Categories
EZ

EZ 21

Takobin Ubangiji

1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ya ɗan mutum, ka fuskanci Urushalima, ka yi magana gāba da masujadanta, ka kuma yi annabci a kan ƙasar Isra’ila.

3 Ka faɗa wa ƙasar Isra’ila, ka ce, ni Ubangiji na ce ina gāba da ita. Zan zare takobina daga cikin kubensa, in karkashe adalai da mugaye daga cikinta.

4 Da yake zan karkashe adalai da mugaye daga cikinta, domin haka takobina zai fito daga cikin kubensa, ya karkashe dukan mutane daga Negeb wajen kudu, har zuwa arewa.

5 Dukan mutane kuwa za su sani, ni Ubangiji, na zare takobina daga cikin kubensa, ba kuwa zan sāke mayar da shi a kubensa ba.

6 “Domin haka, ya kai ɗan mutum, sai ka yi nishi, da ajiyar zuciya, da baƙin ciki mai zafi a gabansu.

7 Idan sun tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Saboda labarin abin da yake zuwa. Sa’ad da ya zo, kowace zuciya za ta narke, hannuwa duka za su yi suwu, kowane ruhu kuma zai suma, gwiwoyi duka kuwa za su rasa ƙarfi kamar ruwa. Ga shi, abin yana zuwa, zai tabbata,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”

8 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

9 “Ya ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce ni Ubangiji na ce,

‘Takobi, takobi wasasshe,

Kuma gogagge!

10 An wasa shi domin kisa,

An goge shi don ya yi walwal kamar walƙiya!’

Ba wanda zai iya tsai da shi, domin kun ƙi karɓar shawara.

11 An ba da takobin a goge shi domin a riƙe. An wasa shi, an kuma goge shi domin a ba mai kashewa.

12 Ka yi kuka, ka yi ihu, ya ɗan mutum, gama takobin yana gāba da jama’ata da dukan shugabannin Isra’ila. An ba da shugabanni da jama’ata ga takobi, sai ka buga ƙirjinka da baƙin ciki.

13 Gama ba don jarraba shi ba ne, sai me kuma idan ka raina sandan? Ni Ubangiji na faɗa.

14 “Domin haka, ya kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka tafa hannuwanka, ka kaɗa takobi sau biyu, har sau uku. Takobin zai kashe waɗanda za a kashe. Takobi ne na yin kashe-kashe mai yawa. Zai kewaye su.

15 Zai sa zukatansu su narke, da yawa kuma su fāɗi a ƙofofinsu. Na ba da takobi mai walƙiya. An yi shi kamar walƙiya, an wasa shi don kashe-kashe.

16 Ka yi sara dama da hagu, duk inda ka juya.

17 Ni kuma zan tafa hannuwana, zan aukar da fushina, ni Ubangiji na faɗa.”

Takobin Sarkin Babila

18 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

19 “Ya ɗan mutum, ka nuna hanya biyu inda takobin Sarkin Babila zai bi. Dukansu biyu za su fito daga ƙasa ɗaya. Ka kafa shaidar hanya a kan magamin hanya zuwa birni.

20 Ka nuna wa takobin hanya zuwa Rabba ta Ammonawa, da hanya zuwa Yahuza, da Urushalima, birni mai garu.

21 Gama Sarkin Babila yana tsaye a mararrabar hanya, inda hanyar ta rabu biyu, yana yin dūbā, yana girgiza kibau, yana neman shawara wurin kan gida, yana dūbān hanta.

22 A hannun damansa, dūbā yana nuna abin da zai sami Urushalima. Zai kafa mata dundurusai, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta da dundurusai, a gina mahaurai, a kuma gina hasumiyar yaƙi.

23 Amma a gare su dūbān nan ba gaskiya ba ce, gama sun riga sun yi rantsuwa mai nauyi, amma zai tuna musu da laifinsu, don a kama su.

24 Domin haka ni Ubangiji Allah na ce, tun da yake kun sa a tuna da laifofinku, an kuma tone su, laifofinku kuma sun bayyana cikin ayyukanku, kun tonu, to, za a kama ku a cikinsu.

25 “Kai kuma ƙazantaccen mugu, yariman Isra’ila, ranarka ta zo, lokacin hukuncinka ya yi.

26 Ni Ubangiji Allah na ce, ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma.

27 Halaka, halaka, zan hallakar, ba za a bar ko alama ba, sai mai shi ya zo, shi ne zan ba shi.”

Hukunci a kan Ammonawa

28 “Kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce, ga abin da Ubangiji Allah ya ce a kan Ammonawa, da a kan zarginsu.

‘An zare takobi don kashe-kashe,

An goge shi don ya yi sheƙi kamar walƙiya!

29 Ka faɗa wa Ammonawa, cewa wahayin da suke gani ƙarya ne annabcin da suke yi kuma ƙarya ne. Su mugaye ne, ranar hukuncinsu tana zuwa. Za a sare wuyansu da takobi.

30 “‘Ka mai da takobinka cikin kubensa. Zan hukunta ka a ƙasarka inda aka haife ka.

31 Zan zubo maka da fushina, in hura maka wutar fushina. Zan bashe ka a hannun mugaye, gwanayen hallakarwa.

32 Za ka zama itacen wuta, za a zubar da jininka a tsakiyar ƙasar. Ba za a ƙara tunawa da kai ba, ni Ubangiji na faɗa.”’

Categories
EZ

EZ 22

Laifofin Urushalima

1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Kai ɗan mutum, za ka shara’anta? Za ka shara’anta birni mai kisankai? To, sai ka faɗa masa dukan ayyukansa na banƙyama.

