Categories
JOSH

JOSH 11

An Ci Yabin da Magoya Bayansa

1 Sa’ad da Yabin Sarkin Hazor ya ji labari, ya aika wa Yobab, Sarkin Madon, da Sarkin Shimron, da Sarkin Akshaf,

2 da sarakunan da suke arewacin ƙasar tuddai, da cikin Araba a kudancin Kinneret, da cikin filayen kwari, da cikin Dor a yamma.

3 Ya kuma aika zuwa ga Kan’aniyawan da suke gabas da yamma, da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke ƙasar tuddai, da Hiwiyawa da suke zaune a gindin Dutsen Harmon a ƙasar Mizfa.

4 Sai suka fita tare da dukan mayaƙansu, babbar runduna mai yawa kamar yashi a bakin teku, da dawakai, da karusai da yawa ƙwarai.

5 Da sarakunan nan duka suka haɗa ƙarfinsu, sai suka je suka kafa sansaninsu a wuri ɗaya a bakin ruwayen Merom domin su yi yaƙi da Isra’ilawa.

6 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, gama gobe war haka zan ba da su ga Isra’ilawa, su karkashe su duka. Za ku daddatse agaran dawakansu, ku kuma ƙone karusansu.”

7 Sai Joshuwa, tare da dukan mayaƙansa, suka je suka mame su, suka auka musu a bakin ruwayen Merom.

8 Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra’ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf.

9 Joshuwa kuwa ya yi musu kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, ya daddatse agaran dawakansu, ya kuma ƙone karusansu.

10 A wannan lokaci Joshuwa ya koma da baya ya ci Hazor, ya kashe sarkinta da takobi, gama a lokacin Hazor ita ce masarautar mulkokin nan.

11 Suka kashe dukan waɗanda suke cikinta da takobi, suka hallakar da su ƙaƙaf, ba wanda ya ragu. Joshuwa kuwa ya ƙone Hazor.

12 Joshuwa kuma ya ci dukan biranen sarakunan nan, da dukan sarakunansu. Ya kashe su da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.

13 Amma mutanen Isra’ila ba su ƙone ko ɗaya daga cikin biranen da suke bisa tuddai ba, sai Hazor kaɗai Joshuwa ya ƙone.

14 Isra’ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba.

15 Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.

Joshuwa Ya Cinye Ƙasar Duka

16 Ta haka kuwa Joshuwa ya ci ƙasan nan duka, da ƙasar tuddai, da Negeb duka, da dukan ƙasar Goshen, da filayen kwari, da Araba, da ƙasar tuddai ta Isra’ila da filayen kwarinta,

17 tun daga Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa wajen Seyir, har zuwa Ba’al-gad a kwarin Lebanon, a gindin Dutsen Harmon. Ya kama sarakunan wuraren nan, ya buge su ya kashe su.

18 Joshuwa ya daɗe yana yaƙi da su.

19 Ba wani birnin da ya yi amana da Isra’ilawa, sai dai Hiwiyawa da suke zaune a Gibeyon. Saura duka kuwa, an ci su da yaƙi.

20 Gama Ubangiji ne ya taurara zukatansu har da za su tasar wa Isra’ilawa da yaƙi don a hallaka su, a shafe su ba tausayi, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

21 A wannan lokaci kuwa Joshuwa ya tafi ya hallaka Anakawa, wato gwarzayen nan da suke ƙasar tuddai, da Hebron, da Debir, da Anab, da dukan ƙasar tuddai ta Yahuza, da dukan ƙasar tuddai ta Isra’ilawa. Joshuwa ya hallaka su sarai duk da biranensu.

22 Babu wani gwarzon da ya ragu a ƙasar mutanen Isra’ila, sai a Gaza, da Gat, da Ashdod kaɗai ne waɗansunsu suka ragu.

23 Haka nan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra’ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.

Categories
JOSH

JOSH 12

Sarakunan da Musa Ya Ci da Yaƙi

1 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra’ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas,

2 Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda yake zaune a Heshbon, wanda yake mulki tun daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa Kogin Yabbok a iyakar Ammonawa,

3 daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga,

4 da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai.

5 Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma’akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon.

6 Sai Musa, bawan Ubangiji, da Isra’ilawa suka ci sarakunan nan da yaƙi, sa’an nan ya ba da ƙasarsu ga Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa.

