Categories
JOSH

JOSH 1

Shirin da Aka Yi don Cin Ƙasar Kan’ana

1 Bayan rasuwar Musa, bawan Ubangiji, Ubangiji ya ce wa Joshuwa ɗan Nun, wanda ya yi wa Musa aiki,

2 “Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama’an nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra’ilawa.

3 Duk inda tafin sawunku ya taka na riga na ba ku, kamar yadda na alkawarta wa Musa.

4 Tun daga jejin, da Lebanon, har zuwa babban kogin, wato Kogin Yufiretis, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum wajen yamma, za ta zama ƙasarku.

5 Ba mutumin da zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Kamar yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai, ba zan kunyatar da kai ba, ba kuwa zan yashe ka ba.

6 Ka dāge, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka yi jagorar wannan jama’a su mallaki ƙasa wadda na rantse zan ba kakanninsu.

7 Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da haka nan za ka arzuta cikin dukan harkokinka.

8 Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.

9 Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”

10 Sai Joshuwa ya umarci shugabannin jama’a, ya ce,

11 “Ku shiga zango, ku umarci jama’a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”

12 Joshuwa kuma ya ce wa Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa,

13 “Ku tuna da maganar da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku da ita, ya ce, ‘Ubangiji Allahnku zai hutar da ku, zai kuma ba ku wannan ƙasa.’

14 Da matanku, da ‘yan ƙanananku, da dabbobinku, za su zauna a ƙasar da Musa ya ba ku a wannan hayin Urdun, amma jarumawanku su haye tare da ‘yan’uwanku da shirin yaƙi domin su taimake su,

15 har lokacin da Ubangiji ya hutar da ‘yan’uwanku kamarku, su kuma su mallaki ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba su, a sa’an nan za ku koma zuwa ƙasar da take mulkinku, ku mallake ta, wato ƙasar da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun wajen gabas.”

16 Su kuwa suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Iyakar abin da ka umarce mu za mu yi, duk inda ka aike mu kuma za mu tafi.

17 Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya a kowane abu haka nan za mu yi maka biyayya, Ubangiji Allahnka dai ya kasance tare da kai kamar yadda ya kasance tare da Musa.

18 Duk wanda ya ƙi bin umarninka, bai kuwa yi biyayya da maganarka da dukan irin abin da ka umarce shi ba, za a kashe shi. Kai dai ka dāge, ka yi ƙarfin hali.”

Categories
JOSH

JOSH 2

Joshuwa Ya Aiki ‘Yan Leken Asirin Ƙasa zuwa Yariko

1 Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu ‘yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, “Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko.” Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka.

2 Sai aka faɗa wa Sarkin Yariko, aka ce, “Ga waɗansu mutane sun shigo nan da daddare domin su bincike ƙasar.”

3 Sarkin Yariko kuwa ya aika wurin Rahab ya ce, “Fito da mutanen da suka zo wurinki, waɗanda suka shiga gidanki, gama sun zo ne domin su leƙi asirin ƙasar duka.”

4 Amma macen ta riga ta ɓoye mutanen nan biyu, sai ta ce, “Gaskiya ce, mutanen sun zo wurina, amma ban san ko daga ina suka zo ba,

5 da maraice kuma, sa’ad da za a rufe ƙofar garin, sai mutanen suka fita, inda suka tafi kuwa ban sani ba, ku bi su da sauri, gama za ku ci musu.”

6 Gama ta riga ta kai su bisa rufin ɗaki, ta rufe su da ƙasheshen rama waɗanda ta shimfiɗa a bisa rufin.

7 Mutanen kuwa suka tafi don su bi bayansu a hanyar Urdun har zuwa mashigai. Da fitar masu bin sawun, sai aka rufe ƙofar garin.

8 Amma kafin ‘yan leƙen asirin ƙasar su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin,

9 ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya ba ku ƙasar, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.

10 Gama mun ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Bahar Maliya ya ƙafe a gabanku a sa’ad da kuka fito daga Masar, da irin abin da kuka yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon da Og, waɗanda kuka hallakar da su sarai.

11 Da muka ji, sai zukatanmu suka narke, har ba sauran ƙarfin hali da ya ragu a kowane mutum saboda ku. Gama Ubangiji Allahnku shi ne Allahn da yake a Sama daga bisa, da duniya a ƙasa.

12 Yanzu fa, ku rantse mini da Ubangiji, kamar yadda na yi muku alheri, haka ku kuma za ku yi wa gidan mahaifina, ku ba ni tabbatacciyar alama.

13 Ku ceci mahaifina, da mahaifiyata, da ‘yan’uwana mata da maza, da dukan abin da yake nasu, ku ceci rayukanmu daga mutuwa.”

