Categories
EZ

EZ 1

Ezekiyel Ya Ga Wahayi na Ɗaukakar Ubangiji

1 A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kogin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah.

2 A kan rana ta biyar ga watan, a shekara ta biyar da aka kai sarki Yekoniya bautar talala,

3 Ubangiji ya yi magana da Ezekiyel, firist, ɗan Buzi, a ƙasar Kaldiyawa, kusa da kogin Kebar. Ikon Ubangiji yana bisa kansa.

4 Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla.

5 Daga tsakiya wutar, sai ga kamannin waɗansu talikai su huɗu. Ga irin kamanninsu, suna kama da mutane.

6 Amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, da fikafikai huɗu.

7 Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne, tafin sawayensu yana kama da na maraƙi, suna walƙiya kamar gogaggiyar tagulla.

8 Suna kuma da hannuwa kamar na mutane a ƙarƙarshin fikafikansu huɗu. Ga yadda fuskoki da fikafikan talikai huɗu ɗin suke.

9 Fikafikansu suna taɓa juna, kowannensu ya miƙe gaba, ba su juyawa sa’ad da suke tafiya.

10 Kamannin fuskokinsu, su huɗu ɗin, kowannensu yana da fuska irin ta mutum a gaba, da fuska irin ta zaki a dama, da fuska irin ta bijimi a hagu, da fuska irin ta gaggafa a baya.

11 Suka kuma buɗe fikafikansu sama. Kowane taliki yana taɓa fiffiken ɗan’uwansa da fikafikansa biyu, da kuma fikafikansa biyu yake rufe jikinsa.

12 Kowannensu kuwa ya miƙe gaba sosai, zuwa inda ruhu ya bishe shi. Sun tafi ba waiwaye.

13 A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa.

14 Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.

15 Da na dubi talikan, sai na ga ƙafafu huɗu kamar na keke a ƙasa kusa da talikan. Ɗaya domin kowane taliki.

16 Ga kamannin ƙafafun da yadda aka yi su. Suna ƙyalƙyali kamar duwatsu masu daraja. Dukansu huɗu fasalinsu ɗaya ne. An yi su kamar wata ƙafa tana cikin wata ƙafa.

17 Sa’ad da suke tafiya, suna tafiya a kowane waje, ba sai sun juya ba.

18 Akwai waɗansu ƙarafa kamar zobe, da idanu kuma tantsai kewaye da ƙafafun.

19 Duk sa’ad da talikan suka motsa, sai kuma ƙafafun su motsa tare da su. Idan kuma talikan suka ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga tare da su.

20 Duk inda ruhu ya nufa, sai talikan su bi, sai kuma ƙafafun su tafi tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.

21 Idan talikan sun motsa, sai ƙafafun kuma su motsa. Idan sun tsaya cik, sai su ma su tsaya. Idan kuma talikan sun ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga sama tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.

22 Sama da talikan akwai kamannin al’arshi mai walƙiya kamar madubi.

23 A ƙarƙashin al’arshin fikafikansu sun miƙe kyam daura da juna. Kowane taliki yana da fikafikai biyu da su yake rufe jikinsa.

24 Sa’ad da suke tafiya, sai na ji motsin fikafikansu kamar amon ruwa, kamar kuma muryar tsawar Maɗaukaki, kamar hayaniyar runduna. Idan sun tsaya cik, sai su saukar da fikafikansu.

25 Sai aka ji murya ta fito daga saman al’arshi ɗin.

26 A saman al’arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta.

27 Daga kwankwasonsa zuwa sama yana walƙiya kamar tagullar da aka kewaye ta da wuta. Daga kwankwasonsa zuwa ƙasa yana haskakawa kamar wuta.

28 Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka nan kamannin hasken da yake kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.

Categories
EZ

EZ 2

Kiran Ezekiyel

1 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka tashi tsaye, zan yi magana da kai.”

2 Da ya yi magana da ni, sai Ruhu ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye, sa’an nan na ji yana magana da ni.

