Categories
2 TAR

2 TAR 31

Shirin Hezekiya domin Firistoci da Lawiyawa

1 Sa’ad da aka gama duka, sai dukan Isra’ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al’amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa’an nan dukan jama’ar Isra’ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.

2 Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi kashi, ko wanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima a ƙofofin Ubangiji, don su yi godiya da yabo.

3 Daga dukiyarsa kuma ya ba da taimako na abin yin hadayun ƙonawa, wato hadayun ƙonawa na safe da na maraice, da hadayun ƙonawa na ranakun Asabar, da na amaryar wata, da na ƙayyadaddun idodi, kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Ubangiji.

4 Hezekiya ya kuma umarci jama’ar da suke zaune a Urushalima su riƙa ba da rabon firistoci da na Lawiyawa, domin su mai da hankali ga dokar Ubangiji.

5 Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko’ina, sai jama’ar Isra’ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu.

6 Jama’ar Isra’ila da na Yahuza waɗanda suke zaune a garuruwan Yahuza, su ma sun kawo tasu zaka ta shanu, da ta tumaki, da ta abubuwan da aka keɓe aka kuma tsarkake domin Ubangiji Allahnsu, suka tara su tsibi tsibi.

7 A wata na uku ne suka fara tattara tsibi tsibin, suka gama a wata na bakwai.

8 Sa’ad da Hezekiya da sarakuna suka zo suka ga tsibi tsibin, sai suka yabi Ubangiji da jama’arsa Isra’ila.

9 Hezekiya kuma ya yi wa firistoci da Lawiyawa tambaya a kan tsibi tsibin.

10 Sai Azariya, babban firist na gidan Zadok, ya amsa masa, ya ce, “Tun lokacin da suka fara kawo sadakarsu a Haikalin Ubangiji, mun ci mun ƙoshi, abin da ya ragu kuwa yana da yawa, gama Ubangiji ya sa wa jama’arsa albarka, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”

11 Sai Hezekiya ya umarce su su shirya ɗakuna a Haikalin Ubangiji, suka kuwa shirya.

12 Da aminci suka kawo sadakokinsu, ta zaka da ta keɓaɓɓun abubuwa. Babban shugaban da yake lura da su kuwa, shi ne Konaniya, Balawe, da Shimai ɗan’uwansa, shi ne na biyu,

13 sa’an nan da Yehiyel, da Azaziya, da Nahat, da Asahel, da Yerimot, da Yozabad, da Eliyel, da Ismakiya, da Mahat, da Benaiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimai waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban Haikalin Allah suka naɗa.

14 Kore kuwa ɗan Imna Balawe, mai tsaron ƙofar gabas, yake lura da hadayu na yardar rai ga Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.

15 Eden, da Miniyamin, da Yeshuwa, da Shemaiya, da Amariya, da Shekaniya suna taimakonsa da zuciya ɗaya a biranen firistoci, don su rarraba wa ‘yan’uwansu rabonsu, tsofaffi da yara, duka ɗaya ne, bisa ga ƙungiyoyinsu,

16 da su kuma waɗanda aka rubuta bisa ga asali, ‘yan samari masu shekara uku zuwa sama, duk dai waɗanda za su shiga Haikalin Ubangiji don yin hidima, kamar yadda aka tsara, bisa ga matsayinsu yadda aka karkasa su.

17 Aka kuma rubuta firistoci bisa ga gidajen kakanninsu, na wajen Lawiyawa kuwa, tun daga mai shekara ashirin zuwa sama, bisa ga matsayinsu, ta yadda aka karkasa su.

18 Aka rubuta firistoci tare da dukan ƙananan ‘ya’yansu, da matansu, da ‘ya’yansu mata da maza, dukansu gaba ɗaya, gama da zuciya ɗaya suka tsarkake kansu.

19 Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa ‘ya’yan Haruna, firist, maza kuwa, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namiji da aka rubuta na Lawiyawa, nasa rabo.

20 Haka kuwa Hezekiya ya yi a dukan Yahuza, ya aikata abin da yake daidai, da aminci, a gaban Ubangiji Allahnsa.

21 Kowane irin aiki da ya kama na hidimar Haikalin Allah, wanda yake kuma bisa ga doka da umarni, na neman Allahnsa, ya yi su da zuciya ɗaya, ya kuwa arzuta.

