Categories
EZ

EZ 41

1 Sai ya kai ni cikin Haikalin, sa’an nan ya auna ginshiƙai. Fāɗin ginshiƙan kamu shida ne a kowane gefe.

2 Fāɗin ƙofar kamu goma ne. Madogaran ƙofar kamu biyar ne a kowane gefe. Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu arba’in ne faɗinsa kuma kamu ashirin ne.

3 Sai ya shiga ɗaki na can ciki, ya auna madogaran ƙofar, ya sami kamu biyu biyu. Tsayin ƙofar kuma kamu shida ne. Faɗin ƙofar kamu bakwai ne.

4 Ya kuma auna ɗaki na ƙurewar ciki, tsawonsa kamu ashirin ne, faɗinsa kuma kamu ashirin. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”

5 Sai kuma ya auna bangon Haikalin, kaurinsa kamu shida ne. Faɗin ɗakunan da suke kewaye da Haikalin kamu huɗu ne.

6 Ɗakunan benaye ne masu hawa uku. Akwai ɗakuna talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da Haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon Haikalin.

7 Faɗin ɗakunan yana ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, gama katangar da take kewaye da Haikali ta yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. A gefen Haikalin akwai matakan hawa. Don haka ana iya hawa daga ɗaki na ƙasa zuwa hawa na uku ta hanyar hawa na biyu.

8 Na ga harsashi mai faɗi kewaye da Haikalin. Tsawon harsashin gini na ɗakunan karan awo mai tsawon kamu shida ne.

9-10 Kaurin katangar waje ta ɗakunan kamu biyar ne. Faɗin filin da yake tsakanin ɗakunan waje da na Haikali kamu ashirin ne kewaye da Haikalin.

11 Ana buɗe ƙofofin ɗakuna a wajen filin da yake tsakanin ɗakuna. Ƙofa ɗaya tana fuskantar wajen arewa, ɗaya kuma tana fuskantar wajen kudu. Faɗin filin da ya ragu kamu biyar ne.

12 Ginin da yake fuskantar farfajiyar Haikali a wajen yamma, faɗinsa kamu saba’in ne. Kaurin ginin kamu biyar ne, tsawonsa kuma kamu tasa’in ne.

13 Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu ɗari. Tsawon farfajiyar, da ginin, da katangarsa, kamu ɗari.

14 Faɗin Haikalin da farfajiyar a fuskar gabas, kamu ɗari.

15-16 Ya kuma auna tsawon ginin da yake fuskantar farfajiyar da take wajen yamma da hanyar fita, kamu ɗari ne. Cikin Haikalin, da ɗaki na can ciki, da shirayi, dukansu uku suna da tagogi masu gagara badau. An manne bangon Haikalin da yake fuskantar shirayin da katako, tun daga ƙasa har zuwa tagogi. [Tagogin kuma an rufe su.]

17-18 An zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a bangon Haikali ciki da waje har zuwa kan ƙofar shiga. Zanen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu.

19 Fuska ɗaya kamar ta mutum tana fuskantar zānen siffar itacen dabino a wannan gefe. Ɗaya fuskar kamar ta sagarin zaki tana fuskantar zānen siffar itacen dabino na wancan gefe. Haka aka zana dukan jikin bangon Haikalin da su.

20 Daga ƙasa zuwa ɗaurin ƙofa, an zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino.

21-22 Madogaran ƙofofin Haikalin murabba’i ne. Akwai wani abu mai kama da bagaden itace a gaban Wuri Mai Tsarki, tsayinsa kamu uku ne, tsawonsa kamu biyu ne. Kusurwoyinsa da gindinsa, da jikinsa na itace ne. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.”

23 Haikali da Wuri Mai Tsarki suna da ƙofa biyu a haɗe.

24 Kowace ƙofa tana da murfi biyu masu buɗewa ciki da waje.

25 A ƙofofin Haikalin an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangon Haikalin. Akwai rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin waje.

26 Akwai tagogi masu gagara badau a kowane gefen ɗakin. An kuma zāna bangon da siffar itatuwan dabino.

Categories
EZ

EZ 42

1 Sa’an nan ya kai ni a farfajiya da yake waje, ya kuma kai ni ɗakunan da yake kusa da farfajiyar Haikali, daura da ginin da yake wajen arewa.

2 Tsawon ginin da yake wajen gefen arewa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu hamsin.

3 A gaban kamu ashirin na farfajiyar da yake can ciki, da kuma a gaban daɓen farfajiyar da take waje, akwai jerin ɗakuna hawa uku uku.

