Categories
A.M.

A.M. 1

Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki

1 Ya Tiyofalas, tarihin nan na farko wanda na rubuta, ya shafi dukan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa,

2 har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.

3 Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba’in, yana zancen al’amuran Mulkin Allah.

4 Sa’ad da yake tare da su, ya umarce su kada su tashi daga Urushalima, amma su jira cikar alkawarin nan da Uba ya yi, “wanda kuka ji daga bakina,

5 domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin ‘yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”

An Ɗauke Almasihu Sama

6 Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra’ila mulki?”

7 Ya ce musu, “Sanin lokatai da zamanai, da Uba ya sa cikin ikonsa, ba naku ba ne.

8 Amma za ku sami iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”

9 Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba.

10 Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi.

11 Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”

Wanda Ya Karɓi Matsayin Yahuza

12 Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da ake kira Dutsen Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya.

13 Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.

14 Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu’a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma ‘yan’uwansa.

15 To, a kwanakin nan Bitrus ya miƙe tsaye cikin ‘yan’uwa, (wajen mutum ɗari da ashirin ne a taron), ya ce,

16 “Ya ku ‘yan’uwana, lalle ne a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya faɗa a dā ta bakin Dawuda a game da Yahuza, wanda ya yi wa masu kama Yesu jagaba.

17 Don an lasafta shi cikinmu dā, an kuma ba shi tasa hidima cikin aikin nan.

18 (To, shi mutumin nan, da ladan mugun aikinsa ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kā, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo.

19 Wannan abu fa ya zama sananne ga dukan mazaunan Urushalima, har ake kiran filin Akaldama da harshensu, wato filin jini.)

20 Domin a rubuce yake a Zabura cewa,

‘Gidansa yă zama yasasshe,

Kada kowa ya zauna a ciki.’

Da kuma,

‘Matsayinsa wani yă gada.’

21 Don haka, lalle wani daga cikin mutanen nan da suke tare da mu, duk lokacin da Ubangiji Yesu yake cuɗanya da mu,

22 tun daga baftismar da Yahaya ya yi, har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi daga wurinmu aka kai shi zuwa Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.”

23 Sai suka nuna mutum biyu, Yusufu mai suna Barsaba, wanda aka yi wa laƙabi da Yustus, da kuma Matiyas.

24 Sai suka yi addu’a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa,

25 yă karɓi matsayi cikin aikin nan da manzancin nan da Yahuza ya bauɗe wa, don yă cike gurbinsa.”

26 Sai suka yi musu kuri’a, Matiyas ya ci, aka kuma sa shi a cikin manzannin nan goma sha ɗaya.

Categories
A.M.

A.M. 2

Zuwan Ruhu Mai Tsarki

1 Da ranar Fentikos ta yi, duk suna tare a wuri ɗaya,

2 farat ɗaya, sai aka ji wani amo daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan da suke zaune.

3 Sai waɗansu harsuna kamar na wuta suka bayyana a gare su, suna rarrabuwa, suna sassauka a kan ko wannensu.

4 Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.

5 To, a Urushalima a lokacin, akwai waɗansu Yahudawa masu bautar Allah daga ko’ina cikin ƙasashen duniya.

6 Da jin dirin nan kuwa, taron ya haɗe, ya ruɗe, domin ko wannensu ya ji suna magana da bakin garinsu.

7 Sai suka yi al’ajabi suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne?

8 Ƙaƙa kuwa ko wannenmu yake ji da bakin garinsu ake magana?

9 Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,

10 da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci,

11 da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manyan al’amuran Allah da bakunan garuruwanmu.”

12 Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?”

13 Amma waɗansu suka yi ba’a suka ce, “Ruwan inabi suka sha suka yi tatul!”

Jawabin Bitrus a Ranar Fentikos

14 Amma Bitrus ya miƙe tare da sha ɗayan nan, ya ɗaga murya ya yi musu jawabi, ya ce, “Ya ku ‘yan’uwana Yahudawa da dukan mazaunan Urushalima, ku kula da wannan, ku kuma saurari maganata.

15 Ai, mutanen nan ba bugaggu ba ne yadda kuke zato, tun da yake yanzu ƙarfe tare na safe ne kawai.

16 Wannan, ai, shi ne abin da Annabi Yowel ya faɗa cewa,

17 ‘Allah ya ce,

A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan ‘yan adam Ruhuna.

‘Ya’yanku mata da maza za su yi annabci,

Wahayi zai zo wa samarinku,

Dattawanku kuma za su yi mafarkai.

18 Hakika, har ma a kwanakin nan zan zubo Ruhuna a kan bayina mata da maza,

Za su kuma yi annabci.

19 Zan nuna abubuwan al’ajabi a sararin sama,

Da mu’ujizai a nan ƙasa,

Wato jini, da wuta, da kuma, hauhawan hayaƙi.

20 Za a mai da rana duhu,

Wata kuma jini,

Kafin Ranar Ubangiji ta zo,

Babbar ranar nan mai girma.

21 A sa’an nan ne zai zamanto kowa ya yi addu’a da sunan Ubangiji zai sami ceto.’

22 “Ya ku ‘yan’uwa, Isra’ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu’ujizai, da abubuwan al’ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani,

23 shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.

24 Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, domin ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.

25 Dawuda kuma ya yi faɗi a game da shi ya ce,

‘Kullum hankalina yana kan Ubangiji,

Yana damana, domin kada in jijjigu.

26 Saboda haka, zuciyata ta yi fari, ina farin ciki matuƙa.

Ko da yake kuma ni jiki ne, zan zauna ina sa zuciya,

27 Domin ba za ka yar da raina a Hades ba,

Ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.

28 Kā sanar da ni hanyoyin rai.

Za ka cika ni da farin ciki ta zamana a zatinka.’

29 Ya ‘yan’uwa, na iya yi muku magana da amincewa a game da kakanmu Dawuda, cewa ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan gare mu har ya zuwa yau.

30 To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa,

31 sai ya hango, ya kuma yi faɗi a kan tashin Almasihu daga matattu, cewa ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba.

32 Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka.

33 Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji.