Categories
2 TAR

2 TAR 32

Assuriyawa sun Yi Barazana ga Urushalima

1 Bayan waɗannan abubuwa, da waɗannan ayyukan aminci, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa Yahuza yaƙi, ya kafa sansani kewaye da garuruwa masu garu, yana zaton zai ci su da yaƙi su zama nasa.

2 Da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo da nufin ya yi yaƙi da Urushalima,

3 sai ya yi shawara shi da jarumawansa da manyan mutanensa, su datse ruwan da yake fitowa daga maɓuɓɓugar da suke bayan birni, suka kuwa taimake shi.

4 Don haka mutane da yawa suka taru suka daddatse dukan maɓuɓɓugai da rafuffuka da suke gudu cikin ƙasar, suna cewa, “Bari mu hana sarakunan Assuriya samun ruwa idan sun iso Urushalima.”

5 Sai ya kama aiki gadangadan, ya sāke gina dukan garukan da suka rushe, ya gina hasumiya a kai, ya kuma gina wani garu bayan wannan, ya ƙara ƙarfin Millo a birnin Dawuda, ya kuma yi makamai na yaƙi da garkuwoyi masu yawan gaske.

6 Sai ya sa manyan sojoji su shugabanci jama’a. Su tattaro su gare shi a dandalin ƙofar birni, ya yi musu magana ta ƙarfafawa ya ce,

7 “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda Sarkin Assuriya, da dukan taron da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.

8 Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza.

9 Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa’an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa,

10 “Ga abin da Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya ce, ‘Ga me kake dogara, da har yanzu kuka dāge a cikin Urushalima, ga shi kuwa, yaƙi ya kewaye ta?

11 Ai, Hezekiya, ba ruɗinku yake yi ba, don ya sa ku mutu da yunwa da ƙishi sa’ad da yake ce muku Ubangiji Allahnku zai cece ku daga hannun Sarkin Assuriya?

12 Ashe, ba wannan Hezekiya ba ne ya ɗauke masujadansa da bagadansa, ya kuma umarci Yahuza da Urushalima, su yi sujada a gaban bagade guda, a kansa ne kuma za su ƙona hadayu?

13 Ashe, ba ku san abin da ni da kakannina muka yi wa dukan jama’ar waɗansu ƙasashe ba? Gumakan al’umman waɗannan ƙasashe sun iya ceton ƙasashensu daga hannuna?

14 Daga cikin dukan gumakan waɗannan al’ummai waɗanda kakannina suka hallakar da su sarai, ba wanda ya iya ceton jama’arsa daga hannuna, har da Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?

15 Yanzu fa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, ko ya ɓad da ku haka, kada kuwa ku gaskata shi, gama ba wani gunki na wata al’umma, ko wani mulki wanda ya taɓa ceton jama’arsa daga hannuna, ko kuma daga hannun kakannina. Wane Allah naku har da zai iya cetonku daga hannuna?’ ”

16 Barorinsa kuwa suka ƙara yin maganganun saɓo gāba da Ubangiji Allah da bawansa Hezekiya.

17 Ya kuma rubuta wasiƙu, ya zargi Ubangiji Allah na Isra’ila, ya yi maganar saɓo, yana cewa, “Kamar yadda gumakan al’umman sauran ƙasashe suka kāsa ceton jama’arsu daga hannuna, haka nan kuma Allahn Hezekiya ba zai iya ceton jama’arsa daga hannuna ba.”

18 Da babbar murya, da Yahudanci kuwa, suka yi ta yin magana da jama’ar Urushalima waɗanda suke kan garu, don a tsoratar da su, a kuma firgita su, don su ci birnin.

19 Suka yi ta magana a kan Allah na Urushalima, kamar yadda suka yi magana a kan gumakan al’ummai, wato aikin hannuwan mutane.

Ubangiji Ya Ceci Hezekiya

20 Sai sarki Hezekiya, da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu’a saboda wannan al’amari, suka yi kuka zuwa Sama.

