Categories
JOSH

JOSH 21

Biranen da Aka Ba Lawiyawa

1 Shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa suka zo wurin Ele’azara, firist, da wurin Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan jama’ar Isra’ila.

2 Suka yi magana da su a Shilo a ƙasar Kan’ana, suka ce musu, “Ubangiji ya umarta ta bakin Musa a ba mu biranen zama da wuraren kiwo domin dabbobinmu.”

3 Bisa ga umarnin Ubangiji, sai jama’ar Isra’ila suka ba Lawiyawa waɗannan birane da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.

4 Kuri’a ta faɗo a kan iyalan Kohatawa. Sai Lawiyawa na zuriyar Haruna firist suka karɓi birane goma sha uku daga kabilar Yahuza, da kabilar Saminu, da kabilar Biliyaminu.

5 Sauran Kohatawa suka karɓi birane goma daga iyalan kabilar Ifraimu, da kabilar Dan, da rabin kabilar Manassa.

6 Gershonawa kuwa suka karɓi birane goma sha uku ta hanyar jefa kuri’a daga iyalan kabilar Issaka, da kabilar Ashiru, da kabilar Naftali, da rabin kabilar Manassa a Bashan.

7 Sai Merariyawa bisa ga iyalansu suka karɓi birane goma sha biyu daga kabilar Ra’ubainu, da ta Gad, da ta Zabaluna.

8 Waɗannan birane da wuraren kiwo nasu su ne jama’ar Isra’ila suka ba Lawiyawa ta hanyar jefa kuri’a kamar yadda Ubangiji ya umarta ta bakin Musa.

9 Daga cikin kabilar Yahuza da kabilar Saminu aka ba zuriyar Haruna waɗannan birane da aka ambata.

10 Zuriyar Haruna tana cikin iyalan Kohatawa waɗanda suke Lawiyawa. Kuri’arsu ce ta fito da farko.

11 Sai aka ba su Kiriyat-arba, wato Hebron, a ƙasar tuddai ta Yahuza tare da wuraren kiwo nata da suke kewaye. Arba shi ne mahaifin Anak.

12 Amma saurukan birnin da ƙauyukansu an ba Kalibu, ɗan Yefunne, su zama mallakarsa.

13 Biranen da aka ba zuriyar Haruna firist ke nan, Hebron tare da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Libna tare da wuraren kiwo nata,

14 da Yattir tare da wuraren kiwo nata, da Eshtemowa tare da wuraren kiwo nata,

15 da Holon tare da wuraren kiwo nata, da Debir tare da wuraren kiwo nata,

16 da Ayin tare da wuraren kiwo nata, da Yutta tare da wuraren kiwo nata, da Bet-shemesh tare da wuraren kiwo nata. Birane tara ke nan daga cikin kabilun nan biyu.

17 Daga cikin kabilar Biliyaminu aka ba su birane huɗu, wato Gibeyon tare da wuraren kiwo nata, da Geba tare da wuraren kiwo nata,

18 da Anatot tare da wuraren kiwo nata, da Almon tare da wuraren kiwo nata.

19 Dukan biranen da aka ba firistoci, wato zuriyar Haruna, guda goma sha uku ne tare da wuraren kiwo nasu.

20-22 Aka ba sauran Kohatiyawa na iyalan Lawiyawa birane huɗu daga kabilar Ifraimu. Aka ba su Shekem tare da wuraren kiwo nata, a ƙasar tuddai ta Ifraimu, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Gezer tare da wuraren kiwo nata, da Yokmeyam tare da wuraren kiwo nata, da Bet-horon tare da wuraren kiwo nata.

23-24 Aka kuma ba su birane huɗu daga kabilar Dan, wato Elteki tare da wuraren kiwo nata, da Gibbeton tare da wuraren kiwo nata, da Ayalon tare da wuraren kiwo nata, da Gat-rimmon tare da wuraren kiwo nata.