3 Ya ce mini, “Ɗan mutum na aike ka zuwa wurin jama’ar Isra’ila, al’umma mai tayarwa, waɗanda suka tayar mini. Su da ubanninsu suna yi ta yi mini laifi har yau.

4 Su mutane ne marasa kunya, masu taurinkai. Ga shi kuwa, na aike ka gare su, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.’

5 Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.

6 “Kai ɗan mutum, kada ka ji tsoronsu, kada kuma ka ji tsoron maganganunsu, ko da ya ke ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya sun kewaye ka, kana kuma zaune tare da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su ‘yan tawaye ne.

7 Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su ‘yan tawaye ne.

8 “Amma kai, ya ɗan mutum, ka ji abin da zan faɗa maka, kada ka zama mai tayarwa kamar ‘yan tawayen nan. Sai ka buɗe bakinka, ka ci abin da zan ba ka.”

9 Da na duba, sai ga hannu yana miƙo mini littafi.

10 Ya buɗe littafin a gabana, akwai rubutu ciki da baya. Ba abin da aka rubuta sai maganganun baƙin ciki, da makoki, da kaito.

Categories
EZ

EZ 3

1 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum ka ci abin da aka ba ka. Ka ci wannan littafi, sa’an nan ka tafi ka yi wa mutanen Isra’ila magana.”

2 Sai na buɗe bakina, sa’an nan ya ba ni littafin in ci.

3 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci littafin nan da na ba ka, ka cika tumbinka da shi.” Sai na ci littafin, na ji shi a bakina da zaƙi kamar zuma.

4 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ka tafi wurin mutanen Isra’ila ka faɗa musu maganata.

5 Gama ba a aike ka a wurin mutane waɗanda suke da baƙon harshe wanda ba ka sani ba, amma zuwa mutanen Isra’ila,

6 ba wurin waɗansu mutane dabam waɗanda suke da baƙon harshe mai wuya ba, wato harshen da ba ka sani ba. Da na aike ka wurin irin mutanen nan da za su ji.

7 Amma mutanen Isra’ila ba za su ji ka ba, ba su kuwa da nufi su ji ni, gama suna da taurinkai da taurin zuciya.

8 Ga shi, na sa fuskarka da goshinka su zama da tauri kamar nasu.

9 Kamar yadda lu’ulu’u ya fi ƙanƙarar dutse ƙarfi, haka nan na sa goshinka ya zama. Kada ka ji tsoronsu, ko kuwa ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su ‘yan tawaye ne.”

10 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, sai ka ji, ka karɓi dukan maganata da zan faɗa maka.

11 Sa’an nan ka tafi wurin mutanenka waɗanda suke cikin bautar talala, ka faɗa musu, ko su ji, ko kada su ji.”

12 Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni, sai na ji murya a bayana, kamar babban motsi, tana cewa, “Yabo ga ɗaukakar Ubangiji a kursiyinsa.”

13 Na kuma ji amon fikafikan talikan ne sa’ad da suka taɓa junansu, da kuma amon ƙafafun da suke kusa da talikan, da amon babban motsi.

14 Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi.

15 Na zo wurin ‘yan bautar talala a Telabib, waɗanda suke bakin kogin Kebar. Na zauna tare da su kwana bakwai, ina ta mamaki.

Ezekiyel Ya Zama Mai Tsaron Isra’ila

16 A ƙarshen kwana bakwai ɗin, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

17 “Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra’ila. Sa’ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina.

18 Idan na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ kai kuwa ba ka faɗakar da shi a kan mugayen ayyukansa don ka ceci ransa ba, wannan mugun mutum zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

19 Amma idan ka faɗakar da mugu, ya kuwa ƙi barin muguntarsa, zai mutu cikin zunubinsa, kai kam ka kuɓuta.

20 “Idan kuma adali ya bar adalci sa’an nan ya aikata zunubi, ni kuwa na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Zai mutu saboda zunubinsa domin ba ka faɗakar da shi ba. Ba za a tuna da ayyukansa na adalci waɗanda ya yi ba, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

21 Amma idan ka faɗakar da adali, kada ya aikata zunubi, shi kuwa bai aikata zunubi ba, hakika zai rayu domin ya ji faɗakar, kai kuma ka kuɓuta.”

