Categories
AYU

AYU 11

Zofar Ya Zargi Ayuba a kan Aikata Laifi

1 Zofar ya amsa.

2 “Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu?

Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai?

3 Ayuba,kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba?

Kana tsammani maganganunka na ba’a

Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?

4 Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne,

Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.

5 Da ma Allah zai amsa maka,

Ya yi magana gāba da kai,

6 Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa.

Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam.

Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.

7 “Kana iya gane matuƙa da iyakar

Girman Allah da na ikonsa?

8 Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba,

Amma ga shi, yana can nesa da kai,

Allah ya san lahira,

Amma kai ba ka sani ba.

9 Fāɗin girman Allah ya fi duniya

Ya kuma fi teku fāɗi.

10 Idan Allah ya kama ka ya gurfanar da kai gaban shari’a,

Wa zai iya hana shi?

11 Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani,

Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu.

12 Idan dakikan mutane sa yi hikima,

To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.

13 “Ayuba, ka shirya zuciyarka,

Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.

14 Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.

15 Sa’an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya,

Da ƙarfi da rashin tsoro.

16 Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka,

Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.

17 Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana.

Kwanakin ranka mafiya duhu

Za su yi haske kamar ketowar alfijir.

18 Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya,

Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa.

19 Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba,

Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka.

20 Amma mugaye za su dudduba ko’ina da fid da zuciya,

Ba su da wata hanyar da za su kuɓuta.

Sauraronsu kaɗai shi ne mutuwa.”

Categories
AYU

AYU 12

Ayuba Ya Ƙarfafa Ikon Allah da Hikimar Allah

1 Ayuba ya amsa.

2 “Aha! Ashe, kai ne muryar jama’a,

Idan ka mutu hikima ta mutu ke nan tare da kai.

3 Amma ni ma ina da hankali gwargwado, kamar yadda kake da shi,

Ban ga yadda ka fi ni ba.

Kowa ya san sukan abin da ka faɗa.

4 Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu,

Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi,

Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu’o’ina.

5 Ba ka shan wahalar kome, duk da haka ka maishe ni abin dariya.

Ka bugi mutumin da yake gab da fāɗuwa.

6 Amma ɓarayi da marasa tsoron

Allah suna zaune cikin salama,

Ko da yake ƙarfinsu ne kaɗai allahnsu.

7 “Don haka tsuntsaye da dabbobi sun fi ka sani,

Suna da abu mai yawa da za su koya maka.

8 Ka roƙi talikan da suke a duniya, da cikin teku, hikimar da suke da ita.

9 Dukansu sun sani ikon Ubangiji ne ya yi su.

10 Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa.

Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.

11 Amma kamar yadda harsunanku suke jin daɗin ɗanɗanar abinci,

Haka nan kuma kunnuwanku suke jin daɗin sauraren kalmomi.

12-13 “Tsofaffi suna da hikima,

Amma Allah yana da hikima da iko.

Tsofaffi suna da tsinkaya,

Amma Allah yana da tsinkaya da ikon aikatawa.

14 Sa’ad da Allah ya rurrushe, wa zai iya sāke ginawa?

Wa kuma zai iya fitar da mutumin da Allah ya sa a kurkuku?

15 Akan yi fari sa’ad da Allah ya hana ruwan sama,

Rigyawa takan zo sa’ad da ya kwararo ruwa.

16 Allah mai iko ne a kullum kuwa cikin nasara yake

Da macuci, da wanda aka cutar, duk ƙarƙashin ikon Allah suke.

17 Yakan mai da hikimar masu mulki wauta,

Yakan mai da shugabanni marasa tunani.

18 Yakan tuɓe sarakuna ya sa su kurkuku.

19 Yakan ƙasƙantar da firistoci da mutane masu iko.

20 Yakan rufe bakin waɗanda aka amince da su.

Yakan kawar da hikimar tsofaffi.

21 Yakan kunyatar da masu iko,

Ya hana wa masu mulki ƙarfi.

22 Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.

23 Yakan sa sauran al’ummai su yi ƙarfi su ƙasaita,

Sa’an nan ya fatattaka su, ya hallaka su.

24 Yakan sa shugabanninsu su zama wawaye,

Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata,

25 Su yi ta lalube cikin duhu, su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.”

Categories
AYU

AYU 13

Ayuba Ya Kāre Mutuncinsa

1-2 “Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa,

Na gane da shi sarai.

Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani.

Ba ku fi ni da kome ba.

3 Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba,

Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita.

4 Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi.

Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba.

