Categories
ISH

ISH 51

Maganar Ta’aziyya ga Sihiyona

1 Ubangiji ya ce,

“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuke so a cece ku,

Ku da kuka zo gare ni neman taimako.

Ku yi tunanin dutse inda kuka fito,

Da mahaƙar duwatsu inda kuka fito.

2 Ku yi tunani a kan kakanku Ibrahim,

Da Saratu, wadda kuke zuriyarta.

Sa’ad da na kira Ibrahim ba shi da ɗa,

Amma na sa masa albarka, na ba shi ‘ya’ya,

Na sa zuriyarsa suka yi yawa.

3 “Zan ji juyayi a kan Sihiyona,

Da dukan masu zama a kufanta.

Ko da yake ƙasarta hamada ce, zan sa ta zama lambu,

Kamar lambun da na dasa a Aidan.

Murna da farin ciki za su kasance a can,

Da waƙoƙi na yabo da godiya zuwa gare ni.

4 “Ku kasa kunne gare ni, ku mutanena,

Ku saurara ga abin da nake faɗa,

Na ba da koyarwata ga al’ummai,

Dokokina za su kawo musu haske.

5 Zan zo da sauri in cece su,

Lokacina na nasara ya yi kusa.

Ni kaina zan yi mulki a kan al’ummai.

Manisantan ƙasashe za su jira ni in zo,

Za su jira da sa zuciya, ni in cece su.

6 Ku duba sammai, ku duba duniya!

Sammai za su shuɗe kamar hayaƙi,

Duniya kuwa za ta yage kamar tsohuwar tufa,

Dukan mutanenta kuma za su mutu.

Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,

Nasarata, ita ce za ta zama ta har abada.

7 “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai,

Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku.

Kada ku ji tsoro sa’ad da mutane suke yi muku ba’a da zagi.

8 Irin waɗannan mutane za su shuɗe kamar tufar da asu ya cinye!

Amma ceton da zan kawo zai dawwama har abada,

Nasarata za ta kasance har abada abadin.”

9 Ya Ubangiji, ka tashi, ka taimake mu!

Ka nuna ikonka, ka cece mu,

Ka nuna ikonka kamar yadda ka yi a dā.

Kai ne ka daddatse dodon ruwa, wato Rahab.

10 Kai ne ka sa teku ta ƙafe,

Ka kuma shirya hanya ta ruwa,

Domin waɗanda kake cetonsu su haye.

11 Su waɗanda ka fansa

Za su kai Urushalima da farin ciki,

Da waƙa, da sowa ta murna.

Za su yi ta murna har abada,

Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.

12 Ubangiji ya ce,

“Ni ne wanda yake ƙarfafa ku.

Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa,

Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?

13 Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku,

Wanda ya shimfiɗa sammai,

Ya kuma kafa harsashin ginin duniya?

Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku,

Da waɗanda suke shiri su hallaka ku?

Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!

14 ‘Yan sarƙa za su fita ba da jimawa ba

Za su yi tsawon rai,

Su kuma sami dukan abincin da suke bukata.

15 “Ni ne Ubangiji Allahnku,

Na dama teku

Na sa raƙumanta suka yi ruri.

Sunana Ubangiji Mai Iko Dukka!

16 Na shimfiɗa sammai,

Na kafa harsashin ginin duniya,

Na ce wa Sihiyona, ‘Ku jama’ata ne!

Na ba ku koyarwata,

Na kuwa kiyaye ku da ikona.’ ”

Ƙarshen Wahalar Urushalima

17 Ya Urushalima, ki farka!

Ki tashi da kanki, ki miƙe!

Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha,

Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!

18 Ba wanda zai yi miki jagora,

Ba wani daga cikin mutanenki

Da zai kama hannunki.

19 Masifa riɓi biyu ta auko miki,

Yaƙi ya lalatar da ƙasarki,

Mutanenki suka tagayyara da yunwa.

20 A kan kusurwar kowane titi

Mutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi,

Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama.

Suka ji ƙarfin fushin Allah.