14 Mutanen kuwa suka ce mata, “Ranmu a bakin naki, idan ba ki tone al’amarinmu ba, za mu yi miki alheri da aminci sa’ad da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”

15 Sa’an nan ta zurarar da su da igiya ta taga, gama gidanta yana haɗe da garun birnin ne.

16 Sai ta ce musu, “Tafi cikin tsaunuka domin kada masu bin sawun su same ku, ku ɓuya a wurin kwana uku, har masu bin sawun su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”

17 Mutanen suka ce mata, “Za mu kuɓuta daga rantsuwarki wadda kika rantsar da mu.

18 A lokacin da za mu shigo ƙasar, sai ki ɗaura wannan jan kirtani a tagar da kika zurarar da mu, ki kuma kawo mahaifinki, da mahaifiyarki, da ‘yan’uwanki, da dukan iyalin gidan mahaifinki a gidanki.

19 Idan waninku ya fita daga ƙofar gidanki zuwa kan titi, to, alhakin jininsa yana bisa kansa, mu kuwa sai mu kuɓuta. Amma idan aka sa wa wani hannu wanda yake cikin gida tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.

20 Amma idan kika tone al’amarin nan namu, to za mu kuɓuta daga rantsuwar da kika rantsar da mu.”

21 Sai ta ce, “Bisa ga maganarku ya zama haka.” Sa’an nan ta sallame su, suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan kirtanin a tagar.

22 Sai suka tafi, suka shiga tsaunuka, suka yi zamansu a can kwana uku har masu bin sawun suka koma, gama masu bin sawun suka yi ta nema ko’ina a hanyar, amma ba su sami kowa ba.

23 Mutanen nan biyu suka sauko daga tsaunuka, suka haye zuwa wurin Joshuwa ɗan Nun, suka faɗa masa dukan abin da ya same su.

24 Suka kuma ce masa, “Hakika, Ubangiji ya ba da ƙasar duka a hannunmu, banda wannan kuma mazaunan ƙasar duka sun firgita saboda mu.”

Categories
JOSH

JOSH 3

Isra’ilawa Sun Haye Urdun

1 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama’ar Isra’ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye.

2 Bayan kwana uku sai shugabannin jama’a suka bibiya zango,

3 suna umartar jama’ar suna cewa, “Sa’ad da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi,

4 domin ku san hanyar da za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai tsakaninku da shi za ku bar rata misalin nisan kamu dubu biyu, kada ku kusace shi.”

5 Sai Joshuwa ya ce wa jama’a, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai aikata abin al’ajabi a tsakiyarku.”

6 Ya kuma ce wa firistocin, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku wuce gaban jama’ar.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban jama’a.

7 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra’ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai.

8 Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, ‘Sa’ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.’ ”

9 Joshuwa kuma ya ce wa Isra’ilawa, “Ku kusato ku ji zantuttukan Ubangiji Allahnku.”

10 Joshuwa kuma ya ƙara da cewa, “Ta haka za ku sani Allah mai rai yana tsakiyarku, ba makawa kuwa zai kori Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Hiwiyawa, da Ferizziyawa, da Girgashiyawa, da Amoriyawa, da Yebusiyawa a gabanku.

11 Ga shi, akwatin alkawari na Ubangijin dukkan duniya yana wucewa a gabanku zuwa cikin Urdun.

12 Yanzu fa, ku ɗauki mutum goma sha biyu daga kabilanku, wato mutum ɗaya daga kowace kabila.

13 A sa’ad da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangijin dukkan duniya, suka tsoma tafin sawunsu cikin ruwan Urdun, ruwan Urdun zai yanke, ruwan da yake gangarowa zai tsaya tsibi guda.”

14-15 (Da kaka Urdun yakan yi cikowa makil.) Jama’a fa, suka tashi daga alfarwansu don su haye Urdun. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suna gaba. Da firistocin suka tsoma ƙafafunsu cikin ruwa daga gefe,

16 sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru wuri ɗaya, ya yi soro daga nesa kusa da Adam, birnin da yake kusa da Zaretan. Ruwan kuma da yake gangarowa zuwa Tekun Araba, wato Tekun Gishiri, aka yanke shi ɗungum. Jama’a kuwa suka haye daura da Yariko.

17 A sa’ad da Isra’ilawa duka suna tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al’ummar ta gama hayewa.

Categories
JOSH

JOSH 4

Duwatsu Goma Sha Biyu da Aka Ɗauka Tsakiyar Urdun

1 Da al’umma duka suka gama haye Urdun, sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,

2 “Ɗauki mutum goma sha biyu daga cikin jama’a, wato mutum ɗaya na kowace kabila.

3 Ka umarce su su ɗauki duwatsu goma sha biyu daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, su haye da su, su ajiye su a masaukin da za su kwana yau.”

4 Sai Joshuwa ya kirawo mutum goma sha biyu waɗanda ya zaɓa daga cikin Isra’ilawa, mutum guda na kowace kabila.

5 Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra’ila.

6 Wannan zai zama alama a gare ku, don ya yiwu wata rana ‘ya’yanku za su tambaye ku, su ce, ‘Ina ma’anar waɗannan duwatsu a gare ku?’

7 Sa’an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa’ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra’ilawa har abada.”

8 Sai Isra’ilawa suka yi yadda Joshuwa ya umarta, suka ɗauki duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun bisa ga yawan kabilansu kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Joshuwa, suka haye da su zuwa inda suka sauka, a can suka ajiye su.