34 Ai, ba Dawuda ne ya hau Sama ba, amma shi kansa ya ce,

‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

Zauna a damana,

35 Sai na sa ka take maƙiyanka.’

36 “Don haka sai duk jama’ar Isra’ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”

37 To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “’Yan’uwa, me za mu yi?”

38 Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,

39 domin alkawarin nan ku aka yi wa, ku da ‘ya’yanku, da kuma dukan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira.”

40 Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku tsirar da kanku daga wannan karkataccen zamani.”

41 Waɗanda suka ya na’am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.

42 Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu’a.

Yadda Zaman Masu Bi Yake

43 Sai tsoro ya kama kowa, aka kuma yi abubuwan al’ajabi da mu’ujizai da yawa ta wurin manzannin.

44 Dukan masu ba da gaskiya suna tare, suna mallakar kome nasu gaba ɗaya.

45 Suka sayar da mallakarsu da kayansu, suka rarraba wa kowa kuɗin, gwargwadon bukatarsa.

46 Kowace rana kuma sukan riƙa zuwa Haikali da nufi ɗaya, suna gutsuttsura gurasa a gidajensu, suna cin abinci da farin ciki ƙwarai, rai kwance,

47 suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.

Categories
A.M.

A.M. 3

An Warkar da Gurgu a Ƙofar Haikali

1 To, Bitrus da Yahaya suna tafiya Haikali a lokacin addu’a, da ƙarfe uku na yamma,

2 sai ga wani mutum da aka haifa gurgu, ana ɗauke da shi. Kowace rana kuwa akan ajiye shi a ƙofar Haikali, wadda ake kira Ƙawatacciyar Ƙofa, don ya roƙi sadaka ga masu shiga Haikali.

3 Da ganin Bitrus da Yahaya suna shiga Haikalin, ya roƙe su sadaka.

4 Bitrus kuwa ya zuba masu ido, tare da Yahaya, ya ce, “Dube mu.”

5 Sai kuwa duk hankalinsa ya koma a kansu, da tsammanin samun wani abu a gunsu.

6 Amma Bitrus ya ce, “Kuɗi kam, ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. Da sunan Yesu Almasihu Banazare, yi tafiya.”

7 Sai Bitrus ya kama hannunsa na dama, ya tashe shi. Nan tāke ƙafafunsa da wuyan sawunsa suka yi ƙarfi.

8 Wuf, sai ya zabura, ya miƙe tsaye, ya fara tafiya, ya shiga Haikalin tare da su, yana tafe, yana tsalle, yana kuma yabon Allah.

9 Duk mutane suka gan shi yana tafe yana yabon Allah.

10 Suka kuwa gane shi ne mai zama a bakin Ƙawatacciyar Ƙofa ta Haikali yana bara. Sai mamaki ya kama su, suna al’ajabi ƙwarai a kan abin da aka yi masa.

Jawabin Bitrus a Shirayin Sulemanu

11 Tun yana riƙe da Bitrus da Yahaya, duk jama’a suka sheƙa a guje zuwa wurinsu a cikin shirayin da ake kira Shirayin Sulemanu, suka ruɗe don mamaki.

12 Da Bitrus ya ga haka, sai ya yi wa jama’a jawabi, ya ce, “Ya ku ‘yan’uwa Isra’ilawa, don me kuke mamakin wannan? Don me kuma kuke ta dubanmu, sai ka ce da ikon kanmu ne, ko kuwa don ibadarmu muka sa shi tafiya?

13 Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi, a gaban Bilatus, sa’ad da ya ƙudura zai sake shi.

14 Amma ku kuka ƙi Mai Tsarkin nan, mai adalci kuka roƙa a saukar muku da mai kisankai,

15 kuka kuwa kashe Tushen Rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga haka.

16 To, sunansa ne, wato ta wurin bangaskiya ga sunansa, shi ne ya ba mutumin nan da kuke gani, kuka kuma sani, ƙarfi. Hakika, bangaskiyar da take ta wurin Yesu ita ta ba mutumin nan cikakkiyar lafiya, a gaban idonku duka.

17 “To, yanzu ‘yan’uwa, na sani da jahilci kuka yi haka, kamar yadda shugabanninku ma suka yi.

18 Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa Almasihunsa zai sha wuya.

19 Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,

20 ya kuma aiko da Almasihun da aka ƙaddara muku tun dā, wato Yesu,

21 wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.

22 Musa ma ya ce, ‘Ubangiji Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin ‘yan’uwanku, kamar yadda ya tashe ni. Lalle ne ku saurari duk abin da ya faɗa muku.

23 Zai zamana kuma duk wanda ya ƙi sauraron annabin nan, za a hallaka shi daga cikin jama’a.’

24 Hakika dukan annabawa da suka yi annabci, wato tun daga kan Sama’ila da waɗanda suka zo daga baya, duk sun yi faɗi a kan waɗannan kwanakin.

25 Ku ne tsatson annabawa, ku ne kuma magadan alkawarin da Allah ya yi wa kakanninku, da ya ce wa Ibrahim, ‘Ta zuriyarka ne za a yi wa dukkan kabilan duniya albarka.’

26 Da Allah ya taso da Baransa, gare ku ne ya fara aiko shi, don yă yi muku albarka ta juyo da ko wannenku ga barin muguntarsa.”

Categories
A.M.

A.M. 4

Bitrus da Yahaya a gaban ‘Yan Majalisa

1 Suna cikin yin magana da jama’a sai firistoci da shugaban dogaran Haikali da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukar musu,

2 don suna koya wa jama’a, suna tabbatar da tashi daga matattu, suna misali da Yesu.

3 Sai suka kama su, suka sa su a gidan waƙafi kafin gobe, don magariba ta riga ta yi.

4 Amma da yawa daga cikin waɗanda suka ji wa’azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.

5 Kashegari shugabanninsu da dattawansu da malamansu na Attaura suka taru a Urushalima,

6 tare da Hanana, babban firist, da Kayafa, da Yahaya, da Iskandari, da kuma duk waɗanda suke dangin babban firist.