3 Sai ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce, birnin da yake kisankai, yana kuma bauta wa gumaka don ya ƙazantar da kansa, lokacinsa zai yi!

4 Ka yi laifi saboda ka zubar da jini, ka ƙazantar da kanka da gumakan da ka yi. Saboda haka ka matso da lokacinka kusa, ƙayyadaddun shekarunka sun cika. Domin haka na maishe ka abin zargi ga sauran al’umma, da abin ba’a ga dukan ƙasashe.

5 Waɗanda suke kusa, da waɗanda suke nesa za su yi maka ba’a, gama kai shahararren mugu ne, cike da hargitsi.

6 Ga shi, kowane shugaban Isra’ila da yake cikinka ya himmantu ga zub da jini bisa ga ikonsa.

7 A cikinka ana raina mahaifi da mahaifiya, ana kuma tsananta wa baƙo, ana cin zalin marayu, da gwauruwa, wato wadda mijinta ya mutu.

8 Ka raina tsarkakan abubuwa, ka kuma ɓata ranar Asabar ɗina.

9 Akwai mutane a cikinka waɗanda suke haddasa rikici don su zubar da jini, akwai kuma mutanen da suke cin abinci a matsafai, akwai mutanen da suke aikata lalata.

10 A cikinka, mutane suna kwana da matan mahaifansu, waɗansu suna kwana da mata a lokacin hailarsu.

11 Wani yakan yi lalata da matar maƙwabcinsa, wani kuma ya kwana da matar ɗansa, wani ya kwana da ‘yar’uwarsa, wato ‘yar mahaifinsa.

12 A cikinka mutane suka karɓi toshi don su zub da jini. Kana ba da rance da ruwa da ƙari, kana kuma cin riba a kan maƙwabcinka saboda cutar da kake yi masa, ka kuwa manta da ni, ni Ubangiji na faɗa.

13 “‘Ga shi, na tafa hannuna saboda ƙazamar riba da ka ci, da jinin da ka zubar.

14 Zuciyarka za ta iya ɗaurewa, hannuwanka kuma za su ƙarfafa a ranar da zan gamu da kai? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.

15 Zan watsar da kai cikin al’ummai, in warwatsa ka cikin ƙasashe, zan kawo ƙarshen mugayen ayyukanka.

16 Za a ƙasƙantar da kai a gaban sauran al’umma, sa’an nan za ka sani ni ne Ubangiji.”’

Tanderun Tsarkakewa

17 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

18 “Ɗan mutum, mutanen Isra’ila sun zama kamar ƙwan maƙera a gare ni. Dukansu sun zama kamar tagulla, da kuza, da baƙin ƙarfe, da darma, a tanderu, sun zama ƙwan maƙera na azurfa.

19 Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da yake dukanku kun zama ƙwan maƙera zan tattara dukanku a Urushalima.

20 Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da darma, da kuza a cikin tanderu, su hura wuta a kansu, don su narkar da su, haka zan tattara ku da zafin fushina in narkar da ku.

21 Zan tattaro ku, in hura muku wutar hasalata, za ku narke a cikinta.

22 Kamar yadda azurfa takan narke a cikin tanderu, haka kuma za ku narke, za ku sani ni, Ubangiji ne, na zubo muku da zafin fushina.”

Laifofin Shugabannin Isra’ila

23 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

24 “Ɗan mutum, ka ce mata, ‘Ke ƙasa ce marar tsarki, wadda ba a yi ruwan sama a kanki ba a lokacin da na yi fushi.’

25 Annabawanta suna kama da zakoki masu ruri waɗanda suke yayyage ganimar da suka samu. Sun kashe mutane, sun ƙwace dukiya da abubuwa masu daraja. Sun sa mata da yawa sun rasa mazansu.

26 Firistocinta sun karya dokokina, sun ƙazantar da tsarkakan abubuwana. Ba su bambanta tsakanin abin da yake mai tsarki da marar tsarki ba, ba su kuma koyar da bambancin da yake tsakanin halal da haram ba. Ba su kiyaye ranar Asabar ɗina ba, da haka suke saɓon sunana.

27 Shugabanninta sun zama kamar kyarketai masu yayyage ganima. Suna yin kisankai don su sami ƙazamar riba.

28 Annabawanta sun yi musu shafe da farar ƙasa, wato wahayan da suke gani, da duban da suke yi musu ƙarya ne. Suna cewa Ubangiji ne ya faɗa, alhali kuwa ni Ubangiji ban faɗa musu kome ba.

29 Mutanen ƙasar sun yi zalunci, sun yi fashi, sun zalunci matalauta da masu fatara. Ba su yi wa baƙo adalci ba, sai cuta.

30 Sai na nemi mutum a cikinsu wanda zai gina garun ya tsaya a hauren garun a gabana, domin kada in hallaka ƙasar, amma ban sami kowa ba.

31 Saboda haka na kwarara musu fushina, na ƙone su da wutar hasalata, na ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 23

‘Yan Mata Biyu

1 Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, akwai waɗansu mata biyu, uwarsu ɗaya.

3 Sun yi karuwanci a Masar, a lokacin ‘yan matancinsu, aka rungumi mamansu da ƙirjinsu.

4 Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi ‘ya’ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.

5 Ohola ta yi karuwanci sa’ad da take zamana. Ta yi ta kai da kawowa a tsakanin kwartayenta, Assuriyawa,

6 waɗanda suke saye da shunayya, su masu mulki da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha’awa, suna bisa kan dawakansu.

