Categories
ISH

ISH 1

1 Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.

Allah Ya Tsauta wa Al’umma Mai Zunubi

2 Ubangiji ya ce, “Duniya da sararin sama, ku kasa kunne ga abin da ni, Ubangiji, nake cewa! ‘Ya’yan da na goya sun tayar mini.

3 Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su abinci. Amma wannan ya fi abin da jama’ata Isra’ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”

4 An hallaka ki, ke al’umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra’ila, kun juya masa baya.

5 Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku hukunci ne? Ya Isra’ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo.

6 Daga kanki har zuwa ƙafafunki, ba inda yake da lafiya a jikinki. Raunuka da ƙujewa da manyan gyambuna sun rufe jikinki, ba a tsabtace raunukanki an ɗaure ba. Ba a yi musu magani ba.

7 An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da ko’ina kufai.

8 Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana.

9 Da a ce Ubangiji Mai Runduna bai rage sauran jama’a ba, da an hallakar da Urushalima gaba ɗaya, kamar yadda aka yi wa Saduma da Gwamrata.

An Kira Su Tuba

10 Ya Urushalima sarakunanki da jama’arki sun zama kamar Saduma da Gwamrata. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa muku. Ku mai da hankali ga abin da Allahnmu yake koya muku.

11 Ya ce, “Kuna tsammani ina jin daɗin dukan hadayun nan da kuke ta miƙa mini? Tumakin da kuke miƙawa hadaya ta ƙonawa, da kitsen kyawawan dabbobinku ya ishe ni. Na gaji da jinin bijimai, da na tumaki, da na awaki.

12 Wa ya roƙe ku ku kawo mini dukan wannan sa’ad da kuka zo yi mini sujada? Wa kuma ya roƙe ku ku yi ta kai da kawowa a kewaye da Haikalina?

13 Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.

14 Ina ƙin bukukuwanku na amaryar wata, da na tsarkakan ranaku. Sun zama nawaya wadda na gaji da ita.

15 “Sa’ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu’ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.

16 Ku yi wanka sarai. Ku daina aikata dukan wannan mugun abu da na ga kuna aikatawa. I, ku daina aikata mugunta.

17 Ku koyi yin abin da yake daidai. Ku ga an aikata adalci, ku taimaki waɗanda ake zalunta, ku ba marayu hakkinsu, ku kāre gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu.”

18 Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al’amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.

19 Idan za ku yi mini biyayya kaɗai za ku ci kyawawan abubuwan da ƙasa take bayarwa.

20 Amma idan kuka ƙi, kuka raina ni, mutuwa ce ƙaddararku. Ni Ubangiji na faɗi wannan.”

Hukuncin Urushalima da Tubanta

21 Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.

22 Ya Urushalima, dā kamar azurfa kike, amma yanzu ba ki da amfani, dā kamar kyakkyawan ruwan inabi kike, amma yanzu baƙin ruwa ne kaɗai.

23 Shugabanninku ‘yan tawaye ne, abokan ɓarayi, a koyaushe sai karɓar kyautai suke yi, da rashawa. Amma ba su taɓa kare marayu a ɗakin shari’a, ko su kasa kunne ga ƙarar da gwauraye suka kawo ba, wato matan da mazansu suka mutu.

24 Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra’ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba.

25 Zan hukunta ku. Zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe, in kawar da dukan ƙazantarku.

26 Zan ba ku shugabanni da mashawarta kamar waɗanda kuke da su dā can. Sa’an nan za a ce da Urushalima adala, amintaccen birni.”

27 Gama Ubangiji mai adalci ne, zai ceci Urushalima da dukan wanda ya tuba a can.

28 Amma zai ragargaza dukan wanda ya yi zunubi, ya tayar gāba da shi, zai kashe duk wanda ya rabu da shi.

29 Za ku yi da na sani, ku da kuka taɓa yin sujada ga itatuwa da dashe-dashen masujada.

30 Za ku bushe kamar busasshen itacen oak, kamar lambun da ba wanda yake ba shi ruwa.

31 Daidai kamar yadda busasshen itacen da tartsatsin wuta ya fāɗa wa, haka mutane masu iko za su hallaka ta wurin mugayen ayyukansu, ba wanda zai iya hana a hallaka su.

