Categories
A.M.

A.M. 21

Tafiyar Bulus zuwa Urushalima

1 Sa’ad da muka rabu da su da ƙyar, muka shiga jirgi muka miƙa sosai zuwa tsibirin Kos, kashegari kuma sai Rodusa, daga nan kuma sai Batara.

2 Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa ƙasar Finikiya, muka shiga muka tafi.

3 Da muka tsinkayo tsibirin Kubrus, muka mai da shi hagun, muka ci gaba zuwa ƙasar Suriya, muka sauka a Taya, don a nan ne jirgin zai sauke kayansa.

4 Da muka sami inda masu bi suke, muka zauna a nan kwana bakwai. Sai Ruhu ya iza su suka gaya wa Bulus kada ya je Urushalima.

5 Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da ‘ya’yansu, suka raka mu bayan gari, sa’an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu’a, muka yi bankwana da juna.

6 Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.

7 Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da ‘yan’uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu.

8 Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.

9 Shi kuwa yana da ‘ya’ya huɗu ‘yan mata, masu yin annabci.

10 To, muna nan zaune ‘yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya.

11 Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al’ummai.’ ”

12 Da muka ji haka, mu da waɗanda suke wurin muka roƙi Bulus kada ya je Urushalima.

13 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”

14 Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Ubangiji ya yi yadda ya so.”

15 Bayan ‘yan kwanakin nan muka shirya muka tafi Urushalima.

16 Waɗansu masu bi daga Kaisariya suka rako mu, suka kawo mu wurin Manason, mutumin Kubrus, wani daɗaɗɗen mai bi, wanda za mu sauka a gunsa.

Bulus Ya Ziyarci Yakubu

17 Da muka zo Urushalima, ‘yan’uwa suka karɓe mu da murna.

18 Kashegari Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan Ikkilisiya kuwa duk suna nan.

19 Bayan da ya gaisa da su, sai ya shiga bayyana musu filla filla abubuwan da Allah ya yi a cikin al’ummai ta wurin hidimarsa.

20 Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan’uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari’a.

21 An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne kake koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al’ummai su yar da Shari’ar Musa. Wai kuma kana ce musu kada su yi wa ‘ya’yansu kaciya, ko kuwa su bi al’adu.

22 To, ƙaƙa ke nan? Lalle za su ji labarin zuwanka.

23 Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu da suka ɗauki wa’adi.

24 Sai ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka, kowa zai sani duk abin da aka gaya musu game da kai, ba wata gaskiya a ciki, kai kuma kana kiyaye Shari’a.

25 Amma game da al’ummai da suka ba da gaskiya, mun aika da wasiƙa a kan mun hukunta, cewa su guji cin abin da aka yanka wa gunki, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.”

26 Sa’an nan Bulus ya ɗibi mutanen nan, kashegari kuma da suka tsarkaka tare, sai ya shiga Haikali domin ya sanar da ranar cikar tsarkakewar tasu, wato ranar da za a ba da sadaka saboda kowannensu.

An Kama Bulus Cikin Haikali

27 Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, Yahudawan ƙasar Asiya suka gan shi a Haikalin, sai suka zuga taron duka, suka danƙe shi,

28 suna ihu suna cewa, “Ya ku ‘yan’uwa Isra’ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko’ina yana koya wa mutane su raina jama’armu da Shari’a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al’ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”

29 Don dā ma can sun ga Tarofimas Ba’afise tare da shi a cikin gari, sun kuma zaci Bulus ya kawo shi Haikalin.

30 Sai duk garin ya ruɗe, jama’a suka ɗungumo a guje suka danƙe Bulus, suka ja shi waje daga Haikalin, nan da nan kuma aka rufe ƙofofi.

31 Suna neman kashe shi ke nan, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar yaƙi, wai Urushalima duk ta hargitse.

32 A nan tāke ya ɗibi soja da jarumawa, suka ruga zuwa wajensu. Su kuwa da ganin shugaban da soja suka daina dūkan Bulus.

33 Sai shugaban ya matsa kusa ya kama Bulus, ya yi umarni a ɗaure shi da sarƙa biyu, sa’an nan ya tambaya ko shi wane ne, da abin da kuma ya yi.

34 Taron kuwa suka ɗau kururuwa, waɗansu suka ce kaza, waɗansu suka ce kaza. Don tsananin hargowa ma har ya kasa samun ainihin tushen maganar, ya yi umarni a kai shi kagarar sojoji.

35 Da Bulus ya zo ga bakin matakala, sai da soja suka kinkime shi saboda haukan taron,

36 don taron jama’a na dannowa a bayansu, suna ihu suna cewa, “A yi da shi!”

Hanzarin Bulus

37 An yi kusan shigar da Bulus kagarar sojoji ke nan, sai ya ce wa shugaban, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai shugaban ya ce, “Ashe, ka iya Helenanci?

38 Shin, ba kai ne Bamasaren nan da shekarun baya ya haddasa tawaye ba, har ya ja mutanen nan dubu huɗu masu kisankai jeji?”

39 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Ai, ni Bayahude ne na Tarsus ta ƙasar Kilikiya, ɗan shahararren birni, ina roƙonka ka bar ni in yi wa mutane jawabi.”