4 A gaban ɗakunan akwai hanya mai faɗin kamu goma, tsawonta kuwa kamu ɗari. Ƙofofinsu suna fuskantar arewa.

5 Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da fāɗi, gama hanyar benen ya cinye wuri fiye da ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya.

6 Ɗakunan suna da hawa uku, amma ba su da ginshiƙai kamar na farfajiyar da suke waje. Saboda haka ɗakunan da suke a hawa na uku ba su kai girman waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya ba.

7 Tsawon katangar waje wadda take gefen ɗakunan farfajiyar waje wanda yake daura da ɗakunan kamu hamsin ne.

8 Tsawon ɗakunan da suke fuskantar farfajiyar waje kamu hamsin ne. Waɗanda suke fuskantar Haikalin kuwa tsawonsu kamu ɗari ne.

9 Ƙasa da ɗakunan nan akwai ƙofa a gefen gabas, in za a shiga cikinsu daga farfajiyar waje.

10 Akwai kuma ɗakuna a faɗin katangar farfajiyar a wajen gabas a gaban wata farfajiyar da gaban wani gini.

11 Akwai hanya a gaban ɗakunan, sun kuma yi kama da ɗakunan da suke wajen arewa. Tsawonsu, da faɗinsu, da yadda aka shirya su, da ƙofofinsu duk iri ɗaya ne.

12 Kamar ƙofofin ɗakunan da suke wajen kudu, haka nan kuma akwai ƙofa a hanyar da take gaban katanga a wajen gabas, in za a shiga.

13 Sa’an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne.

14 Sa’ad da firistoci suka shiga Wuri Mai Tsarki, ba za su fita daga cikinsa zuwa farfajiyar da yake waje ba, sai sun tuɓe rigunan aikinsu, gama rigunan tsarkakakku ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su tafi inda mutane suke.”

15 Sa’ad da ya gama auna cikin Haikalin, ya fito da ni ta ƙofar gabas, sa’an nan ya auna filin da yake kewaye da Haikalin.

16 Ya auna kusurwar gabas da karan awo, kamu ɗari biyar.

17 Sai kuma ya auna kusurwar arewa, kamu ɗari biyar.

18 Kusurwar kudu kamu ɗari biyar.

19 Kusurwar yamma, ita ma kamu ɗari biyar.

20 Ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana kewaye da katanga mai tsawo kamu ɗari biyar ne, fāɗi kuma kamu ɗari biyar don ya raba Wuri Mai Tsarki da sauran wurin.

Categories
EZ

EZ 43

Zatin Ubangiji Ya Koma Haikalin

1 Bayan haka kuma sai ya kai ni ƙofar da take fuskantar gabas.

2 Sai ga zatin Allah na Isra’ila yana tahowa daga gabas. Muryar Allah ta yi amo kamar rurin teku. Duniya kuwa ta haskaka da zatinsa.

3 Wahayin da na gani ya yi kama da wahayin da na gani lokacin da ya hallaka birnin, kamar kuma wanda na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.

4 Zatin Ubangiji ya shiga Haikalin ta ƙofar gabas.

5 Ruhu kuwa ya ɗaga ni, ya kai ni a farfajiya ta can ciki, sai ga zatin Ubangiji ya cika Haikali.

6 Sa’ad da mutumin yake tsaye kusa da ni, sai Ubangiji ya yi magana da ni daga cikin Haikalin.

7 Ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wuri shi ne kursiyin sarautata da kilisaina, inda zan zauna tsakiyar mutanen Isra’ila har abada. Mutanen Isra’ila da sarakunansu ba za su ƙara ɓata sunana mai tsarki ta wurin bauta wa gumaka da gina siffofin sarakunansu da suka mutu ba,

8 ko kuwa ta wurin sa dokin ƙofarsu kusa da dokin ƙofata, da kuma ta kafa madogaran ƙofarsu kusa da nawa, sai dai katangar da ta yi mana tsakani. Sun ɓata sunana mai tsarki da ayyukansu masu banƙyama, don haka na hallaka su saboda sun sa na husata.

9 Yanzu sai su zubar da gumakansu da siffofin sarakunansu nesa da ni, ni kuwa zan zauna a cikinsu har abada.

Ƙa’idodin Haikali da Bagade

10 “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka bayyana Haikalin ga mutanen Isra’ila domin su kunyata saboda muguntarsu, ka kuma sa su auna fasalin Haikalin.

11 Idan sun ji kunyar dukan abin da suka aikata, sai ka nuna musu fasalin Haikalin, da tsarinsa, da wuraren fita, da wuraren shiga, da fasalinsa duka. Ka kuma sanashe su dukan ka’idodinsa, da dukan dokokinsa. Ka rubuta a gaban idanunsu don su kiyaye, su aikata dukan dokokinsa da dukan ka’idodinsa.

