Categories
FAR

FAR 41

Yusufu Ya Fassara wa Fir’auna Mafarkansa

1 Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ma ya yi mafarki, ga shi, yana tsaye a bakin kogin Nilu,

2 sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul suka fito daga Nilu, suka yi kiwo cikin iwa.

3 Ga kuma waɗansu shanu bakwai munana ramammu suka fito daga cikin Nilu a bayansu, suka tsaya kusa da waɗancan shanu a bakin Nilu.

4 Sai shanun nan munana ramammu suka cinye shanun nan bakwai masu sheƙi, masu ƙibar. Sai Fir’auna ya farka.

5 Barci kuma ya kwashe shi, ya sāke yin mafarki a karo na biyu, sai zangarku bakwai masu kauri kyawawa suna girma a kara gudu.

6 Ga shi kuma, a bayansu waɗansu zangarku bakwai suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar.

7 Sai siraran zangarkun suka haɗiye zangarkun nan bakwai masu kauri kyawawa. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne.

8 Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir’auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.

9 Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau, na tuna da laifofina.

10 Sa’ad da ka yi fushi da barorinka, ka sa ni da shugaban masu tuya cikin kurkukun da yake a cikin gidan shugaban masu tsaron fāda,

11 muka yi mafarki dare ɗaya, ni da shi, kowane mutum da irin tasa fassarar mafarkin.

12 Akwai wani Ba’ibrane, ɗan saurayi, tare da mu, bawan shugaban masu tsaron fāda, sa’ad da muka faɗa masa sai ya fassara mana mafarkanmu, ya yi wa kowannenmu fassara bisa kan mafarkinsa.

13 Yadda ya fassara mana haka kuwa ya zama, aka komar da ni matsayina, mai tuya kuwa aka rataye shi.”

14 Sai Fir’auna ya aika a kirawo Yusufu, da gaggawa suka fito da shi daga cikin kurkuku. Da Yusufu ya yi aski, ya sāke tufafinsa ya zo gaban Fir’auna.

15 Fir’auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.”

16 Yusufu ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir’auna da kyakkyawar amsa.”

17 Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, a cikin mafarkina ina tsaye a bakin Kogin Nilu,

18 ga shanu bakwai, masu sheƙi masu ƙiba suka fito daga cikin Nilu suna kiwo cikin iwa.

19 Sai waɗansu shanu bakwai ƙanjamammu, munana, ramammu, irin waɗanda ban taɓa ganinsu a ƙasar Masar ba, suka fito bayansu.

20 Sai ramammun, munanan shanun suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba na farko,

21 amma da suka haɗiye su, ba wanda zai iya sani sun haɗiye su, gama suna nan a ramammunsu kamar yadda suke a dā. Sai na farka.

22 Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda,

23 zangarku bakwai kuma busassu sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar, suka fito a bayansu.

24 Siraran zangarkun kuwa suka haɗiye zangarkun nan bakwai kyawawa masu kauri. Na faɗa wa bokaye, amma ba wanda ya iya yi mini fassararsa.”

25 Yusufu ya ce wa Fir’auna, “Mafarkin Fir’auna ɗaya ne, Allah ya bayyana wa Fir’auna abin da yake shirin aikatawa.

26 Waɗannan shanu bakwai, shekaru bakwai ne, kyawawan zangarkun nan bakwai kuma shekaru bakwai ne, mafarkin ɗaya ne.

27 Ramammun shanun nan bakwai da suka fito a bayansu shekaru bakwai ne, busassun zangarkun nan bakwai waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar kuwa, shekaru bakwai ne na yunwa.

28 Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna, Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin aikatawa.

29 Za a yi shekara bakwai cike da ƙoshi a ƙasar Masar duka,

30 amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar.

31 Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar.

32 Maimaitawar mafarkin nan na Fir’auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.

33 “Yanzu fa bari Fir’auna ya zaɓi mutum mai basira, mai hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar.

34 Bari Fir’auna ya ci gaba da naɗa shugabanni bisa ƙasa, don su tattara humushin amfanin ƙasar Masar na shekarun nan bakwai na ƙoshi.

35 Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir’auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi.

36 Wannan abinci zai zama ajiya domin ƙasar, kariyar shekaru bakwai na yunwa, waɗanda za a yi cikin ƙasar Masar, domin kada ƙasar ta ƙare saboda yunwar.”

An Naɗa Yusufu Mai Mulki a Masar

37 Fir’auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara.

38 Sai Fir’auna ya ce wa fādawansa, “Mā iya samun mutum irin wannan, wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”

39 Domin haka Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka,

40 za ka shugabanci gidana, bisa ga cewarka za a mallaki jama’ata, sai dai da sarauta kaɗai nake gaba da kai.”

41 Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ga shi, na sa ka bisa dukan ƙasar Masar.”

42 Sai Fir’auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya,

43 ya kuma sa shi ya hau karusarsa ta biyu, suka yi ta shela a gabansa, “Ku ba da hanya.” Ta haka fa ya sa ya zama mai mulki bisa dukan ƙasar Masar.

44 Har yanzu dai Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ni ne Fir’auna, ba mutumin da zai ɗaga hannu ko ƙafa cikin dukan ƙasar Masar idan ba da izninka ba.”

45 Fir’auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat ‘yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.

46 Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir’auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir’auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.

47 A cikin shekaru bakwai ɗin nan na ƙoshi, ƙasa ta ba da amfani mai yawan gaske,

48 sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi.