40 Da ya ba shi izini, sai Bulus ya tsaya a kan matakala, ya ɗaga wa jama’a hannu su yi shiru. Da suka yi tsit, sai ya yi musu magana da Yahudanci.

Categories
A.M.

A.M. 22

1 “Ya ku ‘yan’uwa da shugabanni, ku ji hanzarin da zan kawo muku a yanzu.”

2 Da suka ji ya yi musu magana da Yahudanci, sai suka ƙara natsuwa. Sa’an nan ya ce,

3 “Ni bayahude ne, haifaffen Tarsus, ƙasar Kilikiya, amma a nan garin na girma, aka kuma karantar da ni wurin Gamaliyal, bisa ga tsarin tsanantacciyar hanyar nan ta Shari’ar kakanninmu. Ina mai himmar bauta wa Allah, kamar yadda dukanku kuke a yau,

4 har na tsananta wa masu bin wannan hanya, ina karkashe su, ina ɗaure mutane maza da mata, ina jefa su a kurkuku.

5 Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jama’a za su iya shaidata, daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga ‘yan’uwanmu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda suke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.”

Bulus Ya Ba Da Labarin Juyowarsa

6 “Ina cikin tafiya, da na yi kusa da Dimashƙu, wajen rana tsaka, kwamfa sai wani matsanancin haske ya bayyano daga sama, ya haskaka kewaye da ni.

7 Sai na fāɗi, na kuma ji wata murya tana ce mini, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?’

8 Ni kuma na amsa na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai ya ce mini, ‘Ni ne Yesu Banazare wanda kake tsananta wa.’

9 To, waɗanda suke tare da ni sun ga hasken, amma ba su ji kalmomin mai yi mini maganar nan ba.

10 Sai na ce, ‘To, me zan yi, ya Ubangiji?’ Sai ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka shiga Dimashƙu, a can ne za a faɗa maka duk abin da aka ɗora maka ka yi.’

11 Da na kāsa gani saboda tsananin hasken nan, sai waɗanda suke tare da ni suka yi mini jagora, har na isa Dimashƙu.

12 “Sai kuma wani mai suna Hananiya, mai bautar Allah ne wajen bin Shari’a, wanda duk Yahudawan da suke zaune a can suke yabo,

13 ya zo ya tsaya a kusa da ni, ya ce mini, ‘Ya ɗan’uwana Shawulu, ganinka yă komo maka.’ Nan tāke, sai ganina ya komo, na kuwa gan shi.

14 Sai ya ce, ‘Allahn kakanninmu ya zaɓe ka don kă san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji jawabi daga bakinsa.

15 Don za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abin da ka gani, ka kuma ji.

16 To, a yanzu me kake jira? Tashi, a yi maka baftisma a wanke zunubanka ta wurin kira bisa sunansa.’ ”

Kiran Bulus zuwa ga Al’ummai

17 “Da na komo Urushalima, ina addu’a a Haikali, sai wahayi ya zo mini.

18 Na gan shi, yana ce mini, ‘Yi sauri maza ka fita daga Urushalima, don ba za su yarda da shaidarka a kaina ba.’

19 Ni kuma na ce, ‘Ya Ubangiji, ai, su ma kansu sun sani a kowace majami’a na ɗaɗɗaure waɗanda suka gaskata da kai, na kuma daddoke su.

20 Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanas, mashaidin nan naka, ni ma ina a tsaye a gun, ina goyon bayan abin da aka yi, har ma ina tsare tufafin masu kisansa.’

21 Sai ya ce mini, ‘Tashi ka tafi, zan aike ka can nesa a wurin al’ummai.’ ”

Shugaba Ya Tsare Bulus

22 Suna ta sauraronsa har ya iso kalmar nan, sai suka ɗau ihu suka ce, “A kashe shi! A raba irin mutumin nan da duniya, bai kyautu ya rayu ba!”

23 Da suka dinga ihu suna kaɗa mayafansu suna ta ature da ƙura,

24 sai shugaba ya yi umarni a kai Bulus kagarar soja a tuhume shi da bulala, don yă san abin da ya sa suke masa ihu haka.

25 Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da ‘yancin Roma bulala, ba ko bin ba’asi?”

26 Da jarumin ɗin ya ji haka, sai ya je ya shaida wa shugaban, ya ce, “Me kake shirin yi ne? Mutumin nan fa Barome ne.”

27 Sai shugaban ya zo ya ce wa Bulus, “Faɗa mini gaskiya, kai kuwa Barome ne?” Sai ya ce, “I”.

28 Sai shugaban ya amsa ya ce, “Ni fa da kuɗi masu yawa na sami ‘yancin nan.” Bulus ya ce, “ni kuwa da shi aka haife ni.”

29 Saboda haka, waɗanda suke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne, sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.

Bulus a gaban ‘Yan Majalisa

30 Kashegari kuma da shugaban ya so sanin ainihin ƙarar da Yahudawa suke yi a kan Bulus, sai ya kwance shi, ya yi umarni manyan firistoci da dukan majalisa su taru, sa’an nan ya sauko da Bulus ya tsai da shi a gabansu.

Categories
A.M.