7 Da suka tsai da su a tsakiya, suka tuhume su, suka ce, “Da wane iko ne, ko kuwa da wane suna ne, kuka yi haka?”

8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce musu, “Ya ku shugabannin jama’a, da dattawa,

9 in dai ana tuhumarmu ne yau a kan alherin da aka yi wa gajiyayyen mutumin nan, ta yadda aka warkar da shi,

10 to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama’ar Isra’ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.

11 Wannan shi ne dutsen nan da ku magina kuka raina, shi ne kuwa ya zama mafificin dutsen gini.

12 Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”

13 To, da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yahaya, suka kuma gane marasa ilimi ne, talakawa kuma, suka yi mamaki, suka kuwa shaida su, a kan dā suna tare da Yesu.

14 Amma da suka ga mutumin nan da aka warkar ɗin yana tsaye tare da su, suka rasa hanyar yin mūsu.

15 Bayan sun umarce su, su fita daga majalisa, suka yi shawara da juna,

16 suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu’ujiza ta wurinsu, ba mu kuwa da halin yin mūsawa.

17 Amma don kada abin ya ƙara bazuwa a cikin mutane, sai mu yi musu kashedi, kada su kuskura su ƙara yi wa kowa magana, suna kama wannan suna.”

18 Sai suka kirawo manzannin, suka kwaɓe su, kada su kuskura su yi wa kowa magana, ko su ƙara koyarwa suna kama sunan Yesu.

19 Amma Bitrus da Yahaya suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani.

20 Domin mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.”

21 Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama’a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.

22 Mutumin nan da aka yi wa mu’ujizar nan ta warkarwa kuwa ya ba shekara arba’in baya.

Masu Bi Sun Yi Addu’a Su Yi Magana Gabagaɗi

23 Da aka sau su, suka tafi wurin mutanensu, suka ba su labarin duk abin da manyan firistoci da shugabanni suka faɗa musu.

24 Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,

25 wanda ta Ruhu Mai Tsarki, ta bakin kakanmu Dawuda baranka, ka ce,

‘Don me al’ummai suka husata?

Kabilai kuma suka yi makidar al’amuran wofi?

26 Sarakunan duniya sun kafa dāga,

Mahukunta kuma sun haɗa kai,

Suna gāba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.’

27 Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al’ummai da jama’ar Isra’ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.

28 Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.

29 Yanzu kuma ya Ubangiji, dubi wannan kashedin nasu, ka yi wa bayinka baiwar yin maganarka da iyakar ƙarfin hali,

30 kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi albarkacin sunan Baranka mai tsarki Yesu.”

31 Bayan sun yi addu’a, wurin da suke a tattare ya raurawa. Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta faɗar maganar Allah gabagaɗi.

Kome na ‘Yan Ikkilisiya Ɗaya Ne

32 To, duk taron da suka ba da gaskiya kuwa nufinsu ɗaya ne, ra’ayinsu ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai kome nasu ne baki ɗaya.

33 Manzanni kuma suka yi shaida da tabbatarwa mai ƙarfi a kan tashin Ubangiji Yesu daga matattu. Alheri mai yawa yana tare da kowannensu,

34 har ba wanda yake da rashi a cikinsu ko ɗaya, don duk masu gonaki ko gidaje sun sayar da su,

35 sun kawo kuɗin, sun ajiye gaban manzanni, an kuwa rarraba wa kowa gwargwadon bukatarsa.

36 Ana cikin haka sai Yusufu, wani Balawiye, asalinsa mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannin suke kira Barnaba, (wato ɗan ƙarfafa zuciya),

37 ya sayar da wata gonarsa, ya kawo kuɗin ya ajiye a gaban manzannin.

Categories
A.M.

A.M. 5

Hananiya da Safiratu

1 Amma wani mutum mai suna Hananiya, da mata tasa Safiratu, ya sayar da wata mallaka tasa,

2 sai ya ɓoye wani abu daga cikin kuɗin, da sanin matarsa, ya kawo sashin kuɗin kurum ya ajiye a gaban manzanni.

3 Sai Bitrus ya ce, “Kai, Hananiya, ta ƙaƙa Shaiɗan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya, ka kuma ɓoye wani abu daga kuɗin gonar?

4 Kafin ka sayar, ba taka ba ce? Bayan ka sayar kuma, kuɗin ba halalinka ba ne? Ta ƙaƙa ka riya wannan aiki a zuciyarka? Ai, ba mutum ka yi wa ƙarya ba, Allah ka yi wa.”

5 Da jin wannan magana Hananiya ya fāɗi ya mutu. Duk waɗanda suka ji kuwa, matsanancin tsoro ya kama su.

6 Samari suka taso, suka sa shi a likkafani, suka ɗauke shi suka fitar da shi, suka je suka binne shi.

7 Bayan misalin sa’a uku mata tasa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba.

8 Sai Bitrus ya ce mata, “Gaya mini, shin, haka kuka sayar da gonar nan?” Sai ta ce, “I, haka ne.”

9 Amma Bitrus ya ce mata, “Ƙaƙa kuka gama baki ku gwada Ruhun Ubangiji? Kin ji tafiyar waɗanda suka binne mijinki, har sun iso bakin ƙofa ma, za su kuwa ɗauke ki, su fitar da ke.”

10 Nan tāke, ta fāɗi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo, suka iske ta matacciya, suka ɗauke ta suka fitar da ita, suka binne ta a jikin mijinta.

11 Sai matsanancin tsoro ya kama dukan Ikkilisiyar, da kuma dukan waɗanda suka ji labarin waɗannan abubuwa.

An Yi Mu’ujizai da Abubuwan Al’ajabi Masu Yawa

12 To, an yi mu’ujizai da abubuwan al’ajabi masu yawa a cikin mutane ta hannun manzanni. Dukansu kuwa da nufi ɗaya sukan taru a Shirayin Sulemanu.

13 Amma a cikin sauran mutane ba wanda ya yi ƙarfin halin shiga cikinsu, duk da haka kuwa jama’a suna girmama su.

14 Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa suke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama’a masu yawan gaske mata da maza.

15 Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya tafarku, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwa tasa ma ta bi ta kan waɗansunsu.

16 Mutane kuwa suka yi ta taruwa daga garuruwan da suke kewayen Urushalima, suna ta kawo marasa lafiya da waɗanda baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, dukansu kuwa aka warkar da su.

