Categories
2 TAR

2 TAR 21

1 Yehoshafat ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda tare da kakanninsa, ɗansa kuma ya gāji gadon sarautarsa.

Sarki Yoram na Yahuza

2 Yoram yana da ‘yan’uwa maza, su ne Azariya, da Yehiyel, da Zakariya, da Azariya, da Maikel da kuma Shefatiya. Waɗannan ‘ya’ya maza ne na Yehoshafat, Sarkin Yahuza.

3 Tsohonsu ya ba su kyautai da yawa na azurfa da zinariya, da abubuwa masu daraja, da birane masu garu a Yahuza, amma ya ba da mulkin ga Yoram, saboda shi ne ɗan fari.

4 Sa’ad da Yoram ya hau gadon sarautar tsohonsa, ya kahu sosai, sai ya karkashe dukan ‘yan’uwansa da takobi, ya kuma karkashe waɗansu daga cikin sarakunan Yahuza.

5 Yoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya hau gadon sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara takwas.

6 Ya yi yadda sarakunan Isra’ila suka yi, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama matarsa ‘yar Ahab ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.

7 Duk da haka Ubangiji bai yarda ya hallaka gidan Dawuda ba, saboda alkawarin da ya riga ya yi da Dawuda, gama ya riga ya alkawarta zai ba shi haske, shi da ‘ya’yansa maza har abada.

8 A zamaninsa Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.

9 Sai Yoram ya wuce, shi da shugabannin sojojinsa tare da dukan karusansa. Sai ya tashi da dare ya fatattaki Edomawa waɗanda suka kewaye shi, shi da shugabannin karusansa.

10 Har wa yau Edom ya tayar wa Yahuza. A wannan lokaci kuma Libna ta tayar wa mulkinsa, saboda Yoram ya rabu da bin Ubangiji Allah na kakanninsa.

11 A kan wannan kuma, ya yi masujadai a tuddan ƙasar Yahuza, ya sa mutanen Urushalima su zama marasa aminci, ya sa Yahuza ta ratse.

12 Sai annabi Iliya ya rubuta masa wasiƙa ya ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na tsohonka Dawuda ya ce, ‘Da yake ba ka bi halin tsohonka Yehoshafat ba, da halin Asa Sarkin Yahuza,

13 amma ka bi irin halin sarakunan Isra’ila, har ka sa Yahuza da mazaunan Urushalima su zama marasa aminci, yadda gidan Ahab ya yi, ka kuma karkashe ‘yan’uwanka, waɗanda kuke uba ɗaya, waɗanda suka fi ka kirki,

14 ga shi, ni Ubangiji zan aukar da babbar abboba a kan jama’arka, da ‘ya’yanka maza, da matanka, da a kan abin da ka mallaka duka.

15 Kai da kanka kuma za ka kamu da ciwon hanji mai tsanani, saboda tsananin ciwo, hanjinka zai tsintsinke ya yi ta zuba kowace rana.’ ”

16 Sai Ubangiji ya kuta Filistiyawa da Larabawan da suke kusa da Habashawa, su yi gāba da Yoram.

17 Suka zo suka faɗa wa Yahuza da yaƙi. Suka washe dukan dukiyar da aka samu a gidan sarki, suka tafi da ita. Suka kuma kwashe ‘ya’yansa, da matansa, ba wanda aka bar masa, sai Ahaziya autansa.

18 Bayan haka kuma, sai Ubangiji ya sa masa ciwon hanji wanda ba shi warkuwa.

19 Ana nan a ƙarshen shekara biyu, sai cutar ta sa hanjinsa ya zubo, ya kuwa rasu saboda tsananin ciwo. Jama’arsa ba su hura masa wuta ta girmamawa kamar yadda aka yi wa kakanninsa ba.

20 Yana da shekara talatin da biyu, ya ci sarauta, ya yi shekara takwas yana mulki a Urushalima, ba wanda ya yi baƙin cikin mutuwarsa. Aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba a kaburburan sarakuna ba.

Categories
2 TAR

2 TAR 22

Sarki Ahaziya na Yahuza

1 Sai mazaunan Urushalima suka naɗa Ahaziya, autansa, ya gāji gadon sarauta, saboda ƙungiyar mutanen da suka zo tare da Larabawa a sansanin sun karkashe dukan ‘yan’uwansa maza. Ahaziya ɗan Yoram Sarkin Yahuza, ya fara mulki.

2 Ahaziya yana da shekara arba’in da biyu sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikar Omri.

3 Ya kuma bi gurbin gidan Ahab, gama tsohuwarsa ita ce mai ba shi shawarar yadda zai aikata mugunta.

4 Ya kuwa aikata mugunta a gaban Ubangiji kamar gidan Ahab, gama su ne mashawartansa bayan rasuwar tsohonsa, wato shawarar da ta kai shi ga lalacewa.

5 Ya kuwa bi shawararsu. Ya tafi tare da Yehoram ɗan Ahab, Sarkin Isra’ila, don su yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya, a Ramot-gileyad. Suriyawa kuwa suka yi wa Yehoram rauni.

6 Don haka sai ya koma Yezreyel don ya yi jiyyar raunukan da aka yi masa a Rama, sa’ad da suka yi yaƙi da Hazayel Sarkin Suriya. Sai Ahaziya ɗan Yoram, Sarkin Yahuza, ya gangara don ya gai da Yehoram ɗan Ahab a Yezreyel wanda yake rashin lafiya.

Yehu Ya kashe Ahaziya

7 Allah ya ƙaddara hallakar Ahaziya ta zo ta wurin ziyarar da ya kai wa Yehoram. Gama sa’ad da ya zo, sai ya fita tare da Yehoram don su yi yaƙi da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya keɓe don ya kakkaɓe gidan Ahab.