9 Joshuwa kuma ya kafa duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun, a wurin da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya, duwatsun suna nan har wa yau.

10 Gama firistocin da suke ɗauke da akwatin sun tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Joshuwa ya faɗa wa jama’a, da kuma bisa ga dukan abin da Musa ya umarce shi.

Mutanen kuwa suka gaggauta, suka haye.

11 Da jama’a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama’ar.

12 Mutanen Ra’ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da ‘yan’uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su.

13 Mutum wajen dubu arba’in ne (40,000), mayaƙa, suka haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa filayen Yariko.

14 A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Joshuwa a idon dukan Isra’ilawa, har suka ga kwarjininsa dukan kwanakin ransa kamar yadda suka ga na Musa.

15 Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa,

16 “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin shaida, su fito daga cikin Urdun.”

17 Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun.

18 Da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka fito daga tsakiyar Urdun, suka taka sandararriyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya malalo ya tumbatsa kamar dā.

19 Rana ta goma ga watan ɗaya jama’a suka haye Urdun, suka yi zango a Gilgal a gabashin iyakar Yariko.

20 Joshuwa ya kafa duwatsun nan goma sha biyu da suka ɗauko daga Urdun a Gilgal.

21 Sai ya ce wa Isra’ilawa, “Sa’ad da wata rana ‘ya’yanku suka tambayi ubanninsu ma’anar duwatsun nan,

22 sa’an nan za ku sanar da ‘ya’yanku cewa Isra’ilawa sun haye Urdun da ƙafa a kan sandararriyar ƙasa!

23 Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya ƙafe, har kuka haye kamar yadda Ubangiji Allahnku ya sa Bahar Maliya ta ƙafe har muka haye,

24 domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”

Categories
JOSH

JOSH 5

Yin Kaciya da Kiyaye Idin Ƙetarewa a Gilgal

1 Sa’ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan’aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra’ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra’ilawa.

2 A lokacin kuwa Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu, ka yi wa mazajen Isra’ila kaciya.”

3 Sai Joshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa mutanen kaciya a Gibeyat-ha’aralot, wato dutsen kaciya.

4-5 Dalilin da ya sa Joshuwa ya yi musu kaciya ke nan, domin dukan waɗanda aka haifa a hanya cikin jeji bayan fitowarsu daga Masar, ba a yi musu kaciya ba. Dukan mazajen da suka fito daga Masar waɗanda suka isa yaƙi sun rasu cikin jeji a hanyarsu. Waɗannan kuwa an yi musu kaciya kafin fitowarsu.

6 Gama shekara arba’in Isra’ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al’umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.

7 ‘Ya’yansu ne kuwa waɗanda Ubangiji ya tā da su a maimakonsu, su ne Joshuwa ya yi wa kaciya, gama ba su da kaciya, domin a hanya ba a yi musu ba.

8 Da aka gama yi wa al’ummar duka kaciya, sai suka zauna a zango har suka warke.

9 Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “A wannan rana na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka, har wa yau ake kiran sunan wurin Gilgal, wato a kawar.

10 Sa’ad da Isra’ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko.

11 A kashegarin idin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, waina marar yisti da busasshiyar tsaba.

12 Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, mannar ta yanke, mutanen Isra’ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan’ana.

Joshuwa da Mutumin da Yake Riƙe da Takobi

13 Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?”

14 Sai mutumin ya ce, “A’a, gama na zo ne kamar sarkin yaƙin rundunar Ubangiji.”

Sai Joshuwa ya sunkuyar da kansa, ya rusuna har ƙasa, ya yi sujada, ya ce masa, “Wace magana ce Ubangiji yake faɗa wa bawansa?”

15 Sarkin yaƙin rundunar Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Cire takalmanka da suke a ƙafafunka, gama wurin da kake tsaye tsattsarka ne.” Haka kuwa Joshuwa ya yi.

Categories
JOSH

JOSH 6

Faɗuwar Yariko

1 Aka rufe Yariko ciki da waje, ba mai fita, ba mai shiga saboda Isra’ilawa.

2 Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Duba, na ba da Yariko, da sarkinta, da jarumawanta a hannunka.

3 Kai da dukan mayaƙa za ku zagaya birnin sau ɗaya kowace rana har kwana shida.

4 Sai firistoci bakwai su riƙe ƙahonin raguna a gaban akwatin alkawari. Amma a rana ta bakwai za ku zaga birnin sau bakwai, firistoci su yi ta busar ƙahoni.

5 Sa’ad da suka tsawaita busar ƙahoni, sai dukan jama’a su yi ihu da babbar murya, garun birnin kuwa zai rushe tun daga tushensa. Sai mutane su haura, ko wanne ya nufi inda ya fuskanta sosai zuwa cikin birnin.”

6 Joshuwa ɗan Nun kuwa ya kirawo firistoci, ya ce musu, “Ɗauki akwatin alkawarin, sa’an nan firistoci bakwai su ɗauki ƙaho bakwai na raguna su wuce a gaban akwatin alkawarin Ubangiji.”

