Categories
FIT

FIT 11

Musa Ya Hurta Mutuwar ‘Ya’yan Fari

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yanzu dai zan ƙara bugun Fir’auna da Masarawa sau ɗayan nan kawai da annoba. Bayan wannan zai sake ku. Sa’ad da ya bar ku ku tafi, zai iza ƙyeyarku.

2 Sai ka faɗa wa jama’a, kowane mutum da kowace mace su roƙi kayan ado na azurfa da na zinariya daga wurin maƙwabtansu.”

3 Ubangiji kuwa ya sa jama’a su yi farin jini a idanun Masarawa. Musa kuwa ya zama babban mutum a ƙasar Masar a gaban fādawan Fir’auna da kuma gaban jama’ar.

4 Musa ya ce wa Fir’auna, “Ga abin da Ubangiji ya faɗa, ‘A wajen tsakar dare zan ratsa cikin Masar.

5 Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir’auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu.

6 Za a kuwa yi kuka mai zafi ko’ina a ƙasar Masar irin wanda ba a taɓa yi ba, ba kuma za a ƙara yi ba.

7 Amma ko kare ba zai yi wa wani mutum ko dabba na Isra’ila haushi ba, domin ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masarawa da Isra’ilawa.’

8 Sa’an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.

9 Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna ba zai kasa kunne gare ka ba, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin ƙasar Masar.”

10 Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu’ujizai a gaban Fir’auna. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa saki Isra’ilawa daga ƙasarsa ba.

Categories
FIT

FIT 12

Idin Ƙetarewa

1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna cikin ƙasar Masar,

2 wannan wata zai zama wata na farko a shekara a gare su.

3 A faɗa wa dukan taron Isra’ilawa cewa, “A rana ta goma ga watan nan, kowane namiji ya ɗauki ɗan rago ko ɗan akuya daga cikin garke domin iyalinsa, dabba ɗaya domin kowane gida.

4 Idan da wanda iyalinsa ba za su iya cinye dabba guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki dabba guda gwargwadon yawansu.

5 Tilas ne dabbar ta kasance lafiyayyiya ƙalau, bana ɗaya. Za ku kamo daga cikin tumakinku ko awaki.

6 Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da maraice.

7 Sa’an nan ku ɗibi jinin, ku sa a dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar gidajen da za a ci naman dabbobin.

8 A daren nan za ku gasa naman, ku ci da abinci marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.

9 Kada ku ci shi ɗanye ko daffaffe da ruwa, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kayan cikin.

10 Kada ku bar kome ya kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi.

11 Ga yadda za ku ci shi, da ɗamara a gindinku, da takalma a ƙafafunku, da sanda a hannunku, da gaggawa kuma za ku ci shi. Idin Ƙetarewa ne ga Ubangiji.

12 A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji.

13 Jinin da yake bisa gidajenku zai nuna inda kuke. Sa’ad da na ga jinin zan tsallake ku, ba kuma wani bala’in da zai same ku, ya hallaka ku, a lokacin da zan bugi ƙasar Masar.

14 Ranan nan za ta zama ranar tunawa a gare ku, za ku kiyaye ta, ranar idi ga Ubangiji. Dukan zamananku za ku kiyaye ta, idi ga Ubangiji har abada.

15 “Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra’ila.

16 A kan rana ta fari za ku yi tsattsarkan taro, haka kuma za ku yi a rana ta bakwai. A cikin waɗannan ranaku ba za a yi kowane aiki ba, sai na abin da kowa zai ci.

17 Za ku kiyaye idin abinci marar yisti, gama a wannan rana na fitar da rundunarku daga ƙasar Masar. Ku kiyaye wannan rana dukan zamananku. Wannan farilla ce ta har abada.

18 Za ku ci abinci marar yisti da maraice a kan rana ta goma sha huɗu ga wata na fari, har zuwa rana ta ashirin da ɗaya ga watan da maraice.

19 Amma kada a iske yisti a gidajenku har kwana bakwai, gama idan wani ya ci abin da aka sa wa yisti za a fitar da shi daga cikin taron jama’ar Isra’ila, ko shi baƙo ne ko kuwa haifaffen ƙasar.

20 Dukan abin da yake da yisti ba za ku ci shi ba, wato sai abinci marar yisti ne kaɗai za ku ci a dukan gidajenku.”

21 Musa ya kirayi dattawan Isra’ila duka, ya ce musu, “Gaggauta, ku zaɓa wa kanku ɗan tunkiya ko akuya bisa ga iyalanku, ku yanka domin Idin Ƙetarewa.

22 Ku ɗauki tuntun ezob, ku tsoma cikin jinin da yake a kasko, ku yarfa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada kowa ya fita daga gidansa sai da safe.

23 Gama Ubangiji zai ratsa don ya kashe Masarawa, sa’ad da ya ga jinin a bisa kan ƙofar, da dogaran ƙofa duka biyu sai ya wuce ƙofar, ba zai bar mai hallakarwa ya shiga gidanku, ya kashe ku ba.

