Categories
EZ

EZ 31

Ƙaddarar da Za ta Sami Fir’auna da Jama’arsa

1 A kan rana ta fari ga watan uku a shekara ta goma sha ɗaya, Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka ce wa Fir’auna, Sarkin Masar, da jama’arsa.

‘Da wa za a kamanta girmanka?

3 Kana kama da Assuriya mai kama da itacen al’ul a Lebanon,

Mai rassa masu kyau da inuwar kurmi,

Mai tsayi ainun, kansa ya kai cikin gizagizai.

4 Ruwa ya sa ya yi girma,

Danshi ya sa ya yi tsayi.

Koguna sun gudu kewaye da wurin da aka shuka shi.

Yana aikar da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.

5 Sai ya yi tsayi fiye da dukan itatuwan da suke a kurmi,

Rassansa suka yi kauri, suka kuma yi tsayi,

Saboda isasshen ruwa a lokacin tohonsa.

6 Dukan tsuntsayen sararin sama sun yi sheƙunansu a rassansa,

Namomin jeji kuma suka haifi ‘ya’yansu ƙarƙashin rassansa.

Dukan al’ummai suka zauna ƙarƙashin inuwarsa.

7 Girmansa yana da kyau, haka kuma dogayen rassansa,

Gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin ruwa.

8 Ko itatuwan al’ul da suke cikin gonar Allah, ba su kai kyansa ba.

Itatuwan kasharina kuma ba su kai rassansa ba.

Itatuwan durumi kuma ba su kai rassansa ba.

Ba wani itace a gonar Allah wanda ya kai kyansa.

9 Na sa shi ya yi kyau, ga kuma rassansa da yawa.

Dukan itatuwan Aidan, waɗanda suke cikin gonar Allah sun yi ta jin ƙyashinsa.’

10 Domin haka Ubangiji Allah ya ce, “Saboda ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, zuciyarsa kuwa ta yi fariya saboda tsayinsa,

11 zan bashe shi a hannun mai ƙarfi, a cikin al’ummai. Zai sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na fitar da shi.

12 Baƙi mafi bantsoro daga cikin al’ummai sun sare shi, sun bar shi. Rassansa sun faɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka, rassansa kuma sun kakkarye, sun faɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan mutanen duniya sun tashi daga inuwarsa, sun bar shi.

13 Dukan tsuntsayen sararin sama za su zauna a gorarsa. Namomin jeji kuma za su yi ta yawo a cikin rassansa.

14 An yi wannan domin kada itatuwan da suke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da yake shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da ‘yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”

15 Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da ya gangara zuwa lahira, na sa zurfi ya rufe shi, ya yi makoki dominsa. Na tsai da kogunansa, yawan ruwansa ya ƙafe. Na sa Lebanon ta yi duhu saboda shi. Dukan itatuwan jeji kuwa sun yi yaushi saboda shi.

16 Al’ummai suka yi rawar jiki saboda amon faɗuwarsa, sa’ad da na jefar da shi cikin lahira tare da waɗanda suke gangarawa zuwa cikin kabari. Dukan itatuwan Aidan da itatuwa mafi kyau na Lebanon waɗanda suka ƙoshi da ruwa, sun ta’azantu a lahira.

17 Su kuma suka gangara tare da shi zuwa lahira, suka tarar da waɗanda aka kashe da takobi, wato waɗanda daga cikin al’ummai suka yi zama a inuwarsa.

18 “A cikin itatuwan Aidan, da wa za a kamanta darajarka da girmanka? Duk da haka za a kai ka lahira tare da itatuwan Aidan. Za ka zauna tare da marasa kaciya, da waɗanda aka kashe da takobi. Wannan Fir’auna ke nan, da dukan jama’arsa, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 32

Makoki saboda Fir’auna

1 A kan rana ta fari, ga watan goma sha biyu, a shekara ta goma sha biyu, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna, Sarkin Masar, ka ce,

‘Ka aza kanka kamar zaki a cikin al’ummai,

Amma kai kada ne a cikin ruwa.

Ka ɓullo cikin kogunanka,

Ka gurɓata ruwa da ƙafafunka,

Ka ƙazantar da kogunansu.’

3 Ubangiji Allah ya ce,

‘Zan jefa taruna a kanka, a babban taron mutane,

Zan jawo ka cikin taruna.

4 Zan jefar da kai a tudu,

A fili zan jefa ka.

Zan sa tsuntsayen sararin sama su ɗira a kanka,

Zan ƙosar da namomin jeji na dukan duniya da namanka.

5 Zan watsa namanka a kan duwatsu,

In cika kwaruruka da gawarka.

6 Zan watsar da jininka a ƙasa da tuddai,

Magudanan ruwa za su cika da jininka.

7 Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai,

In sa taurarinsu su duhunta,

Zan sa girgije ya rufe rana,

Wata kuma ba zai haskaka ba.

8 Dukan haskokin sama zan sa su zama duhu a gare ka,

In sa ƙasarka ta duhunta, ni Ubangiji Allah na faɗa.’

9 “Zukatan al’ummai da yawa za su ɓaci, sa’ad da na baza labarin halakarka a ƙasashen da ba ka sani ba.

10 Al’ummai da yawa za su gigice saboda abin da zai same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobi a gabansu. A ranar faɗuwarka za su yi rawar jiki a kowane lokaci, kowa saboda ransa.”

11 Ubangiji Allah ya ce, “Takobin Sarkin Babila zai auko maka.

12 Zan sa ƙarfafan mutane masu bantsoro daga cikin al’ummai su kashe jama’arka da takuba.

Za su wofinta girmankan Masar,

Su kuma hallaka jama’arta.

13 Zan hallaka dukan dabbobinta da suke bakin ruwa,

Ba ƙafar mutum ko ta dabba da za ta ƙara gurɓata ruwa.