Sarakunan da Joshuwa Ya Ci da Yaƙi

7 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Joshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammacin Kogin Urdun tun daga Ba’al-gad a kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙa zuwa Seyir. Joshuwa ya ba Isra’ilawa ƙasar gādo bisa ga yadda aka karkasa musu,

8 da ƙasar tuddai, da filayen kwaruruka, da kwarin Araba, da gangaren tuddai, da jejin, da Negeb, wato su Hittiyawa, da Amoriyawa, da Kan’aniyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

9 Sunayen sarakunan su ne, Sarkin Yariko, da Sarkin Ai, da yake kusa da Betel,

10 da Sarkin Urushalima, da Sarkin Hebron,

11 da Sarkin Yarmut, da Sarkin Lakish,

12 da Sarkin Eglon, da Sarkin Gezer,

13 da Sarkin Debir, da Sarkin Geder,

14 da Sarkin Horma, da Sarkin Arad,

15 da Sarkin Libna, da Sarkin Adullam,

16 da Sarkin Makkeda, da Sarkin Betel,

17 da Sarkin Taffuwa, da Sarkin Hefer,

18 da Sarkin Afek, da Sarkin Lasharon,

19 da Sarkin Madon, da Sarkin Hazor,

20 da Sarkin Shimron-meron, da Sarkin Akshaf,

21 da Sarkin Ta’anak, da Sarkin Magiddo,

22 da Sarkin Kedesh, da Sarkin Yakneyam a Karmel,

23 da Sarkin Dor a bakin teku, da Sarkin Goyim na Gilgal,

24 da Sarkin Tirza. Sarakuna talatin da ɗaya ke nan.

Categories
JOSH

JOSH 13

Ƙasar da Ta Ragu da Za A Mallaka

1 Yanzu Joshuwa ya tsufa ƙwarai, sai Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi, ƙasar da za ku mallaka ta ragu da yawa.

2 Wannan ita ce ƙasar da ta ragu, dukan ƙasar Filistiyawa, da ta Geshuriyawa,

3 daga Shihor da yake gabas da Masar zuwa iyakar Ekron a wajen arewa. Wannan ƙasa ta Kan’aniyawa ce. Akwai ƙasar sarakuna biyar na Filistiyawa da yake a Gaza, da Ashdod, da Ashkelon, da Gat, da Ekron, da ƙasar Awwiyawa,

4 da dukan ƙasar Kan’aniyawa a wajen kudu, da Meyara ta Sidoniyawa, zuwa Afek, har zuwa iyakar Amoriyawa,

5 da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat,

6 da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama’ar Isra’ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.

7 Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”

Yankin Ƙasar da Aka Ba Manassa da Ra’ubainu da Gad

8 Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan,

9 daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon,

10 da dukan biranen Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, har zuwa iyakar Amoriyawa,

11 da Gileyad, da yankin ƙasar Geshuriyawa, da Ma’akatiyawa, da dukan Dutsen Harmon, da dukan Bashan, zuwa Salka,

12 da dukan mulkin Og a Bashan, wanda ya yi sarautar Ashtarot da Edirai (Og Kaɗai ne aka bari daga cikin Refayawa). Waɗannan su ne Musa ya ci da yaƙi, ya kore su.

13 Duk da haka jama’ar Isra’ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma’akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra’ilawa har wa yau.

14 Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra’ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.

15 Musa ya riga ya ba Ra’ubainawa nasu gādo bisa ga iyalansu.

16 Nasu yankin ƙasar ya miƙa daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon, da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba,

17 da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba’al, da Ba’al-mayon,

18 da Yahaza, da Kedemot, da Mefayat,

19 da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin,

20 da Bet-feyor, da gangaren Fisga, da Betyeshimot.

21 Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.

22 Jama’ar Isra’ila kuma suka kashe Bal’amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi.

23 Urdun kuwa ya zama iyakar yankin ƙasar jama’ar Ra’ubainu. Wannan shi ne gādon Ra’ubainawa bisa ga iyalansu, da biranensu da ƙauyukansu.

24 Musa kuma ya ba Gadawa gādo bisa ga iyalansu.

25 Yankin ƙasarsu shi ne Yazar, da dukan biranen Gileyad da rabin ƙasar Ammonawa zuwa Arower wadda take gabas da Rabba,

26 daga Heshbon zuwa Ramat-mizfe, da Betonim, daga Mahanayim zuwa karkarar Debir,

27 da a kwarin Ber-aram, da Betnimra, da Sukkot, da Zafon, da kuma ragowar mulkin Sihon, Sarkin Heshbon. Kogin Urdun ne iyakar yankin ƙasarsu har zuwa wutsiyar Tekun Kinneret, a gabashin hayin Urdun.

28 Wannan shi ne yankin ƙasar, haɗe da garuruwa, da ƙauyuka, da aka ba mutanen kabilar Gad bisa ga iyalansu.

29 Musa kuma ya ba rabin jama’ar Manassa rabon gādo bisa ga iyalansu.

30 Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,

31 da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu.