24 Za ku kiyaye waɗannan ƙa’idodi, ku riƙe su farilla, ku da ‘ya’yanku har abada.

25 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku kamar yadda ya alkawarta, wajibi ne ku kiyaye wannan farilla.

26 Sa’ad da ‘ya’yanku suka tambaye ku, ‘Ina ma’anar wannan farilla?’

27 Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.”’ Sai jama’ar suka durƙusa suka yi sujada.

28 Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

Mutuwar ‘Ya’yan Fari

29 Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan ‘ya’yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan ‘ya’yan fari maza na dabbobi.

30 Da dare Fir’auna ya tashi, shi da dukan fādawansa, da dukan Masarawa, suka yi kuka mai tsanani a Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.

31 Sai Fir’auna ya sa aka kirawo masa Musa da Haruna da daren, ya ce musu, “Tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Tafi, ku bauta wa Ubangiji kamar yadda kuka ce.

32 Kwashi garkunanku na tumaki da awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”

33 Masarawa suka iza mutanen su gaggauta, su fita ƙasar, gama suka ce, “Ƙarewa za mu yi idan ba ku tafi ba.”

34 Sai jama’ar suka ɗauki ƙullun da ba a sa masa yisti ba, da ƙorensu na aikin ƙullun, suka ƙunshe a mayafansu, suka saɓa a kafaɗunsu.

35 Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa musu, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi.

36 Ubangiji ya sa jama’a su yi farin jini a wurin Masarawa, saboda haka Masarawa suka ba su abin da suka roƙa. Ta haka suka washe Masarawa.

Isra’ilawa Sun Fita Masar

37 Isra’ilawa mutum wajen zambar ɗari shida maza (600,000), banda iyalansu, suka kama tafiya daga Ramases zuwa Sukkot.

38 Babban taron tattarmuka kuma suka tafi tare da su, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu tinjim.

39 Suka toya abinci marar yisti da ƙullun da suka fita da shi daga Masar, gama ba su sa yisti cikin ƙullun ba domin an iza ƙyeyarsu, ba su sami damar dakatawa ba, ba su kuwa shirya wa kansu guzuri ba.

40 Zaman da Isra’ilawa suka yi a Masar shekara ce arbaminya da talatin.

41 A ranar da shekara arbaminya da talatin ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan rundunar Ubangiji suka fita daga ƙasar Masar.

42 Daren nan da Ubangiji ya sa domin ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, daren ne wanda wajibi ne Isra’ilwa su kiyaye domin su girmama Ubangiji dukan zamanansu.

Ƙa’idodin Idin Ƙetarewa

43 Sai Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Wannan ita ce ƙa’idar Idin Ƙetarewa, baƙo ba zai ci ba.

44 Amma kowane bawa da aka saya da kuɗi ya iya ci, in dai an yi masa kaciya.

45 Amma da baƙo da wanda aka yi ijararsa ba zai ci shi ba.

46 A gidan da aka shirya, nan za a ci, kada a fitar da naman waje, kada kuma a karye ƙashinsa.

47 Dukan taron jama’ar Isra’ila za su kiyaye Idin Ƙetarewa.

48 Idan baƙon da yake zaune tare da ku yana so ya yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji tare da ku, to, sai a yi wa kowane namiji da yake a gidansa kaciya sa’an nan ya iya shiga idin, shi kuma ya zama ɗan ƙasa. Daɗai, marar kaciya ba zai ci ba.

49 Wannan ka’ida ta shafi ɗan ƙasa daidai da baƙon da yake baƙunci tsakaninku.”

50 Isra’ilawa suka yi na’am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.

51 A wannan rana ce Ubangiji ya fitar da Isra’ilawa runduna runduna daga ƙasar Masar.

Categories
FIT

FIT 13

Keɓewar ‘Ya’yan Fari

1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Keɓe mini ‘ya’yan fari maza duka. Kowane ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”

Idin Abinci Marar Yisti

3 Musa ya ce wa jama’a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.

4 A wannan rana kuka fita, wato a watan Abib.

5 Sai ku kiyaye wannan farilla a wannan wata sa’ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, wadda ya rantse wa kakanninku zai ba ku, wato ƙasar da take ba da yalwar abinci.

6 Sai ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai, amma a rana ta bakwai za ku yi idi ga Ubangiji.

7 Abinci marar yisti za a ci har kwana bakwai. Kada a ga wani da abinci mai yisti, ko kuma yisti ɗin kansa, a ko’ina a wurarenku.

8 A wannan rana kowa zai sanar wa ɗansa cewa abubuwan nan da muke yi, muna yi ne don tunawa da abin da Ubangiji ya yi mana sa’ad da ya fitar da mu daga Masar.

9 Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari’ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.