12 Wannan ita ce dokar Haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, za ta zama wuri mai tsarki ƙwarai.

13 “Wannan shi ne girman bagaden bisa ga tsawon kamu. A nan kamu guda daidai yake da kamu guda da taƙi. Gindinsa kamu ɗaya ne, faɗinsa kuma kamu ɗaya, faɗin da’irarsa taƙi guda ne.

14 Tsayin bagaden zai zama kamu biyu daga gindinsa zuwa ƙaramin mahaɗinsa fāɗinsa kuma kamu ɗaya ne. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗi zai zama kamu huɗu, faɗinsa kuwa kamu ɗaya.

15 Tsayin murhun bagaden zai zama kamu huɗu. A kan murhun akwai zanko guda huɗu sun miƙe sama, tsawonsu kamu guda ne.

16 Murhun bagaden zai zama murabba’i ne, wato tsawonsa kamu goma sha biyu, faɗinsa kuma kamu goma sha biyu.

17 Mahaɗin kuma zai zama kamu goma sha huɗu, murabba’i. Faɗin da’irarsa zai zama rabin kamu, kewayen gindinsa zai zama kamu ɗaya. Matakan bagaden za su fuskanci gabas.”

18 Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce waɗannan su ne ka’idodin bagaden. A ranar da za a kafa shi don miƙa hadayun ƙonawa da yayyafa jini a kansa,

19 sai ka ba firistoci na zuriyar Zadok, masu yi mini hidima, bijimai na yin hadaya domin zunubi.

20 Za ka ɗibi jininsa, ka shafa shi a kan zankaye huɗu na bagaden, da kan kusurwa huɗu na mahaɗin da kan da’irarsa. Ta haka za ka tsarkake bagaden, ka yi kafara dominsa.

21 Za ka kuma ɗauki bijimi na yin hadaya domin zunubi, ka kai shi waje, a wurin da aka shirya a bayan Haikalin, ka ƙone shi.

22 A kan rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin yin hadaya don zunubi, bagaden kuma zai tsarkaka, kamar yadda aka tsarkake shi da bijimin.

23 Sa’ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa bijimi da rago marar lahani.

24 Za ka kawo su a gaban Ubangiji, firistoci za su barbaɗe su da gishiri, su miƙa su hadayar ƙonawa ga Ubangiji.

25 Kowace rana za ka riƙa miƙa akuya, da bijimi, da rago, marasa lahani domin yin hadaya don zunubi, har kwana bakwai.

26 Za su yi kafara har kwana bakwai don su tsarkake bagaden, su keɓe shi.

27 Sa’ad da suka cika kwanakin nan bakwai, sa’an nan a kan rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayun ƙonawa da na salama a kan bagaden. Ni kuwa zan karɓe ku, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 44

Hidimar Haikali

1 Ya kuma komo da ni ƙofar waje ta Haikali wadda take wajen gabas. Ƙofar kuwa tana rufe.

2 Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofa za ta kasance a rufe, ba za a buɗe ta ba, ba wanda kuma zai shiga ta cikinta, gama Ubangiji Allah na Isra’ila ya shiga ta cikinta, saboda haka za ta kasance a rufe.

3 Sai dai ɗan sarki zai zauna a cikinta ya ci abinci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin ƙofar, ya kuma fita ta wannan shirayi.”

4 Sa’an nan ya kawo ni a gaban haikalin ta hanyar ƙofar arewa. Da na duba, na ga zatin Ubangiji cike da Haikalin, sai na faɗi rubda ciki.

5 Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka gani da idanunka, ka kuma ji da kunnuwanka dukan abin da zan faɗa maka a kan dukan ka’idodin Haikalin Ubangiji da dukan dokokinsa. Ka lura sosai da waɗanda aka yardar musu su shiga Haikalin, da waɗanda ba a yarda musu su shiga ba.

6 “Ka ce wa ‘yan tawaye, mutanen Isra’ila, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Ku daina ayyukanku na banƙyama.

7 Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa’ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama.

8 Ba ku lura da hidimomina masu tsarki ba, amma kuka sa baƙi su lura da wurina mai tsarki.”’

9 Ubangiji Allah ya ce, “Ba wani baƙo marar imani da marar kaciya, daga cikin dukan baƙin da suke cikin jama’ata Isra’ila da zai shiga wurina mai tsarki.

10 “Amma Lawiyawa waɗanda suka yi nisa da ni, suka rabu da ni, suna bin gumakansu, sa’ad da mutanen Isra’ila suka karkata, za su ɗauki alhakin muguntarsu.

11 Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima.