An Tsananta wa Manzanni

17 Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato ‘yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya,

18 suka kama manzannin, suka sa su kurkuku.

19 Amma da daddare sai wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce,

20 “Ku tafi, ku tsaya a cikin Haikali, ku sanar da jama’a duk maganar wannan rai.”

21 Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa.

To, babban firist ya fito, shi da waɗanda suke tare da shi, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Isra’ilawa, suka aika kurkuku a kawo su.

22 Amma da dogaran Haikali suka je, ba su same su a kurkukun ba, suka dawo suka ba da labari, suka ce,

23 “Mun iske kurkukun a kulle sosai, masu tsaro kuma na tsaro a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.”

24 To, da shugaban dogaran Haikali da manyan firistocin suka ji haka, suka ruɗe ƙwarai a game da su, suka rasa inda abin zai kai.

25 Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai, ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna nan a tsaye a Haikali, suna koya wa jama’a.”

26 Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama’a su jejjefe su da duwatsu.

27 Da suka kawo su, suka tsai da su a gaban majalisar. Sai babban firist ya tambaye su,

28 ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.”

29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.

30 Allahn kakanninmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin kafe shi a jikin gungume.

31 Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra’ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.

32 Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al’amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”

33 Da suka ji haka, sai suka husata ƙwarai da gaske, suna so su kashe su.

34 Amma wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama’a suke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna.

35 Sa’an nan ya ce musu, “Ya ku ‘yan’uwa Isra’ilawa, ku kula fa da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.

36 Shekarun baya wani mutum ya ɓullo, wai shi Tudas, yana mai da kansa wani abu, wajen mutum arbaminya kuma suka bi shi, amma aka kashe shi, mabiyansa kuwa aka watsa su, suka lalace.

37 Bayansa kuma, a lokacin ƙirgen mutane, wai shi Yahuza Bagalile ya ɓullo, ya zuga waɗansu suka yi turu, suka bi shi. Shi ma ya hallaka, duk mabiyansa ma aka warwatsa su.

38 To, yanzu ma, ina gaya muku, ku fita sha’anin mutanen nan, ku ƙyale su. Idan dai niyyarsu ko aikinsu na mutum ne, ai, zai rushe,

39 amma in na Allah ne, ba dama ku rushe su. Kada fa a same ku kuna gāba da Allah.”

40 Sai suka bi shawara tasa, suka kuma kirawo manzannin, suka yi musu dūka, suka kwaɓe su kada su ƙara magana da sunan Yesu, sa’an nan suka sake su.

41 To, suka tashi daga gaban majalisar, suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulakanci saboda sunan Yesu.

42 Kowace rana kuwa, ko a Haikali ko a gida, ba su daina koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu ba.

Categories
A.M.

A.M. 6

Zaɓen Mutum Bakwai Masu Hidima

1 To, a kwanakin nan da yawan masu bi suke Ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, a wajen rabon gudunmawa a kowace rana.

2 Sai goma sha biyun nan suka kirawo duk jama’ar masu bi, suka ce, “Ai, bai kyautu ba mu mu bar wa’azin Maganar Allah, mu shagala a kan sha’anin abinci.

3 Saboda haka, ‘yan’uwa, sai ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku, waɗanda ake yabawa, cike da Ruhu da kuma hikima, waɗanda za mu danƙa wa wannan aiki.

4 Mu kuwa sai mu nace da yin addu’a da kuma koyar da Maganar.”

5 Abin da suka faɗa kuwa ya ƙayatar da jama’a duka. Sai suka zaɓi Istifanas, mutumin da yake cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki, da Filibus, da Burokoras, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya wanda dā ya shiga Yahudanci.

6 Waɗannan ne aka gabatar a gaban manzannin. Bayan sun yi addu’a kuma, suka ɗora musu hannu.

7 Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na’am da bangaskiyar nan.

An Kama Istifanas

8 To, Istifanas, cike da alheri da iko, ya yi ta yin manyan al’ajabai da mu’ujizai a cikin jama’a.

9 Sa’an nan waɗansu na majami’ar da ake kira majami’ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara.

10 Amma ko kaɗan ba dama su yi masa mūsu, domin ya yi magana da hikima, Ruhu na iza shi.

11 Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.”

12 Ta haka suka ta da hankalin jama’a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukar masa, suka kama shi, suka kawo shi a gaban majalisa.

13 Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura,

14 don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al’adun da Musa ya bar mana.”

15 Da duk waɗanda suke zaune a majalisar suka zura masa ido, suka ga fuska tasa kamar fuskar mala’ika take.

Categories
A.M.

A.M. 7

Hanzarin Istifanas

1 Sai babban firist ya ce, “Ashe, haka ne?”

2 Sai Istifanas ya ce, “Ya ku ‘yan’uwa da shugabanni, ku saurare ni. Allah Maɗaukaki ya bayyana ga kakanmu Ibrahim, sa’ad da yake ƙasar Bagadaza, tun bai zauna a Haran ba,

3 ya ce masa, ‘Tashi daga ƙasarku, daga kuma cikin ‘yan’uwanka, ka je ƙasar da zan nuna maka.’

4 Sai ya tashi daga ƙasar Kaldiyawa, ya zauna a Haran. Daga can kuma, bayan mutuwar tsohonsa, Allah ya kawo shi ƙasar nan da yanzu kuke zaune.

5 Amma kuwa shi kansa, bai ba shi gādonta ba, ko da taki ɗaya, sai dai ya yi masa alkawari zai mallakar masa ita, shi da zuriyar bayansa, ko da yake ba shi da ɗa a lokacin.

6 Abin da Allah ya faɗa kuwa shi ne zuriyar Ibrahim za su yi baƙunci a wata ƙasa, mutanen ƙasar kuwa za su bautar da su, su kuma gwada musu tasku har shekara arbaminya.

7 ‘Har wa yau kuma,’ Allah ya ce, ‘Al’ummar da za su bauta wa, ni zan hukunta ta, bayan haka kuma za su fito su bauta mini a wannan wuri.’

8 Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakanninmu sha biyun nan.