21 Ku mutanen Urushalima, masu shan wahala,

Ku da kuke tangaɗi kamar waɗanda suka bugu,

22 Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce,

“Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina.

Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.

23 Zan ba da shi ga waɗanda suke zaluntarku,

Su waɗanda suka sa kuka kwanta a tituna

Suka tattake ku, sai ka ce kun zama ƙura.”

Categories
ISH

ISH 52

Allah Zai Ceci Urushalima

1 Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma!

Birni mai tsarki na Allah,

Ki yafa wa kanki jamali!

Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.

2 Ki kakkaɓe kanki, ya Urushalima!

Ki tashi daga cikin ƙura,

Ki hau gadon sarautarki.

Ki ɓaɓɓale sarƙoƙin da suke ɗaure da ke,

Ke kamammiyar jama’ar Sihiyona!

3 Ubangiji ya ce wa jama’arsa,

“Ba a biya kuɗi domin a saye ku ba,

Amma ga shi, kuka zama bayi.

Ba za a biya kuɗin fansa domin a ‘yantar da ku ba,

Amma, ga shi, za a ‘yantar da ku.

4 Kuka taɓa zaman baƙuntaka a Masar,

Daga baya Assuriyawa suka zalunce ku ba gaira ba dalili.

5 Yanzu kuma, ga shi, yana faruwa a Babila,

Kuka zama kamammu a can, ba gaira ba dalili.

Su da suke mulkinku suna girmankai, suna fāriya,

Suna ta nuna mini raini.

6 Amma zuwa gaba za ku sani

Ni ne Allah, wanda na yi magana da ku.”

7 Me ya fi wannan kyau?

A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu,

Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama.

Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona,

“Allahnki sarki ne!”

8 Waɗanda suke tsaron birni suna sowa,

Suna sowa tare saboda murna!

Za su ga komowar Ubangiji a Sihiyona da idanunsu!

9 Ku ɓarke da sowar murna,

Ku kufan Urushalima!

Ubangiji ya ta’azantar da jama’arsa,

Ya fanshi birninsa.

10 Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki,

Ya ceci jama’arsa,

Dukan duniya kuwa ta gani.

11 Ku fita, ku bar Babila

Ku dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji!

Kada ku taɓa abin da aka hana,

Ku kiyaye kanku da tsarki,

Ku fita ku bar birnin.

12 A wannan lokaci ba za ku bukaci ku fita da garaje ba,

Ba za ku yi ƙoƙari ku tsere ba!

Ubangiji Allah ne zai bishe ku,

Ya kuma kiyaye ku ta kowane gefe.

Bawan Ubangiji Mai Shan Wuya

13 Ubangiji ya ce,

“Bawana zai yi nasara a aikinsa,

Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.

14 Mutane da yawa suka gigice sa’ad da suka gan shi,

Ya munana har ya fita kamannin mutum.

15 Amma yanzu al’ummai da yawa za su yi mamaki a kansa,

Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki.

Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”

Categories
ISH

ISH 53

1 Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu?

Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan?

2 Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girma

Kamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

Ba shi da wani maƙami ko kyan ganin

Da zai sa mu kula da shi.

Ba wani abin da zai sa mu so shi,

Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.

3 Muka raina shi, muka ƙi shi,

Ya daure da wahala da raɗaɗi.

Ba wanda ya ko dube shi.

Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.

4 Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce,

Raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi.

Mu kuwa muna tsammani wahalarsa

Hukunci ne Allah yake yi masa.

5 Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu,

Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata.

Hukuncin da ya sha ya ‘yantar da mu,

Dūkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.

6 Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata,

Ko wannenmu ya kama hanyarsa.

Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa,

Hukuncin da ya wajaba a kanmu.

7 Aka ƙware shi ba tausayi,

Amma ya karɓa da tawali’u,

Bai ko ce uffan ba.

Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa,

Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya,

Bai ko ce uffan ba.

8 Aka kama shi, aka yanke masa shari’a,

Aka tafi da shi domin a kashe shi,

Ba wanda ya kula da ƙaddararsa.

Aka kashe shi saboda zunubin mutanenmu.

