Categories
ISH

ISH 61

Albishirin Ceto ga Sihiyona

1 Ubangiji ya saukar mini da ikonsa.

Ya zaɓe ni, ya aike ni

Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa,

In warkar da waɗanda suka karai a zuci,

In yi shelar kwance ɗaurarru,

Da kuma ‘yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.

2 Ya aike ni in yi shela,

Cewa lokaci ya yi

Da Ubangiji zai ceci mutanensa,

Ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu.

Ya aike ni domin in ta’azantar da masu makoki,

3 Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona

Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki,

Waƙar yabo maimakon ɓacin rai.

Ubangiji kansa zai lura da su,

Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa.

Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai,

Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.

4 Za su sāke gina biranen da suke a rurrushe tun da daɗewa.

5 Ya Urushalima, baƙi za su bauta miki,

Za su lura da garkunanki,

Za su nome gonakinki, su gyara gonakinki na inabi.

6 Amma za a sani, ku firistoci ne na Ubangiji,

Za ku mori dukiyar al’ummai,

Za ku yi fāriya da cewa, taku ce.

7 Kunyarku da shan wulakancinku za su ƙare.

Za ku zauna a ƙasarku,

Za a riɓanya dukiyarku,

Za ku yi ta farin ciki har abada.

8 Ubangiji ya ce,

“Ina ƙaunar aikin gaskiya,

Amma ina ƙin zalunci da aikata laifi.

Da aminci zan ba mutanena lada,

In yi madawwamin alkawari, da su.

9 Za su yi suna a cikin al’ummai,

Dukan wanda ya gan su zai sani,

Su ne mutanen da na sa wa albarka.”

10 Urushalima tana murna saboda abin da Ubangiji ya yi.

Tana kama da amaryar da ta sha ado a ranar aurenta.

Allah ya suturce ta da ceto da nasara.

11 Ba shakka, Ubangiji zai ceci jama’arsa,

Kamar yadda iri yakan tsiro ya yi girma.

Dukan al’ummai kuwa za su yi yabonsa.

Categories
ISH

ISH 62

1 Zan yi magana domin in ƙarfafa Urushalima,

Ba zan yi shiru ba,

Sai na ga adalcinta ya bayyana kamar haske,

Cetonta kuma ya haskaka kamar fitila da dare.

2 Ya Urushalima, al’ummai za su ganki mai gaskiya!

Dukan sarakunansu za su ga darajarki.

Za a kira ki da sabon suna,

Sunan da Ubangiji ya bayar da kansa.

3 Za ki zama kamar kyakkyawan rawani ga Ubangiji,

Wato kambin sarauta mai daraja gare shi.

4 Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba,

Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.”

Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.”

Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,”

Domin Ubangiji ya ji daɗinki,

Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.

5 Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa,

Za ku yi murna tare,

Kamar murnar amarya da ango.

6 Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki

Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana.

Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa,

Ba kuwa za su bari ya manta ba!

7 Ba za su bari ya huta ba, sai ya ceci Urushalima tukuna,

Ya sa ta zama birnin da dukan duniya za ta yaba wa.

8 Ubangiji ya yi alkawari mai ƙarfi,

Ta wurin ikonsa kuwa zai cika shi.

“Hatsinku ba zai ƙara zama abincin abokan gābanku ba,

Baƙi ba za su ƙara shanye ruwan inabinku ba.

9 Amma ku da kuka shuka hatsin kuka kuma girbe shi,

Za ku ci abinci, ku yi yabon Ubangiji!

Ku da kuka lura da itatuwan inabi kuka tara su,

Za ku sha ruwan inabi a filayen Haikalina.”

10 Ku mutanen Urushalima, ku fita daga cikin birni,

Ku gyara hanyoyi domin jama’arku da suke komowa!

Ku shirya babbar hanya,

Ku kawar da duwatsu daga hanyar!

Ku sa alama domin al’ummai su sani,

11 Ubangiji yana sanarwa ga dukan duniya,

Cewa, “Ku ce wa jama’ar Urushalima,

Ubangiji Mai Cetonku yana zuwa,

Yana kawo mutanen da ya cece su.”

12 Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama’ar Allah,”

“Jama’ar da Ubangiji ya Fansa!”

Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,”

“Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”

Categories
ISH

ISH 63

Ranar Ramawa ta Ubangiji

1 Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa?

Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.