25 Daga cikin rabin kabilar Manassa, aka ba su birane biyu, su ne Ta’anak tare da wuraren kiwo nata, da Bileyam tare da wuraren kiwo nata.

26 Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba sauran Kohatawa na iyalan Lawiyawa guda goma ne.

27 Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata.

28-29 Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin kabilar Issaka, biranen su ne, Kishiyon da wuraren kiwo nata, da Daberat da wuraren kiwo nata, da Yarmut da wuraren kiwo nata, da Enganim da wuraren kiwo nata.

30-31 Daga cikin rabon kabilar Ashiru aka ba su birane huɗu, su ne Mishal da wuraren kiwo nata, da Abdon da wuraren kiwo nata, da Helkat da wuraren kiwo nata, da Rehob da wuraren kiwo nata.

32 Daga cikin rabon kabilar Naftali aka ba su birane uku, su ne, Kedesh ta Galili da wuraren kiwo nata, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Hammon da wuraren kiwo nata, da Kartan da wuraren kiwo nata.

33 Dukan birane da wuraren kiwo nasu da aka ba iyalan Gershonawa guda goma sha uku ne.

34-35 Aka ba iyalan Merari na cikin Lawiyawa birane huɗu daga cikin rabon kabilar Zabaluna. Biranen ke nan, Yakneyam da wuraren kiwo nata, da Karta da wuraren kiwo nata, da Rimmon da wuraren kiwo nata, da Nahalal da wuraren kiwo nata.

36-37 Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin rabon kabilar Ra’ubainu. Biranen ke nan, Bezer da wuraren kiwo nata, da Yahaza da wuraren kiwo nata da Kedemot da wuraren kiwo nata, da Mefayat da wuraren kiwo nata.,

38-39 Daga cikin kabilar Gad aka ba su birane huɗu, su ne Ramot ta Gileyad da wuraren kiwo nata, wannan birnin mafaka ne domin wanda ya yi kisankai, da Mahanayim da wuraren kiwo nata, da Heshbon da wuraren kiwo nata, da Yazar da wuraren kiwo nata.

40 Dukan biranen da aka ba iyalan Merari na Lawiyawa guda goma sha biyu ne.

41 Jimillar biranen da wuraren kiwo nasu da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama’ar Isra’ila guda arba’in da takwas ne.

42 Kowane birni yana da wuraren kiwo nasa kewaye da shi.

Isra’ilawa Sun Mallaki Ƙasar

43 Haka kuwa Ubangiji ya ba Isra’ilawa dukan ƙasar da ya rantse zai ba kakanninsu. Suka ci ƙasar, suka zauna a ciki.

44 Ubangiji kuma ya ba da hutawa ko’ina kamar yadda ya rantse wa kakanninsu. Babu wani daga cikin abokan gābansu da ya iya ta da kai da su, gama Ubangiji ya ba da abokan gābansu duka a hannunsu.

45 Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alheri da ya yi wa gidan Isra’ila.

Categories
JOSH

JOSH 22

Bagade a Bakin Urdun

1 Sa’an nan Joshuwa ya kira mutanen kabilar Ra’ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa.

2 Ya ce musu, “Kun aikata dukan abin da Musa, bawan Ubangiji, ya umarce ku, kun kuma yi biyayya da dukan abin da na umarce ku.

3 Ba ku yar da ‘yan’uwanku dukan waɗannan yawan kwanaki, har wa yau ba. Amma kuka kiyaye umarnin Ubangiji Allahnku sosai.

4 Yanzu Ubangiji Allahnku ya ba ‘yan’uwanku hutawa kamar yadda ya faɗa, yanzu dai sai ku koma, ku tafi gida a ƙasarku ta gādo wadda Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun.

5 Sai dai ku kiyaye umarnai da dokokin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa, ku kiyaye dokokinsa, ku manne masa, ku bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku.”

