace masa waɗansu birane, wato Betel tare da ƙauyukanta, da Yeshana tare da ƙauyukanta, da kuma Efron tare da ƙauyukanta.

20 Mulkin Yerobowam bai ƙara farfaɗowa a zamanin Abaija ba. Ubangiji kuma ya bugi Yerobowam, ya mutu.

21 Amma Abaija ya ƙasaita, ya auro mata goma sha huɗu, ya haifi ‘ya’ya maza ashirin da biyu, da ‘ya’ya mata goma sha shida.

22 Sauran ayyukan Abaija, da al’amuransa, da jawabansa, an rubuta su a littafin tarihin annabi Iddo.

Categories
2 TAR

2 TAR 14

Sarki Asa na Yahuza

1 Sarki Abaija kuwa ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda. Ɗansa Asa shi ya gāji gadon sarautarsa. Ƙasar ta sami sakewa har shekara goma a zamaninsa.

2 Asa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.

3 Ya kawar da baƙin bagadai da masujadai, ya rurrushe ginshiƙai, ya kuma tumɓuke Ashtarot.

4 Ya umarci Yahuza su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kiyaye doka, da umarni.

5 Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagadan ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa.

6 Ya giggina birane masu kagara a Yahuza, gama ƙasar tana zaman lafiya. A waɗannan shekaru bai yi yaƙi da kowa ba, saboda Ubangiji ya kawo masa salama.

7 Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta.

8 Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, ‘yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.

9 Sai Zera mutumin Habasha ya zo da soja zambar dubu (1,000,000) da karusa ɗari uku har Maresha, don ya yi yaƙi da su.

10 Don haka sai Asa ya fito ya gamu da shi, suka kuwa jā dāga a kwarin Zefata a Maresha.

11 Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa’ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama’arka.”

12 Ubangiji kuwa ya fatattaki Habashawa a gaban Asa da Yahuza, Habashawa kuwa suka gudu.

13 Sai Asa da jama’ar da suke tare da shi, suka runtume su har zuwa Gerar. Habashawa suka fāɗi duka, ko ɗaya, ba wanda ya ragu da rai, gama an ragargaza su a gaban Ubangiji da gaban sojojin. Mutane suka kwashe ganima mai yawa gaske.

14 Suka hallaka dukan birane da suke kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka washe dukan biranen, gama biranen suna cike da ganima.

15 Suka kware alfarwan masu kiwon dabbobi, suka kora tumaki, da raƙuma masu yawan gaske. Sa’an nan suka komo Urushalima.

Categories
2 TAR

2 TAR 15

Gyare-gyaren da Asa Ya Yi

1 Ruhun Allah kuwa ya sauko a kan Azariya ɗan Oded,

2 sai ya fita ya taryi Asa, ya ce masa, “Ka ji ni, ya Asa, kai da dukan Yahuza da Biliyaminu, Ubangiji yana tare da ku idan kuna tare da shi. Idan kuwa kun neme shi, za ku same shi, amma idan kun rabu da shi, shi ma zai rabu da ku.

3 Isra’ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari’a.

4 Amma lokacin da suke shan wahala suka juyo ga Ubangiji Allah na Isra’ila, suka neme shi, suka same shi.

5 A waɗancan lokatai, ba salama ga mai fita ko ga mai shiga, gama babban hargitsi ya wahalar da dukan mazaunan ƙasashe.

6 An kacancana su, al’umma tana gāba da al’umma, birni kuma gāba da birni, gama Allah ya yi ta wahalshe su da kowace irin wahala.

7 Amma ku sai ku yi ƙarfin hali, kada ku firgita, gama za a ba ku ladan aikinku.”

8 Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.

9 Sai ya tattara dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, da kuma na Ifraimu, da na Manassa, da na Saminu, waɗanda suke zaman baƙunci tare da su. Da yawa daga cikin Isra’ilawa suka yi ƙaura zuwa wurinsa, sa’ad da suka ga Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.

10 Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta sarautar Asa.

11 A ran nan suka miƙa wa Ubangiji hadayun bijimai ɗari bakwai, da tumaki dubu bakwai (7,000) daga cikin ganimar da suka kwaso.