7 Ta yi karuwanci da su, dukan waɗanda suke ƙusoshin Assuriya, ta kuma ƙazantar da kanta tsakanin gumakan da ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

8 Ba ta bar karuwancinta ba, wanda ta yi tun tana a Masar, gama a lokacin ‘yan matancinta mutane sun kwana da ita, sun rungumi ƙirjinta, suka biya kwaɗayinsu a kanta.

9 Domin haka na bashe ta a hannun kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

10 Waɗannan suka tsiraita ta, suka kama ‘ya’yanta mata da maza, suka kashe ta da takobi. Sai ta zama abin karin magana a wurin mata sa’ad da aka hukunta ta.

11 “Ƙanwarta kuwa ta ga wannan, amma duk da haka ta fi ta lalacewa saboda kai da kawowa na karuwanci, wanda ya fi na ‘yar uwarta muni.

12 Ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, a wurin masu mulki da manyan sojoji waɗanda suke saye da kayan yaƙi, suna bisa kan dawakai, dukansu samari ne masu bansha’awa.

13 Na ga ta ƙazantu. Dukansu biyu suka bi hanya ɗaya.

14 “Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a jikin bango, siffofin Kaldiyawa ne aka zāna da jan launi!

15 Sun sha ɗamara a gindinsu, da rawuna a kansu suna kaɗawa filfil. Dukansu suna kama da jarumawa. Su siffofi suna kama da mutanen Babila na ƙasar Kaldiya.

16 Sa’ad da ta gan su, sai ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. Ta aiki jakadu a wurinsu, wato a Kaldiya.

17 Sai Babilawa suka zo wurinta, a gadonta na nishaɗi, suka ƙazantar da ita ta wurin kwana da ita. Bayan da sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su.

18 Ta yi ta karuwancinta a fili, ta bayyana tsiraicinta. Sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita kamar yadda na rabu da ‘yar’uwarta.

19 Duk da haka ta yi ta ƙara karuwancinta, tana tunawa da kwanakin ‘yan matancinta, a lokacin da ta yi karuwancinta a ƙasar Masar.

20 Ta yi ta kai da kawowa tsakanin kwartayenta waɗanda al’auransu kamar na jakai ne, maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne.

21 Haka kika yi ƙawar zucin lalatar da kika yi a lokacin ‘yan matancinki, sa’ad da Masarawa suka rungumi mamanki na ƙuruciya.”

Hukuncin Allah a kan ‘Yan Matan nan Biyu

22 “Domin haka, ya Oholiba, ni, Ubangiji Allah na ce zan kuta kwartayenki su yi gāba da ke, waɗanda kika ji ƙyamarsu, kika rabu da su. Daga kowane sashi zan sa su zo su yi gāba da ke.

23 Babilawa da dukan Kaldiyawa, da Fekod, da Showa, da Kowa, da dukan Assuriyawa tare da su, wato samari masu bansha’awa. Dukansu masu mulki ne, da shugabanni, da jarumawa, da shahararru, dukansu suna kan dawakai.

24 Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari’a a hannunsu, za su kuwa shara’anta ki da irin shari’arsu.

25 Zan yi fushi da ke don su wulakanta ki. Za su datse hancinki da kunnuwanki. Waɗanda suka rage miki za a kashe su da takobi. Za su kama ‘ya’yanki mata da maza, waɗanda suka rage miki kuwa, za a ƙone su da wuta.

26 Za su tsiraita ki, su kuma kwashe lu’ulu’anki.

27 Zan ƙarasa lalatarki da karuwancinki da kika kawo daga ƙasar Masar, don kada ki ƙara ɗaga idonki ki dubi Masarawa, ko ki ƙara tunawa da su.

28 “Gama ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, zan danƙa ki a hannun waɗanda kike ƙinsu, waɗanda kika ƙi su, kika kuwa rabu da su.

29 Za su nuna miki ƙiyayya, za su ƙwace dukiyarki su bar ki tsirara tik, za su kuma buɗe tsiraicin karuwancinki.

30 Lalatarki da karuwancinki su suka jawo miki wannan, gama kin yi karuwanci da sauran al’umma kika ƙazantar da kanki da gumakansu.

31 Kin bi halin ‘yar’uwarki, domin haka zan hukunta ki kamar yadda na hukunta ta.’ ”

32 Ubangiji Allah ya ce,

“Za ki sha babban hukuncin da ‘yar’uwarki ta sha,

Za a yi miki dariya da ba’a,

Gama hukuncin yana da tsanani.

33 Za ki sha wahala da baƙin ciki,

Hukunci na bantsoro da lalacewa,

Shi ne irin hukuncin da aka yi wa ‘yarki Samariya.

34 Ƙoƙon da kika sha hukunci daga ciki, za ki lashe shi,

Ki tattaune sakainunsa,

Ki tsattsage nononki,

Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

35 Ubangiji ya ce, “Da yake kin manta da ni, kin ba ni baya. Don haka ki ɗauki hakkin lalatarki da karuwancinki.”

36 Sai Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ko ka shara’anta wa Ohola da Oholiba? To, sai ka faɗa musu mugayen ayyukansu.

37 Gama sun yi zina da kisankai, sun bauta wa gumakansu, har ma sun miƙa musu ‘ya’yansu maza da suka haifa mini, su zama abincinsu.

38 Ga kuma abin da suka yi mini, sun ƙazantar da Haikalina a ranar, sun kuma ɓata ranar Asabar ɗina.

39 Gama a ranar da suka kashe ‘ya’yansu, suka miƙa su hadaya ga gumakansu, sai suka shiga Haikalina suka ƙazantar da shi. Abin da suka yi ke nan cikin Haidalina.

40 “Kun aiki manzo wurin mutanen da suke nesa su kuwa suka zo. Saboda su kun yi wanka, kun sa kwalli, kun ci ado.