A.M. 23

1 Sai Bulus ya zuba wa majalisar ido ya ce, “Ya ku ‘yan’uwa, bautar Allah nake yi da lamiri mai kyau har ya zuwa yau.”

2 Sai Hananiya babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa.

3 Sai Bulus ya ce masa, “Kai munafiƙi, kai ma Allah zai buge ka! Ashe, wato kana zaune kana hukunta ni bisa ga Shari’a ne, ga shi kuwa kana yin umarni a doke ni, a saɓanin Shari’a?”

4 Sai waɗanda suke tsaye a wurin suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”

5 Sai Bulus ya ce, “Ai, ban sani shi ne babban firist ba, ‘yan’uwa, don a rubuce yake cewa, ‘Kada ka munana shugaban jama’a.’ ”

6 Amma da Bulus ya ga sashe ɗaya Sadukiyawa ne, ɗayan kuma Farisiyawa, ya ɗaga murya a majalisar ya ce, “Ya ‘yan’uwa, ni ma Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ga shi kuwa, saboda na sa zuciya ga tashin matattu ne ake yi mini shari’a.”

7 Da ya faɗi haka sai gardama ta tashi a tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, har taron ya rabu biyu.

8 Sadukiyawa sun ce, wai ba tashin matattu, ba kuma mala’iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.

9 Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala’ika ya yi masa magana fa?”

10 Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, shugaban ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi a kagarar soja.

11 Da daddare sai Ubangiji ya tsaya a kusa da Bulus, ya ce, “Ka yi ƙarfin hali, don kamar yadda ka shaide ni a Urushalima, haka kuma lalle ne ka shaide ni a Roma.”

Ƙulla Shawara a Kashe Bulus

12 Da gari ya waye, Yahudawa suka gama baki suka yi rantsuwa, cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe Bulus.

13 Waɗanda suka ƙulla wannan makirci kuwa sun fi mutum arba’in.

14 Sai suka je wurin manyan firistoci da shugabanni, suka ce, “Mun yi wata babbar rantsuwa, cewa za mu zauna ba ci ba sha sai mun kashe Bulus.

15 Saboda haka, yanzu ku da majalisa ku shaida wa shugaban soja ya kawo muku shi, kamar kuna so ne ku ƙara bincika maganarsa sosai, mu kuwa a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso.”

16 To, ɗan ‘yar’uwar Bulus ya ji labarin farkon da za su yi, ya kuma je ya shiga kagarar soja ya gaya wa Bulus.

17 Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.”

18 Sai jarumin ya ɗauki saurayin ya kai shi gun shugaba, ya ce, “Ɗan sarƙan nan, Bulus, ya kira ni, ya roƙe ni in kawo saurayin nan a wurinka, don yana da wata maganar da zai gaya maka.”

19 Sai shugaban ya kama hannun saurayin, ya ja shi a waje ɗaya, ya tambaye shi a keɓance, “Wace magana za ka gaya mini?”

20 Yaron ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kai musu Bulus majalisa gobe, kamar suna so su ƙara bincika maganarsa sosai.

21 Amma kada ka yardar musu, don fiye da mutum arba’in daga cikinsu suna fakonsa, sun kuma yi rantsuwa a kan ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye suke, yardarka kawai suka jira.”

22 Sai shugaban ya sallami saurayin ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka sanar da ni maganar nan.”

An Aika da Bulus zuwa ga Mai Mulki Filikus

23 Sa’an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba’in, da ‘yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.”

24 Ya kuma yi umarni su shirya wa Bulus dabbobin da zai hau, don su kai shi wurin mai mulki Filikus lafiya.

25 Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka:

26 “Daga Kalaudiyas Lisiyas zuwa ga mafifici mai mulki Filikus. Gaisuwa mai yawa.

27 Bayan haka mutumin nan, Yahudawa sun kama shi, suna kuma gab da kashe shi, sai na yi farat na je da soja na ƙwato shi, saboda na ji cewa shi Barome ne.

28 Da ina so jin laifin da suke zarginsa a kai, sai na kai shi majalisarsu.

29 Na kuwa tarar suna zarginsa a kan maganar Shari’arsu, amma laifin da suka ɗora masa bai kai ga kisa ko ɗauri ba.

30 Da aka buɗa mini cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, nan da nan na aika da shi a gare ka, na kuma umarci masu ƙararsa su faɗi ƙararsu a gabanka. Wassalam.”

31 Saboda haka, sojan suka ɗauki Bulus, kamar yadda aka umarce su, suka kai shi Antibatiris da daddare.

32 Kashegari kuma suka bar barade su ci gaba da shi, su kuwa suka koma kagarar soja.

33 Da baraden suka isa Kaisariya, suka ba mai mulkin wasiƙar, suka kai Bulus a gabansa.

34 Da ya karanta wasiƙar, ya tambayi Bulus ko shi mutumin wane lardi ne? Da ya ji daga Kilikiya yake,

35 ya ce, “Zan saurari maganarka duka, in masu ƙararka sun zo.” Sai kuma ya yi umarni a tsare shi a fadar Hirudus.

Categories
A.M.

A.M. 24

An Kai Ƙarar Bulus

1 Bayan kwana biyar sai babban firist, Hananiya, ya zo tare da waɗansu shugabanni, da kuma wani lauya, mai suna Tartulus, suka yi ƙarar Bulus a gaban mai mulki.