12 Sai suka ƙulla alkawari, cewa za su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu da dukan zuciyarsu da ransu.

13 Duk wanda kuma bai nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, za a kashe shi, ko yaro ko babba, ko mace ko namiji.

14 Sai suka rantse wa Ubangiji da murya mai ƙarfi, suna sowa, suna busa kakaki da ƙaho.

15 Dukan Yahuza ta yi murna saboda rantsuwar, gama da zuciya ɗaya suka rantse, suka kuwa neme shi da iyakar aniya, sun kuwa same shi. Don haka Allah ya hutasshe su a kowane al’amari.

16 Asa kuma ya tuɓe tsohuwarsa, Ma’aka, daga matsayinta na sarauniya don ta ƙera wata siffa mai banƙyama ta Ashtoret. Sai Asa ya sare siffar nan, ya niƙe ta, ya ƙone a rafin Kidron.

17 Amma ba a kawar da masujadan da yake Isra’ila ba, duk da haka zuciyar Asa sarai take, ba wani aibi duk kwanakinsa.

18 Sai ya shigar da sadakar da shi da tsohonsa suka keɓe don Haikalin Ubangiji, wato azurfa, da zinariya, da kwanoni da tasoshi, da finjalai iri iri.

19 Ba a kuma ƙara yin wani yaƙi ba har shekara ta talatin da biyar ta mulkinsa Asa.

Categories
2 TAR

2 TAR 16

Asa ya Haɗa Kai da Ben-hadad

1 A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, sai Ba’asha, Sarkin Isra’ila, ya haura ya fāɗa wa Yahuza da yaƙi, ya gina Rama don ya hana kowa fita, ko shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.

2 Sa’an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa,

3 “Bari mu haɗa kai, da ni da kai kamar yadda ubana da naka suka yi. Ga shi, na aika maka da azurfa da zinariya. Ka tafi ka warware haɗa kan da yake tsakaninka da Ba’asha, Sarkin Isra’ila, don ya janye ya rabu da ni.”

4 Ben-hadad kuwa ya kasa kunne ga sarki Asa, ya aika da shugabannin rundunan sojojinsa suka yi yaƙi da biranen Isra’ila. Suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma’aka, da dukan biranen ajiya na Naftali.

5 Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina gina Rama, ya bar aikin da yake yi.

6 Sa’an nan sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuza, suka kwashe duwatsun da katakan da Ba’asha yake gina Rama da su, ya gina Geba da Mizfa da su.

Annabi Hanani

7 A lokacin nan sai Hanani, maigani, ya zo wurin Asa, Sarkin Yahuza, ya ce masa, “Da yake ka dogara ga Sarkin Suriya, maimakon ka dogara ga Ubangiji Allahnka, shi ya sa rundunar sojojin Sarkin Suriya ta kuɓuta daga hannunka.

8 Ai, Habashawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da karusai da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, sai ya bashe su a hannunka.

9 Idon Ubangiji fa, yana kai da komowa ko’ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya. Ka yi wauta a cikin wannan al’amari. Tun daga yanzu har zuwa nan gaba za ka yi ta fama da yaƙoƙi.”

10 Sai Asa ya yi fushi da maiganin, ya sa shi a kurkuku saboda maganar da ya yi masa, gama ya husata da shi ƙwarai. A wannan lokaci kuma sai Asa ya ƙuntata wa waɗansu daga cikin jama’a.

Ƙarshen Mulkin Asa

11 Ayyukan Asa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra’ila.

12 A shekara ta talatin da tara ta mulkin Asa, sai wani ciwo ya kama shi a ƙafa. Ciwon kuwa ya tsananta ƙwarai, duk da haka Asa bai nemi taimakon Ubangiji ba, sai na magori.

13 Asa fa ya rasu bayan shekara biyu da ciwon, a shekara ta arba’in da ɗaya ta mulkinsa.

14 Aka binne shi a kabarin da shi da kansa ya haƙa a birnin Dawuda. Aka sa shi a makara wadda aka cika da kayan ƙanshi da na turare yadda gwanayen aikin turare suka shirya, suka hura babbar wuta don su darajanta shi.

