Categories
A.M.

A.M. 11

Bitrus Ya Yi wa Ikkilisiyar Urushalima Bayani

1 To, manzanni da ‘yan’uwan da suke a ƙasar Yahudiya suka ji, cewa al’ummai ma sun yi na’am da Maganar Allah.

2 Da Bitrus ya zo Urushalima, ‘yan ɗariƙar masu kaciyar nan suka yi masa sūka,

3 suka ce, “Ga shi, ka shiga wurin marasa kaciya, har ka ci abinci tare da su!”

4 Sai Bitrus ya fara, yana yi musu bayani bi da bi cewa,

5 “Ni dai, ina birnin Yafa ina addu’a, sai wahayi ya zo mini, na ga wani abu na saukowa kamar babban mayafi, an zuro shi daga sama ta kusurwoyinsa huɗu, har ya zo wurina.

6 Da na zuba masa ido, na duba na ga dabbobi, da namomin jeji, da masu jan ciki, da kuma tsuntsaye a ciki.

7 Sai kuma na ji wata murya ta ce mini, ‘Bitrus, ka tashi, ka yanka, ka ci.’

8 Amma na ce, ‘A’a, ya Ubangiji, don ba wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta da ya taɓa shiga bakina.’

9 Sai muryar ta amsa daga Sama ta yi magana ta biyu, ta ce, ‘Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.’

10 An yi wannan sau uku, sa’an nan aka janye abin sama.

11 Ba zato sai ga mutum uku tsaye a ƙofar gidan da muke, an aiko su wurina ne daga Kaisariya.

12 Sai Ruhu ya ce mini in tafi tare da su, ba tare da wata shakka ba. ‘Yan’uwan nan shidda kuma suka rako ni, har muka shiga gidan mutumin nan.

13 Sai ya gaya mana yadda ya ga mala’ika tsaye a gidansa, yana cewa, ‘Ka aika Yafa a kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,

14 shi zai faɗa maka maganar da za ka sami ceto game da ita, kai da jama’ar gidanka duka.’

15 Da fara maganata, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, daidai yadda ya sauko mana tun da farko.

16 Sai na tuna da Maganar Ubangiji, yadda ya ce, ‘Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma ku da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.’

17 Tun da yake Allah ya yi musu baiwa daidai da wadda ya yi mana, sa’ad da muka gaskata da Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni in dage wa Allah!”

18 Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al’ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”

Ikkilisiya a Antakiya ta Suriya

19 To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin nan da ya tashi kan sha’anin Istifanas, sun yi tafiya har ƙasar Finikiya, da tsibirin Kubrus, da birnin Antakiya, ba su yin wa’azin Maganar Allah ga kowa sai ga Yahudawa kaɗai.

20 Amma akwai waɗansunsu, mutanen Kubrus da na Kurane a cikinsu waɗanda da isowarsu Antakiya suka yi wa al’ummai magana, suna yi musu bisharar Ubangiji Yesu.

21 Ikon Ubangiji kuwa na tare da su, har mutane da yawa da suka ba da gaskiya suka juyo ga Ubangiji.

22 Sai labarin nan ya kai kunnen Ikkilisiyar da take Urushalima, Ikkilisiyar kuma ta aiki Barnaba can Antakiya.

23 Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji da dukan zuciyarsu,

24 domin shi mutum ne nagari cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya. Sai mutane masu yawan gaske suka ƙaru ga Ubangiji.

25 Sai Barnaba ya tafi Tarsus neman Shawulu,

26 bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da Ikkilisiya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da suna Kirista.

27 To, a kwanakin nan waɗansu annabawa suka zo Antakiya daga Urushalima.

28 Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabas, ya miƙe tsaye, ya yi faɗi da ikon Ruhu, cewa za a yi wata babbar yunwa, a duniya duka, an yi ta kuwa a zamanin Kalaudiyas.

29 Sai masu bi suka ɗaura niyya, kowa gwargwadon ƙarfinsa, su aika wa yan’uwan da suke ƙasar Yahudiya gudunmawa.

30 Haka kuwa suka yi, suka aika wa dattawan Ikkilisiya ta hannun Barnaba da Shawulu.

Categories
A.M.

A.M. 12

An Kashe Yakubu, an Kulle Bitrus

1 A lokacin nan kuwa sarki Hirudus ya fara gwada wa waɗansu ‘yan Ikkilisiya tasku,

2 har ma ya sare Yakubu ɗan’uwan Yahaya da takobi.

3 Da ya ga abin ya ƙayatar da Yahudawa, har wa yau kuma ya kama Bitrus, shi ma. Kwanakin idin abinci marar yisti ne kuwa.

4 Da ya kama shi, ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, su yi tsaronsa, da niyyar kawo shi a gaban jama’a bayan idin.

5 Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, Ikkilisiya kuwa ta himmantu ga roƙon Allah saboda shi.

An Ceci Bitrus daga Kurkuku

6 A daren da in gari ya waye Hirudus yake da niyyar fito da shi a yi masa hukunci, Bitrus kuwa na barci a tsakanin soja biyu, ɗaure da sarƙa biyu, masu tsaro kuma suna bakin ƙofa suna tsaron kurkukun,

7 sai ga mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka ɗakin, sa’an nan mala’ikan ya bugi Bitrus a kwiɓi, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sarƙar ta zube daga hannunsa.

8 Mala’ikan ya ce masa, “Yi ɗamara, ka sa takalminka.” Sai ya yi. Sai ya ce masa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.”

9 Sai ya fito ya bi shi, bai san abin da mala’ikan nan ya yi hakika ne ba, cewa yake wahayi ake yi masa.

10 Da suka wuce masu tsaron farko da na biyu, suka isa ƙyauren ƙarfe na ƙofar shiga gari, ƙyauren kuwa ya buɗe musu don kansa. Sai suka fita. Sun ƙure wani titi ke nan, nan da nan sai mala’ikan ya bar shi.

