Categories
FIT

FIT 21

Yadda Za a Yi da Bayi

1 “Waɗannan su ne ka’idodin da za a ba Isra’ilawa.

2 Idan ka sayi bawa Ba’ibrane, zai yi bauta shekara shida, a shekara ta bakwai kuwa, a ‘yantar da shi kyauta.

3 Idan yana shi kaɗai aka saye shi, sai ya fita shi kaɗai, idan kuwa yana da aure sa’ad da aka saye shi, sai matarsa ta fita tare da shi.

4 Idan kuwa ubangijinsa ne ya auro masa matar, ta kuwa haifa masa ‘ya’ya mata ko maza, to, matar da ‘ya’yanta za su zama na ubangijinsa, amma shi kaɗai zai fita.

5 Amma idan hakika bawa ya hurta ya ce, yana ƙaunar ubangijinsa, da matarsa, da ‘ya’yansa, ba ya son ‘yancin,

6 to, sai ubangijinsa ya kawo shi a gaban Allah a ƙofa ko a madogarar ƙofa, sa’an nan ubangijinsa ya huda kunnensa da abin hudawa. Zai bauta wa ubangijinsa muddin ransa.

7 “Idan mutum ya sayar da ‘yarsa kamar baiwa, ba za a ‘yanta ta kamar bawa ba.

8 Idan ba ta gamshi maigidanta wanda ya maishe ta kamar ɗaya daga cikin matansa ba, sai ya yarda a fanshe ta. Amma ba shi da iko ya sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.

9 Idan ya ba da ita ga ɗansa ne sai ya maishe ta kamar ‘yarsa.

10 In mutumin ya auri wata kuma, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba.

11 Idan kuwa bai cika mata wajiban nan uku ba, sai ta fita abinta, ba zai karɓi kome ba.”

Dokoki game da Nuna Ƙarfi da Yaji

12 “Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle, shi ma sai a kashe shi.

13 In ba da nufi ya kashe shi ba, amma tsautsayi ne, to, sai mutumin ya tsere zuwa inda zan nuna muku.

14 Amma idan mutum ya fāɗa wa ɗan’uwansa da niyyar kisankai, lalle, sai a kashe shi ko da ya gudu zuwa bagadena.

15 “Wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle, kashe shi za a yi.

16 “Wanda ya saci mutum, ya sayar, ko kuwa a iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.

17 “Wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle kashe shi za a yi.

18 “Idan mutane suka yi faɗa, ɗayan ya jefa ɗayan da dutse, ko ya naushe shi amma bai mutu ba, sai dai ya yi ta jiyya,

19 idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓāta masa, ya kuma lura da shi har ya warke sarai.

20 “In mutum ya dūki bawansa ko baiwarsa da sanda har ya mutu a hannunsa, lalle ne a hukunta shi.

21 Amma idan bawan ya rayu kwana ɗaya ko biyu, to, kada a hukunta shi, gama bawan dukiyarsa ne.

22 “Idan mutum biyu na faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka zai biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara.

23 Amma in wani lahani ya auku, to, sai a hukunta rai a maimakon rai,

24 ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa,

25 ƙuna a maimakon ƙuna, rauni a maimakon rauni, ƙujewa a maimakon ƙujewa.

26 “Idan mutum ya bugi bawansa ko baiwarsa a ido har idon ya lalace, sai ya ‘yanta bawan ko baiwar a maimakon idon.

27 Idan ya fangare haƙorin bawansa ko na baiwarsa, sai ya ‘yanta bawan ko baiwar a maimakon haƙorin.”

Hakkin Masu Abu

28 “Idan sa ya kashe ko mace ko namiji, to, lalle ne a jajjefi san da duwatsu, kada kuma a ci namansa, mai san kuwa zai kuɓuta.

29 Amma idan san ya saba fafarar mutane, aka kuma yi wa mai shi kashedi, amma bai kula ba, har san ya kashe ko mace ko namiji, sai a jajjefi san duk da mai shi.

30 Idan an yanka masa diyya, sai ya biya iyakar abin da aka yanka masa don ya fanshi ransa.

31 Haka kuma za a yi idan san ya kashe ɗan wani ko ‘yar wani.

32 Idan san ya kashe bawa ko baiwa, sai mai san ya biya wa ubangijin bawan, ko baiwar, shekel talatin a kuma jajjefi san.

33 “Idan mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai rufe ba, in sa ko jaki ya fāɗa ciki,

34 mai ramin zai biya mai san ko mai jakin, mushen ya zama nasa.

35 Idan san wani ya yi wa na wani rauni har ya mutu, sai ya sayar da san da yake da rai a raba kuɗin. Haka kuma za su raba mushen.

36 Amma idan dā ma an sani san mafaɗaci ne, mai san kuwa bai kula da shi ba, sai ya biya, wato ya ba da sa a maimakon mushen. Mushen kuwa zai zama nasa.”

Categories
FIT

FIT 22

Dokokin Biya

1 “Idan mutum ya saci sa ko tunkiya, ya yanka ko ya sayar, zai biya shanu biyar a maimakon sa, tumaki huɗu maimakon tunkiya.

2 In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga ya yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa ga kowa ba,

3 sai dai ko in gari ya riga ya waye. Dole ɓarawon ya yi cikakkiyar ramuwa, in kuwa ba shi da abin biya, a sayar da shi a biya abin da ya satar.

4 In kuwa aka iske dabbar da ya satar a hannunsa da rai, ko sa, ko jaki, ko tunkiya, lalle ne ya biya riɓi biyu.

5 “In mutum ya kai dabbarsa kiwo a saura ko a garka, ya bar ta, ta yi ɓarna a gonar wani, ko a gonar inabin wani, sai a sa mai dabbar ya biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka.