7 Ya kuma ce wa jama’a, “Ku wuce, ku zaga birnin, masu makamai kuma su wuce a gaban akwatin Ubangiji.”

8 Kamar yadda Joshuwa ya umarci jama’a, firistoci bakwai waɗanda suke riƙe da ƙaho bakwai na raguna a gaban Ubangiji suka wuce gaba, suna busawa, akwatin alkawari na Ubangiji yana biye da su.

9 Masu makamai kuwa suka wuce gaban firistocin da suke busa ƙahonin, ‘yan tsaron baya suna biye da akwati, ana ta busa ƙahoni.

10 Amma Joshuwa ya umarci mutane cewa, “Ba za ku yi ihu ba, ba kuwa za ku bari a ji muryarku, ko kuwa wata magana ta fito daga bakinku ba, sai ranar da na ce muku ku yi ihu, sa’an nan za ku yi ihu.”

11 Ya kuwa sa akwatin Ubangiji ya zaga birnin, aka zaga da shi sau ɗaya sa’an nan suka koma zango, suka kwana.

12 Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji.

13 Firistoci bakwai ɗin da suke riƙe da ƙahoni bakwai na raguna, suka wuce gaban akwatin Ubangiji suna ta busawa, masu makamai suna tafe a gabansu, ‘yan tsaron baya suna biye da akwatin Ubangiji, ana ta busa ƙahoni.

14 A rana ta biyu kuma suka zaga birnin sau ɗaya, sa’an nan suka koma zango. Haka suka yi ta yi har kwana shida.

15 A rana ta bakwai kuwa suka tashi da sassafe, suka yi sammako, suka zaga birnin yadda suka saba yi har sau bakwai. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai.

16 A zagawa ta bakwai, sa’ad da firistoci suka busa ƙahoni, sai Joshuwa ya ce wa jama’a, “Ku yi ihu, gama Ubangiji ya ba ku birnin.

17 Amma birnin da dukan abin da yake cikinsa haram ne ga Ubangiji, sai a hallaka su. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye ‘yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.

18 Amma sai ku tsare kanku daga abubuwan da aka haramta don a hallaka su. Kada ya zama bayan da kuka haramta su ku sāke ɗaukar wani abu daga cikinsu, har da za ku sa zangon Isra’ilawa ya zama abin hallakarwa, ku jawo masa masifa.

19 Amma dukan azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe keɓaɓɓu ne ga Ubangiji. Za a shigar da su cikin taskar masujadar Ubangiji.”

20 Jama’a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama’ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama’a kuwa suka shiga birnin, kowanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin.

21 Sa’an nan suka hallakar da dukan abin da yake a cikin birnin, da mata da maza, yara da tsofaffi, da shanu da tumaki, da jakai.

22 Sa’an nan Joshuwa ya ce wa mutum biyu ɗin nan da suka leƙo asirin ƙasar, “Tafi gidan karuwar, ku fitar da ita, da dukan waɗanda suke nata kamar yadda kuka rantse mata.”

23 Sai samarin da suka leƙo asirin ƙasar suka shiga, suka fito da Rahab, da mahaifinta, da mahaifiyarta, da ‘yan’uwanta, da dukan waɗanda suke nata, suka fito da dukan danginta, suka saukar da su a bayan zangon Isra’ilawa.

24 Suka ƙone birnin da wuta da dukan abin da yake a cikinsa, sai dai azurfa, da zinariya, da kwanonin tagulla, da na baƙin ƙarfe ne, suka ajiye a cikin taskar masujadar Ubangiji.

25 Amma Joshuwa ya bar Rahab da rai, da ita da iyalin mahaifinta, da dukan waɗanda suke nata. Rahab ta yi zamanta wurin Isra’ilawa har wa yau domin ta ɓoye manzannin da Joshuwa ya aika don su leƙo asirin Yariko.

26 A lokacin nan Joshuwa ya yi musu magana da rantsuwa ya ce,

“La’ananne ne mutum a gaban Ubangiji

Wanda ya tashi don ya sāke gina birnin nan Yariko.

A bakin ɗan farinsa zai kafa tushensa,

A bakin autansa kuma zai gina ƙofofinsa.”

27 Ubangiji yana tare da Joshuwa, ya kuwa yi suna cikin dukan ƙasar.

Categories
JOSH

JOSH 7

Zunubin Akan

1 Amma Isra’ilawa suka ci amana, gama Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza ya ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, Sai Ubangiji ya husata da Isra’ilawa.

2 Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai.

3 Da suka komo wurin Joshuwa, sai suka ce masa, “Kada dukan mutane su tafi, amma a bar mutum wajen dubu biyu ko uku su tafi su bugi Ai, kada a sa dukan mutane su sha wahalar zuwa can, domin su kima ne.”

4 Sai mutum wajen dubu uku daga cikin jama’a suka tafi, amma mutanen Ai suka kore su.

5 Mutanen Ai suka kashe mutum wajen talatin da shida daga cikin Isra’ilawa, suka runtume su tun daga ƙofar garin har zuwa Shebarim, suka yi ta karkashe su har zuwa gangaren. Zukatan mutanen Isra’ila kuwa suka narke, suka zama kamar ruwa.