21 Ubangiji kuwa ya aiki mala’ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa’ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin ‘ya’yan cikinsa suka kashe shi da takobi.

22 Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mazaunan Urushalima daga hannun Sennakerib Sarkin Assuriya, daga kuma hannun dukan maƙiyansa, ya hutar da su ta kowace fuska.

23 Mutane da yawa suka kawo wa Ubangiji sadakoki a Urushalima, suna kuma kawo wa Hezekiya Sarkin Yahuza abubuwa masu daraja. Saboda haka ya sami ɗaukaka a idon dukan sauran al’ummai, tun daga wannan lokaci har zuwa gaba.

Hezekiya Ya Yi Ciwo

24 A kwanakin nan kuwa Hezekiya ya yi ciwo gab da mutuwa, sai ya yi addu’a ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ya ba shi alama.

25 Amma Hezekiya bai nuna godiya a kan amfanin da ya samu ba, saboda girmankai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuza da Urushalima.

26 Amma Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda girmankan da ya yi, shi da mazaunan Urushalima, saboda haka hasalar Ubangiji ba ta faɗa musu a kwanakin Hezekiya ba.

Hezekiya ya Karɓi ‘Yan Saƙo daga Babila

27 Hezekiya yana da dukiya ƙwarai, yana kuma da girma. Sai ya gina wa kansa taskoki inda zai ajiya azurfa, da zinariya, da duwatsu masu daraja, da kayan yaji, da garkuwoyi, da dukan tasoshi, da kwanoni masu daraja.

28 Yana kuma da ɗakunan ajiya na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai. Yana da wuraren turke shanu na kowane iri, yana kuma da garkunan tumaki.

29 Ya kuma giggina wa kansa birane, yana da garkunan tumaki da na awaki, da na shanu a yalwace. Gama Allah ya mallakar masa da abubuwa masu yawa.

30 Hezekiyan nan kuwa ya datse ruwan da yake gangarawa daga kogin Gihon, ya karkatar da su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dawuda. Hezekiya ya arzuta da dukan ayyukan da ya yi.

31 A kan ‘yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al’ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.

Mutuwar Hezekiya

32 Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, ga shi, an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a littafin sarakunan Yahuza da na Isra’ila.

33 Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin ‘ya’yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 TAR

2 TAR 33

Sarki Manassa na Yahuza

1 Manassa yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana mulki a Urushalima.

2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya yi irin ayyukan banƙyama da al’ummai waɗanda Ubangiji ya kore su a gaban jama’ar Isra’ila suke yi.

3 Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba’al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu.

4 Ya kuma giggina bagadai a cikin Haikalin Ubangiji inda Ubangiji ya ce, “A Urushalima sunana zai kasance har abada.”

5 Ya giggina bagadai ga dukan rundunar sama a farfajiyan nan biyu na cikin Haikalin Ubangiji.

6 Ya miƙa ‘ya’yansa maza hadaya ta ƙonawa a kwarin ɗan Hinnom. Ya yi bokanci, ya yi duba, ya yi tsubbu, yana kuma sha’ani da makarai da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji.

7 Sai ya kafa gunkin da ya yi a cikin Haikalin Allah, wanda Allah ya faɗa wa Dawuda da ɗansa Sulemanu ya ce, “A cikin wannan Haikali da a Urushalima, inda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra’ila, zan sa sunana har abada.

8 Ba zan ƙara fitar da Isra’ila daga ƙasar da na ba kakanninku ba, in dai sun lura, sun kiyaye, sun aikata dukan abin da na umarce su, da dukan shari’a, da dokoki, da ka’idodi da aka bayar ta hannun Musa.”

9 Ta haka kuwa Manassa ya lalatar da Yahuza da mazaunan Urushalima. Suka aikata muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama’ar Isra’ila.

Tuban Manassa

10 Ubangiji fa ya yi magana da Manassa da jama’arsa, amma ba wanda ya kula.

11 Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.

12 Amma sa’ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.

13 Sa’ad da ya yi addu’a gare shi, Allah ya karɓi roƙonsa da hurwarsa, ya sāke komar da shi Urushalima da mulkinsa. Sa’an nan ne Manassa ya sani Ubangiji shi ne Allah.