5 Kada ku faɗi kome,

Wani sai ya ce kuna da hikima!

6 “Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata.

7 Me ya sa kuke yin ƙarya?

Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah?

8 Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba?

Kuna goyon bayan Allah?

Za ku goyi bayan Allah sa’ad da aka gurfanar da ni gaban shari’a?

9 Da Allah ya bincike ku sosai,

Zai iske wani abin kirki ne a cikinku?

Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane?

10 Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku,

Duk da haka zai tsauta muku,

11 Ikonsa kuwa zai razana ku.

12 Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai.

13 “Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana.

Duk abin da zai faru, ya faru.

14 A shirye nake in yi kasai da raina.

15 Na fid da zuciya ɗungum.

To, in Allah ya kashe ni, sai me?

Zan faɗa masa ƙarata.

16 Mai yiwuwa ne ƙarfin halina ya cece ni,

Tun da yake ba wani mugun mutumin da zai iya zuwa gaban Allah.

17 Sai a saurari bayanin da zan yi.

18 A shirye nake in faɗi ƙarata,

Domin na sani ina da gaskiya.

19 “Ya Allah, za ka yi ƙarata?

Idan kuwa ka yi, to, a shirye nake in yi shiru in mutu.

20 Ina da abu biyu da zan yi maka roƙo,

Ka yarda da su, sa’an nan ba zan yi ƙoƙari in ɓoye ba.

21 Wato ka daina hukuncin da kake yi mini,

Kada ka sa razanarka ta ragargaza ni.

22 “Ka fara yin magana, ya Allah, ni kuwa zan amsa.

Ko kuma ka bari in yi magana, sa’an nan ka amsa mini.

23 Kuskure da laifi guda nawa na yi?

Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su?

24 Me ya sa kake guduna?

Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi?

25 Ƙoƙari kake ka firgita ni?

Ni ba wani abu ba ne, ganye ne kawai,

Ka fāɗa wa tattaka da yaƙi ne kawai.

26 Ka kawo mugayen ƙararraki a kaina,

Har da laifofin da na yi na ƙuruciya.

27 Ka ɗaure ƙafata da sarƙoƙi,

Kakan lura da kowace takawata,

Har kana bin diddigin sawayena.

28 Saboda wannan na zama abin kallo,

ni kuwa kamar ragargazajjen itace ne, ko diddigaggiyar riga.”

Categories
AYU

AYU 14

Ayuba Ya Yi Tunani a kan Rashin Tsawon Rai

1 “Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.

2 Sukan yi girma su bushe nan da nan kamar furanni,

Sukan shuɗe kamar inuwa.

3 Na ma isa ka dube ni ne, ya Allah?

Ko ka gabatar da ni a gabanka,

Ka yi mini shari’a?

4 Ba wani abu tsarkakakke

Da zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.

5 Tsawon kwanakin ransa, an ƙayyade su tun can,

An ƙayyade yawan watannin da zai yi,

Ka riga ka yanke haka ya Allah, ba su sākuwa.

6 Ka kawar da fuska daga gare shi, ka rabu da shi,

Ka bar shi ya ji daɗin kwanakinsa na fama da aiki idan zai iya.

7 “Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare,

Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.

8 Ko da yake saiwoyinsa sun tsufa,

Kututturensa kuma ya ruɓe a ƙasa,

9 In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.

10 Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan,

Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?

11 “Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu,

Har tekuna kuma su ƙafe.

12 Amma matattu ba za su tashi ba daɗai,

Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan.

Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.

13 “Ya Allah, da ma a ce ka ɓoye ni a lahira,

Ka bar ni a ɓoye, har fushinka ya huce,

Sa’an nan ka sa lokacin da za ka tuna da ni!

14 Idan mutum ya mutu, zai sāke rayuwa kuma?

Amma zan jira lokaci mafi kyau,

In jira sai lokacin wahala ya wuce.

15 Sa’an nan za ka yi kira, ni kuwa zan amsa,

Za ka yi murna da ni, ni talikinka.

16 Sa’an nan za ka lura da kowace takawata

Amma ba za ka bi diddigin zunubaina ba.

17 Za ka soke zunubaina ka kawar da su,

Za ka shafe dukan kurakuran da na taɓa yi.

18 “Lokaci na zuwa sa’ad da duwatsu za su fāɗi,

Har ma za a kawar da duwatsun bakin teku.

19 Ruwa zai zozaye duwatsu, su ragu,

Ruwan sama mai ƙarfi zai kwashe jigawa,

Kai ma ka bar mutane, ba su da sauran sa zuciya ko kaɗan.

