Categories
AYU

AYU 21

Ayuba Ya Yi Magana a kan Wadatar Mugaye

1 Ayuba ya amsa.

2 “Ku kasa kunne ga abin da nake faɗa,

Wannan ita ce ta’aziyyar da nake nema a gare ku.

3 Ku ba ni zarafi in yi magana, sa’an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.

4 “Ba da ‘yan adam nake faɗa ba,

Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.

5 Ku dube ni, ashe, wannan bai isa ya sa ku yi zuru,

Ku firgita, ku yi shiru ba?

6 Sa’ad da na tuna da abin da ya same ni,

Sai jikina ya yi suwu, in yi ta makyarkyata ina rawar jiki.

7 Me ya sa Allah yake barin mugaye

Har su tsufa su kuma yi arziki?

8 ‘Ya’yansu da jikokinsu sukan girma a idonsu.

9 Allah bai taɓa aukar wa gidajensu da bala’i ba,

Ba su taɓa zama a razane ba.

10 Hakika shanunsu suna ta hayayyafa,

Suna haihuwa ba wahala.

11 ‘Ya’yansu suna guje-guje,

Suna tsalle kamar ‘yan raguna,

12 Suna rawa ana kaɗa garaya,

Ana busa sarewa.

13 Suka yi zamansu da salama,

Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.

14 Mugaye sukan ce wa Allah ya ƙyale su kurum,

Ba su so su san nufinsa game da hanyoyinsu.

15 Suna tsammani ba amfani a bauta wa Allah,

Ko a yi addu’a gare shi domin samun wata fa’ida.

16 Sukan ce ta wurin ƙarfinsu ne suka yi nasara,

Amma ban yarda da irin tunaninsu ba.

17 “An taɓa kashe hasken mugun mutum?

Ko masifa ta taɓa fāɗa wa wani daga cikinsu?

Allah ya taɓa hukunta wa mugu da fushi,

18 Ya kuma sa su zama kamar tattakar da iska yake kwashewa?

Ko kuma kamar ƙura wadda hadiri yake kwashewa?

19 “Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa.

A’a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi.

Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.

20 Bari dai a hukunta masu zunubi

Su kuma ga hasalar Allah.

21 Bayan rasuwar mutum,

Ruwansa ne ya sani ko ‘ya’yansa suna jin daɗi?

22 Mutum zai iya koya wa Allah?

Mutum zai iya shara’anta wa Allah Mai Iko Dukka?

23 “Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu,

Suna cikin farin ciki da jin daɗi,

24 Jikunansu kuwa sun yi ɓulɓul.

25 Waɗansu kuwa ba su taɓa sanin farin ciki ba.

Sukan yi dukan kwanakinsu su mutu da baƙin ciki.

26 Amma duk abu guda ne su, mutuwa za su yi, a binne,

Tsutsotsi su lulluɓe su duka.

27 “Na san irin tunaninku na hassada,

28 Kuna ta tambaya, ‘Ina ne gidan babban mutumin nan yanzu,

Wato mutumin da yake aikata mugunta?’

29 “Ashe, ba ku yi magana da matafiya ba?

Ba ku kuma san rahoton da suka kawo ba?

30 A ranar da Allah ya yi fushi, ya yi hukunci,

A kullum mugun ne kaɗai yakan kuɓuta.

31 Ba wanda zai fito fili ya zargi mugun,

Ko ya mayar masa da martani.

32 Sa’ad da aka ɗauke shi zuwa hurumi,

A inda ake tsaron kabarinsa,

33 Dubban mutane sukan tafi wurin jana’izarsa,

Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali.

34 “Amma ku, ƙoƙari kuke yi ku ta’azantar da ni da maganganun banza.

Duk abinda kuka faɗa ƙarya ne!”

Categories
AYU

AYU 22

Elifaz ya Zargi Ayuba a kan Aikata Mugunta

1 Elifaz ya yi magana.

2 “Akwai wani mutum, ko mafi hikima,

Wanda zai amfani Allah?

3 Gaskiyar da kake yi za ta amfani Allah?

Ko kuwa abin kirki da kake yi zai taimake shi?

4 Ai, ba don tsoron Allah da kake yi ba ne,

Ya sa wannan tsautawa da jarrabawa suka same ka.

5 Ko kusa ba haka ba ne,

Amma saboda zunubi mai yawa da ka yi ne.

Saboda kuma dukan muguntar da ka aikata.

6 Don ka sa ɗan’uwanka ya biya ka bashin da kake binsa,

Ka ƙwace tufafinsa, ka bar shi huntu.

