Categories
FIT

FIT 1

Wahalar Isra’ilawa a Masar

1 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’ya maza na Isra’ila, waɗanda suka tafi Masar tare da Yakubu, kowanne da iyalinsa.

2 Su ne Ra’ubainu, da Saminu, da Lawi, da Yahuza,

3 da Issaka, da Zabaluna, da Biliyaminu,

4 da Dan, da Naftali, da Gad, da Ashiru.

5 Zuriyar Yakubu duka mutum saba’in ne, Yusufu kuwa, an riga an kai shi Masar.

6 Ana nan sai Yusufu ya rasu, shi da dukan ‘yan’uwansa na wannan tsara.

7 Amma ‘ya’yan Isra’ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.

8 A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba.

9 Sai ya ce wa mutanensa, “Duba, jama’ar Isra’ila sun cika yawa sun fi ƙarfinmu.

10 Zo, mu san irin dabarar da za mu yi musu, don kada su riɓaɓɓanya, domin in aka faɗa mana da yaƙi, kada su haɗa kai da maƙiyanmu, su yaƙe mu, su tsere daga ƙasar.”

11 Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir’auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.

12 Amma ko da yake Masarawa sun ƙara tsananta musu, duk da haka sai suka ƙara ƙaruwa, suna ta yaɗuwa. Masarawa kuwa suka tsorata saboda Isra’ilawa.

13 Suka kuma tilasta wa Isra’ilawa su yi ta aiki mai tsanani.

14 Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.

15 Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu’a,

16 “Sa’ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”

17 Amma da yake ungozomar masu tsoron Allah ne, ba su yi yadda Sarkin Masar ya umarce su ba, amma suka bar ‘ya’ya maza da rai.

18 Don haka Sarkin Masar ya kirawo ungozomar, ya ce musu, “Me ya sa kuka bar ‘ya’ya maza da rai?”

19 Ungozomar suka ce wa Fir’auna, “Domin matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gama su masu ƙwazo ne, sukan haihu tun ungozomar ba su kai wurinsu ba.”

20 Allah kuwa ya yi wa ungozoman nan alheri. Mutanen suka riɓanya, suka ƙasaita ƙwarai.

21 Allah kuma ya ba ungozoman nan zuriya domin sun ji tsoronsa.

22 Fir’auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, “Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai.”

Categories
FIT

FIT 2

Haihuwar Musa

1 Sai wani mutum, Balawe, ya auro ‘yar Lawi.

2 Matar kuwa ta yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har wata uku.

3 Da ta ga ba za ta iya ƙara ɓoye shi ba, sai ta saƙa kwando da iwa, ta yaɓe shi da katsi, ta sa jaririn a ciki, ta ajiye shi cikin kyauro a bakin Kogin Nilu.

4 Ga ‘yar’uwarsa kuma a tsaye daga nesa don ta san abin da zai same shi.

5 Gimbiya, wato ‘yar Fir’auna, ta gangaro domin ta yi wanka a Kogin Nilu, barorinta ‘yan mata suna biye da ita a gaɓar Kogin Nilu. Da ta ga kwando a cikin kyauro, ta aiki baranyarta ta ɗauko mata shi.

6 Sa’ad da ta tuɗe kwandon ta ga jariri yana kuka. Sai ta ji tausayinsa, ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ibraniyawa ne.”

7 ‘Yar’uwar jaririn kuwa ta ce wa Gimbiya, “In tafi in kirawo miki wata daga cikin matan Ibraniyawa da za ta yi miki renon ɗan?”

8 Sai Gimbiya ta ce mata, “Je ki.” Yarinyar kuwa ta tafi ta kirawo mahaifiyar jaririn.

9 Da ta zo, sai Gimbiya ta ce mata, “Dauki wannan jariri, ki yi mini renonsa, zan biya ki ladanki.” Matar kuwa ta ɗauki jaririn ta yi renonsa.

10 Da jaririn ya yi girma sai ta kai shi wurin Gimbiyar. Yaro kuwa ya zama tallafinta. Ta raɗa masa suna Musa, gama ta ce, “Domin na tsamo shi daga cikin ruwa.”

Musa Ya Gudu zuwa Madayana

11 Ana nan wata rana, sa’ad da Musa ya yi girma, ya tafi wurin mutanensa, sai ya ga yadda suke shan wahala. Ya kuma ga wani Bamasare yana dūkan Ba’ibrane, ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa.

12 Da ya waiwaya, bai ga kowa ba, sai ya kashe Bamasaren, ya turbuɗe shi cikin yashi.

13 Kashegari da ya sāke fita, sai ya ga waɗansu Ibraniyawa biyu suna faɗa da juna. Ya ce wa wanda yake ƙwaran ɗan’uwansa, “Me ya sa kake bugun ɗan’uwanka?”