41 Kun zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabansa. A kansa kuka ajiye turarena da maina.

42 A wurinta akwai hayaniyar taron mutane marasa kula, sai kuma aka kawo mutane irinsu, mashaya daga jeji. Suka sa mundaye a hannuwan matan, suka kuma sa kambi masu kyau a kawunansu.

43 Sai na yi magana a kanta, ita wadda ta ƙare ƙarfinta da yin zina, yanzu za su yi zina da ita da ta zama haka?

44 Suka shiga wurinta kamar yadda akan shiga wurin karuwa. Haka kuwa suka shiga wurin Ohola da Oholiba don su yi zina da su.

45 Amma adalai za su yanka musu hukunci irin wanda akan yi wa mata mazinata, da mata masu kisankai, gama su mazinata ne masu kisankai.

46 “Gama ni Ubangiji Allah na ce, a kawo rundunar soja ta yi yaƙi da su, don su firgita su, su washe su.

47 Rundunar za ta jajjefe su da duwatsu, ta sassare su da takuba. Za ta kuma kashe ‘ya’yansu mata da maza, ta ƙone gidajensu.

48 Ta haka zan kawo ƙarshen lalata a cikin ƙasar domin dukan mata su sami faɗaka, kada su yi lalata kamar yadda kuka yi.

49 Za a hukunta ku saboda lalatarku, za ku sha hukunci saboda zunubin bautar gumaka, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.”

Categories
EZ

EZ 24

Misali a kan Tukunyar da Take Tafasa

1 A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka rubuta sunan wannan rana. Ranar ke nan da Sarkin Babila ya kewaye Urushalima da yaƙi.

3 Ka yi wa ‘yan tawayen nan magana da misali, ka faɗa musu cewa, ni Ubangiji na ce,

‘Ka ɗora tukunya, ka ɗora ta a wuta,

Ka cika ta da ruwa.

4 Ka zuba gunduwoyin nama a ciki,

Dukan gunduwoyi masu kyau, wato cinya da kafaɗa,

Ka cika ta da tantakwashi.

5 Ka kama mafi kyau daga cikin garken,

Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa,

Ka tafasa gunduwoyin,

Ka kuma tafasa tantakwashin.’

6 “Ni Ubangiji Allah na ce,

‘Domin haka kaiton birnin nan mai zubar da jini,

Da tukunya wadda take da tsatsa,

Wadda tsatsarta ba ta fita cikinta ba!

Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa,

Kada ka yi zaɓe.

7 Gama jinin da ta zubar yana tsakiyarta,

Ta zubar da shi a kan dutse,

Ba ta zubar da shi a ƙasa inda za ta rufe shi da ƙura ba.

8 Don a tsokani fushina har in yi sakayya,

Na zuba jinin da ta zubar a kan dutse,

Don kada a rufe shi.’

9 “Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce,

‘Kaitonka, ya birni, mai zubar da jini!

Ni kuma zan tsiba itace da yawa.

10 Ka tula gumagumai, ka kunna wuta,

Ka tafasa naman sosai,

Ka zuba kayan yaji a ciki,

Ka bar ƙasusuwan su ƙone.

11 Ka ɗora tukunyar da ba kome cikinta a bisa garwashi

Domin ta yi zafi, tagullarta ta yi ja wur,

Domin dauɗarta ta narke a ciki,

Tsatsarta kuma ta ƙone.

12 Ta gajiyar da ni a banza,

Wutar ba ta fitar da yawan tsatsarta ba.

13 Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki.

Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba,

To, ba za ki ƙara yin tsabta ba,

Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’

14 Ni, Ubangiji na faɗa, zai tabbata gama zan aikata, ba zan fasa ba, ba kuwa zan ƙyale ba, ba kuma zan bari ba. Zan hukunta ki saboda hanyoyinki da ayyukanki, ni Ubangiji Allah na faɗa ”

Rasuwar Matar Ezekiyel

15 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

16 “Ya ɗan mutum, ga shi, ina gab da ɗauke maka ƙaunatacciyarka farat ɗaya, amma fa, kada ka yi makoki, ko kuka, ko ka zubar da hawaye.

17 Ka yi ajiyar zuciya a hankali, kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka, ka sa takalmanka, kada ka ja amawali, kada kuma ka ci abincin masu makoki.”

18 Sai na yi magana da mutane da safe, da maraice kuwa matata ta rasu. Kashegari da safe, sai na yi kamar yadda aka umarce ni.

19 Mutane kuwa suka tambaye ni dalilin da ya sa nake yin haka.

20 Sai na ce musu, “Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

21 in faɗa wa mutanen Isra’ila, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Zan ƙazantar da Haikalina, abin fariyarku, da abin da idanunku suke jin daɗin ganinsa, da abin faranta zuciyarku. ‘Ya’yanku maza waɗanda kuka bari a baya, za a kashe su da takobi.

22 Za ku kuwa yi kamar yadda na yi, wato ba za ku ja amawali ba, ba kuwa za ku ci abincin masu makoki ba.

23 Za ku naɗa rawunanku, ku sa takalmanku, ba za ku kuma yi makoki ko kuka ba, amma za ku lalace cikin zunubanku. Za ku yi ta nishi.

24 Da haka Ezekiyel zai zama muku alama. Za ku yi kamar yadda ya yi duka. Sa’ad da wannan ya faru, za ku sani nine Ubangiji Allah.’

25 “Kai ɗan mutum, a ranar da zan ɗauke musu madogararsu, da murnarsu, da darajarsu, da abin da idanunsu suka ji daɗin gani, da abin da yake faranta zuciyarsu, da ‘ya’yansu mata da maza,

26 a wannan rana wanda ya tsere zai kawo maka labarin.