11 Da Bitrus ya koma cikin hankalinsa, ya ce, “Yanzu kam na tabbata, Ubangiji ne ya aiko mala’ikansa, ya cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”

12 Da ya gane haka, ya je gidan Maryamu, uwar Yahaya wanda ake kira Markus, inda aka taru da yawa, ana addu’a.

13 Da ya ƙwanƙwasa ƙofar zauren, wata baranya mai suna Roda ta zo ji ko wane ne.

14 Da ta shaida muryar Bitrus, ba ta buɗe ƙofar ba don murna, sai ta koma ciki a guje, ta ce Bitrus na tsaye a ƙofar zaure.

15 Sai suka ce mata, “Ke dai akwai ruɗaɗɗiya.” Ita kuwa ta nace a kan shi ne. Su kuwa suka ce, “To, mala’ikansa ne!”

16 Bitrus dai ya yi ƙwanƙwasawa, da suka buɗe suka gan shi, suka yi ta al’ajabi.

17 Shi kuwa ya ɗaga musu hannu su yi shiru, ya kuma bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakubu da ‘yan’uwa waɗannan abubuwa.” Sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.

18 Da gari ya waye kuwa ba ƙaramar rigima ce ta tashi tsakanin sojan nan ba, kan abin da ya sami Bitrus.

19 Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, ya yi ta tuhumar masu tsaron, ya kuma yi umarni a kashe su. Sa’an nan ya tashi daga ƙasar Yahudiya ya tafi Kaisariya, ya yi ‘yan kwanaki a can.

Mutuwar Hirudus

20 To, Hirudus ya yi fushi ƙwarai da mutanen Taya da na Sidon. Suka zo wurinsa da nufi ɗaya. Bayan sun rinjayi Bilastasa, sarkin fāda, suka nemi zaman lafiya, domin ga ƙasar sarkin nan suka dogara saboda abincinsu.

21 Ana nan a wata rana da aka shirya, Hirudus ya yi shigar sarauta, ya zauna a gadon sarauta, ya yi musu jawabi.

22 Taron mutane kuwa suka ɗauki sowa, suna cewa, “Kai! ka ji muryar wani Allah, ba ta mutum ba!”

23 Nan take sai mala’ikan Ubangiji ya buge shi don bai ɗaukaka Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.

Barnaba da Shawulu

24 Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, tana yaɗuwa.

25 Sai Barnaba da Shawulu suka komo daga Urushalima, bayan sun cika aiken da aka yi musu, suka kuma zo da Yahaya wanda ake kira Markus.

Categories
A.M.

A.M. 13

1 To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.

2 Sa’ad da suke yi wa Ubangiji ibada, suna kuma yin azumi, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Sai ku keɓe mini Barnaba da Shawulu domin aikin da na kira su a kai.”

3 Bayan kuma sun yi azumi, sun kuma yi addu’a, sai suka ɗora musu hannu, suka sallame su.

Manzanni Sun Yi Wa’azi a Kubrus

4 Su kuwa, da Ruhu Mai Tsarki ya aike su, suka tafi Salukiya, daga can kuma suka shiga jirgin ruwa sai tsibirin Kubrus.

5 Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami’un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu.

6 Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafusa, suka iske wani mai sihiri, annabin ƙarya, Bayahude, mai suna Bar-yashu’a,

7 Wanda yake tare da muƙaddas Sarjiyas Bulus, mutum mai basira. Sai muƙaddashin ya kira Barnaba da Shawulu ya nemi jin Maganar Allah.

8 Amma Alimas mai sihirin nan, (don wannan ita ce ma’anar sunansa), ya mūsa musu, yana neman bauɗar da muƙaddashin nan daga bangaskiya.

9 Shawulu kuwa, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba masa ido,

10 ya ce, “Kai babban maha’inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?

11 To, ga shi, hannun Ubangiji na kanka, za ka makance, ba za ka ga rana ba har wani lokaci.” A nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi, ya yi ta neman wanda zai yi masa jagora.

12 Da muƙaddashin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, yana mamaki da koyarwar Ubangiji.

Bulus da Barnaba a Antakiya ta Bisidiya

13 Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafusa a jirgin ruwa, suka isa Bariyata ta ƙasar Bamfiliya. Yahaya kuwa ya bar su, ya koma Urushalima.

14 Amma suka wuce gaba daga Bariyata, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ran Asabar kuma sai suka shiga majami’a suka zauna.

15 Bayan an yi karatun Attaura da littattafan annabawa, shugabannin majami’ar suka aika musu, suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama’a, ai, sai ku yi.”

16 Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce,

“Ya ku ‘yan’uwa Isra’ilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara!

17 Allahn jama’ar nan Isra’ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama’ar sa’ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta.

18 Wajen shekara arba’in yake haƙuri da su cikin jeji.

19 Ya kuma hallaka al’umma bakwai a ƙasar Kan’ana, sai ya raba musu ƙasar tasu gādo, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin.

20 Bayan haka kuma ya naɗa musu mahukunta har ya zuwa zamanin Annabi Sama’ila.

21 Sa’an nan suka roƙa a naɗa musu sarki, sai Allah ya ba su Saul ɗan Kish, mutumin kabilar Biliyaminu, har shekara arba’in.

22 Bayan da ya kawar da shi sai ya gabatar da Dawuda ya zama sarkinsu, ya kuma shaide shi da cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake ƙauna ƙwarai, wanda kuma zai aikata dukan nufina.’

23 Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto, Yesu kamar yadda ya yi alkawari.

24 Kafin ya bayyana a fili kuwa, Yahaya ya yi wa duk jama’ar Isra’ila wa’azi su tuba a kuma yi musu baftisma.

25 Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’

26 “Ya ku ‘yan’uwa, zuriyar Ibrahim, da kuma sauran masu tsoron Allah a cikinku, mu fa aka aiko wa kalmar ceton nan.

27 Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa’an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi.

28 Ko da yake ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi.

29 Da suka cikasa dukkan abin da aka rubuta game da shi, suka sauko da shi daga kan gungumen, suka sa shi a kabari.

30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.

31 Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushalima daga Galili, waɗanda a yanzu su ne shaidunsa ga jama’a.

32 Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,

33 ya cika mana shi, mu zuriyarsu, da ya ta da Yesu daga matattu, yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,

‘Kai Ɗana ne,

Ni Ubanka ne yau.’

34 Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi, a kan cewa ba zai sāke komawa cikin halin ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce,

‘Zan yi muku tsattsarkar albarkar nan da na tabbatar wa Dawuda.’