49 Sai Yusufu ya tsiba tsaba kamar yashin teku, har ya daina aunawa domin ba ta aunuwa saboda yawa.

50 Kafin kuwa shekarun nan na yunwa, an haifa wa Yusufu ‘ya’ya biyu maza, waɗanda Asenat ‘yar Fotifera, firist na On ta haifa masa.

51 Yusufu ya raɗa wa ɗan farin suna, Manassa, yana cewa, “Gama Allah ya sa ni in manta da dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”

52 Na biyun kuma ya raɗa masa suna, Ifraimu, yana cewa, “Gama Allah ya wadata ni a cikin ƙasar wulakancina.”

53 Shekarun nan bakwai na ƙoshi da aka yi cikin ƙasar Masar sun cika,

54 aka fara shekaru bakwai na yunwa kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai aka yi yunwa cikin sauran ƙasashe duka, amma a ƙasar Masar akwai abinci.

55 Sa’ad da yunwa ta game dukan ƙasar, mutanen suka yi wa Fir’auna kuka domin abinci, sai Fir’auna ya faɗa wa Masarawa duka, ya ce, “Ku tafi wurin Yusufu, abin da duk ya faɗa muku, sai ku yi.”

56 Domin haka sa’ad da yunwar ta bazu ko’ina a ƙasar, Yusufu ya buɗe taskokin ajiya, ya yi ta sayar wa Masarawa, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.

57 Duniya duka kuwa ta zo Masar wurin Yusufu, ta sayi hatsi saboda yunwa ta tsananta a duniya duka.

Categories
FAR

FAR 42

‘Yan’uwan Yusufu sun Zo Masar Sayen Abinci

1 A sa’ad da Yakubu ya ji akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa ‘ya’yansa maza, “Me ya sa kuke zuba wa juna ido?

2 Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.”

3 Don haka ‘yan’uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar.

4 Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan’uwan Yusufu tare da ‘yan’uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.”

5 Haka nan ‘ya’yan Isra’ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan’ana.

6 Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama’ar ƙasar duka. ‘Yan’uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa.

7 Da Yusufu ya ga ‘yan’uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?”

Suka ce, “Daga ƙasar Kan’ana muka zo sayen abinci.”

8 Yusufu kuwa ya gane da ‘yan’uwansa amma su ba su gane shi ba.

9 Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”

10 Suka ce masa, “A’a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo.

11 Mu duka ‘ya’yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”

12 Yusufu ya ce musu, “A’a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”

13 Suka ce, “Mu bayinka, ‘yan’uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, ‘ya’yan mutum guda a ƙasar Kan’ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”

14 Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku.

15 Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir’auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan.

16 Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan’uwanku, amma ku, za a tsare ku, don a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya cikinku, idan ba haka ba kuwa, da ran Fir’auna, lalle ku magewaya ne.”

17 Sai ya tura su cikin waƙafi har kwana uku.

18 A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah,

19 sai ku bar ɗan’uwanku ɗaya a tsare a inda aka kulle ku. Idan amintattu ne ku, sauran kuwa su tafi su kai hatsi ga iyalanku mayunwata,

20 sa’an nan su kawo mini autanku. Ta haka za a tabbatar da maganarku, har a bar ku da rai.” Haka kuwa suka yi.

21 Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan’uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa’ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”

22 Sai Ra’ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.

23 Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu.

24 Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.

‘Yan’uwan Yusufu Suka Komo Kan’ana

25 Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu.

26 Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi.

27 Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa.

28 Ya ce wa ‘yan’uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!”

Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”

29 Sa’ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan’ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa,

30 “Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa.

31 Amma muka ce masa, ‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne.

32 Mu sha biyu ne ‘yan’uwan juna, ‘ya’ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan’ana.’

33 “Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, ‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan’uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku.

34 Ku kawo mini autanku, da haka zan sani ku ba magewaya ba ne, amma amintattu ne, zan kuma ba ku ɗan’uwanku, ku yi ta ciniki a ƙasar.’ ”

35 Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin kowannensu a cikin taikinsa. Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana.

36 Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”

37 Ra’ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe ‘ya’yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.”

38 Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan’uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”

Categories
FAR

FAR 43

‘Yan’uwan Yusufu Sun Sāke Komawa Masar da Biliyaminu

1 A halin yanzu, yunwa ta tsananta a ƙasar.

2 Sa’ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.”

3 Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, ‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.’

4 In za ka yarda ka aiki ɗan’uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci.

5 Amma idan ba haka ba, ba za mu tafi ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku ga fuskata ba idan ba ku zo tare da ɗan’uwanku ba.’ ”

6 Sai Isra’ila ya ce, “Don me kuka cuce ni, da kuka faɗa wa mutumin nan, kuna da wani ɗan’uwa?”

7 Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan’uwa?’ Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, ‘Ku zo da ɗan’uwanku’?”

8 Sai Yahuza ya ce wa Isra’ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu.

9 Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada,

10 gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.”

11 Mahaifinsu, Isra’ila ya ce musu, “In tilas haka zai zama, sai ku yi wannan, ku ɗiba daga cikin zaɓaɓɓu, mafiya kyau na albarkar ƙasar a cikin tayakanku, ku kai wa mutumin tsaraba, da ɗan man shafawa na ƙanshi da ‘yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta, da ɓaure.

12 Ku ɗauki kuɗi riɓi biyu a hannunku, ku kuma ɗauki kuɗin da aka mayar muku a tayakanku, kila kuskure ne aka yi.

13 Ku kuma ɗauki ɗan’uwanku, ku tashi ku sāke komawa wurin mutumin.

14 Allah Maɗaukaki ya ba ku tagomashi a gun mutumin, har da zai sakar muku da ɗaya ɗan’uwan nan naku tare da Biliyaminu kuma. Ni kuwa idan na yi rashi, na rasa ke nan.”