27 A ranar bakinka zai buɗe, za ka yi magana da wanda ya tsere, ba kuma za ka zama bebe ba. Da haka za ka zama alama gare su, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

Categories
EZ

EZ 25

Annabci a kan Ammonawa

1 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa, ka yi annabci a kansu.

3 Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra’ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala,

4 domin haka zan bashe ku abin mallaka ga mutanen gabas. Za su kafa alfarwansu a cikinku, su zauna tare da ku. Za su ci amfanin gonakinku, su sha madararku.

5 Zan mai da Rabba makiyayar raƙuma, in mai da biranen Ammonawa garken awaki da tumaki. Sa’an nan ku sani ni ne Ubangiji Allah.”

6 Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra’ila,

7 domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”

Annabci a kan Mowab

8 Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al’ummai,

9 saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab daga garuruwan da suke kan iyaka, waɗanda su ne darajarta, wato Bet-yeshimot, da Ba’al-meyon, da Kiriyatayim.

10 Zan bashe ta duk da Ammonawa su zama abin mallakar mutanen gabas, don kada um’ƙara tunawa da su a cikin al’ummai.

11 Zan hukunta Mowab, sa’an nan za ta sani ni ne Ubangiji.”

Annabci a kan Edom

12 Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Edom ta ɗaukar wa kanta fansa a kan mutanen Yahuza, ta yi babban laifi da ta ɗaukar wa kanta fansa,

13 domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Edom. Zan kashe mutanenta da dabbobinta, zan maishe ta kufai. Za a kashe su da takobi, tun daga Teman har zuwa Dedan.

14 Mutanen Isra’la za su ɗaukar mini fansa a kan Edom. Za su aukar da fushina da hasalata a kan Edom, sa’an nan Edom za ta san sakayyata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Annabci a kan Filistiyawa

15 Ubangiji Allah ya ce, “Tun da yake Filistiyawa sun yi sakayya, sun ɗauki fansa da muguwar zuciya da ƙiyayya marar ƙarewa, don su hallakar,

16 domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Filistiyawa. Zan kashe Keretiyawa, in hallaka sauran mazaunan gāɓar teku.

17 Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.”

Categories
EZ

EZ 26

Annabci a kan Taya

1 A rana ta fari ga watan, a shekara ta goma sha ɗaya, sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

2 “Ɗan mutum, da yake Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Madalla, Urushalima ta rushe, ƙofa ta buɗu, yanzu zan wadata da yake ta zama kufai,’

3 domin haka ni, Ubangiji Allah na ce, ‘Ina gāba da ke, ke Taya, zan kawo al’ummai da yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.

4 Za su hallaka garun Taya, su rurrushe hasumiyarta. Zan ƙan’kare ƙasarta, in maishe ta fā.

5 Za ta zama wurin shanya taruna a tsakiyar teku. Za ta kuma zama ganima ga sauran al’umma. Ni Ubangiji na faɗa.

6 Ya’yanta mata waɗanda suke zaune a filin kasar za a kashe su da takobi, sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”

7 Gama Ubangiji Allah ya ce, “Zan kawo wa Taya Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sarkin sarakuna, daga arewa. Zai zo da dawakai da karusai, da sojojin dawakai, da babbar rundunar sojoji.

8 Zai kashe ya’yanki mata waɗanda suke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa’an nan zai rufe ki da garkuwoyi.

9 Zai rushe garunki da dundurusai, ya rushe hasumiyarki da gatura.

10 Saboda yawan dawakansa, ƙurar da za su tayar za ta rufe ki. Garunki kuma zai girgiza saboda motsin sojojin doki, da na ƙafafu kamar na keke, da na karusai sa’ad da ya shiga ƙofofinki, kamar yadda akan shiga birnin da garunsa ya rushe.

11 Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki, zai kashe mutanenki da takobi. Manyan ginshiƙanki za su rushe.

12 Za su washe dukiyarki da kayan cinikinki. Za su kuma rurrushe garunki da kyawawan gidajenki. Za su kwashe duwatsu, da katakai, da tarkace, su zubar a cikin teku.

13 Zan sa a daina raira waƙoƙi da kaɗa garayu.

14 Zan maishe ki fā, wato wurin shanya taruna. Ba za a sāke gina ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

15 Ubangiji Allah ya ce wa Taya, “Sa’ad da kika fāɗi, ƙasashen da suke a gāɓar teku za su girgiza saboda amon fāɗuwarki, da nishin waɗanda ake yi wa rauni, da kashe-kashen da aka yi a cikinki.

16 Sa’an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci. Za su razana saboda abin da ya same ki.

17 Za su yi makoki saboda ke, su ce,

‘Ke wadda ake zaune cikinki, kin bace daga tekuna,

Ya shahararren birni, wanda yake babba a bakin teku,

Ke da mazaunan da suke cikinki, kun sa mazaunan gāɓar teku su ji tsoro!

18 Yanzu tsibiran za su yi rawar jiki a ranar faɗuwarki.

Ji, tsibiran teku za su gigice saboda shuɗewarki.’ ”

19 Gama Ubangiji Allah ya ce, “Sa’ad da na maishe ki kufai kamar biranen da ba a zauna cikinsu ba, sa’ad da kuma na dulmuye ki cikin zurfin teku,

20 sa’an nan zan tura ki tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna a ƙarƙashin ƙasa inda ya zama kufai, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, don kada a zauna a cikinki, amma zan ƙawata ƙasar masu rai.

21 Zan sa ki yi mummunan ƙarshe, ba za ki ƙara kasancewa ba. Za a neme ki, amma ba za a same ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa!”