14 Bayan haka sai ya gina garu a bayan garin Dawuda a yammacin Gihon, a kwari har zuwa Ƙofar Kifi, ya kewaye da shi zuwa Ofel, ya gina shi da tsayi sosai. Sa’an nan ya sa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuza.

15 Ya kwashe gumaka da siffofi daga cikin Haikalin Ubangiji, da dukan bagadan da ya giggina a bisa dutse na Haikalin Ubangiji da a Urushalima. Ya zubar da su a bayan birnin.

16 Ya kuma komar da bagaden Ubangiji, ya miƙa hadayu na salama da na godiya, ya kuma umarci Yahuza ta bauta wa Ubangiji Allah na Isra’ila.

17 Duk da haka dai jama’a suka ci gaba da miƙa hadayunsu a masujadai, amma ga Ubangiji Allahnsu kaɗai.

Ƙarshen Mulkin Manassa

18 Sauran ayyukan Manassa, da addu’o’insa zuwa ga Allahnsa, da abubuwan da masugani suka faɗa sa’ad da suka yi masa magana da sunan Ubangiji Allah na Isra’ila, suna cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

19 Addu’arsa, da yadda Allah ya karɓi roƙonsa, da dukan zunubinsa, da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujadai, ya kafa Ashtarot da siffofi, kafin ya ƙasƙantar da kansa, suna nan a rubuce a littafin Hozai.

20 Haka fa Manassa ya rasu, suka binne shi a gidansa, sai Amon ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

Sarki Amon na Yahuza

21 Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara biyu yana mulki a Urushalima.

22 Shi ma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Manassa, tsohonsa, ya yi. Amon ya miƙa hadaya ga dukan siffofin da tsohonsa, Manassa, ya yi ya bauta musu.

23 Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji yadda tsohonsa, Manassa, ya yi ba, amma shi Amon ya yi ta yin zunubi a kai a kai.

24 Sai fadawansa suka yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.

25 Jama’ar ƙasar kuwa suka karkashe dukan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar, suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gāji gadon sarautarsa.

Categories
2 TAR

2 TAR 34

Sarki Yosiya na Yahuza

1 Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima.

2 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yana bin al’amuran da kakansa Dawuda ya yi, bai kauce dama ko hagu ba.

Yosiya Yana Gāba da Arnanci

3 A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi.

4 Sai suka farfashe bagadai na Ba’al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu.

5 Ya kuma ƙone ƙasusuwan firistoci a bisa bagadansu, ya tsarkake Yahuza da Urushalima.

6 A biranen Manassa, da na Ifraimu, da na Saminu, har zuwa Naftali, a kangwayensu kewaye da su,

7 ya farfashe bagadai, ya buge Ashtarot da siffofi, ya maishe su gari, ya tumɓuke dukan bagadan ƙona turare a dukan ƙasar Isra’ila, sa’an nan ya koma Urushalima.

An Gano Littafin Shari’a

8 A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan da ya gama tsarkake ƙasar, da Haikalin, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, da Ma’aseya mai mulkin birnin, da Yowa ɗan Yowahaz, wanda suke magatakarda domin su gyara Haikalin Ubangiji Allahnsa.

9 Sai suka zo wurin Hilkiya babban firist, suka ba shi kuɗin da aka kawo a Haikalin Allah, wanda Lawiyawa, masu tsaron ƙofa, suka tattara daga mutanen Manassa da na Ifraimu, daga sauran Isra’ila, da kuma na dukan Yahuza da Biliyaminu, tare da na mazaunan Urushalima.

10 Sai suka ba da kuɗin ga ma’aikata masu lura da Haikalin Ubangiji, da ma’aikatan da suke aiki a Haikalin Ubangiji, don gyare-gyare, su maishe shi kamar yadda yake dā,

11 sai suka ba masassaƙa da magina kuɗin, don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katako, don yin tsaiko da tankar gine-ginen da sarakunan Yahuza suka bari, har suka lalace.

12 Mutanen fa suka yi aiki mai aminci tare da waɗanda suke lura da su domin su gabatar da aiki, wato Yahat da Obadiya, Lawiyawa, ‘ya’yan Merari, maza, da Zakariya da Meshullam na wajen ‘ya’yan Kohatawa, da waɗansu Lawiyawa da suke da gwanintar bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe.