14 Ya amsa, ya ce, “Wa ya naɗa ka sarki ko alƙali a bisanmu? So kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren?”

Sai Musa ya tsorata, ya ce, “Assha, ashe, an san al’amarin!”

15 Da Fir’auna ya ji, sai ya nema ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu daga gaban Fir’auna, ya tafi, ya zauna a ƙasar Madayana. Da ya kai, sai ya zauna a bakin wata rijiya.

16 Ana nan waɗansu ‘yan mata bakwai, ‘ya’yan firist na Madayana suka zo su cika komaye da ruwa domin su shayar da garken mahaifinsu.

17 Sai makiyaya suka zo, suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su, ya kuma shayar da garkensu.

18 Lokacin da suka koma wurin mahaifinsu, Reyuwel, wato Yetro, ya ce musu, “Yaya aka yi yau, kuka komo da sauri haka?”

19 Sai suka ce, “Wani Bamasare ne ya cece mu daga hannun makiyaya, har ya ɗebo ruwa, ya shayar da garkenmu.”

20 Reyuwel kuwa ya ce wa ‘ya’yansa mata, “A ina yake? Me ya sa ba ku zo da shi ba? Ku kirawo shi, ya zo, ya ci abinci.”

21 Musa kuwa ya yarda ya zauna tare da Reyuwel. Sai ya aurar wa Musa da ‘yarsa Ziffora.

22 Ita kuwa ta haifa masa ɗa, ya raɗa masa suna Gershom, gama ya ce, “Baƙo ne ni, a baƙuwar ƙasa.”

23 Ana nan, a kwana a tashi, sai Sarkin Masar ya rasu. Jama’ar Isra’ila suka yi nishi, suka yi kuka kuma saboda bautarsu, kukansu na neman gudunmawa ya kai gun Allah.

24 Allah kuwa ya ji nishinsu, sai ya tuna da alkawarinsa da ya yi wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

25 Allah ya dubi jama’ar Isra’ila, ya kuwa kula da su.

Categories
FIT

FIT 3

Allah a Kira Musa

1 Wata rana, sa’ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato dutsen Allah.

2 A can mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba.

3 Musa kuwa ya ce, “Bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai ƙone ba.”

4 Sa’ad da Ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai Allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, “Musa, Musa.”

Musa ya ce, “Ga ni.”

5 Allah kuwa ya ce, “Kada ka matso kusa, ka cire takalminka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne.”

6 Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.

7 Ubangiji kuwa ya ce, “Na ga wahalar jama’ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu,

8 don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

9 Yanzu fa, ga shi, kukan jama’ar Isra’ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su.

10 Zo, in aike ka wurin Fir’auna domin ka fito da jama’ata, wato Isra’ilawa, daga cikin Masar.”

11 Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi gaban Fir’auna in fito da Isra’ilawa daga cikin Masar?”

12 Sai Allah ya ce, “Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa ni ne na aike ka. Sa’ad da ka fito da jama’ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan.”

13 Sai Musa ya ce wa Allah, “Idan na je wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na ubanninku ya aiko ni gare ku,’ idan sun ce mini, ‘Yaya sunansa?’ Me zan faɗa musu?”

14 Allah kuwa ya ce wa Musa, “NI INA NAN YADDA NAKE,” ya kuma ce, “Haka za ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘NI NE ya aiko ni gare ku.”’

15 Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.

16 Tafi, ka tattara dattawan Isra’ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar.

17 Ya yi alkawari cewa zai fisshe ku daga wahalar Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa. Ƙasa wadda take mai ba da yalwar abinci.’

18 Za su kasa kunne ga muryarka. Sa’an nan kai da dattawan Isra’ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’

19 Amma na sani Sarkin Masar ba zai bar ku ku fita ba, sai an yi masa tilas.

20 Domin haka zan miƙa hannuna in bugi Masar da dukan mu’ujizaina waɗanda zan aikata cikinta, sa’an nan zai bar ku ku fita.

21 “Zan sa wannan jama’a su yi farin jini a idanun Masarawa, sa’ad da kuka fita kuma, ba za ku fita hannu wofi ba.

22 Amma kowace mace za ta roƙi maƙwabciyarta da wadda take cikin gidanta kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, za ku sa wa ‘ya’yanku mata da maza. Da haka za ku washe Masarawa.”

Categories
FIT

FIT 4

1 Musa kuwa ya amsa ya ce, “Ai, ba za su gaskata ni ba, ba kuma za su kasa kunne ga maganata ba, gama za su ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba.”’

2 Amma Ubangiji ya ce masa, “Mene ne wannan a hannunka?”

Ya ce, “Sanda ne.”