35 Domin a wata Zabura ma ya ce,

‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’

36 Dawuda kam, bayan da ya bauta wa mutanen zamaninsa bisa ga nufin Allah, ya yi barci, aka binne shi tare da kakanninsa, ya kuwa ruɓe.

37 Amma shi wannan da Allah ya tashe shi, bai ruɓa ba.

38 Saboda haka, ‘yan’uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.

39 Ta gare shi kuma, duk masu ba da gaskiya suka kuɓuta daga dukan abubuwan da ba dama Shari’ar Musa ta kuɓutar da ku.

40 Saboda haka sai ku mai da hankali, kada abin nan da littattafan annabawa suke faɗa ya aukar muku, wato

41 ‘Ga shi, ku masu rainako,

Za ku ruɗe don mamaki, ku shuɗe!

Domin zan yi wani aiki a zamaninku,

Aikin da ba yadda za a yi ku gaskata,

Ko da wani ya gaya muku.’ ”

42 Suna fita majami’a ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu wannan magana a ran Asabar mai zuwa.

43 Da jama’a suka watse, Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.

44 Da Asabar ta kewayo, kusan duk birnin, suka hallara su ji Maganar Allah.

45 Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa.

46 Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al’ummai.

47 Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce,

‘Na sa ka haske ga al’ummai,

Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”

48 Da al’ummai suka ji haka, suka yi farin ciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, ɗaukacin kuma waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya.

49 Maganar Ubangiji kuwa, sai ta yi ta yaɗuwa a duk ƙasar.

50 Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.

51 Su kuwa suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya.

52 Amma kuwa masu bi suna farin ciki matuƙa, suna kuma a cike da Ruhu Mai Tsarki.

Categories
A.M.

A.M. 14

Bulus da Barnaba a Ikoniya

1 To, a Ikoniya suka shiga majami’ar Yahudawa tare, suka yi wa’azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da al’ummai, suka ba da gaskiya.

2 Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al’ummai, suka ɓata tsakaninsu da ‘yan’uwa.

3 Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa’azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi ta hannunsu.

4 Amma mutanen birni suka rarrabu, waɗansu suka koma bayan Yahudawa, waɗansu kuma bayan manzannin.

5 Sa’ad da al’ummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasar wa manzannin, su wulakanta su, su jejjefe su da duwatsu,

6 suka sami labari, suka gudu zuwa biranen Likoniya wato Listira da Darba, da kuma kewayensu.

7 Nan suka yi ta yin bisharar.

An Jejjefi Bulus a Listira

8 To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba.

9 Yana sauraron wa’azin Bulus, sai Bulus ya zuba masa ido, da ya ga bangaskiyarsa ta isa a warkar da shi,

10 ya ɗaga murya ya ce, “Tashi, ka tsaya cir.” Sai wuf ya zabura, har ya yi tafiya.

11 Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, suka ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa da Likoniyanci, “Lalle, alloli sun sauko mana da siffar mutane!”

12 Sai suka ce Barnaba shi ne Zafsa, Bulus kuwa don shi ne shugaban magana, wai shi ne Hamisa.

13 Sai sarkin tsafin Zafsa, wanda ɗakin gunkinsa yake ƙofar gari, ya kawo bajimai da tutocin furanni ƙofar gari, yana son yin hadaya tare da jama’a.

14 Amma da manzannin nan, Barnaba da Bulus, suka ji haka, suka kyakketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ɗaga murya suna cewa,

15 “Don me kuke haka? Ai, mu ma ‘yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.

16 Shi ne a zamanin dā, ya bar dukan al’ummai su yi yadda suka ga dama.

17 Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”

18 Duk da waɗannan maganganu da ƙyar suka hana jama’ar nan yin hadaya saboda su.

19 Amma waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya, da suka rarrashi taron, suka jejjefe Bulus suka ja shi bayan gari, suna zato ya mutu.

20 Amma da masu bi suka taru a kansa, sai ya tashi ya koma garin. Kashegari kuma ya tafi Darba tare da Barnaba.

21 Bayan sun yi bishara a wannan gari, sun kuma sami masu bi da yawa, suka koma Listira da Ikoniya, da kuma Antakiya,

22 suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga bangaskiya, suna cewa, sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.

23 Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace Ikkilisiya, game da addu’a da azumi, suka danƙa su ga Ubangiji, wanda dā ma suka gaskata da shi.

Komawa Antakiya ta Suriya

24 Da suka zazzaga ƙasar Bisidiya, suka isa ƙasar Bamfiliya.

25 Da kuma suka faɗi Maganar a Bariyata, suka tafi Ataliya.

26 Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu’a alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama.

27 Da suka iso, suka tara jama’ar Ikkilisiya suka ba da labarin dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu, da kuma yadda ya buɗe wa al’ummai ƙofar bangaskiya.

28 Sun kuwa jima a can tare da masu bi.

Categories
A.M.

A.M. 15

Majalisar Ikkilisiyar Urushalima

1 Sai kuma waɗansu mutane suka zo daga Yahudiya suna koya wa ‘yan’uwa, suna cewa, “In ba an yi muku kaciya kamar yadda al’adar Musa take ba, ba dama ku sami ceto.”

2 A kan wannan magana kuwa ba ƙaramar gardama da muhawwara Bulus da Barnaba suka sha yi da mutanen ba. Sai aka sa Bulus da Barnaba da kuma waɗansunsu, su je Urushalima gun manzanni da dattawan Ikkilisiya a kan wannan magana.

3 To, da Ikkilisiya ta raka su, suka zazzaga ƙasar Finikiya da ta Samariya, suna ba da labarin tubar al’ummai, sun kuwa ƙayatar da dukan ‘yan’uwa ƙwarai.

4 Da suka isa Urushalima, Ikkilisiya, da manzanni, da dattawan Ikkilisiya suka yi musu maraba, su kuma suka gaggaya musu dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu.

5 Amma waɗansu masu ba da gaskiya, ‘yan ɗariƙar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su, su bi Shari’ar Musa.”