6 “Idan wuta ta tashi a jeji ta ƙone tarin hatsi, ko hatsin da yake tsaye, ko gona, wanda ya sa wutar lalle ya biya cikakkiyar ramuwa.

7 “Idan mutum ya ba amininsa amanar kuɗi, ko amanar kadara, amma aka sace, in aka sami ɓarawon, a sa shi ya biya ninki biyu.

8 In kuwa ba a sami ɓarawon ba, sai a kawo maigidan a gaban Allah don a tabbatar babu hannunsa a cikin dukiyar amininsa.

9 “A kowane laifi na cin amana, ko sa ne, ko jaki, ko tunkiya, ko tufa, ko kowane ɓataccen abu, da abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin nan a gaban Allah. Wanda Allah ya ce shi ne da laifi, sai ya biya wa ɗayan ninki biyu.

10 “In mutum ya bai wa amininsa amanar jaki, ko sa, ko tunkiya ko kowace irin dabba, amma dabbar ta mutu, ko ta yi rauni, ko ta ɓace, in ba shaida,

11 rantsuwa ce za ta raba tsakaninsu don a tabbatar babu hannunsa a dukiyar amininsa, mai dukiyar kuwa ya yarda da rantsuwar. Wanda aka bai wa amanar ba zai biya ba.

12 In dai sacewa aka yi, sai ya biya mai shi.

13 Idan kuwa naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shida. Ba zai yi ramuwar abin da naman jeji ya kashe ba.

14 “Idan mutum ya yi aron wani abu a wurin maƙwabcinsa, in abin ya yi rauni ko ya mutu, sa’ad da mai abin ba ya nan, lalle ne ya yi ramuwa.

15 Amma in mai abin yana wurin, wanda ya yi aro ba zai yi ramuwa ba. Idan kuwa jingina ce aka yi, kuɗin jinginar ne ramuwar.”

Dokokin Addini da na Inganta Halin Kirki

16 “Idan mutum ya rarrashi budurwa wadda ba a tashinta, har ya ɓata ta, sai ya biya sadaki, ya aure ta.

17 Amma idan mahaifinta bai yarda ya ba da ita gare shi ba, sai mutumin ya ba da sadaki daidai da abin da akan biya domin budurwa.

18 “Kada a bar mace mai sihiri ta rayu.

19 “Duk wanda ya kwana da dabba, lalle kashe shi za a yi.

20 “Wanda ya miƙa hadaya ga wani allah, ba ga Ubangiji ba, sai a hallaka shi ɗungum.

21 “Kada ku wulakanta baƙo ko ku zalunce shi, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

22 Kada ku ci zalun marayu da gwauraye.

23 In kun tsananta musu, ba shakka za su yi kuka gare ni, ni kuma, hakika zan ji kukansu.

24 Zan husata, in sa a kashe ku cikin yaƙi, matanku, su ma, su zama gwauraye, ‘ya’yanku kuwa su zama marayu.

25 “Idan kun ranta wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku kuɗi, ba za ku zama musu kamar masu ba da rance da ruwa ba. Kada ku nemi ruwan kuɗin daga gare su.

26 In har wani ya karɓi rigar amininsa jingina, lalle ne ya mayar masa da ita kafin faɗuwar rana.

27 Gama wannan ne kaɗai mayafinsa, da shi zai rufe huntancinsa. Da me zai rufa ya yi barci? Zan amsa masa kuwa in ya yi kuka gare ni, gama cike nake da juyayi.

28 “Kada ku saɓi Allah, kada kuma ku zagi mai mulkin jama’arku.

29 “Kada ku yi jinkirin fitar da zakar amfanin gonarku ta hatsi da ta abin matsewa.

‘Ya’yan farinku, maza, kuma za ku ba ni su.

30 Haka kuma za ku yi da ‘ya’yan farin shanunku, da na awakinku, da na tumakinku. Ɗan farin zai yi kwana bakwai tare da uwar, amma a rana ta takwas za ku ba ni shi.

31 “Za ku zama keɓaɓɓun mutane a gare ni. Kada ku ci dabbar da naman jeji ya yayyage shi, sai ku jefa wa karnuka.”

Categories
FIT

FIT 23

Adalci da Aikata Gaskiya

1 Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada wani ya haɗa baki da mugu ya zama munafukin mashaidi.

2 Kada ku yi mugunta domin galibin mutane na yi, kada kuwa ku yi shaidar zur a gaban shari’a don ku faranta zuciyar yawancin mutane, domin kada ku sa a kauce wa adalci.

3 Kada ku yi wa matalauci sonkai a gaban shari’a.

4 “Idan wani ya iske san maƙiyinsa ko jakinsa ya ɓace, sai ya komar masa da shi.

5 Idan wani ya ga kaya ya danne jakin maƙiyinsa kada ya tafi ya bar shi da shi, sai ya taimaka a ɗaga masa.

6 “Kada ku rasa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a.

7 Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi da kuma adali, gama ba zan baratar da mugu ba.

8 Kada ku ci hanci, gama cin hanci yakan makantar da masu mulki, yakan kuma karkatar da manufar masu gaskiya.

9 “Kada ku wulakanta baƙo, kun dai san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.”

Shekara ta Bakwai da Rana ta Bakwai

10 “Za ku nomi gonakinku shekara shida, kuna tattara amfaninsu.

11 Amma a shekara ta bakwai, ku bar su su huta kurum, ba za ku girbi kome daga ciki ba, domin mutanenku matalauta su ci abin da ya ragu, namomin jeji kuma su ci. Haka kuma za ku yi da gonakinku na inabi da na zaitun.