Annabi Ya Zama Bebe

22 Ikon Ubangiji yana tare da ni, Ubangiji kuwa ya ce mini, “Tashi, ka tafi ka tsaya a fili, a can zan yi magana da kai.”

23 Sai na tashi na tafi na tsaya a fili, sai ga ɗaukakar Ubangiji a wurin, a tsaye kamar ɗaukakar da na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.

24 Ruhu kuwa ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye. Sai ya yi magana da ni, ya ce, “Ka tafi, ka kulle kanka cikin gida.

25 Ya ɗan mutum, za a ɗaure ka da igiyoyi don kada ka tafi cikin jama’a.

26 Ni kuwa zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka zama bebe, ka kasa tsauta musu, gama su ‘yan tawaye ne.

27 Amma sa’ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi musu magana, ka ce, ‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,’ gama su ‘yan tawaye ne.”

Categories
EZ

EZ 4

Ezekiyel Ya Misalta yadda Za a Kewaye Urushalima da Yaƙi

1 “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki tubali, ka ajiye a gabanka, sa’an nan ka zāna birni a kansa, wato Urushalima.

2 Sa’an nan ka gina mata kagara, da garu da ɗan tudu. Ka kuma kafa mata sansani ka kewaye ta da dundurusai.

3 Ka ɗauki kwano, ka shirya shi kamar garun ƙarfe tsakaninka da birnin, sa’an nan ka zuba ido. Birnin zai zama kamar an kewaye shi da yaƙi, kai kuwa ka kewaye shi da yaƙi. Wannan kuma zai zama alama ga Isra’ilawa.

4 “Sai kuma ka kwanta a hagunka, ni kuwa zan ɗora maka muguntar Isra’ilawa. Za ka ɗauki muguntarsu bisa ga yawan kwanakin da za ka kwanta a hagunka.

5 Gama na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun muguntarsu, wato kwana ɗari uku da tasa’in da za ka kwanta. Ta haka za ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Isra’ila.

6 Sa’ad da ka cika waɗannan kwanaki, sai ka sāke kwantawa, kwanciya ta biyu, a damanka kwana arba’in don ka ɗauki alhakin muguntar mutanen Yahuza. Kwana ɗaya a bakin shekara guda.

7 “Za ka fuskanci Urushalima wadda aka kewaye ta da yaƙi da hannunka a zāge, sa’an nan ka yi annabci a kanta.

8 Ga shi, zan ɗaure ka da igiyoyi don kada ka juya har ka gama misalin adadin kwanakin da za a kewaye Urushalima da yaƙi.

9 “Ka kuma ɗauki alkama, da sha’ir, da wake, da waken soya, da gero, da acca, ka haɗa su a kasko ɗaya, ka yi abinci da su. Shi ne za ka ci a kwanakin na ɗari uku da tasa’in da za ka kwanta.

10 Za a auna maka abincin da za ka ci, kamar nauyin shekel ashirin ne a yini. Za ka ci shi a ƙayyadadden lokaci kowace rana.

11 Za a kuma auna maka ruwan da za ka sha, misalin kwalaba biyu ga yini. Za ka sha ruwan a ƙayyadadden lokaci kowace rana.

12 Za ka yi waina kamar ta sha’ir, ka ci. Za ka toya ta da najasa a idon jama’a.”

13 Ubangiji ya ce, “Haka jama’ar Isra’ila za su ci ƙazantaccen abincinsu a cikin sauran al’umma inda za a kai su bautar talala.”

14 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Tun daga ƙuruciyata har zuwa yau, ban taɓa cin mushe ba, ko abin da namomin jeji suka kashe. Ƙazantaccen nama bai taɓa shiga bakina ba.”

15 Sa’an nan ya ce mini, “To, zan bar ka ka mori taroson shanu maimakon najasa, don ka dafa abincinka.”

16 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ga shi, zan datse abinci a Urushalima. Za su auna abincin da za su ci da tsoro, su kuma auna ruwan da za su sha da damuwa.