3 Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Sai ya jefa shi ƙasa, sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya yi gudunsa.

4 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka ka kama wutsiyarsa.” Ya miƙa hannunsa ya kama shi, ya zama sanda kuma a hannunsa.

5 Sai Ubangiji ya ce, “Ta haka za su gaskata Ubangiji Allah na kakanninsu ne, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya bayyana gare ka.”

6 Sai Ubangiji ya sāke ce masa, “Sa hannunka cikin ƙirjinka.” Sa’ad da ya fitar da shi, ga hannunsa a kuturce fari fat.

7 Allah kuma ya ce masa, “Mai da hannunka cikin ƙirjinka.” Sai ya mai da hannunsa cikin ƙirjinsa. Sa’ad da ya fitar da shi, ga hannun ya koma kamar sauran jikinsa.

8 Ubangiji kuma ya ce, “Idan kuma ba su gaskata ka ba, ba su kuma kula da mu’ujiza ta fari ba, ya yiwu su gaskata ta biyun.

9 Idan ba su gaskata mu’ujizan nan biyu ba, ba su kuma kula da maganarka ba, sai ka ɗibi ruwa daga Kogin Nilu, ka zuba bisa busasshiyar ƙasa. Ruwan zai zama jini a bisa busasshiyar ƙasa.”

10 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

11 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Wa ya yi bakin ɗan adam? Wa ya yi bebe ko kurma, ko mai gani ko makaho? Ko ba ni Ubangiji ba ne?

12 Yanzu fa, tafi, zan kasance tare da bakinka, in koya maka abin da za ka faɗa.”

13 Amma Musa ya ce, “Ya Ubangijina, in ka yarda, ka aiki wani.”

14 Ubangiji kuwa ya hasala da Musa, ya ce, “Haruna ɗan’uwanka Balawe ba ya nan ne? Lalle na san shi ya iya magana, ga shi nan ma, yana fitowa ya tarye ka. Sa’ad da ya gan ka kuwa zai yi murna cikin zuciyarsa.

15 Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi.

16 Shi zai yi maka magana da jama’a, zai zama bakinka, kai kuwa za ka zama kamar Allah a gare shi.

17 Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu’ujizan.”

Musa Ya Koma Masar

18 Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin ‘yan’uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.”

Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”

19 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu.

20 Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da ‘ya’yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa.

21 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa’ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir’auna dukan mu’ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama’a su fita.

22 Za ka ce wa Fir’auna, Ubangiji ya ce, ‘Isra’ila ɗan fārina ne.

23 Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.”’

24 Ya zama kuwa sa’ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi.

25 Sai Ziffora ta ɗauki ƙanƙara ta yanke loɓar ɗanta, ta taɓa gaban Musa da shi, ta ce, “Kai angon jini kake a gare ni.”

26 Sa’an nan Ubangiji ya ƙyale shi. Ta kuma ce, “Kai angon jini ne,” saboda kaciyar.

27 Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi, ka taryi Musa cikin jeji.” Ya kuwa tafi ya tarar da shi a dutsen Allah, ya sumbace shi.

28 Sa’an nan Musa ya faɗa wa Haruna abubuwan da Ubangiji ya aike shi ya yi, da dukan mu’ujizan da ya umarce shi ya aikata.

29 Sai Musa da Haruna suka tafi suka tattara dukan dattawan Isra’ila.

30 Haruna dai ya hurta wa dattawan al’amuran da Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuma aikata mu’ujizan a idanunsu.

31 Dattawan kuwa suka gaskata. Sa’ad da suka ji Ubangiji ya ziyarci Isra’ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada.

Categories
FIT

FIT 5

Musa da Haruna Sun Tafi Gaban Fir’auna

1 Bayan wannan Musa da Haruna suka tafi gaban Fir’auna, suka ce, “Ga abin da Ubangjiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bar jama’ata su tafi domin su yi mini idi cikin jeji.”’

2 Amma Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji, har da zan ji maganarsa, in bar Isra’ilawa su tafi? Ai, ban san Ubangiji ɗin nan ba, balle in bar Isra’ilawa su tafi.”

3 Sai suka ce, “Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi.”

4 Amma Sarkin Masar ya ce wa Musa da Haruna, “Me ya sa kuke hana jama’ar yin aikinsu? Ku tafi wurin aikin gandunku.”

5 Ya kuwa ci gaba ya ce, “Ga jama’ar ƙasar sun yi yawa, yanzu kuna so ku hana su yin aikinsu.”

6 A ran nan fa Fir’auna ya umarci shugbannin aikin gandu da manyan jama’a, ya ce,

7 “Nan gaba kada ku ƙara ba mutanen nan budu na yin tubali kamar dā. Ku sa su, su tafi, su tara budu da kansu.