20 Ka fi ƙarfin mutum, ka kore shi har abada,

Fuskarsa ta rikiɗe sa’ad da ya mutu.

21 ‘Ya’yansa maza za su sami girma,

amma sam, ba zai sani ba,

Sam, ba wanda zai faɗa masa sa’ad da aka kunyatar da su.

22 Ciwon jikinsa da ɓacin zuciyarsa kaɗai yake ji.”

Categories
AYU

AYU 15

Elifaz Ya Tsauta wa Ayuba

1 Elifaz ya yi magana.

2 “Surutai, Ayuba! Surutai!

3 Ba wani mai hikima wanda zai yi magana irin taka,

Ko kuma ya kāre kansa da irin maganganun da ba su da ma’ana.

4 Kana karya jama’a, kana hana su jin tsoron Allah,

Kana hana su yin addu’a gare shi.

5 Mugun lamirinka shi ne yake magana yanzu,

Kana ƙoƙari ka ɓuya a bayan maganganunka na wayo.

6 Ba na bukata in kā da kai,

Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.

7 “Kana tsammani kai ne mutumin da aka haifa na farko?

Sa’ad da Allah ya yi duwatsu kana nan?

8 Ko ka taɓa jin shirye-shiryen da Allah ya yi?

Ko kai kaɗai kake da hikima a cikin mutane?

9 Ba wani abu da ka sani da mu ba mu sani ba.

10 Daga wurin mutanen da suka yi furfura muka koyi hikimarmu.

Mun koyi hikimarmu daga mutane waɗanda aka haife su

Tun kafin a haifi mahaifinka.

11 “Allah yana ta’azantar da kai,

Me ya sa har yanzu ka ƙi kulawa da shi?

Mun yi magana a madadinsa a natse da lafazi mai daɗi.

12 Amma ka ta da hankalinka,

Kana ta zazzare mana ido da fushi.

13 Fushi kake yi da Allah, kana ƙinsa.

14 Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai?

Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah?

15 Me ya sa Allah bai sakar wa mala’ikunsa kome ba?

Har su ma ba tsarkaka suke a gare shi ba.

16 Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa,

Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.

17 “Yanzu ka saurara, ya Ayuba, ga abin da na sani.

18 Mutane masu hikima sun koya mini gaskiya

Wadda suka koya daga wurin kakanninsu,

Ba su kuwa ɓoye mini asirin kome ba.

19 Ƙasaru ‘yantacciya ce daga baƙi

Ba wanda zai raba su da Allah.

20 “Mugun mutum mai zaluntar sauran mutane

Zai kasance da wahala muddin ransa.

21 Zai ji ƙarar muryoyi masu firgitarwa a kunnuwansa.

‘Yan fashi za su fāɗa masa

Sa’ad da yake tsammani ba abin da zai same shi.

22 Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba,

Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.

23 Yana ta yawon neman abinci, yana ta cewa, ‘Ina yake?’

Ya sani baƙin ciki ne yake jiransa a nan gaba. Kamar sarki mai iko,

24 Haka masifa take shirin fāɗa masa.

25 “Wannan shi ne ƙaddarar mutum,

Wanda ya nuna wa Allah yatsa,

Ya kuwa raina Mai Iko Dukka.

26 Wannan mutum mai girmankai ne, ɗan tawaye.

27 Ya ɗauki garkuwarsa kamar ɗan yaƙi,

Ya ruga don ya yi yaƙi da Allah.

28 Shi ne mutumin da ya ci birane da yaƙi,

Ya ƙwace gidajen waɗanda suka tsere,

Amma yaƙi ne zai hallaka birane da gidaje.

29 Arzikinsa ba zai daɗe ba,

Duk abin da ya mallaka ba zai daɗe ba.

Har inuwarsa ma za ta shuɗe,

30 Ba kuwa zai kuɓuta daga duhu ba.

Zai zama kamar itacen da wuta ta ƙone rassansa,

Kamar itace kuma da iska ta kaɗe furensa.

31 Idan wauta tasa ta kai shi ga dogara ga mugunta,

To, mugunta ce kaɗai zai samu.

32 Kafin kwanakinsa su cika zai bushe,

Zai bushe kamar reshe, ba zai ƙara yin ganye ba.

33 Zai ama kamar itacen inabi

Wanda ‘ya’yansa suka kakkaɓe tun kafin su nuna,

Kamar itacen zaitun wanda bai taɓa yin ‘ya’ya ba.