17 Haka abinci da ruwa za su kāsa, za su kuwa dubi juna da damuwa. Za su lalace saboda zunubansu.”

Categories
EZ

EZ 5

Ezekiyel ya Aske Kansa

1 Ubangiji ya ce, “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki takobi mai kaifi, ka more shi kamar askar wanzami, ka aske kanka da gemunka. Ka auna gashin da ma’auni, don ka raba shi kashi uku.

2 Sai ka ƙone kashi ɗaya da wuta a tsakiyar birnin sa’ad da kwanakin kewaye birnin da yaƙi suka cika. Ka kuma ɗauki sulusi ɗaya ka yanyanka da takobi kewaye da birnin. Sulusi ɗayan kuwa za ka watsar ya bi iska. Ni kuwa zan zare takobi a kansu.

3 Za ka ɗibi gashi kaɗan ka ɗaure a shafin rigarka.

4 Daga cikin gashi kaɗan ɗin nan kuma, sai ka ɗibi waɗansu ka sa a wuta. Daga nan ne wuta za ta tashi a Isra’ila duka.”

5 Ubangiji Allah ya ce, “Wannan ita ce Urushalima. Na kafa ta a tsakiyar al’ummai da ƙasashe kewaye da ita.

6 Ga shi, ta tayar wa ka’idodina da muguwar tayarwa fiye da al’ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka’idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina.

7 Domin haka ni na ce, ‘Da yake kin cika rikici fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da suke, kin ƙi yin tafiya cikin dokokina, ba ki kiyaye ka’idodin ba, amma kin bi ka’ikodin al’umman da take kewaye da ke,

8 to, ina gāba da ke, zan hukunta ki a idanun al’ummai.

9 Saboda yawan abubuwa masu banƙyama da kika aikata, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan sāke yin irinsa ba.

10 Ubanni za su cinye ‘ya’yansu, ‘ya’ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko’ina.

11 “‘Tun da yake kin ƙazantar da Haikalina mai tsarki da gumakanki da abubuwanki masu banƙyama, hakika, ni Ubangiji Allah, zan kawar da ke, ba zan ji tausayinki ba, ba kuwa zan haƙura ba.

12 Sulusinki zai mutu da annoba da yunwa. Takobi kuma zai kashe sulusinki, sa’an nan zan watsar da sulusinki ko’ina, zan kuma zare takobi a kansu.

13 “‘Ta haka zan sa fushina ya huce, hasalata kuma a kansu ta lafa, ni kuma in wartsake. Sa’an nan za su sani ni Ubangiji na yi magana da zafin kishi sa’ad da na iyar da fushina a kansu.

14 Zan kuma maishe ki kufai da abin zargi ga al’ummai da suke kewaye da ke, da kuma a idanun dukan masu wucewa.

15 “‘Za ki zama abin zargi, da abin ba’a, da abin faɗaka, da abin tsoro ga al’ummai da suke kewaye da ke sa’ad da na hukunta ki da zarin fushina, ni Ubangiji na faɗa.

16 Gama zan aiko miki da masifu na yunwa domin hallakarwa. Zan aiko miki da su don su hallaka ki. Zan kawo miki yunwa mai tsanani, in sa abincinki ya ƙare.

17 Zan aiko miki da yunwa da namomin jeji, za su washe ‘ya’yanki. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki. Zan kuma kawo takobi a kanki, ni Ubangiji na faɗa.”’

Categories
EZ

EZ 6

Annabci Gāba da Duwatsun Isra’ila

1 Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

2 “Ya ɗan mutum, ka zuba ido wajen duwatsun Isra’ila, sa’an nan ka yi annabci a kansu.

3 Ka ce musu, ‘Ya ku duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji Allah! Haka Ubangiji Allah ya ce a kan duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka. Ga shi, ni kaina, zan kawo takobi a kanku, zan hallaka wuraren tsafinku.