12 “Cikin kwana shida za ku yi aikinku, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, don shanunku da jakunanku su kuma su huta, don bayinku da baƙinku su wartsake.

13 Ku kula da dukan abin da na faɗa muku. Kada a ji bakinku na roƙon kome ga waɗansu alloli.”

Ƙayyadaddun Idodi Uku

14 “Sau uku a shekara za ku yi mini idi.

15 Wajibi ne ku yi idin abinci marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Za ku ci abinci marar yisti kwana bakwai lokacin da aka ayyana a watan Abib, gama a wannan wata ne kuka fito daga Masar. Kada wani ya zo wurina hannu wofi.

16 Ku kuma yi idin nunan fari na amfanin gonakinku da kaka. Sa’an nan kuma za ku yi idin gama tattara amfanin gonakinku a ƙarshen shekara.

17 Sau uku a shekara mazaje za su gabatar da kansu a gaban Ubangiji.

18 “Kada ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti. Kada kuma ku ajiye kitsen abin da aka yanka a lokacin idina, ya kwana.

19 “Wajibi ne ku kawo mafi kyau daga cikin nunan fari na amfanin gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku.

“Kada ku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa.”

Mala’ikan Ubangiji zai Bi da Isra’ilawa

20 “Ni da kaina zan aiki mala’ika a gabanku don ya kiyaye ku a sa’ad da kuke tafiya, ya kuma kai ku inda na shirya muku.

21 Ku nuna masa bangirma, ku kasa kunne ga maganarsa. Kada ku tayar masa, gama ba zai gafarta muku laifofinku ba, gama shi wakilina ne.

22 Idan kun kasa kunne a hankali ga maganarsa, kuka aikata dukan abin da na faɗa, sai in zama maƙiyin maƙiyanku da magabcin magabtanku.

23 Mala’ikana zai wuce gabanku, ya bi da ku inda Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa suke, zan kuma hallakar da su ƙaƙaf.

24 Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu.

25 Za ku bauta wa Ubangiji Allahnku, ni kuwa zan yalwata abincinku da ruwan shanku, in kuma kawar muku da ciwo.

26 A ƙasarku, mace ba za ta yi ɓari ba, ba kuma za a sami marar haihuwa ba. Zan ba ku tsawon rai.

27 “Zan aiki razanata a gabanku, in sa mutanen da za ku gamu da su su ruɗe. Zan sa maƙiyanku duka su ba ku baya, su sheƙa a guje.

28 Zan aiki zirnako a gabanku, su kore muku Hiwiyawa, da Kan’aniyawa, da Hittiyawa.

29 Ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar ta zama kufai har namomin jeji su fi ƙarfinku.

30 Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku ya kai yadda za ku mallaki ƙasar.

31 Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.

32 Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu.

33 Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”

Categories
FIT

FIT 24

Tabbatar da Alkawari

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku zo wurina, kai, da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawa saba’in na Isra’ila. Ku yi sujada daga nesa kaɗan.

2 Musa ne kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama’a su hau tare da shi.”

3 Musa ya tafi, ya faɗa wa jama’a dukan dokokin Ubangiji da ka’idodinsa, sai dukan jama’a suka amsa gaba ɗaya, suka ce, “Za mu kiyaye dukan dokokin da Ubangiji ya ba mu.”

4 Musa kuwa ya rubuta dukan dokokin Ubangiji. Kashegari da sassafe ya gina bagade a gindin dutsen, da kuma ginshiƙai goma sha biyu bisa ga yawan kabilai goma sha biyu na Isra’ila.

5 Ya kuma sa samarin Isra’ila su miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama, da bijimai ga Ubangiji.

6 Sai Musa ya zuba rabin jinin a tasa, sauran rabin jinin kuwa ya yayyafa a kan bagade.

7 Ya kuma ɗauki Littafin Alkawari, ya karanta wa jama’a, sai suka ce, “Za mu yi dukan abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi biyayya.”

8 Musa kuwa ya ɗauki jinin ya watsa wa jama’ar. Sa’an nan ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, wanda yake cikin dokokin nan duka.”

9 Musa ya haura tare da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawan nan saba’in na Isra’ila.

10 Suka ga Allah na Isra’ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.

11 Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra’ila wani abu ba, ko da yake suka ga zatin Allah. Su kuma suka ci suka sha a gaban Allah.

Musa a bisa Dutsen Sina’i

12 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hawo zuwa wurina a bisa dutsen, ka zauna har in ba ka allunan dutse da yake da dokoki da farillan da na rubuta don a koya musu.”

13 Sai Musa ya tashi, shi da baransa Joshuwa, suka tafi, suka hau dutsen Allah.

14 Ya ce wa dattawan, “Ku dakata a nan har mu komo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai ya je wurinsu.” Sa’an nan Musa ya hau bisa dutsen.

15 Da hawan Musa bisa dutsen, girgije ya rufe kan dutsen.

16 Ɗaukakar Ubangiji kuma ta zauna bisa Dutsen Sina’i. Girgijen ya lulluɓe dutsen har kwana shida, a rana ta bakwai kuwa Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen.

17 Isra’ilawa suka ga ɗaukakar Ubangiji kamar wuta mai cinyewa a bisa ƙwanƙolin dutsen.

18 Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba’in da dare arba’in.

Categories
FIT

FIT 25

Sadakoki domin Yin Wuri Mai Tsarki

1 Ubangiji ya ce wa Musa,

2 “Faɗa wa Isra’ilawa su karɓo mini kaya daga dukan wanda ya yi niyyar bayarwa.