6 Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra’ila, suka zuba ƙura a bisa kansu.

7 Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama’an nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun.

8 Ya Ubangiji, me zan ce bayan da Isra’ilawa sun ba da baya ga abokan gābansu?

9 Gama Kan’aniyawa da dukan mazaunan ƙasar za su ji labari, su kewaye mu, su shafe sunanmu daga duniya, to, me za ka yi don sunanka mai girma?”

10 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Tashi, don me ka fāɗi rubda ciki?

11 Isra’ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya.

12 Saboda haka Isra’ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku.

13 Tashi, ka tsarkake jama’a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra’ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku.

14 Da safe kuwa za a gabatar da ku kabila kabila, zai zama kuwa kabilar da Ubangiji ya ware, za a gabatar da ita iyali iyali, iyalin da Ubangiji ya ware kuma, za a gabatar da su gida gida, gidan kuma da Ubangiji ya ware, za a gabatar da su mutum mutum.

15 Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra’ila.’ ”

16 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra’ilawa kabila kabila, aka ware kabilar Yahuza.

17 Ya gabatar da iyalan Yahuza, aka ware iyalin Zera. Ya gabatar da iyalin Zera gida gida, aka ware gidan Zebdi.

18 Ya gabatar da iyalin gidansa mutum mutum, aka ware Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza.

19 Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.”

20 Akan kuwa ya amsa wa Joshuwa, ya ce, “A gaskiya kam, na yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila zunubi. Ga abin da na yi.

21 A cikin kayan ganimar na ga wata kyakkyawar alkyabba irin ta Shinar, da shekel dari biyu na azurfa, da sandan zinariya mai nauyin shekel hamsin, sai na yi ƙyashi, na kwashe su, ga su a binne a ƙasa a alfarwata da azurfa a ƙarƙashi.”

22 Joshuwa ya aika da manzanni, suka sheƙa a guje zuwa alfarwar, suka tarar da abubuwan a binne cikin alfarwarsa da azurfa a ƙarƙashi.

23 Sai suka kwaso suka kawo wa Joshuwa da dukan Isra’ilawa, suka ajiye su a gaban Ubangiji.

24 Joshuwa kuwa tare da dukan Isra’ilawa suka ɗauki Akan, ɗan Zera, da azurfar, da alkyabbar, da sandan zinariya, da ‘ya’yansa mata da maza, da shanunsa, da jakunansa, da tumakinsa, da alfarwarsa, da dukan abin da yake da shi, suka kawo su a Kwarin Akor.

25 Sai Joshuwa ya ce, “Don me ka wahalshe mu? Kai ma, Ubangiji zai wahalshe ka yau!” Dukan Isra’ilawa suka jajjefe su da duwatsu, suka ƙone su da wuta.

26 Suka tara tsibin duwatsu a kansu. Tsibin duwatsun kuwa yana nan har wa yau. Sa’an nan Ubangiji ya huce daga zafin fushinsa. Domin haka ana kiran wurin Kwarin Akor, wato azaba, har wa yau.

Categories
JOSH

JOSH 8

An Ci Ai da Yaƙi

1 Ubangiji kuma ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoro ko ka firgita. Ka ɗauki mayaƙa duka, ka tashi, ka tafi Ai. Ga shi, na riga na ba da Sarkin Ai da mutanensa, da birninsa, da ƙasarsa a hannunka.

2 Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yariko da sarkinta, sai dai ganima da dabbobinta ne za ku washe domin kanku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”

3 Joshuwa kuwa tare da dukan mayaƙa suka yi shirin tashi zuwa Ai. Sai Joshuwa ya zaɓi jarumawa ƙarfafa dubu talatin (30,000), ya aike su da dad dare.

4 Ya umarce su, ya ce, “Ku tafi, ku yi kwanto a bayan birnin, kada ku yi nisa da birni da yawa, amma dukanku ku kasance da shiri sosai.

5 Da ni da dukan mutanen da suke tare da ni za mu je kusa da birnin. Sa’ad da za su fito don su yi karo da mu kamar dā, za mu gudu daga gare su.

6 Za su kuwa fito su bi mu. Mu kuwa za mu janye su nesa da birnin, gama za su ce, ‘Suna gudunmu kamar dā.’ Haka fa, za mu gudu daga gare su.

7 Ku kuwa ku tashi daga kwanto, ku ci birnin, gama Ubangiji Allahnku zai ba da shi a hannunku.

8 A sa’ad da kuka ci birnin, ku sa wa birnin wuta yadda Ubangiji ya ce. Ku lura fa, da abin da na umarce ku.”

9 Sai Joshuwa ya sallame su, suka tafi inda za su yi kwanto. Suka yi fako tsakanin Betel da Ai, yamma da Ai, amma shi ya kwana tare da jama’a.

10 Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe ya tattara mutanen, ya tafi tare da shugabannin Isra’ilawa, suka wuce gaba, suka bi da mutane zuwa Ai.