4 Bagadanku za su zama kango, za a farfasa bagadanku na ƙona turare, zan sa kisassunku su faɗi a gaban gumakansu,

5 zan sa gawawwakin Isra’ilawa a gaban gumakansu, zan warwatsa ƙasusuwanku kewaye da bagadanku.

6 A duk inda kuke zaune, biranenku za su zama kango, wuraren tsafinku da bagadanku za su lalace, gumakanku da bagadanku na ƙona turare za a farfashe su. Za a shafe dukan abin da kuka yi.

7 Za a kashe waɗansu daga cikinku sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji.

8 “‘Duk da haka zan bar waɗansunku da rai, gama waɗansu daga cikinku za su tsere wa takobi, amma zan watsa su cikin sauran al’umma.

9 Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al’ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.

10 Za su kuma sani, ni Ubangiji, ba a banza na ce zan kawo musu wannan masifa ba.”’

11 Ubangiji Allah ya ce, “Ka tafa hannunka, ka ɗage ƙafarka, sa’an nan ka ce, ‘Kaito, kaito, saboda dukan mugayen abubuwan ƙyama da mutanen Isra’ila suka yi, gama takobi, da yunwa, da annoba za su kashe su.

12 Annoba za ta kashe wanda yake nesa, wanda yake kusa kuwa takobi zai kashe shi. Yunwa kuma za ta kashe wanda yaƙi ya kewaye shi. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.

13 Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakinsu sun kwanta tare da gumakansu kewaye da bagadansu a kan kowane tudu, da kan tsaunuka, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, da ƙarƙashin itacen oak mai ganye, duk inda suka miƙa turare mai ƙanshi ga dukan gumakansu.

14 Zan nuna ikona a dukan ƙasar, in mai da ita da wuraren zamansu duka hamada. Ƙasarsu za ta zama hamada har zuwa Dibla. Kowa zai sani ni ne Ubangiji.”’

Categories
EZ

EZ 7

Matuƙa ta Yi

1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ya kai, ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce wa ƙasar Isra’ila, matuƙa ta yi a kan kusurwa huɗu na ƙasar!

3 “Yanzu matuƙarki ta yi. Zan fashe fushina a kanki, zan kuma shara’anta ki bisa ga ayyukanki, in hukunta ki saboda dukan ƙazantarki.

4 Ba zan yafe miki ba, ba kuwa zan ji tausayinki ba, amma zan hukunta ki saboda ayyukanki sa’ad da kike tsakiyar aikata ƙazantarki. Sa’an nan za ki sani ni ne Ubangiji.”

5 Ubangiji Allah ya ce, “Masifa a kan masifa, ga shi, tana zuwa!

6 Matuƙa ta yi, ta farka a kanki, ga shi, ta yi!

7 Ƙaddararku ta auko muku, ya ku mazaunan ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato, ranar tunzuri, ba ta murna da ta sowa a kan duwatsu ba.

8 “Yanzu, ba da jimawa ba, zan fashe hasalata a kanku, in aukar da fushina a kanku, in hukunta ku bisa ga ayyukanku. Zan hukunta ku saboda dukan ƙazantarku.

9 Ba zan yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan hukunta ku bisa ga ayyukanku sa’ad da kuke tsakiyar aikata ƙazantarku, sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji wanda yake hukunta ku.

10 “Ga rana ta zo. Ƙaddararku ta zo, rashin gaskiya ta yi fure, girmankai kuma ya yi toho.

11 Hargitsi ya habaka, ya zama sandan mugunta. Ba wanda zai ragu cikinsu, ko yawaitarsu, ko dukiyarsu, ko wani muhimmi a cikinsu.

12 “Lokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama fushina yana kan taron jama’a duka.

13 Mai sayarwa ba zai ta da ciniki ba sa’ad da suke da rai, gama fushina yana bisa kan dukan taron jama’arsu, ba zai fasa ba. Ba wanda yake zamansa cikin zunubi da zai iya shiryar da kansa.”

Hukunci a kan Zunuban Isra’ila

14 “Sun busa ƙaho, sun gama shiri duka, amma ba wanda ya tafi yaƙi, gama fushina yana kan dukan taron jama’a.