34 Marasa tsoron Allah ba za su sami zuriya ba,

Wuta za ta cinye gidajen da aka gina da dukiyar rashawa.

35 Waɗannan su ne irin mutanen da suke shirya tarzoma, su aikata mugunta.

Kullum zuciyarsu cike take da ruɗarwa.”

Categories
AYU

AYU 16

Ayuba Ya Yi Kukan abin da Allah Yake Yi

1 Ayuba ya yi magana.

2 “Ai, na taɓa jin magana irin wannan,

Ta’aziyyar da kake yi azaba ce kawai.

3 Ka dinga yin magana ke nan har abada?

A kullum maganarka ita ce dahir?

4 In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka,

Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu.

Da sai in kaɗa kaina da hikima,

In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.

5 Da sai in ba ka shawara ta ƙarfafawa,

In yi ta yi maka maganar ta’azantarwa.

6 “Amma ba abin da zan faɗa wanda zai taimaka,

Yin shiru kuma ba zai raba ni da azaba ba.

7 Ka gajiyar da ni, ya Allah,

Ka shafe iyalina.

8 Ka kama ni, kai maƙiyina ne.

Na zama daga fata sai ƙasusuwa,

Mutane suka ɗauka, cewa wannan ya tabbatar ni mai laifi ne.

9 Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa,

Yana dubana da ƙiyayya.

10 Mutane sun buɗe baki don su haɗiye ni

Suna kewaye ni suna ta marina.

11 Allah ya bashe ni ga mugaye.

12 Dā ina zamana da salama,

Amma Allah ya maƙare ni,

Ya fyaɗa ni ƙasa ya ragargaza ni.

Allah ya maishe ni abin bārata.

13 Ya harbe ni da kibau daga kowane gefe.

Kiban sun ratsa jikina sun yi mini rauni,

Duk da haka bai nuna tausayi ba!

14 Ya yi ta yi mini rauni a kai a kai,

Ya fāɗa mini kamar soja da ƙiyayya ta haukata.

15 “Ina makoki saye da tsummoki,

Ina zaune cikin ƙura a kunyace.

16 Na yi ta kuka har fuskata ta zama ja wur,

Idanuna kuma suka yi luhuluhu.

17 Amma ban yi wani aikin kama-karya ba,

Addu’ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.

18 “Duniya, kada ki ɓoye laifofin da aka yi mini!

Kada ki yi shiru da roƙon da nake yi na neman adalci!

19 Akwai wani a Sama

Wanda zai tsaya mini ya goyi bayana.

20 Ina so Allah ya ga hawayena,

Ya kuma ji addu’ata.

21 “Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina,

Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.

22 Yanzu shekaruna wucewa suke yi,

Ina bin hanyar da ba a komawa.”

Categories
AYU

AYU 17

1 “Ƙarshen raina ya gabato, da ƙyar nake numfashi,

Ba abin da ya rage mini sai kabari.

2 Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba’a.

3 Ni amintacce ne, ya Allah, ka yarda da maganata.

Ba wanda zai goyi bayan abin da nake faɗa.

4 Ka baƙantar da hankalinsu, ya Allah,

Kada ka bar su su yi mini duban wulakanci yanzu.

5 A karin maganar mutanen dā an ce,

‘Kowa ya ci amanar abokinsa saboda kuɗi,

‘Ya’yansa sā sha wahala!’

6 Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.

Da mutane suka ji,

Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.

7 Baƙin cikina ya kusa makantar da ni,

Hannuwana da ƙafafuna sun rame,

sun zama kamar kyauro.

8 Duk waɗanda suka zaci su adalai ne sun razana.

Dukansu sun kāshe ni, cewa ni ba mai tsoron Allah ba ne.

9 Har su ma da suke cewa su mutanen kirki ne

Suna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.

10 Amma da a ce dukansu za su zo su tsaya a gabana,

Da ba zan sami mai hikima ko ɗaya daga cikinsu ba.

11 “Kwanakina sun ƙare, shirye-shiryena sun kāsa,

Ba ni da sauran sa zuciya.

12 Amma abokaina sun ce dare shi ne hasken rana,

Sun kuma ce haske yana kusa,

Ko da yake ina cikin duhu.

13 Ba ni da sauran sa zuciya,

Gidana yana lahira,

Inda zan kwanta in yi ta barci cikin duhu.