8 Sa’ad da Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya gamu da sarakunan Yahuza, da ‘ya’yan ‘yan’uwan Ahaziya, maza, suna yi wa Ahaziya hidima, sai ya karkashe su.

9 Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.”

Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.

Sarauniya Ataliya ta Yahuza

10 Da Ataliya tsohuwar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta karkashe duk ‘yan sarautar gidan Yahuza.

11 Amma sai Yehosheba, ‘yar sarki Yoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya, ta sace shi daga cikin ‘ya’yan sarki waɗanda aka kashe su ta sa shi da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ‘yar sarki Yoram, matar Yehoyada firist, ta yi, gama ita ‘yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya ta kashe shi.

12 Yowash yana ɓoye a Haikalin Allah har shekara shida, a lokacin da Ataliya take mulkin ƙasar.

Categories
2 TAR

2 TAR 23

An Ƙwace wa Ataliya Mulki

1 A shekara ta bakwai sai Yehoyada ya yi ƙarfin hali, ya haɗa kansa da shugabanni na ɗari ɗari, wato Azariya ɗan Yeroham, da Isma’ilu ɗan Yehohanan, da Azariya ɗan Obed, da Ma’aseya ɗan Adaya, da kuma Elishafat ɗan Zikri.

2 Sai suka shiga ko’ina cikin Yahuza, suka tattaro Lawiyawa daga dukan biranen Yahuza, da shugabannin gidajen kakannin Isra’ila, suka kuwa zo Urushalima.

3 Sai dukan taron suka yi wa sarki alkawari, a Haikalin Allah. Yehoyada ya ce musu, “Wannan shi ne ɗan sarki, sai ya ci sarauta kamar yadda Ubangiji ya faɗa a kan ‘ya’yan Dawuda, maza.

4 Ga abin da za ku yi. Sulusin firistoci da Lawiyawa waɗanda ba su aiki ran Asabar, su za su yi tsaron ƙofofi.

5 Sulusinsu kuma a fādar sarki, ɗayan sulusin kuwa a gangare, sauran jama’a duka kuwa a filayen Haikalin Ubangiji.

6 Amma kada kowa ya shiga Haikalin Ubangiji, sai dai firistoci da Lawiyawa masu hidima, su ne za su iya shiga, gama su tsarkaka ne. Amma dukan jama’a su kiyaye shari’a, kada su shiga Wuri Mai Tsarki na Ubangiji.

7 Lawiyawa za su kewaye sarkin, ko wanne da makamansa a hannu, duk wanda ya shiga ɗakin, sai a kashe shi. Su kuma kasance tare da sarki in zai shiga ko zai fita.”

8 Sai Lawiyawa da dukan Yahuza suka yi yadda Yehoyada, firist, ya umarta. Kowannensu ya kawo mutanensa waɗanda ba su aiki ran Asabar, da masu kama aiki ran Asabar, gama Yehoyada, firist, bai sallami ƙungiyoyin ba.

9 Sai Yehoyada firist, ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin Haikalin Allah.

10 Sai ya sa mutane duka su yi tsaron sarki, ko wanne da makami a hannu, tun daga gefen kudu har gefen arewa na Haikalin, da kuma kewaye da bagade da Haikali.

11 Sai ya kawo ɗan sarkin, ya sa masa kambi, ya ba shi dokoki goma, aka yi shela aka ce shi ne sarki. Yehoyada da ‘ya’yansa maza suka naɗa shi, suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”

12 Sa’ad da Ataliya ta ji sowar mutane, suna ta ribibi suna yabon sarki, sai ta shiga Haikalin Ubangiji wurin jama’a.

13 Sa’ad da ta duba, sai ga sarki yana tsaye wajen ginshiƙin bakin ƙofa, ga shugabanni da masu busa ƙaho kewaye da sarkin. Dukan jama’a suna murna, suna busa ƙaho, mawaƙa kuma da kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushensu, suna shugabancin shagalin. Sai Ataliya ta yayyage tufafinta ta ce, “Tawaye! Tawaye!”

14 Sai Yehoyada, firist, ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku kawo ta a tsakiyar sojoji, duk wanda ya bi ta a kashe shi da takobi.” Gama firist ɗin ya ce, “kada ku kashe ta a Haikalin Ubangiji.”

15 Sai suka kama ta. Da suka kai Ƙofar Doki ta fādar sarki, sai suka kashe ta a can.

Gyare-gyaren Yehoyada

16 Sai Yehoyada da dukan jama’a, da sarkin, suka ɗauki alkawari za su zama jama’ar Ubangiji.

17 Sai dukan jama’a suka tafi gidan Ba’al, suka rushe shi, suka kuma ragargaza bagadansa, da siffofinsa. Suka kashe Mattan, firist ɗin Ba’al, a gaban bagadan.

18 Yehoyada kuma ya sa matsaran da za su yi tsaron Haikalin Ubangiji a ƙarƙashin ikon firistoci, Lawiyawa, waɗanda Dawuda ya shirya don su lura da Haikalin Ubangiji, su miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, yadda aka rubuta a Attaura ta Musa, da murna da waƙa kamar yadda Dawuda ya shirya.

19 Ya kuma sa ‘yan tsaron ƙofa a ƙofofin Haikalin Ubangiji, don kada wani marar tsarki na kowane iri ya shiga.

20 Sai ya sa shugabanni, da dattawa, da masu mulki, da dukan jama’ar ƙasar, suka rufa wa sarki baya, daga Haikalin Ubangiji suka bi ta Ƙofar Bisa zuwa fādar sarki. Suka zo suka zaunar da sarki a gadon sarauta.