7 Ka hana wa waɗanda suke ji ƙishi ruwan sha,

Ka hana waɗanda suke jin yunwa abinci.

8 Ka mori ikonka da matsayinka,

Don ka mallaki dukan ƙasar.

9 Ba ƙin taimako kaɗai ka yi ba,

Amma har marayu ma ka yi musu ƙwace, ka wulakanta su.

10 Don haka ne yanzu akwai ramummuka ko’ina kewaye da kai,

Tsoro ya kama ka nan da nan.

11 An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,

Rigyawa ta sha kanka.

12 “Ashe, ba a can saman sammai Allah yake zaune ba?

Sai ya sunkuya ya dubi taurari, ko da yake suna can sama ne.

13 Duk da haka ka ce, ‘Allah bai san kome ba.

Gizagizai sun lulluɓe shi, ƙaƙa zai iya yi mana shari’a?’

14 Kana tsammani gizagizai masu duhu sun hana shi gani,

A lokacin da yake tafiya a kan iyakar da take tsakanin duniya da sararin sama.

15 “Ka ɗauka a ranka ka bi gurbin da mugaye suke bi kullum?

16 Kafin ma su kai ga kwanakinsu,

Sai rigyawa ta shafe su.

17 Su ne mutanen da suka ƙi Allah,

Suka kuwa gaskata ba shi da ikon yi musu kome,

18 Ko da yake Allah ne ya arzuta su.

Ba na iya gane tunanin mugaye.

19 Mutanen kirki suna murna,

Marasa laifi kuma suna dariya

Sa’ad da suka ga ana hukunta mugaye.

20 Duk abin da mugu ya mallaka ya hallaka,

Wuta kuwa ta lashe kowane abu da ya ragu.

21 “Yanzu fa, Ayuba, sai ka yi sulhu da Allah,

Ka daina ɗaukarsa kamar maƙiyinka,

In ka yi haka, to, za ka sami albarka.

22 Ka karɓi koyarwar da yake yi,

Ka riƙe kalmominsa a zuciyarka.

23 Hakika sai ka yi tawali’u, ka koma wurin Allah,

Ka kawar da dukan muguntar da ake yi a gidanka.

24 Ka jefar da zinariyarka, zinariyarka mafi kyau,

Ka jefar da ita kamar dutse ko ƙura.

25 Bari Allah Mai Iko Dukka ya zama zinariyarka,

Ya zama azurfa, wadda aka tula dominka.

26 Sa’an nan za ka dogara ga Allah kullayaumin,

Ka kuma tarar shi ne asalin farin cikinka.

27 Sa’ad da ka yi addu’a zai amsa maka,

Za ka kuwa kiyaye alkawaran da ka yi.

28 Za ka yi nasara a kowane abu da za ka yi,

Haske kuma zai haskaka hanyarka.

29 Allah yakan ƙasƙantar da mai girmankai,

Yakan ceci mai tawali’u.

30 Zai ceci wanda yake da laifi,

Idan abin da kake yi daidai ne.”

Categories
AYU

AYU 23

Ayuba Yana Marmarin Kai Ƙara Gaban Allah

1 Ayuba ya amsa.

2 “Duk da haka zan yi tawaye in yi wa Allah gunaguni,

In dinga yin nishi.

3 Da ma na san inda zan same shi,

In kuma san yadda zan kai wurinsa,

4 Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.

5 Ina so in san irin amsar da zai mayar mini,

Ina kuma so in san yadda zai amsa mini.

6 Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni?

A’a, zai saurara in na yi magana.

7 Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra’ayina,

Zai tabbatar da amincina duka.

8 “Na nemi Allah a gaba, amma ban same shi a can ba,

Ban kuwa same shi a baya ba sa’ad da na neme shi.

9 Allah ya tafi wurin aiki a dama,

Ya kuma tafi hagu, amma har yanzu ban gan shi ba.

10 Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki.

Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.

11 Da aminci ina bin hanyar da ya zaɓa,

Ban kuwa taɓa kaucewa daga wannan gefe zuwa wancan ba.

12 A kullum ina aikata abin da Allah ya umarta,

Ina bin nufinsa, ba nufin kaina ba.

13 “Bai taɓa sākewa ba. Ba wanda zai iya gāba da shi,

Ko kuma ya hana shi yin abin da yake so ya aikata.

14 Zai tabbatar da abin da ya shirya domina,

Wannan ma ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ya yi ne.