32 Waɗannan su ne rabon gādon da Musa ya yi lokacin da suke cikin filayen Mowab a hayin gabashin Urdun daura da Yariko.

33 Amma Musa bai ba Lawiyawa gādon yankin ƙasa ba. Ya faɗa musu Ubangiji Allah na Isra’ila, shi ne rabon gādonsu.

Categories
JOSH

JOSH 14

An Rarraba Ƙasar Kan’ana ta Hanyar Kuri’a

1 Waɗannan su ne karkasuwar gādon da Isra’ilawa suka karɓa a ƙasar Kan’ana, wanda Ele’azara, firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin iyalan kabilan Isra’ila suka ba su.

2 Kabilan nan tara da rabi sun karɓi nasu rabon gādo ta hanyar jefa kuri’a, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

3 Gama Musa ya riga ya ba kabilan nan biyu da rabi nasu gādo a wancan hayin Kogin Urdun wajen gabas, amma bai ba Lawiyawa rabon gādo ba.

4 Jama’ar Yusufu kuwa kabila biyu ce, wato Manassa da Ifraimu. Ba a kuma ba Lawiyawa rabon gādo a ƙasar ba, sai dai an ba su biranen da za su zauna, da filayen da za su yi kiwon garkensu.

5 Jama’ar Isra’ila fa suka yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, suka rarraba ƙasar ta hanyar kuri’a.

An Ba Kalibu Hebron

6 Mutanen Yahuza suka je wurin Joshuwa a Gilgal, sa’an nan Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, ya ce masa, “Ka dai san maganar da Ubangiji ya yi wa Musa, mutumin Allah, a Kadesh-barneya a kaina.

7 Ina da shekara arba’in sa’ad da Musa bawan Ubangiji ya aike ni daga Kadesh-barneya don in leƙi asirin ƙasar. Na kuma kawo masa ainihin rahoton yadda yake a zuciyata.

8 Amma ‘yan’uwana da muka tafi tare, sun karya zukatan jama’ar, amma ni na bi Ubangiji Allahna da aminci.

9 Musa kuwa ya rantse a wannan rana ya ce, ‘Hakika duk inda ƙafafunka suka taka a ƙasan nan zai zama gādonka, kai da ‘ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahnka sosai!’

10 Ga shi kuwa, Ubangiji ya kiyaye ni har wa yau, kamar yadda ya faɗa, shekara arba’in da biyar ke nan, tun lokacin da Ubangiji ya faɗa wa Musa wannan magana, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a jeji. Ga shi yau ni mai shekara tamanin da biyar ne.

11 Ga shi kuwa, har wa yau ina da ƙarfi kamar ran da Musa ya aike ni. Kamar yadda ƙarfina yake a dā, haka yake a yanzu domin yaƙi, da kuma kai da kawowa.

12 Saboda haka sai ka ba ni ƙasar tuddai da Ubangiji ya ambata a ranan nan, gama a wannan rana ka ji yadda gwarzaye suke a can da manyan birane masu garu, mai yiwuwa ne Ubangiji zai kasance tare da ni, in kore su kamar yadda Ubangiji ya faɗa.”

13 Joshuwa ya sa wa Kalibu, ɗan Yefunne, albarka. Ya ba shi Hebron ta zama gādonsa.

14 Domin haka Hebron ta zama gādon Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, har wa yau, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra’ila sosai.

15 A dā sunan Hebron Kiriyat-arba ne. Arba kuwa babban mutum ne cikin gwarzayen. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.

Categories
JOSH

JOSH 15

Yankin Ƙasar da Aka Ba Yahuza

1 Rabon da aka ba jama’ar Yahuza bisa ga iyalansu ya yi kudu, a iyakar Edom zuwa jejin Zin, can kudu nesa.

2 Iyakarsu wajen kudu ta miƙa tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga wajen gaɓar da ta fuskanci kudu.

3 Ta milla kudanci hawan Akrabbim, ta zarce zuwa Zin, ta haura kudu da Kadesh-barneya, ta wajen Hesruna har zuwa Addar. Sai ta karkata zuwa Karka.

4 Ta zarce zuwa Azemon, ta bi ta rafin Masar zuwa inda ya gangara a teku. Wannan ita ce iyakar mutanen Yahuza wajen kudu.

5 Iyakarsu wajen gabas ta kama daga Tekun Gishiri zuwa bakin Urdun. Wajen arewa kuwa ta miƙa daga bakin teku a inda Kogin Urdun ya gangara a tekun.

6 Iyakar ta bi zuwa Bet-hogla, ta zarce zuwa arewa da Bet-araba, ta haura zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra’ubainu.

7 Daga kwarin Akor ta wuce zuwa Debir ta yi wajen arewa, sa’an nan ta juya zuwa Gilgal wadda take daura da hawan Adummim wanda yake kudancin gefen kwarin. Sai ta zarce zuwa ruwan En-shemesh, ta ƙare a En-rogel.