21 Dukan jama’ar ƙasar suka yi murna, zaman lafiya ya komo birnin, bayan da an kashe Ataliya.

Categories
2 TAR

2 TAR 24

Sarki Yowash na Yahuza

1 Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi shekara arba’in yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya, daga Biyer-sheba.

2 Yowash ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji a dukan zamanin Yehoyada firist.

3 Sai Yehoyada ya auro masa mata biyu, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

4 Bayan wannan sai Yowash ya yi niyya ya gyara Haikalin Ubangiji.

5 Sai ya tattara firistoci da Lawiyawa, ya ce musu, “Ku shiga biranen Yahuza, ku tattara kuɗi daga dukan Isra’ilawa domin a riƙa gyaran Haikalin Ubangijinku kowace shekara. Ku hanzarta al’amarin fa.” Amma Lawiyawa ba su hanzarta ba.

6 Sai sarki ya kira Yehoyada babban firist, ya ce masa, “Don me ba ka sa Lawiyawa su tafi Yahuza, da Urushalima, su karɓo kuɗin da Musa, bawan Ubangiji, ya aza wa taron jama’ar Isra’ila su kawo domin alfarwar sujada ba?”

7 Gama ‘ya’ya maza na Ataliya, muguwar matan nan, sun kutsa kai a cikin Haikalin Ubangiji, suka yi amfani da dukan tsarkakan kayayyakin Haikalin Ubangiji domin gumaka.

8 Don haka sai sarki ya ba da umarni, a yi babban akwati, a ajiye shi a waje a ƙofar Haikalin Ubangiji.

9 Sai aka yi shela a Yahuza da Urushalima, a kawo wa Ubangiji kuɗin da Musa, bawan Allah, ya aza wa Isra’ila sa’ad da suke cikin jeji.

10 Sai dukan sarakuna, da dukan jama’a, suka yi farin ciki, suka kawo kuɗin da aka aza musu, suka zuba a babban akwatin, har ya cika.

11 Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa ‘yan majalisar sarki babban akwatin sa’ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na’ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da suke cikin babban akwatin, sa’an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.

12 Sarki kuwa da Yehoyada suka ba da kuɗin ga waɗanda suke lura da aikin Haikalin Ubangiji. Suka sa magina, da masassaƙa su gyara Haikalin Ubangiji, suka kuma sa masu aikin baƙin ƙarfe da na tagulla su gyara Haikalin Ubangiji.

13 Sai ma’aikatan da aka sa su yi aikin, suka yi aiki sosai, suka tafiyar da gyaran, suka gyara Haikalin Ubangiji, ƙarfinsa ya koma kamar yadda yake dā.

14 Da suka gama aikin, sai suka kawo wa sarki da Yehoyada sauran kuɗin. Da waɗannan kuɗin aka yi tasoshi, da kayan girke-girke na Haikalin Ubangiji, da kuma kayan hidima da miƙa hadayu na ƙonawa, da tasoshi domin turare, da kwanoni na zinariya da na azurfa.

An sāke Shirin Yehoyada

Suka yi ta miƙa hadayu na ƙonawa a cikin Haikalin Ubangiji, dukan kwanakin Yehoyada.

15 Yehoyada kuwa ya tsufa ƙwarai, ya yi tsawon rai, ya rasu. Ya rasu yana da shekara ɗari da talatin da haihuwa.

16 Suka binne shi a birnin Dawuda a inda ake binne sarakuna, saboda ya aikata nagarta a Isra’ila, da kuma a gaban Allah da Haikalin Allah.

17 Bayan rasuwar Yehoyada, sai sarakunan Yahuza suka zo suka yi mubaya’a a gaban sarki, sarki kuwa ya karɓa.

18 Sai suka ƙyale Haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa Ashtarot da gumaka. Hasala kuwa ta auko a kan Yahuza da Urushalima, saboda wannan mugunta da suka yi.

19 Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba.

20 Sai Ruhun Allah ya sauko wa Zakariya, ɗan Yehoyada, firist, ya tsaya a gaban jama’a ya yi magana da su, ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Don me kuke ƙetare umarnan Ubangiji, har da za ku rasa albarka? Saboda kun rabu da bin Ubangiji, shi ma ya rabu da ku.’ ”

21 Amma suka yi masa maƙarƙashiya, sarki kuma ya ba da umarni, suka jejjefi annabin da duwatsu har ya mutu a farfajiyar Haikalin Ubangiji.

22 Sarki Yowash bai tuna da irin alherin da Yehoyada mahaifin Zakariya ya yi masa ba, amma ya kashe ɗansa. Sa’ad da Zakariya yake bakin mutuwa, sai ya ce, “Bari Ubangiji ya gani ya kuma sāka.”

23 A ƙarshen shekara sai sojojin Suriyawa suka kawo wa Yowash yaƙi suka je Yahuza da Urushalima, suka hallaka dukan shugabannin jama’a, suka kwashi ganima mai yawa, suka aika wa Sarkin Dimashƙu.

24 Ko da yake mutanen Suriya kima ne, duk da haka Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan babbar rundunar Yowash, saboda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu. Ta haka suka hukunta wa Yowash.

25 Sa’ad da suka tafi, sun bar shi da rauni mai tsanani ƙwarai, sai barorinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a gadonsa, saboda ya kashe ɗan Yehoyada firist. Ya mutu, aka binne shi a birnin Dawuda, amma ba su binne shi a kabarin sarakuna ba.