2 Da aka kirawo Tartulus, ya shiga kai ƙarar Bulus, ya ce, “Ya mafifici Filikus, tun da yake ta gare ka ne muke zaman lafiya ƙwarai, ta tsinkayarka ne kuma ake kyautata zaman jama’armu,

3 kullum muna yarda da haka ƙwarai a ko’ina, tare da godiya ba iyaka.

4 Amma don kada in gajiyad da kai, ina roƙonka a cikin nasiharka, ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.

5 Mun tarar da mutumin nan fitinanne ne, yana ta da hargitsi tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya, shi kuma ne turun ɗariƙar Nazarawa.

6 Har ma yana nema ya tozarta Haikali, amma muka kama shi. [Niyyarmu ce mu hukunta shi bisa ga shari’armu.

7 Amma shugaba Lisiyas ya zo ya ƙwace shi daga hannunmu ƙarfi da yaji,

8 ya yi umarni masu ƙararsa su zo a gabanka.] In kuwa ka tuhume shi da kanka, za ka iya tabbatarwa daga bakinsa duk ƙarar da muke tāsarwa.”

9 Yahudawa ma suka goyi bayan haka, suna tabbatarwa haka abin yake.

Hanzarin Bulus a gaban Filikus

10 Da mai mulki ya alamta wa Bulus ya yi magana, sai ya amsa ya ce, “Tun da na sani ka yi shekaru da yawa kana yi wa jama’ar nan shari’a, da farin ciki zan kawo hanzarina.

11 Ai, ka iya tabbatarwa, bai fi kwana goma sha biyu ba tun da na tafi Urushalima yin sujada.

12 Ba su kuwa taɓa samuna ina muhawwara da kowa ba, ko kuwa ta da husuma har mutane su taru a Haikali, ko a majami’u, ko kuwa a cikin birni.

13 Ba kuma za su iya tabbatar maka abin da yanzu suke ƙarata a kai ba.

14 Amma na yarda cewa, bisa ga hanyar nan da suke kira ‘Ɗariƙa’ nake bauta wa Allahn kakanninmu, nake kuma gaskata duk abin da yake a rubuce a cikin Attaura da kuma littattafan annabawa.

15 Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma suke sawa, wato za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.

16 Saboda haka, a kullum nake himma in kasance da lamiri marar abin zargi a wurin Allah da wurin mutane.

17 To, bayan ‘yan shekaru sai na je domin in kai gudunmawa ga jama’armu, in kuma yi sadaka.

18 Ina cikin yin haka sai suka same ni a tsarkake a Haikali, ba kuwa da wani taro ba, balle hargowa. Amma akwai waɗansu Yahudawa daga ƙasar Asiya–

19 su ne kuwa ya kamata su zo nan a gabanka su yi ƙarata, in suna da wata magana a game da ni.

20 Ko kuwa waɗannan mutane kansu su faɗi laifina da suka samu, sa’ad da na tsaya a gaban majalisa,

21 sai ko maganar nan ɗaya tak, da na ɗaga murya na faɗa, sa’ad da nake a tsaye a cikinsu, cewa, ‘Game da maganar tashin matattu ake yi mini shari’a a gabanku yau.’ ”

An Tsare Bulus

22 Filikus kuwa da yake yana da sahihin ilimi a game da wannan hanya ya dakatar da su, ya ce, “In shugaba Lisiyas ya iso, zan yanke muku shari’a.”

23 Ya kuma ba jarumi umarni ya tsare Bulus, amma ya sassauta masa, kada kuwa ya hana mutanensa zuwa wurinsa su kula da shi.

24 Bayan ‘yan kwanaki Filikus ya zo tare da matarsa, Durusila, wata Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus, ya kuwa saurare shi a kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu.

25 Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”

26 Don yana sa rai Bulus zai ba shi kuɗi, shi ya sa ya yi ta kiransa a kai a kai, yana zance da shi.

27 Amma bayan shekara biyu sai Borkiyas Festas ya gāji Filikus. Filikus kuwa don neman farin jini a wurin Yahudawa, ya bar Bulus a ɗaure.

Categories
A.M.

A.M. 25

Bulus Ya Ɗaukaka Ƙara zuwa ga Kaisar

1 To, da Festas ya iso lardinsa, bayan kwana uku sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.

2 Sai manyan firistoci da manyan Yahudawa suka kai ƙarar Bulus gunsa, suka roƙe shi

3 ya kyauta musu, ya aika a zo da shi Urushalima, alhali kuwa sun shirya ‘yan kwanto su kashe shi a hanya.

4 Amma Festas ya amsa ya ce, “Bulus yana a tsare a Kaisariya, ni ma kuwa da kaina ina niyyar zuwa can kwanan nan.”

5 Ya kuma ce, “Saboda haka, sai waɗansu manya a cikinku su taho tare da ni, in kuwa mutumin nan na da wani laifi, su yi ƙararsa.”

6 Bai fi kwana takwas ko goma a wurinsu ba, sai ya tafi Kaisariya. Kashegari kuma ya zauna a kan gadon shari’a, ya yi umarni a zo da Bulus.

7 Da ya zo, Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi a tsaitsaye, suna ta kawo ƙararraki masu yawa masu tsanani a game da shi, waɗanda ma suka kasa tabbatarwa.