8 Duk da haka, kada su kāsa cika yawan tubalin da aka ƙayyade musu da fari. Ai, su ragwaye ne, shi ya sa suke kuka, suna cewa, ‘A bar mu, mu tafi mu miƙa wa Allahnmu hadaya.’

9 Ku sa mutanen su yi aiki mai tsanani har da ba za su sami damar kasa kunne ga maganganun ƙarya ba.”

10 Sai shugabannin aikin gandu da manyan jama’a suka tafi suka faɗa wa jama’a cewa, “Ga abin da Fir’auna ya ce, ‘Ba zan ba ku budu ba.

11 Ku je, ku da kanku, ku nemi budu inda duk za ku iya samowa, amma daɗai, ba za a sawwaƙe muku aikinku ba.”’

12 Sai jama’a suka watsu ko’ina cikin ƙasar Masar, suna tattara budu.

13 Shugabannin aikin gandun suka matsa musu, suna cewa, “Sai ku cika aikinku na kowace rana daidai yadda kuke yi a dā lokacin da ake ba ku budu.”

14 Aka kuwa bulali manya waɗanda suke Isra’ilawa waɗanda shugabannin aikin gandu na Fir’auna suka sa a bisa Isra’ilawa, ana cewa, “Me ya sa jiya da yau ba ku cika yawan tubalin da aka ƙayyade, kamar dā ba?”

15 Manyan Isra’ilawa kuwa suka tafi suka yi kuka a gaban Fir’auna, suka ce, “Me ya sa ka yi wa bayinka haka?

16 Ba a ba mu budu, amma ana ce mana mu yi tubali. Ga shi ma, dūkan bayinka suke yi. Ai, jama’arka ne suke da laifin.”

17 Fir’auna kuwa ya ce musu, “Ku ragwaye ne ƙwarai, shi ya sa kuke cewa a bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji hadaya.

18 Ku tafi, ku kama aiki, ba za a ba ku budu ba, duk da haka za ku cika yawan tubali da aka sa muku.”

19 Manyan Isra’ilawa suka ga lalle sun shiga uku, da yake aka ce dole su cika yawan tubali da aka yanka musu kowace rana.

20 Da suka fita daga gaban Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna, suna jiransu.

21 Suka ce wa Musa da Haruna, “Allah ya duba, ya hukunta ku, gama kun sa mun yi baƙin jini a wurin Fir’auna da barorinsa, har suka ɗauki takobi don su kashe mu.”

Addu’ar Musa

22 Sai Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangijina, me ya sa ka jawo wa wannan jama’a masifa? Me ya sa ka aike ni?

23 Gama tun da na tafi wurin Fir’auna, na yi masa magana da sunanka, ya mugunta wa wannan jama’a, kai kuwa ba ka ceci jama’arka ba ko kaɗan!”

Categories
FIT

FIT 6

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir’auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”

An Sāke Kiran Musa

2 Allah kuma ya yi magana da Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji.

3 Na bayyana ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a kan ni Allah Maɗaukaki ne, amma sunan nan nawa, Yahweh, ban sanasshe su ba.

4 Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci.

5 Yanzu na ji nishin Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuwa tuna da alkawarina.

6 Sai ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan ‘yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku.

7 Zan tallafe ku, ku zama jama’ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya ‘yanto ku daga wulakancin Masarawa.

8 Sa’an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.”’

9 Sai Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne gare shi ba, saboda ɓacin rai da tsananin bauta.

10 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

11 “Tafi gaban Fir’auna, Sarkin Masar, ka faɗa masa ya bar Isra’ilawa su fita ƙasa tasa.”

12 Amma Musa ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Duba, tun da yake Isra’ilawa ba su kasa kunne gare ni ba, yaya Fir’auna zai kasa kunne gare ni, ni mutum mai nauyin baki?”

13 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa da Haruna, su tafi wurin Isra’ilawa da wurin Fir’auna, Sarkin Masar, su ba su umarni, su kuma fito da Isra’ilawa daga cikin ƙasar Masar.

Asalin Musa da Haruna

14 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. ‘Ya’yan Ra’ubainu, maza, ɗan farin Isra’ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra’ubainu.

15 ‘Ya’yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan Bakan’aniya, waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.

16 Waɗannan su ne sunayen ‘ya’yan Lawi bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. Lawi ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.

17 ‘Ya’yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu.

18 ‘Ya’ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku.

19 ‘Ya’ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu.

20 Amram ya auri Yokabed ‘yar’uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai.

21 ‘Ya’yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri.

22 ‘Ya’ya maza na Uzziyel, su ne Mishayel, da Elzafan, da Zitri.

23 Haruna ya auri Elisheba, ‘yar Amminadab ‘yar’uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar.

24 ‘Ya’ya maza na Kora, su ne Assir, da Elkana, da Abiyasaf. Waɗannan su ne iyalin Kora.