26 Waɗannan su ne waɗanda suka yi masa maƙarƙashiyar, Yozakar ɗan Shimeyat wata Ba’ammoniya, da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab.

27 Labarin ‘ya’yansa maza da annabcin da aka kawo a kansa da labarin sāke ginin Haikalin Allah, an rubuta su a sharhin littafin sarakunan. Sai Amaziya ɗan Yowash ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 TAR

2 TAR 25

Sarki Amaziya na Yahuza

1 Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta, ya yi shekara ashirin da tara yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yehowaddin ta Urushalima.

2 Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji, amma bai rasa aikata laifi a zuciyarsa ba.

3 Da ya ga mulkin ya kahu a hannunsa sosai, sai ya karkashe fādawa waɗanda suka kashe tsohonsa, sarki Yowash.

4 Amma bai karkashe ‘ya’yansu ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Shari’a, wato Attaura ta Musa, inda Ubangiji ya yi umarni cewa, “Ba za a kashe iyaye saboda ‘ya’yansu ba, ba za a kuma kashe ‘ya’ya saboda iyaye ba, amma mutum zai mutu saboda laifin kansa.”

5 Sa’an nan Amaziya ya tattara mazajen Yahuza, ya kasa su bisa ga gidajen kakanninsu, a ƙarƙashin shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, a dukan Yahuza da Biliyaminu. Sai ya tara ‘yan shekara ashirin ko fi, ya sami mutum dubu ɗari uku (300,000) ƙarfafa, waɗanda suka isa zuwa yaƙi, wato za su iya riƙon māshi da garkuwa.

6 Ya kuma ɗauko sojan haya, mutum dubu ɗari (100,000) jarumawa daga Isra’ila a bakin talanti ɗari na azurfa.

7 Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, kada ka yarda rundunar sojojin Isra’ila su tafi tare da kai, gama Ubangiji ba ya tare da Isra’ila, wato da dukan Ifraimawan nan.

8 Amma idan ka zaci ta wannan hanya ce za ka zama da ƙarfi don yaƙi, Allah zai kā da kai a gaban maƙiyi, gama Allah yana da iko ya yi taimako, ko kuwa ya ƙi.”

9 Amaziya kuwa ya ce wa annabin Allah, “To, me za mu yi yanzu game da azurfar da muka ba sojojin Isra’ila?”

Sai annabin Allah ya amsa ya ce, “Ubangiji yana da iko ya ba ka fiye da haka.”

10 Sai Amaziya ya sallami rundunar sojojin da suka zo daga Ifraimu, su koma gida. Sai suka yi fushi da Yahuza ƙwarai suka koma gida cike da hasala mai zafi.

11 Amma Amaziya ya yi ƙarfin hali ya shugabanci jama’arsa, suka tafi Kwarin Gishiri, suka karkashe mutanen Seyir dubu goma (10,000).

12 Mutanen Yahuza kuma suka kama waɗansu mutum dubu goma (10,000) da rai, suka kai su a ƙwanƙolin dutse, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa daga ƙwanƙolin dutsen, duka suka yi kaca-kaca.

13 Amma sojojin rundunar da Amaziya ya sallama, bai yarda su tafi yaƙi tare da shi ba, suka faɗa wa biranen Yahuza da yaƙi, tun daga Samariya har zuwa Bet-horon, suka kashe mutum dubu uku (3,000), a cikinsu suka kwashe ganima mai yawan gaske.

14 Da Amaziya ya komo daga kisan Edomawa, sai ya kwaso gumakan mutanen Seyir, ya ajiye su su zama gumakansa, ya yi musu sujada, ya kuma miƙa musu hadaya.

15 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da Amaziya. Ubangiji ya aiki annabi a wurinsa. Annabin ya ce masa, “Don me ka koma ga gumakan da ba su iya ceton jama’arsu daga hannunka ba?”

16 Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.”

Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”

Yaƙi da Isra’ila

17 Sa’an nan Amaziya Sarkin Yahuza, ya yi shawara ya aika wa Yehowash ɗan Yehowahaz ɗan Yehu, Sarkin Isra’ila, ya ce, “Ka zo mu gabza da juna fuska da fuska.”

18 Yehowash Sarkin Isra’ila fa ya aika wa Amaziya Sarkin Yahuza, da amsa ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika wa itacen al’ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana ‘yarka aure,’ sai wani naman jeji na Lebanon da yake wucewa, ya tattake ƙayar.

19 Ka ce, ga shi, ka ci Edom, zuciyarka ta sa ka fāriya. Amma yanzu sai ka yi zamanka, don me ka tsokano wahalar da za ta kā da kai, da kai da Yahuza tare da kai?”

20 Amma Amaziya ya ƙi ji, gama al’amarin daga wurin Allah yake, domin ya bashe su a hannun maƙiyansu, saboda sun koma ga gumakan Edom.

21 Sarkin Isra’ila kuwa ya haura, da shi da Amaziya Sarkin Yahuza, suka gabza da juna fuska da fuska a Bet-shemesh, wadda take a ƙasar Yahuza.

22 Sai Isra’ila ya runtumi Yahuza, kowane mutum ya gudu zuwa gidansa.

23 Yehowash Sarkin Isra’ila, ya kama Amaziya Sarkin Yahuza ɗan Yowash, wato jikan Ahaziya, a Bet-shemesh, ya kawo shi Urushalima. Ya rushe garun Urushalima har tsawon kamu ɗari huɗu, tun daga Ƙofar Ifraimu har zuwa Ƙofar Kusurwa,

24 sai ya kwashe dukan zinariya da azurfa, da dukan tukwane da tasoshi da aka samu a Haikalin Allah, waɗanda iyalin Obededom suke tsaro, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.