8 Amma Bulus ya kawo hanzarinsa ya ce, “Ni ban yi wani laifi game da shari’ar Yahudawa, ko Haikali, ko a game da Kaisar ba, ko kaɗan.”

9 Festas kuwa don neman farin jini wurin Yahudawa, ya amsa ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a kan waɗannan abubuwa a gabana?”

10 Amma Bulus ya ce, “Ai, a tsaye nake a majalisar Kaisar, a inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wa Yahudawa wani laifi ba, kai kanka kuwa ka san da haka sarai.

11 To, in ni mai laifi ne, har na aikata abin da ya isa kisa, ai, ba zan guji a kashe ni ba, amma in ba wata gaskiya a cikin ƙarata da suke yi, to, ba mai iya bashe ni gare su don a faranta musu rai. Na nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar.”

12 Bayan da Festas ya yi shawara da majalisa, sai ya amsa ya ce, “To, ka nema a ɗaukaka ƙararka gaban Kaisar! Gun Kaisar kuwa za ka tafi.”

Bulus a gaban Agaribas da Barniki

13 Bayan ‘yan kwanaki sai sarki Agaribas da Barniki, suka zo Kaisariya don su yi wa Festas maraba.

14 Da yake kuma sun yi kwanaki da dama a can, sai Festas ya rattaba wa sarki labarin Bulus, ya ce, “Akwai wani mutumin da Filikus ya bari a ɗaure,

15 wanda sa’ad da nake Urushalima manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka kawo mini ƙararsa, suka roƙe ni in yi masa hukunci.

16 Ni kuwa na amsa musu na ce, ba al’adar Romawa ba ce a yi wa wani hukunci, don faranta wa wani rai, ba tare da masu ƙarar, da wanda aka kai ƙara, sun kwanta a gaban shari’a ba, ya kuma sami damar kawo hanzarinsa game da ƙarar da aka tāsar.

17 Saboda haka, da suka zo nan tare, ban yi wani jinkiri ba, sai kawai na hau gadon shari’a kashegari, na kuma yi umarni a kawo mutumin.

18 Da masu ƙarar suka tashi tsaye, ba su kawo wata mummunar ƙara yadda na zata a game da shi ba,

19 sai dai waɗansu maganganu da suka ɗora masa a game da addininsu, da kuma wani, wai shi Yesu, wanda ya mutu, amma Bulus ya tsaya a kan, wai yana da rai.

20 Ni kuwa da na rasa yadda zan bincika waɗannan abubuwa, sai na tambayi Bulus ko ya yarda ya je Urushalima a yi masa shari’a a can a kan waɗannan abubuwa.

21 Amma da Bulus ya nema a dakatar da maganarsa sai Augustas ya duba ta, sai na yi umarni a tsare shi har kafin in aika da shi zuwa gun Kaisar.”

22 Sai Agaribas ya ce wa Festas, “Ni ma dai na so in saurari mutumin nan da kaina.” Festas ya ce, “Kā kuwa ji shi gobe.”

23 To, kashegari sai Agaribas da Barniki suka zo a cikin alfarma, suka shiga ɗakin majalisa tare da shugabannin yaƙi da kuma jigajigan garin. Sai aka shigo da Bulus da umarnin Festas.

24 Sai Festas ya ce, “Ya sarki Agaribas, da dukan mutanen da suke tare da mu, kun ga mutumin nan da duk jama’ar Yahudawa suka kawo mini ƙararsa a Urushalima, da kuma nan, suna ihu, bai kamata a bar shi da rai ba.

25 Amma ni ban ga abin da ya yi wanda ya isa kisa ba. Tun da kuma shi kansa ya nema a mai da shari’arsa a gaban Augustas, ƙudura in aika da shi zuwa wurinsa.

26 Amma ba ni da wata tabbatacciyar magana da zan rubuta wa ubangijina game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku, musamman kuwa a gabanka, ya sarki Agaribas, don bayan an yi bincike, ko na abin da zan rubuta.

27 Don ni, a ganina, wauta ce a aika da ɗan sarƙa, ba tare da an nuna laifofin da ya yi ba.”

Categories
A.M.

A.M. 26

Hanzarin Bulus a gaban Agaribas

1 Daga nan, sai Agaribas ya ce wa Bulus, “An ba ka izinin yin magana.”

Sa’an nan fa Bulus ya ɗaga hannu, ya fara kawo hanzarinsa ya ce,

2 “Lalle na yi arziki, ya sarki Agaribas, da yake a gabanka ne zan kawo hanzarina yau a game da duk ƙarata da Yahudawa suka yi,

3 musamman da yake gwani ne kai ga sanin al’adun Yahudawa da maganganunsu. saboda haka, ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.

4 “Irin zaman da na yi tun daga ƙuruciyata, wato tun da farko, a cikin jama’armu da kuma a Urushalima har ya zuwa yau, sananne ne ga dukan Yahudawa.

5 Sun sani tun ainihi, in dai za su yarda su yi shaida, cewa lalle ni Bafarisiye ne bisa ga ɗariƙar nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu.