15 Sai mutane suka ɗauki tsarabar, suka kuma ɗauki riɓin kuɗin a hannunsu tare da Biliyaminu. Suka tashi suka gangara zuwa Masar, suka shiga wurin Yusufu.

16 Sa’ad da Yusufu ya ga Biliyaminu tare da su, ya faɗa wa mai hidimar gidansa, ya ce, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.”

17 Mutumin kuwa ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa, ya shigo da mutanen a gidan Yusufu.

18 Mutanen suka tsorata sabili da an kawo su a cikin gidan Yusufu, sai suka ce, “Ai, saboda kuɗin da aka mayar mana cikin tayakanmu a zuwanmu na farko, shi ya sa aka shigar da mu, domin ya nemi hujja a kanmu, ya fāɗa mana, ya maishe mu bayi, ya kuma ƙwace jakunanmu.”

19 Sai suka hau wurin mai hidimar gidan Yusufu, suka yi magana da shi a ƙofar gida,

20 suka ce, “Ya shugaba, mun zo a karo na farko sayen abinci,

21 amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin kowannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su,

22 ga waɗansu kuɗin kuma mun riƙo a hannunmu, mun gangaro mu ƙara sayen abinci. Ba mu san wanda ya sa kuɗin nan namu a tayakanmu ba.”

23 Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu.

24 Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa’an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna,

25 sai suka shirya tsarabar, domin Yusufu yana zuwa da tsakar rana, saboda sun ji, wai zai ci abinci a nan.

26 Sa’ad da Yusufu ya koma gida, suka kawo tsarabar da suka riƙo masa cikin gida, suka sunkuya har ƙasa a gabansa.

27 Ya tambayi lafiyarsu ya ce, “Mahaifinku yana lafiya, tsohon nan da kuka yi magana a kansa? Yana nan da rai?”

28 Sai suka amsa, “Bawanka, mahaifinmu yana lafiya, har yanzu yana da rai.” Suka sunkuya suka yi masa mubaya’a.

29 Sai ya ɗaga idanunsa, ya ga ɗan’uwansa Biliyaminu, ɗan da mahaifiyarsa ta haifa, ya ce, “Wannan shi ne auta naku, wanda kuka yi mini magana a kansa? Allah ya yi maka alheri ɗana!”

30 Da Yusufu ya ji kamar zai yi kuka sabili da zuciyarsa tana begen ɗan’uwansa, sai ya gaggauta ya nemi wurin yin kuka. Ya shiga ɗakinsa, a can ya yi kuka.

31 Sa’an nan ya wanke fuskarsa, ya fito ya ɗaure, ya umarta a kawo abinci.

32 Aka hidimta masa shi kaɗai, su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sukan ci abinci tare da Ibraniyawa ba, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa.

33 Aka zaunar da ‘yan’uwan Yusufu a gaban Yusufu bisa ga shekarunsu na haihuwa, daga babba zuwa ƙarami. ‘Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.

34 Daga teburin da yake a gabansa aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Biliyaminu ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.

Categories
FAR

FAR 44

Finjalin Yusufu a Taikin Biliyaminu

1 Yusufu ya umarci mai hidimar gidansa, ya ce, “Cika tayakan mutanen nan da abinci iyakar yadda za su iya ɗauka, ka kuma sa kuɗin kowanne a bakin taikinsa,

2 ka sa finjalina na azurfa a bakin taikin autan, tare da kuɗinsa na hatsin.” Sai ya yi kamar yadda Yusufu ya faɗa masa.

3 Gari na wayewa aka sallami mutanen da jakunansu.

4 Tun ba su riga suka yi nisa da garin ba, Yusufu ya ce wa mai hidimar gidansa, “Tashi, ka bi mutanen, in ka iske su ka ce musu,

5 ‘Don me kuka rama alheri da mugunta? Don me kuka sace mini finjalina na azurfa? Da shi ne mai gidana yake sha, da shi ne kuma yake yin istihara. Kun yi kuskure da kuka yi haka.’ ”

6 Lokacin da ya iske su sai ya yi musu waɗannan maganganu.

7 Suka ce masa, “Don me shugabana zai faɗi irin waɗannan maganganu? Allah ya sawwaƙe da bayinka za su aikata irin wannan!

8 Ga shi, kuɗin da muka samu a bakin tayakanmu, mun komo maka da su tun daga ƙasar Kan’ana, ta yaya fa, za mu saci azurfa ko zinariya daga gidan maigidanka?

9 Daga cikinmu barorinka, duk wanda aka sami abin a wurinsa, bari ya mutu, mu kuwa mu zama bayinka, ranka ya daɗe.”

10 Ya ce, “Bari ya zama kamar yadda kuka faɗa, shi wanda aka sami abin a wurinsa zai zama bawana, sauranku kuwa za ku tafi lafiya.”

11 Nan da nan kowa ya saukar da taikinsa ƙasa, kowa kuwa ya buɗe taikinsa.

12 Ya bincika, ya fara daga babba zuwa ƙarami, sai aka iske finjalin a cikin taikin Biliyaminu.

13 Suka kyakkece rigunansu, kowannensu kuwa ya yi wa jakinsa labtu suka koma birnin.

14 Sa’ad da Yahuza da ‘yan’uwansa suka zo gidan Yusufu, suka iske yana nan har yanzu, sai suka fāɗi ƙasa a gabansa.

15 Yusufu ya ce musu, “Wane abu ke nan kuka aikata? Ba ku sani ba, mutum kamata yakan yi istihara?”

16 Sai Yahuza ya amsa, “Me za mu ce wa shugabana? Wace magana za mu yi? Ko kuwa, ta yaya za mu baratar da kanmu? Allah ne ya tona laifin bayinka, ga mu, mu bayin shugabana ne, da mu da shi wanda aka sami finjalin a wurinsa.”