9 Aka yi jana’izarsa tare da maguye.

Aka binne shi tare da masu arziki

Ko da yake bai taɓa yin laifin kome, ko ƙarya ba.

10 Ubangiji ya ce,

“Nufina ne ya sha wahala,

Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara,

Saboda haka zai ga zuriyarsa,

Zai yi tsawon rai,

Ta wurinsa nufina zai cika.

11 Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna,

Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce,

Shi ne bawana, adali,

Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa,

Ya sa su zama mutanena amintattu.

12 Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma,

Matsayi a cikin manyan mutane masu iko.

Da yardarsa ya ba da ransa

Ya ɗauki rabon masu laifi.

Ya maye gurbin masu zunubi da yawa,

Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi.

Ya yi roƙo dominsu.”

Categories
ISH

ISH 54

Ƙaunar Ubangiji ga Isra’ila

1 Urushalima, kika zama kamar matar da ba ta da ɗa.

Amma yanzu kina iya rairawa, ki yi sowa saboda murna.

Yanzu za ki ƙara samun ‘ya’ya fiye da na

Matar da mijinta bai taɓa rabuwa da ita ba!

2 Ki fāɗaɗa alfarwar da kike zama ciki!

Ki ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta!

3 Za ki faɗaɗa kan iyakar ƙasarki a kowane gefe,

Jama’arki za su karɓi ƙasarsu

Wadda al’ummai suke mallaka yanzu,

Biranen da aka bari ba kowa, za su cika da mutane.

4 Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba,

Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba.

Za ki manta da rashin amincinki irin na matar ƙuruciya,

Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki,

Mai kama da na gwauruwa.

5 Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki,

Sunansa Ubangiji Mai Runduna!

Allah Mai Tsarki na Isra’ila mai fansarki ne,

Shi ne mai mulkin dukan duniya!

6 Kina kama da amarya

Wadda mijinta ya rabu da ita, tana baƙin ciki ƙwarai.

Amma Ubangiji yana kiranki zuwa gare shi, ya ce,

7 “A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,

Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.

8 Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci,

Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.”

Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.

9 “Na yi alkawari a zamanin Nuhu,

Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba.

Yanzu kuwa ina miki alkawari,

Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba,

Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.

10 Duwatsu da tuddai za su ragargaje,

Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam.

Zan cika alkawarina na salama har abada.”

Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.

11 Ubangiji ya ce,

“Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,

Ba ki da wanda zai ta’azantar da ke.

Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja.

12 Zan gina hasumiyarki da jan yakutu,

Da ƙofofinki kuma da duwatsu masu haske kamar hasken wuta,

Da garun da ya kewaye ki kuwa zan gina ta da lu’ulu’ai.

13 “Ni kaina zan koya wa mutanenki,

Zan kuwa ba su wadata da salama.

14 Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki.

Za ki tsira daga shan zalunci da razana.

Gama ba za su kusace ki ba.

15 Idan wani ya far miki,

Ya yi ne ba da yardata ba,

Dukan wanda ya hau ki da yaƙi zai fāɗi!

16 “Ni ne na halicci maƙeri

Wanda ya zuga wuta ya kuwa ƙera makamai.

Ni ne kuma na halicci mayaƙi

Wanda yakan mori makamai domin kisa.

17 Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki,

Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki.

Zan kāre bayina,

In kuwa ba su nasara.”

Ubangiji ne ya faɗa.

Categories
ISH

ISH 55

Allah Ya Nuna Jinƙai ga Kowa

1 Ubangiji ya ce,

“Duk mai jin ƙishi ya zo,

Ga ruwa a nan!

Ku da ba ku da kuɗi ku zo,

Ku sayi hatsi ku ci!

Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara,

Ba za ku biya kome ba!

2 Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba?

Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa?

Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa,

Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.

3 “Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni,

Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai!

Zan yi tabbataccen alkawari da ku,

Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.

4 Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al’ummai,

Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.

5 Yanzu kuwa za ku kira al’ummai, baƙi,

Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya,

Amma yanzu za su sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku!

Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra’ila,

Zan sa dukan wannan ya faru,

Zan ba ku girma da daraja.”

6 Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu’a gare shi,

Yanzu da yake kusa.