11 Dukan mayaƙan da suke tare da shi, suka tafi kusa da birnin, suka kafa sansaninsu arewacin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari.

12 Ya kuma zaɓi mutum wajen dubu biyar (5,000) ya sa su yi kwanto tsakanin Betel da Ai, yamma da birnin.

13 Mutanensu suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na ‘yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Joshuwa ya kwana a kwarin.

14 A sa’ad da Sarkin Ai ya ga wannan, shi da mutanensa duka, wato mutanen birnin, suka gaggauta, suka tafi da sassafe zuwa gangaren wajen Araba don su gabza yaƙi da Isra’ilawa, amma bai san akwai ‘yan kwanto a bayan birnin ba.

15 Sai Joshuwa da mutanensa duka suka nuna kamar an rinjaye su, suka yi ta gudu, suka nufi jeji.

16 Saboda haka aka kira dukan mutanen da suke cikin birnin, su fafare su. Da suka fafari Joshuwa, sai aka janye su nesa da birnin.

17 Ba namijin da ya ragu cikin Ai da bai fita ya fafari Isra’ilawa ba, suka bar birnin a buɗe, suka fafari Isra’ilawa.

18 Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Ka miƙa mashin da yake hannunka wajen Ai, gama zan ba da ita a hannunka.” Sai Joshuwa ya miƙa mashin da yake hannunsa wajen birnin. Nan da nan da ya ɗaga hannunsa

19 ‘yan kwanto suka tashi da sauri daga maɓoyansu, suka shiga birnin, suka ci shi, suka yi sauri, suka cuna wa birnin wuta.

20 Da mutanen Ai suka waiga, sai ga hayaƙin birnin ya murtuke zuwa sama, suka rasa ikon da za su gudu gaba ko baya, gama mutanen da suka gudu zuwa jeji, sun juyo kan masu fafararsu.

21 Sa’ad da Joshuwa da dukan Isra’ilawa suka ga ‘yan kwanto sun ci birnin, da kuma hayaƙi ya murtuke bisa, suka juya kan mutanen Ai, suka ɗibge su.

22 Sauran Isra’ilawa kuwa suka fito daga cikin birnin suka fāɗa musu. Har ya zama suna tsakiyar Isra’ilawa gaba da baya. Isra’ilawa suka karkashe su, har ba wanda ya tsira ko ya tsere.

23 Amma suka kama Sarkin Ai da rai, suka kai shi wurin Joshuwa.

24 Sa’ad da Isra’ilawa suka gama karkashe mazaunan Ai duka a jeji inda suka fafare su, sai Isra’ilawa suka koma Ai, suka karkashe waɗanda suke cikinta.

25 A wannan rana aka ƙarasa mutanen Ai duka, mata da maza. Jimillarsu ta kai mutum dubu goma sha biyu (12,000).

26 Joshuwa bai janye hannunsa da riƙon mashin ba, sai da ya hallaka mazaunan Ai sarai.

27 Dabbobi da kayayyaki na birnin kaɗai Isra’ilawa suka kwashe ganima bisa ga faɗar Ubangiji zuwa ga Joshuwa.

28 Haka fa Joshuwa ya ƙone Ai, ya maishe ta tsibin kufai har abada. Tana nan haka har wa yau.

29 Ya rataye Sarkin Ai a bisa itace har maraice. Sa’ad da rana take faɗuwa Joshuwa ya umarta su ɗauke gawarsa daga itacen, su jefa a ƙofar birnin, su tsiba duwatsu da yawa a kanta. Tsibin duwatsun yana nan har wa yau.

An Karanta Albarka da La’ana a Dutsen Ebal

30 Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra’ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal.

31 Ya gina shi kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarci Isra’ilawa, gama haka aka rubuta cikin Attaura ta Musa, aka ce, “Bagaden da aka yi da duwatsun da ba a sassaƙa ba, waɗanda ba mutumin da ya taɓa sa musu guduma.” A bisansa suka miƙa hadayu ta ƙonawa ga Ubangiji, da hadayu na salama.

32 A nan, a idon Isra’ilawa, Joshuwa ya kafa dokokin Musa a bisa duwatsun.

33 Sai Isra’ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama’ar Isra’ila albarka.

34 Bayan haka ya karanta dukan zantuttukan shari’a, da na albarka da na la’ana, bisa ga dukan abin da aka rubuta cikin Attaura.

35 Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra’ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.

Categories
JOSH

JOSH 9

Munafuncin Gibeyonawa

1 Sa’ad da dukan sarakunan da suke hayin Urdun, na cikin ƙasar tuddai, da na ƙasar kwari a gefen Bahar Rum har zuwa Lebanon, wato sarakunan Hittiyawa, da na Amoriyawa, da na Kan’aniyawa, da na Ferizziyawa, da na Hiwiyawa, da na Yebusiyawa, suka ji wannan labari,

2 sai suka tattaru, suka haɗa kansu domin su yaƙi Joshuwa da Isra’ilawa.

3 Amma da mazaunan Gibeyon suka ji abin da Joshuwa ya yi wa Yariko da Ai,

4 sai suka yi musu hila, suka shirya guzuri, suka ɗauki tsofaffin buhuna a kan jakunansu da tsofaffin salkuna na ruwan inabi, yagaggu, sun kuwa sha ɗinki.