6 Sai manzannin da dattawan Ikkilisiya suka taru su duba maganar.

7 Bayan an yi ta muhawwara da gaske, Bitrus ya miƙe, ya ce musu, “Ya ‘yan’uwa, kun sani tun farkon al’amari, Allah ya yi zaɓe a cikinku, cewa dai ta bakina ne al’ummai za su ji maganar bishara, su ba da gaskiya.

8 Allah kuwa, masanin zuciyar kowa, ya yi musu shaida da ya ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.

9 Bai kuma nuna wani bambanci tsakaninmu da su ba, tun da yake ya tsarkake zukatansu saboda bangaskiyarsu.

10 Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?

11 Amma mun gaskata, cewa, albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”

12 Sai duk taron mutane suka yi tsit, suka saurari Barnaba da Bulus, sa’ad da suke ba da labarin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi, da Allah ya yi ga al’ummai ta wurinsu.

13 Bayan sun gama jawabi, Yakubu ya amsa ya ce, “Ya ku ‘yan’uwa, ku saurare ni.

14 Bitrus ya ba da labari yadda Allah ya fara kula da al’ummai, domin ya keɓe wata jama’a daga cikinsu ta zama tasa.

15 Wannan kuwa daidai yake da maganar annabawa, yadda yake a rubuce cewa,

16 ‘Bayan haka kuma zan komo,

In sāke gina gidan Dawuda da ya rushe,

In sāke ta da kangonsa,

In tsai da shi,

17 Domin sauran mutane su nemi Ubangiji,

Wato al’umman da suke nawa.’

18 Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.

19 Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah,

20 sai dai mu rubuta musu wasiƙa, su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.

21 Domin tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin wa’azi da littattafan Musa, ana kuma karanta su a majami’u kowace Asabar.”

Amsar Majalisar Ikkilisiya

22 Sai manzanni da dattawan Ikkilisiya, tare da dukan ‘yan Ikkilisiya, suka ga ya kyautu su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka aiki Yahuza, wanda ake kira Barsaba, da kuma Sila, shugabanni ne cikin ‘yan’uwa,

23 da wannan takarda cewa, “Daga ‘yan’uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga ‘yan’uwanmu na al’ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.

24 Tun da muka sami labari, cewa waɗansu daga cikinmu sun ta da hankalinku da maganganu, suna ruɗa ku, ko da yake ba mu umarce su da haka ba,

25 sai muka ga ya kyautu, da yake bakinmu ya zo ɗaya, mu aiko muku waɗansu zaɓaɓɓun mutane, tare da ƙaunatattunmu Barnaba da Bulus,

26 waɗanda suka sayar da ransu saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu.

27 Don haka, ga shi, mun aiko muku Yahuza da Sila, su ma za su gaya muku waɗannan abubuwa da bakinsu.

28 Domin Ruhu Mai Tsarki ya ga ya kyautu, mu ma mun gani, kada a ɗora muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwa da suke wajibi, wato

29 ku guji abin da aka yanka wa gunki, da cin nama tare da jini, da cin abin da aka maƙure, da kuma fasikanci. In kun tsare kanku daga waɗannan, za ku zauna lafiya. Wassalam.”

30 Su kuma da aka sallame su, suka tafi Antakiya, da suka tara jama’ar, suka ba da wasiƙar.

31 Da suka karanta ta, suka yi farin ciki saboda gargaɗin.

32 Yahuza da Sila kuma, da yake su annabawa ne, suka gargaɗi ‘yan’uwa da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su.

33 Bayan sun yi ‘yan kwanaki a wurin, sai ‘yan’uwa su sallame su lafiya, suka koma wurin waɗanda suka aiko su.

34 [Amma Sila ya ga ya kyautu shi ya zauna a nan.]

35 Bulus da Barnaba kuwa suka dakata a Antakiya, suna koyarwa suna kuma yin bisharar Maganar Ubangiji, tare da waɗansu ma da yawa.

Bulus ya Rabu da Barnaba

36 An jima, Bulus ya ce wa Barnaba, “Bari yanzu mu koma mu dubo ‘yan’uwa a kowane gari da muka sanar da Maganar Ubangiji, mu ga yadda suke.”

37 Barnaba kuwa ya so su tafi da Yahaya, wanda ake kira Markus.

38 Amma Bulus bai ga ya kyautu su tafi da wanda ya rabu da su a ƙasar Bamfiliya, ya ƙi tafiya aiki tare da su ba.

39 Sai matsanancin saɓanin ra’ayi ya auku, har ya kai su ga rabuwa. Barnaba ya ɗauki Markus, suka shiga jirgin ruwa zuwa tsibirin Kubrus,

40 amma Bulus ya zaɓi Sila, bayan ‘yan’uwa sun yi masa addu’a alherin Allah ya kiyaye shi, ya tafi.

41 Bulus ya zazzaga ƙasar Suriya da ta Kilikiya, yana ta ƙarfafa Ikilisiyoyi.

Categories
A.M.

A.M. 16

Timoti Ya Bi Bulus da Sila

1 Sai kuma Bulus ya zo Darba da Listira. Akwai wani almajiri a Listira, mai suna Timoti, ɗan wata Bayahudiya mai bi, ubansa kuwa Bahelene ne.

2 Shi kuwa ‘yan’uwan da suke Listira da Ikoniya na yabonsa.

3 Sai Bulus ya so Timoti ya rako shi, har ya yi masa kaciya saboda Yahudawan da suke waɗannan wurare, don duk sun san ubansa Bahelene ne.

4 Lokacin da suke tafiya suna bin gari gari, suka riƙa gaya wa jama’a ƙa’idodin da manzanni da dattawan Ikkilisiya suka ƙulla a Urushalima, don su kiyaye su.

5 Ta haka ikilisiyoyi suka ƙarfafa a cikin bangaskiya, a kowace rana suna ƙara yawa.

Wahayin Bulus na Mutumin Makidoniya

6 Sai suka zazzaga ƙasar Firijiya da ta Galatiya, saboda Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin Maganar Ubangiji a ƙasar Asiya.

7 Da suka zo kan iyakar ƙasar Misiya, sai suka yi ƙoƙarin zuwa ƙasar Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yardar musu ba.