6 Ai, saboda na sa zuciya ga cikar alkawarin nan ne da Allah ya yi wa kakanninmu nake nan a tsaye a yi mini shari’a.

7 Alkwarin nan kuwa, shi ne wanda kabilanmu goma sha biyu suke himmantuwa ga bauta wa Allah dare da rana, suna sa zuciya su ga cikarsa. Saboda sa zuciyar nan kuma fa Yahudawa suke ƙarata, ya sarki!

8 Yaya cewa Allah yana ta da matattu sa’an nan, ya ƙi gaskatuwa a gare ku?

9 “To, ni kaina ma a dā na ga kamar wajibi ne in yi abubuwa da yawa, na gāba da sunan Yesu Banazare.

10 Na kuwa yi haka a Urushalima, har na sami izini daga manyan firstoci, na kulle tsarkaka da yawa a kurkuku. Har ma a lokacin da ake kashe su ina goyon bayan yin haka.

11 Na kuma sha gwada musu azaba a dukan majami’u, ina ƙoƙarin sa su yin saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.”

Labarin Juyowar Bulus

12 “Cikin halin haka ne, ina tafiya Dimashƙu da izinin manyan firistoci da kuma saƙonsu,

13 da rana a tsaka a hanya, ya sarki, na ga wani haske ya bayyano daga sama, fiye da hasken rana, duk ya haskaka kewaye da ni da abokan tafiyata.

14 Da duk muka fāɗi, sai na ji wata murya tana ce mini da yahudanci, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Da wuya a gare ka ka yi ta shuri bisa a kan tsini.’

15 Ni kuwa sai na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.

16 Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sa ka mai hidima, mashaidi kuma na abubuwan da ka gani a game da ni, da kuma abubuwa waɗanda zan bayyana maka a nan gaba.

17 Zan tsirar da kai daga jama’ar nan da kuma al’ummai, waɗanda zan aike ka a gare su,

18 domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”

Shaidar Bulus a Gaban Yahudawa da Al’ummai

19 “Saboda haka, ya sarki Agaribas, ban ƙi biyayya ga wahayin nan da ya zo mini daga Sama ba.

20 Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa’azi, sa’an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa’an nan kuma na yi wa al’ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.

21 Saboda wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a Haikali, har suna neman kashe ni.

22 Da na sami taimakon Allah kuwa, ga ni a nan har yanzu, ina shaida wa babba da yaro, ba na faɗar kome sai abin da annabawa da Musa suka ce zai auku,

23 cewa dai lalle ne Almasihu yă sha wuya, shi ne kuma zai fara tashi daga matattu, ya sanar da jama’ar nan da al’ummai haske.”

Bulus Yana Fata Agaribas Ya Gaskata

24 Bulus na cikin kawo hanzarinsa, sai Festas ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Bulus, kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”

25 Amma Bulus ya ce, “Ya mafifici Festas, ai, ban ruɗe ba, gaskiya nake faɗa, cikin natsuwa kuwa.

26 Ai, al’amarin nan sananne ne ga sarki, ina kuma masa magana gabagaɗi ne, gama na tabbata ba abin da ya kuɓuce wa hankalinsa cikin al’amarin nan, don wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba.

27 Ya sarki Agaribas, ka gaskata annabawa? Na dai sani ka gaskata.”

28 Sai Agaribas ya ce wa Bulus, “Wato a ɗan wannan taƙaitaccen lokaci kake nufin mai da ni Kirista?”

29 Bulus kuwa ya ce, “Ko a ɗan wannan, ko a mai yawa, ina fata ga Allah, ba kai kaɗai ba, har ma duk waɗanda suke saurarona a yau, su zama kamar yadda nake, sai dai banda sarƙar nan.”

30 Sai sarki ya tashi, haka kuma mai mulki da Barniki, da waɗanda suke a zaune tare da su.

31 Bayan sun keɓe waje ɗaya, suka yi shawara, suka ce, “Ai, mutumin nan bai yi wani abin da ya isa kisa ko ɗauri ba.”

32 Agaribas kuma ya ce wa Festas, “Ba don dai mutumin nan ya riga ya nemi ɗaukaka ƙararsa a gaban Kaisar ba, da sai a sake shi.”

Categories
A.M.

A.M. 27

Bulus Ya Shiga Jirgi zuwa Roma

1 Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu ‘yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.

2 Da muka shiga wani jirgi na Adaramitiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gaɓar Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu.

3 Kashegari ga mu a Sidon. Yuliyas kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya ba shi izini ya je ya gano abokansa, su yi masa taimako.

4 Da muka tashi daga nan a jirgin ruwa sai muka zaga ta bayan tsibirin Kubrus, saboda iska tana gāba da mu.

5 Bayan da muka haye bahar ɗin da yake kusa da kasar Kilikiya da ta Bamfiliya, muka isa Mira ta ƙasar Likiya.

6 A nan jarumin ya sami wani jirgin Iskandariya mai zuwa ƙasar Italiya, ya sa mu a ciki.

7 Muka yi kwana da kwanaki muna tafiya kaɗan kaɗan, har da ƙyar muka kai kusa da Kinidas. Da dai iska ta hana mu ci gaba, muka zaga ta bayan tsibirin Karita kusa da Salmoni.