12 Da yake sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra’ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu.

13 Ba za su zo kusa da ni a matsayin firistoci don su yi mini hidima ba. Ba za su zo kusa da abubuwana masu tsarki ba, amma za su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.

14 Amma duk da haka zan sa su lura da Haikalin, su yi dukan hidimomin da za a yi a cikinsa.

15 “Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa’ad da mutanen Isra’ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16 Za su shiga Wuri Mai Tsarki, su kusaci teburina, su yi mini hidima, su kuma kiyaye umarnina.

17 Sa’ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, sai su sa rigunan lilin, kada su sa abin da aka yi shi da ulu, sa’ad da suke hidima a ƙofofin fili na can ciki, da cikin Haikalin.

18 Za su naɗa rawunan lilin, su sa wandunan lilin. Kada su sa abin da zai sa su yi zuffa.

19 Sa’ad da suka fita zuwa filin da yake waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa’an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.

20 “Ba za su aske kansu ba, ba kuma za su bar zankayensu su yi tsayi ba, sai su sausaye gashin kansu.

21 Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki.

22 Ba za su auri gwauruwa ba, wato wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, sai budurwa daga zuriyar Isra’ila, ko kuwa matar firist wanda ya rasu.

23 “Za su koya wa jama’ata bambancin halal da haram, su kuma nuna musu yadda za su rarrabe tsakanin tsattsarka da marar tsarki.

24 Za su zama masu raba gardama, za su yanke magana bisa ga doka. Za su kiyaye idodina bisa ga tsarinsu. Za su kuma kiyaye ranakun Asabar masu tsarki.

25 “Ba za su kusaci gawa ba, don kada su ƙazantar da kansu, amma saboda mahaifi, ko mahaifiya, ko ɗa, ko ‘ya, ko ‘yar’uwar da ba ta kai ga yin aure ba, ko ɗan’uwa, sa iya ƙazantar da kansu.

26 Bayan ya tsarkaka, sai ya dakata har kwana bakwai.

27 A ranar da zai shiga Wuri Mai Tsarki, can fili na ciki, domin ya yi hidima a wurin, sai ya miƙa hadayarsa don zunubi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

28 “Ba za su sami rabon gādo ba, gama ni ne rabon gādonsu. Ba za ku ba su abin mallaka a cikin Isra’ila ba, ni ne abin mallakarsu.

29 Za su ci hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya domin laifi, kowane keɓaɓɓen abu kuma cikin Isra’ila zai zama nasu.

30 Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku.

31 Firistoci ba za su ci mushen kowane irin tsuntsu ko dabba ba, ba kuma za su ci waɗanda wata dabba ta kashe ba.”

Categories
EZ

EZ 45

Yankin Ƙasar da Za a Keɓe wa Ubangiji

1 “Sa’ad da kuka rarraba ƙasar gādo, sai ku keɓe wa Ubangiji wani wuri domin ya zama yanki mai tsarki, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000]. Dukan yankin zai zama wuri mai tsarki.

2 Daga cikin wannan, murabba’i mai tsawo kamu ɗari biyar, da faɗi ɗari biyar, zai zama wuri mai tsarki, fili kuma mai kamu hamsin zai kewaye wurin nan mai tsarki.

3 A cikin yanki mai tsarki za ka auna tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], inda Wuri Mafi Tsarki zai kasance.

4 Wannan yanki shi ne zai zama wuri mai tsarki na ƙasar. Zai zama na firistoci waɗanda suke hidima a cikin Haikali, waɗanda suke kusatar Ubangiji don su yi masa hidima. Wurin zai zama wurin gina gidajensu da kuma wuri mai tsarki domin Haikalin.

5 Wani sashi kuma mai tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], da faɗi kamu dubu goma [10,000], zai zama na Lawiyawa masu hidima cikin Haikalin, zai zama wurin da za su mallaka, su zauna a ciki.

6 Za ku tsaga wa birnin hurumi mai fāɗi kamu dubu biyar, da tsawo kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], rabe da yankin nan mai tsarki. Hurumin zai zama na mutanen Isra’ila duka.”

Ƙasar Sarki

7 “Ƙasar da take a sashin yankin nan mai tsarki, da hurumin birnin, zai zama na sarki. Zai zama hannun riga da yanki mai tsarki da hurumin birnin a wajen yamma da gabas. Tsawonta zai zama daidai da yanki ɗaya na yankunan kabilan. Za ta miƙe daga yamma zuwa iyakar ƙasar daga gabas.

8 Wannan zai zama yankin ƙasarsa a cikin Isra’ila. Sarakunana kuma ba za su ƙara zaluntar mutanena ba, amma za su ba mutanen Isra’ila ƙasar bisa ga kabilansu.”