13 Su ne shugabannin masu ɗaukar kaya, suke kuma nuna wa kowane ma’aikaci irin aikin da zai yi, waɗansu daga cikin Lawiyawa, magatakarda ne, da ma’aikatan hukuma, da masu tsaron ƙofofi.

14 Sa’ad da suke fitowa da kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya gāno littafin Shari’ar Ubangiji wanda aka bayar ta hannun Musa.

15 Sai Hilkiya ya ce wa magatakarda Shafan, “Na gāno Littafin Shari’a a Haikalin Ubangiji.” Sai Hilkiya ya ba Shafan littafin.

16 Shafan kuma ya kai wa sarki littafin, sa’an nan ya faɗa wa sarki cewa, “Dukan abin da aka sa barorinka su yi suna yi.

17 Sai suka juye kuɗin da aka samu don Haikalin Ubangiji, suka miƙa wa masu lura da aikin, da ma’aikatan.”

18 Magatakarda Shafan kuwa ya faɗa wa sarki, ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta wa sarki littafin.

19 Da sarki ya ji irin maganganun da littafin ya faɗa, sai ya yayyage tufafinsa.

20 Sa’an nan sarki ya umarci Hilkiya, da Ahikan ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mika, da magatakarda Shafan, da Asaya baran sarki, ya ce,

21 “Ku tafi ku yi tambaya a wurin Ubangiji domina, da kuma domin sauran waɗanda suka ragu a Isra’ila da Yahuza, a kan abin da littafin da aka gāno ya faɗa, gama Ubangiji ya yi fushi da mu da hasala mai tsanani saboda kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji, su aikata bisa ga dukan abin da aka faɗa a wannan littafi ba.”

22 Hilkiya kuwa tare da waɗanda sarki ya aika suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, ɗan Harhas, mai lura da wurin ajiyar tufafi, tana zaune a Urushalima, a unguwa ta biyu. Suka faɗa mata saƙon sarki,

23 sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ce in faɗa wa mutumin da ya aiko gare shi,

24 ‘Ni Ubangiji, na ce zan kawo masifa a kan wannan wuri da a kan mazaunan wurin, wato dukan la’anar da aka rubuta a littafin da aka karanta a gaban Sarkin Yahuza.

25 Da yake sun bar bina suka ƙona turare ga gumaka domin su sa ni in yi fushi da dukan ayyukan hannuwansu, saboda haka zan yi fushi da wannan wuri, ba kuwa zan huce ba.’

26 Amma a kan Sarkin Yahuza wanda ya aike ku ku tambayi Ubangiji, ga abin da za ku faɗa masa, ‘Ni Ubangiji, Allah na Isra’ila na ce, a kan maganar da ka ji,

27 da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah, sa’ad da ka ji maganarsa a kan wurin nan da mazaunan wurin, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yayyage tufafinka ka yi kuka a gabana, ni kuma na ji ka.

28 Ga shi, zan kai ka wurin da kakanninka suke, a kabarinka a binne ka da salama, ba za ka ga dukan masifun da zan kawo wa wurin nan da mazaunansa ba.’ ”

Sai suka isar da amsa wurin sarki.

Yosiya Ya Kawar da Arnanci

29 Sarki ya aika a kirawo dukan dattawan Yahuza da na Urushalima.

30 Sai sarki ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan jama’a, babba da yaro. Sai ya karanta dukan maganar da take a littafin alkawari wanda aka gāno a Haikalin Ubangiji, a kunnen dukansu.

31 Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya yi alkawari a gaban Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji, ya kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai yi aiki da alkawarin da yake rubuce a wannan littafi.

32 Ya kuma sa dukan waɗanda suke a Urushalima da na Biliyaminu, su tsaya a kan wannan magana. Mazaunan Urushalima kuwa suka yi yadda alkawarin Allah ya ce, wato Allah na kakanninsu.