8 Suka kuwa ratsa ƙasar Misiya, suka gangara zuwa Taruwasa.

9 Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”

10 Da kuwa ya ga wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu bishara.

Lidiya Ta Ba Da Gaskiya

11 Shi ke nan fa, sai muka tashi a jirgin ruwa daga Taruwasa, muka miƙe sosai har zuwa tsibirin Samutaraki, kashegari kuma sai Niyabolis,

12 daga nan kuma sai Filibi ta ƙasar Makidoniya, wadda take babbar alkarya ce a wannan waje, birnin Romawa ne kuma. A nan birnin muka yi ‘yan kwanaki.

13 Ran Asabar muka fita ƙofar gari, muka je bakin kogi, inda muke tsammani akwai wurin yin addu’a. Nan muka zauna, muka yi wa matan da suka taru magana.

14 Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.

15 Da aka yi mata baftisma tare da jama’ar gidanta, ta roƙe mu ta ce, “Da yake kun amince ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gidana ku sauka.” Sai ta rinjaye mu.

Kulle Manzanni a Kurkukun Filibi

16 Wata rana muna tafiya wurin yin addu’a, sai muka gamu da wata yarinya mai aljani mai duba, tana kuwa samo wa iyayengijinta amfani mai yawa ta wurin dubar.

17 Sai ta riƙa binmu, mu da Bulus, tana ihu tana cewa, “Mutanen nan fa bayin Allah Maɗaukaki ne, suna kuwa sanar da ku hanyar ceto!”

18 Haka ta dinga yi kwana da kwanaki, har Bulus ya ji haushi ƙwarai, ya juya ya ce wa aljanin, “Na umarce ka da sunan Yesu Almasihu, ka rabu da ita.” Nan take kuwa ya rabu da ita.

19 Da iyayengijinta suka ga hanyar samunsu ta toshe, suka danƙe Bulus da Sila, suka ja su har zuwa bakin kasuwa gaban mahukunta.

20 Da suka kai su gaban alƙalai suka ce, “Mutanen nan suna birkita garinmu ƙwarai da gaske, Yahudawa ne kuwa.

21 Suna kuma koyar da al’adun da bai halatta mu karɓa ko mu bi ba, da yake mu Romawa ne.”

22 Sai jama’a suka ɗungumo musu gaba ɗaya, alƙalan kuma suka yi kaca-kaca da tufafinsu, suka tuttuɓe su, suka yi umarni a bulale su da tsumagu.

23 Da aka bulale su da gaske, aka jefa su kurkuku, aka umarci yari ya tsare su da kyau.

24 Shi kuwa da ya karɓi wannan umarni, sai ya jefa su can ciki cikin kurkuku, ya sa su a turu.

25 A wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna waƙoƙin yabon Allah, ‘yan sarka kuwa suna sauraronsu,

26 farat ɗaya, sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, har harsashin ginin kurkuku ya raurawa. Nan da nan ƙofofin suka bubbuɗe, marin kowa kuma ya ɓalle.

27 Da yāri ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa yake ‘yan sarƙa sun gudu.

28 Amma Bulus ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Kada ka cuci kanka, ai duk muna nan!”

29 Sai yari ya ce a kawo fitilu, ya yi wuf ya ruga ciki, ya fāɗi gaban Bulus da Sila, yana rawar jiki don tsoro.

30 Sa’an nan ya fito da su waje, ya ce, “Ya shugabanni, me zan yi in sami ceto?”

31 Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

32 Sa’an nan suka gaya masa Maganar Ubangiji, shi da iyalinsa duka.

33 Nan take da daddaren nan ya ɗebe su, ya wanke musu raunukansu. Nan da nan kuwa aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.

34 Sa’an nan ya kawo su gidansa, ya kawo musu abinci, ya yi ta farin ciki matuƙa, domin shi da iyalinsa duka sun gaskata da Allah.

35 Amma da gari ya waye, sai alƙalan suka aiko dogarai, suka ce, “Suka ce a saki mutanen nan.”

36 Yari kuwa ya shaida wa Bulus maganar, ya ce, “Alƙalai sun aiko a sake ku, saboda haka yanzu sai ku fito, ku tafi lafiya.”

37 Amma Bulus ya ce musu, “Ai, a fili suka daddoke mu, ba ko bin ba’asi, mu ma da muke Romawa bisa ga ‘yangaranci, suka jefa mu a kurkuku, yanzu kuma sā fitar da mu a ɓoye? Sai dai su zo da kansu su fito da mu.”

38 Sai dogarai suka shaida wa alƙalan wannan magana. Su kuwa da suka ji Bulus da Sila Romawa ne suka tsorata.

39 Sa’an nan suka zo suka tubar musu, bayan kuma sun fito da su, suka roƙe su su bar garin.

40 To, da suka fita daga kurkukun, suka tafi wurin Lidiya. Bayan sun ga ‘yan’uwa, suka kuma ƙarfafa musu zuciya, suka tashi.

Categories
A.M.

A.M. 17

Hargitsi a Tasalonika

1 To, da suka bi ta Amfibolis da Aboloniya, suka isa Tasalonika, inda wata majami’ar Yahudawa tāke.

2 Sai Bulus ya shiga wurinsu kamar yadda ya saba, Asabar uku a jere yana muhawwara da su daga cikin Littattafai,

3 yana yi musu bayani, yana kuma tabbatarwa, cewa lalle ne, Almasihu yă sha wuya, ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Yesun nan da nake sanar muku, shi ne Almasihu.”

4 Sai waɗansunsu suka amince, suka koma wajen Bulus da Sila, haka kuma babban taron Helenawa masu ibada, da manyan mata ba kaɗan ba.

5 Amma Yahudawa, saboda kishi, suka ɗibi waɗansu ashararai, ‘yan iska, suka tara jama’a suka hargitsa garin kaf, suka fāɗa wa gidan Yason, suna nemansu don su fito da su gaban taron jama’a.

6 Da ba su same su ba, suka jawo Yason da waɗansu ‘yan’uwa, har gaban mahukuntan garin, suna ihu suna cewa, “Mutanen nan masu ta da duniya a tsaye, ga su sun zo nan ma,

7 har ma Yason ya sauke su! Dukansu kuwa suna saɓa dokokin Kaisar, suna cewa wani ne sarki, wai shi Yesu.”