Ma’aunai na Gaskiya

9 “Ni Ubangiji Allah na ce ku sarakunan Isra’ila, danniya da zaluncin da kuke yi sun isa! Ku yi shari’a bisa ga gaskiya da adalci, ku bar korar mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.

10 “Sai ku kasance da ma’aunai na gaskiya, kamar su mudu da garwa.

11 “Kwanon awo na mudu da na garwa girmansu ɗaya ne. Garwa goma ganga guda ne. Ganga ita ce za ta zama fitaccen ma’auni.

12 “Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”

Hadayu da Sadakoki

13 “Wannan ita ce bayarwar da za ku yi. Za ku ba da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta alkama, da ɗaya daga cikin shida na mudu daga kowace ganga ta sha’ir.

14 Za ku ba da ɗaya daga cikin goma ta garwa daga kowace ganga ta mai. Ganga tana cin garwa goma.

15 Za ku ba da tunkiya ɗaya daga kowane garke mai tumaki ɗari biyu, a cikin Isra’ila.

“Waɗannan su ne hadayu na gari, da na ƙonawa, da na salama, domin a yi musu kafara, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16 “Dukan mutanen ƙasar za su yi wannan bayarwar domin Sarkin Isra’ila.

17 Sarki ne da nawayar ba da hadayun ƙonawa, da na gari, da na sha a lokacin idodi da na amaryar wata, da ranakun Asabar, da lokacin dukan ƙayyadaddun idodin mutanen Isra’ila. Zai kuma ba da hadayu don zunubi da na salama domin a yi wa mutanen Isra’ila kafara.”

Idin Ƙetarewa

18 “Ni Ubangiji Allah na ce, rana ta fari ga watan fari, za ku ɗauki bijimi marar lahani don a tsarkake Haikalin.

19 Firist zai ɗibi jinin hadaya domin zunubi ya shafa shi a madogaran ƙofar Haikalin, da kusurwa huɗu na dakalin bagaden, da ginshiƙan ƙofar fili na can ciki.

20 Za ku yi haka kuma a rana ta bakwai ga watan, saboda wanda ya yi laifi da kuskure, ko da rashin sani. Ta haka ne za ku yi wa Haikalin kafara.

21 “A kan rana ta goma sha huɗu ga watan fari kuma za ku kiyaye Idin Ƙetarewa. Za ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai.

22 A ranar, sarki zai ba da bijimi domin kansa da jama’ar ƙasar, saboda yin hadaya don zunubi.

23 A ranaku bakwai na Idin, zai ba da bijimi bakwai da raguna bakwai marasa lahani hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Kowace rana kuma zai ba da bunsuru hadaya don zunubi.

24 Zai kuma ba da hadaya ta gari, mudu guda domin kowane bijimi, da mudu guda domin kowane rago, da wajen kwalaba shida na mai tare da kowane mudu.

25 “A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, zai kuma ba da abubuwan nan har kwana bakwai domin yin hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari game da mai.”

Categories
EZ

EZ 46

Sarki da Hidimomin Idodi

1 “Ni Ubangiji Allah na ce za a rufe ƙofar fili ta can ciki wadda take fuskantar gabas dukan ranaku shida na aiki, amma za a buɗe ta a ranar Asabar da a amaryar wata.

2 Sarki zai shiga ta ƙofar shirayi daga waje, sa’an nan ya tsaya kusa da ginshiƙin ƙofar. Sai firistoci su miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadayunsa na salama, shi kuwa ya yi sujada s bakin ƙofar, sa’an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da maraice.

3 Jama’ar ƙasar za su yi wa Ubangiji sujada a bakin wannan ƙofa a ranakun Asabar da a amaryar wata.

4 Hadaya ta ƙonawa da sarki zai miƙa wa Ubangiji a ranar Asabar ‘yan raguna shida ne da rago ɗaya marasa lahani.

5 Gārin hadaya da za a yi tare da rago wajen garwa guda ne. Wanda za a yi tare da ‘yan raguna kuwa zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da mai wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta gari.

6 A amaryar wata kuwa zai miƙa bijimi, da ‘yan raguna shida, da rago, dukansu marasa lahani.

7 Gārin hadayar da za a yi tare da bijimin wajen garwa guda ne, haka kuma gari na wadda za a yi tare da ragon, da gari na wadda za a yi tare da ‘yan raguna kuma, zai zama gwargwadon ƙarfinsa. Zai ba da man zaitun wajen kwalaba shida domin kowace garwa ta garin.