17 Amma Yusufu ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da in yi haka! Sai shi wanda aka sami finjalin a hannunsa, shi zai zama bawana, amma ku, ku yi tafiyarku lafiya zuwa wurin mahaifinku.”

Yahuza Ya Yi Gōdō domin Biliyaminu

18 Yahuza ya je wurin Yusufu ya ce, “Ya shugabana, ina roƙonka, ka bar bawanka ya yi magana a kunnuwanka, kada kuma ka bar fushinka ya yi ƙuna bisa bawanka, gama daidai da Fir’auna kake.

19 Ranka ya daɗe, ka tambaye mu, ka ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’

20 Sai muka amsa, ranka ya daɗe, muka ce, ‘Muna da mahaifi, tsoho, da ɗan tsufansa, auta, wanda ɗan’uwansa ya rasu, shi kaɗai ya ragu daga cikin mahaifiyarsa, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’

21 Sai ka ce wa barorinka, ‘Ku kawo shi wurina, don in gan shi.’

22 Ranka ya daɗe, muka kuwa ce, ‘Saurayin ba zai iya rabuwa da mahaifinsa ba, gama in ya rabu da mahaifinsa, mahaifinsa zai mutu.’

23 Sai ka amsa wa barorinka, ka ce, ‘In ba autanku ya zo tare da ku ba, ba za ku ƙara ganin fuskata ba.’

24 “Sa’ad da muka koma a wurin baranka, mahaifinmu, muka mayar masa da dukan abin da ka ce.

25 Don haka sa’ad da mahaifinmu ya ce, ‘Koma, ku sayo mana ɗan abinci,’

26 sai muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, amma idan autanmu zai tafi tare da mu, za mu gangara, gama ba dama mu ga fuskar mutumin sai ko autanmu yana tare da mu.’

27 Sa’an nan baranka, mahaifinmu, ya ce mana, ‘Kun sani ‘ya’ya biyu matata ta haifa mini,

28 ɗayan ya bar ni, na kuwa ɗauka, hakika an yayyage shi kaca kaca, gama ban ƙara ganinsa ba.

29 In kuka ɗauke wannan kuma daga gare ni, mai yiwuwa ne a kashe shi, to, za ku sa baƙin ciki ya ishe ni, da tsufana, har ya kashe ni.’

30-31 “Domin haka kuwa, yanzu, idan na koma wurin baranka, mahaifina, ba tare da saurayin ba, in har bai ga yaron tare da ni ba, zai mutu, gama ransa ya shaƙu da saurayin, barorinka kuwa za su sa baranka, mahaifinmu, ya mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa.

32 Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa ya zauna a kaina a gaban mahaifina duka raina.’

33 Domin haka fa, ina roƙonka, bari ni baranka in zama bawa gare ka, shugabana, a maimakon saurayin a bar saurayin ya koma tare da ‘yan’uwansa.

34 Gama yaya zan iya komawa wurin mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? Ina jin tsoron ganin ɓarnar da za ta auko wa mahaifina.”

Categories
FAR

FAR 45

Yusufu ya Bayyana Kansa ga ‘Yan’uwansa

1 Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa’ad da Yusufu ya bayyana kansa ga ‘yan’uwansa.

2 Ya yi kuka da ƙarfi, har Masarawa suka ji, labarin kuwa ya kai gidan Fir’auna.

3 Yusufu kuwa ya ce wa ‘yan’uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma ‘yan’uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa.

4 Yusufu ya ce wa ‘yan’uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar.

5 Yanzu fa, kada ku damu ko kuwa ku ji haushin kanku domin kun sayar da ni a nan, gama Allah ne ya aike ni a gabanku don in ceci rai.

6 Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.

7 Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa.

8 Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir’auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.

9 “Ku gaggauta, ku hau zuwa wurin mahaifina ku ce masa, ‘Ga abin da Yusufu ɗanka ya ce, “Allah ya maishe ni shugaban Masar duka, ka gangaro wurina kada ka yi wata wata.

10 Za ka zauna a ƙasar Goshen, za ka zauna kusa da ni, kai da ‘ya’yanka da jikokinka, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunanka na shanu, da dukan abin da kake da shi.

11 A nan zan cishe ka, gama akwai sauran shekara biyar masu zuwa na yunwa, don kada ka tsiyace, kai da iyalinka, da duk wanda yake tare da kai.’ ”

12 Yanzu, da idanunku kun gani, idanun ɗan’uwana Biliyaminu kuma sun gani, cewa bakina ne yake magana da ku.

13 Ku faɗa wa mahaifina dukan darajar da nake da ita a Masar da dukan abin da kuka gani. Ku gaggauta ku gangaro mini da mahaifina a nan.”

14 Sai Yusufu ya rungumi ɗan’uwansa Biliyaminu ya yi ta kuka, Biliyaminu ma ya yi kuka a bisa kafaɗun Yusufu.

15 Ya sumbaci ‘yan’uwansa duka, ya yi kuka bisansu, bayan wannan sai ‘yan’uwansa suka yi taɗi da shi.

16 Sa’ad da labari ya kai gidan Fir’auna cewa, “’Yan’uwan Yusufu sun zo,” abin ya yi wa Fir’auna da fādawansa daɗi ƙwarai.