6 To, Joshuwa ya sa musu albarka, sa’an nan ya sallame su, suka koma gida.

7 Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da ‘yan’uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa’ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka,

8 ya ce musu, “Ku koma gidajenku da wadata mai yawa, da dabbobi masu yawa, da azurfa, da zinariya, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da tufafi masu yawa. Ku raba da ‘yan’uwanku ganimar da kuka kwaso daga abokan gabanku.”

9 Sai Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka koma gida. Suka yi bankwana da sauran ‘yan’uwansu Isra’ilawa a Shilo ta ƙasar Kan’ana. Suka koma ƙasar Gileyad, ƙasar da suka gāda bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Musa.

10 Sa’ad da suka kai Gelilot, kusa da Urdun, a gefen da yake wajen ƙasar Kan’ana, suka gina babban bagade a wurin.

11 Sauran Isra’ilawa kuwa suka ji labari cewa, “Ga shi, Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa sun gina bagade a Gelilot a kan iyakar ƙasar Kan’ana, a wajen hayinsu na yammacin Urdun.”

12 Da Isra’ilawa suka ji haka sai dukansu suka tattaru a Shilo don su kai musu yaƙi.

13 Mutanen Isra’ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele’azara, firist, wurin Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad.

14 Shugabanni goma suka tafi tare da shi, shugaba ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila. Kowane ɗayansu shugaba ne a danginsa a kabilar Isra’ila.

15 Da suka zo wurin Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu,

16 “In ji dukan taron jama’ar Ubangiji, ‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra’ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?’ Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade.

17 Zunubin da aka yi a Feyor, ashe, bai ishe mu ba, har annoba ta wahalar da taron jama’ar Ubangiji? Ga shi, har yanzu ma ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba.

18 Za ku kuma daina bin Ubangiji ne yau? Idan kuka tayar masa yau, gobe zai yi fushi da dukan jama’ar Isra’ila.

19 Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji inda alfarwa ta sujada take, ku sami abin mallaka a tsakaninmu, amma kada ku tayar wa Ubangiji, ku kuma tayar mana ta wurin gina wa kanku wani bagade dabam da bagaden Allahnmu.

20 Lokacin da Akan, ɗan Zera, ya yi rashin aminci cikin abubuwan da aka haramta, ai, dukan Isra’ilawa aka hukunta. Ba shi kaɗai ya hallaka don zunubinsa ba.”

21 Sai Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka amsa wa shugabannin iyalan Isra’ilawa suka ce,

22 “Allah Maɗaukaki, Allah Ubangiji ya sani, bari Isra’ilawa kuma da kansu su sani. Idan tayarwa ce, ko kuwa mun yi wa Ubangiji rashin aminci ne, to, kada ku bar mu da rai yau.

23 Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana.

24 Saboda gudun gaba ne muka yi haka, domin kada wata rana ‘ya’yanku su ce wa ‘ya’yanmu, ‘Ba ruwanku da Ubangiji, Allah na Isra’ila.

25 Gama Ubangiji ya sa Kogin Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku Ra’ubainawa da Gadawa domin haka ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’ To, da haka ‘ya’yanku su hana ‘ya’yanmu yi wa Ubangiji sujada.

26 Don haka muka ce, ‘Bari mu gina bagade, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba,

27 amma domin ya zama shaida tsakaninmu da ku, da tsakanin zuriyarmu da taku, don mu ci gaba da bautar Ubangiji da hadayunmu na ƙonawa, da na sadaka, da na salama.’ ‘Ya’yanku kuma ba za su ce wa ‘ya’yanmu, ‘Ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’

28 Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, ‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.’

29 Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.”

30 Sa’ad da Finehas, firist, da shugabannin jama’a, wato shugabannin iyalan Isra’ila, suka ji maganar da Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka faɗa, suka ji daɗi a rai.

31 Sa’an nan Finehas, ɗan Ele’azara, firist, ya ce wa Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa, “Yau mun sani Ubangiji yana tare da mu domin ba ku ci amanar Ubangiji ba.”