25 Ele’azara, ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin ‘ya’ya mata na Futiyel. Ita kuwa ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan kabilar Lawi bisa ga kabilansu.

26 Wannan Haruna ne da Musa, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana su fito da Isra’ilawa daga cikin ƙasar Masar, ƙungiya ƙungiya.

27 Su ne waɗanda suka yi magana da Sarkin Masar ya bar Isra’ilawa su fita daga Masar. Musa da Haruna ne suka yi wannan.

Umarnin Ubangiji ga Musa da Haruna

28 Wata rana Ubangiji ya yi magana da Musa a ƙasar Masar ya ce,

29 “Ni ne Ubangiji, sai ka faɗa wa Fir’auna, Sarkin Masar, dukan abin da na faɗa maka.”

30 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, yaya Fir’auna zai kasa kunne gare ni?”

Categories
FIT

FIT 7

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, zan maishe ka kamar Allah ga Fir’auna. Ɗan’uwanka, Haruna kuwa, zai zama manzonka.

2 Kai za ka faɗa wa Haruna, ɗan’uwanka, dukan abin da na umarce ka, shi kuwa zai faɗa wa Fir’auna ya bar Isra’ilawa su fita ƙasa tasa.

3 Amma zan taurare zuciyar Fir’auna don in aikata alamu da mu’ujizai cikin ƙasar Masar.

4 Amma Fir’auna ba zai kasa kunne gare ku ba, don haka zan miƙa hannuna a bisa Masar, zan fitar da rundunar jama’ata, wato Isra’ilawa, daga ƙasar Masar ta wurin hukuntaina masu iko.

5 Masarawa kuma za su sani ni ne Ubangiji sa’ad da na miƙa hannuna gāba da Masar, don in fito da Isra’ilawa daga tsakiyarsu.”

6 Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su.

7 Musa yana da shekara tamanin, Haruna kuwa yana da shekara tamanin da uku sa’ad da suka yi magana da Fir’auna.

Sandan Haruna

8 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

9 “Idan Fir’auna ya ce muku, ‘Aikata waɗansu al’ajabai don ku nuna isarku,’ sai ka faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa, ya jefa shi ƙasa a gaban Fir’auna. Sandan kuwa zai zama maciji.”

10 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa a gaban Fir’auna. Da sandan ya fāɗi, sai ya zama maciji.

11 Fir’auna kuwa ya kirawo shahararrun malamai, da masu sihiri, su kuma su yi haka ta wurin sihirinsu na Masarawa.

12 Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, sai sandunan suka zama macizai. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu.

13 Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Jini

14 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna yana da taurin zuciya, ga shi, ya ƙi sakin jama’ar.

15 Ka tafi wurinsa da safe daidai lokacin da ya fita zai tafi Kogin Nilu. Ka jira don ka sadu da shi a bakin Nilu. Ka kuma ɗauki sandan nan wanda ya juye ya zama maciji.

16 Za ka faɗa wa Fir’auna cewa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya aike ni gare ka da cewa ka saki jama’ar Ubangiji domin su yi masa hidima a jeji. Amma ga shi, har yanzu ba ka yi biyayya ba.

17 Ubangiji ya ce, za ka sani shi ne Ubangiji ta wurin abin da zan aikata. Zan bugi ruwan Nilu da sandan da yake hannuna, ruwan kuwa zai rikiɗe ya zama jini.

18 Kifayen da suke cikin Nilu za su mutu. Nilu kuwa zai yi ɗoyi, har da Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.”’

19 Ubangiji kuma ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya ɗauki sandansa ya miƙa shi a bisa ruwayen Masar, da kogunansu, da rafuffukansu, da fadamunsu, da dukan tafkunansu don ruwansu ya zama jini. Jini zai kasance ko’ina a ƙasar Masar, i, har ma cikin randuna.

20 Musa da Haruna kuwa suka yi daidai kamar yadda Ubangiji ya umarta. Sai Haruna ya ta da sandansa sama ya bugi ruwan Nilu a gaban Fir’auna da fādawansa. Dukan ruwan Nilu kuwa ya rikiɗe jini.

21 Kifayen da suke cikin Nilu suka mutu. Nilu kuwa ya yi ɗoyi, har Masarawa ba su iya shan ruwansa ba. Ko’ina kuma a ƙasar Masar akwai jini.