8 Sa’ad da sarki zai shiga, sai ya shiga ta ƙofar shirayin, ya kuma fita ta nan.

9 “Sa’ad da jama’ar ƙasar sun zo yi wa Ubangiji sujada a lokatan ƙayyadaddun idodi, wanda ya shiga ta ƙofar arewa, sai ya fita ta ƙofar kudu. Wanda kuma ya shiga ta ƙofar kudu, sai ya fita ta ƙofar arewa. Kada kowa ya fita ta ƙofar da ya shiga, amma sai kowa ya fita ta akasin ƙofar da ya shiga.

10 Sa’ad da suka shiga, sai sarki ya shiga tare da su, sa’ad da suka fita kuma, sai ya fita.

11 A lokacin idodi da ƙayyadaddun lokatai, gārin hadayar da za a yi tare da bijimi wajen garwa guda ne, haka kuma na wadda za a yi tare da ragon, na wadda za a yi tare da ‘yan ragunan kuwa, sai mutum ya kawo gwargwadon ƙarfinsa. A kuma kawo wajen kwalaba shida na man zaitun domin kowace garwa ta gari.

12 “Sa’ad da sarki ya kawo hadayar ƙonawa ko hadayar salama ta yardar rai ga Ubangiji, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai kuwa miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko ta salama kamar yadda yakan yi a ranar Asabar. Bayan da ya fita, sai a rufe ƙofa.

13 “Kowace safiya za a yi hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji da ɗan rago bana ɗaya marar lahani.

14 Tare da hadaya ta ƙonawa, za a ba da wajen ɗaya bisa shida na garwar gari, da kwalaba biyu na man zaitun don cuɗa gari, domin a yi hadaya ga Ubangiji. Wannan ita ce ka’idar hadaya ta ƙonawa ta yau da kullum.

15 Za a ba da ɗan rago, da gari, da mai, kowace safiya domin yin hadaya ta ƙonawa.

16 “Ni Ubangiji Allah na ce, idan sarki ya yi wa wani daga cikin ‘ya’yansa kyauta daga cikin gādonsa, sai kyautar ta zama ta ‘ya’yansa, dukiyarsu ce ta gādo.

17 Amma idan sarki ya yi wa wani daga cikin barorinsa kyauta daga cikin gādonsa, kyautar za ta zama tasa har shekarar ‘yantarwa, sa’an nan kyautar za ta koma a hannun sarki. ‘Ya’yansa maza ne kaɗai za su riƙe kyauta daga cikin gādonsa din din din.

18 Kada sarki ya ƙwace rabon gādon jama’a, ya hana musu. Sai ya ba ‘ya’yansa maza rabon gādo daga cikin abin da yake nasa, amma kada ya ƙwace wa jama’ata abin da suka mallaka har su warwatse.”

19 Sai mutumin ya bi da ni ta hanyar da take gefen ƙofa mai fuskantar arewa, wajen jerin tsarkakakkun ɗakuna na firistoci, waɗanda suke fuskantar arewa. Na kuma ga wani wuri daga can ƙurewar yamma.

20 Sai ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya domin laifi, da hadaya domin zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gāri, domin kada su kai su a filin waje, su sa wa mutane tsarki.”

21 Ya kuma kai ni a farfajiyar waje, ya bi da ni zuwa kusurwa huɗu na farfajiya. Akwai ɗan fili a kowace kusurwa.

22 Girman kowane ɗan fili tsawonsa kamu arba’in ne, faɗin kuma kamu talatin.

23 A cikin kowane ɗan fili na kusurwa huɗu ɗin akwai jerin duwatsu. Aka gina murhu ƙarƙashin jerin duwatsun.

24 Sa’an nan ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a Haikali za su dafa hadayun da jama’a suka kawo.”

Categories
EZ

EZ 47

Kogin da Yake Malalowa daga Haikali

1 Ya komo da ni zuwa ƙofar Haikalin, sai ga ruwa yana bulbulowa daga ƙarƙashin bakin ƙofar Haikalin a wajen gabas, gama Haikalin na fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa daga gefen kudancin bakin ƙofar Haikalin, a kudancin bagaden.

2 Sai ya fito da ni ta hanyar ƙofar arewa, ya kewaya da ni zuwa ƙofar waje wadda take fuskantar gabas. Ruwan kuwa yana gangarowa kaɗan kaɗan daga wajen kudu.

3 Mutumin ya nufi wajen gabas da ma’auni a hannunsa, ya auna kamu dubu, sa’an nan ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan ya kama ni idon ƙafa.

4 Sai kuma ya auna kamu dubu, ya sa ni in haye ruwan. Zurfin ruwan kuwa ya kama ni gwiwa. Sai ya sāke auna kamu dubu, ya sa in haye ruwan, sai zurfin ruwan ya kai ga kama ni gindi.