10 Sai ku kiyaye farillan nan kowace shekara a lokacinta.”

‘Ya’yan Fari

11 “Sa’ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan’aniyawa wadda zai ba ku kamar yadda ya rantse muku, ku da kakanninku,

12 sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Kowane ɗan farin dabbarku na Ubangiji ne.

13 Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. Idan kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Kowane ɗan farin ‘ya’yanku, sai ku fanshe shi.

14 In wata rana ‘ya’yanku suka tambaye ku cewa, ‘Ina ma’anar wannan?’ Sai ku ce musu, ‘Da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar, daga gidan bauta.

15 Gama sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan ‘ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da ‘ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan ‘ya’yan farinmu, maza.’

16 Al’amarin nan kuwa zai zama matuni kamar alama a hannunku ko a goshinku, gama da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar.”

Al’amudin Gizagizai da na Wuta

17 Da Fir’auna ya bar jama’a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, “Don kada jama’a su sāke tunaninsu sa’ad da suka ga yaƙi, su koma Masar.”

18 Amma Allah ya kewaya da jama’a ta hanyar jeji, wajen Bahar Maliya. Isra’ilawa kuwa suka fita daga ƙasar Masar da shirin yaƙi.

19 Musa ya kuma ɗauki ƙasusuwan Yusufu, gama Yusufu ya riga ya rantsar da Isra’ilawa su kwashe ƙasusuwansa daga Masar sa’ad da Allah ya ziyarce su.

20 Sai suka ci gaba da tafiya daga Sukkot suka yi zango a Etam a gefen jejin.

21 Da rana Ubangiji yakan yi musu jagora da al’amudin girgije, da dare kuwa da al’amudin wuta, domin ya ba su haske domin su iya tafiya dare da rana.

22 Al’amudan nan biyu kuwa, na girgijen da na wutar, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.

Categories
FIT

FIT 14

Hayen Bahar Maliya

1 Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Faɗa wa Isra’ilawa su juya su yi zango a gaban Fi-hahirot tsakanin Migdol da bahar, a gaban Ba’alzefon. Sai ku yi zango gab da bahar.

3 Gama Fir’auna zai ce, ‘Aha, Isra’ilawa sun rikice cikin ƙasar, hamada kuwa ta cinye su.’

4 Zan taurare zuciyar Fir’auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir’auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra’ilawa suka yi.

5 Da aka faɗa wa Sarkin Masar jama’a sun gudu, sai shi da fādawansa suka sāke tunaninsu game da jama’ar, suka ce, “Me muka yi ke nan, da muka bar Isra’ilawa su fita daga cikin bautarmu?”

6 Ya kuwa shirya karusarsa, ya ɗauki rundunarsa tare da shi.

7 Ya kuma ɗauki zaɓaɓɓun karusai ɗari shida da sauran karusan Masar duka waɗanda shugabanni suke bi da su.

8 Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, Sarkin Masar, sai ya bi Isra’ilawa sa’ad da suka fita gabagaɗi.

9 Masarawa kuwa, da dukan dawakan Fir’auna, da karusai, da mahayan dawakansa, da askarawansa, suka bi su, suka ci musu a inda suka yi zango a bakin bahar, kusa da Fi-hahirot wanda ya fuskanci Ba’alzefon.

10 Da Fir’auna ya matso, Isra’ilawa kuwa suka ɗaga idanunsu suka ga Masarawa tafe, sun tasar musu, sai suka firgita ƙwarai, suka yi kuka ga Ubangiji.

11 Suka ce wa Musa, “Donin ba makabarta a Masar, shi ya sa ka fito da mu, mu mutu a jeji? Me ke nan ka yi mana da ka fito da mu daga Masar?

12 Ashe, ba abin da muka faɗa maka tun a Masar ke nan ba cewa, ‘Ka rabu da mu, mu bauta wa Masarawa’? Gama gwamma mu bauta wa Masarawa da mu mutu a jeji.”

13 Sai Musa ya ce wa jama’a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.

14 Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!”

15 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Me ya sa kake yi mini kuka? Faɗa wa Isra’ilawa su ci gaba.

16 Ɗaga sandanka, ka miƙa hannunka a bisa bahar, ka raba shi, domin Isra’ilawa su taka busasshiyar ƙasa cikin bahar, su haye.

17 Ni kuwa zan taurare zukatan Masarawa domin su bi su. Ta haka zan ci nasara bisa Fir’auna da rundunansa, da karusansa, da mahayan dawakansa.

18 Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji, sa’ad da na sami nasara bisa kan Fir’auna, da karusansa, da mahayan dawakansa.”

19 Mala’ikan Allah kuwa wanda yake tafiya a gaban rundunar Isra’ila ya tashi ya koma bayansu, haka kuma al’amudin girgijen ya tashi daga gabansu ya tsaya a bayansu.

20 Ya shiga tsakanin sansanin Masarawa da zangon Isra’ilawa. Girgije mai duhu na tsakaninsu, amma ya haskaka wajen Isra’ilawa har gari ya waye, ba wanda ya kusaci wani.