9 “Kakannin nan kuwa, da yake suna kishin Yusufu, suka sayar da shi, aka kai shi Masar. Amma Allah na tare da shi,

10 ya kuma tsamo shi daga dukan wahala tasa, ya ba shi farin jini da hikima a gun Fir’auna, Sarkin Masar, shi kuwa ya naɗa shi mai mulkin Masar, ya kuma danƙa masa jama’ar gidansa duka.

11 To, sai wata yunwa ta auku a dukan ƙasar Masar da ta Kan’ana, game da matsananciyar wahala, har kakanninmu suka rasa abinci.

12 Amma da Yakubu ya ji akwai alkama a Masar, ya aiki kakanninmu tafiyar farko.

13 A tafiyarsu ta biyu Yusufu ya sanar da kansa ga ‘yan’uwansa, asalinsa kuma ya sanu ga Fir’auna.

14 Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukan ‘yan’uwansa, mutum saba’in da biyar.

15 Sai Yakubu ya tafi Masar. A can ma ya mutu, shi da kakanninmu.

16 Sai aka ɗebo su aka mai da su Shekem, aka sa su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗi azurfa a wurin ‘ya’yan Hamor a nan Shekem.

17 “Amma da lokacin cikar alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya gabato, jama’ar suka ƙaru, suka yawaita ƙwarai a ƙasar Masar,

18 har aka yi wani sarki a Masar, wanda bai san ko wane ne Yusufu ba.

19 Wannan sarki kuwa ya cuci kabilarmu, yana gwada wa kakanninmu tasku, yana sawa a yar da jariransu, don kada su rayu.

20 A lokacin nan ne aka haifi Musa, yaro kyakkyawan gaske. Sai aka rene shi wata uku a gidan ubansa.

21 Da aka yar da shi waje, ‘yar Fir’auna ta ɗauke shi tallafinta, ta goya shi kamar ɗanta.

22 Sai aka karantar da Musa dukan ilimin Masarawa, shi kuwa mutum mai iko ne a cikin magana da ayyukansa.

23 “Yana gab da cika shekara arba’in ke nan, sai ya faɗo masa a rai yă ziyarci ‘yan’uwansa Isra’ilawa.

24 Da ya ga ana cutar ɗayansu, ya tare wanda ake wulakantawa, ya rama masa, ya buge Bamasaren, ya mutu.

25 Ya zaci ‘yan’uwansa sun gane ta hannunsa ne Allah zai cece su. Amma ba su gane ba.

26 Kashegari kuma waɗansu suna faɗa, sai ya nemi shirya su, ya ce, ‘Ku jama’a, ku ‘yan’uwa ne fa, don me kuke cutar juna?’

27 Amma mai cutar ɗan’uwa nasa ya ture Musa, ya ce, ‘Wa ya sa ka shugaba da alƙali a kanmu?

28 Wato kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren nan na jiya?’

29 Da jin wannan magana, Musa ya gudu ya yi baƙunci a ƙasar Madayana, inda ya haifi ‘ya’ya biyu maza.

30 “To, bayan shekara arba’in, wani mala’ika ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a wani kurmi a jejin Dutsen Sina’i.

31 Da Musa ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya matso domin ya duba, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

32 ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allahn Ibrahim da Ishaku da Yakubu.’ Sai jikin Musa ya ɗauki rawa, bai kuma iya ƙarfin halin dubawa ba.

33 Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Tuɓe takalminka, domin wurin da kake tsayen nan, tsattsarka wuri ne.

34 Hakika, na ga wulakancin da ake yi wa mutanena da suke Masar, na ji nishinsu, na kuma sauko don in cece su. To, a yanzu sai ka zo in aike ka Masar.’

35 “To, shi Musan nan da suka ƙi, suna cewa, ‘Wa ya sa ka shugaba kuma alƙali?’ shi ne Allah ya aiko ya zama shugaba, da mai ceto, ta taimakon mala’ikan nan da ya bayyana a gare shi a cikin kurmin nan.

36 Shi ne kuwa ya fito da su, bayan ya yi abubuwan al’ajabi da mu’ujizai a ƙasar Masar, da Bahar Maliya, da kuma a cikin jeji, har shekara arba’in.

37 Wannan shi ne Musan da ya ce wa Isra’ilawa, ‘Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin ‘yan’uwanku, kamar yadda ya tashe ni.’

38 Shi ne kuma wanda yake a cikin Ikkilisiyar nan a jeji tare da mala’ikan da ya yi masa magana a Dutsen Sinai, tare da kakanninmu kuma. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana domin ya kawo mana.

39 Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciya tasu ta koma ƙasar Masar.

40 Suka ce wa Haruna, ‘Ka yi mana gumakan da za su yi mana jagaba, don Musan nan kam, da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya auku a gare shi ba.’

41 A lokacin nan suka ƙera ɗan maraƙi, suka yanka wa gunkin nan hadaya, suka riƙa farin ciki da aikin da suka yi da hannunsu.

42 Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari, yadda yake a rubuce a littafin annabawa cewa,

‘Ya ku jama’ar Isra’ila,

Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya,

Har shekara arba’in a cikin jeji?

43 Ai, yawo kuka yi da alfarwar Molek,

Da surar tauraron gunki Ramfan,

Wato surorin nan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.

Ni kuwa zan kawar da ku a can bayan Babila.’

44 “Dā kakanninmu suna da alfarwar shaida a jeji, irin wadda mai maganar nan da Musa ya umarta a yi, daidai fasalin da ya gani.

45 Alfarwan nan ita ce kakanninmu suka gāda, suka kuma kawo ƙasar nan a zamanin Joshuwa, bayan sun mallake ƙasar al’umman da Allah ya kora a gaban idonsu. Alfarwan nan kuwa tana nan har ya zuwa zamanin Dawuda,

46 wanda ya sami tagomashi wurin Allah, har ya nemi alfarmar yi wa Allahn Yakubu masujada.

47 Amma Sulemanu ne ya yi wa Allah gini.

48 Duk da haka Maɗaukaki ba ya zama a gidaje, ginin mutum. Yadda Annabi Ishaya ya ce,

49 ‘Allah ya ce, Sama ita ce kursiyina,

Ƙasa kuwa matashin ƙafata.