14 Zan sa ruwansu ya yi garau,

In sa kogunansu su malala kamar mai,

Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15 Sa’ad da na mai da ƙasar Masar kufai,

In raba ƙasar da abin da take cike da shi,

Sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta,

Daga nan za su sani ni ne Ubangiji.

16 Wannan ita ce waƙar makokin. ‘Yan matan al’ummai za su raira wa Masar da jama’arta duka, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Lahira

17 A rana ta goma sha biyar ga wata na fari, a shekara ta goma sha biyu, Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

18 “Ɗan mutum, ka yi kuka saboda jama’ar Masar. Ka tura su tare da sauran al’umma zuwa lahira wurin waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.

19 Ka ce, ‘Su wa kika fi kyau? Ki gangara, ki kwanta tare da marasa imani.’

20 “An zare takobi don a kashe jama’ar Masar. Za su fāɗi a tsakiyar waɗanda aka kashe da takobi.

21 Manyan jarumawa daga lahira za su yi magana a kansu da mataimakansu, su ce, ‘Marasa imani waɗanda aka kashe da takobi, sun gangaro, ga su nan kwance shiru!’

22 “Assuriya tana can da dukan taron jama’arta. Kaburburansu suna kewaye da ita. An kashe dukansu da takobi.

23 An binne su a can ƙurewar lahira. Taron jama’arta suna kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Su ne suka haddasa tsoro a cikin ƙasar.

24 “Elam tana can da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Sun gangara da rashin imaninsu zuwa lahira. Su ne suka haddasa tsoro a duniya. Sun sha kunyarsu tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari.

25 An shirya mata gado tare da matattu. Kaburburan dukan sojojinta suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, amma a dā sun yaɗa tsoro a duniya. Yanzu kuwa suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari. An tara su tare da waɗanda aka kashe.

26 “Meshek da Tubal suna can da dukan sojojinsu. Kaburburan sojojinsu suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, gama sun yaɗa tsoro a duniya.

27 Ba su kwanta kusa da manyan jarumawan da aka kashe ba, waɗanda suka tafi lahira da makamansu, aka yi musu matasan kai da takubansu, aka rufe ƙasusuwansu da garkuwoyinsu, gama manyan jarumawan nan sun baza tsoro a duniya.

28 Amma za a karya ku, ku kwanta tare da marasa imani, tare da waɗanda aka kashe da takobi.

29 “Edom kuma tana can tare da sarakunanta da dukan shugabanninta masu iko, Suna kwance tare da waɗanda aka kashe da takobi, marasa imani, masu gangarawa zuwa cikin kabari.

30 “Dukan shugabannin arewa suna can, da dukan Sidoniyawa. Da kunya, suna gangarawa tare da waɗanda aka kashe, ko da yake a dā sun haddasa tsoro saboda ikonsu. Yanzu suna kwance tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.

31 “Sa’ad da Fir’auna zai gan su, zai ta’azantu a kan rundunarsa da aka kashe da takobi. Lalle Fir’auna da dukan rundunarsa za su ta’azantu. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

32 “Ko da yake na sa Fir’auna ya haddasa tsoro a duniya, duk da haka zan sa a kashe shi tare da rundunarsa. Za su kwanta tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 33

Wajibin Mai Tsaro [Eze 3.16-21]

1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka yi magana da mutanenka, ka faɗa musu cewa, ‘Idan na zare takobi a kan wata ƙasa, idan mutanen ƙasar suka ɗauki wani mutum daga cikinsu, suka sa shi ya zama ɗan tsaronsu,

3 idan ya ga an taso wa ƙasar da takobi, sai ya busa ƙaho don ya faɗakar da jama’ar.

4 Idan wani ya ji amon ƙahon, amma bai kula ba, har takobin ya zo ya kashe shi, hakkin jininsa yana bisa kansa.

5 Gama ya ji amon ƙahon, bai kuwa kula ba, hakkin jininsa zai zauna a bisa kansa. Amma idan ya kula da faɗakar, zai tsira da ransa.

6 Idan kuwa ɗan tsaron ya ga takobi yana zuwa, amma bai busa ƙahon don ya faɗakar da mutanen ba, takobin kuwa ya zo, ya kashe wani daga cikinsu, shi wanda aka kashe ya mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa daga hannun ɗan tsaron.’

7 “Yanzu fa, kai ɗan mutum, na sa ka zama ɗan tsaro a al’ummar Isra’ila. Duk lokacin da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su.

8 Idan na hurta, cewa hakika mugu zai mutu, amma ba ka faɗakar da shi don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa ba, wannan mugun zai mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

9 Amma idan ka faɗakar da mugu don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa, idan bai juyo ya bar muguwar hanyarsa ba, zai mutu saboda laifinsa, amma za ka tsira da ranka.”

Ayyukan Allah Daidai Ne [Eze 18.21-32]

10 “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra’ila, ‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ’

11 Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra’ila?’

12 “Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa’ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi.

13 Idan na ce wa adali, ba shakka zai rayu, amma idan ya dogara ga adalcin da ya riga ya yi, sa’an nan ya shiga aikata laifi, ba za a tuna da ayyukan adalcinsa na dā ba. Zai mutu saboda laifin da ya yi.

14 Idan kuma na ce wa mugu ba shakka zai mutu, amma idan ya bar laifinsa, ya shiga aikata adalci,

15 idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa’an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba.

16 Ba za a tuna da laifofin da ya aikata a dā ba, gama ya aikata adalci da gaskiya, zai rayu.

17 “Amma mutanenka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce,’ alhali kuwa tasu ce ba daidai ba.