15 Don haka in rawar jiki a gabansa saboda tsoro.

16 Allah Mai Iko Dukka ya lalatar da ƙarfin halina.

Allah ne ya tsorata ni,

17 Amma ban damu da damu ba,

Ko da yake duhu ya dunɗe idanuna.”

Categories
AYU

AYU 24

Ayuba Ya Yi Kuka da Yake Allah Bai Kula da Mugunta Ba

1 “Me ya sa Allah bai tsai da ranar da zai yi shari’a ba?

Me ya sa ba ya tsai da ranar adalci ga

Waɗanda suka bauta masa?

2 Mugaye sukan ci iyaka,

Don su ƙara yawan gonarsu.

Sukan saci tumaki su zuba cikin garkunansu.

3 Sukan saci jakunan marayu,

Su kama san gwauruwa,

Su ce sai ta biya basusuwanta.

4 Sukan hana matalauta samun halaliyarsu,

Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.

5 Kamar jakunan jeji waɗanda sukan nemi abinci a busasshen jeji,

Haka matalauta suke,

Ba inda za su iya samo wa ‘ya’yansu abinci.

6 Ya zama tilas a gare su su girbe gonakin da ba nasu ba,

Su tattara ‘ya’yan inabi daga gonakin mugaye.

7 Da dare sukan kwanta, ba su da abin rufa,

Ba su da abin da zai hana su jin sanyi.

8 Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda yake kwararowa daga kan duwatsu.

Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.

9 “Mugaye sukan bautar da yara marayu,

Sukan kama ‘ya’ya matalauta a bakin bashin da suke bi.

10 Amma tilas matalauta su fita huntaye, ba sa da abin sutura.

Tilas su girbi alkama suna kuwa jin yunwa.

11 Suna matse mai daga ‘ya’yan zaitun.

Suna kuma matse ruwan inabi daga ‘ya’yan inabi,

Amma su kansu suna fama da ƙishi.

12 Kana jin kukan waɗanda suka yi rauni da

Waɗanda suke baƙin mutuwa a birni,

Amma Allah bai kula da addu’o’insu ba.

13 “Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske,

Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.

14 Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci,

Da dare kuma ya yi fashi.

15 Mazinaci yakan jira sai da magariba,

Sa’an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.

16 Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje,

Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.

17 Gama tsananin duhu kamar safiya yake gare su,

Sun saba da razanar duhu.

18 “Rigyawa takan ci mugun mutum,

Ƙasar da ya mallaka kuwa tana ƙarƙashin la’anar Allah.

Ba ya kuma iya zuwa aiki a gonar inabinsa.

19 Kamar dusar ƙanƙara take a lokacin zafi da a lokacin fari,

Haka mai zunubi yakan shuɗe daga ƙasar masu rai.

20 Ba wanda zai tuna da shi,

mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba.

Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai.

Za a sare mugunta kamar itace.

21 Haka yake samun wanda ya wulakanta gwauraye.

Bai kuma nuna alheri ga matan da ba su haihu ba.

22 Allah, da ikonsa, yakan hallaka masu ƙarfi,

Allah yakan aikata, sai mugun mutum ya mutu.

23 Ya yiwu Allah ya bar shi ya yi zamansa lafiya,

Amma a kowane lokaci zai sa ido a kansa.

24 Mugun mutum yakan ci nasara ɗan lokaci,

Daga nan sai ya yi yaushi kamar tsiro,

Ya yi yaushi kamar karan dawa da aka yanke.

25 Akwai wanda zai iya cewa, ba haka ba ne?

Akwai wanda zai tabbatar da cewa kalmomina ba gaskiya ba ne?”

Categories
AYU

AYU 25

Bildad Bai Yarda Allah Zai Baratar da Mutum Ba

1 Bildad ya amsa.

2 “Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa,

A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama.

3 Akwai wanda zai iya ƙidaya mala’ikun da suke masa hidima?

Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?

4 Akwai wanda ya isa ya zama adali,

Ko mai tsarki a gaban Allah?

5 Hasken wata ba haske ba ne a gare shi,

Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.

6 To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.

Me mutum ya daɗa a gaban Allah?”

Categories
AYU

AYU 26

Ayuba Ha Hurta Sarautar Allah

1 Ayuba ya amsa.

2 “Kai ne mai taimakon marar ƙarfi,

Kai ne mai ceton rarrauna!

3 Kai ne kake ba marar hikima shawara,

Kai kake sanar da ilimi mai ma’ana a wadace!