7 Bari mugaye su bar irin al’amuransu,

Su sāke irin tunaninsu.

Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu,

Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.

8 Ubangiji ya ce,

“Tunanina ba kamar irin naku ba ne,

Al’amurana kuma dabam suke da naku.

9 Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,

Haka al’amurana da tunanina suke nesa da naku.

10 “Maganata kamar dusar ƙanƙara take,

Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya.

Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba,

Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.

11 To, haka maganar da na faɗa take,

Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata,

Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.

12 “Za ku fita daga cikin Babila da murna,

Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama.

Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa,

Itatuwa za su yi ta sowa don murna!

13 Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu,

Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa.

Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada,

Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”

Categories
ISH

ISH 56

Sakamakon Cikar Alkawarin Ubangiji

1 Ga jawabin da Ubangiji ya yi, “Ku kiyaye gaskiya ku yi adalci, gama cetona yana zuwa nan da nan, za a kuwa bayyana adalcina.

2 Mai albarka ne mutumin da yake aikata wannan, da ɗan adam da yake riƙe da shi kam, wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ƙazantar da ita ba, wanda kuma ya tsame hannunsa daga aikata kowace irin mugunta.”

3 Kada baƙon da ya hada kansa da mutanen Ubangiji ya ce, hakika Ubangiji zai ware shi daga jama’arsa.

Kada kuma baban ya ce shi busasshen itace ne.

4 Ga abin da Ubangiji ya ce, wa mutanen nan, “Ku babani waɗanda kuka kiyaye Asabar ɗina, ku da kuka zaɓi abubuwan da suka gamshe ni, kuka kuwa cika alkawarina da aminci,

5 zan ba ku matuni da suna a Haikalina da cikin garukana, da sun fi na ‘ya’ya mata da maza. Zan ba ku tabbataccen suna wanda ba za a raba ku da shi ba.”

6 Ubangiji ya ce wa baƙin da suka bi shi, don su yi masa hidima, suna ƙaunar sunansa, sun kuma zama bayinsa, dukan wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ɓata ta ba, ya kuma cika alkawarinsa da aminci,

7 “Zan kai ku tsattsarkan dutsena, in sa ku yi murna a masujadata. Hadayunku na ƙonawa da sadakokinku za su zama abin karɓa a bagadena. Za a kira Haikalina wurin yin addu’a na dukan jama’a.”

8 Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra’ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”

Kā da Tsafin Isra’ila

9 Dukanku namomin jeji ku zo ku ci, dukanku namomin jeji.

10 Matsaransa makafi ne, dukansu marasa ilimi ne. Dukansu kamar karnuka ne bebaye, ba su iya haushi ba, suna kwance suna ta mafarki, suna jin daɗin rurumi!

11 Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba.

12 Sukan ce, “Zo mu samo ruwan inabi, bari mu cika cikinmu da barasa. Gobe ma kamar yau za ta zama, har ma fiye da haka.”

Categories
ISH

ISH 57

1 Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala’i.

2 Ya shiga da salama yana hutawa a kabarinsa, shi wanda ya yi tafiya da adalci.

3 Amma ku ku matso nan kusa, ku ‘ya’ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinaci da karuwa.

4 Wa kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke wage baki, kuna zaro harshe? Ashe, ku ba ‘ya’yan masu laifi ba ne, zuriyar marikita,

5 ku da muguwar sha’awa take ƙonawa a tsakanin itatuwan oak, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. Ku da kuka karkashe ‘ya’yanku a cikin kwaruruka, da a ƙarƙashin duwatsu masu tsayi?

6 Rabonku yana cikin duwatsu masu sulɓi na cikin kwari. A gare su kuka kwarara hadaya ta sha, kuka kawo hadaya ta gari. Kuna tsammani zan ji daɗin waɗannan al’amura?

7 A kan dogayen duwatsu masu tsayi kuka sa gadonku. A can kuka haura don ku miƙa hadaya.

8 A bayan ƙofa da madogaran ƙofa kuka kafa gumakanku. Kun rabu da ni, kun kware gadonku, kuna hau kun fāɗaɗa shi, kuka ƙulla yarjejeniya tsakaninku da su. Kuna ƙaunar gadonsu, kun dubi tsiraici.