25 Sarki Amaziya ɗan Yowash, Sarkin Yahuza, ya rayu shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra’ila.

26 Sauran ayyukan Amaziya, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra’ila.

27 Daga lokacin da Amaziya ya bar bin Ubangiji, sai suka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, amma ya gudu zuwa Lakish, sai suka sa a bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.

28 Sai suka kawo shi a bisa dawakai, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

Categories
2 TAR

2 TAR 26

Sarki Azariya na Yahuza

1 Dukan jama’ar Yahuza fa suka ɗauki Azariya, ɗan shekara goma sha shida, suka naɗa shi sarki, ya gāji gadon sarautar tsohonsa Amaziya.

2 Ya gina Elat, ya komar da ita ga Yahuza, bayan rasuwar sarki.

3 Azariya yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu, sunan tsohuwarsa Yekoliya ta Urushalima.

4 Azariya ya yi abin da yake daidai saboda Ubangiji, bisa ga dukan irin abin da tsohonsa Amaziya ya aikata.

5 Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.

6 Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.

7 Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa, da Larabawa, waɗanda suke zaune a Gur-ba’al, da kuma Me’uniyawa.

8 Ammonawa kuma suka kawo masa haraji, sunan Azariya ya kai har kan iyakar Masar, gama ya shahara ƙwarai.

9 Banda haka kuma, Azariya ya gina hasumiyai a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, da Ƙofar Kwari, da kan kusurwa, ya kuma yi musu kagara.

10 Ya kuma gina hasumiyai a jeji, ya haƙa tafukka masu yawa, saboda yana da garkunan dabbobi da yawa, da waɗanda suke Shefela da waɗanda suke a filin tudu. Yana kuma da manoma da masu yi wa kurangar inabi aski a tuddai, da wajen ƙasashe masu dausayi, gama shi mai son noma ne ƙwarai.

11 Har yanzu kuma, Azariya yana da rundunar sojoji waɗanda suka iya yaƙi ƙungiya ƙungiya, yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’aseya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin ‘yan majalisar sarki.

12 Jimillar shugabannin gidajen kakanni na ƙarfafan mutane jarumawa, dubu biyu da ɗari shida (2,600) ne.

13 Suna da sojoji dubu ɗari uku da dubu bakwai da ɗari biyar (307,500) a ƙarƙashin ikonsu waɗanda suke da ƙarfin yin yaƙi sosai, da za su taimaki sarki a kan maƙiyansa.

14 Azariya ya shirya wa sojojinsa garkuwoyi, da māsu, da kwalkwali, da sulke, da bakuna, da duwatsun majajjawa.

15 A Urushalima ya yi na’urori waɗanda gwanayen mutane ne suka ƙago don a sa su a hasumiya, da kan kusurwoyi, don a harba kibau, da manyan duwatsu. Da haka sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako mai banmamaki, har ya zama mai ƙarfin gaske.

An Hukunta Azariya Saboda Girmankai

16 Amma sa’ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.

17 Amma Azariya firist, ya bi shi tare da firistoci tamanin na Ubangiji, mutane ne jarumawa.

18 Sai suka hana sarki Azariya, suka ce masa, “Ba aikinka ba ne, Azariya, ka ƙona turare ga Ubangiji, wannan aikin firistoci ne, ‘ya’yan Haruna, waɗanda aka keɓe su don ƙona turare. Fita daga wurin nan mai tsarki, gama ka yi kuskure, ba za ka sami daraja daga wurin Ubangiji Allah ba.”

19 Azariya ya yi fushi, a lokacin kuwa yana riƙe da farantin ƙona turare a hannunsa, sa’ad da ya yi fushi da firistocin, sai kuturta ta faso a goshinsa, a nan gaban firistocin a cikin Haikalin Ubangiji, wajen bagaden ƙona turare.

20 Sai Azariya babban firist tare da sauran firistocin suka dube shi, sai ga kuturta a goshinsa! Sai suka tunkuɗa shi waje nan da nan. Shi kansa ma ya hazarta ya fita saboda Ubangiji ya buge shi.

21 Ta haka sarki Azariya ya kuturce, har zuwa ranar mutuwarsa. Saboda kuturtarsa, ya zauna a keɓe a wani gida, gama an fisshe shi daga Haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa shi ya shugabanci iyalin gidan sarki, yana kuma mulkin jama’ar ƙasa.

22 Sauran ayyukan Azariya, daga farko har zuwa ƙarshe, annabi Ishaya ɗan Amoz ya rubuta su.

23 Azariya ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a hurumin sarakuna, gama suka ce, “Shi kuturu ne.” Sai Yotam ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 TAR

2 TAR 27

Sarki Yotam na Yahuza

1 Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha ‘yar Zadok.

2 Ya aikata abin da yake daidai saboda Ubangiji, kamar dukan abin da tsohonsa Azariya ya yi, sai dai bai kutsa cikin Haikalin Ubangiji ba. Amma jama’a suka ci gaba da aikata rashin kirki.

3 Ya gina ƙofar bisa, ta Haikalin Ubangiji, ya yi gine-gine masu yawa a garun Ofel.

4 Ya kuma gina birane a ƙasar tuddai ta Yahuza, da kagara, da hasumiya a tuddai masu kuramu.

5 Ya yi yaƙi da Sarkin Ammonawa, ya kuwa ci nasara, har Ammonawa suka ba shi talanti ɗari na azurfa a wannan shekara, da alkama mudu dubu goma (10,000) da sha’ir mudu dubu goma (10,000). Haka Ammonawa suka yi ta biya a shekara ta biyu da ta uku.