8 Daga nan iyakar ta bi ta kwarin ɗan Hinnom a wajen kudancin kafaɗar Yebus, wato Urushalima. Ta kuwa bi ta dutsen da yake shimfiɗe daura da kwarin Hinnom wajen yamma, a arewacin ƙarshen kwarin Refayawa.

9 Ta kuma milla daga kan dutsen zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa, daga can zuwa biranen Dutsen Efron. Daga can kuma ta karkata zuwa Ba’ala, wato Kiriyat-yeyarim.

10 Ta kuma kewaye kudancin Ba’ala zuwa Dutsen Seyir. Ta zarce zuwa arewacin kafaɗar Dutsen Yeyarim, wato Kesalon. Daga nan ta gangara zuwa Bet-shemesh, ta kuma wuce zuwa Timna.

11 Iyakar kuma ta biya wajen kafaɗar tudun, arewa da Ekron, sa’an nan ta karkata zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba’ala, ta tafi zuwa Yabneyel, sa’an nan ta gangara a teku.

12 Bakin Bahar Rum, ita ce iyaka a wajen yamma. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama’ar Yahuza bisa ga iyalansu.

Kalibu Ya Ci Hebron da Debir da Yaƙi

13 Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama’ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyat-arba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak.

14 Daga can sai Kalibu ya kori ‘ya’yan Anak, maza, su uku, da Sheshai, da Ahiman, da Talmai, zuriyar Anak.

15 Daga can kuma ya tafi ya fāɗa wa mazaunan Debir, dā sunan Debir Kiriyat-sefer ne.

16 Kalibu ya ce, “Duk wanda ya bugi Kiriyat-sefer, har ya ci ta, zan ba shi ‘yata Aksa aure.”

17 Otniyel kuwa, ɗan Kenaz, ɗan’uwan Kalibu, ya ci Kiriyat-sefer. Kalibu kuwa ya ba shi Aksa ‘yarsa aure.

18 Da ta zo wurinsa, ya zuga ta ta roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”

19 Ta kuwa ce masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ina roƙonka ka ba ni maɓuɓɓugar ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugar tuddai da na kwari.

Biranen Kabilar Yahuza

20 Wannan shi ne gādon jama’ar Yahuza bisa ga iyalansu.

21 Biranen jama’ar Yahuza da suke can kudu sosai wajen iyakar Edom, su ne Kabzeyel, da Eder, da Yagur,

22 da Kina, da Dimona, da Adada,

23 da Kedesh, da Hazor, da Yitnan,

24 da Zif, da Telem, da Beyalot,

25 da Hazor-hadatta, da Kiriyot-hesruna, wato Hazor,

26 da Amam, da Shema, da Molada,

27 da Hazar-gadda, da Heshmon, da Bet-felet,

28 da Hazar-shuwal, da Biyer-sheba, da Biziyotaya,

29 da Ba’ala, da Abarim, da Ezem,

30 da Eltola, da Kesil, da Horma,

31 da Ziklag, da Madmanna, da Sansanna,

32 da Labayot, da Shilhim, da Ayin, da Rimmon. Birane ashirin da tara ke nan da ƙauyukansu.

33 Na filayen kwarin kuwa, su ne Eshtawol, da Zora, da Ashna,

34 da Zanowa, da En-ganim, da Taffuwa, da Enayim,

35 da Yarmut, da Adullam, da Soko, da Azeka,

36 da Shayarim, da Aditayim, da Gedera, da Gederotayim. Birane goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.

37 Da kuma Zenan, da Hadasha, da Migdal-gad,

38 da Dileyan, da Mizfa, da Yokteyel,

39 da Lakish, da Bozkat, da Eglon,

40 da Kabbon, da Lahmam, da Kitlish,

41 da Gederot, da Bet-dagon, da Na’ama, da Makkeda, birane goma sha shida ke nan da ƙauyukansu.

42 Da kuma Libna, da Eter, da Ashan,

43 da Yifta, da Ashna, da Nezib,

44 da Kaila, da Akzib, da Maresha, birane tara ke nan da ƙauyukansu.

45 Da kuma Ekron da garuruwanta da ƙauyukanta.

46 Daga Ekron zuwa tekun, da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.

47 Ashdod da garuruwanta da ƙauyukanta, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta zuwa rafin Masar da Bahar Rum da bakinta.

48 Birane na cikin ƙasar tuddai kuwa, su ne Shamir, da Yattir, da Soko,

49 da Danna, da Kiriyat-sanna, wato Debir,

50 da Anab, da Eshtemowa, da Anim,

51 da Goshen, da Holon, da Gilo. Birane goma sha ɗaya ke nan da ƙauyukansu.