Wane wuri kuma za ku gina mini?

Ko kuwa wane wuri ne wurin hutuna?

50 Ba da ikona na halicci dukan waɗannan abubuwa ba?’

51 “Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Mai Tsarki tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi.

52 A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,

53 ku ne kuwa kuka karɓi Shari’a ta wurin mala’iku, amma ba ku kiyaye ta ba!”

An Kashe Istifanas da Jifa

54 Da suka ji haka, suka husata ƙwarai da gaske, har suka ciji baki don jin haushinsa.

55 Amma Istifanas, a cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya zuba ido sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye a dama ga Allah.

56 Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”

57 Amma suka ɗauki ihu ƙwarai, suka tattoshe kunnuwansu, suka aukar masa da nufi ɗaya,

58 suka fitar da shi a bayan gari suka yi ta jifansa da dutse. Shaidu kuwa suka ajiye tufafinsu wurin wani saurayi, wai shi Shawulu.

59 Suna ta jifan Istifanas, shi kuwa yana ta addu’a, yana cewa, “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”

60 Sa’an nan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.

Categories
A.M.

A.M. 8

1 Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas.

Shawulu Ya Yi wa Ikkilisiya Ɓarna Ƙwarai

A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.

2 Sai waɗansu mutane masu bautar Allah suka binne Istifanas, suka yi masa kuka ƙwarai.

3 Amma Shawulu ya yi ta yi wa Ikkilisiya ɓarna ƙwarai da gaske, yana shiga gida gida, yana jan mata da maza, yana jefa su a kurkuku.

An Yi Wa’azin Bishara a Samariya

4 To, waɗanda aka warwatsar nan kuwa, suka yi ta zazzagawa suna yin bishara.

5 Filibus ya tafi birnin Samariya, yana ta yi musu wa’azin Almasihu.

6 Da taron suka ji, suka kuma ga mu’ujizan da Filibus yake yi, da nufi ɗaya suka mai da hankali ga abin da ya faɗa.

7 Domin da yawa masu baƙaƙen aljannu suka rabu da su, aljannun kuwa na ta ihu. Shanyayyu da guragu da yawa kuma an warkar da su.

8 Saboda haka aka yi ta farin ciki a garin ƙwarai da gaske.

9 Akwai wani mutum kuwa, mai suna Saminu, wanda dā yake sihiri a birnin, har yana ba Samariyawa mamaki, yana cewa shi wani muhimmi ne.

10 Duk jama’a kuwa suka mai da hankali a gare shi, babba da yaro, suna cewa, “Mutumin nan, ai, ikon nan ne na Allah, da ake kira mai girma.”

11 Sai suka mai da hankali gare shi, don ya daɗe yana ta ba su al’ajabi da sihirinsa.

12 Amma da suka gaskata bisharar da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, duka aka yi musu baftisma mata da maza.

13 Har Saminu da kansa ma ya ba da gaskiya, bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu’ujizai da manyan al’ajibai, ya yi mamaki ƙwarai.

14 To, da manzannin da suke Urushalima suka ji Samariyawa sun yi na’am da Maganar Allah, suka aika musu da Bitrus da Yahaya.

15 Su kuwa da suka iso, suka yi musu addu’a don su sami Ruhu Mai Tsarki,

16 domin bai sauko wa ko wannensu ba tukuna, sai dai kawai an yi musu baftisma ne da sunan Ubangiji Yesu.

17 Sai suka ɗora musu hannu, suka kuwa sami Ruhu Mai Tsarki.

18 To, da Saminu ya ga, ashe, ta ɗora hannun manzanni ne ake ba da Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,

19 ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iko, don kowa na ɗora wa hannu, yă sami Ruhu Mai Tsarki.”

20 Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah!

21 Ba ruwanka da wannan al’amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.

22 Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.

23 Domin na ga kai tushen ɗaci ne, kana kulle a cikin mugunta.”

24 Sai saminu ya amsa ya ce, “Ku roƙar mini Ubangiji kada ko ɗaya daga cikin abin da kuka faɗa ya aukar mini.”

25 To, bayan manzannin sun tabbatar da Maganar Ubangiji, sun faɗe ta, suka koma Urushalima, suna yin bishara a ƙauyukan Samariyawa da yawa.

Filibus da Mutumin Habasha

26 Sai wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Tashi, ka yi kudu, ka bi hanyar da ta fito daga Urushalima zuwa Gaza,” wato hanyar hamada.

27 Sai ya tashi ya tafi. Ga wani mutumin Habasha, wani bābā, mai babban matsayi a mulkin Kandakatu, sarauniyar Habasha, shi ne kuwa ma’ajinta, ya zo Urushalima ne yin sujada,

28 yana komawa gida a zaune a cikin keken dokinsa, yana karatun littafin Annabi Ishaya.

29 Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa ka yi kusa da keken dokin nan.”

30 Sai Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?”

31 Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare.

32 Wannan kuwa shi ne nassin da yake karantawa, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka. Kamar yadda ɗan rago yake shiru a hannun mai sausayarsa, Haka, ko bakinsa bai buɗe ba.

33 An yi masa ƙasƙanci har an hana masa gaskiya tasa. Wa yake iya ba da labarin zamaninsa? Domin an katse ransa daga duniya.”

34 Sai bābān ya ce wa Filibus, “Shin kam, annabin nan, maganar wa yake yi? Tasa ko ta wani?”

35 Sai Filibus ya buɗe baki ya fara da wannan Nassi, yana yi masa bisharar Yesu.

36 Suna cikin tafiya, suka iso wani ruwa, sai bābān ya ce, “Ka ga ruwa! Me zai hana a yi mini baftisma?”

37 Filibus ya ce, “In dai ka ba da gaskiya da zuciya ɗaya, ai, sai a yi maka.” Bābān ya amsa ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu ɗan Allah ne.”

38 Sai ya yi umarni a tsai da keken dokin. Sai dukansu biyu suka gangara cikin ruwan, Filibus da bābān, ya yi masa baftisma.

39 Da suka fito daga ruwan, Ruhun Ubangiji ya fauce Filibus, bābān kuma bai ƙara ganinsa ba. Sai ya yi ta tafiya tasa yana farin ciki.