Categories
2 TAR

2 TAR 17

Mulkin Yehoshafat ya Kahu

1 Yehoshafat ɗansa kuwa ya gāji gadon sarautarsa, ya kahu sosai gāba da Isra’ila.

2 Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi.

3 Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat saboda ya bi halin tsohonsa da ya yi da fari, bai kuwa nemi Ba’al ba.

4 Ya nemi Allah na ubansa, ya bi umarnansa. Bai bi halin Isra’ila ba.

5 Saboda haka ne Ubangiji ya ba shi ikon riƙon wannan mulki. Yahuza duka kuwa ta kawo wa Yehoshafat haraji, ya kuwa zama riƙaƙƙen mai dukiya, wanda kuma ake girmamawa.

6 Zuciyarsa ta ƙarfafa cikin al’amuran Ubangiji. Ya kawar da masujadai, da Ashtarot daga ƙasar Yahuza.

7 A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya aika da ma’aikatansa, su Ben-hail, da Obadiya, da Zakariya, da Netanel, da kuma Mikaiya don su yi koyarwa a biranen Yahuza.

8 Tare da su kuma akwai Lawiyawa, da Shemaiya, da Netaniya, da Zabadiya, da Asahel, da Shemiramot, da Jonatan, da Adonaija, da Tobiya, da Tob-adonaija, tare da waɗannan Lawiyawa akwai firistoci, Elishama da Yehoram.

9 Suka koyar a Yahuza, suna tare da Littafin Shari’ar Ubangiji, wato Attaura. Suka shiga ko’ina a biranen Yahuza suka koyar da jama’a.

Gawurtar Yehoshafat

10 Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashen da suke kewaye da Yahuza, har ba su iya fāɗa wa Yehoshafat da yaƙi ba.

11 Sai waɗansu daga cikin Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa domin haraji. Larabawa ma suka kawo masa raguna dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700), da bunsurai dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700).

12 Yehoshafat ya daɗa ƙasaita, ya giggina kagarai, da biranen ajiya a Yahuza.

13 Yana kuwa da manya manyan wuraren ajiya a biranen Yahuza.

Yana kuma da gwarzayen sojoji masu yawa a Urushalima.

14 Ga jimillar sojojin bisa ga gidajen kakanninsu. Na Yahuza mai shugabannin dubu dubu, shugaba Adana yana shugabancin sojoji dubu ɗari uku (300,000) gwarzaye.

15 Mai bi masa, sai shugaba Yehohanan yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000).

16 Mai biye da Yehohanan kuma shi ne shugaba Amasiya, ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa don bauta wa Ubangiji, shi kuma yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000) gwarzaye.

17 Na Biliyaminu kuma sarkin yaƙi shi ne Eliyada, gwarzo ne, yana shugabancin sojoji dubu ɗari biyu (200,000), ‘yan baka da garkuwa.

18 Na biye da Eliyada kuma shi ne shugaba Yehozabad wanda yake da sojoji dubu ɗari da dubu tamanin (180,000) shirayayyu don gabza yaƙi.

19 Waɗannan suke yi wa sarki hidima, banda waɗanda sarki ya sa a birane masu kagara ko’ina a Yahuza.

Categories
2 TAR

2 TAR 18

Annabi Mikaiya Ya Gargaɗi Ahab

1 Yehoshafat ya arzuta, ya kuma sami ɗaukaka sai ya yi ma’amala da Ahab ta wurin aurayya.

2 Bayan ‘yan shekaru sai ya kai wa Ahab ziyara a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki masu yawan gaske, da bijimai da yawa, domin Yehoshafat da mutanen da suke tare da shi. Ahab ya rinjaye shi don su fāɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi.

3 Sai Ahab, Sarkin Isra’ila, ya ce wa Yehoshafat, Sarkin Yahuza, “Za ka tafi tare da ni zuwa Ramot-gileyad?”

Sai ya amsa, ya ce, “Ni ma kamarka ne, jama’ata kuma kamar jama’arka ce, za mu je yaƙin tare da kai.”

4 Yehoshafat kuma ya ce wa Sarkin Isra’ila, “Sai ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”

5 Ahab kuwa ya tattara annabawa, mutum ɗari huɗu, ya ce musu, “Mu je mu faɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi, ko in haƙura?”