3 Ga irin sadakokin da za ku karɓa, zinariya, da azurfa, da tagulla,

4 da ulu mai launin shuɗi, da mai launin shunayya, da mai launin ja, da lilin mai laushi, da gashin akuya,

5 da jemammun fatun raguna, da fatun awaki, da itacen ƙirya,

6 da mai domin fitila, da kayan yaji domin man keɓewa, da turaren ƙonawa,

7 da onis, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

8 Za su yi tsattsarkan wuri domina, don in zauna tare da su.

9 Za ku yi mazaunina da kayayyakinsa duka, bisa ga irin fasalin da zan nuna maka.”

Akwatin Alkawari

10 “Sai ku yi akwatin alkawari da itacen maje, tsawonsa ya zama kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa ya zama kamu ɗaya da rabi.

11 Ku dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje. Ku yi wa gyaffansa ado da gurun zinariya.

12 Za ku yi wa akwatin ƙawanya huɗu na zinariya ku liƙa a kowace kusurwar akwatin, wato ƙawanya biyu a kowane gefe na tsawon.

13 Za ku kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.

14 Ku sa sandunan a kafar kowace ƙawanya da take gyaffan akwatin saboda ɗaukarsa.

15 Za a bar sandunan cikin ƙawanen akwatin, kada a zare su.

16 A kuma sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka a cikin akwatin.

17 “Za ku yi wa akwatin murfi da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

18 Za ku yi siffofin kerubobi biyu da ƙerarriyar zinariya, ku sa a gefen nan biyu na murfin.

19 Siffar kerub ɗaya a kowane gefe. Ku yi su ta yadda za su zama ɗaya da murfin.

20 Fikafikan kerubobin za su miƙe bisa domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin.

21 Za ku sa murfin bisa akwatin. A cikin akwatin kuwa za ku sa allunan da suke da dokokin da zan ba ka.

22 A nan zan zo in sadu da kai, in yi magana da kai, wato tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari. Zan ba ka umarnaina duka don Isra’ilawa.”

Teburin Gurasar Ajiyewa ga Ubangiji

23 “Ku yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

24 Ku dalaye shi da zinariya tsantsa, ku kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya.

25 Za ku yi wa tebur ɗin dajiya mai fāɗin tafin hannu, ku kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya.

26 Za ku yi ƙawanya huɗu da zinariya, ku sa a kusurwa huɗu na ƙafafun teburin.

27 Ƙawanen za su kasance kusa da dajiyar don su riƙe sandunan ɗaukar teburin.

28 Ku yi sanduna da itacen ƙirya, sa’an nan ku dalaye su da zinariya. Da su za a riƙa ɗaukar teburin.

29 Da zinariya tsantsa kuma za ku yi farantansa, da kwanonin tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin yin hadayu na sha.

30 Kullum za ku riƙa ajiye gurasar da kuke kawo mini a bisa teburin.”

Alkuki

31 “Ku kuma yi alkuki da zinariya tsantsa. Ku yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙuna, da mahaɗai, da furanninsa a haɗe da shi za ku yi su.

32 Alkukin ya kasance da rassa shida, rassa uku a kowane gefe.

33 A kowane reshe na alkuki za a yi ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond. Ya kasance kuma da mahaɗai da furanni.

34 Za a yi wa gorar alkukin ƙoƙuna huɗu masu kamar tohon almond, da mahaɗai da furanni.

35 A gindin kowane reshe biyu za a yi mahaɗi ɗaya.

36 Da mahaɗai da rassan za su kasance a haɗe da alkukin. Da ƙerarriyar zinariya za a yi su.

37 Ku kuma yi fitilu bakwai, ku sa su a bisa alkukin ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.

38 Ku kuma yi hantsuka da farantai da zinariya tsantsa.

39 Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya za ku yi alkukin da waɗannan abubuwa duka.

40 Sai ku lura, ku yi waɗannan abubuwa duka bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.”

Categories
FIT

FIT 26

Alfarwa, Wato Wurin da Allah Zai Zauna

1 “Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.

2 Tsawon kowane labule zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida.

3 Labule biyar biyar, za a harhaɗa, a ɗinka.

4 Ku kuma yi wa labulen nan biyu hantuna na shuɗi a karbunsu na bisa.

5 Za ku yi wa kowane labule hantuna hamsin. Hantunan labulen nan biyu su yi daura da juna.

6 Za ku yi maɗauri guda hamsin da zinariya don a haɗa hantuna na labulen nan domin alfarwa ta zama ɗaya.

7 “Ku yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki, da za ku rufe alfarwar da shi.

8 Tsawon kowanne zai zama kamu talatin, fāɗinsa kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida.

9 Za ku harhaɗa biyar ku ɗinka. Haka kuma za ku yi da sauran shidan. Ku ninka na shida riɓi biyu, ku yi labulen ƙofar alfarwa da shi.

10 Za ku kuma sa hantuna hamsin a karbun labulen daga bisa. Haka nan kuma za a sa hantuna hamsin a karbun ɗayan.

11 Sa’an nan ku yi maɗauri hamsin da tagulla, ku ɗaura hantunan da su don ku haɗa alfarwar ta zama ɗaya.

12 Ragowar rabin labulen da yake a bisa alfarwar, sai a bar shi yana reto a bayan alfarwar.

13 Kamu ɗayan da ya ragu a kowane gefe na tsawon, sai a bar shi yana reto a kowane gefe domin ya rufe alfarwar.

14 Za ku yi abin rufe alfarwa da fatun raguna da aka rina ja, za ku kuma yi wani abin rufewa da fatun da aka jeme.

15 “Za ku yi alfarwar da katakon itacen ƙirya. Za ku kakkafa su a tsaye.