6 Yotam ya shahara, saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.

7 Sauran ayyukan Yotam, da dukan yaƙe-yaƙensa da al’amuransa, an rubuta su a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuza.

8 Ya ci sarauta, yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima.

9 Sai Yotam ya rasu, suka binne shi a birnin Dawuda. Ahaz ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 TAR

2 TAR 28

Sarki Ahaz na Yahuza

1 Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima. Amma shi bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi ba.

2 Ya aikata irin al’amuran da sarakunan Isra’ila suka yi. Ya kuma yi gumakan Ba’al na zubi.

3 Banda haka ma ya ƙona turare a kwarin ɗan Hinnom, ya ƙone ‘ya’yansa maza bisa ga ƙazantattun al’adun al’ummai, waɗanda Ubangiji ya kore su daga gaban mutanen Isra’ila.

4 Ya miƙa hadayu, ya ƙona turare a masujadai da a bisa tuddai, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa.

Yaƙin Suriya da Isra’ila

5 Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya bashe shi a hannun Sarkin Suriya. Suka ci shi da yaƙi suka kama mutanensa da yawa, suka kai su Dimashƙu. Aka kuma bashe shi a hannun Sarkin Isra’ila, wanda ya ci shi da yaƙi, ya kashe masa mutane masu yawa.

6 Gama Feka, ɗan Remaliya, ya kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000) cikin Yahuza a rana ɗaya, dukansu kuwa jarumawa ne, don sun bar bin Ubangiji Allah na kakanninsu.

7 Sai Zikri wani ƙaƙƙarfan mutumin Ifraimu, ya kashe Ma’aseya ɗan sarki, da Azrikam, sarkin fāda, da Elkana wanda yake daga sarki sai shi.

8 Mutanen Isra’ila kuwa suka kwaso ‘yan’uwansu da suka kama, mutum dubu ɗari biyu (200,000), mata, da ‘ya’ya mata, da ‘ya’ya maza. Suka kuma kwaso ganima mai yawan gaske daga gare su. Suka kawo ganimar a Samariya.

Annabcin Oded

9 Amma wani annabin Ubangiji yana nan, sunansa Oded. Shi wannan annabi ya tafi ya taryi rundunar da ta zo Samariya, ya ce musu, “Ga shi, saboda Ubangiji Allah na kakanninku ya yi fushi da Yahuza, ya bashe su a hannunku, ku kuka kashe su da zafin fushi wanda ya kai har sama.

10 Yanzu kuwa kuna niyya ku mai da jama’ar Yahuza da ta Urushalima su zama bayinku mata da maza. Ashe, ku kanku ba ku da waɗansu zunuban da kuka yi wa Ubangiji Allahnku?

11 Yanzu fa, sai ku saurare ni, ku mayar da kamammun da kuka kwaso daga ‘yan’uwanku gama Ubangiji yana fushi da ku ƙwarai.”

12 Waɗansu daga cikin shugabannin ‘ya’ya maza na Ifraimu, wato su Azariya ɗan Yohenan, da Berikiya ɗan Meshillemot, da Yehizkiya ɗan Shallum, da Amasa ɗan Hadlai suka tashi suka tsayar da masu komowa daga wurin yaƙin.

13 Suka ce musu, “Kada ku shigo nan da waɗanda kuka kamo daga wurin yaƙin, gama so kuke ku jawo mana laifi a gaban Ubangiji, a kan manyan zunuban da muka riga muka yi, gama Ubangiji yana fushi da Isra’ila ƙwarai.”

14 Don haka sai sojoji suka bar waɗanda suka kamo daga wurin yaƙi, da ganima a gaban sarakuna da dukan taron.

15 Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin ‘yan’uwansu a Yariko, wato birnin itatuwan dabino, sa’an nan suka koma Samariya.

Ahaz Ya Roƙi Assuriya Taimako

16 A wannan lokaci kuwa sarki Ahaz ya nemi taimako wurin sarakunan Assuriya.

17 Gama Edomawa suka sāke kai wa Yahuza yaƙi, suka kama mutane suka tafi da su.

18 Filistiyawa kuma sun kai hari a biranen ƙasar Shefela, da Negeb ta Yahuza, har suka ci Bet-shemesh, da Ayalon, da Gederot, da Soko da ƙauyukanta, da Timna da ƙauyukanta, da Gimzo da ƙauyukanta. Sai suka zauna a can.

19 Ubangiji kuwa ya ƙasƙantar da Yahuza, saboda Ahaz Sarkin Yahuza ya yi ganganci a Yahuza, ya zama marar aminci ga Ubangiji.

20 Sai Tiglatfilesar, Sarkin Assuriya, ya zo ya yi yaƙi da shi, ya wahalshe shi, maimakon ya taimake shi.

21 Sai Ahaz ya kwaso kaya daga Haikalin Ubangiji, da fādar sarki, da na sarakuna, ya ba Sarkin Assuriya, amma sam, bai taimake shi ba.

22 Duk da wannan wahala da sarki Ahaz yake sha a wannan lokaci, sai ƙara rashin aminci yake yi ga Ubangiji.

23 Gama ya miƙa hadaya ga gumakan Dimashƙu, ga waɗanda suka ci shi da yaƙi, ya ce, “Saboda gumakan sarakunan Suriya sun taimake su, ni ma zan miƙa musu hadaya don su taimake ni.” Amma suka zama masa dalilin lalacewa, shi da dukan Isra’ila.

24 Sai Ahaz kuma ya tattara tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya farfashe su. Ya kuma kukkulle ƙofofin Haikalin Ubangiji, ya gina wa kansa bagadai a kowane lungu na Urushalima.