Sai suka ce, “Ka tafi, gama Allah zai ba da ita a hannun sarki.”

6 Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji a nan wanda za mu tambaye shi kuma?”

7 Sai Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Akwai sauran mutum guda wanda za mu iya neman nufin Ubangiji daga gare shi, shi ne Mikaiya, ɗan Imla, amma na ƙi shi saboda ba ya yin annabcin kirki a kaina, sai dai na rashin alheri kullum.”

Amma Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”

8 Sa’an nan Sarkin Isra’ila ya kira wani jarumi ya ce masa, “Maza ka kawo Mikaiya ɗan Imla.”

9 A sa’an nan Sarkin Isra’ila, da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune kowa a gadon sarautarsa, kowane ya caɓa ado, suna kuwa zaune a filin da yake ƙofar Samariya. Dukan annabawa kuwa suna ta yin annabci a gabansu.

10 Sai Zadakiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Suriyawa har su hallaka!’ ”

11 Dukan annabawa kuma suka yi annabci, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot-gileyad ka ci nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannun sarki.”

12 Jarumin fa da ya je ya kira Mikaiya ɗin, ya ce masa, “Ka kula fa, dukan maganganun da annabawa suke yi, sun yi wa sarki daɗi. Don haka kai ma ka yi maganar da za ta gamshi sarki kamar yadda suka yi.”

13 Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji abin da Allahna ya faɗa mini, shi zan faɗa.”

14 Da Mikaiya ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu haura zuwa Ramot-gileyad mu fāɗa mata da yaƙi, ko in haƙura?”

Mikaiya kuwa ya amsa, ya ce, “Ka haura, gama za ka ci nasara, gama za a bashe su a hannunka.”

15 Amma sarki ya ce masa, “Har sau nawa zan rantsar da kai don kada ka faɗa mini kome, sai gaskiya da sunan Ubangiji?”

16 Mikaiya kuwa ya ce, “Ina ganin dukan Isra’ilawa a warwatse bisa tsaunuka, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Ubangiji kuma ya ce, ‘Waɗannan ba su da makiyayi, bari dukansu, kowa ya koma gidansa da salama.’ ”

17 Sarkin Isra’ila fa ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, cewa ba zai yi annabcin alheri game da ni ba, sai na rashin alheri?”

18 Sai Mikaiya ya ce, “Ji maganar Ubangiji, na ga Ubangiji yana zaune a bisa kursiyinsa, dukan rundunan sama suna tsaye dama da shi da hagu da shi.

19 Sai Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab, Sarkin Isra’ila, don ya haura zuwa Ramot-gileyad ya fāɗi?’ Sai wannan ya faɗi abu kaza, wancan kuma ya faɗi abu kaza.

20 Sai wani ruhu ya zo ya tsaya a gaban Ubangiji, ya ce, ‘Ni zan ruɗe shi.’ Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Ta ƙaƙa?’

21 Sai ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakin dukan annabawansa.’ Sa’an nan Ubangiji ya ce, ‘To, za ka ruɗe shi har ka yi nasara. Je ka, ka yi haka nan.’

22 “Saboda haka Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan annabawanka, gama Ubangiji ya faɗa, masifa za ta same ka.”

23 Sai Zadakiya ɗan Kena’ana, ya matso ya mari Mikaiya a kumatu ya ce, “Ta wace hanya ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai.”

24 Mikaiya kuwa ya ce, “Za ka gani a ranar da ka shiga ƙuryar ɗaki na can ciki don ɓuya.”

25 Sai Sarkin Isra’ila ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku komar da shi wurin Amon mai mulkin birnin, da yarima Yowash.

26 Ku ce, ‘Sarki ya ce ku sa wannan mutum a kurkuku, ku ciyar da shi da ɗan abinci da ruwa kaɗan har in komo lafiya.’ ”

27 Sai Mikaiya ya ce, “Idan har ka komo lafiya, wato Ubangiji bai yi magana da ni ba ke nan.” Sai ya ce, “Ku ji, ya ku jama’a duka.”