8 Muna bin gefen gaɓarsa da ƙyar, har muka isa wani wuri mai suna Amintacciyar Mafaka, wadda take kusa da birnin Lasiya.

9 Da yake an ɓata lokaci mai yawa, tafiyar ma ta riga ta zama mai hatsari, lokacin azumi kuwa ya wuce, sai Bulus ya gargaɗe su,

10 ya ce musu, “Ya ku jama’a, na dai ga tafiyar nan za ta zamanto da masifa da hasara mai yawa, ba wai ta kaya da jirgi kawai ba, har ma ta rayukanmu.”

11 Amma jarumin soja, ya fi mai da hankali ga maganar mai tuƙin jirgin da kuma ta mai jirgin, a kan abin da Bulus ya faɗa.

12 Da yake mafakar nan ba ta kamaci jirage su ci damuna a ciki ba, sai yawanci suka kawo shawara a tashi daga nan, ko ta ƙaƙa su iya kaiwa Finikiya, wata mafakar tsibirin Karita, mai duban gabas maso arewa da kuma gabas maso kudu, su ci damuna a can.

Hadiri a Teku

13 Da iska ta buso daga kudu sannu sannu, a tsammaninsu muradinsu ya biya ke nan, sai suka janye anka suka bi ta gefen tsibirin Karita gab da gaci.

14 Ba da jimawa ba kuwa sai ga wata gawurtacciyar iska da ake kira Yurokilidon ta bugo daga tsibirin.

15 Da iskar ta bugo jirgin, har ya kasa fuskantarta, sai muka sallama mata, ta yi ta kora mu.

16 Da muka bi ta jikin wani ɗan tsibiri wai shi Kauda muka samu muka yi iko da ƙaramin jirginmu da ƙyar.

17 Bayan suka jawo ƙaramin jirgi ɗin a cikin babban jirgi, sai suka yi dabara suka ɗaɗɗaura igiyoyi ta gindin babban jirgin, suka rage shi. Don kuma gudun kada a fyaɗa su a yashin nan na Sirtis mai haɗiye kome, suka sauke filafilai, aka kora jirgin haka.

18 Saboda hadiri yana sa mu tangaɗi ƙwarai da gaske, kashegari sai suka fara watsar da kayan da jirgin ya ɗauko, a ruwa.

19 A rana ta uku kuma, su da kansu suka jefar da kayan aikin jirgin.

20 Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, gawurtacciyar iskar hadiri kuma ta yi ta bugunmu, sai muka fid da zuciya da tsira.

21 Da yake an daɗe ba cin abinci, sai Bulus ya miƙe a tsaye a tsakiyarsu, ya ce, “Ya ku jama’a, da kun ji maganata, da ba ku taso daga tsibirin Karita kun fāɗa wannan masifa da hasara ba.

22 To, a yanzu, ina yi muku gargaɗi ku yi ƙarfin hali, don ba wanda zai yi hasarar ransa a cikinku, sai dai a yi hasarar jirgin.

23 Don a daren jiya wani mala’ikan Allah wanda ni nasa ne, nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni,

24 ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’

25 Saboda haka, sai ku yi ƙarfin hali, ya ku jama’a, domin na gaskata Allah a kan cewa, yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka za a yi.

26 Amma fa lalle ne a fyaɗa mu a wani tsibirin.”

27 A dare na goma sha huɗu, ana ta kora mu sakaka a bahar Adariya, wajen tsakar dare sai masu tuƙi suka zaci mun yi kusa da ƙasa.

28 Sai suka gwada zurfin ruwan, suka sami gaba ashirin, da muka ci gaba kaɗan, sai suka sāke gwadawa, suka sami gaba goma sha biyar.

29 Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki anka guda huɗu na bayan jirgin, suka ƙagauta gari ya waye.

30 Masu tuƙi suna neman gudu daga jirgin ke nan, har sun zura ƙaramin jirgi a cikin ruwa, wai don a ga kamar za su ja su anka ɗin ne daga goshin jirgin su sake su,

31 sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.”

32 Sai sojan suka yayyanke igiyoyin ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.

33 Da gari ya yi kusan wayewa sai Bulus ya roƙe su su taɓa ɗan abinci, ya ce, “Yau fa kwana goma sha huɗu ke nan kuke zaman jira, ba wani abin da kuka ci.

34 Saboda haka, ina roƙonku ku ci abinci, don lafiyarku, tun da yake ba wanda ko gashin kansa zai yi ciwo a cikinku.”

35 Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci.

36 Sai duk suka farfado, su ma kansu suka ci abinci.

37 Mu duka a cikin jirgin kuwa mutum metan da saba’in da shida ne.

38 Da suka ci suka ƙoshi, sai suka riƙa rage wa jirgin nauyi, suka yi ta zub da alkama a cikin ruwa.

Ragargajewar Jirgi

39 Da gari ya waye ba su shaida ƙasar ba, amma dai sun lura da wani lungu da gaci mai yashi, sai kuma suka yi shawara cewa in mai yiwuwa ne su kai jirgin kan yashin.

40 Sai suka daddatse su anka duka, suka bar su a ruwa, suna kuma ɓalle maɗaurin abin juyar da jirgin a lokacin, sa’an nan kuma suka ta da filafilan goshin jirgin daidai iska, suka doshi gaci.