8 Da mutanen gari da mahukunta suka ji wannan, hankalinsu ya tashi.

9 Ba su sake su ba, sai da suka karɓi kuɗin lamuni a hannun Yason da sauransu.

Manzanni a Biriya

10 Nan da nan kuwa da dare ya yi, ‘yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Biriya. Da suka isa can kuma suka shiga majami’ar Yahudawa.

11 To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.

12 Saboda haka da yawa daga cikinsu suka ba da gaskiya, har da waɗansu Helenawa ba kaɗan ba, mata masu daraja, da kuma maza.

13 Amma da Yahudawan Tasalonika suka ji labari Bulus yana sanar da Maganar Allah a Biriya ma, suka je suka zuga taro masu yawa a can ma, suna ta da hankalinsu.

14 Nan da nan kuwa ‘yan’uwa suka tura Bulus bakin bahar, amma Sila da Timoti suka dakata a nan.

15 Waɗanda suka rako Bulus kuwa, sai da suka kai shi har Atina. Bayan Bulus ya yi musu saƙon umarni zuwa wurin Sila da Timoti, cewa su zo wurinsa da gaggawa, suka tafi.

Bulus a Atina

16 To, sa’ad da Bulus yake dākonsu a Atina, ya ji haushi ƙwarai da ya ga ko’ina gumaka ne a birnin.

17 A kowace rana ya yi ta muhawwara a cikin majami’a da Yahudawa, da waɗansu masu ibada, da kuma waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.

18 Har wa yau kuma waɗansu Abikuriyawa da Sitokiyawa masu ilimi suka ci karo da shi. Waɗansu suka ce, “Me wannan mai surutu yake nufi?” Waɗansu kuwa suka ce “Ga alama, mai yin wa’azin bāƙin alloli ne”– domin kawai yana yin bisharar Yesu, da kuma tashi daga matattu.

19 Sai suka riƙe shi suka kai shi Tudun Arasa, suka ce, “Ko ka faɗa mana wace irin baƙuwar koyarwa ce wannan da kake yi?

20 Domin ka kawo mana abin da yake baƙo a gare mu, muna kuwa so mu san ma’anarsa.”

21 Alhali kuwa duk Atinawa da baƙinsu ba abin da suke yi, sai kashe zarafinsu wajen jin baƙon abu, ko kuma ɗorar da shi.

22 Sai Bulus ya miƙe a tsakiyar Tudun Arasa, ya ce, “Ya ku mutanen Atina, na dai lura, ku masoyan ibada ne ƙwarai, ta kowane fanni.

23 Don sa’ad da nake zagawa, na duba abubuwan da kuke yi wa ibada, har ma na tarar da wani bagadin hadaya da wannan rubutu a sama da shi cewa, ‘Saboda Allahn da ba a sani ba.’ To, shi wanda kuke yi wa sujada ba a tare da kun san shi ba, shi nake sanar muku.

24 Allahn da ya halicci duniya da dukkan abin da yake cikinta, shi da yake Ubangijin sama da ƙasa, ba ya zama a haikalin ginin mutum.

25 Haka kuma ba ya neman wani taimako gun mutum, sai ka ce wani abu yake bukata, tun da yake shi kansa ne yake ba dukkan mutane rai, da numfashi, da dukkan abubuwa.

26 Shi ne kuma ya halicci dukkan al’umma daga tsatso ɗaya, domin su zauna a dukan sararin duniya, ya kuma ƙayyade zamanansu da iyakokin ƙasashensu,

27 wato nufinsa shi ne su neme shi, ko watakila sā laluba su same shi, alhali kuwa ba ya nesa da kowane ɗayanmu.

28 Domin

‘Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance,’

kamar yadda waɗansu mawaƙanku ma suka ce,

‘Hakika, mu ma zuriya tasa ce.’

29 To, da yake mu zuriyar Allah ne, ai, bai kamata mu tsammaci Allah na kama da wata surar zinariya, ko ta azurfa, ko ta dutse ba, wadda mutum ya ƙago ta dabararsa.

30 Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko’ina su tuba,

31 tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari’a, shari’a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”

32 Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai waɗansu suka yi ba’a, amma waɗansu suka ce, “Game da wannan magana kam, mā sāke jin abin da za ka faɗa.”

33 Sai Bulus ya fita daga cikinsu.

34 Amma waɗansu mutane suka koma wajensa suka ba da gaskiya, a cikinsu har da Diyonisiyas, ɗan majalisar Tudun Arasa, da wata mace mai suna Damarisa, da waɗansu dai haka.

Categories
A.M.

A.M. 18

Bulus a Koranti

1 Bayan haka Bulus ya tashi daga Atina ya tafi Koranti.

2 Can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da mata tasa Bilkisu, don wai Kalaudiyas ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu.

3 Da yake kuma sana’arsu ɗaya ce, maɗinkan tanti ne, ya sauka a wurinsu, suka yi ta aiki tare.

4 Ya kuma yi ta yin muhawwara a majami’a a kowace Asabar, yana ta rinjayar Yahudawa da al’ummai.

5 Sa’ad da Sila da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya dukufa a kan yin wa’azi, yana tabbatar wa Yahudawa, cewa Almasihu dai Yesu ne.

6 Da suka mūsa masa, suna ta zaginsa, ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku yana a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin al’ummai zan je.”

7 Sai ya tashi daga nan ya je gidan wani mutum mai suna Titus Yustus mai ibada, gidansa kuwa gab da majami’a yake.

8 Sai Kirisbus, shugaban majami’ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama’ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.

9 Wata rana da daddare, Ubangiji ya yi wa Bulus wahayi, ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, sai dai ka yi ta wa’azi, kada ka yi shiru,

10 domin ina tare da kai, ba kuma wanda zai fāɗa ka ya cuce ka, domin ina da mutane da yawa a wannan birni.”

11 Sai Bulus ya zauna a nan har shekara ɗaya da wata shida, yana ta koyar da Maganar Allah a cikinsu.

12 Amma sa’ad da Galiyo yake muƙaddashin ƙasar Akaya, Yahudawa suka tasar wa Bulus da nufi ɗaya suka kawo shi a gaban shari’a,

13 suka ce, “Mutumin nan na rarrashin mutane, wai su bauta wa Allah ta hanyar da Shari’ar ta hana.”