2 Me ya sa tufafinsa suke da ja haka, kamar na mutumin da ya tattake ‘ya’yan inabi domin ya sami ruwan inabi?

3 Ubangiji ya amsa ya ce, “Na tattake al’ummai kamar ‘ya’yan inabi, ba kuwa wanda ya taimake ni. Na tattake su cikin fushina, jininsu kuwa ya fantsamar wa dukan tufafina.

4 Na ga lokacin da zan fanshi mutanena ya yi, lokaci ne da zan hukunta wa abokan gābansu.

5 Na yi mamaki sa’ad da na duba, sai na ga ba wanda zai taimake ni. Amma fushina ya sa na sami ƙarfi, har ni kaina na ci nasara.

6 Da fushina na tattake dukan sauran al’umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”

Alherin Ubangiji ga Isra’ila

7 Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa,

Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana.

Ya sa wa jama’ar Isra’ila albarka mai yawa,

Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.

8 Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su

9 daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala’ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,

10 amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.

11 Amma suka tuna da zamanin dā, zamanin Musa bawan Ubangiji, suka yi tambaya suka ce, “Yanzu fa, ina Ubangiji yake wanda ya ceci shugabannin jama’arsa daga teku? Ina Ubangiji yake, wanda ya ba Musa iko musamman?

12 Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al’amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama’arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”

13 Sa’ad da Ubangiji ya bi da su ta ruwa mai zurfi, suka taka kamar ingarmun dawakai, ba su ko yi tuntuɓe ba.

14 Kamar yadda ake bi da shanu cikin kwari mai dausayi, haka Ubangiji ya ba mutanensa hutawa. Haka kuma Ubangiji ya bi da mutanensa, ya kuwa kawo ɗaukaka ga sunansa.

Addu’ar Neman Jinƙai da Taimako

15 Ya Ubangiji, ka dube mu daga Sama, wurin da kake cike da tsarki da ɗaukaka. Ina kulawan nan da kake yi mana? Ina ikon nan naka? Ina ƙaunan nan taka da juyayin nan naka? Kada ka watsar da mu.

16 Kai ne Ubanmu. Ko kakanninmu, wato su Ibrahim da Yakubu, ba za su iya taimakonmu ba, amma kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu. Kai ne Mai Fansarmu a koyaushe.

17 Don me ka bari muka ɓata daga al’amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.

18 Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka.

19 Mun zama kamar ba ka taɓa zama mai mulkinmu ba, kamar mu kuma ba mu taɓa zama mutanenka ba.

Categories
ISH

ISH 64

1 Don me ba za ka kware sararin sama, ka sauko ba? Duwatsu za su gan ka, su girgiza saboda tsoro!

2 Za su karkaɗu kamar ruwan da yake tafasa a wuta. Ka zo ka bayyana ikonka a kan abokan gābanka, ka sa al’ummai su yi rawar jiki a gabanka.

3 Ka taɓa zuwa ka yi abubuwan banrazana waɗanda ba mu sa tsammani ba, duwatsu suka ganka suka kaɗu domin tsoro.

4 Ba wanda ya taɓa gani ko jin labarin wani Allah kamarka, wanda ya yi waɗannan ayyuka ga waɗanda suka sa zuciyarsu gare shi.

5 Ka amince da waɗanda suke murna su aikata abin da yake daidai, su waɗanda suka tuna da yadda kake so su yi zamansu. Ka yi fushi da mu, amma muka ci gaba da yin zunubi, har da fushin da ka yi ƙwarai, muka ci gaba da aikata abin da ba daidai ba, tun daga zamanan dā.

6 Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.

7 Ba wanda ya juyo gare ka ya yi addu’a, ba wanda ya je gare ka neman taimako. Ka ɓuya mana, ka kuwa yashe mu saboda zunubanmu.

8 Amma kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu,

9 saboda haka kada ka yi fushi da mu ainun, ko ka riƙe da zunubanmu har abada, mu dai mutanenka ne, ka yi mana jinƙai.

10 Keɓaɓɓun biranenka suna kama da hamada, aka kuma ƙaurace wa kufan Urushalima.

11 Haikalinmu, kyakkyawan keɓaɓɓen wuri inda kakanninmu suka yi yabonka, aka lalatar da shi da wuta, dukan wuraren da muka ƙauna aka lalatar da su.