18 Sa’ad da adali ya daina aikata adalci, ya shiga aikata laifi, zai mutu saboda laifinsa.

19 Sa’ad da kuma mugu ya daina aikata mugunta, ya shiga aikata adalci da gaskiya, zai rayu saboda adalcinsa.

20 Amma duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ya mutanen Isra’ila, zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”

Labarin Faɗuwar Urushalima

21 A rana ta biyar ga watan goma, a shekara ta goma sha biyu ta zaman bautar talala da aka kai mu, sai wani ɗan gudun hijira daga Urushalima ya zo wurina, ya ce, “Birnin ya fāɗi.”

22 A maraicen da ya wuce kafin ɗan gudun hijirar ya iso, Ubangiji ya ƙarfafa ni, ya kuma buɗe bakina a lokacin da mutum ya zo wurina da safe. Bakina kuwa ya buɗe, ban zama bebe ba kuma.

23 Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

24 “Ɗan mutum, mazaunan wuraren nan da aka lalatar a ƙasar Isra’ila, suna cewa, ‘Ibrahim shi kaɗai ne, duk da haka an ba shi ƙasar duka, balle fa mu da muke da yawa, lalle ƙasar tamu ce.’

25 “Domin haka, sai ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah ya ce, “Kuna cin nama da jininsa, kuna bautar gumaka, kuna kuma yin kisankai, da haka za ku mallaki ƙasar?

26 Kun sa dogararku ga takobi kuna aikata abubuwan bankyama, kowannenku kuma yana zina da matar maƙwabcinsa, da haka za ku iya mallakar ƙasar?”’

27 “Ka faɗa musu, ‘Ubangiji ya ce, “Hakika, waɗanda suke a wuraren da aka lalatar, za a kashe su da takobi, wanda kuma yake a saura zan sa namomin jeji su cinye shi. Waɗanda kuma suke cikin kagara, da kogwannin duwatsu, annoba za ta kashe su.

28 Zan mai da ƙasar kufai marar amfani, fariya za ta ƙare. Tuddan Isra’ila za su zama kufai, ba wanda zai ratsa ta cikinsu.

29 Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa’ad da na mai da ƙasar kufai marar amfani saboda dukan ayyukansu na banƙyama.” ’ ”

Sakamakon Wa’azin Annabin

30 Ubangiji ya ce, “Ɗan mutum, mutanenka sun taru a kan garu da cikin ƙofofin gidaje, suna magana da juna a kanka cewa, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’

31 Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.

32 A gare su ka zama gwanin kiɗa da waƙa, gama suna so su ji abin da kake faɗa, amma ba za su aikata ba.

33 Sa’ad da abin da kake faɗa ya cika [ba shakka kuwa zai cika], sa’an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.”

Categories
EZ

EZ 34

Annabci a kan Makiyayan Isra’ila

1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra’ila, ka ce musu, ‘Ku masu kiwon mutanen Isra’ila, ni Ubangiji Allah na ce, kaito, kaito, ku masu kiwon mutanen Isra’ila, kuna kiwon kanku kawai! Ashe, ba makiyaya ne suke kiwon tumaki ba?

3 Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba.

4 Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.

5 Sai suka warwatsu saboda rashin makiyayin kirki, suka zama abincin namomin jeji.

6 Tumakina sun watse, suna yawo a kan dukan duwatsu da tuddai, sun warwatsu a duniya duka, ba wanda zai nemo su.’

7 “Domin haka, ku ji maganata, ku makiyaya.

8 Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Hakika da yake tumakina sun zama ganimar dukan namomin jeji, saboda rashin makiyayin kirki, makiyayana kuma ba su nemo su ba, amma suka yi kiwon kansu, ba su yi kiwon tumakin ba,

9 to, ku makiyaya, sai ku saurara ga maganata.

10 Ga shi, ina gāba da ku, zan nemi tumakina a hannunku. Zan hana ku yin kiwon tumakin, ku kuma ba za ku ƙara yin kiwon kanku ba. Zan ƙwace tumakina daga hannunku, domin kada su ƙara zama abincinku.”’

Makiyayi Mai Kyau

11 “Ni Ubangiji Allah na ce, ni kaina zan nemi tumakina.

12 Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.

13 Zan fito da su daga cikin sauran al’umma, in tattaro su daga ƙasashe dabam dabam, in kawo su ƙasarsu, in yi kiwonsu a kan tuddan Isra’ila, kusa da maɓuɓɓugai, da cikin dukan wuraren da mutane suke zaune a ƙasar.

14 Zan yi kiwonsu a makiyaya mai kyau. Ƙwanƙolin tuddan Isra’ila zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a makiyaya mai kyau, za su yi kiwo a makiyaya mai dausayi a kan tuddan Isra’ila.

15 Ni kaina zan yi kiwon tumakin, in ba su hutawa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16 “Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.

17 “Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ku kuma garkena, zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin rago da bunsuru.

18 A ganinku abu mai kyau ne, bayan da kun yi kiwo a makiyaya mai kyau, sa’an nan ku tattake sauran makiyayar da ƙafafunku? Sa’ad da kuka sha ruwa mai kyau, sai kuma ku gurɓata sauran da ƙafafunku?

19 Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake da ƙafafunku, su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku!’

20 “Saboda haka, ni, Ubangiji Allah, na ce, ‘Zan shara’anta tsakanin turkakkun tumaki da ramammu.

21 Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku, har kun watsar da su.

22 Zan ceci garken tumakina, ba za su ƙara zama ganima ba. Zan kuma shara’anta tsakanin tunkiya da tunkiya.

23 Zan sa musu makiyayi guda, wato bawana Dawuda. Zai yi kiwonsu, ya zama makiyayinsu.

24 Ni kuma, Ubangiji, zan zama Allahnsu. Bawana Dawuda kuwa zai zama sarkinsu.’ Ni Ubangiji na faɗa.

25 “Zan yi alkawarin salama da su. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar, domin tumakin su zauna lafiya a jeji, su kwana cikin kurmi.