33 Yosiya kuwa ya kawar da dukan abubuwan banƙyama daga dukan ƙasar da jama’ar Isra’ila suke da ita. Ya sa dukan waɗanda suke a Isra’ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. A dukan kwanakin ransa, ba su kauce daga bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.

Categories
2 TAR

2 TAR 35

Yosiya Ya Yi Idin Ƙetarewa

1 Yosiya kuwa ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima. A rana ta goma sha huɗu ga wata na fari suka yanka ragon Idin Ƙetarewa.

2 Ya sa firistoci a matsayinsu, ya ƙarfafa su a hidimar Haikalin Ubangiji.

3 Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra’ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra’ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama’arsa Isra’ila.

4 Ku karkasa kanku bisa ga gidajen kakanninku ƙungiya ƙungiya, ku bi bayanin Dawuda, Sarkin Isra’ila, da na ɗansa Sulemanu.

5 Ku tsaya a Wuri Mai Tsarki, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin ‘yan’uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa.

6 Ku yanka abin Idin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku shirya wa ‘yan’uwanku su yi bisa ga maganar Ubangiji ta hannun Musa.”

7 Sarki Yosiya fa ya ba da gudunmawar abin yin hadaya ga waɗanda ba firistoci ba, waɗanda suke wurin, raguna da ‘yan awaki daga cikin garken tumaki da na awaki, yawansu ya kai dubu talatin (30,000) da kuma bijimai dubu uku (3,000). Waɗannan duk daga mallakar sarki ne.

8 Da yardar rai manyan ma’aikatansa, sarakunansa, suka ba da gudunmawa ga jama’ar, da firistoci, da Lawiyawa. Hilkiya, da Zakariya, da Yehiyel, manyan ma’aikatan Haikalin Allah, suka ba firistoci abin yin hadaya don Idin Ƙetarewa, tumaki da awaki dubu biyu da ɗari shida (2,600), da bijimai ɗari uku.

9 Konaniya kuma tare da Shemaiya da Netanel, ‘yan’uwansa, da Hashabiya, da Yehiyel, da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, su suka ba Lawiyawa abin yin hadayar Idin Ƙetarewa, raguna da ‘yan awaki dubu biyar (5,000), da bijimai ɗari biyar.

10 Sa’ad da aka shirya yin hidimar, firistoci suka tsaya a wurinsu, Lawiyawa kuwa suka tsaya bisa ga ƙungiyoyinsu, yadda sarki ya umarta.

11 Sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewar. Sa’an nan firistoci suka karɓi jinin daga gare su, suka yayyafa, Lawiyawa kuma suka yi ta fiɗa.

12 Sa’an nan suka keɓe hadayu na ƙonawa domin su rarraba bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakanni waɗanda su ba firistoci ba ne, don su miƙa wa Ubangiji kamar yadda aka rubuta a littafin Musa. Haka nan kuma suka yi da bijiman.

13 Suka gasa ragon hadayar Idin Ƙetarewa bisa ga ka’idar, sai suka dafa tsarkakan hadayu a tukwane, da manyan tukwane, da kwanoni, nan da nan suka kai wa waɗanda ba firistoci ba.

14 Daga baya kuma suka shirya wa kansu da firistoci, saboda firistoci, ‘ya’yan Haruna, maza, suna ta hidimar miƙa hadayu na ƙonawa, da kuma na kitse, har dare. Don haka Lawiyawa suka shirya wa kansu abinci, suka kuma shirya wa firistoci, ‘ya’yan Haruna, maza.

15 Mawaƙa, ‘ya’yan Asaf, maza, suna wurinsu bisa ga umarnin Dawuda, da Asaf, da Heman, da kuma Yedutun maigani na sarki, matsaran ƙofofi kuma suna a kowace ƙofa, ba lalle sai su bar wurin hidimarsu gama ‘yan’uwansu Lawiyawa sun shirya musu nasu.

16 Haka fa aka shirya dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Idin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda Yosiya sarki ya umarta.

17 Jama’ar Isra’ila waɗanda suke wurin, suka kiyaye Idin Ƙetarewa, da kuma idin abinci marar yisti har kwana bakwai.

18 Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa irin wannan ba tun kwanakin annabi Sama’ila, ba wani kuma daga cikin sarakunan Isra’ila da ya kiyaye Idin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya kiyaye shi tare da firistoci, da Lawiyawa, da dukan mutanen Yahuza da na Isra’ila, waɗanda suke a wurin, da kuma mazaunan Urushalima.