Categories
ISH

ISH 2

Madawwamin Mulkin Salama

1 Ga jawabin da Allah ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz a kan Yahuza da Urushalima.

2 A kwanaki masu zuwa,

Dutse inda aka gina Haikali zai zama mafi tsayi duka.

Al’ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi.

3 Jama’arsu za su ce,

“Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji,

Zuwa ga Haikalin Allah na Isra’ila.

Za mu koyi abin da yake so mu yi,

Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.

Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa,

Daga Sihiyona yake magana da jama’arsa.”

4 Zai sulhunta jayayyar da yake tsakanin manyan al’ummai,

Za su mai da takubansu garemani,

Masunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace,

Al’ummai ba za su ƙara fita zuwa yaƙi ba,

Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.

Hukuncin Allah a kan Masu Girmankai

5 Yanzu fa, zuriyar Yakubu, bari mu yi tafiya a cikin hasken da Ubangiji ya ba mu!

6 Ya Allah, ka rabu da jama’arka, zuriyar Yakubu. Ƙasa ta cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas, daga kuma ƙasar Filistiya. Jama’a suna bin baƙin al’adu.

7 Ƙasarsu tana cike da azurfa da zinariya, dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu tana cike da dawakai, karusansu kuma ba iyaka.

8 Ƙasarsu tana cike da gumaka, suna sujada ga abubuwan da suka yi da hannuwansu.

9 Za a ƙasƙantar da kowane mutum, a kunyata shi. Kada ka gafarta musu, ya Ubangiji!

10 Za su ɓuya a cikin kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa!

11 Rana tana zuwa sa’ad da girmankan ‘yan adam zai ƙare, zai kuma lalatar da fāriyar ‘yan adam. Sa’an nan Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka.

12 A wannan rana, Ubangiji Mai Runduna zai ƙasƙantar da kowane mai iko, da kowane mai girmankai, da kowane mai fāriya.

13 Zai hallaka dogayen itatuwan al’ul na Lebanon, da dukan itatuwan oak na ƙasar Bashan.

14 Zai baje duwatsu da tuddai masu tsayi,

15 da kowace doguwar hasumiya, da ganuwar kowace kagara.

16 Zai nutsar da jiragen ruwa mafi girma mafi kyau.

17 Girmankan ɗan adam zai ƙare, za a hallakar da fāriyar ɗan adam, Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka sa’ad da wannan rana ta yi,

18 za a shafe gumaka ƙaƙaf.

19 Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa’ad da ya zo domin ya girgiza duniya.

20 Sa’ad da wannan rana ta yi za su zubar da gumakan da suka yi na zinariya da azurfa, za su bar wa ɓeraye da jemagu.

21 Sa’ad da Ubangiji ya zo domin ya girgiza duniya, jama’a za su ɓuya a cikin kogwannin tuddai da ramummukan duwatsu, suna ƙoƙari su ɓuya daga fushinsa, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa.

22 Kada ku dogara ga ‘yan adam. Wace daraja take gare su?

Categories
ISH

ISH 3

Hukuncin Ubangiji a kan Yahuza da Urushalima

1 Yanzu fa Ubangiji, Ubangiji Mai Runduna, yana gab da ya kwashe kowane abin da kowane mutum da jama’ar Urushalima da na Yahuza suke dogara da su. Zai kwashe abincinsu da ruwan shansu,

2 da jarumawansu, da sojojinsu, da alƙalansu, da annabawansu, da masu yi musu duba, da manyan mutanensu,

3 da shugabannin sojojinsu, da na farar hula, da ‘yan siyasarsu, da kowane mai aikin sihiri don ya sarrafa abubuwan da yake faruwa.

4 Ubangiji zai sa yaran da ba su balaga ba su mallaki jama’ar.

5 Za a yi ta cutar juna. Matasa ba za su girmama manyansu ba, talakawa ba za su girmama na gaba da su ba.

6 Lokaci yana zuwa sa’ad da mutanen wani dangi za su zaɓi ɗaya daga cikinsu, su ce, “Kai da kake da ɗan abin sawa za ka zama shugabanmu a wannan lokaci na wahala.”

7 Amma zai amsa, ya ce, “Ba ni ba dai! Ba zan iya taimakonku ba. Ba ni ma da abinci sam, ko tufafi ma. Kada ku naɗa ni shugabanku!”