40 Amma aka ga Filibus a Azotus. Sai ya zaga dukan garuruwa, yana yin bishara, har ya isa Kaisariya.

Categories
A.M.

A.M. 9

Juyowar Shawulu

1 Shawulu kuwa yana kan tsananta kashedi da gāba da masu bin Ubangiji, cewa zai kashe su, sai ya je wurin babban firist,

2 ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami’un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.

3 Yana tafiya ke nan, ya yi kusa da Dimashƙu, ba zato sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi.

4 Sai ya fāɗi, ya kuma ji wata murya tana ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”

5 Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

6 Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”

7 Abokan tafiyarsa kuwa suka rasa bakin magana, suna jin muryar, amma ba su ga kowa ba.

8 Sai Shawulu ya tashi, amma da ya buɗe ido ya kasa gani. Sai aka yi masa jagora, aka kai shi Dimashƙu.

9 Kwanansa uku ba ya gani, ba ya kuma ci, ba ya sha.

10 To, akwai wani mai bi a Dimashƙu, mai suna Hananiya. Ubangiji ya yi masa magana cikin wahayi ya ce, “Hananiya.” Shi kuwa ya ce, “Na’am, ya Ubangiji.”

11 Sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka tafi titin nan da ake kira Miƙaƙƙiye, ka tambaya a gidan Yahuza, ko akwai wani mutumin Tarsus, mai suna Shawulu, ga shi nan, yana addu’a,

12 har ma a cikin wahayi ya ga wani mutum, mai suna Hananiya, ya shigo ya ɗora masa hannu, don ya sāke samun ganin gari.”

13 Amma Hananiya ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, na sha jin labarin mutumin nan gun mutane da yawa, kan yawan muguntar da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.

14 Ga shi kuma manyan firistoci sun ba shi izini ya ɗaure duk mai yin addu’a da sunan har a nan ma.”

15 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, je ka, domin shi ma’aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yă sanar da sunana ga al’ummai, da sarakuna, da kuma Isra’ilawa.

16 Domin zan sanar da shi yawan wuyar da lalle zai sha saboda sunana.”

17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”

18 Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ya sāke gani. Sa’an nan ya tashi, aka yi masa baftisma.

19 Sai ya ci abinci, ƙarfinsa kuma ya komo.

Shawulu Ya Yi Wa’azi a Dimashƙu

Shawulu kuwa ya yi ‘yan kwanaki tare da masu bi da suke Dimashƙu.

20 Nan da nan ya fara wa’azin Yesu a majami’unsu, cewa shi ne Ɗan Allah.

21 Duk waɗanda suka ji shi, suka yi ta al’ajabi, suka ce, “Ashe, ba wannan ne ya watsa masu yin addu’a da sunan nan a Urushalima ba? Ya zo nan ne ma da niyyar ya kai su gaban manyan firistoci a ɗaure.”

22 Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da suke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa, cewa Yesu shi ne Almasihu.

Shawulu Ya Kuɓuce wa Yahudawa

23 Bayan an ɗan daɗe Yahudawa suka ƙulla shawara su kashe shi.

24 Amma Shawulu ya sami labarin makircinsu. Dare da rana suna fako a ƙofofin gari don su kashe shi,

25 amma da daddare almajiransa suka tafi da shi, suka zura shi ta wata taga a jikin garu cikin babban kwando.

Shawulu a Urushalima

26 Da ya zo Urushalima ya yi ƙoƙarin shiga cikin masu bi, amma duk suka ji tsoronsa, don ba su gaskata shi mai bi ba ne.

27 Amma Barnaba ya kama hannunsa ya kai shi wurin manzannin, ya gaya musu yadda Shawulu ya ga Ubangiji a hanya, da yadda Ubangiji ya yi masa magana, da kuma yadda ya yi wa’azi gabagaɗi da sunan Yesu a Dimashƙu.

28 Daga nan ya yi ta cuɗanya da su a Urushalima,

29 yana wa’azi gabagaɗi da sunan Ubangiji. Ya kuma riƙa magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana muhawwara da su, amma suka yi ta neman kashe shi.

30 Da ‘yan’uwa suka fahimci haka, suka kawo shi Kaisariya, suka aika da shi Tarsus.

31 Sa’an nan ne Ikkilisiyar duk ƙasar Yahudiya, da ta Galili, da ta Samariya ta sami lafiya, ta ingantu sosai, suna tafiyar da al’amuransu da tsoron Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki na taimakonsu, har suka yawaita.

An Warkar da Iniyasu

32 To, da Bitrus ya zazzaga lardi duka, sai kuma ya je wurin tsarkakan nan da suke zaune a Lidda.

33 Nan ya tarar da wani mutum, mai suna Iniyasu, wanda yake kwance a kan gado shekara takwas, yana shanyayye.

34 Sai Bitrus ya ce masa, “Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka kintsa gadonka.” A nan tāke ya tashi.

35 Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, suka juyo ga Ubangiji.

Bitrus Ya Ta Da Tabita daga Matattu

36 A Yafa kuwa akwai wata mai bi, mai suna Tabita, wato Dokas ke nan. Matar nan kuwa lazimar aiki nagari ce, da kuma gudunmawa.

37 A lokacin nan ta yi rashin lafiya, ta mutu. Da suka yi mata wanka, suka shimfiɗe ta a kan bene.

38 Da yake Lidda kusa da yafa take, da masu bi suka ji Bitrus na can, suka aiki mutum biyu wurinsa, su roƙe shi ya zo wurinsu ba da jinkiri ba.

39 Sai Bitrus ya tashi ya tafi tare da su. Da ya iso suka kai shi benen. Dukan mata waɗanda mazansu suka mutu suka tsaya kusa da shi, suna kuka, suna nunnuna riguna da tufafi da Dokas ta yi musu tun suna tare.

40 Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu’a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.

41 Ya kuwa miƙa mata hannu ya tashe ta. Sai ya kira tsarkaka da matan waɗanda mazansu suka mutu ya miƙa musu ita rayayyiya.

42 Labari ya bazu a dukan Yafa, mutane da yawa kuwa suka gaskata da Ubangiji.

43 To, ya zauna kwanaki da yawa a Yafa a gidan wani majemi mai suna Saminu.

Categories
A.M.