19 A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya aka yi Idin Ƙetarewa.

Rasuwar Yosiya

20 Bayan wannan duka, sa’ad da Yosiya ya shirya Haikali, sai Neko Sarkin Masar, ya zo don ya yi yaƙi a Karkemish wadda take a Yufiretis, sai Yosiya ya fito don ya kara da shi.

21 Amma Neko ya aika ‘yan saƙo su faɗa masa su ce, “Me ya gama mu da juna, ya Sarkin Yahuza? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da Sarkin Assuriya! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada ya hallaka ka.”

22 Duk da haka Yosiya bai yarda ya koma ba, sai ya ɓad da kama don ya yi yaƙi da shi. Bai yarda da magana wadda Allah ya faɗa wa Neko ba, sai suka kama yaƙi a filin Magiddo.

23 Maharba suka harbi sarki Yosiya, sai ya ce wa barorinsa, “Ku ɗauke ni ku tafi da ni, gama an yi mini mummunan rauni.”

24 Barorinsa kuwa suka ɗauke shi daga cikin karusa, suka sa shi a karusa ta biyu, suka kawo shi Urushalima, sai ya rasu. Aka binne shi a hurumin kakanninsa. Yahuza da Urushalima fa suka yi makoki domin Yosiya.

25 Irmiya kuma ya hurta makoki domin Yosiya. Haka nan kuma dukan mawaƙa mata da maza, suka ambaci Yosiya cikin makokinsu har yau. Suka sa waɗannan su zama farali a Isra’ila, ga shi kuma, an rubuta su a Littafin Makoki.

26 Sauran ayyukan Yosiya, da kyawawan ayyukansa, waɗanda ya yi bisa ga abin da aka rubuta a Shari’ar Ubangiji,

27 ayyukansa na fari da na ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuza.

Categories
2 TAR

2 TAR 36

Sarki Yehowahaz na Yahuza

1 Jama’ar ƙasa kuwa suka ɗauki Yehowahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki. Ya gaji tsohonsa a Urushalima.

2 Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima wata uku.

3 Sai Sarkin Masar ya tuɓe shi daga sarautarsa ta Urushalima, ya sa su biya gandu, su ba da azurfa talanti ɗari, da zinariya talanti guda.

4 Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwansa, sarki a Yahuza da Urushalima. Ya sa masa sabon suna Yehoyakim. Amma Neko ya ɗauko Yehowahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai shi Masar.

Sarki Yehoyakim na Yahuza

5 Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa.

6 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya ɗaure shi da sarƙoƙi, ya kai shi Babila.

7 Nebukadnezzar kuma ya kwaso waɗansu tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya kai Babila, ya ajiye su a fādar Babila.

8 Sauran ayyukan Yehoyakim da irin abubuwan da ya yi na banƙyama, da irin laifofinsa, suna nan, an rubuta su a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuza. Ɗansa Yekoniya kuwa ya gāji gadon sarautarsa.

An Kama Sarki Yekoniya

9 Yekoniya yana da shekara takwas sa’ad da ya ci sarauta, ya yi sarauta a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.

10 Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan’uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.

Sarki Zadakiya na Yahuza

11 Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima.

12 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. Bai nuna ladabi a gaban annabi Irmiya ba, wanda ya faɗa masa abin da Ubangiji ya ce.

Fāɗuwar Urushalima

13 Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra’ila.

14 Dukan manyan firistoci da sauran jama’a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al’ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima.

15 Sai Ubangiji, Allah na kakanninsu, ya yi ta aika musu da manzanni saboda yana juyayin jama’arsa da wurin zaman zatinsa.

16 Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba’a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba’a, sai Ubangiji ya husata da jama’arsa don abin ya kai intaha.

An Kai Yahuza Bautar Talala

17 Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.

18 Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila.

19 Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja.

20 Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na ‘ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa,

21 don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba’in, ta kiyaye asabatai.

22 Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.

23 Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da suke nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.”