26 Zan sa su, da wuraren da suke kewaye da tuduna dalilin samun albarka. Zan aiko da ruwan sama a lokacinsa, zai kuma zama ruwan albarka.

27 Itatuwan saura za su yi ‘ya’ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani. Za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su sani ni ne Ubangiji, sa’ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.

28 Ba za su ƙara zama ganimar al’ummai ba, namomin jejin ƙasar kuma ba za su cinye su ba. Za su yi zamansu lafiya, ba wanda zai tsorata su.

29 Zan ba su gonaki masu dausayi don kada yunwa ta ƙara far musu a ƙasar, kada kuma su ƙara shan zargi wurin sauran al’umma.

30 Za su sani ni Ubangiji Allahnsu, ina tare da su, mutanen Isra’ila kuwa su ne mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.

31 “Ku tumakin makiyayata, ku mutane ne, ni kuwa Allahnku ne, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 35

Annabci a kan Dutsen Seyir

1 Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir, ka yi annabci a kansa.

3 Ka faɗa masa, ni Ubangiji Allah na ce,

Ga shi, ina gāba da shi, wato Dutsen Seyir.

Zan miƙa hannuna gāba da shi,

Zan maishe shi kufai, in lalatar da shi.

4 Zan lalatar da biranensa,

In maishe su kufai marar amfani,

Sa’an nan zai sani ni ne Ubangiji.

5 “Saboda ya riƙe ƙiyayya din din din, ya ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, da lokacin da adadin horonsu ya cika,

6 don haka, ni Ubangiji na ce, hakika zan sa a zub da jininsa. Mai zub da jini zai fafare shi, da yake shi ma ya zub da jini, domin haka mai zub da jini zai fafare shi.

7 Zan mai da Dutsen Seyir kufai marar amfani. Zan kashe duk mai shiga ko mai fita a cikinsa.

8 Zan cika duwatsunsa da gawawwaki. Waɗanda za a kashe da takobi za su faɗi a kan tuddansa, da cikin kwarurukansa, da cikin dukan kwazazzabansa.

9 Zan maishe shi kufai marar amfani har abada. Ba wanda zai zauna a cikin biranensa. Sa’an nan zai sani ni ne Ubangiji.

10 “Da yake ya ce al’umman nan biyu, da ƙasashen nan biyu za su zama nasa, ya mallake su, ko da yake Ubangiji yana cikinsu,

11 domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, hakika zan saka masa gwargwadon fushinsa, da kishinsa, da ƙiyayyar da ya nuna musu. Zan sanar da kaina a gare su sa’ad da na hukunta shi.

12 Zai sani Ubangiji ne wanda ya ji dukan zarge zargen da ya yi wa duwatsun Isra’ila, da ya ce, ‘An maishe su kufai marar amfani, an ba mu su mu cinye!’

13 Na ji tsiwa da dukan surutan da ya yi mini.

14 “Ni Ubangiji Allah zan maishe shi kufai marar amfani, domin dukan duniya ta yi farin ciki.

15 Kamar yadda ya yi farin ciki saboda gādon jama’ar Isra’ila, da ya zama kufai marar amfani, haka nan zan yi da shi, wato Seyir. Zai zama kufai marar amfani, wato Dutsen Seyir da dukan Edom. Sa’an nan mutane za su sani ni ne Ubangiji!”

Categories
EZ

EZ 36

Albarkar Ubangiji a kan Ƙasar Isra’ila a Gaba

1 “Kai ɗan mutum, ka yi annabci a kan duwatsun Isra’ila, ka ce, ‘Ya duwatsun Isra’ila, ku ji maganar Ubangiji.’

2 Ubangiji Allah ya ce, da yake maƙiya suna cewa, ‘Madalla, tsofaffin tuddai sun zama mallakarmu yanzu,’

3 sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Da yake sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al’umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane.

4 Domin haka, ku duwatsun Isra’ila, sai ku ji maganar Ubangiji Allah. Ni Ubangiji Allah, na ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, da kufai, da yasaassun birane waɗanda suka zama ganima da abin ba’a ga al’umman da suke kewaye,

5 ni, Ubangiji Allah, ina yin magana da zafin kishina gāba da sauran al’umma, da dukan Edom, gama da farin ciki da raini suka mallaki ƙasata, suka washe ta.’

6 “Domin haka ka yi wa ƙasar Isra’ila annabci, ka ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al’ummai.’

7 “Domin haka ni Ubangiji Allah na rantse, cewa al’umman da suke kewaye da ku su ma za su sha zargi.

8 Amma ku, ya duwatsun Isra’ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanen Isra’ila, gama za su komo gida ba da jimawa ba.

9 Ga shi, ni naku ne, zan juyo wurinku. Za a kafce ku, a yi shuka!

10 Zan sa dukan mutanen Isra’ila su riɓaɓɓanya a cikinku. Za su zauna cikin biranen, su gina rusassun wurare.

11 Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa’an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji.

12 Zan kuma sa mutanena, Isra’ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe ‘ya’yansu ba.

13 “Ni Ubangiji Allah na ce, da yake mutane sukan ce muku, ‘Kuna cinye mutane, kuna kuma kashe ‘ya’yan al’ummarku,

14 saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba kuwa za ku ƙara kashe ‘ya’yan al’ummarku ba. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15 Ba zan ƙara bari ku sha zargi wurin sauran al’umma ba, ba kuwa za ku ƙara shan kunya a gaban jama’a ba, ba kuma zan ƙara sa al’ummarku ta yi tuntuɓe ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

16 Ubangiji Kuma ya yi magana da ni, ya ce,

17 “Ɗan mutum, sa’ad da mutanen Isra’ila suka zauna a ƙasar kansu, sun ƙazantar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Halinsu a gare ni ya zama kamar rashin tsarkin mace a lokacin hailarta.