8 Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa.

9 Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.

10 Adalai za su yi murna, kome zai tafi musu daidai. Za su ji daɗin abin da suka aikata.

11 Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.

12 Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama’ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu.

Ya jama’ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.

Ubangiji Yana Hukunta Jama’arsa

13 Ubangiji a shirye yake ya hurta maganarsa, a shirye yake ya hukunta al’ummai.

14 Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama’arsa a gaban shari’a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta.

15 Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama’ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

Hukunci a kan Matan Urushalima

16 Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara’a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas.

17 Amma zan hukunta su, in aske kawunansu, in bar su ƙwal.”

18 Rana tana zuwa sa’ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu,

19 da hannuwansu. Zai raba su da lulluɓinsu,

20 da hulunansu. Zai raba su da layun da suke sa wa damatsansu, da kwankwasonsu,

21 da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu.

22 Ubangiji zai raba su da dukan kyawawan rigunansu na ado, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakunkunansu,

23 da rigunansu na yanga, da ƙyallayensu na lilin, da adikai, da gyale masu tsawo waɗanda suke sawa a kawunansu.

24 Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!

25 Jama’ar garin, i, har da ƙarfafan mutane, za a kashe su a yaƙi.

26 Ƙofofin birnin za su yi makoki, su yi kuka.

Za a kamanta birnin da matar da take zaune a ƙasa tsirara.

Categories
ISH

ISH 4

1 Sa’ad da wannan lokaci ya yi, mata bakwai za su riƙe mutum guda su ce, “Mā iya ciyar da kanmu, mu kuma tufasar da kanmu, amma in ka yarda, bari mu ce kai ne mijinmu, domin kada mu sha kunyar zaman gwagwarci.”

An Ceci Urushalima

2 Lokaci na zuwa sa’ad da Ubangiji zai sa kowane tsiro da kowane itacen da take a ƙasar su girma su yi kyau. Dukan jama’ar Isra’ila waɗanda suka ragu za su yi fāriya, su yi murna saboda amfanin da ƙasar take bayarwa.

3 Duk wanda aka rage a Urushalima, wanda Ubangiji ya nufa da rayuwa, za a ce da shi mai tsarki.

4 Ta wurin ikonsa Ubangiji zai shara’anta al’ummar, ya kuma tsarkake ta, ya wanke laifin Urushalima, har da na jinin da aka zubar a can.

5 Sa’an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka.

6 Ɗaukakarsa za ta inuwantar da birnin daga zafin rana, ta sa ya zama lafiyayyen wurin da aka kāre daga ruwan sama da hadiri.

Categories
ISH

ISH 5

Waƙar Gonar Inabi

1 Ku saurara in raira muku wannan waƙa,

Waƙar abokina da gonar inabinsa.

Abokina yana da gonar inabi

A wani tudu mai dausayi.

2 Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun,

Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau.

Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu,

Ya kuma haƙa rami inda za a matse ‘ya’yan inabin.

Ya yi ta jira don ‘ya’yan inabin su nuna,

Amma ko wannensu tsami take gare shi.

3 Saboda haka, abokina ya ce, “Ku jama’ar da yake zaune a Urushalima da Yahuza, ku shara’anta tsakanina da gonar inabina.

4 Akwai abin da ban yi mata ba? Me ya sa ta yi ‘ya’yan inabi masu tsami, maimakon ‘ya’yan inabi masu kyau da nake sa zuciya.

5 “Ga abin da zan yi wa gonar inabina. Zan cire shingen da yake kewaye da ita, in rushe bangon da ya kāre ta, in bar namomin jeji su cinye ta, su tattake ta.

6 Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”

7 Isra’ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna,

Jama’ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa.

Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau,

Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai!

Ya zaci za su aikata abin da yake daidai,

Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!

Mugaye Sun Shiga Uku

8 Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar.

9 Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye.

10 Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”

11 Kun shiga uku! Kukan tashi da sassafe ku fara sha, ku yi ta sha har yamma ta yi sosai, ku raba dare kuna buguwa.

12 A cikin bukukuwanku kuna kaɗa garaya, da bandiri, da bushe-bushe, da ruwan inabi. Amma ba ku gane da abin da Ubangiji yake yi ba.