52 Da kuma Arab, da Duma, da Eshan,

53 da Yanim, da Bet-taffuwa, da Afeka,

54 da Hunta, da Kiriyat-arba, wato Hebron, da Ziyor, birane tara ke nan da ƙauyukansu.

55 Da kuma Mawon, da Karmel, da Zif, da Yutta,

56 da Yezreyel, da Yokdeyam, da Zanowa,

57 da Kayin, da Gebeya, da Timna, birane goma ke nan da ƙauyukansu.

58 Halhul, da Bet-zur, da Gedor,

59 da Ma’arat, da Bet-anot da Eltekon, birane shida ke nan da ƙauyukansu.

60 Da kuma Kiriyat-ba’al, wato Kiriyat-yeyarim, da Rabba, birane biyu ke nan da ƙauyukansu.

61 Biranen da suke a jeji kuwa su ne Bet-araba, da Middin, da Sekaka,

62 da Nibshan, da Birnin Gishiri, da En-gedi, birane shida ke nan da ƙauyukansu.

63 Amma jama’ar Yahuza ba su iya korar Yebusiyawa waɗanda suke zaune a Urushalima ba, don haka Yebusiyawa suka yi zamansu da jama’ar Yahuza cikin Urushalima har wa yau.

Categories
JOSH

JOSH 16

Yankin Ƙasar da Aka Ba Ifraimu da Manassa

1 Rabon zuriyar Yusufu ya milla tun daga Urdun zuwa wajen Yariko, gabas da ruwan Yariko zuwa jejin. Ya haura daga Yariko zuwa ƙasar tuddai zuwa Betel.

2 Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa’an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa.

3 Sai ya gangara yamma zuwa karkarar Yafletiyawa har zuwa karkarar Bet-horon wadda take cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, sa’an nan ya gangara a teku.

4 A nan ne jama’ar Yusufu, wato Manassa da Ifraimu, suka sami nasu gādo.

5 Karkarar jama’ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu.

6 Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta’anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa.

7 Daga Yanowa sai ta gangara zuwa Atarot da Nayaran, ta kuma gegi Yariko, sa’an nan ta gangara a Urdun.

8 Daga Taffuwa, sai iyakar ta yi yamma zuwa rafin Kana, sa’an nan ta gangara a teku. Wannan shi ne gādon Ifraimawa bisa ga iyalansu,

9 tare da garuruwan da ƙauyukan da aka keɓe wa Ifraimawa daga cikin gādon jama’ar Manassa.

10 Amma ba su kori Kan’aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan’aniyawa ka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan’aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole.

Categories
JOSH

JOSH 17

1 Aka ba kabilar Manassa, ɗan farin Yusufu, nata rabon gādo. Makir ɗan farin Manassa, uban Gileyad, aka ba shi Gileyad da Bashan domin shi jarumi ne.

2 Aka kuma raba wa sauran mutanen kabilar Manassa nasu rabon gādo bisa ga iyalansu, wato Abiyezer, da Helek, da Asriyel, da Shekem, da Hefer, da Shemida. Waɗannan su ne ‘ya’yan Manassa, maza, bisa ga iyalansu.

3 Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa ba shi da ‘ya’ya maza, sai dai mata. Sunayensu ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

4 Suka zo wurin Ele’azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da ‘yan’uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da ‘yan’uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji.

5 Saboda haka kuwa Manassa ya sami kashi goma banda ƙasar Gileyad da Bashan da yake hayin gabashin Urdun,

6 domin jikokin Manassa mata sun sami gādo tare da jikokinsa maza. Aka ba sauran mutanen kabilar Manassa ƙasar Gileyad.

7 Yankin ƙasar Manassa ya kai daga Ashiru zuwa Mikmetat wadda take gabas da Shekem. Iyakar kuma ta miƙa kudu zuwa mazaunan En-taffuwa.

8 Ƙasar Taffuwa tana hannun mutanen Manassa, amma mutanen Ifraimu ne suke da garin Taffuwa wanda yake iyakar yankin Manassa.

9 Iyakar kuma ta gangara zuwa rafin Kana. Waɗannan birane da suke kudancin rafin, na Ifraimu ne, ko da yake suna cikin biranen Manassa. Iyakar Manassa kuwa ta bi gefen arewacin rafin ta gangara a Bahar Rum.

10 Ƙasar wajen kudu ta Ifraimu ce, ta wajen arewa kuwa ta Manassa. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Mutanen Ashiru suna wajen arewa, mutanen Issaka kuwa wajen gabas.

11 A yankin ƙasar Issaka da na Ashiru, Manassa yana da waɗannan wurare, Bet-sheyan da ƙauyukanta, da Ibleyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Endor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Magiddo da ƙauyukanta, da sulusin Nafat.