14 Bulus na shirin yin magana ke nan sai Galiyo ya ce wa Yahudawan, “Ku Yahudawa! Da ma wani laifi ya yi, ko munafunci, da sai in iya sauraronku.

15 Amma tun da yake gardama ce kawai a kan kalmomi, da sunaye, da kuma shari’arku, ai, sai ku ji da ita, ku da kanku. Ni kam, ba ni da niyyar yin shari’a irin waɗannan abubuwa.”

16 Sai ya kore su daga ɗakin shari’a.

17 Sai duk suka kama Sastanisu, shugaban majami’a, suka yi masa dūka a gaban gadon shari’a. Amma Galiyo ko yă kula.

Bulus Ya Koma Antakiya ta Suriya

18 Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa’adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da ‘yan’uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila.

19 Sai suka isa Afisa, a can ne kuma ya bar su, shi kuwa ya shiga majami’a ya yi muhawwara da Yahudawa.

20 Sai suka roƙe shi ya ƙara jimawa a wurinsu, amma bai yarda ba.

21 Sai dai ya yi bankwana da su, ya ce, “Zan dawo wurinku in Allah ya so.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.

22 Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima, ya gaisa da Ikkilisiya, sa’an nan ya tafi Antakiya.

23 Bayan da ya ɗan jima a nan, ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ta Firijiya, yana bin gari gari, yana ƙarfafa dukan masu bi.

Afolos ya Yi Wa’azi a Afisa

24 To, wani Bayahude mai suna Afolos ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani ne kuwa, ya san Littattafai ƙwarai da gaske.

25 An karantar da shi tafarkin Ubangiji, da yake kuma muhimmanci ne ƙwarai, yakan yi ta magana kan al’amuran Yesu, yana kuma koyar da su sosai, amma fa baftismar Yahaya kaɗai ya sani.

26 Sai ya fara wa’azi gabagaɗi a majami’a, amma da Bilkisu da Akila suka ji maganarsa, suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai.

27 Da ya so hayewa zuwa ƙasar Akaya, ‘yan’uwa suka taimake shi, suka rubuta wa masu bi wasiƙa su karɓe shi hannu biyu biyu. Da kuwa ya isa, ya yi matuƙar taimako ga waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin alherin Ubangiji,

28 don yā kayar da Yahudawa ƙwarai a gaban jama’a, yana tabbatar musu ta wurin Littattafai cewa Almasihu dai Yesu ne.

Categories
A.M.

A.M. 19

Bulus a Afisa

1 To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi,

2 sai ya ce musu, “Kun sami Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma ji zuwan Ruhu Mai Tsarki ba.”

3 Sai ya ce, “To, wace baftisma ke nan aka yi muku?” Suka ce, “Irin ta Yahaya ce.”

4 Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.”

5 Da suka ji haka, aka yi musu baftisma da sunan Ubangiji Yesu.

6 Da Bulus ya ɗora musu hannu, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, suka kuwa yi magana da waɗansu harsuna, suna annabci.

7 Su wajen sha biyu ne duka duka.

8 Sai ya shiga majami’a yana wa’azi gabagaɗi, ya kuma yi wata uku yana muhawwara da su, yana kuma rinjayarsu a kan al’amarin Mulkin Allah.

9 Amma da waɗansu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushen wannan hanya gaban jama’a, sai ya rabu da su, ya keɓe masu bi, yana ta muhawwara da su a kowace rana makarantar Tiranas.

10 Shekara biyu ana wannan, har dukan mazaunan ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da al’ummai duka.

‘Ya’yan Siba

11 Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi waɗansu mu’ujizai da ba a saba gani ba,

12 har akan kai wa marasa lafiya adikansa, ko tufafinsa da yake sawa yana aiki, sun kuwa warke daga cuce-cucensu, baƙaƙen aljannu kuma sun rabu da su.

13 Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari, matsubbata, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake wa’azi.”

14 To, akwai ‘ya’ya bakwai maza, na wani babban firist na Yahudawa, mai suna Siba, duk suna yin wannan abu.

15 Amma aljanin ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma ku wane ne?”

16 Mutumin nan mai aljanin sai ya daka tsalle, ya fāɗa musu, ya fi ƙarfinsu dukkansu, ya ci ɗunguminsu, har suka fita daga gidan a guje, a tuɓe, suna masu rauni.

17 Wannan abu fa ya sanu ga dukan mazaunan Afisa, Yahudawa da al’ummai duka, duka kuma tsoro ya kama su, aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu.

18 Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu a fili.

19 Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone a gaban jama’a duka. Da suka yi wa littattafan nan kima, sai suka ga sun kai kuɗi azurfa dubu hamsin.

20 Sai kuma Maganar Ubangiji ta ƙara haɓaka, ta kuma fifita ƙwarai.

Hargitsi a Afisa

21 Bayan waɗannan al’amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”

22 Da ya aiki mataimakansa biyu Makidoniya, wato Timoti da Arastas, shi kuwa ya ɗan dakata a ƙasar Asiya.

23 A lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan hanya ba.

24 Domin akwai wani maƙerin farfaru, mai suna Dimitiriyas, mai ƙera surorin haikalin Artimas da azurfa, ba kuwa ƙaramar riba yake jawo wa masu yin wannan sana’a ba.

25 Sai ya tara su da duk ma’aikatan irin wannan sana’a, ya ce, “Ya ku jama’a, kun sani fa da sana’ar nan muke arziki.

26 Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.

27 Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.”

28 Da suka ji haka suka hasala ƙwarai, suka kuma ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

29 Sai garin duk ya ruɗe, jama’a suka ruga zuwa dandali da nufi ɗaya, suna jan Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya, abokan tafiyar Bulus.

30 Bulus ya so shiga taron nan, amma masu bi suka hana shi.

31 Waɗansu zaɓaɓɓun mutanen ƙasar Asiya, waɗanda suke abokansa, su ma suka aika masa, suka roƙe shi kada ya kuskura ya shiga dandalin nan.