Categories
EZ

EZ 27

Makoki a kan Taya

1 Sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ya kai ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.

3 Ka ce mata, ita wadda take zaune a mashigin teku, wadda take kuma kasuwar mutanen da suke bakin teku, ni Ubangiji Allah na ce,

‘Ke Taya, kin ce ke kyakkyawa ce cikakkiya!

4 Teku ta kewaye kan iyakarki,

Maginanki sun ƙawata ki.

5 Sun yi katakanki da itacen fir na Senir,

Sun sari itacen al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.

6 Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan.

Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim,

Sa’an nan sun manne masa hauren giwa.

7 An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar,

Don ya zama alama.

An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.

8 Mazaunan Sidon da Arwad su ne matuƙa,

Masu hikima, waɗanda suke cikinki, su ne jagora.

9 Dattawan Gebal da masu hikimarta suna tare da ke,

Suna tattoshe mahaɗan katakon jirginki,

Dukan matuƙan jiragen ruwa sun zo wurinki don kasuwanci.

10 “ ‘Mutanen Farisa, da na Lud, da na Fut suna cikin sojojinki don su yi miki yaƙi. Sun rataya garkuwoyi, da kwalkwali a cikinki. Sun samo miki daraja.

11 Mutanen Arward sun kewaye kan garunki. Mutanen Gamad kuma suna tsaron hasumiyarki. Sun rataya garkuwoyinsu a jikin garunki. Sun ƙawata ki ƙwarai.

12 “‘Tarshish abokiyar cinikinki ce, saboda yawan dukiyarki ta sayi kayan cinikinki da azurfa, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma.

13 Mutanen Yawan, da na Tubal, da na Meshek, abokan kasuwancinki, sun sayi kayan cinikinki da mutane da tasoshin tagulla.

14 Mutanen Togarma kuma sun sayi kayan cinikinki da dawakai da dawakan yaƙi, da alfadarai.

15 Mutane Dedan abokan cinikinki ne. Kasashe da yawa kuma na gaɓar teku sun zama kasuwarki. Sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.

16 Suriya kuma abokiyar cinikinki ce saboda yawan kayan cinikinki. Sun sayi kayan cinikinki, da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.

17 Mutanen Yahuza da na ƙasar Isra’ila abokan cinikinki ne. Sun sayi kayan cinikinki da alkama, da zaitun, da ‘ya’yan ɓaure, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.

18 Dimashƙu kuma ta zama abokiyar cinikinki saboda yawan kayan cinikinki da yawan dukiyarki. Ta sayi kayanki da ruwan inabin Helbon, da farin ulu.

19 Mutanen Dan, da Yawan, da ulu suka sayi kayanki, wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.

20 Dedan ta sayi kayanki da kayan dawakai.

21 Mutanen Arabiya da shugabannin Kedar sun sayi kayanki da ‘yan raguna, da raguna, da awaki.

22 ‘Yan kasuwar Sheba da Ra’ama sun sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri iri, da duwatsu masu daraja iri iri, da zinariya.

23 Garuruwan Haran, da Kanne, da Aidan, da fataken Sheba, da Asshur, da Kilmad sun yi ciniki da ke.

24 Sun sayar miki da tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da darduma masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tufka da kyau.

25 Jiragen ruwan Tarshish suna jigilar kayan cinikinki.

Don haka kin bunƙasa,

Kin ɗaukaka a tsakiyar tekuna.

26 “ ‘Matuƙanki sun kai ki cikin babbar teku,

Iskar gabas ta farfasa ki a tsakiyar teku.

27 Dukiyarki, da kayan cinikinki, da hajarki,

Da ma’aikatanki da masu ja miki gora,

Da masu tattoshe mahaɗan katakanki,

Da abokan cinikinki, da dukan sojojinki,

Da dukan taron jama’ar da take tare da ke,

Sun dulmuya cikin tsakiyar teku a ranar halakarki.

28 Saboda kukan masu ja miki gora, ƙasa ta girgiza.

29 “ ‘Daga cikin jiragen ruwansu dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su zo.

Matuƙan jiragen ruwa da masu jagora za su tsaya a gaɓar teku.

30 Za su yi kuka mai zafi dominki.

Za su yi hurwa, su yi birgima cikin toka.

31 Za su aske kansu saboda ke, su sa tufafin makoki.

Za su yi kuka mai zafi dominki.

32 A cikin makokinsu dominki, suna kuka, suna cewa,

Wa yake kama da Taya,

Ita wadda take shiru a tsakiyar teku?

33 Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,

Kin wadatar da al’ummai,

Kin arzuta sarakunan duniya da yawan dukiyarki da hajarki.

34 Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafa,

Hajarki da dukan ma’aikatan jirgin ruwanki sun nutse tare da ke.

35 Dukan mazaunan ƙasashen gāɓar teku

Sun gigice saboda masifar da ta auko miki.

Dukan sarakunansu sun tsorata ƙwarai,

Fuskokinsu sun yamutse.

36 ‘Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yi miki ba’a,

Saboda kin zama musu barazana.

Ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”

Categories
EZ

EZ 28

Annabci a kan Sarkin Taya

1 Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

2 “Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce,

‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma,

Har ka ce kai allah ne,

Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna,

To, kai mutum ne kawai, ba allah ba,

Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.

3 Lalle ka fi Daniyel hikima,

Ba asirin da yake ɓoye a gare ka.

4 Ta wurin hikimarka da ganewarka ka samo wa kanka dukiya,

Ka tattara zinariya da azurfa a baitulmalinka.

5 Saboda yawan hikimarka na yin kasuwanci, ka ƙara dukiyarka,

Sai dukiyarka ta sa zuciyarka ta cika da alfarma.’