4 Kana tsammani wane ne zai ji maganganunka duka?

Wane ne ya iza ka ka yi irin wannan magana?

5 “Lahira tana rawa,

Mazaunanta suna rawar jiki don tsoro.

6 Lahira tsirara take a gaban Allah,

Haka kuma Halaka take a gaban Allah.

7 Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum,

Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.

8 Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa,

Girgijen kuwa bai kece ba.

9 Ya rufe kursiyinsa, ya shimfiɗa girgije a kansa.

10 Ya shata da’ira a kan fuskar teku,

A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.

11 Ginshiƙan samaniya sun girgiza,

Sun firgita saboda tsautawarsa.

12 Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku,

Da saninsa ya hallaka dodon ruwan nan, wato Rahab.

13 Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi garau,

Ikonsa ne kuma ya sha zarar macijin nan mai gudu.

14 Amma waɗannan kaɗan ne kawai daga cikin al’amuransa.

Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa.

Amma wa zai iya fahimtar ikon tsawarsa?”

Categories
AYU

AYU 27

Ayuba Ya Bayyana Rabon Mugaye

1 Ayuba ya amsa.

2 “Na rantse da Allah Mai Iko Dukka,

Wanda ya ƙwace mini halaliyata,

Wanda ya ɓata mini rai.

3 Muddin ina numfashi,

Ruhun Allah kuma yana cikin hancina

4 Bakina ba zai faɗi ƙarya ba,

Harshena kuma ba zai hurta maganganun yaudara ba.

5 Allah ya sawwaƙa in ce kun yi daidai,

Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.

6 Ina riƙe da adalci kam, ba kuwa zan sake shi ba,

Zuciyata ba ta zarge ko ɗaya daga cikin kwanakin raina ba.

7 “Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum,

Wanda ya tashi gāba da ni ya zama kamar marar adalci.

8 Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah?

Sa’ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa?

9 Allah kuwa zai ji kukansa sa’ad da wahala ta same shi?

10 Ko Mai Iko Dukka zai zama abin farin ciki a gare shi?

Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?

11 “Zan koya muku zancen ikon Allah,

Abin da yake na wajen Mai Iko Dukka ba zan ɓoye ba.

12 Ga shi kuwa, dukanku kun gani da kanku,

Me ya sa kuka zama wawaye?

13 “Wannan shi ne rabon mugaye daga wurin Allah,

Gādo ne kuma wanda azzalumai za su karɓa daga wurin Mai Iko Dukka.

14 Idan ‘ya’yansu sun riɓaɓɓanya za su zama rabon takobi,

Zuriyarsu kuwa ba za su sami isasshen abinci ba.

15 Waɗanda suka tsira, annoba za ta kashe su,

Matansu ba za su yi makokin mutuwarsu ba.

16 Ko da yake sun tsibe azurfa kamar turɓaya,

Sun tara tufafi kamar ƙasa,

17 Za su tara, amma adalai za su sa,

Marasa laifi ne za su raba azurfar.

18 Sun gina gidajensu kamar saƙar gizo-gizo,

Kamar bukkar mai tsaro.

19 Attajirai za su kwanta, amma daga wannan shi ke nan,

Za su buɗe ido su ga dukiyan nan ba ta.

20 Razana za ta auka musu kamar rigyawa.

Da dare iska za ta tafi da su.

21 Iskar gabas za ta fauce su su tafi,

Ta share su ta raba su da wurin zamansu.

22 Za ta murɗe su ba tausayi,

Hakika za su yi ƙoƙari su tsere daga ikonsa,

Sai su yi ƙundumbala.

23 Kowa zai tafa hannu yă yi musu tsaki har su tashi daga wurin da suke.”

Categories
AYU

AYU 28

Samun Hikima Yana da Wuya

1 “Hakika akwai ma’adinai na azurfa,

Da wuraren da ake tace zinariya.

2 Mutane sukan haƙo baƙin ƙarfe daga ƙasa,

Sukan narkar da tagulla daga dutse.

3 Mutane sukan kawar da duhu,

Sukan kuma bincike zuzzurfar iyaka,

Sukan haƙo duwatsun da suke cikin duhu, duhu baƙi ƙirin.

4 Sukan haƙa loto a fadama nesa da mutane,

Sukan kafa abin lilo su yi ta lilo nesa da mutane.

5 “Daga cikin ƙasa ake samun abinci,

Amma a ƙarƙashinta yakan zama kamar wuta.

6 Akwai duwatsu masu daraja cikin duwatsunta,

Akwai zinariya a ƙurarta.