9 Kun tafi wurin Molek da mai, da turare iri iri da kuka riɓaɓɓanya. Kun aika jakadunku can nesa, kun aike su su gangara, har zuwa lahira.

10 Kun damu saboda nisan hanyarku, amma ba ku ce, “Ba shi da wani amfani ba.” Ƙarfinku ya sake sabunta ranku, don haka ba ku suma ba.

11 Ubangiji ya ce, “Wa ya sa ku fargaba, kuke jin tsoronsa, har kuka yi ƙarya? Ba ku tuna da ni, ko ku kula da ni ba? Ashe, ban yi haƙuri tun da daɗewan nan ba, duk da haka kuwa ba ku ji tsorona ba?

12 Zan ba da labarin adalcinku da ayyukanku, amma ba za su taimake ku ba.

13 Sa’ad da kuka ta da murya kuka yi kuka, to, bari tattaruwar gumakanku su cece ku! Iska za ta fauce su, numfashi zai kawar da su. Amma wanda ya fake gare ni zai mallaki ƙasar. Zai kuma yi sujada a Haikalina.”

Taimakon Allah da Warkarwa

14 Ubangiji ya ce, “Ku gina, ku shirya hanya. Ku kawar da kowane abin sa tuntuɓe daga kan hanyar jama’ata!”

15 Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali’u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali’u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.

16 Ba zan yi ta gāba da ku, ko in yi ta fushi da ku har abada ba. Gama ruhu zai yi suma a gabana, da numfashin su waɗanda na halitta.

17 Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.

18 “Na ga al’amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta’azantar da su tare da masu makoki.

19 Salama, salama,” in ji Ubangiji, “Ga wanda yake nesa da wanda yake kusa. Zan warkar da su.

20 Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, gama ba ta iya natsuwa. Ruwanta kuma yana tumbatsa, ya gurɓace, ya ƙazantu.”

21 Allah ya ce, “Ba salama ga mugaye.”

Categories
ISH

ISH 58

Kiyaye Azumi yadda ya Kamata

1 Ubangiji ya ce, “Ku yi kuka da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa! Ku ta da muryoyinku kamar busar ƙaho. Ku shaida wa jama’ata laifinsu, ku shaida wa zuriyar Yakubu zunubansu.

2 Duk da haka suna ta nemana kowace rana, suna murna su san al’amurana, sai ka ce su al’umma ce wadda take aikata adalci, wadda kuma ba ta rabu da dokokin Allahnta ba. Suna roƙona in yi musu shari’ar adalci, suna murna su zo kusa da Allah.”

3 Mutane sukan ce, “Me ya sa muka yi azumi, Ubangiji bai gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, Ubangiji kuwa bai kula ba?”

Ubangiji ya ce musu, “Duba, a ranar da kuke azumi, nishaɗin kanku kuke nema, kuna zaluntar dukan ma’aikatanku.

4 Duba, kuna azumi don ku yi jayayya ne, ku yi ta faɗa, ku yi ta naushin juna. Irin wannan azumi naku a wannan rana, ba zai sa a ji muryarku a can Sama ba.

5 Irin azumin da nake so ke nan ne? Wato ranar da mutum zai ƙasƙantar da kansa kawai. Wato ku sunkuyar da kanku ne kamar jema, ku kuma shimfiɗa tsumma, ku barbaɗa toka a inda kuke zama. Kun iya ce da wannan azumi, karɓaɓɓiyar rana ga Ubangiji?

6 “To, ba irin wannan azumi ne na zaɓa ba? Wato ku kwance sarƙoƙin mugunta, ku kwance masu karkiya, ku ‘yantar da waɗanda ake zalunta, ku kakkarye kowace karkiya.

7 Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga ‘yan’uwanku.

8 “Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, za ku warke nan da nan. Adalcinku zai yi muku jagora, zatina zai rufa muku baya.