13 Don haka za a kwashe ku, ku zama ‘yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama’a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.

14 Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama’a masu hayaniya.

15 Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su.

16 Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara’anta jama’arsa.

17 A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.

18 Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba.

19 Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra’ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”

20 Kun shiga uku! Kun ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta. Kun mai da duhu shi ne haske, haske kuwa duhu. Kun mai da abin da yake mai ɗaci mai zaƙi, mai zaƙi kuwa kun maishe shi mai ɗaci.

21 Kun shiga uku! A tsammaninku ku masu hikima ne, masu wayo ƙwarai.

22 Kun shiga uku! Jarumawan kwalabar ruwan inabi! Masu ƙarfin zuciya marasa tsoro a gauraya shaye-shaye!

23 Amma kukan ƙyale masu laifi waɗanda suka ba ku rashawa, kukan kuwa ƙi yi wa marasa laifi shari’ar gaskiya.

24 Don haka, kamar yadda tattaka da busasshiyar ciyawa sukan yanƙwane su ƙone a wuta, saiwoyinku za su ruɓe, furanninku kuma za su bushe. Iska za ta kwashe su, domin kun ƙi abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah Mai Tsarki na Isra’ila, ya koya muku.

25 Ubangiji yana fushi da jama’arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba.

26 Ubangiji ya ba da alama a kirawo al’ummar da take nesa. Ya yi musu fīto su zo daga bangon duniya. Ga shi kuwa sun iso da sauri nan da nan.

27 Ko ɗaya ba wanda ya gaji, ba kuwa wanda ya yi tuntuɓe. Ba su yi gyangyaɗi ko barci ba. Ba abin ɗamarar da ya kwance, ba igiyar takalmin da ta tsinke.

28 Kibansu masu tsini ne, bakunansu kuwa a shirye suke don yin harbi. Kofaton dawakansu suna da ƙarfi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun karusansu kamar guguwa ne.

29 Sojojinsu na ruri kamar zakunan da suka kashe nama, suna kuwa ɗauke da shi don kada wani ya ƙwace musu.

30 Sa’ad da ranar ta yi, za su yi ruri a kan Isra’ila da ƙarfi kamar rurin teku. Ku duba ƙasan nan! Duhu da damuwa! Duhu ya haɗiye hasken.

Categories
ISH

ISH 6

Allah Ya Kira Ishaya Ya Zama Annabi

1 A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali.

2 Kewaye da shi sai ga waɗansu talikai masu kama da harshen wuta a tsaye, ko wannensu yana da fikafikai shida. Ko wannensu ya rufe fuskarsa da fiffike biyu, jikinsa kuma da fiffike biyu, sauran fiffike biyu ɗin kuma, da su yake tashi.

3 Suna ta kiran junansu suna cewa,

“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki!

Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne!

Ɗaukakarsa ta cika duniya.”

4 Amon muryoyinsu ya sa harsashin ginin Haikali ya girgiɗa, Haikalin kansa kuma ya game da hayaƙi.

5 Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”

6 Sa’an nan ɗaya daga cikin talikan ya tashi ya sauko zuwa gare ni, yana riƙe da garwashin wuta wanda ya ɗauko da arautaki daga bagade.

7 Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”

8 Sai na ji Ubangiji yana cewa, “Wa zan aika? Wa zai zama manzonmu?”

Sai na amsa na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”

9 Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama’a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”

10 Sa’an nan ya ce mini, “Ka sa hankalin mutanen nan ya dushe, kunnuwansu su kurunce, idanunsu su makance, har da ba za su iya gani, ko ji, ko fahimta ba. In da za su yi haka mai yiwuwa ne su sāke juyowa gare ni in warkar da su.”

11 Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?”

Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.

12 Zan sa jama’a su tafi nesa, in sa ƙasar duka ta zama kango.

13 Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.”

Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama’ar Allah zuwa gaba.

Categories
ISH

ISH 7

Jawabi zuwa ga Sarki Ahaz

1 Sa’ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra’ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.

2 Labari ya kai gun Sarkin Yahuza, cewa sojojin Suriya sun shiga ƙasar Isra’ila. Sai shi da dukan jama’arsa suka firgita ƙwarai, suna ta kaɗuwa kamar itatuwan da iska take kaɗawa.