Mutuwar Ahab

28 Sarkin Isra’ila fa, da Yehoshafat Sarkin Yahuza, suka haura zuwa Ramot-gileyad.

29 Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama, in shiga yaƙi, amma kai, sai ka sa rigunanka.” Sarkin Isra’ila kuwa ya ɓad da kama, suka shiga yaƙi.

30 Sarkin Suriya ya umarci shugabannin karusansa, ya ce, “Kada ku yi yaƙi da yaro ko babba, sai dai da Sarkin Isra’ila, shi kaɗai.”

31 Sa’ad da shugabannin karusai suka ga Yehoshafat, suka ce, “Wannan ne Sarkin Isra’ila,” sai suka juya suka yi yaƙi da shi. Amma Yehoshafat ya yi kururuwa, Ubangiji Allah ya kuɓutar da shi, Allah kuwa ya kawar da su daga gare shi.

32 Da shugabannin karusai suka ga, ashe, ba Sarkin Isra’ila ba ne, sai suka daina binsa suka juyo.

33 Amma wani mutum ya harba kibiya haka kawai, ya sami Sarkin Isra’ila a mahaɗin kafaɗa. Sai sarkin ya ce wa wanda yake korar karusarsa, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin, gama an yi mini rauni.”

34 Ran nan yaƙin ya tsananta, Sarkin Isra’ila kuma ya jingina a cikin karusarsa, yana fuskantar Suriyawa har maraice, rana na fāɗuwa yana rasuwa.

Categories
2 TAR

2 TAR 19

Annabi Yehu Ya Tsauta wa Yehoshafat

1 Yehoshafat Sarkin Yahuza ya koma gidansa a Urushalima lafiya.

2 Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka.

3 Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da gumakan Ashtarot daga ƙasar, ka sa zuciyarka ga neman Allah.”

Yehoshafat Ya Zaɓi Alƙalai

4 Yehoshafat ya yi zamansa a Urushalima, ya sāke shiga jama’a, tun daga Biyer-sheba har zuwa ƙasar tuddai ta Ifraimu, ya komar da su zuwa wurin Ubangiji, Allah na kakanninsu.

5 Sai ya naɗa alƙalai a ƙasar, a dukan biranen Yahuza masu kagara, birni birni.

6 Sai ya ce wa alƙalan, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.

7 Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”

8 Yehoshafat kuma ya naɗa waɗansu Lawiyawa, da firistoci, da waɗansu shugabannin iyalan Isra’ilawa, saboda su yi shari’a tsakani da Ubangiji, su daidaita tsakanin masu jayayya. A Urushalima za su zauna.

9 Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma.

10 A duk lokacin da ‘yan’uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari’a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari’a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da ‘yan’uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi.

11 Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji. Zabadiya, ɗan Isma’ilu mai mulkin gidan Yahuza, shi ne shugabanku a kan dukan al’amuran da suke na wajen sarki. Lawiyawa kuwa su zama muhimman ma’aikatanku. Kada ku ji tsoro a cikin aikinku, Ubangiji kuwa ya kasance tare da masu gaskiya.”

Categories
2 TAR

2 TAR 20

Yaƙi da Mowab, da Ammon, da Edom

1 Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me’uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat.

2 Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat cewa, “Mutane masu yawan gaske suna zuwa su yi yaƙi da kai daga Edom, da kuma teku, har sun iso Hazazon-tamar,” wato En-gedi.

3 Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza.

4 Yahuza suka tattaru don su nemi taimako daga wurin Ubangiji. Daga cikin dukan biranen Yahuza, mutane suka zo don su nemi Ubangiji.

5 Sai Yehoshafat ya tsaya a gaban taron jama’ar Yahuza da na Urushalima, a Haikalin Ubangiji, a gaban sabuwar farfajiya,

6 ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al’umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.

7 Ya Allahnmu, kai ne ka kori jama’ar ƙasan nan a gaban jama’arka Isra’ila, ka kuma ba da ita har abada ga zuriya masoyinka Ibrahim.