16 Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi.

17 Za a fiƙe kan kowane katako. Haka za ku yi da dukan katakan.

18 Za ku shirya katakan alfarwa kamar haka, katakai ashirin wajen gefen kudu.

19 Ku kuma yi kwasfa arba’in da azurfa da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin kwasfa.

20 Za ku kuma kafa katakai ashirin wajen gefen arewa na alfarwar.

21 Haka kuma za ku yi kwasfa arba’in da azurfa dominsu. Kwasfa biyu domin kowane katako.

22 A wajen yamma ga alfarwa kuma ku kafa katakai shida.

23 Ku kuma sa katakai biyu a kowace kusurwa ta yamma a alfarwa.

24 Katakan nan kuwa, sai a haɗa su daga ƙasa zuwa sama, a ɗaure. Haka za a yi da katakan kusurwan nan biyu. Za su zama na kusurwa biyu.

25 Za a sami katakai takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da kwasfa biyu.

26 “Sai ku yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya.

27 Biyar kuma domin katakai na wancan gefe. Har yanzu kuma biyar domin katakai na gefen yamma.

28 Sandan da yake tsakiyar katakan zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe.

29 Za ku dalaye katakan da zinariya, ku kuma yi musu ƙawanen zinariya inda za a sa sandunan. Za ku dalaye sanduna kuma da zinariya.

30 Ta haka za ku yi alfarwar bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.

31 “Za ku yi labule da lallausan zaren lilin, mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A yi shi da gwaninta, a zana siffofin kerubobi a kansa.

32 Ku rataye shi a bisa dirkoki huɗu nan itacen ƙirya waɗanda aka dalaye da zinariya, da maratayansu na zinariya waɗanda aka sa cikin kwasfa huɗu na azurfa.

33 Za ku sa labulen a ƙarƙashin maɗauran, sa’an nan ku shigar da akwatin alkawari a bayan labulen. Labulen zai raba tsakanin Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki.

34 Ku sa murfin a bisa akwatin alkawari a Wuri Mafi Tsarki.

35 Sai ku sa teburin a gaban labulen wajen arewa, ku kuma sa alkukin a kudancin alfarwar daura da teburin.

36 Haka nan kuma za ku yi wa ƙofar alfarwa makari da lallausan zaren lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi, aikin mai gwaninta.

37 Ku yi dirkoki biyar da itacen ƙirya saboda makarin, ku dalaye su da zinariya. Ku kuma yi maratayansu da zinariya. Ku yi wa waɗannan dirkoki kwasfa biyar da tagulla.”

Categories
FIT

FIT 27

Bagade

1 “Za ku yi bagaden da itacen ƙirya, mai tsawo kamu biyar, da fāɗi kamu biyar, tsayinsa kamu uku. Bagaden zai zama murabba’i.

2 A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla.

3 Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.

4 Za ku kuma yi wa bagaden raga da tagulla, sa’an nan ku sa wa ragar ƙawane a kusurwoyinta huɗu.

5 Za ku sa ragar a cikin bagaden a tsakiya.

6 Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa’an nan ku dalaye su da tagulla.

7 Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa.

8 Za ku yi bagaden da katakai, sa’an nan ku roɓe cikinsa. Ku yi shi bisa ga fasalin da na nuna maka bisa dutsen.

Farfajiyar Alfarwar

9 “Za ku yi wa alfarwa farfajiya. A kudancin farfajiyar, sai ku rataye labule mai tsawo kamu ɗari wanda aka saƙa da lallausan zaren lilin.

10 Za ku yi masa dirkoki guda ashirin, da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.

11 A wajen arewa kuma, sai ku rataya labule mai tsawon kamu ɗari. Ku yi masa dirkoki da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.

12 Fāɗin labulen a wajen yamma na farfajiyar, zai zama kamu hamsin. A yi wa labulen dirkoki goma, a kuma yi wa dirkokin kwasfa goma.

13 Fāɗin labulen wajen gabas na farfajiyar zai zama kamu hamsin.

14 Labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

15 Haka kuma labulen ƙofa na wancan gefe zai zama kamu goma sha biyar, da dirkoki uku tare da kwasfansu uku.

16 Za a saƙa labule mai kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai launi shuɗi, da shunayya, da mulufi domin ƙofar farfajiyar. Za a sa wa ƙofar dirkoki huɗu tare da kwasfansu huɗu.

17 Za a yi wa dukan dirkokin da suke kewaye da farfajiyar maɗaurai da maratayai na azurfa, da kwasfa ta tagulla.

18 Tsawon farfajiyar zai zama kamu ɗari, fāɗinta kamu hamsin, tsayinta kamu biyar. Za a saƙa labulenta da lallausan zaren lilin, a kuma yi kwasfanta da tagulla.

19 Da tagulla kuma za a yi turakun alfarwar, da turakun farfajiyar, da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a cikin alfarwar.”

Kulawa da Fitila

20 “Sai a umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen man zaitun tatacce domin fitilar. Za a kunna fitilar ta yi ta ci koyaushe.

21 Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da ‘ya’yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka’ida har abada ga Isra’ilawa.”

Categories
FIT

FIT 28

Tufafin Firistoci

1 “Daga cikin ‘ya’ya maza na Isra’ila sai ka kirawo ɗan’uwanka Haruna tare da ‘ya’yansa, Nadab, da Abihu, da Ele’azara, da Itamar, su zama firistoci masu yi mini aiki.

2 A ɗinka wa Haruna ɗan’uwanka, tufafi masu tsarki domin daraja da kwarjini.

3 Ka kuma yi magana da gwanayen sana’a duka waɗanda na ba su fasaha, don su ɗinka wa Haruna tufafi, gama za a keɓe shi ya zama firist ɗina.