5 Suka kuma sa tsofaffin takalma waɗanda suka sha gyara, da tsofaffin tufafi. Dukan guzurinsu ya bushe, ya yi fumfuna.

6 Suka tafi wurin Joshuwa da Isra’ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”

7 Amma Isra’ilawa suka ce wa Hiwiyawa, “Watakila kuna zaune a tsakiyarmu ne, to, ƙaƙa za mu yi muku alkawari?”

8 Su kuwa suka ce wa Joshuwa, “Mu bayinka ne.”

Joshuwa kuwa ya ce musu, “Su wane ne ku? Daga ina kuka zo kuma?”

9 Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar,

10 da dukan abin da ya yi wa sarakunan nan biyu na Amoriyawa waɗanda suke a hayin Urdun, wato Sihon, Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake a Ashtarot.

11 Dattawanmu da dukan mazaunan ƙasarmu suka ce mana mu ɗauki guzuri a hannunmu don tafiya, mu tafi taryarku, mu ce muku, ‘Mu bayinku ne, yanzu dai sai ku yi mana alkawari.’

12 Wannan abinci, da ɗuminsa muka ɗauko shi daga gidajenmu a ranar da muka fito zuwa gare ku, amma ga shi, yanzu ya bushe ya yi fumfuna.

13 Waɗannan salkunan ruwan inabi kuma da muka cika sababbi ne, amma ga shi, sun kyakkece, waɗannan tufafinmu kuma da takalmanmu sun tsufa saboda tsawon hanya!”

14 Sai Isra’ilawa suka ɗiba daga cikin guzurin Hiwiyawa, amma ba su nemi shawara wurin Ubangiji ba.

15 Joshuwa kuwa ya yi amana da su, ya yi musu alkawari zai bar su da rai. Shugabannin jama’a kuma suka rantse musu.

16 Amma a rana ta uku bayan da suka yi alkawari da su, suka ji cewa, su maƙwabtansu ne, suna zaune a cikinsu.

17 Sai Isra’ilawa suka kama hanyarsu a rana ta uku suka isa biranen mutanen, wato Gibeyon, da Kefira, da Biyerot, da Kiriyat-yeyarim.

18 Amma Isra’ilawa ba su kashe su ba, domin shugabannin jama’a sun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra’ila. Dukan jama’a kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.

19 Amma shugabanni suka ce wa dukan jama’a, “Mun riga mun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra’ila, don haka yanzu ba shi yiwuwa mu taɓa su.

20 Abin da za mu yi musu ke nan, a bar su da rai saboda rantsuwar da muka rantse musu don kada mu jawo wa kanmu fushin Ubangiji!”

21 Suka ƙara da cewa, “A bar su da rai domin su zama masu sarar mana itace, da masu ɗebo mana ruwa.”

22 Joshuwa kuwa ya kirawo su, ya ce musu, “Me ya sa kuka ruɗe mu da cewa, ‘Muna nesa da ku ƙwarai,’ ga shi kuwa, a tsakiyarmu kuke zaune?

23 Yanzu fa ku la’anannu ne, a cikinku ba za a rasa bayin da za su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin masujadar Allahnmu ba.”

24 Sai suka amsa wa Joshuwa, suka ce, “Domin bayinka sun ji labari Ubangiji Allahnka ya umarci bawansa Musa ya ba ku ƙasar duka, ku hallaka dukan mazaunan ƙasar a gabanku, don haka muka ji tsoronku ƙwarai saboda rayukanmu, shi ya sa muka yi haka.

25 Yanzu dai muna a hannunka, ka yi yadda ka ga ya yi maka kyau.”

26 Haka kuwa ya yi musu, ya cece su daga hannun Isra’ilawa, har ba su kashe su ba.

27 Amma Joshuwa ya sa su su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama’a da bagaden Ubangiji. Zai zama aikinsu na yau da kullum a wurin da Ubangiji zai zaɓa.

Categories
JOSH

JOSH 10

An Ci Amoriyawa da Yaƙi

1 Da Adonizedek, Sarkin Urushalima, ya ji yadda Joshuwa ya ci Ai, har ya hallakar da ita sarai kamar yadda ya yi wa Yariko da sarkinta, da kuma yadda mazaunan Gibeyon suka yi amana da Isra’ilawa, har suna zama cikinsu.

2 sai ya tsorata ƙwarai, gama Gibeyon babban birni ce kamar ɗaya daga cikin alkaryai, har ma ta fi Ai girma, mazajenta duka kuwa ƙarfafa ne.

3 Adonizedek Sarkin Urushalima, ya aika zuwa ga Hoham Sarkin Hebron, da Firam Sarkin Yarmut, da Yafiya Sarkin Lakish, da Debir Sarkin Eglon, ya ce,

4 “Ku zo, ku taimake ni, mu yaƙi Gibeyon, gama ta yi amana da Joshuwa da Isra’ilawa.”