32 Sa’an nan Finehas, ɗan Ele’azara, firist, da shugabannin suka komo daga wurin Ra’ubainawa da Gadawa a ƙasar Gileyad, zuwa ƙasar Kan’ana wurin mutanen Isra’ila, suka ba su rahoton abin da suka ji.

33 Mutanen Isra’ila suka ji daɗin rahoton da aka ba su, suka yabi Allah, ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su hallaka ƙasar da Ra’ubainawa da Gadawa suke zaune ba.

34 Ra’ubainawa da Gadawa suka sa wa bagaden suna Shaida, domin in ji su, “Shi shaida ne a tsakaninmu, cewa Ubangiji shi ne Allah.”

Categories
JOSH

JOSH 23

Joshuwa Ya Yi wa Jama’a Jawabi

1 An daɗe bayan da Ubangiji ya hutar da Isra’ilawa daga abokan gābansu waɗanda suke kewaye da su. Joshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa.

2 Sai Joshuwa ya kira Isra’ilawa duka, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, da jarumawansu, ya ce musu, “Yanzu na tsufa, shekaruna sun yi yawa,

3 kun dai ga abin da Ubangiji Allahnku ya yi da waɗannan al’ummai duka saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.

4 Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al’umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma.

5 Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Za ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku.

6 Domin haka sai ku yi ƙarfin hali ƙwarai, ku riƙe, ku aikata dukan abin da aka rubuta a littafin dokokin Musa, kada ku kauce dama ko hagu,

7 domin kada ku yi cuɗanya da sauran al’umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.

8 Amma ku manne wa Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi har wa yau.

9 Gama Ubangiji ya kori manyan al’ummai ƙarfafa daga gabanku, har wa yau ba mutumin da ya isa ya yi hamayya da ku.

10 Mutuminku guda zai runtumi mutum dubu nasu, tun da yake Ubangiji Allahnku ne yake yaƙi dominku, kamar yadda ya alkawarta muku.

11 Ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku.

12 Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al’umman nan da take tare da ku, har kuka yi aurayya da juna,

13 to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al’umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.

14 “A yanzu ina gaba da bin hanyar da kowa a duniya yakan bi, ku duka kuwa, a zukatanku da rayukanku, kun sani dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba.

15 Amma kamar yadda Ubangiji Allahnku ya cika alkawaran da ya yi muku, haka nan kuma Ubangiji zai aukar muku da masifu, har ya hallaka ku daga ƙasan nan mai albarka da Ubangiji Allahnku ya ba ku.

16 Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”

Categories
JOSH

JOSH 24

Jawabin Joshuwa na Bankwana a Shekem

1 Joshuwa kuma ya tara dukan kabilan Isra’ila a Shekem, ya kuma kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra’ila. Suka hallara a gaban Allah.

2 Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra’ila ya ce, ‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka.

3 Sai na ɗauki kakanku Ibrahim daga wancan hayin Kogi, na kawo shi ƙasar Kan’ana, na sa zuriyarsa ta yawaita. Na ba shi Ishaku.

4 Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da ‘ya’yansa suka gangara zuwa Masar.

5 Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku.

6 Na kuwa fitar da kakanninku daga Masar. Da suka zo Bahar Maliya, sai Masarawa suka fafari kakanninku da karusai da mahayan dawakai har zuwa teku.

7 A sa’ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa.

8 Sa’an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu.

9 Haka kuma Balak, ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya tashi ya yi yaƙi da Isra’ila, har ya gayyaci Bal’amu, ɗan Beyor, ya zo ya la’anta ku.

10 Amma ban saurari Bal’amu ba, saboda haka ya sa muku albarka, ta haka na cece ku daga hannunsa.

11 Da kuka haye Urdun, kuka zo Yariko, mutanen Yariko kuwa suka yi yaƙi da ku, haka kuma Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Kan’aniyawa da Hittiyawa, da Girgashiyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, amma na ba da su a gare ku.

12 Na kuma aiki zirnako a gabanku, waɗanda suka kori sarakunan nan biyu na Amoriyawa daga gabanku. Ba takobinku, ko bakanku ya kore su ba.