12 Ya Ubangiji, dukan wannan bai sa ka yi wani abu ba? Ba za ka yi kome ba, kana kuwa sa mu yi ta shan wuya, har fiye da yadda muke iya daurewa?

Categories
ISH

ISH 65

Hukuncin Allah a kan Masu Tawaye

1 Ubangiji ya ce, “Na shirya in amsa addu’o’in mutanena, amma ba su yi addu’a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al’ummar ba ta yi addu’a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, ‘Ga ni nan, zan taimake ku.’

2 Kullum ina a shirye domin in marabci waɗannan mutane, waɗanda saboda taurinkansu suka yi ta aikata abin da ba daidai ba, suka bi hanyoyin kansu.

3 Suka yi ta ƙara sa ni fushi ta wurin rashin kunyarsu. Suka miƙa hadayu irin na arna a ɗakunan tsafi da suke a lambu, suka kuma ƙona turare a kan bagadan arna.

4 Da dare sukan tafi cikin kogwanni da kaburbura, suna neman shawarar kurwar matattu. Waɗannan mutane sukan ci naman alade, su kuma sha romon naman da aka miƙa hadaya irin ta arna.

5 Sa’an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.

6 “Na riga na ƙudura hukuncinsu, shari’ar da aka yanke kuwa an rubuta ta. Ba zan ƙyale abin da suka aikata ba, amma zan sāka musu

7 saboda zunubansu da zunuban kakanninsu. Gama suka ƙona turare a ɗakunan tsafin arna na kan tuddai, suka kuwa faɗi mugun abu a kaina. Saboda haka zan hukunta su yadda ya cancance su.”

8 Ubangiji ya ce, “Ba wanda ya lalatar da ‘ya’yan inabi, maimakon haka sai suka yi ruwan inabi da su. Ni kuwa ba zan hallakar da dukan mutanena ba, zan ceci waɗanda suke bauta mini.

9 Zan sa wa Isra’ilawa waɗanda suke na kabilar Yahuza albarka, zuriyarsu kuma za su mallaki ƙasata da duwatsuna. Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda suke bauta mini za su zauna a can.

10 Za su yi mini sujada, za su kai tumakinsu da shanunsu wurin kiwo a kwarin Sharon a wajen yamma, da kuma a kwarin Akor a wajen gabas.

11 “Amma ba haka zai zama ba, ga ku da kuka rabu da ni, ku waɗanda kuka yi watsi da Sihiyona, tsattsarkan dutsena, kuka yi sujada ga Gad da Meni, wato allolin sa’a da na ƙaddara.

12 Mutuwa ta ƙarfi da yaji za ku yi, gama sa’ad da na yi kiranku ba ku amsa ba, ba ku kasa kunne ba kuwa sa’ad da nake magana da ku. Kuka zaɓa ku yi mini rashin biyayya, ku kuma aikata mugunta.

13 Saboda haka ina faɗa muku, cewa su waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yi mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya.

14 Za su raira waƙa don farin ciki, amma ku za ku yi kuka da karayar zuci.

15 Zaɓaɓɓun mutane ne za su mori sunayenku wajen la’antarwa. Ni, Ubangiji, zan kashe ku. Amma zan ba da sabon suna ga waɗanda suke yi mini biyayya.

16 Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”

Sabuwar Sama da Sabuwar Duniya

17 Ubangiji ya ce, “Ina yin sabuwar duniya da sabon sararin sama. Abubuwa na dā za a manta da su ɗungum.

18 Ku yi murna da farin ciki a kan abin da na halitta. Sabuwar Urushalima da nake halittawa za ta cika da murna, jama’arta kuma za su yi farin ciki.

19 Ni kaina kuma zan cika da murna saboda Urushalima da jama’arta. Ba kuka a can, ba bukatar neman taimako.

20 Jarirai ba za su mutu tun suna jarirai ba, ko wanne zai cika yawan kwanakinsa kafin ya mutu. Waɗanda suke masu shekara ɗari da haihuwa su ne samari. Waɗanda suka mutu kafin wannan lokaci, to, alama ce, ta cewa na hukunta su.

21-22 Mutane za su gina gidaje su kuwa zauna a cikinsu, ba waɗansu dabam za su mori gidajen ba. Za su dasa gonakin inabi su kuwa ji daɗin ruwan inabi, ba waɗansu dabam za su sha shi ba. Mutanena za su yi tsawon rai kamar itatuwa. Za su ci cikakkiyar moriyar abubuwan da suka yi aikinsu.