41 Amma da muka isa wata mahaɗar ruwa, sai suka tura jirgin ya dunguri yashi, har goshinsa ya cije ya kasa motsi, ƙarshensa kuma ya fara ragargejewa saboda haukan raƙuman ruwa.

42 Sai sojan suka yi niyya su kashe ‘yan sarka, don kada wani ya yi ninƙaya ya tsira.

43 Amma jarumin da ya so ya ceci Bulus, ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci,

44 sauran kuwa waɗansu suka hau katako, waɗansu kuma suka hau tarkacen jirgin. Da haka duk suka kai gaci lafiya.

Categories
A.M.

A.M. 28

Bulus a Tsibirin Malita

1 Bayan da muka tsira, sai muka ji, ashe, sunan tsibirin nan Malita ne.

2 Mutanen garin kuwa sun yi mana alheri matuƙar alheri, don sun hura wuta sun karɓe mu, mu duka, saboda ana ruwa, ga kuma sanyi.

3 Sa’ad da Bulus ya tattaro waɗansu ƙirare rungume guda ya sa a wutar, sai ga wani maciji ya bullo saboda zafi, ya ɗafe masa a hannu.

4 Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”

5 Bulus kuwa ya karkaɗe ƙwaron a cikin wutar, bai kuwa ji wani ciwo ba.

6 Su kuwa suna zaton wurin zai kumbura, ko kuwa farat ɗaya ya fāɗi matacce. Amma da aka daɗe suka ga ba abin da ya same shi, suka sāke magana suka ce lalle shi wani Allah ne.

7 A nan kusa kuwa akwai wani fili, mallakar shugaban tsibirin nan, mai suna Babiliyas. Shi ne ya karɓe mu, ya sauke mu a cikin martaba har kwana uku.

8 Ashe, uban Babiliyas yana a kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu’a, ya ɗora masa hannu ya warkar da shi.

9 Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkar da su.

10 Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da muke bukata.

Bulus Ya Isa Roma

11 Bayan wata uku muka tashi a cikin wani jirgin Iskandariya, wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwaye Maza.

12 Da muka zo Sirakusa muka kwana uku a nan.

13 Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana, iska ta taso daga kudu, kashegari kuma muka kai Butiyoli.

14 A nan muka tarar da waɗansu ‘yan’uwa, suka roƙe mu mu kwana bakwai tare da su. Da haka dai har muka isa Roma.

15 Da ‘yan’uwa na can suka ji labarinmu, sai da suka zo don su tarye mu har Kasuwar Abiyus, da kuma wurin nan da ake kira Maciya Uku. Da kuwa Bulus ya sadu da su, ya yi godiya ga Allah, jikinsa kuma ya yi ƙarfi.

16 Da muka shiga Roma aka yardar wa Bulus ya je ya sauka abinsa tare da sojan da yake tsaronsa.

Wa’azin Bulus a Roma

17 Bayan kwana uku ya kira manyan Yahudawan birnin. Da suka taru sai ya ce musu, “Ya ku ‘yan’uwa, ko da yake ban yi wa jama’armu wani laifi ba, ko laifi a game da al’adun kakanninmu, duk da haka an bashe ni ɗaurarre ga Romawa tun daga Urushalima.

18 Su kuwa da suka tuhume ni, suna so su sake ni, don ban yi wani laifi da ya isa kisa ba.

19 Amma da Yahudawa suka ƙi yarda, sai ya zamar mini dole in nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar, ba don ina ƙarar jama’armu ba ne.

20 Shi ya sa na nema in gana da ku, tun da yake dai saboda sa zuciyar nan da Isra’ila take yi ne nake ɗaure da sarƙan nan.”

21 Sai suka ce masa, “Mu kam, ba mu sami wata wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, ba kuwa wani ɗan’uwanmu da ya zo nan ya kawo labarinka, ko yă faɗi wata mummunar magana game da kai.

22 Amma muna so mu ji daga bakinka abin da yake ra’ayinka, don in dai ta ɗariƙar nan ne, mun sani ko’ina ana kushenta.”

23 Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa’an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.

24 Waɗansu sun rinjayu da maganarsa, amma waɗansu sun ƙi gaskatawa.

25 Da suka kasa yarda a junansu, kafin su watse sai Bulus ya yi musu magana ɗaya ya ce, “Ashe kuwa, Ruhu Mai Tsarki daidai ya faɗa, da ya yi wa kakanninku magana ta bakin Annabi Ishaya cewa,

26 ‘Je ka wurin jama’ar nan, ka ce,

Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,

Za ku gani kuma, amma ba za ku gane ba faufau.

27 Don zuciyar jama’ar nan ta yi kanta,

Sun toshe kunnuwansu,

Sun kuma runtse idanunsu,

Wai don kada su gani da idanunsu,

Su kuma ji da kunnuwansu,

Su kuma fahimta a zuciyarsu,

Har su juyo gare ni in warkar da su.’

28 To, sai ku sani, wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al’ummai, su kam za su saurara.”

29 (Da ya faɗi haka, sai Yahudawa suka tashi suna ta muhawwara da juna.)

30 Sai Bulus ya zauna a nan a gidan da yake haya, har shekara biyu cikakku, yana maraba da duk wanda ya je wurinsa,

31 yana ta wa’azin Mulkin Allah, da koyar da al’amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.