9 Sa’an nan za ku yi kira, ni kuwa zan amsa, za ku yi kuka, ni kuwa zan ce muku, ‘Ga ni.’

“Idan kuka kawar da karkiya daga cikinku, kuka daina nuna wa juna yatsa, da faɗar mugayen maganganu,

10 idan kuka ƙosar da mayunwata, kuka biya bukatar waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu, duhunku kuma zai zama kamar hasken tsakar rana.

11 Zan bi da ku kullayaumin, zan biya bukatarku da abubuwa masu kyau, in sa ƙasusuwanku su yi ƙarfi, ku zama kamar lambun da ake masa banruwa, za ku zama kamar maɓuɓɓugar ruwa da ba ta ƙonewa.

12 Za ku sāke gina tsofaffin kufanku na dā can, za ku sāke kafa tushen zuriya da yawa. Za a kira ku, ‘Masu gyaran abin da ya lalace, masu sāke gyaran gidaje.’ ”

13 Ubangiji ya ce, “Idan kun juyo kuna kiyaye ranar Asabar, kuka daina annashuwarku a tsattsarkar ranata, kuka kuma kira Asabar ranar murna, tsattsarkar rana ta Ubangiji, mai daraja, idan kun girmama ta, har kuka daina bin son zuciyarku, ba ku kuma bar shagulgula su ɗauke hankalinku ba, ko ku hurta maganganun banza,

14 sa’an nan ne za ku yi murna cikin Ubangiji, zan sa ku a kan maɗaukakan wurare na duniya. Zan kuma ciyar da ku da gādon mahaifinku Yakubu, ni Ubangiji na faɗa.”

Categories
ISH

ISH 59

Faɗar Muguntar Al’ummar

1 Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.

2 Amma laifofinku suka raba tsakaninku da Allahnku. Zunubanku ne kuma suka sa ya juya daga gare ku don kada ya ji ku.

3 Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma sun ƙazantu da mugunta, leɓunanku kuma suna faɗar ƙarairayi, harsunanku kuwa suna raɗar mugunta.

4 Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari’a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta.

5 Kuna ƙyanƙyashe ƙwan kāsa, kuna saƙa da saƙar gizogizo. Duk wanda ya ci ƙwayayenku zai mutu, ƙwan da ya fashe zai ƙyanƙyashe kububuwa.

6 Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya.

7 Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku.

8 Hanyar salama ba ku san ta ba. Ba adalci a hanyoyinku, kukan karkatar da hanyoyinku, ba wanda zai yi tafiya lafiya a cikinku.

9 Mutane suna cewa, “Don haka ne, yin gaskiya ya yi nisa da mu, adalci kuwa bai iske mu ba. Muna ta neman haske, sai ga duhu, muna neman haske, sai muka yi tafiya cikin duhu.

10 Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke.

11 Dukanmu muna gurnani kamar beyar, muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci, amma ina. Muna ta neman ceto, amma ya yi nisa da mu.

12 “Gama laifofinmu sun yi yawa a gabanka, zunubanmu kuwa suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu suna tare da mu, muna kuwa sane da laifofinmu,

13 wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su.

14 Aikata gaskiya ya kawu, adalci ya tsaya daga can nesa, gama gaskiya ta fāɗi a dandali, sahihanci ba zai shiga ba.

15 Gaskiya ba ta, wanda ba ya aikata mugunta ya zama ganima.”

Ubangiji ya gani, bai kuwa ji daɗi ba, da yake gaskiya ba ta.

16 Ya ga ba wani mutum, ba kuwa wanda zai taimaki waɗanda ake zalunta. Sa’an nan da ikon kansa ya yi nasara, adalcinsa ya goyi bayansa.

17 Ya rufe ƙirjinsa da sulken adalci, da kwalkwalin ceto a kansa. Ya sa rigar ɗaukar fansa, ya yafa alkyabbar ikonsa.

18 Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa.

19 Saboda haka waɗanda suke yamma za su ji tsoron sunan Ubangiji, waɗanda suke wajen gabas kuma za su ji tsoron ɗaukakarsa, gama zai zo kamar rafi mai tsananin gudu, wanda iskar Ubangiji take korawa.