6 “Saboda haka Ubangiji Allah ya ce,

‘Da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah,

7 Don haka zan tura baƙi a kanka,

Waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’umma.

Za su zare takubansu a kan kyakkyawar hikimarka,

Za su ɓara darajarka.

8 Za su jefar da kai cikin rami,

Za ka mutu kamar waɗanda suka mutu a tsakiyar teku.

9 Har yanzu za ka ce kai allah ne a gaban waɗanda suke ji maka rauni, Ko da yake kai mutum ne kawai, ba Allah ba?

10 Za ka yi mutuwa irin ta kare ta hannun baƙi,

Gama ni Ubangiji Allah na faɗa.’ ”

Makoki a kan Sarkin Taya

11 Ubangiji kuma ya yi magana da ni ya ce,

12 “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Sarkin Taya, ka ce Ubangiji Allah ya ce,

‘Kai cikakke ne, cike da hikima da jamali!

13 Kana cikin Aidan, gonar Allah.

An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja,

Tare da zinariya.

Kana da molo da abin busa.

A ranar da aka halicce ka

Suna nan cikakku.

14 Na keɓe ka ka zama mala’ika mai tsaro,

Kana bisa tsattsarkan dutsen Allah,

Ka yi tafiya a tsakiyar duwatsu na wuta.

15 Daga ranar da aka halicce ka ba ka da laifi cikin al’amuranka,

Sai ran da aka iske mugunta a cikinka.

16 A wurin yawan kasuwancinka,

Ka yi rikici da yawa har ka yi zunubi.

Don haka na jefar da kai daga dutsen Allah

Kamar ƙazantaccen abu.

Na hallaka ka daga tsakiyar duwatsu na wuta,

Kai mala’ikan tsaro.

17 Zuciyarka ta yi alfarma saboda kyanka,

Ka lalatar da hikimarka ta wurin nuna darajar kanka.

Na jefar da kai zuwa ƙasa,

Na tone asirinka a gaban sarakuna don su kallace ka.

18 Saboda yawan muguntarka da rashin gaskiyarka cikin kasuwanci,

Ka ƙazantar da tsarkakakkun wurarenka.

Don haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka,

Na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suka kallace ka.

19 Dukan waɗanda suka san ka a cikin al’ummai

Za su gigice saboda masifar da ta auko maka,

Za ka zama barazana ga al’ummai,

Ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.”’

Annabci a kan Sidon

20 Ubangiji ya yi magana da ni kuma, ya ce,

21 “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon, ka yi annabci a kanta.

22 Ka ce, Ubangiji Allah ya ce,

‘Duba, ina gāba da ke, ya Sidon,

Zan bayyana ikona a cikinki,

Za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na hukunta ta,

Na bayyana tsarkina a cikinta.

23 Zan aukar mata da annoba da jini a titunanta.

Waɗanda za a ji musu rauni da takobi

Za su fāɗi matattu a tsakiyarta.

Za a tasar mata a kowane waje.

Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”

Isra’ila Za ta Sami Albarka

24 “ ‘A kan mutanen Isra’ila kuwa, al’ummai da suke kewaye da su, waɗanda suka raina su, ba za su ƙara zamar musu kamar sarƙaƙƙiya da ƙaya ba. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.’

25 “Ubangiji Allah ya ce, ‘Sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga cikin sauran al’umma, inda na watsar da su, na kuma bayyana tsarkina a cikinsu a kan idon al’ummai, sa’an nan za su zauna a ƙarsarsu wadda na ba bawana Yakubu.

26 Za su zauna lafiya a cikinta, za su gina gidaje, su yi gonakin inabi. Za su zauna gonakin inabi. Za su zauna lafiya sa’ad da na hukunta maƙwabtansu waɗanda suka wulakanta su. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”

Categories
EZ

EZ 29

Annabci a kan Masar

1 A kan rana ta goma sha biyu ga watan goma a shekara ta goma, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Fir’auna Sarkin Masar, ka yi annabci gāba da shi da dukan Masar.

3 Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce,

‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir’auna Sarkin Masar,

Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna,

Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.

4 Zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka,

In kuma sa kifayen kogunanka su manne a ƙamborinka,

Zan jawo ka daga cikin tsakiyar kogunanka,

Da dukan kifayen kogunanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,

5 Zan yashe ka, kai da dukan kifayen kogunanka cikin jeji.

Za ka fāɗi a fili, ba kuwa wanda zai ɗauke ka, ya binne ka.

Zan sa ka zama abincin namomin jeji da tsuntsayen sararin sama.

6 A sa’an nan mazaunan Masar za su sani ni ne Ubangiji,

Domin sun zama wa mutanen

Isra’ila kamar sandan iwa.

7 Sa’ad da suka riƙe ka,

Sai ka karye ka tsattsaga hannuwansu.

Sa’ad da suka jingina da kai,

Sai ka karye, har ka sa kwankwasonsu ya firgiza.

8 Saboda haka, ni Ubangiji Allah na ce zan jawo takobi a kanka, in kashe mutanenka, duk da dabbobi.

9 Ƙasar Masar za ta zama kufai, marar amfani. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji.

“ ‘Domin ka ce, “Kogin Nilu nawa ne, ni na yi shi,”

10 ina gāba da kai da kogunanka. Zan mai da ƙasar Masar kufai sosai, marar amfani, tun daga Migdol zuwa Sewene har zuwa iyakar Habasha.