14 Zan ce kabari shi ne mahaifina,

Tsutsotsin da suke cinye ni su ne mahaifiyata, da ‘yan’uwana mata.

15 Ina ne zan sa zuciyata?

Wane ne ya ga inda zan sa ta?

16 Akwai wanda ya yi shiri a binne shi tare da ni,

Mu tafi tare da shi zuwa lahira?”

Categories
AYU

AYU 18

Bildad Ya Bayyana Abin da Za a Yi wa Mugun Mutum

1 Bildad ya amsa.

2 “Ayuba, mutane kamarka sun taɓa yin shiru?

Da ka yi ƙoƙari ka kasa kunne da mun yi magana da kai.

3 Me ya sa kake tsammani mu dakikai ne kamar shanu?

4 Cutar kanka kake yi saboda fushin da kake ji.

Duniya za ta ƙare ne sabili da kai?

Za a kawar da duwatsu sabili da kai?

5 “Za a kashe hasken mugun mutum,

Harshen wutarsa ba zai ƙara ci ba.

6 Fitilar da take cikin alfarwarsa ba za ta ba da haske ba.

7 A dā gagau yake tafiya, amma yanzu ɗingishi yake yi,

Shawararsa ta kāshe shi.

8 Yana tafiya, sai ya fāɗa cikin tarko.

Tarkon ya kama ƙafafunsa.

9 Tarko ya kama diddigensa ya riƙe shi,

10 An binne masa tarko a ƙasa,

An kafa masa tarko a hanyarsa.

11 “Kewaye da shi duka razana tana jiransa,

Duk inda ya nufa tana biye da shi,

12 Dā attajiri ne, amma yanzu ya talauce,

Kusa da shi bala’i na tsaye yana jiransa.

13 Mummunan ciwo ya bazu ko’ina a jikinsa,

Yana sa hannuwansa da ƙafafunsa su ruɓe,

14 Dā yana zaune lafiya,

Sai razana ta tatike shi,

Ta jawo shi zuwa ga Sarkin Mutuwa.

15 Yanzu kowa zai iya zama a alfarwarsa,

Bayan da an karkashe ƙwayoyin cuta da farar wuta.

16 Saiwoyinsa da rassansa suka yi yaushi suka bushe.

17 Sunansa ya ƙare a gida da a jeji,

Ba wanda yake ƙara tunawa da shi.

18 Za a kore shi daga ƙasar masu rai,

Za a kore shi daga haske zuwa duhu.

19 Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.

20 Daga gabas zuwa yamma, duk wanda ya ji labarin ƙaddarar da ta same shi,

Zai yi makyarkyata, ya yi rawar jiki don tsoro.

21 Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,

Wannan ita ce ƙaddarar mutane waɗanda ba su damu da kome na Allah ba.”

Categories
AYU

AYU 19

Bangaskiyar Ayuba Ta Sa Allah Zai Goyi Bayansa

1 Ayuba ya amsa.

2 “Me ya sa kuke azabta ni da maganganu?

3 A kowane lokaci kuna wulakanta ni,

Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina.

4 Da a ce ma na aikata abin da yake ba daidai ba ne,

Da me ya cuce ku?

5 Tsammani kuke kun fi ni ne,

Kuna ɗauka cewa wahalar da nake sha

Ta tabbatar ni mai laifi ne.

6 Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini,

Ya kafa tarko don ya kama ni.

7 Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba,

Amma ba wanda ya kasa kunne.

Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.

8 Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa,

Ya rufe hanyata da duhu,

9 Gama ya kwashe dukiyata duka,

Ya ɓata mini suna.

10 Ya mammangare ni,

Ya tumɓuke sa zuciyata,

Ya bar ni in yi yaushi, in mutu.

11 Allah ya zaburo mini da fushi,

Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.

12 Ya aiko da rundunar sojansa don ta fāɗa mini,

Suka haƙa ramummuka kewaye da alfarwata inda za su yi kwanto.

13 “’Yan’uwana sun yashe ni,

Na zama baƙo ga idon sanina.

14 Dangina da abokaina sun tafi.

15 Waɗanda sukan ziyarce gidana sun manta da ni.

Barorina mata na gidana sun maishe ni kamar baƙo daga wata ƙasa.

16 Sa’ad da na kira barana, ba ya amsawa,

Ko a lokacin da na roƙe shi ya taimake ni.

17 Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina,

‘Yan’uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni.

18 ‘Yan yara sukan raina ni su yi mini dariya sa’ad da suka gan ni.