15 Takobi yana zare a waje, annoba da yunwa suna ciki. Wanda yake waje takobi zai kashe shi, wanda kuma yake ciki annoba da yunwa za su kashe shi.

16 Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.

17 Dukan hannuwa sun raunana, dukan gwiyoyi kuma sun zama marasa ƙarfi kamar ruwa.

18 Sun sa tufafin makoki, razana ta kama su, fuskokinsu kuma suna cike da kunya, akwai sanƙo a kawunansu.

19 Sun watsar da azurfarsu a titi, zinariyarsu kuma ta zama kamar ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba, a ranar fushin Ubangiji. Ba za su iya ƙosar da su ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu.

20 Suna fariyar banza da kyawawan kayan adonsu, na zinariya da azurfa. Da su suka yi siffofi masu banƙyama, da ƙazantattun abubuwa. Domin haka zan maishe su ƙazantattun abubuwa a gare su.

21 “Zan ba da su ganima ga baƙi, da kwaso ga mugayen mutanen ƙasar. Za su lalatar da su.

22 Zan kuwa juya daga gare su. Zan bar su su ƙazantar da Haikalina. Mafasa za su shiga su ƙazantar da shi.

23 “Sai ka ƙera surƙa, gama ƙasar tana cike da alhakin jini, birnin kuma yana cike da hargitsi.

24 Zan kawo al’ummai masu muguntar gaske su mallaki gidajensu. Zan sa fariyar masu ƙarfi ta ƙare. Za a ƙazantar da masujadansu.

25 Sa’ad da wahala ta zo, za su nemi salama, amma ba za su same ta ba.

26 Masifa a kan masifa, jita-jita a kan jita-jita. Suna neman wahayi daga wurin annabi, amma doka ta lalace a wurin firist, shawara kuma ta lalace a wurin dattawa.

27 Sarki yana makoki, yarima kuma zai fid da zuciya. Hannuwan mutanen ƙasar sun shanye saboda razana. Zan sāka musu bisa ga ayyukansu, zan kuma hukunta su kamar yadda suka hukunta waɗansu. Za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

Categories
EZ

EZ 8

Wahayin Abubuwan Banƙyama da ake Yi a Urushalima

1 A kan rana ta biyar ga wata na shida a shekara ta shida ta zaman talala, sa’ad da nake zaune a gidana, dattawan Yahuza kuma suna zaune a gabana, sai ikon Ubangiji Allah ya sauka a kaina.

2 Da na duba, sai ga siffa wadda dake da kamannin mutum. Daga kwankwason siffar zuwa ƙasa yana da kamannin wuta, daga kwankwason kuma zuwa sama yana da haske kamar na tagulla.

3 Sai ya miƙa hannu, ya kama zankon kaina. Ruhu kuma ya ɗaga ni bisa tsakanin sama da ƙasa, ya kai ni Urushalima cikin wahayi zuwa ƙofar farfajiya ta ciki, wadda take fuskantar arewa, inda mazaunin siffa ta tsokano kishi yake.

4 Sai ga ɗaukakar Allah na Isra’ila a wurin, kamar wahayin da na gani a fili.

5 Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka, ka duba wajen arewa.” Na kuwa ɗaga idanuna wajen arewa, na kuma ga siffa ta tsokano kishi a mashigin ƙofar bagade na wajen arewa.

6 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwa masu banƙyama da mutanen Isra’ila suke yi a nan don su kore ni nesa da Haikalina? Ai, za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka.”

7 Ya kuma kai ni ƙofar shirayi. Sa’ad da na duba, sai ga wani rami a bangon.

8 Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka haƙa bangon.” Da na haƙa bangon, sai ga ƙofa.

9 Ya ce, mini, “Ka shiga ka ga abubuwan banƙyama da suke aikatawa a nan.”

10 Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra’ila kewaye da bangon.