11 Mutum ko dabba ba zai ratsa ta cikinta ba. Za ta zama kufai har shekara arba’in.

12 Zan mai da ƙasar Masar kufai fiye da sauran ƙasashe. Biranenta za su zama kufai marar amfani, fiye da sauran birane har shekara arba’in. Zan kuma warwatsar da Masarawa a cikin sauran al’umma.’ ”

13 Ubangiji Allah ya ce, “Bayan shekara arba’in zan tattaro Masarawa daga cikin sauran al’umma inda aka warwatsar da su.

14 Zan komo da Masarawa, in maido su a ƙasar Fatros, ƙasarsu ta ainihi. Za su zama mulki marar ƙarfi.

15 Za su zama rarraunan mulki a cikin mulkoki. Ba za su ƙara ɗagawa sauran al’umma kai ba. Zan sa su zama kaɗan, har da ba za su ƙara mallakar waɗansu al’ummai ba.

16 Ba za su ƙara zama abin dogara ga mutanen Isra’ila ba, gama Isra’ilawa za su tuna da laifin suka yi, suka nemi taimakon Masarawa. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.”

17 A kan rana ta fari ga watan fari a shekara ta ashirin da bakwai, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

18 “Ɗan mutum, Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya sa sojojinsa su matsa wa Taya. Kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta yi kanta, amma duk da haka shi, tare da sojojinsa, bai sami hakkin wahalar da ya sha a Taya ba.”

19 Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Zan ba Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ƙasar Masar, zai kwashe dukiyarta, ya lalatar da ita, ya washe ta ganima. Za ta zama abin biyan sojojinsa.

20 Na ba shi ƙasar Masar saboda wahalar da ya sha, gama ni suka yi wa aiki. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

21 “A ranan nan zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda ya zama babban sarki, zan kuma buɗe bakinka a tsakiyarsu. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

Categories
EZ

EZ 30

Lalacewar Masar

1 Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce Ubangiji Allah ya ce maka ka yi kuka, kana cewa,

‘Kaito, kaito saboda wannan rana!’

3 Gama ranar ta gabato,

Ranar Ubangiji ta yi kusa,

Rana ce ta gizagizai,

Ranar halakar al’ummai.

4 Takobi zai fāɗa a kan Masar,

Azaba kuma za ta sami Habasha.

Za a kashe mutane a Masar,

Za a kwashe dukiyarta,

A rushe harsashin gininta.

5 “Yaƙi zai ci Habasha, da Fut, da Lud, da dukan Arabiya, da Libya, da mutanen ƙasar da suka haɗa kai da su.”

6 Ubangiji ya ce,

“Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi.

Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare.

Za a kashe su da takobi tun daga Migdol zuwa Sewene.

7 Za ta zama kufai fiye da sauran ƙasashe,

Biranenta kuma za su zama kufai, marar amfani, fiye da sauran birane.

8 Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji,

Sa’ad da na kunna wuta cikin Masar,

Na kuma kakkarya dukan masu taimakonta.

9 “A ranan nan manzanni masu sauri za su fito daga wurina a jiragen ruwa, su tsoratar da Habashawa, ba zato. Azaba za ta auko a kansu a ranar hallakar Masar. Ga ta nan, ta zo.”

10 Ubangiji Allah ya ce,

“Zan sa dukiyar Masar ta ƙare

Ta hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila,

11 Shi da mutanensa,

Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al’umma,

Za a kawo su don su hallakar da ƙasar.

Za su zare takubansu a kan Masar,

Su cika ƙasar da gawawwaki.

12 Zan busar da Kogin Nilu,

Zan kuma sayar da ƙasar ga mugaye.

Zan sa ƙasar ta lalace

Da dukan abin da yake cikinta,

Ta hannun baƙi,

Ni Ubangiji, na faɗa.”

13 Ubangiji Allah ya ce,

“Zan hallakar da gumaka

Da siffofi a Memfis.

Ba za a ƙara samun hakimi a ƙasar Masar ba,

Saboda haka zan aukar da tsoro a ƙasar Masar.

14 Zan sa Fatros ta zama kufai,

Zan kunna wa Zowan wuta,

Zan kuma shara’anta No.

15 Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,

Wato kagarar Masar,

Zan datse jama’ar No.

16 Zan kunna wa Masar wuta.

Felusiyum za ta sha azaba mai tsanani,

No kuwa za a tayar mata da hankali,

Za a rurrushe garukanta.

Za a tasar wa Memfis dukan yini.

17 Samarin Awen da na Fi-beset

Za a kashe su da takobi,

Matan kuma za su tafi bauta.

18 A Tafanes rana za ta yi duhu,

Sa’ad da na karya mulkin ƙasar Masar,

Ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare,

Za a rufe ta da gizagizai.

‘Ya’yanta mata kuwa za a kai su bauta.

19 Ta haka zan hukunta Masar,

Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

20 A kan rana ta bakwai ga watan fari, a shekara ta goma sha ɗaya, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

21 “Ɗan mutum, na karya hannun Fir’auna, Sarkin Masar, ga shi, ba za a ɗora hannun ba, don kada ya warke ya zama da ƙarfi yadda zai iya riƙon takobi.”

22 Ubangiji Allah kuma ya ce, “Ina gāba da Fir’auna, Sarkin Masar, zan karya hannuwansa duka biyu, da lafiyayyen da kuma wanda na riga na karya. Zan sa takobinsa ya faɗi daga hannunsa.

23 Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al’umma, in kuma warwatsa su a ƙasashen duniya.

24 Zan ƙarfafa hannun Sarkin Babila, in sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai yi nishi a gaban Sarkin Babila, kamar mutumin da aka yi wa raunin ajali.

25 Zan ƙarfafa hannuwan Sarkin Babila, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobina a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai miƙe shi a kan ƙasar Masar.

26 Zan watsar da Masarawa a cikin sauran al’umma, in warwatsa su a ƙasashen duniya. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji.”