23 Aikin da suka yi zai yi nasara, ‘ya’yansu ba za su gamu da bala’i ba, zan sa musu albarka duk da zuriyarsu har dukan zamanai.

24 Zan amsa addu’o’insu tun ma kafin su gama yin addu’a gare ni.

25 Kyarketai da ‘yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci budu kamar yadda shanu suke yi. Maciji ba zai ƙara zama abu mai hatsari ba. A kan Sihiyona tsattsarkan dutsena, ba za a sami wani abu da zai cutar ba, ko wani mugun abu.”

Categories
ISH

ISH 66

Hukuncin Ubangiji da Wadatar Sihiyona

1 Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?

2 Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali’u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.

3 “Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu’a ga gumaka. Suna jin daɗin al’amuran banƙyama a lokacin yin sujada.

4 Saboda haka zan aukar musu da masifa, ainihin abin da suke jin tsoro, gama ba wanda ya amsa sa’ad da na yi kira, ko ya kasa kunne sa’ad da na yi magana. Suka zaɓa su yi mini rashin biyayya, su kuma aikata mugunta.”

5 Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga ‘yan’uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba’a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya!

6 Ku kasa kunne! Waccan babbar hayaniya cikin birni, wancan amo a Haikali, amon Ubangiji ne da yake hukunta abokan gābansa!

7 “Tsattsarkan birnina yana kama da uwa wadda ta haifi ɗa, ba tare da naƙuda ba.

8 Ko akwai wanda ya taɓa gani ko ya ji labari irin wannan abu? Ko an taɓa haihuwar al’umma rana ɗaya? Sihiyona ba za ta sha wahala ba kafin a haifi al’umma.

9 Kada ku zaci zan kawo jama’ata a wurin haihuwa in kuma hana ta haihuwa.” Ubangiji ne ya faɗa.

10 Ku yi murna tare da Urushalima

Ku yi farin ciki tare da ita,

Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan!

Ku yi murna tare da ita yanzu,

Dukanku da kuka yi makoki dominta!

11 Za ku ji daɗin wadatarta,

Kamar yaro a ƙirjin mamarsa.

12 Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al’ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna.

13 Zan ta’azantar da ku a Urushalima, kamar yadda uwa take ta’azantar da ɗanta.

14 Sa’ad da kuka ga wannan ya faru, za ku yi murna, wannan zai ba ku ƙarfi da lafiya. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji, mai taimakon masu biyayya gare ni, ina kuwa nuna fushina a kan abokan gābana.”

15 Ubangiji zai zo da wuta. Zai hau a kan fikafikan hadiri, domin ya hukunta waɗanda yake fushi da su.

16 Zai hukunta dukan mutanen duniya da wuta da takobi, waɗanda ya same su da laifi, za su kuwa mutu.

17 Ubangiji ya ce, “Ƙarshe ya kusa ga waɗanda suka tsabtace kansu domin sujadar arna, suka kuma yi jerin gwano zuwa ɗakin tsafi a lambu, inda suka ci naman alade da na ɓera, da waɗansu abinci masu banƙyama.

18 Na san tunaninsu da ayyukansu. Ina zuwa domin in tattara jama’ar dukan al’ummai. Sa’ad da suka tattaru, za su ga abin da ikona zai yi,

19 su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu.

“Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al’ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al’ummai.

20 Za su taho da ‘yan ƙasarku daga al’ummai, su kawo mini su kyauta. Za su zo da su a tsattsarkan dutsena, wato Urushalima, za su kawo su a kan dawakai, da alfadarai, da raƙuma, da cikin karusai, kamar dai yadda Isra’ilawa suke kawo hadaya ta hatsi a Haikali cikin tsabtatattun ƙore.

21 Zan sa waɗansu su zama firistoci da Lawiyawa.”

22 Ubangiji ya ce, “Kamar yadda sabuwar duniya da sabon sararin sama za su tabbata ta wurin ikona, haka zuriyarku da sunanku za su tabbata.

23 A kowane bikin amaryar wata, da kowace ranar Asabar, jama’ar kowace al’umma za su zo su yi mini sujada a nan cikin Urushalima.

24 Sa’ad da suke tafiya, za su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa. Tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, wutar da take ƙona su kuma ba za ta taɓa mutuwa ba. Dukan mutane za su ji ƙyamarsu.”