25 A kowane birni na Yahuza, ya yi masujadai inda zai ƙona turare ga gumaka, ya sa Ubangiji, Allah na kakanninsa ya yi fushi.

26 Sauran ayyukansa da dukan al’amuransa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra’ila.

27 Ahaz ya rasu, suka binne shi cikin birnin Urushalima, amma ba su kai shi hurumin sarakunan Isra’ila ba. Hezekiya ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 TAR

2 TAR 29

Sarki Hezekiya na Yahuza

1 Hezekiya ya ci sarauta sa’ad da yake da shekara ashirin da biyar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abaija, ‘yar Zakariya.

2 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi duka.

Hezekiya Ya Tsabtace Haikali

3 A shekara ta fari ta mulkinsa, a wata na farko, sai ya buɗe ƙofofin Haikalin Ubangiji ya gyaggyara su.

4 Sai ya shigo da firistoci da Lawiyawa, ya tara su a filin da yake wajen gabas.

5 Sai ya ce musu, “Ku ji ni, ya ku Lawiyawa. Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake Haikalin Ubangiji Allah na kakanninku, ku kawar da ƙazantar da yake a Wuri Mai Tsarki.

6 Gama kakanninmu sun yi rashin aminci, sun aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnmu, sun rabu da shi sun ba da baya ga mazaunin Ubangiji.

7 Sun kuma rurrufe ƙofofin shirayi suka kashe fitilu, sun daina ƙona turare ko miƙa hadayun ƙonawa a Wuri Mai Tsarki ga Allah na Isra’ila.

8 Don haka Ubangiji ya yi fushi da Yahuza da Urushalima, ya sa suka zauna da tsoro, abin banmamaki, abin ba’a kamar yadda kuke gani da idanunku.

9 Saboda wannan an kashe kakanninmu da takobi, ‘ya’yanmu mata, da ‘ya’yanmu maza da matanmu, an kai su bauta.

10 “Yanzu na yi niyya a zuciyata in yi alkawari da Ubangiji Allah na Isra’ila, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da mu.

11 ‘Ya’yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.”

12-14 Sa’an nan sai Lawiyawa suka tashi,

na Kohatawa, Mahat ɗan Amasai, da Yowel ɗan Azariya,

na Merari, Kish ɗan Abdi, da Azariya ɗan Yehallelel,

na Gershonawa, Yowa ɗan Zimma, da Eden ɗan Yowa,

na Elizafan, Shimri da Yehiyel,

na Asaf, Zakariya da Mattaniya,

na Heman, Yehiyel da Shimai,

na Yedutun, Shemaiya da Uzziyel.

15 Sai suka tattara ‘yan’uwansu maza, suka tsarkake kansu, suka shiga bisa ga umarnin sarki, bisa ga maganar Ubangiji domin su tsabtace Haikalin Ubangiji.

16 Firistoci fa, suka shiga can cikin Haikalin Ubangiji domin su tsabtace shi. Suka kwaso dukan ƙazantar da yake a Haikalin Ubangiji, suka zuba ta a farfajiyar Haikalin Ubangiji. Sai Lawiyawa suka kwashe, suka zubar a rafin Kidron.

17 A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.

An Sāke Keɓe Haikali

18 Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya suka ce, “Mun tsabtace Haikalin Ubangiji duka, da bagaden hadayar ƙonawa tare da dukan tasoshi, da tukwane, da teburin gurasar ajiyewa da kuma dukan kayayyakin da yake ciki.

19 Dukan kayayyakin da sarki Ahaz ya lalatar a zamaninsa, sa’ad da ya zama marar aminci, mun shirya su mun tsarkake su, suna nan a gaban bagaden Ubangiji.”

20 Sarki Hezekiya kuwa ya tashi da sassafe ya tattara manyan gari suka haura zuwa Haikalin Ubangiji.

21 Suka kawo bijimai bakwai, da raguna bakwai, da ‘yan raguna bakwai, da bunsurai bakwai, domin yin hadaya don zunubi saboda mulkin, da Wuri Mai Tsarki, da kuma Yahuza. Sai ya umarci firistoci, wato ‘ya’yan Haruna, maza, su miƙa su a kan bagaden Ubangiji.

22 Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin, suka yayyafa a jikin bagaden. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka nan kuma suka yanka ‘yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden.

23 Sa’an nan suka kawo wa sarki da taron jama’a bunsuran yin hadaya domin zunubi, suka ɗora hannuwansu a kan bunsuran.

24 Sai firistocin suka yanka su suka tsarkake bagaden da jinin bunsuran, don a yi kafara saboda dukan Isra’ila. Gama sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi saboda dukan Isra’ila.

25 Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.

26 Lawiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dawuda, firistoci kuwa suna riƙe da ƙahoni.

27 Sai Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawar a bisa bagaden. Sa’ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa, sai aka fara raira waƙa ga Ubangiji, aka busa ƙaho, sai sauran masu kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushe na Dawuda, Sarkin Isra’ila, suka kama.

28 Dukan taron suka yi sujada, mawaƙa suna ta raira waƙa, masu ƙahoni suka yi ta busa. Aka yi ta yin haka har lokacin da aka gama miƙa hadayar ƙonawa.

29 Bayan da an gama yin hadaya ta ƙonawa, sai sarki, tare da dukan waɗanda suke tare da shi, suka sunkuya suka yi sujada.

30 Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.

31 Hezekiya kuwa ya amsa ya ce, “Yanzu dai kun tsarkake kanku ga Ubangiji. Sai ku zo kusa ku kawo hadayu da sadakoki na godiya a Haikalin Ubangiji.” Sai taron suka kawo hadayu da sadakoki na godiya, dukan waɗanda suka yi niyya kuwa suka kawo hadayu na ƙonawa.