7 Tsuntsu mai cin nama bai san wannan hanya ba.

Shaho ma bai gan ta ba.

8 Namomin jeji ba su taɓa bin hanyar ba,

Ko zaki ma bai taɓa binta ba.

9 “Mutane sun iya sarrafa ƙanƙarar dutse,

Suna kuma iya tumɓuke tushen duwatsu.

10 Sukan haƙa magudanar ruwa cikin duwatsu,

Idanunsu sukan ga kowane abu mai daraja.

11 Sukan datse rafuffuka su hana su gudu,

Su binciko abin da yake ɓoye, ya fito sarari.

12 Amma ina, a ina za a iya samun hikima?

A ina za a samo haziƙanci?

13 Mutane ba su san darajar hikima ba,

Ba a samunta a ƙasar masu rai.

14 Zurfafa sun ce, ‘Ba ta a cikinmu,’

Tekuna kuma sun ce, ‘Ba ta tare da mu.’

15 Ba za a saye ta da zinariya tsantsa ba.

Azurfa ba za ta iya biyan tamaninta ba.

16 Ko zinariyar Ofir, ko onis,

Ko saffir, wato duwatsu masu daraja, ba za su iya biyan tamaninta ba.

17 Ba daidai take da zinariya ko madubi ba,

Ba za a iya musayarta da kayayyakin da aka yi da zinariya tsantsa ba.

18 Kada ma a ko ambaci murjani,

Da duwatsu masu walƙiya.

Gama tamanin hikima ya fi na lu’ulu’ai mafiya daraja duka.

19 Ba za a daidaita tamaninta da na duwatsun tofaz na Habasha ba.

Tamaninta ya fi na zinariya tsantsa.

20 “To, daga ina hikima ta fito?

A wane wuri kuma haziƙanci yake?

21 Ba talikin da ya iya ganinta,

Ko tsuntsun da yake tashi sama.

22 Halaka da Mutuwa sun ce,

‘Da kunnuwanmu mun ji ƙishin-ƙishin a kanta.’

23 “Allah ne kaɗai ya san hanya zuwa gare ta,

Ya san inda hikima take,

24 Saboda yana ganin duniya ɗungum,

Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.

25 Sa’ad da Allah ya sa iska ta hura,

Ya yi wa tekuna iyaka.

26 Sa’ad da ya ba da umarni ga ruwan sama,

Da kuma hanyar da tsawa za ta bi,

27 Shi ya san hikimar, shi ya sanar,

Ya tabbatar da ita, ya bincike ta sarai.

28 “Allah ya ce wa mutane,

‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima,

Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.’ ”

Categories
AYU

AYU 29

Ayuba Ya Tuno da Farin Cikinsa na Dā

1 Ayuba ya ci gaba da magana.

2 Da ma ina cikin lokacin da ya wuce ne,

Lokacin da Allah yake lura da ni,

3 Sa’ad da fitilarsa take haskaka mini,

Ta wurin haskensa kuma nake tafiya da duhu,

4 Kwanakin da nake gaɓar raina,

Lokacin da ni’imar Allah take kan gidana,

5 Sa’ad da Mai Iko Dukka yake tare da ni,

‘Ya’yana duka kuma suka kewaye ni,

6 Sa’ad da aka wanke ƙafafuna da madara,

Duwatsu kama suna ɓulɓulo mini da rafuffukan mai!

7 A sa’ad da nakan tafi kofar birni,

In shirya wurin zamana a dandali,

8 Da samari sun gan ni, sai su kawar da jiki,

Tsofaffi kuma su miƙe tsaye,

9 Sarakuna sun yi shiru sun kame bakinsu.

10 Manyan mutane sukan yi shiru, harshensu ya liƙe a dasashi.

11 Waɗanda suka ji labarina sukan sa mini albarka,

Waɗanda suka gan ni sukan yi na’am da ni.

12 Domin sa’ad da matalauta suka yi kuka, ni nake cetonsu,

Nakan taimaki marayu waɗanda ba su da mai taimako.

13 Waɗanda suke bakin mutuwa sukan sa mini albarka,

Na taimaki gwaurayen da mazansu suka mutu,

Su raira waƙa don murna.

14 Adalci shi ne suturata,

Gaskiya ita ce rigata da rawanina.

15 Ni ne idon makafi, guragu kuma, ni ne ƙafarsu.

16 Ni mahaifi ne ga matalauta,

Nakan bincika don in warware al’amarin da ya dami baƙi.