32 Taron kuwa, waɗansu suka ta da murya su ce kaza, waɗansu su ce kaza, don duk taron a ruɗe yake, yawancinsu ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba.

33 Da Yahudawa suka gabatar da Iskandari, waɗansu suka ɗauka a kan shi ne sanadin abin. Iskandari kuwa ya ɗaga hannu a yi shiru, don ya kawo musu hanzari,

34 amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa’a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

35 To, da magatakardan garin ya kwantar da hankalin jama’a, ya ce, “Ku mutanen Afisa! Wane mutum ne bai san cewa musamman birnin Afisawa ne suke kula da haikalin mai girma Artimas ba, da kuma dutsen nan da ya faɗo daga sama?

36 To, da yake ba dama a yi musun waɗannan abubuwa, ai, ya kamata ku natsu, kada ku yi kome da garaje.

37 Ga shi, kun kawo mutanen nan, su kuwa ba su yi sata a ɗakin uwargijiya ba, ba su kuma saɓi uwargijiyarmu ba.

38 To, in Dimitiriyas da abokan sana’arsa suna da wata magana a game da wani, ai, ga ɗakin shari’a a buɗe, ga kuma mahukunta, sai su kai ƙara.

39 Amma in wani abu kuke nema dabam, to, ai, sai a daidaita a majalisa ke nan.

40 Hakika muna cikin hatsarin amsa ƙara a kan tawaye saboda al’amarin nan na yau, tun da yake ba za mu iya ba da wani hanzari game da taron hargitsin nan ba.”

41 Da ya faɗi haka ya sallami taron.

Categories
A.M.

A.M. 20

Bulus Ya Koma Makidoniya da Hellas

1 Bayan hargowar nan ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.

2 Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa masu zuciya ƙwarai, ya zo ƙasar Hellas,

3 ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa’ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.

4 Subataras Babiriye, ɗan Burus, shi ya raka shi, tare da Aristarkus da Sakundas, mutanen Tasalonika, da Gayus Badarbe, da Timoti, har ma da Tikikus da Tarofimas, mutanen Asiya,

5 waɗanda suka riga tafiya suka jira mu a Taruwasa.

6 Mu kuwa muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa, bayan idin abinci marar yisti, muka iske su a Taruwasa bayan kwana biyar. Nan muka zauna har kwana bakwai.

Taruwar Bankwana a Taruwasa

7 A ranar farko ta mako kuma, da muka taru don gutsuttsura gurasa, Bulus ya yi masu jawabi, don ya yi niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta jan jawabin nasa har tsakar dare.

8 Akwai kuwa fitilu da yawa a benen da muka taru.

9 Da wani saurayi a zaune a kan taga, mai suna Aftikos, sai barci ya ci ƙarfinsa sa’ad da Bulus yake ta tsawaita jawabi, da barci mai nauyi ya kwashe shi, sai ya faɗo daga can hawa na uku, aka ɗauke shi matacce.

10 Amma Bulus ya sauka ƙasa, ya miƙe a kansa, ya rungume shi, ya ce, “Kada ku damu, ai, yana da rai.”

11 Da Bulus ya koma sama, ya gutsuttsura gurasa ya ci, ya daɗe yana magana da su, har gari ya waye, sa’an nan ya tashi.

12 Sai suka tafi da saurayin nan a raye, daɗin da suka ji kuwa ba kaɗan ba ne.

Tafiya a Teku daga Taruwasa zuwa Militas

13 Mu kuwa muka yi gaba zuwa jirgin, muka miƙe sai Asus da nufin ɗaukar Bulus daga can, don dā ma haka ya shirya, shi kuwa ya yi niyyar bi ta ƙasa.

14 Da ya same mu a Asus, muka ɗauke shi a jirgin, muka zo Mitilini.

15 Daga nan kuma muna tafe a jirgin ruwan dai, kashegari kuma sai ga mu daura da tsibirin Kiyos. Kashegari kuma, ga mu a tsibirin Samas, kashegari kuma sai Militas.

16 Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Afisa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, in mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.

Bulus Ya Yi wa Dattawan Ikkilisiyar Afisa Jawabi

17 Daga Militas ne ya aika Afisa a kira masa dattawan Ikkilisiya.

18 Da suka zo wurinsa sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san irin zaman da na yi a cikinku, tun ran da na sa ƙafata a ƙasar Asiya,

19 ina bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u, har da hawaye, da gwaggwarmaya iri iri da na sha game da makircin Yahudawa.

20 Kun kuma san yadda ban ji nauyin sanar da ku kowane abu mai amfani ba, ina koya muku a sarari, da kuma gida gida,

21 ina tabbatar wa Yahudawa da al’ummai duka sosai wajibcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijinmu Yesu.

22 To, ga shi kuma, yanzu zan tafi Urushalima, Ruhu yana iza ni, ban kuwa san abin da zai same ni a can ba,

23 sai dai Ruhu Mai Tsarki yakan riƙa tabbatar mini a kowane gari, cewa ɗauri da shan wuya na dākona.

24 Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.

25 To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.

26 Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa na kuɓuta daga hakkin kowa,

27 domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.

28 Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.

29 Na sani bayan tashina waɗansu mugayen kyarketai za su shigo a cikinku, ba kuwa za su ji tausayin garken ba.

30 Har ma a cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.

31 Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna, shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye.

32 To, yanzu na danƙa ku ga Ubangiji, maganar alherinsa kuma tă kiyaye ku, wadda ita take da ikon inganta ku, ta kuma ba ku gādo tare da dukan tsarkaka.

33 Ban yi ƙyashin kuɗin kowa ba, ko kuwa tufafin wani.

34 Ku da kanku kun sani hannuwan nan nawa su suka biya mini bukace-bukacena, da na waɗanda suke tare da ni.

35 Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”

36 Da Bulus ya faɗi haka, ya durƙusa, duka suka yi addu’a tare.

37 Sai duk suka fashe da kuka, suka rungume Bulus, suna ta sumbantarsa,

38 suna baƙin ciki tun ba ma saboda maganar da ya faɗa ba, cewa ba za su ƙara ganinsa ba. Daga nan suka rako shi har bakin jirgi.