20 Zai zo Sihiyona ya zama mai fansa ga waɗanda suke na Yakubu, su da suka juya suka bar mugunta.

21 Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan ‘ya’yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”

Categories
ISH

ISH 60

Darajar Urushalima a Gaba

1 Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana,

Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!

2 Duhu zai rufe sauran al’umma,

Amma hasken Ubangiji zai haskaka a kanki,

Daukakarsa za ta kasance tare da ke!

3 Za a jawo al’ummai zuwa ga haskenki,

Sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.

4 Ki duba kewaye da ke, ki ga abin da yake faruwa,

Mutanenki suna ta tattaruwa domin su komo gida!

‘Ya’yanki maza za su taho daga nesa,

Za a ɗauki ‘ya’yanki mata kamar yara.

5 Za ki ga wannan, ki cika da farin ciki,

Za ki yi rawar jiki saboda jin daɗi.

Za a kawo miki dukiyar al’ummai,

Wato waɗanda suke a ƙasashen hayi.

6 Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa.

Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi.

Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi!

7 Dukan tumaki na Kedar da Nebayot,

Za a kawo miki su hadaya,

A kuwa miƙa su a kan bagade domin Ubangiji ya ji daɗi.

Ubangiji zai darajanta Haikalinsa fiye da dā.

8 Waɗannan jiragen ruwa fa? Suna tafe kamar gizagizai,

Kamar kurciyoyi suna komowa gida.

9 Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe,

Suna kawo mutanen Allah gida.

Suna tafe da azurfa da zinariya,

Domin su girmama sunan Ubangiji,

Allah Mai Tsarki na Isra’ila,

Wanda ya sa dukan al’ummai su girmama mutanensa.

10 Ubangiji ya ce wa Urushalima,

“Baƙi ne za su sāke gina garukanki,

Sarakunansu kuma za su bauta miki.

Na hukunta ki da fushina,

Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.

11 Ƙofofinki za su kasance a buɗe dare da rana,

Domin sarakunan al’ummai su kawo miki dukiyarsu.

12 Amma al’umman da ba su bauta miki ba,

Za a hallakar da su.

13 “Itatuwan fir da irinsu

Mafi kyau daga jejin Lebanon,

Za a kawo su domin a sāke gina ki, ke Urushalima,

Domin a ƙawata Haikalina,

A darajanta birnina.

14 ‘Ya’ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo,

Su rusuna, su nuna bangirma.

Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki.

Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’

‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra’ila.’

15 “Ba za a ƙara ƙinki, a yashe ki ba,

Ki zama birnin da aka fita aka bari ba kowa ciki.

Zan sa ki zama babba, mai ƙayatarwa kuma,

Wurin yin farin ciki har abada abadin.

16 Al’ummai da sarakuna za su lura da ke

Kamar yadda uwa take lura da ɗanta.

Za ki sani, ni Ubangiji, na cece ki,

Allah Mai Iko Dukka na Isra’ila ya fanshe ki.

17 “Zan kawo miki zinariya maimakon tagulla,

Azurfa maimakon baƙin ƙarfe,

Tagulla kuma maimakon itace.

Za ki sami baƙin ƙarfe maimakon dutse.

Masu mulkinki ba za ƙara zaluntarki ba,

Zan sa su yi mulki da gaskiya da salama.

18 Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba,

Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba.

Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu,

Za ki yi yabona domin na cece ki.

19 “Rana ba za ta ƙara zama haskenki da rana ba,

Ko wata ya zama haskenki da dare.

Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki,

Hasken ɗaukakata zai haskaka a kanki.

20 Kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.

Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki,

Mai daɗewa fiye da na rana da na wata.

21 Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai,

Za su kuwa mallaki ƙasar har abada.

Ni na dasa su, ni na yi su

Domin su bayyana girmana ga duka.

22 Har ma da iyalin da suka fi ƙanƙanta da ƙasƙanci,

Za su zama babbar al’umma,

Kamar al’umma mai iko.

Zan sa wannan ya faru nan da nan

Sa’ad da lokacin da ya dace ya yi.

Ni ne Ubangiji!”