12 Amma mutanen Manassa ba su iya su mallaki waɗannan birane ba, don haka Kan’aniyawa suka yi zamansu a wuraren.

13 Amma sa’ad da Isra’ilawa suka yi ƙarfi sai suka tilasta su su yi musu aikin dole, amma ba su iya korarsu ba.

14 Kabilan Yusufu suka ce wa Joshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo guda ɗaya? Ga shi kuwa, muna da jama’a mai yawa, gama Ubangiji ya sa mana albarka.”

15 Joshuwa kuwa ya amsa musu, ya ce, “Idan ku babbar jama’a ce, har ƙasar tuddai ta Ifraimu ta kāsa muku, to, sai ku shiga jeji ku sheme wa kanku wuri a ƙasar Ferizziyawa da ta Refayawa.”

16 Sai mutanen kabilan Yusufu suka ce, “Ƙasar tuddai ba ta ishe mu ba, ga kuma Kan’aniyawa da suke zaune a filin, da waɗanda suke a Bet-sheyan da ƙauyukanta, da waɗanda suke cikin Kwarin Yezreyel suna da karusan ƙarfe.”

17 Joshuwa kuma ya ce wa jama’ar gidan Yusufu, wato kabilar Ifraimu da ta Manassa, “Ku babbar jama’a ce, ga shi kuma, kuna da ƙarfi, ba kashi ɗaya kaɗai za ku samu ba,

18 amma ƙasar tuddai kuma za ta zama taku, ko da yake jeji ne. Sai ku sheme, ku mallaka duka. Gama za ku kori Kan’aniyawa, ko da yake su ƙarfafa ne, suna kuma da karusan ƙarfe.”

Categories
JOSH

JOSH 18

Rarraba Ƙasa a Shilo

1 Da jama’ar Isra’ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.

2 Har yanzu akwai sauran kabila bakwai na Isra’ila waɗanda ba su sami gādonsu ba tukuna.

3 Sai Joshuwa ya ce wa jama’ar Isra’ila, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku?

4 Ku ba ni mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su auna ƙasar yadda za a raba ta gādo, sa’an nan su komo wurina.

5 Sai su raba ƙasar kashi bakwai. Kabilar Yahuza za ta ci gaba da zama a yankin ƙasarta a wajen kudu, mutanen gidan Yusufu kuwa su zauna a yankin ƙasarsu a wajen arewa.

6 Ku auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sa’an nan ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuwa zan jefa muku kuri’a a gaban Ubangiji Allahnmu.

7 Lawiyawa ba su da rabo tare da ku gama aikin Ubangiji shi ne rabonsu, da rabin ta Manassa sun riga sun sami nasu rabo wanda Musa, bawan Ubangiji, ya ba su a hayin gabashin Urdun.”

8 Joshuwa ya umarci mutanen da za su tafi su auna ƙasar, ya ce, “Ku shiga cikin ƙasar duka, ku auna sa’an nan ku komo wurina, ni kuwa zan jefa muku kuri’a a gaban Ubangiji a nan Shilo.”

9 Sai mutanen suka tafi, suka ratsa ƙasar tudu da ta gangare, suka auna ƙasar, suka raba ta kashi bakwai, suka lasafta garuruwan da suke ciki, sa’an nan suka koma wurin Joshuwa a Shilo.

10 Joshuwa kuwa ya jefa musu kuri’a a gaban Ubangiji a Shilo. Ta haka ya rarraba ƙasar ga jama’ar Isra’ila, kowa ya sami rabonsa.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Biliyaminu

11 Kuri’ar kabilar Biliyaminu bisa ga iyalanta ta fito. Yankin ƙasar da ya faɗo mata ke nan, ya zama a tsakanin yankin ƙasar kabilar Yahuza da na jama’ar Yusufu.

12 A wajen arewa iyakar ta tashi daga Urdun, ta bi ta tsaunin da yake arewa da Yariko, ta kuma haura tudu wajen yamma, har zuwa hamadar Bet-awen inda ta ƙare.

13 Daga can iyakar ta yi kudu, ta nufi cibiyar Luz, wato Betel, ta gangara zuwa Atarot-addar a bisa dutsen da yake kudu da Bet-horon ta kwari.

14 Daga nan iyakar ta nausa ta nufi yammacin kudancin dutse da yake kudu, daura da Bet-horon, sa’an nan ta tsaya a Kiriyat-ba’al, wato Kiriyat-yeyarim, birnin Yahuza. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

15 A wajen kudu kuwa iyakar ta fara daga karkarar Kiriyat-yeyarim, daga can ta miƙa zuwa Efron a maɓuɓɓugar ruwan Neftowa.

16 Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel.

17 Sai ta nausa ta yi wajen arewa zuwa En-shemesh, sa’an nan ta tafi Gelilot wanda yake daura da hawan Adummim. Daga nan ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ra’ubainu.