5 Ya sāke auna kamu dubu kuma, sai ruwan ya zama kogi har ban iya in haye ba, gama ruwan ya hau, ya zama da zurfin da ya isa ninƙaya. Ya zama kogin da ba za a iya hayewa ba.

6 Sai ya tambaye ni, ya ce. “Ɗan mutum, ka ga wannan?”

Sa’an nan ya komo da ni zuwa gāɓar kogin.

7 Sa’ad da nake tafiya, sai na ga itatuwa da yawa a kowace gāɓar kogin.

8 Ya kuma ce mini, “Wannan ruwa yana gangarowa zuwa wajen gabas har zuwa cikin Araba. Zai shiga ruwan teku marar gudu, ruwan tekun kuwa zai zama ruwan daɗi.

9 Kowace halitta mai rai da take cikin wannan ruwa za ta rayu. Za a sami kifaye da yawa a ciki, domin wannan ruwa zai kai wurin ruwan tekun, zai kuwa zama ruwan daɗi. Duk inda ruwan nan ya tafi kowane abu zai rayu.

10 Masunta za su tsaya a gāɓar tekun daga En-gedi zuwa En-eglayim. Gāɓar teku za ta zama wurin shanya taruna. Za a sami kifaye iri iri a cikinta kamar kifaye na Bahar Rum.

11 Amma ruwan fadamunsa ba zai yi daɗi ba, za a bar shi a gishirinsa.

12 A kowace gāɓar kogin, itatuwa iri iri na abinci za su yi girma. Ganyayensu ba za su bushe ba, itatuwan kuma ba za su fasa yin ‘ya’ya ba, amma su za su yi ta bayarwa a kowane wata, gama ruwansu yana malalowa daga Haikalin. ‘Ya’yansu abinci ne, ganyayensu kuwa magani ne.”

Iyakar Ƙasar

13 Ubangiji Allah ya ce, “Waɗannan su ne kan iyaka da za su raba ƙasar gādo ga kabilan Isra’ila goma sha biyu. Yusufu zai sami rabo biyu.

14 Za ku raba daidai, gama na rantse zan ba kakanninku wannan ƙasa, za ta kuwa zama gādonku.

15 “A wajen arewa, iyakar za ta kama daga Bahar Rum, ta bi ta hanyar Hetlon zuwa Zedad,

16 da Hamat, da Berota, da Sibrayim, wadda take a iyakar tsakanin Dimashƙu da Hamat, har zuwa Hazer-hattikon wadda take iyakar Hauran.

17 Iyakar za ta bi daga teku zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu. Iyakar Hamat tana wajen arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.

18 “A wajen gabas, iyakar za ta kama daga Hazar-enan tsakanin Hauran da Dimashƙu, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra’ila zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.

19 “A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.

20 “A wajen yamma, Bahar Rum shi ne iyakar zuwa ƙofar Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

21 “Za ku kuwa raba ƙasar a tsakaninku bisa ga kabilan Isra’ila.

22 Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da suke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi ‘ya’ya a cikinku. Za su zama kamar ‘ya’yan Isra’ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra’ila,

23 a cikin kabilar da baƙon yake zaune, nan ne za ku ba shi nasa gādo, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Categories
EZ

EZ 48

Rarraba Ƙasar

1 “Ga sunayen kabilan da rabon gādonsu. Yankin Dan, shi ne daga iyakar arewa daga tekun. Ya bi ta Hetlon zuwa ƙofar Hamat, har zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu daga arewa, daura da Hamat. Ya zarce daga gabas zuwa yamma.

2 Yankin Ashiru yana kusa da yankin Dan, daga gabas zuwa yamma.

3 Yankin Naftali yana kusa da yankin Ashiru daga gabas zuwa yamma.

4 Yankin Manassa yana kusa da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.

5 Yankin Ifraimu yana kusa da yankin Manassa daga gabas zuwa yamma.

6 Yankin Ra’ubainu yana kusa da yankin Ifraimu daga gabas zuwa yamma.

7 Yankin Yahuza yana kusa da yankin Ra’ubainu daga gabas zuwa yamma.

8 “Kusa da yankin Yahuza daga gabas zuwa yamma, sai yankin da za ku keɓe. Faɗinsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], tsawonsa kuma daidai da tsawon yankunan kabilai daga gabas zuwa yamma. Haikali zai kasance a tsakiyar yankin.

9 “Yankin da za ku keɓe wa Ubangiji, tsawonsa zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗinsa kuwa kamu dubu goma [10,000].

10 Wannan tsattsarkan yanki shi ne rabon firistoci. Tsawonsa wajen arewa, kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] ne, faɗinsa a wajen yamma kuwa, kamu dubu goma [10,000] ne, a wajen gabas faɗinsa kamu dubu goma [10,000], a wajen kudu tsawonsa kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000]. Haikalin Ubangiji zai kasance a tsakiyarsa.

11 Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci daga zuriyar Zadok waɗanda suka kiyaye umarnina, ba su karkace kamar yadda Lawiyawa suka yi lokacin da jama’ar Isra’ila suka karkace ba.

12 Zai zama rabonsu daga tsattsarkan yankin ƙasar da take kusa da yankin Lawiyawa.

13 Gab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuma kamu dubu goma [10,000]. Tsawonsa duka zai zama kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], faɗi kuwa kamu dubu goma [10,000].

14 Daga cikinsa ba za su sayar ba, ko su musayar, ba kuma za su jinginar da wannan keɓaɓɓen yankin ƙasa ba, gama tsattsarka ne na Ubangiji.

15 “Ragowar yankin mai faɗin kamu dubu biyar [5,000], da tsawon kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], zai zama hurumin birnin, inda za a yi gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar yankin.

16 Ga yadda girman birnin zai kasance, a wajen arewa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen kudu kuwa kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen gabas kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500], a wajen yamma kuma kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500].

17 Birnin zai kasance da hurumi a kewaye da shi. A wajen gabas kamu metan da hamsin, a wajen yamma kamu metan da hamsin, a wajen kudu kamu metan da hamsin, a wajen arewa kuma kamu metan da hamsin.

18 Ragowar tsawon yankin da yake gab da tsattsarkan yankin, zai zama kamu dubu goma [10,000] a wajen gabas, a wajen yamma kamu dubu goma [10,000]. Amfanin da yankin zai bayar, zai zama abincin ma’aikatan birnin.

19 Ma’aikatan birnin za su samu daga dukan kabilan Isra’ila, za su noma yankin.

20 Dukan yankin da za ku keɓe zai zama murabba’i mai kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000], wato tsattsarkan yankin tare da hurumin birnin.

21 “Ragowar kowane gefe na tsattsarkan yankin da hurumin birnin, zai zama na sarki. Tun daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] na tsattsarkan yankin, zuwa iyakar da take wajen gabas, daga kamu dubu ashirin da dubu biyar [25,000] kuma zuwa iyakar wajen yamma, hannun riga da yankunan kabilan zai zama na sarki. Tsattsarkan yankin da wuri mai tsarki na Haikali za su kasance a tsakiyarsa.

22 Rabon Lawiyawa da hurumin birnin za su kasance a tsakiyar yankin da yake na ɗan sarki. Yankin ɗan sarki zai kasance a tsakanin yankin Yahuza da yankin Biliyaminu.

23 “Sauran kabilan kuwa za su samu. Biliyaminu zai sami yankinsa daga gabas zuwa yamma.

24 Yankin Saminu yana kusa da yankin Biliyaminu daga gabas zuwa yamma.

25 Yankin Issaka yana kusa da yankin Saminu daga gabas zuwa yamma.

26 Yankin Zabaluna yana kusa da yankin Issaka daga gabas zuwa yamma.

27 Yankin Gad yana kusa da yankin Zabaluna daga gabas zuwa yamma.

28 “Kusa da yankin Gad zuwa kudu, iyakar za ta bi ta Tamar zuwa ruwan Meriba-kadesh, sa’an nan ta bi rafin Masar zuwa Bahar Rum.”

29 Ubangiji ya ce, “Wannan ita ce hanyar da za ku raba gādo tsakanin kabilan Isra’ila. Waɗannan kuwa su ne yankunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Ƙofofin Birni

30 “Ƙofofin birnin a gefen arewa, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500] ne.

31 Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Ra’ubainu, da Ƙofar Yahuza, da Ƙofar Lawi. Ana kiran sunayen ƙofofin birnin da sunayen kabilan Isra’ila.

32 A gefen gabas, kamu dubu huɗu ne da ɗari biyar [4,500]. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Yusufu, da Ƙofar Biliyaminu, da Ƙofar Dan.

33 A gefen kudu, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500]. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Saminu, da Ƙofar Issaka, da Ƙofar Zabaluna.

34 A gefen yamma, kamu dubu huɗu da ɗari biyar [4,500] ne. Ƙofofi uku ne, wato Ƙofar Gad, da Ƙofar Ashiru, da Ƙofar Naftali.

35 Da’irar birnin kamu dubu goma sha takwas [18,000] ne. Daga wannan lokaci za a kira birnin, ‘Ubangiji Yana Nan!”’