Categories
EZ

EZ 11

An Tsauta wa Mugayen Shugabanni

1 Sai Ruhu ya ɗaga ni sama, ya kai ni ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji wadda dake fuskantar gabas. Sai ga mutum ashirin da biyar a bakin ƙofar. A cikinsu na ga Yazaniya ɗan Azzur, da Felatiya ɗan Benaiya, shugabannin jama’a.

2 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan su ne mutanen da suke ƙulla mugunta, waɗanda suke ba da muguwar shawara a cikin birnin.

3 Waɗanda suke cewa, ‘Lokacin gina gidaje bai yi kusa ba. Wannan birni tukunya ce mai ɓararraka, mu ne kuwa naman.’

4 Saboda haka ka yi musu annabci marar kyau, ka yi annabci, ya ɗan mutum!”

5 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kaina, ya ce mini, “Ka ce, ‘In ji Ubangiji, haka kuke tunani, ku mutanen Isra’ila, gama na san abin da yake cikin zuciyarku.

6 Kun kashe mutane da yawa a wannan birni, har kun cika titunansa da gawawwaki.’

7 “Domin haka Ubangiji Allah ya ce, ‘Gawawwakin da kuka shimfiɗa a cikin birnin su ne naman, birnin kuwa shi ne tukunya mai ɓararraka, amma za a fitar da ku daga cikinsa.

8 Kun tsorata saboda takobi, ni kuwa zan kawo muku takobi,’ in ji Ubangiji Allah.

9 ‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku.

10 Za a kashe ku da takobi. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra’ila, sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji.

11 Birnin ba zai zama muku tukunya mai ɓararraka ba, ba kuwa za ku zama nama a cikinsa ba. Zan hukunta ku duk inda kuke a Isra’ila.

12 Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji, gama ba ku kiyaye dokokina da ka’idodina ba, amma kuka kiyaye ka’idodin sauran al’umma waɗanda suke kewaye da ku.”’

13 Sa’ad da nake yin annabci, sai Felatiya ɗan Benaiya, ya rasu. Sai na faɗi rubda ciki na fashe da kuka, na ce, “Ya Ubangiji Allah, za ka ƙare sauran mutanen Isra’ila ƙaƙaf ne?”

Allah Ya Yi wa Waɗanda aka Kai Bautar Talala Alkawari

14 Ubangiji kuwa ya yi magana da ni, ya ce,

15 “Ɗan mutum, ‘yan’uwanka, da danginka, da mutanenka da suke cikin bautar talala tare da kai, da dukan mutanen Isra’ila, su ne waɗanda mazaunan Urushalima suke ce musu, ‘Ku yi nisa da Ubangiji, mu aka mallakar wa wannan ƙasa.’

16 “Domin haka, ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah na ce, ko da yake na kai su nesa tsakanin al’ummai, na warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama Haikali a gare su a ɗan lokaci, a ƙasashen da suka tafi.’

17 “Saboda haka ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al’ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra’ila.’

18 Sa’ad da suka koma a ƙasar za su kawar da dukan abin da ya ƙazantar da ita, da dukan irin abar ƙyama da take cikinta.

19 Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu. Zan kawar musu da zuciya ta dutse, in ba su zuciya mai taushi,

20 domin su kiyaye dokokina, da ka’idodina, su aikata su. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.

21 Amma waɗanda zuciyarsu ta karkata zuwa ga bin ƙazantattun abubuwa masu banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, ni Ubangiji na faɗa.”

Ɗaukakar Ubangiji ta Rabu da Urushalima

22 Sa’an nan kerubobin suka ɗaga fikafikansu tare da ƙafafunsu. Ɗaukakar Ubangiji kuwa tana bisa kansu.

23 Sai ɗaukakar Ubangiji ta bar tsakiyar birni, ta tsaya a bisa kan dutse wanda yake wajen gabas da birnin.

24 Ruhu kuwa ya ɗauke ni a cikin wahayi, ya kai ni Kaldiya wurin ‘yan zaman talala. Sa’an nan wahayin da na gani ya rabu da ni.

25 Sai na faɗa wa ‘yan zaman talala dukan abin da Ubangiji ya nuna mini.

Categories
EZ

EZ 12

Kwatancin Kwashewarsu zuwa Bautar Talala

1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan ‘yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su ‘yan tawaye ne.

3 Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa’an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su ‘yan tawaye ne.

4 Za ka fitar da kayanka da rana a kan idonsu, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Kai kuma da kanka za ka tafi da maraice a kan idonsu, kamar yadda mutane masu tafiyar zaman talala sukan yi.

5 Ka huda katanga a kan idonsu, sa’an nan ka fita daga ciki.

6 A gabansu za ka ɗauki kayan, ka saɓa shi a kafaɗarka, ka tafi da shi da dare. Za ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na maishe ka alama ga jama’ar Isra’ila.”

7 Na kuwa yi kamar yadda aka umarce ni. Na fitar da kayana da rana, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Da maraice na huda katanga da hannuwana, sa’an nan na fita da duhu, ina ɗauke da kayana a kafaɗa, a kan idonsu.

8 Da safe kuwa Ubangiji ya yi mini magana, ya ce,

9 “Ɗan mutum, ashe, mutanen Isra’ila, ‘yan tawayen nan, ko suka ce maka, ‘Me kake yi?’

10 Ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Wannan jawabi ya shafi shugabannin Urushalima da dukan mutanen Isra’ila, waɗanda suke cikinta.’

11 Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku, kamar yadda na yi, haka za a yi da ku, za a kai ku bauta.’