13 Na ba ku ƙasar da ba ku yi wahala a kanta ba, da biranen da ba ku gina ba, ga shi, kuna zaune a ciki, kuna kuma cin ‘ya’yan inabi, da na zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba.’

14 “To fa, ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa da sahihanci da aminci, ku yi watsi da gumakan da kakanninku suka bauta wa a hayin Kogin Yufiretis, da cikin Masar.

15 Idan ba ku da nufi ku bauta wa Ubangiji, to, yau sai ku zaɓi wanda za ku bauta wa, ko gumakan da kakanninku suka bauta wa a wajajen hayin Kogin Yufiretis, ko kuma gumakan Amoriyawa waɗanda kuke zaune a ƙasarsu, amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”

16 Jama’a kuwa suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji, har a ce mu bauta wa gumaka.

17 Gama Ubangiji Allahnmu ne ya fisshe mu da kakanninmu daga ƙasar Masar, a gidan bauta. Shi ne wanda ya aikata manyan alamu a idonmu, ya kuma kiyaye mu a dukan hanyar da muka bi, da cikin dukan al’umman da muka ratsa.

18 Ubangiji kuwa ya kore mana dukan Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar, domin haka za mu bauta wa Ubangiji, gama shi ne Allahnmu.”

19 Amma Joshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, gama shi Allah mai tsarki ne, mai kishi kuma, ba kuwa zai gafarta laifofinku da zunubanku ba.

20 Idan kun rabu da Ubangiji, kun bauta wa gumaka, sai ya juyo ya wulakanta ku, ya hallaka ku, ko da yake ya riga ya nuna muku alheri.”

21 Jama’a kuwa suka ce wa Joshuwa, “A’a, mu dai za mu bauta wa Ubangiji ne.”

22 Joshuwa kuma ya ce wa mutanen, “Ku ne shaidun kanku da kanku, kun zaɓi Ubangiji don ku bauta masa.”

Sai suka ce, “I, mu ne shaidu.”

23 Joshuwa ya ce, “To, ku kawar da gumakan da suke cikinku, ku sa zuciyarku ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.”

24 Jama’a suka ce wa Joshuwa, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.”

25 A wannan rana, Joshuwa ya yi alkawari da jama’a a Shekem, ya kafa musu dokoki da ka’idodi.

26 Ya kuwa rubuta waɗannan kalmomi a littafin Shari’ar Ubangiji. Ya kuma ɗauki wani babban dutse, ya kafa a ƙarƙashin itacen oak a wuri mai tsarki na Ubangiji.

27 Sai ya ce wa jama’a, “Wannan dutse shi ne shaida a kanmu, gama ya ji dukan abin da Ubangiji ya faɗa mana, domin haka zai zama shaida a kanku, don kada ku yi wa Allahnku ƙarya.”

28 Joshuwa kuwa ya sallami jama’ar, kowane mutum ya koma wurin gādonsa.

Rasuwar Joshuwa da ta Ele’azara

29 Bayan waɗannan al’amura, sai Joshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya rasu yana da shekara ɗari da goma da haihuwa.

30 Suka binne shi a ƙasar gādonsa a Timnat-sera wadda take cikin karkarar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga’ash.

31 Isra’ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji a dukan zamanin Joshuwa, da dukan zamanin dattawan da suka wanzu bayansa, waɗanda suka san dukan ayyukan da Ubangiji ya aikata domin Isra’ilawa.

32 Kasusuwan Yusufu, waɗanda jama’ar Isra’ila suka kawo daga Masar, an binne su a Shekem a yankin ƙasar da Yakubu ya saya a bakin azurfa ɗari daga wurin ‘ya’yan Hamor mahaifin Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusufu.

33 Ele’azara, ɗan Haruna kuma ya rasu, aka binne shi a Gebeya a garin ɗansa, Finehas, wanda aka ba shi a ƙasar tuddai ta Ifraimu.