3 Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Ka ɗauki ɗanka Sheyar-yashub ka je ka sami sarki Ahaz. Za ka same shi a hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a wajen ƙarshen wuriyar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake sama da ita.

4 Faɗa masa ya zauna da shiri, ya natsu, kada ya ji tsoro ko ya damu. Fushin sarki Rezin da Suriyawansa da na sarki Feka ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ‘yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.

5 Suriya tare da Isra’ila da sarkinta sun ƙulla maƙarƙashiya.

6 Nufinsu su kai wa ƙasar Yahuza yaƙi, su tsoratar da jama’a, don su haɗa kai da su, sa’an nan su naɗa ɗan Tabeyel.

7 “Amma ni Ubangiji na hurta, faufau wannan ba zai faru ba.

8 Don me? Saboda Dimashƙu ita ce ƙarfin Suriya, sarki Rezin kuwa shi ne ƙarfin Dimashƙu. Isra’ila kuwa a shekara sittin da biyar masu zuwa za ta karkasu, har ba za ta iya rayuwa ta zama al’umma ba.

9 Samariya ita ce ƙarfin Isra’ila, sarki Feka kuma shi ne ƙarfin Samariya.

“Idan bangaskiyarku ba ta da ƙarfi, to, ba za ku dawwama ba.”

Immanuwel

10 Ubangiji ya aika wa Ahaz da wani jawabi, ya ce,

11 “Ka roƙi Ubangiji Allahnka ya ba ka alama. Yana yiwuwa daga can zurfin lahira ne, ko kuma daga can cikin sama ne.”

12 Ahaz ya amsa, ya ce, “Ba zan nemi wata alama ba. Ba zan jarraba Ubangiji ba.”

13 Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama’a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure?

14 Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.

15 In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa.

16 Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku za su zama kango.

17 “Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra’ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!

18 “A lokacin nan, Ubangiji zai yi feɗuwa ya kirawo Masarawa su zo kamar ƙudaje daga manisantan mazaunan Kogin Nilu, ya kuma kirawo Assuriyawa su zo daga ƙasarsu kamar ƙudajen zuma.

19 Za su zo jingim su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, za su rufe kowane fili mai ƙayayuwa da kowace makiyaya.

20 “A lokacin nan, Ubangiji zai yi ijara da wanzami daga wancan hayi na Yufiretis, wato Sarkin Assuriya! Zai aske gyammanku, da gashin kawunanku, da na jikunanku.

21 “A lokacin nan, ko da karsana ɗaya da awaki biyu kaɗai manomi yake da su,

22 za su ba da isasshiyar madarar da za ta biya dukan bukatarsa. Hakika dukan waɗanda suka ragu a ƙasar za su sami yawan albarka su ƙoshi.

23 “A lokacin nan, waɗannan kyawawan gonakin inabi waɗanda suke da kurangar inabi dubu, kuɗin kowace gonar inabi azurfa dubu guda ne, gonakin za su cika da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.

24 Ba wanda yake da ƙarfin hali da zai iya tafiya can, sai ko wanda yake da kwari da baka. Hakika ƙasar duka za ta cika da sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa.

25 Dukan tuddai inda dā akan shuka amfanin gona, za su cika da ƙayayuwa, har da ba mai iya zuwa wurin. Zai zama wurin kiwon shanu da tumaki.”

Categories
ISH

ISH 8

Sunan Ɗan Annabi

1 Ubangiji ya ce mini, “Ka ɗauki allo babba ka rubuta a kansa da manyan harufa, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’

2 Nemo mutum biyu amintattu, wato Uriya firist, da Zakariya ɗan Yeberekiya su zama shaidu.”

3 Bayan wannan na yi jima’i da matata annabiya. Ta ɗauki ciki, ta haifi ɗa namiji, Ubangiji ya ce mini, “Ka raɗa masa suna, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’

4 Kafin yaron ya isa kiran mama ko baba, Sarkin Assuriya zai kwashe dukan dukiyar Dimashƙu da dukan ganimar Samariya.”

Sarkin Assuriya Yana Zuwa

5 Ubangiji kuma ya sāke yi mini magana.

6 Ya ce, “Saboda wannan jama’a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa, suka yi ta rawar jiki a gaban sarki Rezin da sarki Feka,

7 ni Ubangiji kuwa, zan kawo Sarkin Assuriya da dukan sojojinsa su fāɗa wa Yahuza. Za su tasar musu kamar rigyawar Kogin Yufiretis wadda ta yi ambaliya ta shafe kowace gaɓa.