5 Sarakunan nan biyar na Amoriyawa, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon, suka tattaru da dukan rundunansu, suka haura, suka kafa wa Gibeyon sansani don su yaƙe ta.

6 Gibeyonawa dai suka aika zuwa wurin Joshuwa a zango cikin Gilgal cewa, “Kada ka yar da bayinka. Ka zo wurinmu da sauri, ka cece mu, ka taimake mu, gama dukan sarakunan Amoriyawa da suke zaune a ƙasar tuddai sun tattaru a kanmu.”

7 Sai Joshuwa ya tashi daga Gilgal da dukan mayaƙa, da dukan jarumawa tare da shi.

8 Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.”

9 Sai Joshuwa ya tafi ya auka musu ba labari, gama daga Gilgal ya bi dare zuwa can.

10 Ubangiji kuwa ya sa suka gigice a gaban Isra’ilawa. Isra’ilawa suka kashe su da yawa a Gibeyon, suka runtume su ta hanyar haurawa zuwa Bet-horon. Suka yi ta karkashe su har zuwa Azeka da Makkeda.

11 Sa’ad da suke gudun Isra’ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.

12 Sa’an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra’ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce,

“Ke rana, ki tsaya a Gibeyon,

Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.”

13 Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya,

Har al’ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābansu.

Ai, wannan a rubuce yake a littafin Yashar. Rana dai ta tsaya a tsaka, ta yi jinkirin faɗuwa da misalin yini guda.

14 Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.

15 Sa’an nan Joshuwa ya koma zango a Gilgal tare da dukan Isra’ilawa.

16 Waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda.

17 Aka faɗa wa Joshuwa cewa, “An sami sarakunan nan biyar, sun ɓuya a kogo a Makkeda.”

18 Sai Joshuwa ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu, ku rufe bakin kogon, sa’an nan ku sa mutane su yi tsaronsu.

19 Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a hannunku.”

20 Joshuwa da jama’ar Isra’ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu.

21 Sa’an nan dukan mutane suka koma wurin Joshuwa a sansani a Makkeda lafiya. Ba kuma mutumin da ya tsokani Isra’ilawa.

22 Sa’an nan Joshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon, ku kawo mini waɗannan sarakuna biyar da suke a kogon.”

23 Suka yi haka nan, suka kawo masa sarakunan nan biyar daga cikin kogon, wato Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron, da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish, da Sarkin Eglon.

24 Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra’ilawa, sa’an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.

25 Sai Joshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, gama haka Ubangiji zai yi da dukan abokan gābanku waɗanda za ku yi yaƙi da su.”

26 Sa’an nan Joshuwa ya buga su, ya kashe su, ya kuma rataye kowane ɗayansu a bisa itace. Suka yini a rataye har maraice.

27 Amma sa’ad da rana take faɗuwa, Joshuwa ya umarta, aka saukar da gawawwakinsu daga bisa itatuwan, aka jefa su cikin kogon inda suka ɓuya. Sa’an nan suka rufe bakin kogon da manyan duwatsu. Har wa yau suna nan.

28 A wannan rana kuwa Joshuwa ya ci Makkeda da yaƙi, ya kashe mutanenta da sarkinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Ya yi wa Sarkin Makkeda kamar yadda ya yi wa Sarkin Yariko.

29 Joshuwa ya zarce, da shi da dukan Isra’ilawa zuwa Libna, suka yi yaƙi da Libna.

30 Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra’ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.

31 Joshuwa kuma ya zarce daga Libna, da shi da Isra’ilawa duka , zuwa Lakish, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.

32 Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa suka cinye ta da yaƙi cikin kwana biyu. Suka bugi kowane mutum da yake cikinta da takobi kamar yadda suka yi wa Libna.

33 Horam, Sarkin Gezer kuwa, ya kawo wa Lakish gudunmawa, Joshuwa kuwa ya buge shi tare da mutanensa, har ba wanda ya ragu.

34 Joshuwa kuma ya zarce tare da dukan Isra’ilawa daga Lakish zuwa Eglon, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.

35 A ran nan suka cinye ta, suka buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi. Ya hallakar da su a wannan rana kamar yadda ya yi wa Lakish.

36 Joshuwa kuma ya haura tare da dukan Isra’ilawa daga Eglon zuwa Hebron, suka auka mata.

37 Suka cinye ta, suka buge ta, da sarkinta, da garuruwanta, da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.

38 Sai Joshuwa ya juya tare da dukan Isra’ilawa zuwa Debir, ya auka mata.

39 Ya cinye ta da yaƙi, da sarkinta, da garuruwanta. Ya buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Kamar yadda ya yi wa Hebron, da Libna da sarkinta, haka kuma ya yi wa Debir da sarkinta.

40 Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarta.

41 Joshuwa kuma ya cinye su da yaƙi tun daga Kadesh-barneya har zuwa Gaza, da dukan ƙasar Goshen har zuwa Gibeyon.

42 Joshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya, gama Ubangiji Allah na Isra’ila ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.

43 Sa’an nan Joshuwa ya komo tare da dukan Isra’ilawa zuwa zango a Gilgal.