21 Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre.

22 Isra’ilawa kuwa suka bi ta tsakiyar bahar, a busasshiyar ƙasa. Ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.

23 Masarawa kuwa suka bi su har tsakiyar bahar, da dawakan Fir’auna duka, da karusansa, da mahayan dawakansa.

24 Da asubahin fāri, Ubangiji, daga cikin al’amudin wuta da na girgije, ya duba rundunar Masarawa, ya gigitar da su.

25 Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra’ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”

26 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa bahar domin ruwa ya koma bisa kan Masarawa, da bisa karusansu, da mahayan dawakansu.”

27 Gari na wayewa sai Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, ruwan kuwa ya koma kamar yadda yake a dā. Da Masarawa suka yi ƙoƙarin tserewa, sai ruwan ya rufe su. Ubangiji kuwa ya hallaka su a tsakiyar bahar.

28 Ruwan ya komo ya rufe dukan karusai, da mahayan dawakai, da dukan rundunar Fir’auna waɗanda suka bi ta cikin bahar, ba ko ɗaya da ya ragu.

29 Amma Isra’ilawa suka yi tafiya a busasshiyar ƙasa a tsakiyar bahar, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu.

30 A wannan rana, Ubangiji ya ceci Isra’ilawa daga hannun Masarawa. Isra’ilawa kuwa suka ga gawawwakin Masarawa a bakin bahar.

31 Isra’ilawa suka ga gawurtaccen aikin da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa. Isra’ilawa kuwa suka ji tsoron Ubangiji, suka gaskata Ubangiji da bawansa Musa.

Categories
FIT

FIT 15

Waƙar Musa

1 Musa da jama’ar Isra’ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,

“Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara,

Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.

2 Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,

Shi ne wanda ya cece ni.

Wannan ne Allahna, zan yabe shi,

Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.

3 Ubangiji mayaƙi ne,

Yahweh ne sunansa.

4 “Karusan Fir’auna da rundunarsa, ya jefar cikin bahar,

Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.

5 Rigyawa ta rufe su,

Suka nutse cikin zurfi kamar dutse.

6 Ya Ubangiji dantsen damanka, mai iko ne,

Ya Ubangiji, dantsen damanka ya ragargaza magabta.

7 Cikin girman ɗaukakarka, ka kā da maƙiyanka, ka aika da hasalarka,

Ka cinye su kamar ciyawa.

8 Da hucin numfashin hancinka ruwa ya tattaru,

Rigyawa ta tsaya kamar tudu,

Zurfafan ruwa suka daskare a tsakiyar bahar.

9 Magabcin ya ce, ‘Zan bi, in kama su, in raba ganima,

Muradina a kansu zai biya, zan zare takobina, hannuna zai hallaka su.’

10 Ka hura iskarka, bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.

11 “Ya Ubangiji, wane ne kamarka a cikin alloli?

Wa yake kamarka a cikin ɗaukaka da tsarki?

Mai banrazana cikin mafifitan ayyuka, mai aikata mu’ujizai.

12 Ka miƙa dantsen damanka, ƙasa ta haɗiye su.

13 Da tabbatacciyar ƙaunarka, ka bi da jama’arka da ka fansa,

Ka bi da su da ƙarfinka zuwa tsattsarkan mazauninka.

14 Al’ummai suka ji suka yi rawar jiki,

Tsoro ya kama mazaunan Filistiya.

15 Sarakunan Edom suka tsorata,

Shugabannin Mowab suna rawar jiki,

Dukan mazaunan Kan’ana sun narke.

16 Tsoro da razana sun aukar musu,

Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse,

Har jama’arka, ya Ubangiji, suka haye,

I, jama’arka, ya Ubangiji, suka haye,

17 Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka,

Wurin, ya Ubangiji, da ka maishe shi tsattsarkan mazauninka,

Tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, wanda ka kafa da ikonka.

18 Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”

19 Gama sa’ad da dawakan Fir’auna, da karusansa, da mahayan dawakansa suka shiga bahar, Ubangiji ya komar da ruwan bahar a bisansu, amma Isra’ilawa suka yi tafiya a busassiyar ƙasa ta tsakiyar bahar.

20 Sai Maryamu, annabiya, ‘yar’uwar Haruna, ta ɗauki kuru cikin hannunta. Mata duka suka fita, suka bi ta da kuwaru suna ta rawa.

21 Maryamu tana raira musu waƙa tana cewa,

“Raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara,

Doki da mahayinsa, ya jefar cikin bahar.”

Maɓuɓɓugan Ruwan Ɗaci

22 Musa kuwa ya bi da Isra’ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba.

23 Sa’ad da suka zo Mara, sun kasa shan ruwan Mara saboda ɗacinsa, don haka aka sa masa suna Mara.

24 Sai mutanen suka yi wa Musa gunaguni suna cewa, “Me za mu sha?”

25 Musa ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sa’an nan Musa ya karyi itacen, ya jefa cikin ruwa, ruwan kuwa ya zama mai daɗi.