4 Waɗannan su ne irin tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da falmaran, da taguwa, da zilaika, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna, da ‘ya’yansa tufafi tsarkaka, don su zama firistoci masu yi mini aiki.

5 Sai su yi amfani da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.

6 “Za su yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya da mulufi, da lallausan zaren lilin, aikin gwani.

7 Za a yi mata kafaɗa biyu, sa’an nan a haɗa su a karbunsu.

8 Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi falmaran, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Za a yi mata saƙar gwaninta.

9 A kuma ɗauki duwatsu biyu masu daraja, a zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila a kai.

10 Sunaye shida a kowane dutse bi da bi bisa ga haihuwarsu.

11 Za a zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila a bisa duwatsun nan kamar yadda mai yin aiki da lu’ulu’u yakan zana hatimai. Za a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya.

12 A sa duwatsun a kafaɗun falmaran domin a riƙa tunawa da ‘ya’yan Isra’ila. Haruna zai rataya sunayensu a kafaɗunsa a gaban Ubangiji domin a tuna da su.

13 Za ku yi tsaiko biyu na zinariya,

14 ku kuma yi tukakkun sarƙoki biyu na zinariya tsantsa. Za ku ɗaura wa tsaikunan nan tukakkun sarƙoƙi.

15 “Ku kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji domin neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa falmaran ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.

16 Ƙyallen maƙalawa a ƙirji zai zama murabba’i, a ninke shi biyu tsawonsa da fāɗinsa su zama kamu ɗaya ɗaya.

17 Sai a yi jeri huɗu na duwatsun a kanta. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.

18 A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon.

19 A jeri na uku, a sa yakinta, da idon mage, da ametis.

20 A jeri na huɗu, a sa beril, da onis, da yasfa. Za a sa su cikin tsaiko na zinariya.

21 A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zana sunayen kamar hatimi.

22 Ku kuma yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirji tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa.

23 Za ku yi ƙawanya biyu na zinariya, ku sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

24 Ku sa tukakkun sarkoƙin nan biyu na zinariya a cikin ƙawanya biyu na zinariya da suke a gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a haɗa su daga gaba a kafaɗun falmaran.

25 Za ku kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a cikin tsaikuna, sa’an nan a sa shi a gaban kafaɗun falmaran.

26 Ku kuma yi waɗansu ƙawane na zinariya, a sa su a sauran kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefe na cikin da yake manne da falmaran.

27 Ku kuma yi waɗansu ƙawanya biyu na zinariya, a sa su a ƙashiyar kafaɗu biyu na falmaran daga gaba, a sama da abin ɗamaran nan.

28 Za su ɗaure ƙyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanensa haɗe da ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya zauna bisa abin ɗamarar falmaran, don kuma kada ya yi sako-sako a bisa falmaran.

29 Duk sa’ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai ɗauki sunayen ‘ya’yan Isra’ila a gaban Ubangiji kullum, a kan ƙyallen maƙalawa domin nemar musu nufin Allah.

30 Za ku kuma sa Urim da Tummin a kan ƙyallen maƙalawar domin su kasance a zuciyar Haruna sa’ad da ya shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai kokekoken Isra’ilawa a gaban Ubangiji.

31 “Sai ku yi taguwar falmaran da shuɗi duka.

32 Za a yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A yi wa wuyan shafi, sa’an nan a yi wa wuyan basitsa, wato cin wuya, domin kada ya kece.

33 Za a yi wa karbun taguwar ado da fasalin ‘ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu.

34 Za a jera su bi da bi, wato ‘ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya.

35 Sai Haruna ya sa taguwar sa’ad da yake aiki. Za a ji ƙarar ƙararrawar a lokacin da yake shiga da lokacin da yake fita Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji don kada ya mutu.

36 “Sai kuma a yi allo na zinariya tsantsa, a zana rubutu irin na hatimi a kansa haka, ‘MAI TSARKI GA UBANGIJI.’

37 Sai a ɗaura shi da shuɗiyar igiya a rawanin daga gaba.

38 Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji.

39 “Ku saƙa zilaika da lallausan zaren lilin. Ku yi rawani da lallausan zaren lilin, ku kuma saƙa abin ɗamara mai ado.

40 “Za a yi wa ‘ya’yan Haruna, maza, zilaiku, da abubuwan ɗamara, da huluna don daraja da kwarjini.

41 Ka sa wa Haruna, ɗan’uwanka, da ‘ya’yansa maza, sa’an nan ka zuba musu mai, ka keɓe su, ka tsarkake su domin su zama firistoci masu yi mini aiki.

42 Sai kuma ku yi musu mukurai na lilin don su rufe tsiraicinsu daga kwankwaso zuwa cinya.

43 Haruna da ‘ya’yansa maza za su sa su sa’ad da suke shiga alfarwa ta sujada ko kuwa sa’ad da suka kusaci bagade domin su yi aiki cikin Wuri Mai Tsarki domin kada su yi laifin da zai zama sanadin mutuwarsu. Wannan zai zama doka ga Haruna da zuriyarsa har abada.”

Categories
FIT

FIT 29

Keɓewar Haruna da ‘Ya’yansa Maza

1 “Abin da za ka yi wa Haruna da ‘ya’yansa ke nan don ka keɓe su su zama firistoci masu yi mini aiki. Za ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani,

2 da abinci marar yisti, da waina wadda aka cuɗe da mai, wadda aka yi da garin alkama mai laushi.