17 Sai Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Ka faɗa wa ‘yan’uwanka su yi wannan, ‘Ku yi wa dabbobinku laftu ku koma a ƙasar Kan’ana.

18 Ku ɗauko mahaifinku da iyalanku, ku zo wurina, ni kuwa zan ba ku yankin ƙasa mafificiya a Masar, za ku ci moriyar ƙasar.’

19 Ka kuma umarce su ka ce, ‘Ku ɗauki kekunan shanu daga ƙasar Masar domin ‘yan ƙanananku da matanku, ku ɗauko mahaifinku, ku zo.

20 Kada ku damu da kayayyakinku, gama abin da yake mafi kyau duka a ƙasar Masar naku ne.’ ”

21 Haka kuwa ‘ya’yan Isra’ila suka yi. Yusufu kuma ya ba su kekunan shanu bisa ga umarnin Fir’auna, ya ba su guzuri don hanya.

22 Ga kowane ɗayansu ya ba da rigar ado, amma ga Biliyaminu ya ba da azurfa ɗari uku, da rigunan ado biyar.

23 Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa.

24 Ya sallami ‘yan’uwansa. Da suna shirin tashi, sai ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya.”

25 Suka haura daga Masar, suka zo ƙasar Kan’ana zuwa wurin Yakubu mahaifinsu.

26 Suka ce masa, “Har yanzu Yusufu yana nan da rai, shi ne kuwa mai mulki bisa ƙasar Masar duka.” Sai gabansa ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.

27 Amma sa’ad da suka faɗa masa jawaban Yusufu duka, waɗanda ya faɗa musu, sa’ad da kuma ya ga kekunan shanun da Yusufu ya aiko don a ɗauke shi, sai ruhun mahaifinsu Yakubu ya farfaɗo.

28 Isra’ila ya ce, “I, ya isa, ɗana Yusufu yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”

Categories
FAR

FAR 46

Yakubu da Iyalinsa suka Tafi Masar

1 Isra’ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku.

2 Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.”

Ya amsa ya ce, “Na’am.”

3 Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al’umma.

4 Ni kuwa zan gangara tare da kai zuwa Masar, ni kuma zan sāke haurowa tare da kai. Lokacin mutuwarka za ka mutu a hannun Yusufu.”

5 Sai Yakubu ya tashi daga Biyer-sheba, ‘ya’yan Isra’ila maza kuwa suka ɗauki mahaifinsu Yakubu, da ‘yan ƙananansu da matansu a cikin kekunan shanun da Fir’auna ya aika a ɗauko su.

6 Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan’ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka,

7 ‘ya’yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, ‘ya’yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.

8 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’ya maza na Isra’ila, wato Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra’ubainu, ɗan farin Yakubu.

9 ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza kuwa, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.

10 ‘Ya’yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan wata Bakan’aniya.

11 ‘Ya’yan Lawi, maza, su ne Gershon, da Kohat, da Merari.

12 ‘Ya’yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan’ana). ‘Ya’yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.

13 ‘Ya’yan Issaka, maza, su ne Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron.

14 ‘Ya’yan Zabaluna, maza, su ne Sered, da Elon, da Yaleyel,

15 (waɗannan su ne ‘ya’yan Lai’atu, maza, waɗanda ta haifa wa Yakubu cikin Fadan-aram, da ‘ya tasa kuma Dinatu, ‘ya’yansa mata da maza duka, mutum talatin da uku ne).

16 ‘Ya’yan Gad, maza, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, da Ezbon, da Eri, da Arodi, da Areli.

17 ‘Ya’yan Ashiru, maza, su ne Yimna, da Yishuwa, da Yishwi, da Beriya, da Sera, ‘yar’uwarsu. ‘Ya’yan Beriya, maza kuma, su ne Eber da Malkiyel.

18 Waɗannan su goma sha shida, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Zilfa, wadda Laban ya bai wa Lai’atu, ‘yarsa.

19 ‘Ya’ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu.

20 Asenat ‘yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar.

21 ‘Ya’yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na’aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar.

22 Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.

23 Hushim shi ne ɗan Dan.

24 ‘Ya’yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum.

25 Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa ‘yarsa Rahila.

26 Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan ‘ya’yansa, su mutum sittin da shida ne.

27 ‘Ya’yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba’in.

Yakubu da Iyalinsa a Masar

28 Isra’ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen,

29 sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra’ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa.

30 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.”

31 Yusufu ya ce wa ‘yan’uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir’auna, in ce masa, ‘’yan’uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā yake a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina,)

32 mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.’

33 To, sa’ad da Fir’auna zai kira ku, ya tambaye ku, ‘Mece ce sana’arku?’

34 Sai ku ce, ‘Ranka ya daɗe, mu makiyayan shanu ne tun muna ‘yan yara har zuwa yau, da mu da kakanninmu,’ don ku sami wurin zama a ƙasar Goshen, gama kowane makiyayi abin ƙyama ne ga Masarawa.”

Categories
FAR

FAR 47

1 Yusufu ya shiga ya yi magana da Fir’auna, ya ce, “Mahaifina da ‘yan’uwana, da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunan shanu, da dukan abin da suka mallaka, sun zo daga ƙasar Kan’ana, yanzu suna ƙasar Goshen.”

2 Daga cikin ‘yan’uwansa kuma ya ɗauki mutum biyar ya gabatar da su a gaban Fir’auna.

3 Sai Fir’auna ya ce wa ‘yan’uwan nan nasa, “Mece ce sana’arku?”

Suka amsa wa Fir’auna, suka ce, “Ranka ya daɗe, mu makiyaya ne, kamar yadda iyayenmu suke.”