18 Sai na husata da su saboda jinin da suka zuba a cikin ƙasar, da kuma yadda suka ƙazantar da ƙasar da gumakansu.

19 Na warwatsa su cikin al’ummai, suka kuwa warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu.

20 Amma sa’ad da suka tafi cikin al’ummai, sai suka ɓata sunana mai tsarki a duk inda suka tafi. Sai mutane suka yi magana a kansu cewa, ‘Waɗannan jama’ar Ubangiji ne, amma dole ne su fita daga cikin ƙasarsa.’

21 Amma na damu saboda sunana mai tsarki wanda mutanen Isra’ila suka sa aka ɓata shi a wurin al’ummai inda suka tafi.

22 “Domin haka sai ka faɗa wa mutanen Isra’ila, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ba saboda ku ba ne, ya mutanen Isra’ila, zan yi wani abu, amma saboda sunana mai tsarki wanda kuka ɓata a wurin al’ummai inda kuka tafi.

23 Zan ɗauki fansa saboda sunana mai tsarki, mai girma, wanda aka ɓata a wurin al’ummai, ku kuma kuka ɓata shi a cikinsu. Al’ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na tabbatar da tsarkina a wurinku a kan idonsu.

24 Zan kwaso ku daga cikin al’ummai, in tattaro ku daga dukan ƙasashe, in kawo ku cikin ƙasarku.

25 Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.

26 Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa’an nan in sa muku zuciya mai taushi.

27 Zan sa ruhuna a cikinku, in sa ku bi dokokina, ku kiyaye ka’idodina.

28 Za ku zauna cikin ƙasar da na ba kakanninku. Za ku zama mutanena, ni kuma in zama Allahnku.

29 Zan tsarkake ku daga dukan ƙazantarku. Zan kuma sa hatsi ya yi yalwa, ba zan bar yunwa ta same ku ba.

30 Zan sa ‘ya’yan itatuwa da amfanin gona su yalwata, don kada ku ƙara shan kunya saboda yunwa a wurin al’ummai.

31 Sa’an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama.

32 Ni Ubangiji Allah na ce, sai ku sani, ba saboda ku ba ne zan aikata wannan. Ku kunyata, ku gigita saboda hanyoyinku, ya mutanen Isra’ila!”’

33 Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da zan tsarkake ku daga dukan muguntarku, zan sa ku zauna cikin biranenku, ku gina rusassun wurare.

34 Ƙasar da take kufai a dā za ku kafce ta maimakon yadda take kufai a kan idon dukan masu wucewa.

35 Za su ce, ‘Wannan ƙasa wadda take kufai a dā ta zama kamar gonar Aidan, ga kuma rusassun wuraren da suka zama kufai, da rusassun birane, yanzu ana zaune a cikinsu, an kuma gina musu garu.’

36 Sa’an nan al’umman da suka ragu kewaye da ku za su sani, ni Ubangiji na sāke gina rusassun wuraren da suka zama kufai. Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”

37 Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra’ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki.

38 Kamar garken tumaki na hadaya, kamar garken tumaki a Urushalima a lokacin ƙayyadaddun idodi, haka rusassun birane za su cika da ɗumbun mutane. Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji.”

Categories
EZ

EZ 37

Kwarin Busassun Ƙasusuwa

1 Ikon Ubangiji kuwa ya sauko a kaina, Ruhunsa kuma ya fito da ni ya ajiye ni a tsakiyar kwari wanda yake cike da ƙasusuwa.

2 Sai ya zagaya da ni cikinsu, ga su kuwa, suna da yawa a cikin kwarin, busassu ragau.

3 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa kuwa za su rayu?”

Ni kuwa na amsa na ce, “Ya Ubangiji Allah, sani na gare ka.”

4 Sai ya ce mini, “Ka yi annabci a kan ƙasusuwan nan ka faɗa musu su saurari maganata.

5 Gama ni Ubangiji Allah zan hura musu numfashi, za su kuwa rayu.

6 Zan sa musu jijiyoyi da tsoka, in rufe da fata, in kuma hura musu numfashi, sa’an nan za su rayu, su sani ni ne Ubangiji.”

7 Sai na yi annabci kamar yadda ya umarce ni. Da na yi annabcin sai aka ji motsi da girgiza. Sai ƙasusuwan suka harhaɗu da juna, ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu.

8 Da na duba, sai ga jijiyoyi a kansu, nama kuma ya baibaye su, sa’an nan fata ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.

9 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan iska, ka ce mata, ni Ubangiji Allah na ce ta zo daga kusurwa huɗu, ta hura a kan waɗannan matattu domin su rayu.”

10 Na kuwa yi annabci kamar yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga cikinsu, suka rayu, suka tashi, suka tsaya da ƙafafunsu. Sun zama babbar runduna ƙwarai.

11 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra’ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’

12 “Domin haka ka yi annabci ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce zan buɗe kaburburansu, in tashe su daga cikin kaburburansu. Zan kuma komar da su gida zuwa ƙasar Isra’ila.

13 Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu.

14 Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa’an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”

Mutanen Yahuza da Isra’ila Za Su Zama Mulki Guda

15 Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

16 “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra’ila, magoyan bayansa.’

17 Ka haɗa su su zama sanda guda a hannunka.

18 Sa’ad da kuma jama’arka suka ce maka ka nuna musu abin da kake nufi da waɗannan,

19 sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce zan karɓe sandan Yusufu, wanda yake a hannun Ifraimu da mutanen Isra’ila magoyan bayansa, in haɗa shi da sandan Yahuza in maishe su sanda guda a hannuna.

20 “Sa’ad da sandunan da ka yi rubutu a kansu suna hannunka a gabansu,

21 sai ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji Allah na ce, zan komo da jama’ar Isra’ila daga wurin al’ummai inda suka warwatsu, zan tattaro su daga ko’ina, in maido su ƙasarsu.