11 Dattawan Isra’ila saba’in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.

12 Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ko ka ga abin da dattawan Isra’ilawa suke yi a cikin duhu? Kowa yana cikin ɗakin zānannun siffofin gumaka, sukan ce, ‘Allah ba ya ganinmu. Ubangiji ya rabu da ƙasan nan.”’

13 Ya kuma ce mini, “Har yanzu dai za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka waɗanda suke aikatawa.”

14 Sai ya kai ni a bakin ƙofar arewa ta Haikalin Ubangiji, ga kuwa mata a zaune suna kuka domin gunkin nan, Tammuz.

15 Sa’an nan ya ce mini, “Ya ɗan mutum, ka ga wannan? Har yanzu ma za ka ga abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”

16 Ya kuma kai ni farfajiya ta can cikin Haikalin Ubangiji. Na ga mutum wajen ashirin da biyar a ƙofar Haikalin Ubangiji a tsakanin shirayi da bagade, suka juya wa Haikalin Ubangiji baya, suka fuskanci wajen gabas, suna yi wa rana sujada.

17 Ya kuma ce mini, “Ya ɗan mutum, ka ga wannan? Wato mutanen Yahuza ba su mai da aikata abubuwa masu banƙyama nan wani abu ba. Sun cika ƙasar da hargitsi, suna ta tsokanar fushina. Ga shi, suna hura hanci a gabana.(Eze 9.9; Eze 16.26

18 Zan yi hukunci mai zafi, ba zan yafe ba, ba kuma zan ji tausayi ba, ko da yake suna kuka da babbar murya a kunnuwana ba zan ji su ba.”

Categories
EZ

EZ 9

An Kashe Masu Laifi

1 Sai na ji Allah ya yi kira da babbar murya, ya ce, “Ku matso kusa, ku masu hukunta wa birnin, kowa ya zo da makaminsa na hallakarwa a hannu.”

2 Sai ga mutum shida sun taho daga wajen ƙofa wadda take daga bisa wadda ta fuskanci arewa. Kowa yana da makaminsa na kisa a hannu. Tare da su kuma akwai wani mutum saye da rigar lilin, yana kuma rataye da gafaka. Sai suka tafi suka tsaya a gefen bagaden tagulla.

3 Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tashi daga kan siffar kerubobi inda take zaune zuwa bakin ƙofar Haikalin. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da rigar lilin, wanda yake rataye da gafaka.

4 Ya ce masa, “Ka ratsa cikin birni, wato Urushalima, ka sa shaida a goshin mutanen da suke ajiyar zuciya, suna damuwa saboda dukan abubuwa masu banƙyama waɗanda ake aikatawa a birnin.”

5 Na kuma ji ya ce wa sauran, “Ku bi shi, ku ratsa cikin birnin, ku kashe, kada ku yafe, kada kuwa ku ji tausayi.

6 Ku kashe tsofaffi, da samari, da ‘yan mata, da ƙananan yara, da mata, amma kada ku taɓa wanda yake da shaida. Sai ku fara a Haikalina.” Suka kuwa fara da dattawan da suke a gaban Haikalin.

7 Ya kuma ce musu, “Ku ƙazantar da Haikalin, ku cika farfajiya da kisassu, sa’an nan ku tafi!” Sai suka tafi, suka yi ta kashe mutanen da suke cikin birnin.

8 Sa’ad da suke karkashewar, aka bar ni, ni kaɗai, sai na faɗi rubda ciki, na yi kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah za ka hallaka dukan sauran Isra’ilawa saboda zafin fushinka a kan Urushalima?”

9 Sa’an nan ya ce mini, “Zunubin mutanen Isra’ila da Yahuza ya kasaita ƙwarai. Ƙasar tana cike da jini, birnin kuma yana cike da rashin imani, gama sun ce, ‘Ubangiji ya rabu da ƙasar, ba ya ganinmu.’

10 Ni kam, idona ba zai yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan sāka musu bisa ga ayyukansu.”

11 Sai ga mutumin da yake saye da rigar lilin, wanda kuma yake rataye da gafaka, ya komo da jawabi cewa, “Na aikata yadda ka umarci ni.”