32 Jimillar hadayu na ƙonawa waɗanda taron suka kawo, su ne bijimai saba’in, da raguna ɗari, da ‘yan raguna ɗari biyu, waɗannan duka kuwa don hadaya ne ta ƙonawa ga Ubangiji.

33 Abubuwan da aka keɓe kuwa bijimai ɗari shida ne, da tumaki dubu uku (3,000).

34 Amma su firistoci kima ne, don haka sun kāsa fiɗa dukan dabbobin da za a miƙa su hadaya ta ƙonawa. Sai ‘yan’uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu.

35 Banda hadayu masu yawa na ƙonawa da aka yi, akwai kuma kitse na hadaya ta salama, akwai kuma hadaya ta sha don kowace hadaya ta ƙonawa.

Da haka fa aka maido hidimar Haikalin Ubangiji.

36 Hezekiya da dukan jama’a suka yi murna saboda abin da Allah ya yi wa jama’a, gama farat ɗaya abin ya faru.

Categories
2 TAR

2 TAR 30

Yin Idin Ƙetarewa

1 Sai Hezekiya ya aika zuwa ga dukan Isra’ila da Yahuza, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa ga Ifraimu, da Manassa, cewa sai su zo Haikalin Ubangiji a Urushalima, domin su yi Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra’ila.

2 Gama sarki da sarakunansa da dukan majalisar da take a Urushalima sun tsai da shawara a yi Idin Ƙetarewa a wata na biyu,

3 gama ba su iya yinsa a lokacinsa ba, saboda yawan firistocin da suka tsarkake kansu bai isa ba, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.

4 A ganin sarki da na jama’a duka, shirin ya yi daidai.

5 Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra’ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra’ila a Urushalima, gama jama’a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba.

6 Sai mazanni suka tafi ko’ina da ina a dukan ƙasar Isra’ila da ta Yahuza da wasiƙu daga wurin sarki da sarakunansa, yadda sarki ya umarta.

“Ya ku jama’ar Isra’ila, ku komo wurin Ubangiji Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra’ila domin ya sāke juyowa zuwa ga sauranku, waɗanda kuka kuɓuta daga hannun sarakunan Assuriya.

7 Kada fa ku zama kamar kakanninku ko ‘yan’uwanku, marasa bangaskiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu, saboda haka ya maishe su kufai kamar yadda kuka gani.

8 Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.

9 Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, ‘yan’uwanku da ‘ya’yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”

10 Manzannin fa suka tafi gari gari a ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, har zuwa Zabaluna, amma suka yi musu dariyar raini, suka yi musu ba’a.

11 Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali’u, suka zo Urushalima.

12 Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.

13 Mutane da yawa kuwa suka zo Urushalima don su yi idin abinci marar yisti a wata na biyu, aka yi babban taro.

14 Sai suka kama aiki, suka kawar da bagadan da suke cikin Urushalima, da dukan bagadan ƙona turare suka kwashe suka zubar a kwarin Kidron.

15 Suka yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Suka sa firistoci da Lawiyawa su sha kunya, saboda haka sai suka tsarkake kansu, suka kawo hadayu na ƙonawa a Haikalin Ubangiji.

16 Sai suka ɗauki matsayinsu wanda aka ayyana bisa ga dokar Musa, mutumin Allah, firistocin suka yarfa jinin da suka karɓa daga hannun Lawiyawa.

17 Gama akwai waɗansu da yawa daga cikin taron waɗanda ba su tsarkake kansu ba, saboda haka ya zama tilas Lawiyawa su yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa saboda dukan wanda ba shi da tsarki, domin a tsarkake shi ga Ubangiji.

18 Gama akwai jama’a jingim, da yawa kuwa mutanen Ifraimu ne, da na Manassa, da na Issaka, da na Zabaluna, da ba su tsarkake kansu ba, duk da haka sun ci Idin Ƙetarewa ba yadda aka ƙayyade ba. Sai Hezekiya ya yi addu’a dominsu, yana cewa, “Ya Ubangiji mai alheri, ka gafarta wa ko wanne

19 wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko bai yi bisa kan dokar tsarkakewa na Wuri Mai Tsarki ba.”

20 Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya, ya warkar da jama’ar.

21 Jama’ar Isra’ila waɗanda suke a Urushalima kuwa sun yi idin abinci marar yisti da murna mai yawa, har kwana bakwai. Lawiyawa kuma da firistoci suka yabi Ubangiji kowace rana, suna raira waƙa da iyakar ƙarfinsu ga Ubangiji.

22 Hezekiya kuwa ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna fasaha a hidimar Ubangiji.

An Ƙara Yin Idin

Mutane fa suka ci abincin idin har kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta yin godiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu.

23 Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna.

24 Gama Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu bakwai (7,000), don yin hadayu, sarakuna kuma sun ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu goma (10,000). Firistoci da yawa suka tsarkake kansu.

25 Dukan taron Yahuza, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan taron jama’a da suka zo daga Isra’ila, da baƙi waɗanda suka zo daga ƙasar Isra’ila, da baƙin da suka zauna a Yahuza, suka yi murna.

26 Saboda haka an yi babban farin ciki a Urushalima, gama tun daga zamanin Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra’ila, ba a yi wani abu kamar haka a Urushalima ba.

27 Sai firistoci da Lawiyawa suka tashi suka sa wa jama’a albarka, aka kuwa ji muryarsu, addu’arsu kuma ta kai wurin zamansa a Sama.