3 Ka sa waɗannan abu cikin kwando, sa’an nan ka kawo su cikin kwandon, ka kuma kawo ɗan bijimin da raguna biyu ɗin.

4 “Ka kawo Haruna da ‘ya’yansa maza a ƙofar alfarwar ta sujada, ka yi musu wanka.

5 Sa’an nan ka kawo tufafin, ka sa wa Haruna zilaikar, da taguwar falmaran, da falmaran ɗin, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa’an nan ka ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.

6 Za ka naɗa masa rawanin, sa’an nan ka ɗora kambi mai tsarki a bisa rawanin.

7 Ka kuma ɗauki man keɓewa, ka zuba masa a ka domin ka keɓe shi.

8 “Sa’an nan ka kawo ‘ya’yansa maza, ka sa musu zilaikun.

9 Ka kuma ɗaura musu ɗamara, ka sa musu hulunan. Aikin firist kuwa zai zama nasu har abada bisa ga dokar. Haka za ka keɓe Haruna da ‘ya’yansa maza.

10 “A kuma kawo bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada. Haruna da ‘ya’yansa maza za su ɗora hannuwansu a kan bijimin.

11 Za ka yanka bijimin a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

12 Za ka ɗibi jinin bijimin ka sa a bisa zankayen bagaden da yatsanka. Sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden.

13 Ka cire dukan kitsen da yake rufe da kayan cikin, da kitsen da yake manne da hanta, da wanda yake manne a ƙoda biyu ɗin. Ka ƙone su a bisa bagaden.

14 Amma naman bijimin da fatarsa, da tarosonsa, za ka ƙone da wuta a bayan zango, wannan hadaya ce don zunubi.

15 “Sai a kawo rago ɗaya, Haruna kuwa da ‘ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a bisa ragon.

16 Sa’an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa, ka yayyafa shi kewaye a kan bagaden.

17 Ka kuma yanyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikinsa, da ƙafafunsa, ka haɗa su da gunduwoyin, da kan.

18 Sa’an nan ka ƙone ragon duka a bisa bagaden don ya ba da ƙanshi. Wannan hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, wato hadayar da aka ƙone da wuta.

19 “A kuma kawo ɗayan ragon, Haruna kuma da ‘ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a bisa ragon.

20 Sa’an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa ka shafa bisa leɓatun kunnen Haruna na dama, da bisa leɓatun kunnuwan ‘ya’yansa maza na dama, da a kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi a kewaye a kan bagaden.

21 Ka ɗiba daga cikin jinin da yake bisa bagaden, da man keɓewa, ka yayyafa wa Haruna da tufafinsa, da bisa ‘ya’yansa maza, da tufafinsu don a tsarkake Haruna, da ‘ya’yansa maza, da tufafinsu.

22 “Sai ka ɗebe kitsen ragon, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebe kitsen da yake rufe da kayan ciki, da dunƙulen kitsen da yake a bisa hanta, da ƙoda biyu ɗin da kitsensu, da cinyar dama, gama ragon na keɓewa ne.

23 Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, sai ka ɗauki malmala ɗaya, da waina ɗaya da aka yi da mai, da ƙosai ɗaya.

24 Za ka sa waɗannan duka a hannun Haruna da na ‘ya’yansa maza. Sai su kaɗa su domin hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.

25 Sa’an nan za ka karɓe su daga hannunsu, ka ƙone su a bisa bagaden kamar hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Ita hadaya ce ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji.

26 “Za ka ɗauki ƙirjin ragon da aka yanka don keɓewar Haruna, ka kaɗa shi don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan ƙirji zai zama rabonka.

27 Za ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa da za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon keɓewa, wanda yake na Haruna da wanda yake na ‘ya’yansa maza.

28 Wannan zai zama rabon Haruna da na ‘ya’yansa maza daga wurin Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.

29 “Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na ‘ya’yansa maza bayan rasuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su.

30 Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga alfarwa ta sujada, domin ya yi aiki a Wuri Mai Tsarki.

31 “Sai ka ɗauki naman ragon keɓewa, ka dafa shi a wuri mai tsarki.

32 Haruna da ‘ya’yansa maza za su ci naman da abinci da yake a cikin kwandon a ƙofar alfarwa ta sujada.

33 Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.

34 Amma idan naman keɓewar ko abincin ya ragu har safiya, sai ka ƙone abin da ya ragu, kada a ci, gama tsattsarka ne.

35 “Haka nan za ka yi wa Haruna da ‘ya’yansa maza bisa ga dukan abin da na umarce ka. Kwana bakwai za ka ɗauka domin keɓewarsu.

36 A kowace rana za ka miƙa bijimi na hadaya domin zunubi ta yin kafara. Za ka tsarkake bagaden lokacin da ka yi kafara dominsa. Ka zuba masa mai, ka keɓe shi.

37 Kwana bakwai za ka ɗauka na yin kafara don bagaden, ka keɓe shi, haka kuwa bagaden zai zama mafi tsarki. Duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.”

Hadayu na Yau da Kullum

38 “Wannan shi ne abin da za a miƙa a bisa bagaden kullum, ‘yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya.

39 Za a miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da maraice.

40 Haɗe da rago na fari, za a miƙa mudun gari mai laushi garwaye da rubu’in moɗa na tataccen mai, da rubu’in moɗa na ruwan inabi domin hadaya ta sha.

41 Ɗaya ragon kuma a miƙa shi da maraice. Za a miƙa shi tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha kamar wadda aka yi da safe ɗin domin ta ba da ƙanshi mai daɗi, gama hadaya ce wadda aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

42 Wannan hadaya ta ƙonawa za a riƙa yinta dukan zamananku a bakin ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, inda ni zan sadu da kai in yi magana da kai.