8 Za su sheƙa cikin ƙasar Yahuza kamar rigyawa wadda ta kai har kafaɗa, ta rufe kome da kome.”

Allah yana tare da mu! Fikafikansa a buɗe suke su tsare ƙasar .

9 Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al’umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro!

10 Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.

Ubangiji Za Ku Ji Tsoro

11 Bisa ga ikonsa mai girma Ubangiji ya faɗakar da ni kada in bi hanyar da jama’ar ke bi. Ya ce,

12 “Kada ka haɗa kanka da jama’a cikin ƙulle-ƙullensu, kada kuma ka ji tsoron abubuwan da su suke jin tsoro.

13 Ka tuna fa, ni Ubangiji Mai Runduna, mai tsarki ne. Wajibi ne ni kaɗai za ka ji tsoro.

14 Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama’ar mulkokin Yahuza da Isra’ila da mutanen Urushalima.

15 Da yawa za su yi tuntuɓe su faɗi. Za su faɗi, a kuwa ragargaza su. Za a kama su da tarko.”

16 Almajiraina su ne za su lura, su kuma kiyaye jawabin da Allah ya ba ni.

17 Ubangiji ya ɓoye kansa daga jama’arsa, amma ni na dogara gare shi, na kafa zuciyata a gare shi.

18 Ga ni tare da ‘ya’yan da Ubangiji ya ba ni. Ubangiji Mai Runduna, wanda kursiyinsa a kan Dutsen Sihiyona yake, ya maishe mu rayayyen jawabi ga jama’ar Isra’ila.

19 Mutane za su riƙa ce muku ku nemi shawarar ‘yan bori da masu sihiri waɗanda suke shaƙe muryar, har ba a jin abin da suke faɗa. Za su ce, “Ai, ma, ya kamata mutane su nemi shawara daga aljannu, su kuma nemi shawarar matattu saboda masu rai.”

20 Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga ‘yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”

Lokacin Wahala

21 Mutane za su yi ta kai da kawowa a ko’ina cikin ƙasar, cikin matsuwa da yunwa. A yunwar da suke sha da haushin da suke ji, za su zagi sarkinsu, su kuma zagi Allahnsu. Har ma zai yiwu su ɗaga ido su dubi sararin sama,

22 ko su zura wa ƙasa ido, amma ba abin da za su gani, sai wahala da duhu mai banrazana, inda za a kora su a ciki.

Categories
ISH

ISH 9

Haihuwar Sarkin Salama

1 Ba sauran baƙin ciki ga wadda take shan azaba. Dā an ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zabaluna da na Naftali, amma nan gaba wannan jiha za ta sami daraja, tun daga Bahar Maliya, zuwa gabashin ƙasar a wancan sashe na Urdun, har zuwa Galili kanta, wurin da baƙi suke zaune.

2 Jama’ar da suka yi tafiya cikin duhu,

Sun ga babban haske!

Suka zauna a inuwar mutuwa,

Amma yanzu haske ya haskaka su.

3 Ka ba su babbar murna, ya Ubangiji,

Ka sa su yi farin ciki.

Suna murna da abin da ka aikata,

Kamar yadda mutane suke murna sa’ad da suke girbin hatsi,

Ko sa’ad da suke raba ganima.

4 Gama ka karya karkiyar da ta nawaita musu,

Da kuma sandan da ake dukan kafaɗunsu da shi.

Kai ne, ya Ubangiji, ka kori al’ummar

Da ta zalunci jama’arka, ta kuma zambace su,

Daidai da yadda dā ka kori rundunar sojojin Madayana tuntuni.

5 Takalman sojojin da suka kawo yaƙi

Da dukan tufafinsu da suka birkiɗe da jini,

Za a ƙone su da wuta!

6 Ga shi, an haifa mana ɗa!

Mun sami yaro!

Shi zai zama Mai Mulkinmu.

Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al’ajabi,”

“Allah Maɗaukaki,”

“Uba Madawwami,”

“Sarkin Salama.”

7 Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba,

Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin,

Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa,

Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,

Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.

Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.

Ubangiji Ya Yi Fushi da Isra’ila

8 Ubangiji ya hurta hukunci a kan mulkin Isra’ila, da a kan zuriyar Yakubu.

9 Dukan jama’ar Isra’ila, duk wanda yake zaune a birnin Samariya, zai sani Ubangiji ne ya aikata haka. Yanzu suna da girmankai suna fāriya. Sun ce,

10 “Gine-ginen da aka yi da tubali sun rushe, amma za mu sāke gina su da dutse. An sassare ginshiƙan da aka yi da itacen durumi, amma za mu sāke kakkafa su da kyawawan itatuwan al’ul.”

11 Ubangiji ya kuta maƙiyansu daga Rezin su fāɗa su da yaƙi.

12 Suriya daga gabas, da Filistiya daga yamma, sun wage bakinsu don su haɗiye Isra’ila. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

13 Jama’ar Isra’ila ba su tuba ba, ko da yake Ubangiji Mai Runduna ya hukunta su, duk da haka ba su juyo ba.

14 A rana ɗaya Ubangiji zai hukunta shugabannin Isra’ila da jama’arta. Zai hallaka kawunansu da ƙafafunsu, da dabino da iwa,

15 wato tsofaffi da manyan mutane su ne kawunan, ƙafafu kuwa su ne annabawan da suke koyar da ƙarairayi!

16 Su waɗanda suke bi da jama’an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum.

17 Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

18 Muguntar jama’a tana ci kamar wutar da take cinye ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya. Tana ci kamar wutar dawa wadda hayaƙinta take murtukewa har sama.

19 Saboda Ubangiji Mai Runduna ya yi fushi, hukuncinsa yana ci kamar wuta ko’ina a ƙasar, yana hallakar da jama’a, kowa na ta kansa.

20 A ko’ina a ƙasar jama’a sukan wawashe su ci ɗan abincin da suke iya samu, amma ba su taɓa ƙoshi ba. Har ‘ya’yansu ma suke ci!

21 Jama’ar Manassa da jama’ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

Categories
ISH

ISH 10

1 Kun shiga uku! Kuna kafa dokokin rashin gaskiya don ku zalunci jama’ata.

2 Ta haka kuke hana wa talakawa hakkinsu, kuna kuma ƙin yi musu shari’ar gaskiya. Ta haka kuke ƙwace dukiyar gwauraye, wato matan da mazansu suka rasu, da ta marayu.

3 Me za ku yi sa’ad Allah zai hukunta ku? Me za ku yi kuma sa’ad da ya kawo muku masifa daga wata ƙasa mai nisa? Ina za ku sheƙa neman taimako? A ina kuma za ku ɓoye dukiyarku?

4 Za a kashe ku a yaƙi, ko a kwashe ku, kamammun yaƙi. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.

Allah Zai Sarrafa Sarkin Assuriya

5 Ubangiji ya ce, “Assuriya! Ina yin amfani da Assuriya kamar kulki don in hukunta waɗanda nake fushi da su.

6 Na aiki Assuriya ta faɗa wa al’ummar da ba ta tsoron Allah, da yaƙi, wato jama’ar da ta sa na yi fushi. Na aike su su yi waso su yi sata, su tattake jama’a kamar ƙura a tituna.”

7 Amma Sarkin Assuriya yana da nasa mugayen shirye-shirye da zai yi. Ya yi niyya ya hallaka al’ummai masu yawa.

8 Ya yi kurari, ya ce, “Kowane shugaban mayaƙana sarki ne!

9 Na ci biranen Kalno da na Karkemish. Na ci biranen Hamat da na Arfad. Na kuma ci Samariya da Dimashƙu.

10 Na miƙa hannuna don in hukunta wa waɗannan mulkoki masu bauta wa gumaka, wato gumakan sun yi yawa fiye da na Urushalima, da na Samariya.

11 Na hallaka Samariya da dukan gumakanta, haka ma zan yi wa Urushalima da siffofin da suke yi wa sujada a can.”

12 Ubangiji ya ce, “Sa’ad da na gama abin da nake yi a kan Dutsen Sihiyona da cikin Urushalima, zan hukunta Sarkin Assuriya saboda dukan kurarinsa da girmankansa.”