22 Zan maishe su al’umma guda a ƙasar Isra’ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al’umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.

23 Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama’ata, ni kuma zan zama Allahnsu.

24 Bawana Dawuda zai sarauce su. Dukansu za su sami shugaba guda. Za su bi ka’idodina su kiyaye dokokina.

25 Za su zauna a ƙasar da kakanninsu suka zauna, wadda na ba bawana Yakubu. Su da ‘ya’yansu da jikokin ‘ya’yansu za su zauna a can har abada. Bawana Dawuda kuwa zai sarauce su har abada.

26 Zan ƙulla dawwamammen alkawarin salama da su. Zan sa musu albarka, in yawaita su. Zan kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.

27 Wurin Zamana zai kasance a tsakiyarsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.

28 Sa’an nan al’ummai za su sani, ni ne na tsarkake Isra’ila sa’ad da na kafa Haikalina a tsakiyarsu har abada.”

Categories
EZ

EZ 38

Annabci a kan Gog

1 Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2 “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog na ƙasar Magog, babban shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal, ka yi annabci a kansa,

3 ka ce Ubangiji Allah ya ce, ‘Ga shi, ina gaba da kai, ya Gog, babban shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal.

4 Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi cikin muƙamuƙanka, in fitar da kai, da dukan sojojinka, da dawakai da mahayansu. Su babbar runduna ce saye da makamai, wato garkuwoyi, da takuba a zāre,

5 mutanen Farisa, da Habasha, duk da Fut. Dukansu suna saye da garkuwa da kwalkwali,

6 da Gomer tare da dukan sojojinsa, da Bet-togarma daga ƙurewar arewa, da dukan sojojinsa, su jama’a mai yawa, suna tare da kai.

7 Ka shirya, ka kuma zama da shiri, kai da dukan rundunar da suka tattaru kewaye da kai, ka zama ɗan tsaronsu.

8 Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra’ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama’a suka tattaru daga sauran al’umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al’ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya.

9 Za ka ci gaba, kana zuwa kamar hadiri, za ka rufe ƙasar kamar gizagizai, kai da rundunarka, da jama’a masu yawa tare da kai.”’

10 Ubangiji Allah ya ce, “A wannan rana tunani zai shiga cikin zuciyarka, za ka ƙirƙiro muguwar dabara,

11 ka ce, ‘Zan haura, in tafi ƙasar da garuruwanta ba su da garu, in fāɗa wa mutanen da suke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare,

12 don in washe su ganima, in fāda wa wuraren da aka ɓarnatar waɗanda ake zaune a cikinsu yanzu, in kuma fāɗa wa jama’ar da aka tattaro daga cikin al’ummai waɗanda suka sami shanu da dukiya, suna zaune a cibiyar duniya.’

13 Sheba da Dedan, da ‘yan kasuwar Tarshish, da dukan garuruwa za su ce maka, ‘Ka zo kwasar ganima ne? Ko ka zo ka tattaro rundunarka don ka yi waso, ka kwashe azurfa da zinariya, da bisashe, da dukiya, ka kwashe babbar ganima?’

14 “Saboda haka ɗan mutum, yi annabci, ka faɗa wa Gog, cewa ni Ubangiji Allah na ce, ‘A wannan rana sa’ad da jama’ata Isra’ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba?

15 Za ka taso daga wurin da kake, can ƙurewar arewa, da jama’a mai yawa tare da kai, babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi, dukansu a kan dawakai.

16 Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra’ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al’ummai su san ni sa’ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.”’

17 Ubangiji Allah ya ce, “Kai ne wanda na yi magana a kanka a zamanin dā ta wurin bayina annabawan Isra’ila, cewa a shekaru masu zuwa zan kawo ka, ka yaƙe su.

18 Amma a wannan rana sa’ad da Gog zai kawo wa ƙasar Isra’ila yaƙi, ni Ubangiji Allah zan hasala.

19 Gama a kishina da zafin hasalata na hurta, cewa a wannan rana za a yi babbar girgiza a ƙasar Isra’ila.

20 Kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da bisashe, da dukan masu rarrafe, da dukan mutanen da suke duniya, za su yi makyarkyata a gabana. Za a jefar da duwatsu ƙasa, tsaunuka za su fādi, kowane bango zai rushe.

21 Zan razana Gog da kowace irin razana, ni Ubangiji Allah na faɗa. Mutanensa za su sassare junansu da takubansu.

22 Zan hukunta shi da annoba da kuma zub da jini. Zan yi masa ruwa da ƙanƙara, da wuta, da kibritu za a makaka a kansa da rundunarsa, da dukan jama’ar da suke tare da shi.

23 Da haka kuwa zan bayyana girmana da tsarkina in kuma sanar da kaina ga al’ummai. Ta haka za su sani ni ne Ubangiji.”

Categories
EZ

EZ 39

Cin Nasara a kan Gog

1 “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa Gog shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal cewa, ‘Ni Ubangiji Allah ina gāba da kai.

2 Zan juya ka in sa ka gaba in tashi daga ƙurewar arewa, in kawo ka don ka fāɗa wa duwatsun Isra’ila.

3 Sa’an nan zan karya bakan da yake a hannun hagunka, in sa kiban da suke a hannun damanka su fāɗi.

4 Za ka fāɗi matacce a kan duwatsun Isra’ila, kai da dukan rundunanka, da jama’ar da suke tare da kai. Zan ba da gawawwakinka ga tsuntsaye da dabbobi masu cin nama.

5 Za ka mutu a filin saura, gama haka ni Ubangiji Allah na faɗa.’

6 Zan aika da wuta a kan Magog, da a kan waɗanda suke zaman lafiya a ƙasashen gāɓar teku, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.

7 Zan sanar da sunana mai tsarki a tsakiyar jama’ata, wato Isra’ila, ba zan ƙara bari a ɓata sunana mai tsarki ba, al’ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji Mai Tsarki a cikin Isra’ila.