Categories
EZ

EZ 10

Ɗaukakar Ubangiji ta Rabu da Haikali

1 Da na duba sararin sama da yake bisa kawunan kerubobi, sai na ga wani abu ya bayyana kamar yakutu. Fasalinsa kamar na kursiyi.

2 Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da rigar lilin. “Ka shiga ƙarƙashin ƙafafun kerubobin, ka cika tafin hannunka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin, ka watsa bisa kan birnin.”

Na kuwa ga ya tafi.

3 Kerubobin kuwa suna tsaye a gefen kudu na Haikalin a sa’ad da mutumin ya shiga, girgije kuma ya cika farfajiyar da take can ciki.

4 Ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga kan kerubobin zuwa ƙofar Haikalin. Girgije kuwa ya cika Haikalin, hasken zatin Ubangiji ya cika farfajiyar.

5 Sai aka ji amon fikafikan kerubobin a filin da yake can waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa’ad da yake magana.

6 Ya kuwa umarci wanda yake saye da lilin ɗin, ya ce, “Ka ɗibi wuta daga ƙarƙashin ƙafafun da suke tsakanin kerubobin.” Sai ya tafi ya tsaya a gefen ƙafar.

7 Kerub kuwa ya miƙa hannunsa daga tsakanin kerubobi zuwa wurin wutar da take tsakanin kerubobin, ya ɗebo wutar, ya zuba a ahannun mutumin da yake saye da rigar lilin. Shi kuwa ya karɓa, ya fita.

8 Kerubobin suna da hannuwa kamar na ‘yan adam a ƙarƙashin fikafikansu.

9 Da na duba, sai na ga ƙafa guda huɗu kusa da kerubobin. Kowane kerub yana da ƙafa ɗaya kusa da shi. Ƙafafun suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja.

10 Dukansu kuwa kamanninsu ɗaya, kamar ƙafa a cikin ƙafa.

11 Sa’ad da suke tafiya, sukan tafi kowane waje, ba sai sun juya ba. Duk wajen da ƙafar gaba ta nufa, nan sauran za su bi, ba sai sun juya ba.

12 Suna da idanu a jikunansu ko’ina, a bayansu, da hannuwansu, da fikafikansu da kuma ƙafafunsu.

13 Na ji ana kiran ƙafafun, ƙafafun guguwa.

14 Kowane kerub yana da fuska huɗu. Fuska ta fari ta kerub ce, fuska ta biyu ta mutum ce, fuska ta uku ta zaki ce, fuska ta huɗu kuwa ta gaggafa ce.

15 Kerubobin kuwa suka tashi sama. Waɗannan su ne talikai huɗu waɗanda na gani a bakin kogin Kebar.

16 Sa’ad da kerubobin suka tafi, ƙafafun kuma sukan tafi tare da su. Sa’ad da suka ɗaga fikafikansu don su tashi daga ƙasa zuwa sama, ƙafafun kuma ba su barinsu.

17 Sa’ad da suka tsaya cik, sai ƙafafun su ma su tsaya cik, sa’ad da suka tashi sama, sai su kuma su tashi tare da su, gama ruhun talikan yana cikinsu.

18 Sai ɗaukakar Ubangiji ta tashi daga bakin ƙofar Haikalin, ta tsaya bisa kerubobin.

19 Kerubobin kuwa suka ɗaga fikafikansu, suka tashi daga ƙasa, suka yi sama a kan idona, suka tafi da ƙafafun gab da su. Suka tsaya a ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji. Ɗaukakar Allah na Isra’ila kuwa tana bisa kansu.

20 Waɗannan su ne talikan da na gani a ƙarƙarshin kursiyin Allah na Isra’ila a bakin kogin Kebar, na kuwa sani su kerubobi ne.

21 Kowannensu yana da fuska huɗu, da fiffike huɗu. A ƙarƙashin fikafikansu suna da hannuwa irin na ‘yan adam.

22 Kamannin fuskokinsu kuma daidai yake da kamannin fuskokin da na gani a bakin kogin Kebar. Sai suka tafi, kowa ya nufi gabansa sosai.