19 Aminaina na kusa sukan dube ni, duban ƙyama,

Waɗanda na fi ƙaunarsu duka sun zama maƙiyana.

20 Fatar jikina ta saki, ba ƙarfi,

Da ƙyar na kuɓuta.

21 Ku abokaina ne! Ku ji tausayina!

Ikon Allah ya fyaɗa ni ƙasa.

22 Me ya sa kuke ɓata mini rai kamar yadda Allah ya yi?

Azabar da kuka yi mini har yanzu ba ta isa ba?

23 “Da ma a ce wani zai rubuta abin da nake faɗa,

Ya rubuta shi a littafi!

24 Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse,

Ya rubuta su don su tabbata har abada!

25 Amma na sani akwai wani a Samaniya

Wanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini.

26 Ko da yake ciwo ya riga ya cinye fatata,

A wannan jiki zan ga Allah.

27 Zan gan shi ido da ido,

Ba kuwa zai zama baƙo a gare ni ba.

“Zuciyata ta karai saboda ku mutane kun ce,

28 ‘Ta ƙaƙa za mu yi masa azaba?’

Kuna neman sanadin da za ku fāɗa mini.

29 Amma yanzu, sai ku ji tsoron takobi,

Ku ji tsoron takobin da yake kawo hasalar Allah a kan zunubi.

Don haka za ku sani akwai wani mai yin shari’a.”

Categories
AYU

AYU 20

Zofar Ya Nuna Rabon Mugu

1 Zofar ya amsa.

2 “Ayuba, ka ɓata mini rai,

Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.

3 Abin da ka faɗa raini ne,

Amma na san yadda zan ba ka amsa.

4 “Hakika ka sani tun daga zamanin dā,

Sa’ad da aka fara sa mutum a duniya,

5 Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.

6 Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama.

Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.

7 Amma zai shuɗe kamar ƙura.

Waɗanda dā suka san shi,

Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.

8 Zai ɓace kamar mafarki, kamar wahayi da dad dare,

Ba kuwa za a ƙara ganinsa ba.

9 Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.

10 Tilas ‘ya’yansa maza su biya zambar da ya yi wa matalauta,

Tilas hannuwansa su biya dukiyar da ya ƙwace.

11 Ko da yake gagau yake, ma’aikaci ne kuma sa’ad da yake yaro,

Duk da haka ba da jimawa ba, zai zama ƙura.

12-13 Ɗanɗana mugunta yana da daɗi a gare shi ƙwarai,

Yakan sa wata a bakinsa don ya riƙa jin daɗin tsotsanta.

14 Amma a cikinsa wannan abinci yakan zama da ɗaci,

Ɗacinsa kamar na kowane irin dafi mai ɗaci ne.

15 Mugun mutum yakan harar da dukiyar da ya samu ta hanyar zamba,

Allah zai karɓe ta har da wadda ya ci a cikin cikinsa.

16 Abin da mugu ya haɗiye kamar dafi yake,

Yakan kashe shi kamar saran maciji mai mugu dafi.

17 Zai mutu bai ga kogunan man zaitun ba,

Ba kuwa zai ga rafuffukan da suke da yalwar albarka ba.

18 Tilas ya rabu da dukan abin da ya yi wahalarsa.

Ba dama ya mori dukiyarsa,

19 Saboda zalunci da rashin kula da matalauta,

Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.

20 “Har abada ba zai kai ga samun abin da yake wahala ba.

21 Sa’ad da ya ci ba zai yi saura ba,

Gama yanzu dukiyarsa ta ƙare.

22 A lokacin da yake gaɓar samunsa,

Baƙin ciki mai nauyin gaske zai ragargaza shi.

23 Bari ya ci duk irin abin da yake so!

Allah zai hukunta shi da hasala da fushi.

24 Lokacin da yake ƙoƙari ya kuɓuta daga takobin baƙin ƙarfe,

Za a harbe shi da bakan tagulla ya fāɗi warwar.

25 Kibiya za ta kafe a jikinsa

Tsininta zai yi ta ɗiɗɗiga da jini,

Razana ta kama zuciyarsa.

26 Aka hallaka dukan abin da ya tattara,

Wutar da ba hannun mutum ya kunna ba

Ta ƙone shi, shi da iyalinsa duka.

27 Samaniya ta bayyana zunubin wannan mutum,

Duniya kuma ta ba da shaida gāba da shi.

28 Dukan dukiyarsa za a hallaka ta a rigyawar fushin Allah.

29 “Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,

Wadda Allah ya ƙayyade musu.”