17 Nakan karya muƙamuƙin marar adalci,

In sa yă saki ganimar da yă kama.

18 “Da na zaci zan mutu cikin sutura,

Kwanakina kuma su riɓaɓɓanya, su yi yawa kamar yashi,

19 Saiwoyina a shimfiɗe suke cikin ruwa,

Dukan dare raɓa na sauka a kan rassana .

20 Darajata garau take a gare ni,

Bakana kullum sabo yake a hannuna.

21 Mutane sukan kasa kunne su jira, su yi shiru

Sa’ad da nake ba da shawara.

22 Bayan na gama magana ba wanda zai ƙara wata magana.

Maganata takan shige su.

23 Suna jirana kamar yadda ake jiran ruwan sama,

Da baki buɗe, kamar yadda ake jiran ruwan bazara.

24 Nakan yi musu murmushi sa’ad da suka fid da zuciya,

Ba su yi watsi da fara’ata ba.

25 Nakan zaɓar musu hanyar da za su bi,

Ina zaune kamar sarki a tsakanin mayaƙansu,

Kamar mai ta’azantar da masu makoki.”

Categories
AYU

AYU 30

Ayuba Ya Yi Kuka saboda Masifunsa

1 “Amma yanzu waɗanda na girme su, sai ba’a suke mini,

Waɗanda iyayensu maza ba su fi karnukan da suke kiwon garken tumakina ba.

2 Wace riba zan samu ta wurin ƙarfin hannuwansu waɗanda ba su da sauran kuzari?

3 Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame,

Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.

4 Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci,

Sukan ci doyar jeji.

5 Aka kore su daga cikin mutane,

Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,

6 Sai a kwazazzabai suke zama

Da a ramummuka da kogwannin duwatsu.

7 Suka yi ta kuka a jeji,

Suka taru wuri ɗaya a cikin sarƙaƙƙiya.

8 Mutane ne marasa hankali marasa suna!

Aka kore su daga ƙasar.

9 “Yanzu na zama abin waƙa gare su,

Abin ba’a kuma a gare su.

10 Suna ƙyamata, guduna suke yi,

Da ganina, sai su tofa mini yau.

11 Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙanta ni,

Saboda haka sun raba ni da zuriyata,

12 A hannun dama ‘yan tā da zaune tsaye sun taso mini,

Sun runtume ni, sun tura ni a hanyarsu ta hallakarwa.

13 Sun datse hanyata,

Sun jawo mini bala’i,

Ba kuwa wanda ya hana su.

14 Sun kutsa kamar waɗanda suka karya doka,

Sun auka mini da dukan ƙarfinsu kamar yadda suka yi nufi.

15 Sun firgita ni,

Sun kori darajata kamar da iska,

Wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije.

16 “Yanzu zuciyata ta narke

Kwanakin wahala sun same ni.

17 Da dare ƙasusuwana karkaɗuwa suke,

Azaba tana ta gaigayata ba hutawa.

18 An yi mini kamun kama-karya,

An ci wuyan rigata.

19 Allah ya jefar da ni cikin laka,

Na zama kamar ƙura ko toka,

20 “Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba,

Na yi addu’a kuma, amma ba ka kula da ni ba.

21 Ka zama mugu a gare ni,

Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.

22 Ka jefa ni cikin guguwa, ka sa ni in hau ta,

Ka yi ta shillo da ni cikin rugugin hadiri.

23 Hakika na sani za ka kai ni ga mutuwa,

Gidan da aka ƙaddara wa kowane mai rai.

24 “Ashe, wanda yake gab da gagarumar hallaka,

Ba zai miƙa hannu ya roƙi taimako a masifar da yake sha ba?

25 Ashe, ban yi kuka saboda wanda yake shan wahala ba?

Ashe, ban yi ɓacin rai saboda matalauta ba?

26 Amma sa’ad da na sa zuciya ga alheri, sai ga mugunta,

Sa’ad da nake jiran haske, sai ga duhu ya zo.

27 Zuciyata tana tafasa, ba ta kwanciya,

Kwanakin wahala sun auko mini.

28 Na yanƙwane, amma ba yanƙwanewar rana ba,

Na tsaya a gaban taron jama’a, ina roƙon taimako.

29 “Na zama ɗan’uwan dila,

Na kuma zama aminin jiminai.

30 Fatata ta takura, ta zama baƙa,

Ƙasusuwana suna zogi saboda zafi,

31 Saboda haka garayata ta zama ta makoki,

Sarewata kuma ta zama muryar masu kuka.”