22 Masu sihiri kuma na Masar suka yi haka, su ma, ta wurin sihirinsu, don haka zuciyar Fir’auna ta daɗa taurarewa, ya kuwa ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

23 Sai ya juya, ya koma fādarsa, bai ko kula da abin da aka yi ba.

24 Dukan Masarawa suka tattone ramummuka a bakin Nilu, suna neman ruwan sha, gama ba su iya shan ruwan Nilu ba.

25 Kwana bakwai suka cika bayan da Ubangiji ya bugi Kogin Nilu.

Categories
FIT

FIT 8

Annobar Kwaɗi

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tafi wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ubangiji ya ce ka saki jama’arsa domin su yi masa sujada.

2 Idan ka ƙi sakinsu, zai hore ka da kwaɗi.

3 Nilu zai cika da kwaɗi, za su tashi, su shiga cikin fādarka, da ɗakin kwanciyarka, da gadonka, har da gidajen fadawanka da jama’arka. Za su kuma shiga matuyanka da kwanon tuwonka,

4 har ma za su hau bisa kanka, da jama’arka, da dukan fādawanka.’ ”

5 Sai Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa sandansa a bisa koguna, da rufuffuka, da tafkuna don ya sa kwaɗi su fito, su rufe ƙasar Masar.

6 Haruna ya miƙa sandansa a bisa ruwayen Masar, kwaɗi kuwa suka fito, suka rufe ƙasar Masar.

7 Masu sihiri kuma suka sa kwaɗi su fito a bisa ƙasar Masar ta wurin sihirinsu.

8 Sai Fir’auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce su roƙi Ubangiji ya kawar masa da kwaɗin, shi da mutanensa, sa’an nan zai saki jama’ar, su tafi su miƙa wa Ubangiji hadaya.

9 Musa ya ce wa Fir’auna, “In ka yarda, a wane lokaci ne kake so in roƙa maka, kai da barorinka da jama’arka domin a kawar da kwaɗin daga gidajenku, a hallakar muku da su, sai dai na cikin Kogin Nilu za a bari?”

10 Fir’auna ya ce, “Gobe ne.”

Musa kuwa ya ce, “Za a yi kamar yadda ka faɗa, domin ka sani babu wani allah kamar Ubangiji Allahnmu.

11 Kwaɗin za su rabu da ku, da kai, da gidanka, da fādawanka, da jama’arka, sai na cikin Nilu kaɗai za a bari.”

12 Da Musa da Haruna suka fita daga gaban Fir’auna, sai Musa ya roƙi Ubangiji ya kawar da kwaɗin nan da suka azabta wa Fir’auna.

13 Ubangiji kuwa ya karɓi addu’ar Musa, sai kwaɗin da suke cikin gida da waɗanda suke kewaye da gida, da waɗanda suke cikin saura suka mutu.

14 Aka tsiba su tsibi tsibi. Suka sa ƙasar ta yi ɗoyi.

15 Da Fir’auna ya ga an kawar masa da kwaɗin, sai ya taurare zuciyarsa, ya ƙi jinsu kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Kwarkwata

16 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa hannunsa ya bugi ƙurar ƙasar, ta zama kwarkwata a ƙasar Masar.

17 Haka kuwa suka yi. Haruna ya miƙa sandansa ya bugi ƙurar ƙasa, sai ta zama kwarkwata a bisa ‘yan adam, da bisa dabbobi. Dukan ƙurar ta zama kwarkwata ko’ina cikin ƙasar Masar.

18 Masu sihiri suka ƙokarta su sa kwarkwata ta bayyana ta wurin sihirinsu, amma ba su iya ba. Kwarkwata kuma ta yayyaɓe ‘yan adam da dabbobi.

19 Sai masu sihiri suka ce wa Fir’auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Annobar Ƙudaje

20 Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir’auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama’ata domin su yi mini sujada.

21 In kuwa ka ƙi sakin jama’ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama’arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa.

22 A wannan rana fa zan keɓe ƙasar Goshen inda jama’ata suke don kada ƙudaje su taɓa wurin, ta haka ne za ka sani ni Ubangiji ina nan a duniya.

23 Zan sa iyaka tsakanin jama’ata da jama’arka. Gobe ne wannan mu’ujiza za ta auku.”’

24 Haka kuwa Ubangiji ya aikata. Ƙudaje masu yawa suka shiga gidan Fir’auna, da gidan fādawansa, da ko’ina a ƙasar Masar. Ƙasar kuwa ta lalace saboda ƙudaje.

25 Sa’an nan Fir’auna ya kirawo Musa da Haruna, ya ce, “Tafi, ku yi wa Allahnku hadaya a ƙasan nan.”

26 Amma Musa ya ce, “Ba zai kyautu a yi haka ba, gama irin dabbobin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadaya da su, haramu ne ga Masarawa. Idan fa muka miƙa hadaya da waɗannan dabbobi da suke haramu a idon Masarawa za su jajjefe mu da duwatsu.