A.M. 10

Bitrus da Karniliyas

1 An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.

2 Shi kuwa mutum ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana yana ba jama’a sadaka hanu sake, yana kuma addu’a ga Allah a kai a kai.

3 Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala’ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”

4 Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala’ikan kuma ya ce masa, “Addu’arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.

5 To, yanzu, sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,

6 ya sauka a gun Saminu majemi, wanda gidansa yake a bakin bahar.”

7 Da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.

8 Da ya ba su labarin kome, ya aike su Yafa.

9 Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu’a, wajen rana tsaka.

10 Yunwa ta kama shi, har ya so ya ci wani abu. Ana cikin shirya abincin, sai wahayi ya zo masa,

11 ya ga sama ta dare, wani abu kuma yana saukowa kamar babban mayafi, ana zuro shi ƙasa ta kusurwoyinsa huɗu.

12 Cikinsa akwai kowace irin dabba, da masu jan ciki, da tsuntsaye.

13 Sai ya ji wata murya ta ce masa, “Bitrus, tashi, ka yanka ka ci.”

14 Amma Bitrus ya ce, “A’a, ya Ubangiji, don ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta ba.”

15 Sai ya sāke jin murya, ji na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.”

16 Da an yi wannan sau uku, nan da nan aka yi sama da abin.

17 Bitrus na a cikin damuwa ƙwarai a kan ko mece ce ma’anar wahayin da aka yi masa, sai ga mutanen da Karniliyas ya aiko tsaye a ƙofar zaure, sun riga sun tambayi gidan Saminu,

18 suna sallama, suna tambaya ko Saminu da ake kira Bitrus a nan ya sauka.

19 Tun Bitrus yana bibiya wahayin nan, Ruhu ya ce masa, “Ga mutum uku nan suna nemanka.

20 Tashi, ka sauka, ku tafi tare, ba da wata shakka ba, domin ni ne na aiko su.”

21 Sai Bitrus ya sauka wurin mutanen, ya ce musu, “Ga ni, ni ne kuke nema. Wace magana yake tafe da ku?”

22 Sai suka ce, “Wani jarumi ne, wai shi Karniliyas, mutumin kirki, mai tsoron Allah, wanda duk jama’ar Yahudawa suke yabo, shi ne wani tsattsarkan mala’ika ya umarce shi, ya aiko ka je gidansa, ya ji maganarka.”

23 Sai Bitrus ya shigo da su, ya sauke su.

Kashegari ya tashi suka tafi tare, waɗansu ‘yan’uwa kuma daga Yafa suka raka shi.

24 Kashegari kuma suka shiga Kaisariya. Dā ma Karniliyas na tsammaninsu, har ya gayyato ‘yan’uwansa da aminansa.

25 Bitrus na shiga gidan ke nan sai Karniliyas ya tarye shi, ya fāɗi a gabansa, ya yi masa sujada.

26 Amma Bitrus ya tashe shi, ya ce, “Tashi, ai, ni ma ɗan adam ne.”

27 Bitrus na zance da shi, ya shiga ya tarar mutane da yawa sun taru.

28 Ya ce musu, “Ku da kanku kun sani, bai halatta Bayahude ya cuɗanya, ko ya ziyarci wani na wata kabila dabam ba. Amma Allah ya nuna mini kada in ce da kowa marar tsarki, ko mai ƙazanta.

29 Saboda haka da aka neme ni, na zo, ban ce a’a ba. To, yanzu ina so in ji abin da ya sa kuka kira ni.”

30 Sai Karniliyas ya ce, “Yau kwana uku ke nan, wajen war haka, ina addu’ar ƙarfe uku na yamma a gidana, sai ga wani mutum tsaye a gabana, yana saye da tufafi masu ɗaukar ido,

31 ya ce, ‘Ya Karniliyas, an amsa addu’arka sadakarka kuma ta zama abar tunawa ga Allah.

32 Saboda haka sai ka aika Yafa a kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus, yă sauka a gidan Saminu majemi a bakin bahar.’

33 Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”

Bitrus Ya Yi Jawabi a Gidan Karniliyas

34 Sai Bitrus ya kāda baki ya ce, “Hakika na gane lalle Allah ba ya tara,

35 amma a kowace al’umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ne a gare shi.

36 Allah ya aiko wa Isra’ilawa maganarsa, ana yi musu bisharar salama ta wurin Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa.

37 Kun dai san labarin nan da ya bazu a duk ƙasar Yahudiya, an fara tun daga ƙasar Galili, bayan baftismar da Yahaya ya yi wa’azi,

38 wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.

39 Mu kuwa shaidu ne ga duk abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da Urushalima. Shi ne kuma suka kashe ta wurin kafa shi a jikin gungume.

40 Shi ne Allah ya tasa a rana ta uku, ya kuma yarda ya bayyana,

41 ba ga dukan jama’a ba, sai dai ga shaidun nan da Allah ya zaɓa tun dā, wato mu ke nan, da muka ci muka sha tare da shi, bayan ya tashi daga matattu.

42 Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa’azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sa mai hukunta rayayyu da matattu.

43 Shi ne duk annabawa suka yi wa shaida, cewa albarkacin sunansa duk mai gaskatawa da shi zai sami gafarar zunubai.”

An Ba Al’ummai Ruhu Mai Tsarki

44 Bitrus na a cikin wannan magana, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko wa dukan masu jinta.

45 Sai Yahudawa masu bi, ɗaukacin waɗanda suka zo tare da Bitrus, suka yi mamakin ganin har al’ummai ma an zubo musu baiwar Ruhu Mai Tsarki.

46 Domin sun ji suna magana da waɗansu harsuna, suna ta ɗaukaka Allah. Sa’an nan Bitrus ya ce,

47 “Akwai mai iya hana ruwan da za a yi wa mutanen nan baftisma, waɗanda suka sami Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda mu ma muka samu?”

48 Sai ya yi umarni a yi musu baftisma da sunan Yesu Almasihu. Sa’an nan suka roƙe shi ya ƙara ‘yan kwanaki a gunsu.