4 Suka kuma ce wa Fir’auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan’ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”

5 Fir’auna ya ce wa Yusufu, “Mahaifinka da ‘yan’uwanka sun zo wurinka.

6 Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da ‘yan’uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”

7 Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir’auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir’auna albarka.

8 Fir’auna kuma ya ce wa Yakubu, “Nawa ne shekarun haihuwarka?”

9 Yakubu ya ce wa Fir’auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”

10 Yakubu kuwa ya sa wa Fir’auna albarka, sa’an nan ya fita daga gaban Fir’auna.

11 Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da ‘yan’uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir’auna ya umarta.

12 Yusufu ya bai wa mahaifinsa da ‘yan’uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan ‘ya’yansu.

Hidimar Yusufu a Lokacin Yunwa

13 A yanzu cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwar ta tsananta ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka matsu saboda yunwar.

14 Yusufu kuwa ya ƙwalƙwale dukan kuɗin da yake akwai a ƙasar Masar da a ƙasar Kan’ana, domin hatsin da suka saya. Yusufu kuma ya kawo kuɗin cikin gidan Fir’auna.

15 Sa’ad da aka kashe kuɗin da yake a Masar duka da na ƙasar Kan’ana, Masarawa duka suka zo wurin Yusufu, suka ce, “Ka ba mu abinci, don me za mu mutu a kan idonka? Gama kuɗinmu sun ƙare.”

16 Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.”

17 Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara.

18 Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana.

19 Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakunmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna, ka kuma ba mu iri domin mu rayu, kada mu mutu don kuma kada ƙasar ta zama kango.”

20 Ta haka Yusufu ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da saurukansu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama halaliyar Fir’auna.

21 Yusufu ya mai da jama’ar bayi daga wannan kan iyaka na Masar zuwa wancan.

22 Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir’auna ya yanka musu, da rabon da Fir’auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba.

23 Yusufu ya ce wa jama’ar, “Ga shi, a yau na saya wa Fir’auna ku da gonakinku. Yanzu fa, ga iri dominku, za ku shuka gonakin.

24 Da haka za ku ba da kashi ɗaya cikin biyar ga Fir’auna, kashi huɗu cikin biyar kuwa ya zama naku din iri na shuka a gonakinku, don kuma abincinku, da na iyalan gidanku, da na ‘yan ƙanananku.”

25 Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ko ya gamshe ka, ya shugaba, mā zama bayin Fir’auna.”

26 Sai Yusufu ya kafa doka daga wannan rana har wa yau game da ƙasar Masar wadda ta ce, Fir’auna zai sami kashi ɗaya daga cikin biyar, sai dai gonakin firistoci kaɗai ne ba su zama na Fir’auna ba.

Wasiyyar Yakubu

27 Ta haka fa Isra’ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai.

28 Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba’in da bakwai.

29 A sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, ya kira ɗansa Yusufu ya ce masa, “Idan zan sami tagomashi a idonka, ka sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka ɗau alkawari za ka aikata mini aminci da gaskiya. Kada ka binne ni a Masar,

30 amma bari in kwanta tare da kakannina, ka ɗauke ni daga Masar, ka binne ni a makabartarsu.”

Ya amsa ya ce, “Zan aikata yadda ka faɗa.”

31 Sai Yakubu ya ce, “Rantse mini.” Sai Yusufu ya rantse masa. Sa’an nan sai Isra’ila ya mai da kai bisa kan gadonsa.

Categories
FAR

FAR 48

Yakubu Ya Sa wa Ifraimu da Manassa Albarka

1 Ya zama fa bayan waɗannan al’amura, aka faɗa wa Yusufu, “Ga mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ‘ya’yansa biyu maza, Manassa da Ifraimu ya tafi ya gai da mahaifinsa.

2 Sa’ad da aka ce wa Yakubu, “Ɗanka Yusufu ya zo wurinka,” sai Yakubu ya ƙoƙarta ya tashi zaune a kan gadon.

3 Yakubu ya ce wa Yusufu, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana ya sa mini albarka,

4 ya ce mini, ‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al’ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.’

5 Yanzu fa, a kan waɗannan ‘ya’yanka maza biyu da aka haifa a Masar kafin zuwana, su nawa ne, Ifraimu da Manassa za su zama nawa, kamar yadda su Ra’ubainu da Saminu suke.

6 ‘Ya’ya waɗanda za a haifa a bayansu za su zama naka, za a kira su da sunan ‘yan’uwansu cikin gādonsu.

7 Sa’ad da nake zuwa daga Mesofotamiya, sai Rahila ta rasu a hannuna a ƙasar Kan’ana a kan hanya, ga shi kuwa, da sauran tazara kafin a kai Efrata. Na kuwa binne ta a Efrata,” wato Baitalami.

8 Sa’ad da Isra’ila ya ga ‘ya’yan Yusufu, maza, ya ce, “Su wane ne waɗannan?”

9 Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “’Ya’yana ne maza waɗanda Allah ya ba ni a nan.”

Sai ya ce, “Kawo su gare ni, ina roƙonka, domin in sa musu albarka.”

10 Yanzu fa, idanun Isra’ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su.

11 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na ‘ya’yanka.”

12 Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra’ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa.

13 Yusufu ya ɗauki su biyu ɗin, Ifraimu a hannunsa na dama zuwa hannun hagun Isra’ila, Manassa kuma a hannunsa na hagu zuwa dama na Isra’ila, ya kawo su kusa da shi.