8 “Ga shi, ranar da na ambata tana zuwa, hakika kuwa tana zuwa, ni Ubangiji Allah na faɗa.

9 Sa’an nan su mazaunan biranen Isra’ila za su tattara makaman mutane, wato garkuwoyi, da bakuna, da kibau da kulake, da māsu, su yi ta hura wuta da su, har ya kai shekara bakwai.

10 Ba za su yi wahalar zuwa jeji don nemo itacen wuta ba, gama za su yi ta hura wuta da makaman. Za su washe waɗanda suka washe su a dā, ni Ubangiji na faɗa.

11 “A wannan rana zan ba Gog makabarta a Isra’ila, a kwarin matafiya a gabashin teku. Makabartar za ta kashe hanyar matafiya, gama a can za a binne Gog da dukan rundunar da take tare da shi. Za a kira wurin Hamongog, wato Kwarin Rundunar Gog.

12 Jama’ar Isra’ila za su yi wata bakwai suna binne su don su tsabtace ƙasar.

13 Dukan jama’ar ƙasar za su yi aikin binnewar, zai zama daraja a gare su a ranar da zan bayyana ɗaukakata, ni Ubangiji Allah na faɗa.

14 A ƙarshen wata bakwai ɗin za su keɓe waɗansu mutane domin su bi ko’ina cikin ƙasar, su binne sauran gawawwakin da suka ragu a ƙasar don su tsabtace ta.

15 Sa’ad da waɗannan suke bibiyawa a cikin ƙasar, duk wanda ya ga ƙashin mutum, sai ya kafa wata alama kusa da ƙashin don masu binnewa su gani, su ɗauka, su binne a Kwarin Rundunar Gog.

16 Akwai gari a wurin, za a sa masa suna Hamona, wato runduna. Ta haka za su tsabtace ƙasar.

17 “Ni Ubangiji Allah na ce, kai ɗan mutum, sai ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan bisashe daga ko’ina, su zo idi wanda nake shirya musu a duwatsun Isra’ila. Za su ci nama su kuma sha jini.

18 Za su ci naman mutane masu iko, su sha jinin shugabannin duniya, waɗanda aka kashe kamar yadda ake yanka raguna, da ‘yan tumaki, da awaki, da bijimai, da dukan turkakkun Bashan.

19 Za su ci kitse, har su gundura, su sha jini kuma, har su bugu a idin da nake shirya musu.

20 Za a ƙosar da su da naman dawakai, da na mahayansu da na mutane masu iko, da na dukan mayaƙa, ni Ubangiji na faɗa.”

Komowar Mutanen Isra’ila

21 “Zan nuna ɗaukakata a cikin al’ummai, dukan al’ummai kuwa za su ga hukuncin da na yi da ikon da na nuna kansu.

22 Tun daga wannan rana har zuwa gaba, jama’ar Isra’ila za su sani, ni ne Ubangiji Allahnsu.

23 Al’ummai kuma za su sani an kai jama’ar Isra’ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha’inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi.

24 Na yi gwargwadon lalatarsu da laifofinsu, na kawar da fuskata daga gare su.

25 “Saboda haka, ni Ubangiji Allah, na ce yanzu zan komo da zuriyar Yakubu daga bauta in nuna mata jinƙai. Zan yi kishi domin sunana mai tsarki.

26 Sa’ad da suka komo suka zauna lafiya a ƙasarsu, za su manta da abin kunyar da suka yi da dukan ha’incin da suka yi mini. Ba wanda zai ƙara firgita su, ba kuwa mai tsorata su.

27 Zan nuna wa sauran al’umma ni mai tsarki ne ta wurin komo da mutanen Isra’ila daga cikin al’ummai, da ƙasashen al’ummai magabtansu.

28 Sa’an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu, domin na kore su daga ƙasarsu zuwa bautar talala cikin al’ummai, sa’an nan na sāke tattaro su zuwa cikin ƙasarsu. Daga cikinsu ba zan bar ko ɗaya a cikin al’ummai ba.

29 Ba kuma zan ƙara kawar da fuskata daga gare su ba, sa’ad da na saukar da Ruhuna a kan jama’ar Isra’ila, ni Ubangiji na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 40

Wahayin Haikalin da Ezekiyel Ya Gani

1 A ranar goma ga wata na farko a shekara ta ashirin da biyar ta zamanmu a bautar talala, a shekara ta goma sha huɗu da cin birnin, ikon Ubangiji ya sauko a kaina.

2 A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra’ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni.

3 Sa’ad da ya kai ni can sai ga wani mutum, kamanninsa sai ka ce tagulla, yana riƙe da igiyar rama da wani irin ƙara na awo a hannunsa, yana tsaye a bakin ƙofa.

4 Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama’ar Isra’ila abin da ka gani duka.”

5 Abin da na gani Haikali ne. Akwai katanga kewaye da filin Haikalin. Tsawon karan awon kuma da yake a hannun mutumin kamu shida ne. Sai ya auna faɗin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.

6 Ya tafi kuma wajen ƙofar gabas ya hau matakanta, ya auna dokin ƙofar, faɗinta kamu shida ne.

7 Tsawon ɗakin ‘yan tsaro kamu shida ne, faɗinsa kuma kamu shida. Kamu biyar ne yake tsakanin ɗaki da ɗaki. Dokin ƙofa kuma da yake kusa da shirayin bakin ƙofar Haikali kamu shida ne.

8 Ya kuma auna shirayin bakin ƙofar da take fuskantar Haikali, kamu shida.

9 Sa’an nan ya auna shirayin bakin ƙofar kamu takwas ne. Sai kuma ya auna ginshiƙan shirayin kamu biyu ne. Shirayin ƙofar yana fuskantar ciki.