12 Sarkin da yake cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa, ya fita da duhu. Zai huda katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada ya ga ƙasar da idanunsa.

13 Zan yarɓa masa ragata in kama shi. Zan kai shi Babila, wato ƙasar Kaldiyawa, duk da haka ba zai gan ta ba, ko da yake zai rasu a can.

14 Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi, masu taimakonsa da sojojinsa ko’ina. Zan zare takobi in runtume su.

15 “Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa’ad da na watsa su cikin sauran al’umma da cikin ƙasashe.

16 Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, da yunwa, da annoba, don su tuba, su hurta dukan ayyukansu na banƙyama a cikin al’ummai inda suka tafi. Za su sani ni ne Ubangiji.”

Kwatancin Annabin da Yake Rawar Jiki

17 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

18 “Ɗan mutum, ka ci abincinka da rawar jiki, ka sha ruwanka da makyarkyata da damuwa.

19 Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da suke a ƙasar Isra’ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suke zaune cikinta.

20 Biranen da ake zaune a cikinsu za su zama kufai, ƙasar kuma za ta zama kango, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

Sanannen Karin Magana da Jawabi Marar Daɗi

21 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

22 “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da ake faɗa a ƙasar Isra’ila cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba”?

23 Ka faɗa musu, ka ce ni Ubangiji Allah na ce zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba. Amma ka faɗa musu, cewa kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.

24 “Wahayin ƙarya da dūbā na kiran kasuwa za su ƙare a Isra’ila.

25 Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku ‘yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”

26 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

27 “Ɗan mutum, ga shi, mutanen Isra’ila suna cewa, ‘Wahayin da ya gani na wani lokaci ne can gaba, yana annabci a kan wani zamani ne na can.’

28 Domin haka ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji na ce maganata ba za ta yi jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 13

An La’anci Maƙaryatan Annabawa

1 Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ya ɗan mutum, ka yi annabci a kan annabawan Isra’ila. Ka yi annabci a kan waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayin kansu, ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji!’

3 “Ubangiji Allah ya ce kaito ga wawayen annabawa waɗanda suke bin ra’ayin zuciyarsu, ba su kuwa ga wani wahayi ba.

4 Ya Isra’ila, annabawanki suna kamar diloli a kufai.

5 Ba ku ƙaura zuwa inda garu ya tsage ba, ba ku gina wa mutanen Isra’ila garu don su kāre kansu a lokacin yaƙi, a ranar Ubangiji ba.

6 Suna faɗar ƙarya, suna kuma yin duban ƙarya, suna cewa, ‘Ubangiji ya ce,’ alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba, duk da haka sun sa zuciya ga cikawar maganarsu.

7 Wahayin ƙarya ne kuka gani, kuna yin duban ƙarya, sa’ad da kuke cewa, ‘Ubangiji ya faɗa,’ ko da yake ni Ubangiji ban faɗa ba.

8 “Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, da yake kun yi maganar wofi, kun ga wahayin ƙarya, ina gāba da ku.

9 Ikona zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya, waɗanda suke kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin mutanen Isra’ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Za ku kuwa sani, ni ne Ubangiji Allah.

10 “Domin sun ɓad da mutanena suna cewa, ‘Salama,’ sa’ad da ba salama, sa’ad da kuma mutanen suke gina garu marar aminci, sai annabawan nan su shafe shi da farar ƙasa,

11 ka faɗa wa waɗanda suka shafe garun da farar ƙasa, cewa zai faɗi. Za a yi rigyawa da ƙanƙara, da babban hadiri mai iska.

12 Sa’ad da garun ya faɗi, ashe, ba za a tambaye ku ba cewa, ‘Ina shafen farar ƙasar da kuka yi masa?’

13 “Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da hasalata zan sa babban hadiri mai iska, da rigyawa, da manyan ƙanƙara su hallaka shi.

14 Zan rushe garun da kuka shafe da farar ƙasa. Za a baje shi, a bar tushen a fili. Za ku halaka a tsakiyarsa sa’ad da ya fāɗi, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

15 “Ta haka zan aukar da hasalata a kan garun, da a kan waɗanda suka shafe shi da farar ƙasa. Sa’an nan zan faɗa muku, cewa garun ya faɗi tare da waɗanda suka shafe shi da farar ƙasa.

16 Wato annabawan Isra’ila waɗanda suka yi annabci a kan Urushalima, suka ga wahayin salama dominta, ga shi kuwa, ba salama, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

An La’anci Mata Masu Annabcin Ƙarya

17 “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka ɗaure wa matan mutanenka fuska, waɗanda suke annabci bisa ga son zuciyarsu. Ka yi annabci a kansu,

18 ka ce, ‘Ubangiji Allah ya ce, kaiton matan da suke ɗinka wa mutane kambuna, suna yi wa mutane rawunan dabo bisa ga zacinsu don su farauci rayukan mutane. Za ku farauci rayukan mutanena, sa’an nan ku bar rayukan waɗansu don ribar kanku?

19 Kun saɓi sunana a cikin mutanena don a tafa muku sha’ir, a ba ku ɗan abinci. Kuna kashe mutane waɗanda bai kamata su mutu ba, kuna barin waɗanda bai kamata su rayu ba ta wurin ƙaryace-karyacen da kuke yi wa mutanena waɗanda suke kasa kunne ga ƙaryace-ƙaryacen.’

20 “Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce, ina gāba da kambunanku da kuke farautar rayuka da su. Zan tsintsinke su daga damatsanku, in saki rayuka waɗanda kuka farauto kamar tsuntsaye.

21 Zan kuma kyakketa rawunanku na dabo, in ceci mutanena daga hannunku, ba za su ƙara zama ganima a hannunku ba, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

22 “Kun karya zuciyar adali ta wurin ƙaryarku, ko da yake ni ban karya zuciyarsa ba. Kun ƙarfafa wa mugu gwiwa, don kada ya bar hanyarsa ta mugunta, ya tsira.

23 Domin haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi dūba. Zan ceci mutanena daga hannunku. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”

Categories
EZ

EZ 14

An La’anci Bautar Gumaka

1 Waɗansu dattawa na Isra’ila suka zo wurina, suka zauna a gabana.

2 Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

3 “Ɗan mutum, waɗannan mutane sun sa zukatansu ga bin gumaka, sun sa abin tuntuɓe a gabansu, zan fa yarda su yi tambaya a wurina?

4 “Sai ka faɗa musu, cewa Ubangiji Allah ya ce duk mutumin Isra’ila, wanda ya manne wa gumaka, ya sa abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan kuma ya zo wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa gwargwadon yawan gumakansa,

5 domin in kama zukatan mutanen Isra’ila waɗanda suka zama baƙi a gare ni, saboda gumakansu.

6 “Domin haka ka ce wa mutanen Isra’ila, ‘Ubangiji ya ce ku tuba, ku rabu da gumakanku, da abubuwanku na banƙyama.

7 “‘Gama duk wanda yake na Isra’ila da dukan baƙin da suke baƙunta cikin Isra’ila, wanda ya rabu da ni, ya manne wa gumakansa, ya sa abin tuntuɓe a gabansa, sa’an nan ya zo yana roƙona a wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa.

8 Zan yi gāba da mutumin nan, zan sa ya zama abin nuni, da abin karin magana, in datse shi daga cikin mutanena, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

9 “Idan aka ruɗi annabin har ya yi magana, ni Ubangiji, ni ne na rinjaye shi, zan miƙa hannuna gāba da shi, zan hallaka shi daga cikin mutanena, Isra’ila.

10 Za su ɗauki alhakin hukuncinsu, wato hukuncin annabin, da hukuncin mai yin roƙonsa duk ɗaya ne,

11 don kada mutanen Isra’ila su ƙara rabuwa da ni, ko kuma su ƙara ƙazantar da kansu ta wurin laifofinsu, amma za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Hukuncin Allah a kan Urushalima

12 Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

13 “Ɗan mutum, sa’ad da wata ƙasa ta yi mini laifi na rashin aminci, ni kuwa na miƙa hannuna gāba da ita, na toshe hanyar abincinta, na aika mata da yunwa, na kashe mata mutum duk da dabba,

14 ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.

15 “Idan na sa namomin jeji su ratsa cikin ƙasar, su lalatar da ita har ta zama kufai yadda mutum ba zai iya ratsawa ta cikinta ba saboda namomin jejin,

16 ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci ‘ya’ya mata ko ‘ya’ya maza ba, su ne kaɗai za su tsira, amma ƙasa za ta zama kufai.

17 “Idan kuwa na jawo wa ƙasar takobi, na ce bari takobi ya ratse ƙasar, har na kashe mata mutum duk da dabba,

18 ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci ‘ya’ya mata ko ‘ya’ya maza ba, su kaɗai za su tsira.

19 Ko kuma na aika da annoba a ƙasar, na kashe mutum duk da dabba da fushina,

20 ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci ‘ya’ya mata ko ‘ya’ya maza ba, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu.

21 “Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Balle fa sa’ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi, wato takobi, da yunwa, da mugayen namomin jeji, da annoba, don in kashe mutum duk da dabba!

22 Idan kuwa waɗansu sun wanzu daga cikinta suka fita da ‘ya’yansu mata da maza zuwa wurinta, za ka ga halinsu da ayyukansu, za ka tabbata, masifar da na aukar wa Urushalima, ba kawai ba ne.

23 Bisa ga halinsu da ayyukansu za ka gane abin da na yi musu ba kawai ba ne,’ ni Ubangiji na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 15

Misali a kan Kurangar Inabi

1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum da me itacen kurangar inabi ya fi wani itace? Da me reshen kurangar inabi ya fi wani reshen itacen da yake a kurmi?

3 Za a sami itace a cikin kuranga a yi aiki da shi? Ko kuwa mutane za su iya samun maratayi a cikinta don su rataye kaya?

4 Ga shi, akan sa ta a wuta. Sa’ad da wutar ta cinye kanta da gindinta tsakiyarta kuma ta babbake, tana da amfani don yin wani aiki kuma?

5 Ga shi ma, lokacin da take cikakkiya, ba ta da wani amfani, balle bayan da wuta ta babbake ta, za a iya yin amfani da ita?

6 “Domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, kamar itacen kurangar inabi a cikin itatuwan kurmi, wanda na sa ya zama itacen wuta, haka zan sa mazaunan Urushalima su zama.

7 Zan yi gāba da su, ko da yake sun tsere wa wuta, duk da haka wuta za ta cinye su. Za ku sani ni ne Ubangiji sa’ad da na tashi yin gāba da su.

8 Zan sa ƙasar ta zama kufai domin sun yi rashin aminci, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 16

Rashin Amincin Urushalima da Samariya

1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta na banƙyama.

3 Ka faɗa wa Urushalima abin da ni Ubangiji Allah na ce mata.”

Ubangiji ya ce, “Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne. Mahaifinki Ba’amore ne, mahaifiyarki kuwa Bahittiya ce.

4 Game da haihuwarki kuwa, ran da aka haife ki, ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka da ruwa don a tsabtace ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba, ba a naɗe ki cikin tsummoki ba.

5 Ba wanda ya ji tausayinki da zai yi miki waɗannan abubuwa na jinƙai, amma aka jefar da ke a waje, gama kin zama abin ƙyama a ranar da aka haife ki.

6 “Sa’ad da na wuce kusa da ke, na gan ki kina birgima cikin jinin haihuwarki, sai na ce miki lokacin da kike cikin jinin, ‘Ki rayu!’ I, na ce miki lokacin da kike cikin jinin, ‘Ki rayu!’

7 Na sa kin girma kamar tsiro a cikin saura. Kika yi girma, kika yi tsayi, kika zama cikakkiyar budurwa, kika yi mama, gashin kanki kuwa ya yi tsawo, amma duk da haka tsirara kike tik a lokacin.

8 “Sa’ad da na sāke wucewa kusa da ke, na dube ki, ga shi, kin kai lokacin da za a ƙaunace ki, sai na yafe miki tufata, na rufe tsiraincinki, na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

9 “Sa’an nan na yi miki wanka da ruwa, na wanke jinin haihuwarki na shafe ki da mai.

10 Na sa miki rigar da aka yi wa ado, na kuma sa miki takalmin fata, na yi miki ɗamara da lilin mai kyau, na yi miki lulluɓi da siliki.

11 Na kuwa caɓa miki ado, na sa mundaye a hannuwanki, da abin wuya a wuyanki.

12 Na kuma sa ƙawanya a hancinki, da ‘yan kunne a kunnenki, da kyakkyawan kambi bisa kanki.

13 Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa. Tufafinki kuwa na lilin mai kyau ne, da siliki waɗanda aka yi musu ado. Kin ci lallausan gāri, da zuma, da mai. Kin yi kyau ƙwarai har kin zama sarauniya.

14 Kin shahara a cikin sauran al’umma saboda kyanki, gama kyanki ya zama cikakke saboda ƙawata ki da na yi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

15 “Amma kin dogara ga kyanki, kika yi karuwanci saboda shahararki. Kin yi ta karuwancinki da kowane mai wucewa.

16 Kin ɗauki waɗansu rigunanki, kika yi wa kanki masujadai masu ado, sa’an nan kika yi karuwanci a cikinsu, irin abin da ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a yi ba nan gaba.

17 Kin kuma ɗauki kayan adonki na zinariyata da azurfata waɗanda na ba ki, kin yi wa kanki siffofin mutane don ki yi karuwanci da su.

18 Kin ɗauki tufafinki da aka yi musu ado, kika lulluɓe su, sa’an nan kika ajiye maina da turarena a gabansu.

19 Abincina da na ba ki kuma, wato lallausan gāri, da mai, da zuma, waɗanda na ciyar da ke da su, kin ajiye a gabansu don ƙanshi mai daɗi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

20 “Kin kuma kwashe ‘ya’yana mata da maza waɗanda kika haifa mini kin miƙa su hadaya ga gumaka. Karuwancinki, ba ƙanƙanen abu ba ne.

21 Kin karkashe ‘ya’yana, kin sa su ratsa cikin wuta.

22 A cikin aikata dukan abubuwanki na banƙyama kuma, da karuwancinki, ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, lokacin da kike tsirara tik, kina birgima cikin jinin haihuwarki.

23 “Bayan dukan muguntarki (Kaito, kaitonki! Ni Ubangiji Allah na faɗa),

24 sai kika gina wa kanki ɗakunan tsafi a kowane fili.

25 Kika kuma gina ɗakin tsafi a kowane titi. Kin waƙala darajarki, kin ba da kanki ga kowane mai wucewa, ta haka kika yawaita karuwancinki.

26 Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi. Kin yawaita karuwancinki don ki tsokani fushina.

27 “Domin haka na miƙa hannuna gāba da ke, na rage rabonki, na ba da ke ga abokin gābanki masu haɗama, ‘yan matan Filistiyawa waɗanda suka ji kunya saboda halinki na lalata.

28 “Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa domin ba ki ƙoshi ba. Kin yi karuwanci da su duk da haka ba ki ƙoshi ba.

29 Kin yawaita karuwancinki da Kaldiya, ƙasar ciniki, duk da haka ba ki ƙoshi ba.

30 “Kin cika uzuri,” in ji Ubangiji Allah. “Duba, kin aikata waɗannan abubuwa duka, ayyuka na karuwa marar kunya.

31 Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da yake ba ki karɓar kuɗi.

32 Ke mazinaciyar mace, mai kwana da kwartaye maimakon mijinki!

33 Maza sukan ba dukan karuwai kuɗi, amma ke ce mai ba kwartayenki kuɗi, kina ba su kuɗi don su zo wurinki don kwartanci daga ko’ina.

34 Kin yi dabam da sauran mata a cikin karuwancinki, da yake ba wanda ya bi ki don yin karuwanci, ba a ba ki kuɗi, ke ce kike ba da kuɗi, domin haka kin sha bamban.”

35 Domin haka, ya ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji.

36 “Ubangiji Allah ya ce, da yake kunyarki ta bayyana, an buɗe tsiraicinki cikin karuwancinki, saboda kuma gumakanki, da jinin ‘ya’yanki da kika miƙa wa gumakanki,

37 domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani.

38 Zan hukunta ki kamar yadda akan hukunta mata waɗanda suka ci amanar aure, suka zub da jini. Zan hallaka ki cikin zafin fushina da kishina.

39 Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.

40 “Za su kuta taron mutane a kanki, za su jajjefe ki da duwatsu, su yayanka ki gunduwa gunduwa da takubansu.

41 Za su kuma ƙone gidajenki, su hukunta ki a gaban mata da yawa. Ni kuwa zan sa ki bar karuwanci, ba za ki ƙara ba da kuɗi ga kwartayenki ba.

42 Sa’an nan fushina a kanki zai huce, kishina a kanki zai ƙare. Zan huce, ba zan yi fushi ba kuma.

43 Da yake ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, amma kika husatar da ni da waɗannan abubuwa, domin haka zan sāka miki alhakin ayyukanki. Kin yi lalata, banda ayyukanki na banƙyama kuma, ni Ubangiji na faɗa.”

44 Ubangiji ya ce, “Ga shi, duk mai yin amfani da karin magana, zai faɗi wannan karin magana a kanki. ‘Kamar yadda mahaifiya take haka ‘yar take.’

45 Ke ‘yar mahaifiyarki ce wadda ta ƙi mijinta da ‘ya’yanta. Ke kuma ‘yar’uwar ‘yar’uwanki mata ce waɗanda suka ƙi mazansu da ‘ya’yansu. Mahaifiyarki Bahittiya ce, mahaifinki kuwa Ba’amore ne.

46 “’Yarki ita ce Samariya wadda take zaune da ‘ya’yanta mata wajen arewa da yake. Ƙanwarki ita ce Saduma wadda take zaune kudu da ke tare da ‘ya’yanta mata.

47 Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.

48 “Hakika ni Ubangiji Allah na ce Saduma ƙanwarki da ‘ya’yanta mata ba su yi kamar yadda ke da ‘ya’yanki mata kuka yi ba.

49 Wannan shi ne laifin Saduma, ƙanwarki, ita da ‘ya’yanta mata, suna da girmankai domin suna da abinci a wadace, suna zama a sangarce, amma ba su taimaki matalauta da masu bukata ba.

50 Su masu alfarma ne, sun aikata abubuwa masu banƙyama a gabana, saboda haka na kawar da su sa’ad da na gani.

51 “Samariya ba ta aikata rabin zunubin da kika aikata ba. Abubuwan banƙyama da kika aikata sun sa ‘yan’uwanki sun zama kamar adalai.

52 Ke kuma sai ki sha kunyarki, gama kin sa ‘yan’uwanki mata su sami rangwamin shari’a saboda zunubanki da kika aikata fiye da nasu, gama gwamma su da ke. Sai ki ji kunya, ki sha ƙasƙancinki, gama kin sa ‘yan’uwanki mata su zama kamar adalai.”

53 Ubangiji ya ce wa Urushalima, “Zan komo da Saduma da Samariya da ‘ya’yansu mata daga bauta. Sa’an nan zan komo da ke daga bauta tare da su,

54 don ki sha ƙasƙanci saboda abin kunyar da kika aikata. Ƙasƙancinki zai ta’azantar da ‘yan’uwanki mata.

55 ‘Yan’uwanki mata, wato Saduma da ‘ya’yanta mata za su koma kamar yadda suke a dā, Samariya kuma da ‘ya’yanta mata za su koma kamar yadda suke a dā. Ke kuma da ‘ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kuke a dā.

56 Ashe, ba ƙanwarki, Saduma, ta zama abar karin magana a bakinki a kwanakin fariyarki,

57 kafin asirin muguntarki ya tonu ba? Amma yanzu kin zama abin zargi ga ‘ya’yan Edom mata, da waɗanda suke kewaye da ita, da ‘ya’yan Filistiyawa mata waɗanda suke kewaye, waɗanda suke raina ki.

58 Kina ɗauke da hukuncin lalatarki da na abubuwanki masu banƙyama, ni Ubangiji na faɗa.”

Alkawarin da Zai Dawwama

59 “Ni Ubangiji Allah na ce, zan yi miki yadda kika yi, ke da kika yi rantsuwar kafara, kika ta da alkawari.

60 Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin kuruciyarki. Zan ƙulla madawwamin alkawari da ke.

61 Sa’an nan za ki tuna da ayyukanki, ki ji kunya, sa’ad da na ɗauki yarki da ƙanwarki, na ba ki su, su zama ‘ya’yanki mata, amma ba a kan alkawarin da na yi da ke ba.

62 Zan ƙulla alkawarina da ke, za ki sani ni ne Ubangiji,

63 domin ki tuna, ki gigice, ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, sa’ad da na gafarta miki dukan abin da kika aikata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 17

Misalin Gaggafa da Kurangar Inabi

1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen Isra’ila ka-cici-ka-cici, da kuma misali.

3 Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al’ul.

4 Ta karya kan tohonsa mafi tsawo, ta kai shi a ƙasar ciniki, ta dasa shi a birnin ‘yan kasuwa.

5 Sai kuma ta ɗauki irin na ƙasar, ta dasa shi a wuri mai dausayi kusa da ruwa mai yawa. Ta dasa shi kamar itacen wardi.

6 Ya yi toho, ya zama kuranga mai yaɗuwa. Rassanta suka tanƙwasa wajenta. Saiwoyinta suka kama ƙasa sosai. Haka ta zama kuranga, ta yi rassa da ganyaye.

7 “ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuranga ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajenta, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajenta tun daga inda aka dasa ta, don gaggafar ta yi mata banruwa.

8 An dasa ta a wuri mai dausayi inda akwai ruwa da yawa don ta yi ganyaye, ta kuma ba da ‘ya’ya, ta zama kurangar inabi ta ƙwarai.’

9 Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ko wannan kurangar inabi za ta ci gaba? Ashe, gaggafa ta farko ba za ta tumɓuke saiwoyinta, ta sassare rassanta, don ganyayenta da suke tohuwa su bushe ba? Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba.

10 Idan aka sāke dasa ta kuma za ta yi amfani? Ba za ta bushe sarai sa’ad da iskar gabas ta hura ba? Lalle za ta bushe tun daga inda aka dasa ta ta yi girma.”’

Fassarar Misalin

11 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

12 “Ka tambayi mutanen Isra’ila, ‘yan tawayen nan cewa, ‘Ba ku san ma’anar waɗannan abubuwa ba?’ Ka faɗa musu, cewa Sarkin Babila ya zo Urushalima, ya tafi da sarkinta da shugabanninta zuwa Babila.

13 Sai ya dauƙi wani daga zuriyar sarauta, ya yi alkawari da shi, ya kuma rantsar da shi. Ya kwashe mutanen ƙasa masu maƙami,

14 don sarautar ƙasar ta raunana, ta kāsa ɗaga kanta, amma ta tsaya dai ta wurin cika alkawarinsa.

15 Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa’an nan ya tsere?

16 “Ni Ubangiji Allah, na ce, hakika wannan sarki zai mutu a Babila, domin bai cika rantsuwarsa da alkawarin da ya yi wa Sarkin Babila, wanda ya naɗa shi ba.

17 Fir’auna da yawan sojojinsa masu ƙarfi, ba za su taimake shi da yaƙin ba, sa’ad da Babilawa suka gina mahaurai da kagarai don su kashe mutane da yawa.

18 Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.

19 “Domin haka ni Ubangiji Allah, na ce, hakika zan nemi hakkin rantsuwar da ya yi mini, da alkawarin da ya yi mini, waɗanda bai cika ba.

20 Zan kafa masa tarko in kama shi, sa’an nan in kai shi Babila inda zan yi masa shari’a saboda ya tayar mini.

21 Dukan sojojinsa zaɓaɓɓu za a kashe su da takobi, za a watsar da waɗanda suka ragu ko’ina. Za ku sani ni Ubangiji ne na faɗa.”

Alkawarin Sa Zuciya

22 Ga abin da Ubangiji Allah ya ce,

“Ni kaina zan cire toho a kan itacen al’ul mai tsawo.

Daga cikin sababbin rassansa zan karya lingaɓu,

In dasa shi a tsauni mai tsayi.

23 A ƙwanƙolin tsaunin Isra’ila zan dasa shi

Don ya fito da rassa, ya ba da ‘ya’ya,

Ya zama itacen al’ul na gaske.

Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa,

Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.

24 Dukan itatuwan jeji za su sani,

Ni Ubangiji nakan sa manyan itatuwa su zama ƙanana,

In sa ƙanana kuma su zama manya,

In sa ɗanyen itace ya bushe,

In sa busasshen itace kuma ya zama ɗanye, Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”

Categories
EZ

EZ 18

Hakkin Kowa

1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra’ila cewa,

‘Ubanni sun ci ‘ya’yan inabi masu tsami,

Hakoran ‘ya’ya kuwa sun mutu’?

3 “Ni Ubangiji Allah na ce, hakika, ba za a ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.

4 Ga shi, dukan rayuka nawa ne, da ran uban da na ɗan, duka nawa ne. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu.

5 “Ga irin mutumin da zai rayu, mutumin da yake adali, yana bin shari’a, yana kuma aikata abin da yake daidai,

6 idan ba ya cin abinci a ɗakin tsafi, bai bauta wa gumakan mutanen Isra’ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, ba yakan kwana da mace a lokacin hailarta ba,

7 wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa,

8 wanda ba ya ba da bashi da ruwa, ko tare da wani ƙari, wanda yake hana hannunsa yin mugunta, amma yana goyon bayan gaskiya tsakanin masu gardama,

9 wanda yake bin dokokina, yana kuma kiyaye ka’idodina da aminci, shi adali ne. Hakika zai rayu, ni Ubangiji na faɗa.

10 “Amma idan ya haifi ɗa wanda ya zama ɗan fashi, mai kisankai, yana yi wa ɗan’uwansa ɗaya daga cikin abubuwan nan, [ko shi kansa,

11 bai yi irin waɗannan abubuwa ba,] wato yana cin abinci a ɗakin tsafi, yana kwana da matar maƙwabcinsa,

12 yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama,

13 yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.

14 “Amma idan wannan mutum ya haifi ɗa wanda ya ga dukan laifofin da mahaifinsa ya yi, sa’an nan ya ji tsoro, bai kuwa yi haka ba,

15 bai ci abinci a ɗakin tsafi ba, bai bauta wa gumakan mutanen gidan Isra’ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba,

16 bai ci zalin kowa ba, bai karɓi jingina ba, bai yi ƙwace ba, amma yana ba mayunwaci abinci, yana ba huntu tufa,

17 yana hana hannunsa aikata mugunta, bai ba da bashi da ruwa ko wani ƙari ba, yana kiyaye ka’idodina, yana kuma bin dokokina, ba zai mutu saboda laifin mahaifinsa ba, amma zai rayu.

18 Amma mahaifinsa, da yake ya yi zalunci, ya yi wa ɗan’uwansa ƙwace ya aikata mugun abu a cikin mutanensa, zai mutu saboda muguntarsa.

19 “Za ku yi tambaya cewa, ‘Me ya sa ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba?’ Sa’ad da ɗan ya bi shari’a, ya yi abin da yake daidai, ya kiyaye dokokina sosai, lalle zai rayu.

20 Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.

Ayyukan Allah Daidai Ne

21 “Amma idan mugu ya bar dukan muguntarsa da ya aikata, ya kiyaye dokokina, ya bi shari’a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu, ba zai mutu ba.

22 Ba za a bi hakkin laifin da ya aikata ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi.

23 Ni Ubangiji Allah, na ce, ina jin daɗin mutuwar mugu ne? Ban fi so ya bar mugun halinsa ya rayu ba?

24 “Amma idan adali ya bar yin adalci, ya aikata mugunta, ya yi abubuwa masu banƙyama waɗanda mugu yake aikatawa, zai rayu? Ayyukansa na adalci waɗanda ya aikata, ba za a tuna da su ba, faufau. Zai mutu saboda rashin amincin da ya yi da laifin da ya aikata.

25 “Amma kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ku ji ya ku mutanen Isra’ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?

26 Sa’ad da adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda muguntarsa.

27 Idan kuma mugu ya bar muguntarsa da yake yi, ya kuwa bi shari’a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu.

28 Domin ya yi tunani, ya bar laifofin da ya aikata, zai rayu, ba zai mutu ba.

29 Amma mutanen Isra’ila suna cewa hanyar Ubangiji ba daidai ba ce. Ya mutanen Isra’ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?

30 “Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra’ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka.

31 Ku rabu da laifofin da kuka yi mini, sa’an nan ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon hali. Don me za ku mutu, ya ku jama’ar Isra’ila?

32 Ni Ubangiji Allah na ce ba na murna da mutuwar kowa, saboda haka sai ku tuba domin ku rayu.”

Categories
EZ

EZ 19

Makoki a kan Hakiman Isra’ila

1 “Sai ka yi makoki domin hakiman Isra’ila,

2 Ka ce, ‘Mahaifiyarka zakanya ce a cikin zakoki,

Ta yi zamanta tare da ‘yan zakoki,

Ta yi renon kwiyakwiyanta.

3 Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,

Ya zama sagari,

Sai ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.

4 Da al’ummai suka ji labarinsa,

Sai suka kama shi cikin wushefensu,

Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa Masar.

5 Sa’ad da ta ga wanda ta sa zuciya a kansa ya tafi,

Sai ta ɗauki ɗaya kuma daga cikin kwiyakwiyanta,

Ta goye shi ya zama sagari.

6 Sai ya yi ta kai da kawowa a cikin zakoki,

Ya zama sagari,

Ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.

7 Ya lalatar da kagaransu,

Ya mai da biranensu kufai,

Ƙasar da waɗanda suke cikinta suka tsorata da jin rurinsa.

8 Sai al’ummai suka kafa masa tarko a kowane waje,

Sun kafa masa tarko,

Suka kama shi cikin wushefensu.

9 Suka sa masa ƙugiyoyi, sa’an nan suka sa shi cikin suru,

Suka kai shi wurin Sarkin Babila.

Suka sa shi a kurkuku don kada a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra’ila.’ ”

Busasshiyar Kurangar Inabi

10 “ ‘Mahaifiyarka tana kama da kurangar inabi,

Wadda aka dasa kusa da ruwa,

Ta ba da ‘ya’ya da rassa da yawa, saboda isasshen ruwa.

11 Rassanta masu ƙarfi sun zama sandunan masu mulki,

Ta yi tsayi zuwa sama duk da rassan,

Ana hangenta daga nesa.

12 Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi,

Aka jefar da ita ƙasa.

Iskar gabas ta busar da ita,

‘Ya’yanta suka kakkaɓe,

Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.

13 Yanzu na dasa ta a jeji, cikin busasshiyar ƙasa,

14 Wuta ta fito daga jikinta

Ta cinye rassanta da ‘ya’yanta,

Don haka ba wani reshe mai ƙarfi da ya ragu, wanda zai zama sandan mulki.

Wannan makoki ne, ya kuwa tabbata makoki.’ ”

Categories
EZ

EZ 20

Yadda Ubangiji ya Bi da Isra’ila

1 A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta bakwai, sai waɗansu dattawan Isra’ila suka zo don su yi roƙo a wurin Ubangiji. Suka zauna a gabana.

2 Ubangiji kuwa ya yi magana da ni ya ce,

3 “Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra’ila cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce kun zo ku yi roƙo a wurina, amma hakika, ba na roƙuwa a gare ku.’

4 “Za ka shara’anta su? Ɗan mutum, shara’anta su. To, sai ka sanar da su abubuwa masu banƙyama waɗanda kakanninsu suka yi.

5 Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra’ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,

6 a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da take da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka.

7 Sai na ce musu, ‘Bari kowane ɗayanku ya yi watsi da abubuwan banƙyama da kuke jin daɗinsu, kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masarawa, gama ni ne Ubangiji Allahnku.’

8 Amma suka tayar mini, ba su ji ni ba, ba su yi watsi da abubuwan banƙyama da suke jin daɗinsu ba, ba su rabu da gumakan Masarawa ba. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar musu da fushina a ƙasar Masar.

9 Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana cikin sauran al’umma inda mutanen Isra’ila suke zaune, gama na sanar da kaina ga mutanen Isra’ila, a gaban sauran al’umma kuma, sa’ad da na fito da mutanen Isra’ila, daga ƙasar Masar.

10 “Sai na fisshe su daga ƙasar Masar, na kawo su cikin jeji.

11 Na ba su dokokina da ka’idodina, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu.

12 Na kuma ba su ranar Asabar don ta zama alama tsakanina da su, don kuma su sani ni ne Ubangiji wanda yake tsarkake su.

13 Amma mutanen Isra’ila suka tayar mini a cikin jeji, ba su bi dokokina da ka’idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka ɓata ranar Asabar ƙwarai. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu.

14 Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana a cikin sauran al’umma waɗanda a kan idonsu na fisshe su.

15 Na kuma rantse musu a cikin jeji, cewa ba zan kai su ƙasar da na ba su ba, ƙasar da take cike da yalwar albarka, wato ƙasar da take mafi albarka duka,

16 domin sun ƙi su bi ka’idodina da dokokina. Suka ɓata ranar Asabar ɗina, gama zuciyarsu ta fi so ta bauta wa gumaka.

17 “Duk da haka na yafe musu, ban hallaka su ba, ban kuma shafe su a jeji ba.

18 Sai na ce wa ‘ya’yansu a jeji, ‘Kada ku bi dokokin ubanninku, ko kuwa ku kiyaye ka’idodinsu, kada kuma ku ɓata kanku da gumakansu.

19 Ni ne Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dokokina da ka’idodina sosai.

20 Ku kiyaye ranar Asabar ɗina domin ta zama alama tsakanina da ku, domin kuma ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’

21 “Amma ‘ya’yansu suka tayar mini, ba su kiyaye dokokina da ka’idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka kuma ɓata ranar Asabar ɗina. Sai na yi tunani zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu a jeji.

22 Amma na yi haƙuri saboda sunana, domin kada a saɓi sunana a gaban sauran al’umma waɗanda suka gani na fito da mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar.

23 Na rantse musu a jeji, cewa zan warwatsar da su cikin sauran al’umma, da sauran ƙasashe

24 domin ba su kiyaye ka’idodina da dokokina ba, suka ɓata ranar Asabar ɗina, suka bauta wa gumakan kakanninsu.

25 Sai kuma na ba su dokoki da ƙa’idodi marasa amfani, waɗanda ba za su rayu ta wurinsu ba.

26 Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa ‘ya’yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.

27 “Domin haka, ya ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah, na ce kakanninku sun saɓe ni da ba su amince da ni ba.

28 Gama sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa’ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’

29 Sai na ce, ‘Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’ Domin haka aka kira sunan wurin Bama, wato tudu.

30 Domin haka ka ce wa mutanen Isra’ila, ‘Ni Ubangiji Allah na ce za ku ƙazantar da kanku kamar yadda kakanninku suka yi? Za ku bi abubuwan da suka yi na banƙyama?

31 Sa’ad da kuke miƙa hadaya, kuna miƙa ‘ya’yanku hadaya ta ƙonawa, kuna ƙazantar da kanku ta wurin gumakanku har wa yau, to, za ku iya tambayata, ya ku mutanen Isra’ila? Ni Ubangiji Allah ba na tambayuwa gare ku.

32 Tunanin nan da kuke yi a zuciyarku, cewa kuna so ku zama kamar sauran al’umma da kabilan ƙasashe, ku bauta wa itace da dutse, ba zai taɓa faruwa ba.’

33 “Hakika, ni Ubangiji Allah na ce, zan sarauce ku ƙarfi da yaji, da fushi,

34 da ƙarfi da yaji da fushi kuma, zan fito da ku daga cikin mutane, in tattaro ku daga sauran ƙasashe inda aka warwatsa ku.

35 Zan kawo ku cikin ruƙuƙin jama’a, in yi muku shari’a fuska da fuska.

36 Kamar yadda na yi wa kakanninku shari’a a jejin ƙasar Masar, haka kuma zan yi muku shari’a, ni Ubangiji Allah na faɗa.

37 “Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sanda, in ƙulla alkawarina da ku.

38 Zan fitar da ‘yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.

39 “Ya ku, mutanen Isra’ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da yake ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.

40 “Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra’ila, dukan mutanen Isra’ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau.

41 Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa’ad da na fisshe ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku. Zan nuna tsarkina a cikinku a idon sauran al’umma.

42 Za ku sani ni ne Ubangiji sa’ad da na kawo ku ƙasar Isra’ila, ƙasar da na rantse zan ba kakanninku.

43 A nan za ku tuna da ayyukanku da dukan abubuwa da kuka ɓata kanku da su. Za ku ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata.

44 Za ku sani ni ne Ubangiji sa’ad da na yi muku haka saboda sunana, ba saboda mugayen ayyukanku ba, ya ku mutanen Isra’ila. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Annabci a kan Kudu

45 Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

46 “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen kudu ka ja kunnen mutanen kudu, ka kuma yi annabci gāba da kurmin ƙasar Negeb.

47 Ka ce wa kurmin Negeb, ‘Ka ji maganar Ubangiji, gama Ubangiji Allah ya ce zai kunna wuta a cikinka, za ta kuwa cinye kowane ɗanyen itace, da kowane busasshen itacen da take cikinka. Ba za a kashe harshen wutar ba. Harshen wutar zai babbake kowace fuska daga kudu zuwa arewa.

48 Dukan masu rai za su sani ni Ubangiji ne na kunna wutar, ba wanda zai kashe ta.”’

49 Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, suna cewa misalai kawai, nake yi.”