14 Isra’ila ya miƙa hannunsa na dama, ya ɗora bisa kan Ifraimu wanda yake ƙarami, hannunsa na hagu kuma bisa kan Manassa, yana harɗe da hannuwansa, gama Manassa shi ne ɗan fari.

15 Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce,

“Allah na Ibrahim da Ishaku,

Iyayena da suka yi tafiyarsu a

gabansa,

Allah da ya bi da ni

Dukan raina har wa yau, ya sa musu

albarka.

16 Mala’ikan da ya fanshe ni

Daga dukan mugunta,

Ya sa wa samarin albarka,

Bari a dinga ambatarsu da sunana,

Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena,

Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama

taron jama’a a tsakiyar duniya.”

17 Sa’ad da Yusufu ya ga mahaifinsa ya ɗora hannun damansa a bisa kan Ifraimu, ransa bai so ba, ya ɗauke hannun mahaifinsa, domin ya kawar da shi daga kan Ifraimu zuwa kan Manassa.

18 Sai Yusufu ya ce wa mahaifinsa, “Ba haka ba ne baba, gama wannan ne ɗan fari. Sa hannunka na dama a bisa kansa.”

19 Amma mahaifinsa ya ƙi, ya ce, “Na sani, ɗana, na sani, shi ma zai zama al’umma, zai ƙasaita, duk da haka ƙanensa zai fi shi ƙasaita, zuriyarsa kuwa za ta zama taron al’ummai.”

20 Ya sa musu albarka a wannan rana, yana cewa,

“Ta gare ku Isra’ila za su sa albarka

da cewa,

‘Allah ya maishe ku kamar Ifraimu

da Manassa.’ ”

Da haka ya sa Ifraimu gaba da Manassa.

21 Isra’ila ya ce wa Yusufu, “Ga shi, ina bakin mutuwa, amma Allah zai kasance tare da kai, zai kuma sāke komar da kai ƙasar kakanninka.

22 Ni ne nake ba ka Shekem, kashi ɗaya fiye da ‘yan’uwanka, wanda na ƙwace da takobina da bakana daga hannun Amoriyawa.”

Categories
FAR

FAR 49

Faɗar Yakubu a kan ‘Ya’yansa

1 Yakubu ya kirawo ‘ya’yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa.

2 “Ku taru ku ji, ya ku ‘ya’yan

Yakubu, maza,

Ku kuma kasa kunne ga Isra’ila

mahaifinku.

3 “Ra’ubainu, kai ɗan farina

ne, ƙarfina,

Ɗan balagata, isasshe kuma, mafi

ƙarfi duka cikin ‘ya’yana.

4 Kamar ambaliyar ruwa mai fushi

kake,

Amma ba za ka zama mafi daraja

ba,

Domin ka hau gadon mahaifinka,

Sa’an nan ka ƙazantar da shi.

5 “Saminu da Lawi ‘yan’uwa ne,

Suka mori takubansu cikin ta da

hankali.

6 Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba,

Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsu

ba,

Gama cikin fushinsu suka kashe

mutane,

Cikin gangancinsu kuma suka

gurgunta bijimai.

7 La’ananne ne fushinsu domin mai

tsanani ne,

Da hasalarsu kuma, gama bala’i ce.

Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar

Yakubu,

In ɗaiɗaitar su su cikin Isra’ilawa.

8 “Yahuza, ‘yan’uwanka za su yabe

ka,

Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka,

‘Yan’uwanka za su rusuna a

gabanka.

9 Yahuza ɗan zaki ne,

Ya kashe ganima sa’an nan ya komo

wurin ɓuyarsa.

Yahuza kamar zaki yake,

Yakan kwanta a miƙe,

Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane

shi.

10 Yana riƙe da sandan mulkinsa,

Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa,

Har Shilo ya zo.

Zai mallaki dukan jama’o’i.

11 Zai ɗaure aholakinsa a kurangar

inabi,

A kuranga mafi kyau,

Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi,

Ruwan inabi ja wur kamar jini.

12 Idanunsa za su yi ja wur saboda shan

ruwan inabi,

Haƙoransa kuma su yi fari fat

saboda shan madara.

13 “Zabaluna zai zauna a gefen teku,

Zai zama tashar jiragen ruwa,

Kan iyakarsa kuma zai kai har

Sidon.

14 “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa,

Ya kwanta a miƙe tsakanin

jakunkunan shimfiɗa.

15 Saboda ya ga wurin hutawa ne mai

kyau,

Ƙasar kuma mai kyau ce,

Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa domin

ɗaukar kaya,

Ya zama bawa, yana yin aiki mai

wuya.

16 “Dan zai zama mai mulki ga

mutanensa

Kamar ɗaya daga cikin kabilan

Isra’ila.

17 Dan zai zama maciji a gefen hanya,

Zai zama kububuwa a gefen turba,

Mai saran diddigen doki

Don mahayin ya fāɗi da baya.

18 Ina zuba ido ga cetonka, ya

Ubangiji.

19 “Gad, ‘yan fashi za su kai masa hari,

Shi kuwa zai runtume su.

20 “Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfani

mai yawa,

Zai kuma yi tanadin abincin da ya

dace da sarki.

21 “Naftali sakakkiyar barewa ce,

Mai haihuwar kyawawan ‘ya’ya.

22 “Yusufu jakin jeji ne,

Jakin jeji a gefen maɓuɓɓuga

Aholakan jeji a gefen tuddai.

23 Maharba suka tasar masa ba tausayi

Suka fafare shi da kwari da baka.

24 Duk da haka bakunansu sun

kakkarye.