18 Sai ta wuce ta yi arewa daura da gefen Bet-araba, daga nan ta gangara zuwa Araba.

19 Ta kuma zarce zuwa arewa daura da gefen Bet-hogla, ta tsaya a arewacin gaɓar Tekun Gishiri a ƙarshen Urdun wajen kudu.

20 Kogin Urdun shi ne iyakar a wajen gabas. Waɗannan su ne iyakokin yankin ƙasar da iyalan kabilar Biliyaminu suka gāda.

21 Biranen iyalan kabilar Biliyaminu ke nan Yariko, da Bet-hogla, da Emekkeziz,

22 da Bet-araba, da Zemarayim, da Betel,

23 da Awwim, da Fara, da Ofra,

24 da Kefar-ammoni, da Ofni, da Geba. Birane goma sha biyu ke nan tare da ƙauyukansu.

25 Akwai kuma Gibeyon, da Rama, da Biyerot,

26 da Mizfa, da Kefira, da Moza,

27 da Rekem, da Irfeyel, da Tarala,

28 da Zela, da Elef, da Yebus, wato Urushalima, da Gebeya, da Kiriyat. Birane goma sha huɗu ke nan tare da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon mutanen Biliyaminu bisa ga iyalansu.

Categories
JOSH

JOSH 19

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Saminu

1 Kuri’a ta biyu ta faɗa kan kabilar Saminu bisa ga iyalanta. Nasu rabon gādon yana tsakiyar rabon gādon kabilar Yahuza.

2 Waɗannan su ne wuraren da suka gāda, Biyer-sheba, da Sheba, da Molada,

3 da Hazar-shuwal, da Bilha, da Ezem,

4 da Eltola, da Betul, da Horma,

5 da Ziklag, da Bet-markabot, da Hazar-susa,

6 da Bet-lebawot, da Sharuhen. Garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.

7 Akwai kuma Ayin, da Rimmon, da Eter, da Ashan. Garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,

8 da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da waɗannan garuruwa tun daga Ba’alat-biyer, wato Ramot ta Negeb. Wannan shi ne rabon gādon iyalan kabilar Saminu.

9 Gādon kabilar Saminu yana cikin yankin ƙasar rabon kabilar Yahuza domin rabon kabilar Yahuza ya yi mata yawa, don haka kabilar Saminu ta sami gādo daga cikin tsakiyar gādon kabilar Yahuza.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Zabaluna

10 Kuri’a ta uku ta faɗa a kan kabilar Zabaluna bisa ga iyalanta. Yankin ƙasar gādonsu ya kai har Sarid.

11 Iyakar ta hau wajen yamma zuwa Marala, ta kai Dabbeshet da rafin da yake gabas da Yakneyam.

12 Daga Sarid, ta nufi wajen gabas zuwa iyakar Kislotabar, sa’an nan ta bi ta Daberat da Yafiya.

13 Daga can ta miƙa wajen gabas zuwa Gat-hefer da Et-kazin, har zuwa Rimmon inda ta nausa zuwa Neya.

14 Daga wajen arewa iyakar ta juya zuwa Hannaton, sa’an nan ta faɗa a kwarin Iftahel.

15 Waɗannan garuruwa, da Kattat, da Nahalal, da Shimron, da Idala, da Baitalami, suna cikin garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar kabilar Zabaluna.

16 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin gādon mutanen Zabaluna bisa ga iyalansu.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Issaka

17 Kuri’a ta huɗu ta faɗo a kan kabilar Issaka bisa ga iyalanta.

18 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar su ne, Yezreyel, da Kesullot, da Shunem,

19 da Hafarayim, da Shiyon, da Anaharat,

20 da Rabbit, da Kishiyon, da Ebez,

21 da Remet da En-ganim, da En-hadda, da Bet-fazzez.

22 Iyakar kuma ta bi ta Tabor, da Shahazuma, da Bet-shemesh. Sa’an nan ta gangara a Kogin Urdun. Akwai garuruwa goma sha shida da ƙauyukansu.

23 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke a yankin ƙasar da kabilar Issaka ta gāda bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Ashiru

24 Kuri’a ta biyar ta fāɗo a kan kabilar Ashiru bisa ga iyalanta.

25 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar, su ne Helkat, da Hali, da Beten, da Akshaf,

26 da Alammelek, da Amad, da Mishal. A wajen yamma, iyakar ta bi ta Karmel da Shihor-libnat.

27 Daga nan sai ta nausa wajen gabas, ta bi ta Bet-dagon, da Zabaluna, da kwarin Iftahel a wajen arewa zuwa Bet-emek da Nayil. Ta yi gaba a wajen arewa zuwa Kabul,

28 da Hebron, da Rehob, da Hammon, da Kana, har ta bi ta Sidon Babba.