A nan ne Ubangiji ya kafa musu dokoki da ka’idodi, a nan ne kuma ya gwada su.

26 Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”

27 Daga nan suka je Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa goma sha biyu, da itatuwan giginya saba’in. A nan suka yi zango a bakin ruwa.

Categories
FIT

FIT 16

Manna da Makware

1 Taron jama’ar Isra’ila suka tashi daga Elim suka shiga jejin Sin wanda yake tsakanin Elim da Sina’i, a rana ta goma sha biyar ga watan biyu bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.

2 Sai dukan taron jama’ar Isra’ilawa suka yi wa Musa da Haruna gunaguni cikin jejin, suka ce musu,

3 “Da ma mun mutu ta ikon Ubangiji a ƙasar Masar lokacin da muka zauna kusa da tukwanen nama, muka ci abinci muka ƙoshi. Ga shi, kun fito da mu zuwa cikin jeji don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”

4 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ga shi, zan sauko muku da abinci daga sama. A kowace rana jama’a za su fita su tattara abin da zai ishe su a yini, da haka zan gwada su, ko za su kiyaye maganata, ko babu.

5 A kan rana ta shida, sai su ninka abin da suka saba tattarawa na kowace rana, su shirya shi.”

6 Musa da Haruna kuwa suka ce wa Isra’ilawa, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fisshe ku daga ƙasar Masar.

7 Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, gama ya ji gunagunin da kuka yi a kansa, gama wane, mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”

8 Musa ya kuma ce, “Da yamma Ubangiji zai ba ku nama ku ci, da safe kuwa zai ƙosar da ku da abinci, gama Ubangiji ya riga ya ji irin gunagunin da kuka yi a kansa. Ai, gunagunin ba a kanmu yake ba, wane mu? A kan Ubangiji ne kuka yi.”

9 Musa ya ce wa Haruna, “Faɗa wa taron jama’ar Isra’ila, su matso nan a gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninsu.”

10 Sa’ad da Haruna yake magana da taron jama’ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.

11 Ubangiji kuwa ya yi magana da Musa ya ce,

12 “Na ji gunagunin Isra’ilawa, amma ka faɗa musu cewa, ‘A tsakanin faɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe za ku kuma ƙoshi da abinci. Sa’an nan za ku sani, ni Ubangiji Allahnku ne.”’

13 Da maraice makware suka zo suka rufe zangon, da safe kuma raɓa ta kewaye zangon.

14 Sa’ad da raɓar ta kaɗe, sai ga wani abu tsaki-tsaki mai laushi, fari, kamar hazo a ƙasa.

15 Sa’ad da Isra’ilawa suka gan shi, suka ce wa junansu, “Manna,” wato “Mece ce wannan?” Gama ba su san irinta ba.

Musa kuwa ya ce musu, “Wannan ita ce abincin da Ubangiji ya ba ku, ku ci.

16 Abin da Ubangiji ya umarta ke nan, kowannenku ya tattara wadda ta ishe shi ci, kowa ya sami mudu daidai bisa ga yawan mutanen da yake cikin kowace alfarwa.”

17 Isra’ilawa suka yi haka nan, suka tattara, waɗansu suka zarce, waɗansu kuma ba su kai ba.

18 Amma da aka auna da mudu, ta waɗanda suka zarce ba ta yi saura ba, ta waɗanda ba su kai ba, ba ta gaza ba. Kowane mutum ya tattara daidai cinsa.

19 Musa ya ce musu, “Kada wani ya ci, ya bar saura har safiya.”

20 Amma waɗansu ba su kasa kunne ga Musa ba, suka bar saura, har ta kwana, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su.

21 Kowace safiya sukan tattara ta, kowa gwargwadon cinsa, amma da rana ta yi zafi sai manna ɗin ta narke.

22 A kan rana ta shida suka tattara biyu ɗin abin da suka saba, kowane mutum mudu biyu biyu. Sai shugabannin taron suka zo suka faɗa wa Musa.

23 Shi kuwa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarta, ‘Gobe ranar hutawa ce ta saduda, Asabar ce, tsattsarka ga Ubangiji. Ku toya abin da za ku toya, ku kuma dafa abin da za ku dafa. Abin da kuka ci kuka rage, ku ajiye don gobe.”’

24 Suka ajiye har gobe kamar yadda Musa ya umarta, amma ba ta yi ɗoyi ba, ba ta kuwa yi tsutsotsi ba.

25 Sai Musa ya ce, “Ita za ku ci yau, gama yau Asabar ce ga Ubangiji. Yau ba za ku same ta a saura ba.

26 Kwana shida za ku tattara ta, amma a rana ta bakwai wadda take asabar, ba za a iske kome ba.”

27 Amma a rana ta bakwai ɗin waɗansu mutane suka tafi don su tattara, ba su kuwa sami kome ba.

28 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi kiyaye dokokina da umarnaina?