Damatsansu sun yayyage

Ta wurin ikon Allah Mai Girma na

Yakubu,

Makiyayi, Dutse na Isra’ila.

25 Ta wurin Allah na mahaifinka wanda

zai taimake ka,

Ta wurin Allah Mai Iko Dukka

wanda zai sa maka albarka

Albarkun ruwan sama daga bisa,

Da na zurfafa daga ƙarƙashin

ƙasa,

Da albarkun mama da na mahaifa.

26 Albarkun hatsi da na gari

Albarkun daɗaɗɗun duwatsu,

Abubuwan jin daɗi na madawwaman

tuddai,

Allah ya sa su zauna a kan Yusufu,

Da a goshin wanda aka raba shi da

‘yan’uwansa.

27 “Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa,

Da safe yakan cinye abin da ya

kaso,

Da maraice kuma yakan raba abin da

ya kamo.”

28 Waɗannan duka su ne kabilan Isra’ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa’ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.

Rasuwar Yakubu da Jana’izarsa

29 Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama’ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte,

30 a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.

31 A can aka binne Ibrahim da Saratu matarsa. A can kuma suka binne Ishaku da Rifkatu matarsa. A can kuma na binne Lai’atu.

32 Da saurar da kogon da yake cikinta, an saye su daga Hittiyawa.”

33 Sa’ad da Yakubu ya gama yi wa ‘ya’yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama’arsa waɗanda suka riga shi.

Categories
FAR

FAR 50

1 Yusufu kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya sumbace shi.

2 Sai Yusufu ya umarci barorinsa masu magani, su shafe gawar mahaifinsa da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe Isra’ila da maganin hana ruɓa.

3 Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi masa makoki na kwana saba’in.

4 Sa’ad da kwanakin makokin suka wuce, Yusufu ya yi magana da iyalin gidan Fir’auna, ya ce, “Idan fa yanzu na sami tagomashi a wurinku, ku yi magana, ina roƙonku a gaban Fir’auna, ku ce masa,

5 ‘Sa’ad da mahaifina yake bakin mutuwa, ya sa ni in yi masa alkawari, cewa zan binne shi a kabarin da ya haƙa wa kansa a ƙasar Kan’ana.’ Don haka in ya yarda ya bar ni in je in binne mahaifina, sa’an nan in komo.”

6 Fir’auna ya amsa, ya ce, “Ka haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya rantsar da kai.”

7 Saboda haka, Yusufu ya haura ya binne mahaifinsa, tare da shi kuma dukan barorin Fir’auna suka haura, da dattawan gidan Fir’auna, da dukan dattawan ƙasar Masar,

8 da kuma dukan iyalin gidan Yusufu, da ‘yan’uwansa, da iyalin gidan mahaifinsa. Sai ‘yan ƙananansu, da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanunsu, aka bari a ƙasar Goshen.

9 Da karusai da mahayan dawakai kuma suka tafi tare da shi. Babbar ƙungiya ce ƙwarai.

10 Sa’ad da suka kai farfajiyar masussukar Atad, wanda yake wajen Urdun, a nan ne fa suka yi makoki, da babban makoki da baƙin ciki mai zafi. Aka kuwa yi kwana bakwai ana makokin mahaifinsa.

11 Sa’ad da Ka’aniyawa mazaunan ƙasar, suka ga makokin da aka yi a farfajiyar masussukar Atad, sai suka ce, “Wannan makoki mai zafi ne ga Masarawa.” Don haka aka sa wa wurin suna Abel-mizrayim, wanda yake wajen Urdun.

12 Haka ‘ya’yansa suka yi masa kamar yadda ya umarta,

13 gama ‘ya’yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan’ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.

14 Bayan da Yusufu ya binne mahaifinsa, ya koma Masar tare da ‘yan’uwansa da dukan waɗanda suka tafi tare da shi don jana’izar mahaifinsa.

Yusufu ya Tabbatar wa ‘Yan’uwansa ba zai Rama Ba

15 Sa’ad da ‘yan’uwan Yusufu suka ga mahaifinsu ya rasu, suka ce, “Mai yiwuwa ne Yusufu zai ƙi jininmu, ya sāka mana dukan muguntar da muka yi masa.”

16 Saboda haka suka aika wa Yusufu da jawabi, suka ce, “Mahaifinka ya ba da wannan umarni kafin rasuwarsa,

17 ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin ‘yan’uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa’ad da suka yi magana da shi.

18 ‘Yan’uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.”

19 Amma Yusufu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ni ba a matsayin Allah nake ba.

20 A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama’a masu yawa waɗanda suke da rai a yau.

21 Don haka kada ku ji tsoro, zan tanada muku, ku da ƙanananku.” Ta haka ya ta’azantar da su, ya yi musu magana ta kwantar da zuciya.

Rasuwar Yusufu

22 Haka fa Yusufu ya zauna a Masar, shi da iyalin gidan mahaifinsa. Yusufu kuwa ya yi shekara ɗari da goma a duniya.

23 Yusufu fa ya ga ‘ya’yan Ifraimu har tsara ta uku, aka kuma haifi ‘ya’yan Makir ɗan Manassa, aka karɓe su cikin iyalin Yusufu.

24 Yusufu kuwa ya ce wa ‘yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”

25 Sa’an nan Yusufu ya rantse wa ‘ya’yan Isra’ila da cewa, “Hakika Allah zai ziyarce ku, ku kuma sai ku haura da ƙasusuwana daga nan.”

26 Yusufu ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Sai suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Aka kuwa sa shi a akwatin gawa cikin Masar.