29 Daga can ta nausa zuwa Rama, ta bi ta garun birnin Taya, sai kuma ta nausa zuwa Hosa, sa’an nan ta gangara Bahar Rum, wajen Mahalab, da Akzib,

30 da Umma, da Afek, da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.

31 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar da kabilar Ashiru ta gāda bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Naftali

32 Kuri’a ta shida ta faɗo a kan kabilar Naftali bisa ga iyalanta.

33 Tasu iyaka, ta miƙa daga Helef, daga itacen oak da yake cikin Za’anannim, da Adami-nekeb, da Yabneyel har zuwa Lakkum, sa’an nan ta tsaya a Kogin Urdun.

34 Iyakar kuma ta juya wajen kudu zuwa Aznot-tabor, daga can ta miƙa zuwa Hukkok, sa’an nan ta kai Zabaluna wajen kudu, da Ashiru wajen yamma, da Yahuza wajen gabas wajen Urdun.

35 Garuruwan da yake da garu su ne, Ziddim, da Zer, da Hammat, da Rakkat, da Kinneret,

36 da Adama, da Rama, da Hazor,

37 da Kedesh, da Edirai, da En-hazor,

38 da Iron, da Migdal-el, da Horem, da Bet-anat, da Bet-shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.

39 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon gādon kabilar Naftali da iyalanta.

Yankin Ƙasar da Aka Ba Kabilar Dan

40 Kuri’a ta bakwai ta faɗo a kan kabilar Dan bisa ga iyalanta.

41 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar gādonta ke nan, da Zora, da Eshtawol, da Ir-shemesh,

42 da Shalim, da Ayalon, da Itla,

43 da Elon, da Timna, da Ekron,

44 da Elteki, da Gebbeton, da Ba’alat,

45 da Yahud, da Bene-berak, da Gat-rimmon,

46 da Meyarkon, da Rakkon, tare da karkarar da take gefen Yaffa.

47 Sa’ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan.

48 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan bisa ga iyalanta.

Yankin Ƙasar da aka Ba Joshuwa

49 Sa’ad da mutanen Isra’ila suka gama rarraba gādon ƙasar, suka ba Joshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikin nasu.

50 Bisa ga umarnin Ubangiji, suka ba shi garin da ya roƙa, wato Timnatsera a ƙasar tudu ta Ifraimu. Ya sāke gina garin, ya kuwa zauna a ciki.

51 Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Ele’azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin kakannin gidajen kabilan jama’ar Isra’ila, suka rarraba ta hanyar jefa kuri’a a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada a Shilo. Ta haka suka gama rarraba ƙasar.

Categories
JOSH

JOSH 20

An Keɓe Biranen Mafaka

1 Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa,

2 “Ka faɗa wa jama’ar Isra’ila, su keɓe biranen mafaka waɗanda na faɗa wa Musa ya faɗa muku.

3 Domin idan wani mutum ya yi kisankai ba da niyya ba, ba kuma da saninsa ba, sai ya tsere zuwa can. Biranen za su zama muku mafaka daga mai bin hakkin jini.

4 Wanda ya yi kisankan sai ya tsere zuwa ɗaya daga cikin biranen, ya tsaya a bakin ƙofar birnin, ya bayyana wa dattawan garin abin da ya same shi. In sun ji, sai su shigar da shi a birnin, su ba shi wurin zama, ya zauna tare da su.

5 Idan mai bin hakkin jinin ya bi shi, ba za su ba shi wanda ya yi kisankan ba, domin bai kashe maƙwabcinsa da gangan ba, ba kuma ƙiyayya a tsakaninsu dā ma.

6 Zai yi zamansa a birnin har lokacin da aka gabatar da shi gaban dattawa don shari’a, sai kuma bayan rasuwar babban firist na lokacin, sa’an nan wanda ya yi kisankan zai iya komawa garinsu da gidansa daga inda ya tsere.”

7 Saboda haka suka keɓe Kedesh ta Galili a ƙasar tuddai ta Naftali, da Shekem ta ƙasar tuddai ta Ifraimu, da Kiriyat-arba, wato Hebron, ta ƙasar tuddai ta Yahuza.

8 A hayin Urdun, gabas da Yariko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ra’ubainu, da Ramot cikin Gileyad ta kabilar Gad, da Golan cikin Bashan ta kabilar Manassa.

9 Waɗannan su ne biranen mafaka da aka keɓe domin dukan Isra’ilawa, da baƙin da suke baƙuntaka cikinsu. Don duk wanda ya yi kisankai ba da niyya ba zai iya tserewa zuwa can don kada ya mutu ta hannun mai bin hakkin jini. Zai zauna a can har lokacin da za a gabatar da shi a gaban taron jama’a.