29 Lura fa, Ubangiji ne ya ba ku ranar Asabar, domin haka a rana ta shida yakan ba ku abinci na kwana biyu. Kowanne ya yi zamansa a inda yake. Kada kowa ya bar inda yake a rana ta bakwai ɗin.”

30 Sai jama’a suka huta a rana ta bakwai.

31 Isra’ilawa kuwa suka sa wa wannan abinci suna, Manna. Manna wata irin tsaba ce kamar farin riɗi. Ɗanɗanarta kuwa kamar waina ce da aka yi da zuma.

32 Sai Musa ya ce, “Ubangiji ya umarta a cika mudu da ita, a adana ta dukan zamananku domin kowane zamani a ga irin abincin da ya ciyar da ku cikin jeji lokacin da ya fito da ku daga ƙasar Masar.”

33 Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki tukunya, ka zuba mudu guda na manna a ciki, ka ajiye a gaban Ubangiji, a adana har dukan zamananku.”

34 Kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, haka Haruna ya ajiye ta a gaban akwatin alkawari domin kiyayewa.

35 Shekara arba’in Isra’ilawa suka yi suna cin manna, har suka kai ƙasar da take da mutane, suka ci manna, har zuwa kan iyakar ƙasar Kan’ana.

36 Mudu ɗaya humushin garwa ɗaya ta gari.

Categories
FIT

FIT 17

Ruwa daga Dutse

1 Dukan taron jama’ar Isra’ila suka tashi daga jejin Sin, suna tafiya daga zango zuwa zango bisa ga umarnin Ubangiji. Suka yi zango a Refidim, amma ba ruwan da jama’a za su sha.

2 Domin haka jama’a suka zargi Musa suka ce, “Ba mu ruwa, mu sha.”

Musa ya amsa musu ya ce, “Don me kuke zargina? Don me kuke gwada Ubangiji?”

3 Amma jama’a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, “Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, domin ka kashe mu ne, da mu, da ‘ya’yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?”

4 Sai Musa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Me zan yi wa jama’an nan? Ga shi, saura kaɗan su jajjefe ni da duwatsu.”

5 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ɗauki waɗansu dattawa daga cikin jama’ar Isra’ila, ka wuce a gaban jama’ar. Ka kuma ɗauki sandanka wanda ka bugi Nilu da shi, ka tafi.

6 Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama’a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra’ila.

7 Sai aka sa wa wurin suna, “Masaha” da “Meriba”, saboda Isra’ilawa suka yi husuma, suka kuma jarraba Ubangiji suna cewa, “Ubangiji yana tare da mu, ko babu?”

Yaƙi da Amalekawa

8 Amalekawa suka zo su yi yaƙi da Isra’ilawa a Refidim.

9 Sai Musa ya ce wa Joshuwa, “Zaɓo mana mutane, ka fita ka yi yaƙi da Amalekawa gobe. Zan tsaya a bisa dutsen da sandan mu’ujiza a hannuna.”

10 Joshuwa kuwa ya yi yadda Musa ya faɗa masa, ya fita ya yi yaƙi da Amalekawa. Musa, da Haruna, da Hur kuma suka hau kan dutsen.

11 Muddin hannun Musa na miƙe, sai Isra’ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara.

12 Sa’ad da hannuwan Musa suka gaji, Haruna da Hur suka ɗauki dutse suka ajiye wa Musa, ya zauna a kai, su kuwa suka tsaya a gefen damansa da hagunsa suna tallabe da hannunsa sama, suka tallabe su har faɗuwar rana.

13 Joshuwa kuwa ya ragargaza rundunar Amalekawa da takobi.

14 Ubangiji ya ce wa Musa, “Rubuta wannan a littafi domin a tuna da shi, ka kuma faɗa wa Joshuwa zan shafe Amalekawa ɗungum.”

15 Sai Musa ya gina bagade ya sa masa suna, Yahweh Nissi, wato Ubangiji ne tutarmu.

16 Ya ce, “Ubangiji ya tabbata zai yaƙi Amalekawa har abada.”

Categories
FIT

FIT 18

Yetro Ya Ziyarci Musa

1 Yetro, firist na Madayana, surukin Musa, ya ji dukan abin da Allah ya yi wa jama’arsa, wato Musa da Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya fito da su daga Masar.

2 Ya kawo Ziffora matar Musa, wadda Musa ya aika da ita gida.

3 Yetro kuma ya kawo ‘ya’yanta biyu maza, Gershom da Eliyezer tare da ita. Gama Musa ya ce, “Ni baƙo ne a baƙuwar ƙasa.” Saboda haka ne ya raɗa wa ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, suna, Gershom.

4 Ya kuma ce, “Allah na ubanan shi ne ya taimake ni, ya cece ni daga takobin Fir’auna,” saboda haka ya raɗa wa ɗayan, suna, Eliyezer.