27 Za mu yi tafiya kwana uku a jeji kafin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu kamar yadda ya umarce mu.”

28 Sai Firauna ya ce, “Zan bar ku ku tafi, ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya a jeji, sai dai kada ku tafi da nisa. Ku kuma yi mini addu’a.”

29 Musa kuwa ya ce, “Nan da nan da tashina daga gabanka, zan yi addu’a ga Ubangiji, ƙudajen kuwa za su rabu da kai, da fādawanka, da jama’arka gobe, kada ka sāke yin ruɗi, ka ƙi barin jama’ar su tafi, su miƙa wa Ubangiji hadaya.”

30 Musa ya fita daga wurin Fir’auna, ya roƙi Ubangiji.

31 Ubangiji kuwa ya aikata bisa ga roƙon Musa. Ƙudajen suka rabu da Fir’auna, da fādawansa, da jama’arsa. Ko ƙuda ɗaya bai ragu ba.

32 Duk da haka Fir’auna ya taurare zuciyarsa a wannan lokaci kuma, ya ƙi sakin jama’ar.

Categories
FIT

FIT 9

Mutuwar Dabbobi

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir’auna, ka faɗa masa cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama’ata domin su yi mini sujada.

2 Amma idan ka ƙi sakinsu, wato kana ta riƙonsu,

3 to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani.

4 Zan raba tsakanin dabbobin Isra’ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra’ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin.

5 Gobe ne zan aikata al’amarin nan a ƙasar.”’

6 Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al’amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra’ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba.

7 Sai Fir’auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra’ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saki jama’ar ba.

Marurai

8 Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, “Dibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa ta sama a gaban Fir’auna.

9 Tokar za ta zama kamar ƙura a dukan ƙasar Masar, ta zama marurai, suna kuwa fitowa a jikin mutum da dabba a dukan ƙasar Masar.”

10 Sa’an nan suka ɗauko toka daga matoya, suka tsaya a gaban Fir’auna. Da Musa ya watsa ta sama, sai ta zama marurai suna ta fitowa a jikin mutum da dabba.

11 Amma masu sihirin suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran, gama suka kamu da maruran kamar sauran Masarawa.

12 Ubangiji kuma ya taurare zuciyar Fir’auna har ya ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa wa Musa.

Ƙanƙara

13 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka je ka sami Fir’auna, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama’ata domin su yi mini sujada.

14 A wannan karo, ni da kaina zan kawo maka, da fādawanka, da jama’arka annoba, domin ka sani babu mai kama da ni a dukan duniya.

15 Gama da ni kaina na miƙa dantsena na buge ka da jama’arka da annoba, ai, da an hallakar da ku a duniya ƙaƙaf.

16 Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.

17 Har yanzu kana fariya a kan jama’ata, ba ka sake su ba.

18 Gobe war haka zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda Masar ba ta taɓa gani ba tun kafawarta, har zuwa yanzu.

19 Yanzu fa, sai ka ba da umarni a lura da awaki, da dukan abin da yake naku wanda yake a saura, gama duk mutum ko dabba wanda ya ragu a saura, wato wanda ba a kawo shi gida ba, zai mutu sa’ad da ƙanƙarar ta zo.”’

20 Akwai waɗansu daga cikin fādawan Fir’auna waɗanda suka tsorata saboda abin da Ubangiji ya faɗa, sai suka kawo bayinsu da dabbobinsu cikin gida.

21 Amma waɗanda ba su kula da abin da Ubangiji ya faɗa ba, suka bar bayinsu da dabbobinsu a waje cikin saura.

22 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa mutum da dabba da bisa dukan itatuwan saura a dukan ƙasar Masar.”

23 Sai Musa ya miƙa sandansa sama, Ubangiji kuwa ya aiko da tsawa da ƙanƙara, wuta kuwa ta bi ƙasar. Ubangiji ya sa aka yi ƙanƙara a bisa ƙasar Masar.

24 Ƙanƙarar tana faɗowa, wuta kuma tana tartsatsi a cikin ƙanƙara. Aka yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda ba a taɓa yi ba cikin dukan ƙasar Masar tun lokacin da ta zama al’umma.

25 Ƙanƙarar ta bugi ko’ina a Masar. Dukan abin da yake cikin saura, mutum duk da dabba, da tsire-tsire duka, ƙanƙara ta buge su. Duk itatuwan da yake a saura aka ragargaza su.

26 Sai dai a ƙasar Goshen inda Isra’ilawa suke, ba a yi ƙanƙara ba.

27 Fir’auna ya aika, aka kirawo Musa da Haruna, ya ce musu, “Lalle a wannan karo na yi laifi, Ubangiji shi ne da gaskiya. Ni da jama’ata muke da kuskure.