10 Akwai ɗakuna uku na ‘yan tsaro a kowane gefe na ƙofar gabas, girmansu iri ɗaya ne. Ginshiƙansu kuma girmansu ɗaya ne.

11 Ya kuma auna fāɗin bakin ƙofar, kamu goma ne, tsayin ƙofar kuwa kamu goma sha uku ne.

12 Akwai, ‘yar katanga a gaban ɗakunan ‘yan tsaron, faɗinta kamu ɗaya ne a kowane gefe. Girman ɗakunan ‘yan tsaron kuwa kamu shida ne a kowane gefe.

13 Daga bayan rufin ɗaya ɗakin ‘yan tsaro zuwa bayan ɗayan rufin ya auna filin ya sami kamu ashirin da biyar.

14 Ya yi ginshiƙai kamu sittin. Akwai ɗakuna kewaye da shirayin da yake bakin ƙofa.

15 Daga gaban ƙofar shiga, zuwa kurewar shirayi na can ciki kamu hamsin ne.

16 Akwai tagogi masu murfi da yake fuskantar ɗakunan ‘yan tsaro da kuma ginshikansu waɗanda suke wajen ƙofa a kewaye, haka nan kuma shirayin. Daga ciki kuma akwai tagogi a kewaye. A kowane ginshiƙi an zana siffar itatuwan dabino.

17 Sai ya kawo ni a fili na waje, ga ɗakuna da daɓe kewaye da filin. Akwai ɗakuna talatin a gaban daɓen.

18 Daɓen ya bi ta daidai gefen ƙofofin. Wannan shi ne daɓen da yake ƙasa ƙasa.

19 Sai ya auna nisan da yake tsakanin fuskar ciki ta ƙofar da take ƙasa zuwa fuskar waje ta filin ciki, ya sami kamu ɗari wajen gabas da arewa.

20 Ya kuma auna tsayin ƙofar arewa da faɗinta wadda take fuskantar filin waje.

21 Tana da ɗakuna uku na ‘yan tsaro a kowane gefe. Girman ginshiƙanta da shirayinta, daidai suke da ƙofa ta fari. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.

22 Girman tagoginta, da na shirayin, da na siffar itatuwan dabinon da aka zana iri ɗaya ne da na ƙofar da ta fuskanci gabas. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki.

23 Fili na ciki yana da ƙofa daura da ƙofar arewa da ta gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.

24 Ya kuma kai ni wajen kudu, sai kuma ga wata ƙofa. Ya auna ginshiƙanta da shirayinta. Girmansu ɗaya ne, kamar na sauran.

25 Akwai tagogi kewaye da ƙofar, da shirayinta kamar na sauran. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.

26 Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki. An zana siffar itatuwan dabino a ginshiƙanta, ɗaya a kowane gefe.

27 Akwai wata ƙofa a kudancin fili na can ciki. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.

28 Ya kuma kai ni fili na can ciki, wajen ƙofar kudu, sai ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran.

29 Haka kuma ɗakunanta na ‘yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu ɗaya yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kamu ashirin da biyar ni.

30 Akwai shirayi kewaye, tsawonsa kamu ashirin da biyar ne, faɗinsa kuma kamu biyar ne.

31 Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje. An zana siffar itatuwan dabino a ginshikanta. Tana kuma da matakai takwas.

32 Sai kuma ya kai ni a fili na can ciki wajen gabas. Ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran.

33 Haka nan kuma ɗakunanta na ‘yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu daidai yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.

34 Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Tana da matakai takwas.

35 Sa’an nan kuma ya kai ni ƙofar arewa, ya auna ta. Girmanta daidai yake da na sauran.

36 Haka kuma ɗakunanta na ‘yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.

37 Ginshiƙai suna fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Ita ma matakanta takwas ne.

38 Akwai ɗaki, wanda ƙofarsa take duban ginshiƙan gyaffan ƙofofin, a wurin ake wanke hadayar ƙonawa.

39 A shirayin ƙofar akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yanka hadayar ƙonawa, da hadaya don zunubi da laifi.

40 Akwai tebur biyu a sashin waje na shirayin ƙofar arewa, akwai kuma waɗansu tebur biyu a ɗayan sashin shirayin ƙofar.

41 A gab da ƙofar akwai tebur huɗu, a waje ɗaya kuma akwai huɗu. Duka guda takwas ke nan, inda za a riƙa yanka dabbobin da za a yi hadaya da su.

42 Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu, tsawon da faɗin kowanne kamu ɗaya da rabi rabi ne, tsayi kuwa kamu guda ne. A nan za a ajiye kayan yanka hadayar ƙonawa, da ta sadaka.

43 Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye da cikin ɗakin, tsawonsu taƙi-taƙi. Za a riƙa ajiye naman hadaya a kan teburorin.

44 Ya kai ni fili na can ciki, sai ga ɗakuna biyu a filin. Ɗaya yana wajen ƙofar arewa, yana fuskantar kudu. Ɗayan kuma yana wajen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.

45 Sai ya ce mini, “Wannan ɗaki wanda yake fuskantar kudu na firistoci ne waɗanda suke lura da Haikalin.

46 Ɗakin da yake fuskantar arewa na firistoci ne waɗanda suke lura da bagade. Waɗannan su ne zuriyar Zadok waɗanda su kaɗai ne daga cikin Lawiyawa da suke da iznin kusatar Ubangiji don su yi masa hidima.”

47 Ya auna filin, tsawonsa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu ɗari, wato murabba’i ke nan. Bagade kuma yana a gaban Haikalin.

48 Ya kuma kai ni a shirayin Haikalin. Ya auna ginshiƙan shirayin, kamu biyar ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar kuwa kamu uku ne a kowane gefe.

49 Tsawon shirayin kamu ashirin ne, faɗinsa kuwa kamu goma sha ɗaya. Akwai matakan hawa, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe.