Categories
FIT

FIT 31

Waɗanda za su Yi alfarwa ta Sujada

1 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

2 “Ga shi, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.

3 Na cika shi da Ruhuna, da hikima, da basira, da ilimi, da fasaha,

4 don ya yi fasalin abubuwa na zinariya, da azurfa, da tagulla,

5 da yankan duwatsu masu tamani na jerawa, da sassaƙa itace, da kowane irin aikin fasaha.

6 Ga shi kuma, ni da kaina, na sa Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan tare da shi, na kuma sa hikima a zukatan masu hikima, don su yi dukan abin da na umarce ka

7 a kan alfarwar ta sujada da akwatin alkawari, da murfin da yake bisansa, da dukan kayayyakin da yake cikin alfarwar,

8 da teburin da kayayyakinsa, da alkuki na zinariya tsantsa tare da dukan kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,

9 da bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa,

10 da saƙaƙƙun tufafi, wato da tsarkakakkun tufafin Haruna da na ‘ya’yansa maza domin aikin firistoci,

11 da man keɓewa, da turaren nan mai ƙanshi domin Wuri Mai Tsarki. Za su yi su duka kamar yadda na umarce ka.”

Ranar Hutawa

12 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

13 “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.

14 Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama’arsa.

15 A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduda ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi.

16 Domin wannan fa Isra’ilawa za su kiyaye ranar Asabar, su kiyaye ta dukan zamanansu, gama madawwamin alkawari ne.

17 Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra’ilawa, cewa a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da ƙasa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta.”’

18 Sa’ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina’i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.

Categories
FIT

FIT 32

Ɗan Maraƙin Zinariya

1 Da mutane suka ga Musa ya yi jinkirin saukowa daga dutsen, sai suka taru wurin Haruna, suka ce masa, “Tashi, ka yi mana allahn da zai shugabance mu, gama ba mu san abin da ya faru da Musa ɗin wanda ya fisshe mu daga ƙasar Masar ba.”

2 Haruna ya ce musu, “Ku tuttuɓe zobban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na ‘ya’yanku maza da mata, ku kawo mini.”

3 Sai jama’a duka suka tuttuɓe zobban zinariya da suke a kunnuwansu, suka kawo wa Haruna.

4 Ya karɓi zobban a hannunsu, sai ya narkar da su, ya sassaƙa shi da kurfi, ya siffata ɗan maraƙi. Da jama’a suka gani, sai suka ce, “Allahnku ke nan, ya Isra’ila, wanda ya fisshe ku daga Masar.”

5 Sa’ad da Haruna ya gani, ya gina bagade a gaban siffar maraƙin, ya yi shela, ya ce, “Gobe akwai idi ga Ubangiji.”

6 Kashegari da sassafe, suka tashi, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama. Jama’ar kuma suka zauna su ci su sha, suka kuma tashi suna rawa.

7 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama’arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu.

8 Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra’ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar.”’

9 Ya kuma ce wa Musa, “Na ga jama’an nan suna da taurinkai.

10 Yanzu dai, ka bar ni kawai fushina ya yi ƙuna a kansu, ya cinye su, amma kai zan maishe ka babbar al’umma.”

11 Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar?

12 Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, don ƙeta ce ya fitar da su, don ya kashe su cikin duwatsu, ya shafe su sarai daga duniya?’ Ka janye zafin fushinka, kada kuma ka jawo wa jama’arka masifa.

13 Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada.”’

14 Ubangiji kuwa ya huce, ya janye niyyarsa ta jawo masifa a kan jama’arsa.

15 Musa ya sauko daga kan dutsen da allunan dutsen nan biyu na shaida a hannunsa. Allunan rubutattu ne ciki da baya.

16 Allunan kuwa aikin Allah ne, rubutun kuma na Allah ne da ya zāna a kan allunan.

17 A sa’ad da Joshuwa ya ji hayaniyar jama’ar, sai ya ce wa Musa, “Akwai hargowar yaƙi a zangon.”

18 Musa kuwa ya ce, “Ai, wannan ba hargowar nasara ba ce, ba kuma ta waɗanda yaƙi ya ci ba ce, amma hayaniyar waƙa nake ji.”

19 Yana kusato zango, sai ya ga siffar ɗan maraƙi, mutane na ta rawa. Musa kuwa ya harzuƙa, ya watsar da allunan da suke hannunsa a gindin dutsen, suka farfashe.

20 Ya ɗauki siffar ɗan maraƙin da suka yi, ya ƙone ta, ya niƙe, ta zama gari, ya barbaɗa a ruwa, ya sa Isra’ilawa su sha.

21 Musa ya ce wa Haruna, “Me waɗannan mutane suka yi maka, da ka jawo musu babban zunubi?”

22 Haruna kuwa ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, kada ka ji haushina, ka san jama’an nan sarai da irin halinsu na son aikata mugunta.

23 Sun ce mini, ‘Yi mana allahn da zai shugabance mu, gama Musa, mutumin da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya same shi ba.’

24 Ni kuwa sai na ce musu, ‘Bari duk wanda yake da zinariya ya tuɓe.’ Waɗanda suke da ita, suka tuɓe, suka kawo mini, ni kuwa na zuba su cikin wuta, daga nan wannan maraƙi ya fito.”

25 Musa ya ga jama’ar sun sangarce, domin Haruna ya sa su sangarce, ya bar su su bauta wa gunki har suka zama abin kunya a gaban magabtansu.

26 Musa ya tsaya a ƙofar zango, ya ce, “Duk wanda yake wajen Ubangiji ya zo wurina.” Sai Lawiyawa suka tattaru a wurinsa.

27 Ya ce musu, “Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘Kowane mutum ya rataya takobinsa, ya kai ya kawo daga ƙofa zuwa ƙofa cikin zango duka, kowa ya kashe ɗan’uwansa, kowa ya kashe zumunsa, kowa ya kashe maƙwabcinsa.”’

28 Lawiyawa kuwa suka yi yadda Musa ya faɗa. A ranan nan aka kashe mutum wajen talata (3,000).

29 Sai Musa ya ce, “Yau kun ba da kanku ga Ubangiji, gama kowane mutum ya kashe ɗansa da ɗan’uwansa, ta haka kuka jawo wa kanku albarka yau.”

30 Kashegari, Musa ya ce wa mutane, “Kun aikata babban zunubi. Yanzu kuwa zan tafi wurin Ubangiji, watakila zan iya yin kafara domin zunubanku.”

31 Musa ya koma wurin Ubangiji, ya ce, “Kaito, mutanen nan sun aikata zunubi mai girma, sun yi wa kansu gunkin zinariya.

32 Amma ina roƙonka ka gafarta zunubansu, in kuwa ba haka ba, ina roƙonka ka shafe sunana daga cikin littafin da ka rubuta.”

33 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ai, dukan wanda ya yi mini zunubi, shi ne zan shafe sunansa daga cikin littafina.

34 Yanzu fa, sai ka tafi, ka bi da mutanen zuwa wurin da zan faɗa maka, ga shi, mala’ikana zai wuce gabanka. Duk da haka a ranar da zan waiwaye ku, zan hukunta su saboda zunubinsu.”

35 Sai Ubangiji ya aika wa mutanen da annoba saboda ɗan maraƙin da suka sa Haruna ya yi musu.

Categories
FIT

FIT 33

An Ba da Umarni a Kama Tafiya

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi, ka kama hanya, kai da jama’ar da ka fisshe su daga ƙasar Masar, zuwa ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, na ce, ‘Ga zuriyarka zan ba da ita.’

2 Zan kuwa aiki mala’ika a gabanka. Zan kuma kori Kan’aniyawa da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Farizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

3 Ka kama hanya zuwa ƙasa mai yalwar abinci, amma fa ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurin kai, domin kada in hallaka ku a hanya.”

4 Da jama’ar suka ji wannan mugun labari, sai suka yi nadama. Ba wanda ya sa kayan ado.

5 Gama Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurin kai. In na yi tafiya tare da ku, nan da nan zan hallaka ku. Domin haka fa, yanzu, ku tuɓe kayan adonku, domin in san abin da zan yi da ku.”’

6 Domin haka Isra’ilawa suka tuɓe kayan adonsu tun daga dutsen Horeb har zuwa gaba.

Alfarwa ta Sujada

7 Musa ya ɗauki alfarwa, ya kafa ta a bayan zango, nesa da zango. Ya kuwa sa mata suna, Alfarwa ta Sujada. Duk wanda yake neman Ubangiji, sai ya tafi alfarwa ta sujada, wanda yake a bayan zango.

8 Duk sa’ad da Musa ya tafi wurin alfarwar, jama’a duka sukan tashi tsaye, kowa ya tsaya a ƙofar alfarwarsa, ya kallaci Musa, har ya shiga alfarwar.

9 Sa’ad da Musa ya shiga alfarwar, al’amudin girgije ya sauko ya tsaya bisa ƙofar alfarwar, Ubangiji kuma ya yi magana da Musa.

10 A sa’ad da jama’a suka ga al’amudin girgijen nan na tsaye a ƙofar alfarwar, sai jama’ar duka su tashi su yi sujada, kowa a ƙofar alfarwarsa.

11 Ta haka Ubangiji ya riƙa yin magana da Musa baki da baki, kamar yadda mutum yakan yi magana da amininsa. Sa’ad da Musa ya koma cikin zango kuma, baransa, Joshuwa, ɗan Num, saurayi, ba zai fita daga cikin alfarwar ba.

Alkawarin Zatin Ubangiji

12 Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’

13 Yanzu ina roƙonka idan na sami tagomashi a gare ka, ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma sami tagomashi a wurinka, ka kuma tuna, wannan al’umma jama’arka ce.”

14 Ubangiji kuwa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.”

15 Musa kuwa ya ce masa, “In ba za ka tafi tare da mu ba, to, kada ka ɗaga mu daga nan.

16 Yaya zan sani ko na sami tagomashi a wurinka, ni da jama’arka, in ba ka tafi tare da mu ba? Yaya ni da jama’arka, za a bambanta mu da sauran jama’ar da suke a duniya?”

17 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka ce, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”

18 Musa kuwa ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini kanka.”

19 Sai Ubangiji ya ce masa, “Zan wuce a gabanka, Ni Ubangiji zan yi shelar sunana a gabanka, zan kuma yi alheri ga wanda nā yi wa alheri, in nuna jinƙai ga wanda nā yi wa jinƙai.”

20 Ya kuma ce, “Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama mutum ba zai gan ni ba, ya rayu.”

21 Ubangiji ya ce, “Ga wani wuri kusa da ni inda za ka tsaya bisa dutsen.

22 A sa’ad da zatina yake wucewa, zan sa ka a tsaguwar dutsen, in rufe ka da hannuna har in wuce,

23 sa’an nan in ɗauke hannuna, za ka kuwa ga bayana, amma ba za ka ga fuskata ba.”

Categories
FIT

FIT 34

Allunan Dutse na Biyu

1 Ubangiji ya ce wa Musa, “Sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farkon, ni kuwa in rubuta kalmomin da suke cikin alluna na farko da ka farfasa.

2 Da safe ka shirya, ka zo Dutsen Sina’i ka gabatar da kanka gare ni a kan dutsen.

3 Kada wani mutum ya zo tare da kai, kada a ga kowane mutum a ko’ina a kan dutsen, kada a bar garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”

4 Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau Dutsen Sina’i, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya riƙe allunan nan biyu na dutse a hannunsa.

5 Ubangiji kuwa ya sauko cikin girgije ya tsaya tare da shi a can, ya yi shelar sunansa.

6 Ya kuma gifta a gaban Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya.

7 Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi, wanda ba zai kuɓutar da mai mugunta ba, amma saboda laifin iyaye nakan hukunta ‘ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu.”

8 Sai Musa ya hanzarta, ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya yi sujada.

9 Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama’a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”

Sabunta Alkawari

10 Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na yi alkawari, cewa a gaban dukan jama’a zan aikata al’ajabai irin waɗanda ba a taɓa aikatawa a duniya ba, ko cikin wata al’umma. Dukan mutanen da kuke zaune tare da su za su ga aikina, gama zan aikata abin bantsoro a cikinku.

11 Ku kiyaye abin da na umarce ku a wannan rana. Ga shi, zan kora muku Amoriyawa, da Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

12 Ku fa kula da kanku, kada ku kuskura, ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, don kada su zama muku alƙalai.

13 Sai ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al’amudansu, ku sassare gumakansu.

14 “Ba za ku yi wa wani allah sujada ba, sai dai ni, gama sunana Mai Kishi, gama ni Allah mai kishi ne.

15 Kada ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar don kada sa’ad da suke shagulgulan bidi’arsu ga allolinsu, suna miƙa musu hadaya, waninsu ya gayyace ku ku ci abin hadayarsa.

16 Kada kuma ku auro wa ‘ya’yanku maza ‘yan matansu ‘ya’ya matansu kuma su yi shagulgulan bidi’ar allolinsu, har su sa ‘ya’yanku su bi allolinsu.

17 “Kada ku yi wa kanku alloli na zubi.

18 “Sai ku kiyaye idin abinci marar yisti har kwana bakwai a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a watan Abib kuka fito Masar. A lokacin za ku ci abinci marar yisti kamar yadda na umarce ku.

19 “Kowane ɗan farin mutum, ko na dabba nawa ne, duk da ‘ya’yan farin dabbobinku, wato ɗan farin saniya da na tunkiya.

20 Ɗan farin jaki kuwa za ku fansa da ɗan rago, in kuwa ba za ku fansa da ɗan rago ba, sai ku karya wuyansa. Za ku fanshi kowane ɗan fari. Kada a sami wanda ya zo gabana hannu wofi.

21 “Cikin kwana shida za ku yi aiki, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, ko lokacin noma ne, ko lokacin girbi sai ku huta.

22 “Ku kuma kiyaye idin mako, wato idin girbin nunan fari na alkama, da idin gama tattara amfanin gonaki a ƙarshen shekara.

23 “Sau uku cikin shekara mazajenku duka za su hallara a gabana, ni Ubangiji Allah na Isra’ila.

24 Gama zan kori al’ummai daga gabanku, in fāɗaɗa kan iyakarku. Ba wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokatan nan uku na shekara da kukan hallara a gaban Ubangiji Allahnku.

25 “Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti ba, kada kuma a bar hadaya ta Idin Ƙetarewa ta kwana.

26 “Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku.

“Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”

27 Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Rubuta waɗannan kalmomi, gama daidai suke da kalmomin alkawarin da suke tsakanina, da kai, da Isra’ila.”

28 Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato dokokin nan goma.

Musa Ya Sauko daga Dutsen

29 Sa’ad da Musa ya sauko daga Dutsen Sina’i da alluna biyu na alkawarin a hannunsa, ashe, bai sani ba, amma fuskarsa tana annuri saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji.

30 Sa’ad da Haruna da dukan jama’ar Isra’ila suka ga fuskar Musa tana annuri, suka ji tsoro su kusace shi.

31 Sai Musa ya kirawo Haruna tare da shugabannin jama’ar duka, suka zo wurinsa, shi kuwa ya yi magana da su.

32 Daga nan jama’ar Isra’ila duka suka matsa kusa, Musa kuwa ya ba su dukan dokoki waɗanda Ubangiji ya ba shi a bisa Dutsen Sina’i.

33 Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa.

34 Amma duk lokacin da ya je gaban Ubangiji domin ya yi magana da shi, sai ya kware lulluɓin, har lokacin da ya fito. Idan ya fito, sai ya faɗa wa jama’ar Isra’ila abin da aka umarce shi.

35 Jama’ar Isra’ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa’an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.

Categories
FIT

FIT 35

Ka’idodin Ranar Hutawa

1 Sai Musa ya tattara dukan taron jama’ar Isra’ila, ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku ku yi.

2 Cikin kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai Asabar ce tsattsarka ta Ubangiji ta hutawa sosai. Duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta, sai a kashe shi.

3 Ba za ku hura wuta a ranar Asabar a wuraren zamanku ba.”

Sadaka domin Yin Alfarwa ta Sujada

4 Musa kuma ya ce wa taron jama’ar Isra’ila duka, “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya umarta,

5 ku karɓi sadaka daga cikinku saboda Ubangiji. Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka ta zinariya, da azurfa, da tagulla,

6 da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin, da gashin awaki,

7 da fatun raguna da aka rina suka zama ja, da fatun awaki, da itacen ƙirya,

8 da man fitila, da kayan yaji domin man keɓewa da turaren ƙonawa,

9 da duwatsu masu tamani, da duwatsun da za a mammanne a falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.”

Kayayyakin Alfarwa ta Sujada

10 “Bari dukan wanda yake da fasaha a cikinku ya zo, ya yi aikin da Ubangiji ya umarta a yi,

11 wato aikin alfarwa ta sujada, da alfarwarta da murfinta, da maratayai, da katakanta da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

12 da akwati da sandunansa, da murfinsa, da labulen ƙofar.

13 Da tebur da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,

14 da alkuki don haske, da kayayyakinsa, da fitilunsa, da man fitila,

15 da bagaden turaren ƙonawa da sandunansa, da man keɓewa mai ƙanshi, da turaren ƙonawa, da labulen ƙofar alfarwa ta sujada,

16 da bagaden ƙona hadaya da ragarsa ta tagulla da sandunansa, da kayayyakinsa duka, da daro da gammonsa,

17 da labulen farfajiya da dirkokinsa da kwasfansu, da labulen ƙofar farfajiyar,

18 da turakun alfarwa, da turakun farfajiyar, da igiyoyinsu,

19 da saƙaƙƙun tufafi na yin aiki a Wuri Mai Tsarki, da tsarkakakkun tufafin Haruna firist, da tufafin ‘ya’yansa maza na aikin firist.”

Jama’a sun Kawo Sadaka

20 Sa’an nan dukan taron jama’ar Isra’ila suka tashi daga wurin Musa.

21 Duk wanda ya yi niyya, da wanda ruhunsa ya iza shi ya kawo wa Ubangiji sadaka don yin alfarwa ta sujada, da dukan ayyukansa, da tsarkakakkun tufafi.

22 Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da ‘yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji.

23 Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su.

24 Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi.

25 Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

26 Sai kuma dukan mata masu hikima, waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki.

27 Su shugabanni suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

28 Suka kuma kawo kayan yaji, da man fitila, da man keɓewa, da turaren ƙonawa.

29 Sai dukan mata da maza na Isra’ilawa waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kawo kowane irin abu domin yin aikin da Ubangiji ya umarci Musa. Suka kawo sadaka ta yardar rai ga Ubangiji.

Waɗanda Suka Yi Aikin Alfarwa ta Sujada

30 Sai Musa ya ce wa Isra’ilawa, “Ga shi, Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.

31 Ya cika shi da ruhu na hikima, da basira, da sani, da fasaha na iya yin kowane irin aiki.

32 Domin ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta, waɗanda za a yi da zinariya, da azurfa, da tagulla.

33 Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta.

34 Ubangiji ya ba Bezalel, da Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, hikimar koya wa waɗansu sana’a.

35 Gama ya cika su da hikima ta yin kowane irin aiki na sassaƙa da na zāne-zāne, da na yin ɗinke-ɗinke da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin, da na yin saƙa. Sun iya yin kowane irin aiki da yin zāne-zāne.

Categories
FIT

FIT 36

1 “Da Bezalel da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima, waɗanda Ubangiji ya ba su hikima da basira na sanin yin kowane irin aiki, za su shirya Wuri Mai Tsarki kamar yadda Ubangiji ya umarta.”

Jama’a Sun Kawo Sadaka Mai Yawa

2 Sai Musa ya kirayi Bezalel, da Oholiyab, da kowane mutum mai hikima wanda Ubangiji ya ba shi hikima a zuciya, da duk wanda zuciyarsa ta iza shi ya zo, ya yi aikin.

3 Su kuwa suka karɓa daga wurin Musa dukan sadaka ta yardar rai da Isra’ilawa suka kawo don yin aikin alfarwa ta sujada. Jama’a suka yi ta kawo masa sadaka ta yardar rai kowace safiya.

4 Sai masu hikiman da suke yin aiki na alfarwa ta sujada suka ɗan dakatar da aiki suka tafi wurin Musa.

5 Suka ce masa, “Jama’a suna ta kawo sadaka fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.”

6 Sai Musa ya umarce su su yi shela a zango cewa, “Kada wata mace ko wani namiji ya sāke kawo sadaka don aikin alfarwa ta sujada.” Sai jama’a suka daina kawowa.

7 Gama abin da aka kawo ya isa yin aikin, har da ragi.

Yin Alfarwa ta Sujada

8 Sai dukan mutane masu gwaninta daga cikin ma’aikatan, suka yi alfarwa da labule goma. An yi labulen da lallausan zaren lilin na shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.

9 Tsawon kowane labule kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Dukan labulen girmansu ɗaya ne.

10 Ya ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, haka kuma ya yi da sauran labule biyar.

11 Sai ya sa shuɗɗan hantuna a karbun labule na fari da na biyu.

12 Ya sa hantuna hamsin a karbun labule na fari, haka kuma ya sa na biyun. Dukan hantunan suna daura da juna.

13 Ya kuma yi maɗauri hamsin na zinariya, ya harhaɗa labule da juna da maɗauran domin alfarwa ta zama ɗaya.

14 Ya kuma yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki domin ya rufe alfarwa.

15 Tsawon kowane labule kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne. Labule goma sha ɗayan nan girmansu ɗaya ne.

16 Ya harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, shida kuma ya harhaɗa su wuri ɗaya.

17 Sai ya yi hantuna hamsin, ya sa a karbu na bisa na labule na farin, haka kuma ya sa hantuna hamsin a karbun sama na labule na biyu.

18 Ya kuma yi maɗaurai da tagulla waɗanda zai harhaɗa hantuna da su don alfarwa ta zama ɗaya.

19 Ya yi wa alfarwa murfi da fatun raguna da aka rina ja, ya kuma yi wani abin rufewa da fatuna da aka jeme.

20 Ya kuma yi katakan alfarwa da itacen ƙirya.

21 Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi ne.

22 Kowane katako an fiƙe bakinsa biyu don a harhaɗa su tare, haka ya yi da dukan katakan alfarwa.

23 Yadda ya yi da katakan alfarwa ke nan, ya kafa katakai ashirin a fuskar kudu.

24 Sai ya yi kwasfa arba’in da azurfa domin katakai ashirin. Kowane katako yana da kwasfa biyu saboda bakinsa biyu da aka fiƙe.

25 A fuska ta biyu ta wajen arewa ta alfarwa, ya kafa katakai ashirin.

26 Ya kuma yi kwasfa arba’in na azurfa. Kowane katako yana da kwasfa biyu.

27 Ya yi katakai shida a bayan alfarwa a fuskar yamma.

28 Ya kuma yi katakai biyu don kusurwar baya ta alfarwa.

29 Aka haɗa katakai daga ƙasa har zuwa sama inda aka haɗa su a ƙawanya ta fari, haka ya yi da su a kusurwoyin nan biyu.

30 Akwai katako takwas da kwasfansu na azurfa guda goma sha shida. Kowane katako yana da kwasfa biyu.

31 Sai ya yi sanduna na itacen ƙirya, sanduna biyar domin katakan gefe ɗaya na alfarwa,

32 sanduna biyar kuma domin katakan ɗaya gefen na alfarwa, biyar kuma domin katakan da yake baya na alfarwa wajen yamma.

33 Ya sa sandan da yake a tsakiya ya wuce daga wannan gefe zuwa wancan gefe.

34 Ya dalaye katakai da zinariya. Ya yi musu ƙawane na zinariya inda za a sarƙafa sandunan. Ya kuma dalaye sandunan da zinariya.

35 Ya kuma yi labule da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin, ya kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.

36 Ya yi wa labulen dirkoki huɗu da itacen ƙirya. Sai ya dalaye su da zinariya. Ya kuma yi musu maratayai da zinariya. Ya yi wa dirkokin nan kwasfa huɗu da azurfa.

37 Ya yi wa ƙofar alfarwa labulen da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. Ya yi wa labulen ado.

38 Ya haɗa labulen da dirkokinsa biyar, da maratayansu. Ya dalaye kawunansu da maɗauransu da zinariya, amma ya dalaye kwasfansu guda biyar da tagulla.

Categories
FIT

FIT 37

Yin Akwatin Alkawari

1 Bezalel ya yi akwati da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

2 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa ciki da waje, ya kuma yi masa dajiya da zinariya kewaye da shi.

3 Ya sa masa ƙawanya huɗu na zinariya a kan kusurwoyinsa huɗu, ƙawane biyu a wannan gefe, biyu kuma a wancan gefe.

4 Ya kuma yi sandunan da itacen ƙirya, ya dalaye su da zinariya.

5 Sai ya zura sandunan cikin ƙawanen da suke a gyaffan akwatin don ɗaukarsa.

6 Ya yi murfin da zinariya tsantsa, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi.

7 Ya kuma ƙera siffofin kerubobi biyu da zinariya, ya maƙala su a gefe biyu na murfin.

8 Kerub ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a wancan gefe. Ya yi su a haɗe da murfin a gefe biyu na murfin.

9 Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwantar da murfin da fikafikansu. Fuskokinsu kuma na duban juna, suna kuma fuskantar murfin.

Yin Tebur

10 Sai kuma ya yi tebur da itacen ƙirya, tsawsonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

11 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, ya yi masa dajiya da zinariya.

12 Ya yi masa dajiya mai fāɗin tafin hannu kewaye da shi, ya kuma yi wata dajiya da zinariya kewaye da ita.

13 Ya yi wa tebur ɗin ƙawane huɗu na zinariya, ya manna ƙawane a kusurwoyi huɗu na ƙafafunsa.

14 Ƙawanen suna kusa da dajiyar inda za a zura sanduna na ɗaukar teburin.

15 Ya yi sanduna da itacen ƙirya don ɗaukar teburin. Sa’an nan ya dalaye su da zinariya.

16 Ya yi kayan teburin da zinariya tsantsa, wato farantansa, da kwanonin tuya, da kwanoninsa, da butoci domin yin hadaya ta sha.

Yin Alkuki

17 Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin.

18 Akwai rassan fitila guda shida, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.

19 A kowane reshe na alkukin akwai ƙoƙuna uku masu kamar tohon almond, akwai kuma mahaɗai da furanni.

20 A bisa alkukin kuma akwai ƙoƙuna guda huɗu da aka yi su kamar tohon almond, da mahaɗai, da furanni.

21 Akwai mahaɗi kuma a ƙarƙashin kowane reshe biyu biyu na dukan rassan guda shida, a miƙe daga alkukin.

22 An ƙera mahaɗai da rassan alkuki a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi alkukin da dukan kome nasa a haɗe.

23 Da zinariya tsantsa ya yi fitilu bakwai, da hantsuka da farantansa.

24 Da zinariya tsantsa na talanti ɗaya ya yi alkukin da kayayyakinsa duka.

Yin Bagaden Ƙona Turare

25 Ya yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, shi murabba’i ne, tsayinsa kuma kamu biyu ne, zankayensa kuwa a haɗe suke da shi.

26 Ya dalaye shi da zinariya tsantsa, da bisansa, da kewayen gyaffansa, da zankayensa. Ya kewaye shi kuma da dajiya ta zinariya.

27 Ya sa masa ƙawane biyu na zinariya a gyaffansa a ƙarkashin dajiya daura da juna don a zura sandunan ɗaukarsa.

28 Ya kuma yi sanduna biyu da itacen ƙirya, sa’an nan ya dalaye su da zinariya.

Yin Man Keɓewa da Turare

29 Ya yi tsattsarkan mai na keɓewa da kuma turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yakan yi.

Categories
FIT

FIT 38

Bagaden Ƙona Hadaya

1 Ya kuma yi bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku.

2 Ya yi masa zankaye a kusurwoyinsa huɗu. Zankayen a haɗe suke da shi. Ya dalaye bagaden da tagulla.

3 Da tagulla ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta.

4 Ya yi wa bagaden raga da tagulla, ya sa ta a tsakiya.

5 Ya sa ƙawane huɗu a kusurwoyi huɗu na ragar tagulla don zura sanduna.

6 Ya kuma yi sanduna da itacen ƙirya, ya dalaye su da tagulla.

7 Sai ya zura sandunan cikin ƙawane na gyaffan bagaden don ɗaukarsa. Ya yi bagaden da itace sa’an nan ya robe cikinsa.

Yin Daron Wanka

8 Ya yi daron wanka da tagulla, da gammonsa na tagulla, daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.

Farfajiyar Alfarwa ta Sujada

9 Ya kuma yi farfajiya. Ya yi labulenta na gefen kudu da lallausan zaren lilin, tsawonsu kamu ɗari ne.

10 Da tagulla aka yi dirkokinsa ashirin, da kwasfan dirkoki guda ashirin, amma da azurfa aka yi maratayan dirkoki da maɗaurai.

11 Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne. An yi dirkokinsa guda ashirin da kwasfansu ashirin da tagulla, amma an yi maratayan dirkoki da maɗaurai da azurfa.

12 Labule na gefen yamma kamu hamsin ne, dirkokinsa kuwa guda goma ne, da kwasfansu guda goma. An yi maratayan dirkoki, da maɗaurai da azurfa.

13 Tsawon gefen gabas kamu hamsin ne.

14 Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da dirkokinsu guda uku da kwasfan dirkoki guda uku.

15 Akwai kuma labule mai kamu goma sha biyar a gefe biyu na ƙofar farfajiyar. Labulen yana da dirkoki guda uku da kwasfan dirkoki guda uku.

16 Duk labulen da yake kewaye da farfajiya an yi shi da lallausan zaren lilin.

17 An yi kwasfan dirkoki duka da tagulla, amma maratayan dirkoki da maɗauransu an yi su da azurfa. An dalaye kawunansu da azurfa. Dirkokin farfajiya duka suna da maɗaurai na azurfa.

18 An yi wa labulen ƙofar farfajiya ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin. Tsawonsa kamu ashirin, tsayinsa kamu biyar daidai da labulen farfajiya.

19 An yi dirkokin labulen guda huɗu, da kwasfan dirkoki guda huɗu da tagulla, amma da azurfa aka yi maratayan dirkokin. An dalaye kawunansu da maɗauransu da azurfa.

20 An yi turakun alfarwa ta sujada da na farfajiya duka da tagulla.

Ƙarafan da aka yi Amfani da Su

21 Wannan shi ne lissafin abubuwan da aka yi alfarwa ta sujada da su, yadda aka lasafta bisa ga umarnin Musa domin aikin Lawiyawa a ƙarƙashin jagorar Itamar, ɗan Haruna firist.

22 Sai Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.

23 Tare da shi kuma ga Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan, gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan zaren lilin.

24 Dukan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita na alfarwa ta sujada sadaka ce talanti ashirin da tara ne da shekel ɗari bakwai da talatin bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

25 Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama’a talanti ɗari ne, da shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba’in da biyar (1,775) bisa ga ma’aunin kuɗin da ake aiki da shi.

26 Kowane mutum da aka ƙidaya ya ba da rabin shekel. Duk mai shekara ashirin ko fi an ƙidaya shi, aka sami maza dubu ɗari shida da dubu uku da ɗari biyar da hamsin (603,550).

27 An mori azurfa talanti ɗari don yin kwasfa na alfarwa, da kwasfa na labule. An yi kwasfa ɗari da azurfa talanti ɗari, wato kwasfa ɗaya talanti ɗaya ke nan.

28 An yi maratayan dirkoki da azurfa shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba’in da biyar (1,775), sa’an nan an dalaye kawunansu, an kuma yi musu maɗaurai.

29 Tagullar da aka bayar kuwa, talanti saba’in da shekel dubu biyu da ɗari huɗu (2,400).

30 Da tagullar ce ya yi kwasfan ƙofar alfarwa ta sujada, da bagade, da ragarsa, da dukan kayayyakin bagaden.

31 Da tagullar kuma aka yi kwasfan farfajiya, da kwasfan ƙofar farfajiya, da dukan turakun alfarwar da na farfajiyar.

Categories
FIT

FIT 39

Yin Tufafin Firistoci

1 An yi wa firistoci tufafi masu kyau na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, domin yin aiki a Wuri Mai Tsarki. Suka yi wa Haruna tsarkakan tufafi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

2 Ya yi falmaran da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

3 An kuma buga zinariya fake-fake, suka yanyanka ta zare-zare don su yi saƙa da ita tare da zane na shuɗi, da na shunayya, da na mulufi, da na lallausan lilin, aikin gwani mai fasaha.

4 Suka yi wa falmaran kafaɗu, sa’an nan suka haɗa su a gefenta biyu na sama.

5 Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

6 Sai aka gyaggyarta duwatsu masu daraja aka jera su cikin tsaiko na zinariya. Aka zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila a kan duwatsun kamar yadda akan yi hatimi.

7 Aka sa su a kan kafaɗun falmaran don su zama duwatsun tunawa da Isra’ila kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

8 Aka kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji da gwaninta kamar yadda aka yi wa falmaran aiki da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

9 Ƙyallen maƙalawa a ƙirji murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya ɗaya ne.

10 Sai suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na fari aka sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.

11 A jeri na biyu aka sa turkos, da saffir, da daimon.

12 A jeri na uku aka sa yakinta, da idon mage, da ametis.

13 A jeri na huɗu aka sa beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.

14 An zana sunayen ‘ya’yan Isra’ila goma sha biyu a kan duwatsu masu daraja kamar yadda akan yi hatimi.

15 Sai suka yi tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

16 Suka yi tsaiko biyu na zinariya da ƙawane biyu na zinariya. Sai suka sa ƙawanen nan biyu a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

17 Suka kuma zura sarƙoƙin nan biyu na zinariya a ƙawanen nan biyu na zinariya na gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

18 Sai suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun falmaran daga gaba.

19 Suka kuma yi ƙawane biyu na zinariya, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da falmaran.

20 Suka yi waɗansu ƙawane biyu na zinariya, suka maƙala su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na falmaran kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar falmaran.

21 Sai suka ɗaure ƙawanen ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar falmaran don kada ya kwance daga falmaran, sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

22 Ya kuma saƙa taguwa ta falmaran da shuɗi duka.

23 An yi wa taguwar wuyan wundi kamar sulke, aka daje wuyan don kada ya kece.

24 A karbun taguwar, suka yi fasalin ‘ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

25 Suka kuma yi ƙararrawa da zinariya tsantsa, suka sa su a tsakankanin fasalin ‘ya’yan rumman kewaye da karbun taguwa.

26 An jera su bi da bi, wato fasalin rumman yana biye da ƙararrawa. Haka aka jera su kewaye da karbun taguwar yin aiki, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

27 Suka saƙa zilaika da lallausan zaren lilin don Haruna da ‘ya’yansa.

28 Suka kuma yi rawani, da huluna, da mukurai da lallausan lilin.

29 Sun kuma yi abin ɗamara da lallausan lilin mai launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. Aka yi mata ɗinkin ado kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

30 Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, “MAI TSARKI GA UBANGIJI.”

31 Suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Ƙarewar Aikin

32 Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra’ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

33 Sai suka kawo wa Musa alfarwa da dukan kayayyakinta, wato da maratayanta, da katakanta, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

34 da murfi na fatun raguna da na awaki, da labulen,

35 da akwatin alkawari da sandunansa, da murfinsa,

36 da tebur, da kayayyakinsa duka, da gurasar ajiyewa,

37 da alkuki na zinariya tsantsa da fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,

38 da bagade na zinariya, da man keɓewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar alfarwar,

39 da bagade na tagulla da ragarsa ta tagulla, da sandunansa da dukan kayayyakinsa, da daro da gammonsa,

40 da labulen farfajiya da dirkokinta, da kwasfanta, da labulen ƙofarta, da igiyoyinta, da turakunta, da dukan kayayyakin yin aiki a alfarwa ta sujada,

41 da tufafin ado na aiki a Wuri Mai Tsarki, wato tsarkakan tufafin Haruna firist, da tufafin ‘ya’yansa maza don su yi aikin firistoci.

42 Isra’ilawa sun yi dukan aiki kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

43 Da Musa ya duba dukan aikin, ga shi kuwa, sun yi shi daidai, kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Musa ya sa musu albarka.

Categories
FIT

FIT 40

Kafawar Alfarwa ta Sujada da Keɓewarta

1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa,

2 “A kan rana ta fari ga wata na fari za ka kafa alfarwa ta sujada.

3 Sai ka sa akwatin alkawari a cikinta sa’an nan ka kāre shi da labule.

4 Ka shigar da tebur ɗin, ka shirya kayayyakinsa daidai. Ka kuma shigar da alkukin, ka sa fitilu a bisansa.

5 Ka ajiye bagade na zinariya na ƙona turare a gaban akwatin alkawari, sa’an nan ka rataya labulen ƙofar alfarwa.

6 Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada,

7 ka kuma ajiye daro tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa’an nan ka zuba ruwa a ciki.

8 Sai ka yi farfajiya ka kewaye wurin sa’an nan ka rataya labulen ƙofar farfajiyar.

9 “Ka ɗauki man keɓewa, ka shafa wa alfarwa da dukan abin da yake cikinta, domin ka tsarkake ta da kayayyakinta duka, za ta kuwa zama tsarkakakkiya.

10 Ka shafa wa bagade na ƙona hadaya da kayayyakinsa duka man domin ka tsarkake shi, bagaden kuma zai zama mafi tsarki.

11 Ka kuma shafa wa daron da gammonsa man keɓewa, da haka za ka tsarkake shi.

12 “Ka kuma kawo Haruna da ‘ya’yansa maza a ƙofar alfarwa ta sujada, ka yi musu wanka da ruwa.

13 Sa’an nan ka sa wa Haruna tufafi tsarkaka ka shafa masa man domin ka tsarkake shi ya yi mini aiki na firist.

14 Sai ka kawo ‘ya’yan Haruna maza, ka kuma sa musu taguwoyi.

15 Sa’an nan ka shafa musu mai kamar yadda ka shafa wa mahaifinsu domin su yi mini aiki a matsayin firistoci. Shafa musu man zai sa su zama firistoci din din din dukan zamanansu.”

16 Haka kuwa Musa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

17 A rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu, aka kafa alfarwa.

18 Sai musa ya kafa alfarwa, ya kafa kwasfanta, ya jera katakanta, ya sa mata sandunanta, ya kakkafa dirkokinta.

19 Sa’an nan ya shimfiɗa murfi a bisa alfarwa ya rufe alfarwar kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

20 Sai ya ɗauki dokoki goma ɗin, ya sa a akwatin, ya kuma zura sandunan a ƙawanen akwatin, sa’an nan ya sa murfin a bisansa.

21 Ya kawo akwatin a cikin alfarwa, sa’an nan ya sa labulen don kāre akwatin alkawari, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

22 Musa ya sa teburin cikin alfarwa ta sujada, a wajen gefen arewa na alfarwa, a gaban labulen.

23 Sa’an nan ya jera gurasa daki-daki a bisa teburin a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

24 Ya kuma sa alkukin a cikin alfarwa ta sujada daura da teburin a wajen gefen kudu na alfarwa.

25 Ya kunna fitilun a gaban Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

26 Ya kuma sa bagade na zinariya a cikin alfarwa ta sujada daga gaban labulen.

27 Sai ya ƙona turare mai ƙanshi a bisansa kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

28 Ya sa labule a ƙofar alfarwa.

29 Ya kuma sa bagade na ƙona hadaya a ƙofar alfarwa ta sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da ta gari kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

30 Ya kuma sa daro a tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, sa’an nan ya zuba ruwa a ciki don wanka.

31 A cikinsa Musa da Haruna da ‘ya’yansa maza sukan wanke hannuwansu da ƙafafunsu,

32 sa’ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada, da sa’ad da sukan kusaci bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

33 Ya kuma yi farfajiya kewaye da alfarwa da bagaden, ya sa labulen ƙofar farfajiyar. Da haka Musa ya gama aikin.

Saukowar Girgije a bisa Alfarwa ta Sujada

34 Sa’an nan girgije ya rufe alfarwa ta sujada, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa.

35 Musa kuwa bai iya shiga alfarwa ta sujada ba domin girgijen yana zaune a bisanta, ɗaukakar Ubangiji kuma ta cika alfarwa.

36 Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan alfarwa.

37 Idan girgijen bai tashi ba, su kuma ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.

38 Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan alfarwa da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.