8 Suka kuwa zauna a cikinta, suka gina Wuri Mai Tsarki saboda sunanka cewa,

9 ‘Idan wani mugun abu ya same mu, kamar takobi, ko hukunci, ko annoba, ko yunwa, to, za mu tsaya a gaban wannan gida, a gabanka kuma, gama sunanka yana cikin gidan nan, idan mun yi maka kuka saboda wahalarmu, kai kuwa za ka ji, ka cece mu.’

10 “Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra’ilawa su kai musu yaƙi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra’ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.

11 Dubi irin sakayyar da suka zo su yi mana, so suke su kore mu daga mallakarka, wanda ka gādar mana.

12 Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”

13 A sa’an nan kuwa mutanen Yahuza suna tsaye a gaban Ubangiji, su da ƙananansu, da matansu, da ‘ya’yansu.

14 A tsakiyar taron sai Ruhun Ubangiji ya sauka a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benaiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, Balawe, na ‘ya’yan Asaf, maza.

15 Sai Yahaziyel ya ce, “Ku ji, ku dukanku, mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da sarki Yehoshafat, ga abin da Ubangiji yake faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ko ku razana saboda wannan babban taro, gama wannan yaƙi ba naku ba ne, amma na Allah ne.

16 Ku gangara ku fāɗa musu gobe. Ga shi kuwa, za su haura ta hawan Ziz, za ku tarar da su a ƙarshen kwarin a gabashin jejin Yeruyel.

17 Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”

18 Yehoshafat fa ya sunkuyar da kansa ƙasa, dukan Yahuza da mazaunan Urushalima kuma suka fāɗi ƙasa a gaban Ubangiji, suna masa sujada.

19 Sai Lawiyawa daga Kohatawa da Koratiyawa suka tashi tsaye suka yabi Ubangiji Allah na Isra’ila da babbar murya.

20 Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa’ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”

21 Sa’ad da ya yi shawara da jama’a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa’ad da suke tafe a gaban runduna, su ce,

“Ku yi godiya ga Ubangiji,

Saboda madawwamiyar ƙaunarsa

Tabbatacciya ce har abada.”

22 Sa’ad da suka fara raira waƙa, suna yabo, sai Ubangiji ya sa wa mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, ‘yan kwanto, ‘yan kwanton kuwa suka fatattake su.

23 Gama mutanen Ammon da na Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka kansu da kansu.

24 Da mutanen Yahuza suka zo hasumiyar tsaro ta jeji, suka duba sai suka ga gawawwaki kawai a kwance, ba wanda ya tsira.

25 Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna ta kwasar ganimar saboda yawanta.

26 Sai suka taru a kwarin Beraka, wato albarka, a rana ta huɗu, a nan suka yabi Ubangiji. Don haka har wa yau ake kiran wurin, “Kwarin Beraka.”

27 Sai kowane mutumin Yahuza da na Urushalima, tare da Yehoshafat shugabansu, suka koma Urushalima suna murna, gama Ubangiji ya sa su yi farin ciki saboda maƙiyansu.

28 Suka shigo Urushalima da molaye da garayu, da ƙaho zuwa Haikalin Ubangiji.

29 Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa’ad da suka ji Ubangiji ya yi yaƙi da maƙiyan Isra’ilawa.

30 Mulkin Yehoshafat kuwa ya sami salama, gama Allahnsa ya ba shi hutawa a kowane gefe.

Ƙarshen Mulkin Yehoshafat

31 Yehoshafat ya yi mulkin Yahuza. Yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan tsohuwarsa Azuba, ‘yar Shilhi.

32 Ya bi tafarkin tsohonsa, Asa, bai kuwa kauce ba, ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

33 Duk da haka ba a kawar da masujadai ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.

34 Sauran ayyukan Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin tarihin Yehu ɗan Hanani, wanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra’ila.

35 Bayan haka sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya haɗa kai da Ahaziya Sarkin Isra’ila, wanda ya aikata mugunta.

36 Ya haɗa kai da shi, suka gina jiragen ruwa don su riƙa zuwa Tarshish. A Eziyon-geber suka gina jiragen ruwan.

37 Sai Eliyezer ɗan Dodawahu mutumin Maresha, ya yi annabci gāba da Yehoshafat, ya ce, “Saboda ka haɗa kanka da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Don haka jiragen ruwa suka farfashe, suka kāsa tafiya Tarshish.