43 Nan ne zan sadu da Isra’ilawa in tsarkake wurin da ɗaukakata.

44 Zan tsarkake alfarwa ta sujada da bagaden, zan kuma tsarkake Haruna da ‘ya’yansa maza don su zama firistoci masu yi mini aiki.

45 Zan zauna tare da Isra’ilawa, in zama Allahnsu.

46 Za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu wanda ya fisshe su daga Masar don in zauna tare da su. Ni ne Ubangiji Allahnsu.”

Categories
FIT

FIT 30

Bagaden Ƙona Turare

1 “Za ku yi bagaden ƙona turare. Za ku yi shi da itacen ƙirya.

2 Tsawonsa da fāɗinsa kamu guda guda ne, zai zama murabba’i, amma tsayinsa ya zama kamu biyu. Za a haɗa zankayensa su zama ɗaya da shi.

3 Za ku dalaye shi, da bisansa, da gyaffansa, da zankayensa da zinariya tsantsa. Ku kuma yi masa dajiyar zinariya.

4 Za ku yi masa ƙawanya biyu na zinariya a ƙarƙashin dajiyar gefe da gefe, daura da juna. Ƙawanen za su zama inda za a zura sandunan ɗaukarsa.

5 Za ku yi sandunan da itacen ƙirya, ku dalaye su da zinariya.

6 Sai ku ajiye bagaden a gaban labulen akwatin alkawari da murfin akwati inda zan sadu da kai.

7 Haruna kuwa zai ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kowace safiya lokacin da yake gyarta fitilun.

8 Zai kuma ƙona turaren sa’ad da ya kunna fitilun da almuru. Za a riƙa ƙona turare kullum a gaban Ubangiji dukan zamananku.

9 Ba za a ƙona wani irin turare dabam ba a bisansa, ba kuma za a miƙa hadaya ta ƙonawa, ko ta gari, ko ta sha, a bisansa ba.

10 Sau ɗaya a shekara Haruna zai yi kafara a bisa zankayensa. Zai yi kafara a bisansa da jinin hadaya don zunubi ta yin kafara. Za a riƙa yin wannan dukan zamananku, gama bagaden mai tsarki ne ga Ubangiji.”

Kuɗin Haikali

11 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa,

12 “A sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, sai ko wannensu ya biya fansar kansa ga Ubangiji domin kada annoba ta buge su lokacin da za ku ƙidaya su.

13 Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.

14 Duk wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar tun daga mai shekara ashirin ko fi, zai ba da wannan sadaka ga Ubangiji.

15 Lokacin da kuke ba da wannan sadaka ga Ubangiji saboda kafarar rayukanku, mai samu ba zai zarce ba, matalauci kuma ba zai ba da abin da ya gaza abin da aka ƙayyade ba.

16 Za ku karɓi kuɗin nan na kafara daga wurin Isra’ilawa, ku ajiye shi domin aiki a alfarwa ta sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar kansu.”

Daron Tagulla na Wanke Hannu

17 Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

18 “Sai ku yi daro da tagulla don wanka. Ku yi masa gammo da tagulla, ku ajiye shi tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, ku zuba ruwa a ciki.

19 A wurin ne Haruna da ‘ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu.

20 Sa’ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa’ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su.

21 Su wanke hannuwansu da ƙafafunsu don kada su mutu. Yin wannan zai zama musu da zuriyarsu farilla dukan zamanansu.”

Man Keɓewa da Turare

22 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

23 “Ɗauki kayan yaji masu kyan gaske, ruwan mur na shekel ɗari biyar, da kirfa mai daɗin ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin, da turaren wuta mai ƙanshi na shekel ɗari biyu da hamsin,

24 da kashiya na shekel ɗari biyar bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi, da moɗa ɗaya na man zaitun.

25 Da waɗannan za ku yi man keɓewa mai tsarki yadda mai yin turare yake yi, zai zama man keɓewa mai tsarki.

26 Za a shafa wa alfarwa ta sujada da akwatin alkawari wannan mai.

27 A kuma shafa wa teburin da kayayyakinsa, da alkukin da kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,

28 da bagaden hadaya ta ƙonawa da kayayyakinsa, da daron da gammonsa.

29 Ta haka za a tsarkake su domin su zama masu tsarki sosai. Duk abin da ya taɓa su zai tsarkaka.

30 Za ka zuba wa Haruna da ya’yansa maza mai, ka keɓe su domin su zama firistocina masu yi mini aiki.

31 Sai ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Wannan mai, mai tsarki ne a gare ni domin keɓewa a dukan zamananku.

32 Ba za a shafa wa kowa ba, ba kuma za a yi wani mai irinsa ba, gama man tsattsarka ne, saboda haka zai kasance tsattsarka a gare ku.

33 Duk wanda ya yi wani irinsa ko kuwa ya shafa wa wani, za a raba shi da jama’arsa.”’

34 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ɗauki kayan yaji masu ƙanshi, su stakte, da onika, da galbanum tare da lubban. Su zama daidai wa daida.

35 Da waɗannan za a yi turare yadda mai yin turare yake yi, a sa masa gishiri, ya zama tsabtatacce, tsarkakakke.

36 A ɗauki kaɗan daga ciki, a niƙa, sa’an nan a ɗiba daga ciki, a ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin alfarwa ta sujada a inda zan sadu da kai. Wannan turare zai zama muku mafi tsarki.

37 Irin turaren nan da za ku yi, ba za ku yi wa kanku irinsa ba. Zai zama abu mai tsarki a gare ku, gama na Ubangiji ne.

38 Duk wanda ya yi irin turaren nan don amfanin kansa, za a raba shi da jama’arsa.”