5 Sai Yetro ya kawo wa Musa ‘ya’yansa maza da matarsa a cikin jeji inda suka yi zango kusa da dutsen Allah.

6 Aka faɗa wa Musa, “Ga surukinka, Yetro, yana zuwa wurinka da matarka da ‘ya’yanta biyu tare da ita.”

7 Musa kuwa ya fita ya marabce shi, ya sunkuya, ya sumbace shi. Suka gaisa, suka tambayi lafiyar juna, sa’an nan suka shiga alfarwa.

8 Sai Musa ya faɗa wa surukinsa dukan abin da Ubangiji ya yi da Fir’auna da Masarawa saboda Isra’ilawa, ya kuma faɗa masa dukan wahalar da suka sha a kan hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.

9 Yetro kuwa ya yi murna saboda alherin da Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa da yadda ya cece su daga hannun Masarawa.

10 Yetro kuma ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da Fir’auna, wanda kuma ya ceci jama’arsa daga bautar Masarawa.

11 Yanzu na sani Ubangiji yake gāba da sauran alloli duka, gama ya ceci Isra’ilawa daga tsanantawar da Masarawa suka yi musu.”

12 Yetro, surukin Musa kuwa, ya miƙa hadaya ta ƙonawa da sadaka ga Allah. Sai Haruna ya zo tare da dattawan Isra’ila duka don su ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.

13 Kashegari da Musa ya zauna garin yi wa jama’ar shari’a, mutane suka kekkewaye shi tun dage safiya har zuwa yamma.

14 Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama’a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama’a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?”

15 Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah.

16 A sa’ad da suke da wata matsala sukan zo wurina, ni kuwa nakan daidaita tsakanin mutum da maƙwabcinsa, nakan kuma koya musu dokokin Allah da umarnansa.”

17 Amma surukin Musa ya ce, “Abin nan da kake yi ba daidai ba ne.

18 Kai da jama’an nan da suke tare da kai za ku rafke, saboda abin da kake yi ya fi ƙarfinka, kai kaɗai ba za ka iya ba.

19 Yanzu sai ka saurari maganata, zan ba ka shawara, Allah kuwa ya kasance tare da kai. Za ka wakilci jama’a a gaban Allah, ka kai matsalolinsu gare shi.

20 Ka koya musu dokokin da umarnan, ka nuna musu hanyar da ya kamata su yi.

21 Ka kuma zaɓa daga cikin jama’a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama’a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.

22 Za su yi wa mutane shari’a koyaushe, amma kowace babbar matsala sai su kawo maka, ƙaramar matsala kuwa su yanke da kansu. Da haka za su ɗauki nauyin jama’a tare da kai don ya yi maka sauƙi.

23 In ka bi wannan shawara, in kuma Allah ya umarce ka da yin haka, za ka iya ɗaukar nawayar jama’ar. Mutane duka kuwa za su yi zamansu lafiya.”

24 Musa kuwa ya saurari maganar surukinsa, ya yi abin da ya ce duka.

25 Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra’ilawa ya naɗa su shugabannin jama’a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.

26 Suka yi ta yi wa jama’a duka shari’a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu.

27 Sa’an nan Musa ya sallami surukinsa, ya koma garinsu.

Categories
FIT

FIT 19

Isra’ilawa a Dutsen Sina’i

1 Isra’ilawa sun kai jejin Sina’i a farkon watan uku bayan fitowarsu daga ƙasar Masar.

2 Da suka tashi daga Refidim, suka shiga jejin Sina’i, sai suka yi zango gaban dutsen.

3 Musa kuwa ya hau bisa dutsen don ya sadu da Allah.

Ubangiji ya kira shi daga kan dutsen, ya ce, “Abin da za ka faɗa wa gidan Yakubu, wato Isra’ilawa ke nan,

4 ‘Kun dai ga abin da na yi da Masarawa, da yadda na ɗauke ku kamar yadda gaggafa take ɗaukar ‘yan tsakinta, na kawo ku gare ni.

5 Yanzu fa, in za ku yi biyayya da ni, ku kuma kiyaye maganata, za ku zama mutanena. Dukan duniya tawa ce, amma ku za ku zama zaɓaɓɓiyar jama’ata,

6 za ku zama daular firistoci da al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne zantuttukan da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”

7 Sa’an nan Musa ya je ya kira taron dattawan jama’a, ya bayyana musu dukan zantuttukan da Ubangiji ya umarce shi.

8 Dukan jama’a kuwa suka amsa masa baki ɗaya, suka ce, “Dukan abin da Ubangiji ya faɗa za mu aikata.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama’ar suka bayar.

9 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, ni da kaina, ina zuwa a gare ka cikin duhun girgije, domin jama’a su ji sa’ad da nake magana da kai, domin su amince da kai tutur.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama’ar suka bayar.

10 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin jama’a ka tsarkake su yau da kuma gobe, su kuma wanke tufafinsu.