28 Ku roƙi Ubangiji ya tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”

29 Musa ya ce masa, “Da fitata daga cikin birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, walƙiya kuwa za ta tsaya, ƙanƙara kuma ta daina, don ku sani duniya ta Ubangiji ce.

30 Amma dai na sani, da kai da fādawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.”

31 Rama da sha’ir suka lalace, gama sha’ir ya riga ya nuna, rama kuwa tana huda.

32 Amma alkama da maiwa ba su lalace ba, gama kakarsu ba ta yi ba tukuna.

33 Sai Musa ya fita daga wurin Fir’auna ya rabu da birnin. Ya yi addu’a ga Ubangiji sai walƙiya da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.

34 Da Fir’auna ya ga an ɗauke ruwa, da ƙanƙara, da kuma walƙiya, sai ya sāke yin zunubi, ya taurare zuciyarsa, da shi da fādawansa.

35 Zuciyar Fir’auna ta taurare, har ya ƙi sakin Isra’ilawa kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta bakin Musa.

Categories
FIT

FIT 10

Fara

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da ta fādawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,

2 domin kuma ka sanar da ‘ya’yanka da jikokinka yadda na shashantar da Masarawa, na kuma aikata waɗannan mu’ujizai a tsakiyarsu. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.”

3 Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama’ata don su tafi su yi mini sujada.

4 In kuwa ka ƙi yarda ka bar jama’ata su tafi, to, gobe zan aiko da fara cikin ƙasarka,

5 za ta rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za ta cinye sauran abin da ya kuɓuta daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a ƙasar.

6 Za su cika fādarka, da dukan gidajen fādawanka, da na dukan Masarawa. Iyayenka da kakanninka ba su taɓa ganin irin faran nan ba, tun daga ran da suke ƙasar, har wa yau.”’ Sai ya juya ya fita daga gaban Fir’auna.

7 Fādawan Fir’auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?”

8 Aka komar da Musa da Haruna gaban Fir’auna. Sai Fir’auna ya ce musu, “Ku tafi ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”

9 Musa ya amsa, “Da samarinmu, da tsofaffinmu za mu tafi, da ‘ya’yanmu mata da maza za su fita tare da mu, da kuma garkunanmu da shanunmu, gama wajibi ne mu yi idi a gaban Ubangiji.

10 Fir’auna ya ce musu, “To, Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba, gama kuna da niyyar mugunta a zuciyarku.

11 Sai dai ku mazaje, ku tafi ku bauta wa Ubangiji, gama abin da kuke so ke nan.” To, aka kore su daga gaban Fir’auna.

12 Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa ƙasar Masar domin fara ta zo. Farar kuwa za ta rufe ƙasar Masar, ta cinye duk tsire-tsire da ganyayen da suke cikin ƙasar, da iyakar abin da ƙanƙara ta rage.”

13 Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar.

14 Farar ta mamaye ƙasar Masar, ta rufe dukan ƙasar. Ba a taɓa ganin fara ta taru da yawa kamar haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin kamar haka ba.

15 Ta rufe dukan fuskar ƙasa har ƙasar ta yi duhu. Ta cinye kowane tsiro na ƙasar da dukan ‘ya’yan itatuwa waɗanda ƙanƙara ta rage. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.

16 Fir’auna ya aika da gaggawa a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

17 Amma ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma roƙar mini Ubangiji Allahnku ya ɗauke mini wannan mutuwa.”

18 Sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna, ya tafi ya roƙi Ubangiji.

19 Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba.

20 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, Fir’auna kuwa ya ƙi sakin Isra’ilawa.

Duhu

21 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.”

22 Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuwa yi duhu baƙi ƙirin har kwana uku a dukan ƙasar Masar.

23 Mutum bai iya ganin ɗan’uwansa ba, ba kuma mutumin da ya iya fita gidansa har kwana uku. Amma akwai haske inda Isra’ilawa suke zaune.

24 Fir’auna ya kirawo Musa da Haruna ya ce musu, “Ku tafi ku bauta wa Ubangiji, sai dai ku bar tumakinku, da awakinku, da shanunku a nan, amma ku ku tafi da ‘ya’yanku.”

25 Musa kuwa ya ce, “In haka ne, kai ka ba mu abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadayu da su.

26 Don haka sai mu tafi da dabbobinmu, ko kofato ba za a bari a baya ba, gama daga cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.”

27 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna har bai yarda ya sake su ba.

28 Fir’auna ma ya ce wa Musa, “Tafi, ka ba ni wuri, ka mai da hankali fa, kada in ƙara ganinka, gama ran da na sāke ganinka ran nan kā mutu.”

29 Sai Musa ya amsa ya ce, “Haka nan ne kuwa, ba zan ƙara ganin fuskarka ba.”