13 Sarkin Assuriya ya yi kurari ya ce, “Dukan waɗannan ni da kaina na yi su. Ni ƙaƙƙarfa ne, mai hikima, mai wayo. Na kawar da kan iyakokin da suke tsakanin ƙasashen sauran al’umma, na kwashe dukan abin da suka tattara suka adana. Kamar bijimi, haka na tattake mutanen da suke zaune a can.

14 Al’umman duniya kamar sheƙar tsuntsaye suke. Na tattara dukiyarsu, a sawwaƙe kamar yadda ake tattara ƙwai, ba tsuntsun da ya buɗe baki don ya yi mini kuka!”

15 Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”

16 Ubangiji Mai Runduna zai aukar da cuta don ya hukunta waɗanda suke ƙosassu yanzu. Za su ji jikinsu na ta ƙuna kamar wuta.

17 Allah da yake hasken Isra’ila, zai zama wuta. Allah, Mai Tsarki na Isra’ila, zai zama harshen wuta, wanda zai ƙone kowane abu rana ɗaya, har da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.

18 Jeji mai dausayi da ƙasar noma za a lalatar da su ƙaƙaf, kamar yadda ciwon ajali yake hallaka mutum.

19 Sai ‘yan itatuwa kaɗan za su ragu, ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.

Mutanen Isra’ila Kima ne Za Su Komo

20 Lokaci zai yi sa’ad da jama’ar Isra’ila da suka ragu ba za su ƙara dogara ga al’ummar da ta kusa hallaka su ba. Hakika za su dogara ga Ubangiji Allah, Mai Tsarki na Isra’ila.

21 Kaɗan daga cikin jama’ar Isra’ila za su koma wurin Allahnsu Mai Iko Dukka.

22 Ko da yake yanzu akwai jama’ar Isra’ila da yawa, yawansu kuwa kamar yashin teku, duk da haka, sai kaɗan ne za su komo. An tanada wa jama’a hallaka, sun kuwa cancanci hallakar.

23 Hakika a ƙasar duka, Ubangiji Allah Mai Runduna zai kawo hallaka kamar yadda ya ce zai yi.

Ubangiji Zai Hukunta Assuriya

24 Ubangiji Mai Runduna ya ce wa jama’arsa da suke Sihiyona, “Kada ku ji tsoron Assuriyawa, ko da yake suna wahalshe ku kamar yadda Masarawa suka yi.

25 Saura kaɗan in gama hukuncin da nake yi muku, sa’an nan in hallaka su.

26 Ni, Ubangiji Mai Runduna, zan bulale su da bulalata, kamar yadda na bugi mutanen Madayana a dutsen Oreb. Zan sa Assuriyawa su sha wahala kamar yadda Masarawa suka sha.

27 A lokacin nan zan ‘yantar da ku daga mulkin Assuriya, karkiyarsu ba za ta ƙara zama kaya mai nauyi a wuyanku ba.”

Mahara Sun Faɗa Musu da Yaƙi

28 Magabta suna cikin Ayiyat! Sun bi ta Migron! Sun bar kayayyakinsu a Mikmash!

29 Sun ƙetare hanya suka kwana a Geba! Mutanen Rama suka firgita. Mutanen da suke cikin Gibeya, garin sarki Saul, sun gudu.

30 Ku yi ihu, ku mutanen Gallim! Ku kasa kunne, ku mutanen Layish! Ku amsa, ku mutanen Anatot!

31 Jama’ar Madmena da na Gebim suna gudu su tsira da rayukansu.

32 Yau abokan gāba suna cikin Nob, daga can suke nuna wa Dutsen Sihiyona yatsa, wato wanda yake cikin Urushalima.

33 Ubangiji Mai Runduna zai sa su ragargaje har ƙasa, kamar rassan da aka sassare daga itace. Masu girmankai da manyansu za a datse su ƙasa, a ƙasƙantar da su.

34 Ubangiji zai sassare su har ƙasa kamar yadda ake sassare itatuwa da gatari a tsakiyar kurmi, kamar yadda itatuwa mafi kyau na Lebanon za su fāɗi.