11 Su shirya saboda rana ta uku, gama a kan rana ta uku zan sauko a bisa dutsen Sina’i a gabansu duka.

12 Sai ka yi wa jama’a iyaka kewaye da dutsen, ka faɗa musu cewa, ‘Ku yi hankali kada ku hau dutsen ko ku taɓa shi. Duk wanda ya taɓa dutsen za a kashe shi,

13 za a jajjefe shi da duwatsu ko a harbe shi da kibiya, kada kowa ya taɓa dutsen da hannu. Wannan kuwa ya shafi mutane duk da dabbobi, tilas ne a kashe su.’ Sa’ad da aka busa ƙahon rago, sai mutane su taru a gindin dutsen.”

14 Da Musa ya gangaro daga dutsen zuwa wurin mutane, ya tsarkake su. Su kuwa suka wanke tufafinsu.

15 Sai Musa ya ce musu, “Ku shirya saboda rana ta uku, kada ku kusaci mace.”

16 A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama’ar da suke cikin zango suka yi rawar jiki.

17 Musa kuwa ya fito da jama’a daga zango ya shugabance su, su sadu da Allah, suka tsattsaya a gindin dutsen.

18 Ga shi, hayaƙi ya tunnuƙe dutsen Sina’i duka, saboda Ubangiji ya sauko a bisa dutsen da wuta. Hayaƙi kuwa ya tunnuƙe, ya yi sama kamar na wurin narka ma’adinai, dutsen duka ya girgiza ƙwarai.

19 Da busar ƙaho ta ƙara tsananta, sai Musa ya yi magana, Ubangiji kuwa ya amsa masa da tsawa.

20 Ubangiji ya sauko bisa dutsen Sina’i bisa ƙwanƙolin dutsen. Ya kirawo Musa zuwa ƙwanƙolin dutsen, Musa kuwa ya hau.

21 Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, ka faɗakar da jama’ar, don kada su ƙetare kan iyakar, su zo garin a kalli Ubangiji, da yawa daga cikinsu kuwa su mutu.

22 Ko firistocin da za su kusato Ubangiji, sai su tsarkake kansu, don kada in hukunta su.”

23 Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutanen ba za su iya hawan dutsen Sina’i ba, gama kai da kanka ka umarce mu cewa, ‘Ku sa iyaka kewaye da dutsen, ku tsarkake shi.’ ”

24 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Sauka, ka hau tare da Haruna. Amma kada ka bar firistoci da jama’a su ƙetare kan iyakar su hau zuwa wurina, don kada in hukunta su.”

25 Sai Musa ya sauka wurin jama’a ya faɗa musu.

Categories
FIT

FIT 20

Dokoki Goma

1 Allah ya faɗi dukan waɗannan zantuttuka, ya ce,

2 “Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.

3 “Kada ka kasance da waɗansu alloli sai ni.

4 “Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa.

5 Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta ‘ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.

6 Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararrakin da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.

7 “Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.

8 “Tuna da rana Asabar, ka kiyaye ta da tsarki.

9 Za ku yi dukan ayyukanku cikin kwana shida,

10 amma rana ta bakwai keɓaɓɓiya ce ga Ubangiji Allahnka. A ranar ba za ka yi kowane irin aiki ba, ko kai, ko ‘ya’yanka, ko barorinka, ko dabbobinka, ko kuwa baƙon da yake zaune tare da ku.

11 Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.

12 “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

13 “Kada ka yi kisankai.

14 “Kada ka yi zina.

15 “Kada ka yi sata.

16 “Kada ka ɓāta sunan maƙwabcinka.

17 “Kada ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka, ko barorinsa mata da maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abin da yake nasa.”

Jama’a suka Tsorata

18 Da jama’a suka ji tsawar hadiri, da ƙarar ƙaho mai tsanani suka kuma ga walƙiya, da dutsen yana hayaƙi, sai suka ji tsoro suka yi rawar jiki, suka tsaya nesa.

19 Suka ce wa Musa, “Kai, ka yi magana da mu, za mu ji, amma kada Allah ya yi magana da mu don kada mu mutu.”

20 Musa kuwa ya ce wa jama’a, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo ne don ya jarraba ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”

21 Sai jama’a suka tsattsaya nesa, Musa kuwa ya matsa kusa da girgije mai duhu inda Allah yake.

Dokoki a kan Bagadai

22 Ubangiji ya ce wa Musa, “Haka za ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku da kanku kun ji na yi magana da ku daga sama.

23 Banda ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa da na zinariya.

24 Za ku gina mini bagade na ƙasa. A kansa za ku miƙa mini hadayu na ƙonawa da na salama, da tumakinku da shanunku. A duk inda na sa a tuna da sunana zan zo wurinku in sa muku albarka.

25 Idan kuwa za ku gina mini bagade na dutse, kada ku gina mini da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama idan guduma ta taɓa duwatsun sun haramtu.

26 Kada ku yi wa bagadena matakai domin kada tsiraicinku ya bayyana a bisansu sa’ad da kuke hawansu.”’